YAR NAJERIYA CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun gani na da shi na farko, zuciya ta bata kara zama lafiya ba, rayuwa ta bata kara komawa daidai ba har yau shekaru talatin a gaba. Ya jirkita rayuwa ta upside-down ta duk yadda yake so, ya hargitsa tunani na ya mayar da shi yadda yaga dama, ya zamo silar da na san cewa ZABIYA ma mutum ne kuma mai ‘yanci, amma kuma shigowar sa cikin rayuwar tawa ba farin-ciki ta haifar ba sai akasin sa. In ma da farin-cikin to takaitace ne na wani dan kayyadadden lokaci. He gave me love but the people around him gave me hatred.+
“What are you crying for Hasna’u?”
Ya tambaya cikin kulawa. Ban yi niyyar Magana ba amma sai naji bazan iya share shi ba, duk da na san ba abinda zai iya akan kawo min Inna ta. Ko gano min dalilin rashin zuwan ta.
“’Yan gidan ku basu zo bane?” Ya sake tambaya kafin in bashi waccan amsar. Ganewa da yayi cewa hankali na ba ya jikina sabida yunwar da ke sakadata. Ban san san da nace masa.
“Ai ni bani da ‘yan gida, Innace kawai take zuwa min kuma bata zo ba. Ba kuka nake yi ba hutawa nake yi Sir” .
“Baki da Wa ko Ya, kuma baki da kanne? You have no relatives? Baban ki fa?”
Muryarsa is husky mai zurfi da kauri ta ‘yan boko mai ratsawa har cikin zuciyar mutum. Murya raunane nace, “tun ina ciki Babana ya rasu, ni kadai ce a wurin Inna ta”.1
Sai ya ce “to dan jira ni ina zuwa ko?”
Kafin in ce komai ya juya cikin takun sassarfa ya bar wajen. Bai jima ba ya dawo da farar leda a hannun sa ya mika min, sannan yace.
“Zan turo kanwata Nusaiba ta kawo miki abinci, ita muka zo wa visiting. Though i’m working here. Na hango ki anan na dauka kuka kike yi, don na san ki tun da jimawa a clinic”. Hannu biyu na sa na karba, tare da cewa.
“Thank you so much Sir”.
Ya taka a sannu ya bar wajen, amma kamshin kakkarfan masculine turaren sa bai bar shiga hanci na ba. Na bishi da kallo ina kiyasi, a very soft-hearted gentleman indeed! Har sunana ya sani, to ta ina? Sai na tuna da sanda na je clinic an tambayi sunana kuma an rubuta a folder.
Na maida duba na ga ledar da ya bani, wadda sanyin abinda ke ciki ke ta taba cinya ta, na fiddo gorar dake ciki yoghurt ne mai sanyi kuma mai girma, sai ruwan FARO mara san yi. Har karkashin zuciyata nagode masa, na kuma yi masa addu’ar alkhairi. Ashe har yanzu akwai sauran mutane masu son taimako saboda Allah?
“Nusaiba zuba abinci ki kaima waccan yarinyar ta karkashin bishiya?”
Kyakkyawar budurwar ‘yar hutu wadda aka kira Nusaiba, da ganin ta ka san she’s born from a silver spoon, ta juya tana kallon inda Yayan nata ya nuna mata, da sauri ta juyo ta dube shi cikin mamaki. “Waccan zabiyar?” Har tana kwalalo ido waje. Ya kalle ta da mamaki “ZABIYA ba mutum bane?” Sai Maman su ta dago daga kan waya da take dannawa ta dube su tana tambaya.
“Menene wai? Ya kamata ku tashi mu tafi rana ta yi” tace da ‘dan nata dake tsaye, amma duk hankalin sa yana kan Hasna’u. Nusaiba ta ce “Mama wai Yaya ne yace in kaiwa zabiyar can abinci” Mama ta ce “Zabiya kuma? A kwanon wa za’a kaiwa zabiyar abinci ba dai nawa ba?” Nusaiba ta yi dariya amma suna hada ido da Yayan nata ba shiri ta hadiye dariyar ta. Sabida mugun kallon da ya wurga mata.
Kawai sai gani suka yi ya sunkuya ya dauki plate yana zuba abincin da kan sa, ya loda soyayyen naman kaza da salad ya rufe yayi gaba abin sa.
