YAR SHUGABA CHAPTER 10

YAR SHUGABA 
CHAPTER 10
Wani wajen shak’atawa ta kaisu ba wancen na farko ba, sun samu k’asan wata bishiya suka zauna kan kujeru, ga table a tsakiya, an kawo musu drinks ne da ruwa, Basma ko kallon Yaya Aryan batayi ba kuma tak’i magana, jikin Yaya Aryan yayi sanyi sai ya kwantar da murya yace”Basma fushi kike dani?” kallo d’aya ta mishi a fak’aice sai ta kauda kai gefe, murmushi yayi yace “haba k’anwata ki daina fushi dani mana, bana son ganin b’acin ranki, burina in saki farin ciki har k’arshen rayuwana” d’agowa tayi suka had’a ido, idonunta fal da hawaye suna gabda zubowa, da sauri Yaya Aryan ya tara hannunsa a fuskanta domin hawayen ya sauka bisa tafin hannunsa, cikin wani irin murya wanda shi kanshi baisan yanada ita ba, mai dad’i da zak’i yace “Basma karki min asaran hawayenki ya kai ga zuba a k’asa, ba tare da na sharesu ba, ki yafe ma Yayanki, ba zai zake b’ata miki raiba” murmushi tayi na jin dad’i, saita runtse idonta hawayen suka sauka bisa hannunsa, Yaya Aryan ya koma ya zauna, suna kallon juna ya d’aga hannunsa zuwa bakinsa ya lashe digon hawayen ya shanye, Basma saita tafa masa rap rap rap, cike da farin ciki tace “wow, Yaya Aryan yau kawai na tabbatar da cewa ka d’aunke ni jinin jikinka kuma ‘yar uwanka” murmushi yayi yace “ke ce baki sani ba amma tun ranar da kika bani hak’uri na d’auke ki a haka, kawai dai na d’an nuna miki ni din Namiji ne” hararansa tayi na wasa tace “ohoo dama shiyasa ka ke basar dani domin kaga rauni na ko, amma ba komai tunda ka fahimci yanda na d’auke ka” dariya yayi yace “sosai na sani, Basma kin zama haske a rayuwana da Ahalina, sanadinki Umma da Deeja da Ni kaina muna farin ciki, kin mana abinda ban san dame zan biya ki ba face Allah ya baki miji nagari, ya kuma baki Aljannah” murmushi tayi najin dad’in abinda yace har cikin taranta, Abu d’aya ne taji ya mata wani iri lokacin da ta tuno da Yaya Shureym, tambayar kanta ta shiga yi,”yanzu inna yi aure shikenan Yaya Shureym ya rabani da Yaya Aryan kenan?” Nan danan taji zuciyarta ya mata wani iri, ganin ta lula duniyar tunani, sai Yaya Aryan ya matso da fuskansa ya hura mata iskan bakinsa, nan take ta dawo hayyacinta, sai duk suka zubawa juna ido, suna baiwa junansu wasu sak‘onnin cikin kwayar idonsu, suna karantar wajuna sirrin zuciyansu, sun d’auki tsawon minti biyar kana Yaya Aryan ya kashe mata ido d’aya, da sauri ta sunne kai k’asa alaman jin kunya, a gaskiya duk wanda ya gansu a wannan yanayin, babu abinda mutum zaice illa Aryan da Basma masoya ne. Yaya Aryan ya d’auko kujeransa ya dawo kusa da ita, da muryansa mai dad’i yace “k’anwata meyasa ba kya jin kunyar kallon kwayar ido na? ke ce mace ta farko da take iya kallon ido na harta karanta wasu sirri dake ciki, domin ido na na d’aya daga cikin abinda kewa mutane kwarjini” murmushi tayi kawai ba tace komai ba, ya cigaba da cewa “Amma na fahimci idanunmu sun fara sanin sirrin dake cikin juna, kema haka idonki yake kamar nawa” Basma sunkuyar da kai tayi k’asa, bata tab’a jin nauyi ko kunyar wani namiji ba sai akan Yaya Aryan, wasa take da yatsun hannunta, ta kasa motsi mai k’arfi, gaba d’aya tanajin ta a cikin sabon yanayi da bata tab’ajiba game da wani d’a namiji ba sai akan Yaya Aryan, a yanzu kunya da kwarjininsa ke tasiri a jikinta, Yaya Aryan ya kira sunanta yace “Basma kinyi shuru k0 yau ba kya jin tsokana ne, magana da kuma fad’a?” murmushi tayi tace “ai Kaine kake magana, tun d’azu kake wasu bayanai da ban fahimcesu ba” murmushi yayi yace “kina so ki sansu?” tace “eh ina so” yace “to d’ago fuskanki ki kalleni, zaki fahimci abinda nake nufi acikin ido na” ta d’auki minti d’aya kafin ta d’ago fuskanta, suka had’a ido ko wanne fuskansa da murmushi, sakonni suke zubawa zuciyoyinsu, ko wanne idonsa yayi tamkar mangyada aciki, bugun zuciyarsu yana buguwa a hankali. zan iya ce muku suna bugawa kusan a tare, idanun su yana k’eftawa a hankali tamkar ba zasu rufe ba, numfashinsu yana fita a hankali kamar basa cikin duniyarmu, sun d’auki tsawon minti bakwai, kana Basma ta yi ajiyar zuciya ta sun kuyar da kai, shima Yaya Aryan ajiyan zuciya yayi, cikin wani irin murya kamar yana rad’a yace, Basma kin fatimci abinda nake nufi yanzu?” murmushi tayi kawai ba tace komai ba. 
Wayar Basma ce tayi ringing, Yaya Shureym ne ya kirata, a wannan lokacin sai taji sam bataji dad