Nusaiba ta ce “oh ni ‘ya su! Yaya SAHEEB akwai jaye-jaye”. Mama tace “in ya dawo da plates din ki zubar, dan kankanbar tsiya kawai da fin kowa iyawa.”
“Take this food Hasna’u”.
Da farko ban yi niyyar karba ba, amma intonation din cikin muryar sa ya nuna how much he cares ga son na ci abincin, da yadda ya damu da kadaicin da ya riske ni a ciki. Sannan Inna ta sha ce da ni ba’a maida hannun kyauta baya.
STORY CONTINUES BELOW
Hannu biyu na san a karba, a karo na biyu, tare da cewa “nagode Sir”
“Sunana Saheeb”.
“nagode Uncle, ni kuma sunana Hasna’u Dabo. Zan iya cewa kana da kirki Uncle?”
Murmushi yayi yace “maza ki ci ki kai musu plate din ki koma hostel, saura kadan lokaci ya cika, tunda Mamanki ta kai har yanzu bata zo ba to bazata zo ba, khair insha Allah”.
Daga haka ya bar wajen, ni kuma har ya kule na kasa dauke ido a kan sa. Ina mamakin kyakkyawar zuciya irin tasa.
Tunda nake ban taba cin abinci mai dadin wannan ba, kunne na har wani irin kaikayi yake yi, sannan ga nama zuqu-zuqu dana kasa tantance na kaza ne, ko na zabo ne ko na dawisu ne don dadin sa, nayi masa cin hani’an na dau plate din zuwa inda suke, har sun fara haramar tafiya. Suna nannade katon kilishin da suka zauna a kai.
“Kin gama Hasna’u?” Ya fada tun kafin na karaso gare su.
“Na gama Uncle kuma nagode sosai”. Na fada ina mika masa farantin, tare da kokarin russunawa don gaida Maman na su, sai ji nayi an tankwabar da shi ya fadi kasa.
“Me zamuyi farantin da zabiya ta ci abinci? Allah kayi mana tsari da mummunar haihuwa”.
Ban taba jin kalaman da suka doke ni irin wadannan ba, duk da ba yau aka fara goranta min halitta ba. Amma wannan matar babba ce ban zaci irin wadannan kalaman na rashin darajta dan adam daga bakin ta ba. Yawanci duk masu yi min gorin zabiya tsaarrraki na ne sai ko Hassan da Hussaini ‘ya’yan Kawu na. A nan makarantar dai dalibai ‘yan uwa na basa mu’amala da ni amma ba’a faya goranta min da kakkausan harshe irin haka ba, sai da ace “Hasna – Zabiya”.
Sai na juya sannu a likkafa hawaye cike da ido na na bar wurin. Ina jin shi yana “haba Mama! Haba don Allah Mama! Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi……”. Sauran maganganun ban bari sun shiga kunnuwa na ba domin takawa na yi da gudu na karasa hostel ina mai nadamar karbar abincin su. Saidai wannan karamci na wanda ya kira kan sa SAHEEB ya kasa dakushewa daga zuciya ta.
To haka ‘yan adam muke dama kowa da halin sa, sai ka ga da ya fi uwa hankali, kuma a hakan dai ita ce mahaifiyar sa.
Tun daga wannan ranar na soma daurawa kaina damuwa wadda a baya bana damun kai na. Ganewa da nayi cewa halitta ta abin kyama ne ga wasu bangaren al’umma. Damuwar da ba ni kadai ta soma yi wa illah ba, har da karatu na.
Performance dina yayi kasa sosai lokacin da aka hada continuous assessment, ni da nake daukar na daya sai gani kowa ya doke ni. Mr Samson shine class master din mu kuma shi ya fara noticing something is wrong a tare da ni, duk da cewa dama can ni din ba ma’abociyar walwala bace amma bana wasa da karatu. Ganin wannan fadowa kasa da nayi warwas, yasa Mr. Samson kira na staff-room.
“Hasna do you know that your marks are poor? ( Hasna kin san cewa makin ki bai yi kyau ba?) Kina da damuwa ne ko baki da lafiya ne?”
Idanuwa na sukayi rau-rau suna shirin zubar da hawaye. Mr. Samson ya dage sai ya ji abinda ke damu na, ni kuma na rasa me zan ce masa. Da zan iya, da na ce masa so nake ya samo min mai, wanda in na shafa zan koma baka (kirin). Ko mutane sa daina kyama ta da goranta min. The stigma attach to my disability is tormenting my heart.
To amma bazan iya gaya masa hakan ba kada ya ga rashin hankali na, (canza halittar Allah) sannan sauran malaman duka sun bada hankalin su a kan mu. Kowa so yake ya ji dalili na na komawa ba fuss a karatu. Sabida kowa da ya sanni ya san mai kokari ce kuma zaqaqura. Daga dalibai har malamai.
Sai kawai na samu baki na da cewa “bani da lafiya ne”. Don dai na samu Mr. Samson ya kyale ni. Domin kuwa bai da maganin abinda ke damu na.
Mr. Samson ya ce “Oh my dear, me ke damun ki?”
“Bana iya barci, zuciya ta tana min wani irin ciwo, ido na baya gani sosai, in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”.
Daya daga cikin malaman mu yace “you need to see a doctor Hasna, if possible za’a kai ki babban asibiti ki ga ophthalmologist”.
“Kafin nan za’a kai ki clinic ki ga Dr. Saheeb ku tattauna shi zai san likitan da ya dace ki gani, da asibitin da ya dace a kai ki a yi miki glasses”.
“SAHEEB! SAHEEB! A ina na taba jin wannan sunan???
“Haba shiyasa naga tana copying note ba daidai ba” inji Malam Lawal.
“Short-sightedness is part of their defect ai, da wuya ka ga zabiyan da ke da cikakken gani” inji Uncle Salisu.
STORY CONTINUES BELOW
Mr. Samson wanda malamin bautar kasa ne kuma kabila amma mai kirkin gaske da kula da daliban sa, shi ya sa ni a gaba ya kai ni har clinic din makaranta da kan sa.
Dan asibitin namu karami ne wanda yafi dacewa a kira shi dispensary. Su biyu kacal ke aiki a cikin sa shi da Nurse Saratu, sai kuma cleaner mai tsabtace asibitin.
Lokacin da muka shiga rubutu yake a cikin wata folder, nurse din kuma tana sakawa wata student karin ruwa, da alama ita ya gama dubawa.
Ko da Samson yayi masa sallama alamar ya zauna yayi masa da biron hannun sa ba tare da ya dago don ganin masu shigowa ba. Sai da ya gama rubutun sa tsaf, sannan ya dago ya dube mu.
Wasu irin idanuwa gare shi masu sheki da haske (sparkle) da suka sa na kasa dauke ido a kan sa ba tare da na san kallon sa nake ba. Ina jin Mr. Samson yana gaya masa matsaloli na tare da cewa “ina jin tausayin zabiyar nan, don Allah Saheeb ka duba ta sosai”.
Dago kan sa da kallo na da yayi da ‘sparkling eyes’ din sa, da kuma kallon haushin da ya watsawa Mr. Samson saida suka sa na kusa narkewa a kujerar gaban sa da na ke zaune sabida tsoron idanun sa masu matukar kwarjini.
“Ita ta ce ma ita abun tausayi ce? Don kawai tana exceptional child? You are to be encouraging her on her defect, not to weaken her. Words like yours are not encouraging at all”. Mr. Samson ya ce “I’m sorry Saheeb, Hasna is among my favourite students, dawowar ta kasa a aji ya dame ni, i don’t mean to devalue her.” Ya ce “ka je zan yi Magana da ita”.
Bayan fitar Mr. Samson cigaba yayi da rubutun sa, har sai da ya gama sannan ya aje biron ya dube ni, a cikin idanun sa concern ne da kulawa tsantsa.
“Hasna’u zan iya sanin abinda ke damun ki? Da yasa har malaman ki suka yi noticing cewa kin yi kasa sosai a karatu?”
Hawaye suka cicciko ido na, amma ban san meyasa ba na ji shi kam zan iya gaya masa hakikanin damuwa ta, na samu confidence a tare da shi tun lokacin da ya taimake ni ya bani abinci, ya kuma ce da mahaifiyar sa da ta kira ni ‘zabiya’ Ubangiji da ya halicci kowanne dan adam ya karrama shi”. Tun daga wancan lokacin na ji ina respecting din sa sannan ya dade da zama cikin rai na na kasa manta shi.
“Uncle Saheeb, so nake na koma baka (black), ina nufin kalar ‘yan Africa, don Allah idan akwai maganin da zai maida ni baka ka bani, ina da ciwo a cikin raina, babu inda yake min ciwo sai zuciya ta tun lokacin da na gane fari na abnormality ne ba kyau bane.
Uncle ko kawa banida ita a makarantar nan sabida ni zabiya ce…. A gidan mu su Hassan da Hussaini ba mai alaqa da ni sai mahaifiya ta, ban taba ganin mutum iri na ba a garin mu bakidaya, meyasa ni kadai ce zabiya? Kuma meyasa aka haife ni haka? Ji nake na tsani kai na bana ko son ganin fuska ta a mudubi”.
Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, ya dade bai manta yarinyar ba, sabida ita duk sanda ya ga zabiya sai ya waiwaya ko ita ce. Ya dora fuskar sa akan tafukan sa ya soma Magana cikin lallashi.
“who told you ke kadai ce zabiya a duniya? There are millions of Albinos around the world wadanda nasu yafi naki muni. In kin duba ke kam naki da sauki akan wadanda ko kuda ne ya sauka akan fuskar su sai yayi musu tabo.
Amma a haka suke rayuwar su cikin godiyar Allah. In kina so ki rayu kamar kowa, sai kin cire damuwar abnormality din ki daga ran ki, kin sa a ran ki cewa haka Allah ke son ganin ki, ki fidda maganganun mutane da damuwar su a ran ki domin ba duka keda imani akan Ubangiji ke halitta yadda yake so ba.
Me yasa kike son komawa baqa? Hasna you are special a yadda Allah ya yi ki. Wasu makafi ne, wasu kurame ne basu ji basu gani. Wasu kuwa duk an hada musu rashin ji da rashin gani. Wasu kuwa guragu ne basu da kafa. Su kuma su ce me Hasna? Sai su ce lallai sai sun bawa kan su abinda Allah bai ga damar basu ba? Hasna’u ki karfafa imanin ki, in ba haka ba zaki karawa kan ki lalura, kwakwalwar ki ta tabu da damuwa. Kin ga lalura ta karu kenan. Ni na gaya miki in kika cire wanan damuwar a ran ki, kika tsaya ki kayi karatu mai nagarta AN AMAZING HUSBAND na zuwa, wanda ba zai taba kallon abnormality din ki a matsayin nakasa ko abin kyama ba”.
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi nayi, murmushin da ban taba yin irin sa a tsayin rayuwa ta ba, babu wanda ya taba gaya min maganganu masu dadi da karfafawa irin na Uncle Saheeb. Koda kuwa ace ya fada ne kawai don ya faranta min, ba hakikanin gaskiyar kenan ba, na yi alkawarin bin duk abinda ya ce don tsira da lafiya ta, ba zan so kam in zamo mentally-retarded bayan zama albino ba kuma. Na alkawartawa rai na daga yau zan so kai na, zan koyawa kaina (self-love and self-determinatio) tare da rungumar kaddarar da Ubangiji ke so na da ita.
Maganar da ya ambata ta cewa amazing husband na zuwa idan na tsaya na yi karatu ita kadai nake da inkari (ja) a kan ta.
“Na ji duk abinda ka ce Uncle Saheeb, na kuma yi alkawarin bin duka shawarwarin ka, amma ka cire maganar amazing husband na riga na sa a raina har abada bazan yi aure ba. Karatun kadai zanyi ta yi har sai naga karshen sa (idan ana gani), amma bazan taba yin aure ba uncle, ban taba sanya raina ba”.
Uncle Saheeb, sai ya kura min ido, zuwa can ya ce “if that is your decision I must say it’s a WRONG decision (idan wannan shine hukuncin ki sai in ce gurbataccen hukunci ne). Wanda ke nuna still kina kalubalantar Ubangijinki da halittar da yayi miki.
Aure sunnah ne kuma Allah ya halatta shi akan kowanne musulmi mai lafiyar da zai iya aure. Don haka Hasna’u ki cire wannan doctrine din daga zuciyar ki, ki sa a ran ki duk sanda Allah ya kawo miki miji za ki yi aure. Uncle Samson ya gaya min kina da issue da idanun ki”.
“Eh Uncle bana ganin rubutu dai-dai akan allo, kuma in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”.
Uncle Saheeb ya dube ni cikin ido, duk da haka babu alamar tausayi na cikin kwayar idanun sa. Wani yanayi ne a cikin idanun sa wanda ya sha gaban in kwatanta shi da komai, sabida da ban taba gani a tare da kowa ba.
“Now, tell me about yourself, ‘yan wane gari ne ku kuma meyasa Innar ki bata zo visiting ba?”
“Rashin zuwan Inna ya kara min damuwa don bata taba fashin zuwan ba tun da na fara makaranta. Mu ‘yan garin nan ne amma asalin Babana dan Kabo ne”. Na gaya masa tarihi na bakidaya. (Uncle Saheeb tun daga wancan lokacin har zuwa yau bai daina tunanin hanyoyin inganta rayuwa ta ba).
“Go to your class Hasna’u. In an yi hutu tunda saura sati biyu zan zo har gidan ku na kai ki asibitin Murtala ki ga ophthalmologist. Insha Allah you will have a fitted glasses wanda zai taimaka miki.
“kin min alkawarin daga yau kin cire damuwar halitta daga ran ki ko? Zaki komawa karatun ki yadda kike yi a can baya? If possible har ma ya fi na baya?”
Ina murmushi na gyada masa kai.
“Madallah Hasna, now go to your class, an kusa kada kararrawar tashi”.
Na juya na fita daga clinic bayan nayi masa godiya mai yawa. Da gaske na ji zuciyata ta yi wasai daga kuncin data ke ciki. (Counselling pays).
******
Hasna’u na bada baya ya janyo system din sa, ya shiga internet sai ya samu kan sa da kasa cigaba da yin aikin da yake yi,sabida tunanin Hasna’u, ya hau yin kyakkyawan bincike a kan albinism. Ko akwai treatment din sa a likitance?
Abinda ya fara cin karo da shi shine “Albinism is inheried condition (wato gadon sa ake yi cikin jini) amma Hasna ta ce ita ba gada ta yi ba. Zai iya yiwuwa cikin ancesstors din ta wani ke da shi bata sani ba.
Binciken sa ya cigaba da gaya masa cewa;
“It happens beacause they have less MILANIN than usual in the body. Melanin gives skin, hair, and eyes their colour. Except for vision problem, most people with albinism are just as healthy as anyone else”. (Yana faruwa ne a sakamakon rashin melanin yadda ya kamata a cikin jikin dan adam. Melanin shine abinda ke baiwa fata, gashi da ido kalar su. In kika dauke matsalar raunin gani, yawancin zabiya lafiyayyu ne kamar kowa).
Sai ya koma tambayar menene MELANIN?
MELANIN is the pigment that is responsible for our beautiful variety of skin tones and shades, eye colours and hair colours.
Not only melanin provide pigmentation for human skin, hair and eyes, it also provides protection against the harmful effect of ultraviolet (UV) rays.
Sai ya koma binciken menene treatment din sa a likitance?
“Because albinism is a genetic disorder it cannot be cured, treatment focuses on getting proper eye care and monitoring skin for signs of abnormalities”. (Tunda ya kasance gadar sa ake cikin jini, to ba shi da magani, treatment dinsa daya ne kula da lafiyar ido yadda ya kamata da kula da fata koda zata samu sabon sauyi) Darmatologist and ophthalmologist sune professionals wadanda Zabiya ke gani akai-akai.
Saheeb, sai ya hada kai da tebirin sa, yana tunanin hanyar da zai bi ya tallafi rayuwar zabiya HASNA’U. Hasna’un da ya fahimci bata da wani cikakken gata bayan mahaifiyar ta, wadda itama bata da karfi.
Abu na farko daya tsayar cikin ran sa shine tsayawa lafiyar idanun ta da fatar ta for any abnormality sign, don kada ta rasa ganin ta gabadaya, ta hanyar kai ta ga kwararren ophthalmology Dr. Abubakar Turaki Abdullahi, sannan da zuwa ya binciko halin da Innar ta ke ciki, wanda ya hana ta zuwa ganin ta. Daya al’amarin dake sakadar ruhin sa yaki yake da shi ko ta halin kaka da karfin tsiya don bai ga ta ina yiwuwar sa zata kasance ba in ya tuna an ce “It’s a genetic disorder!”
-TAKORI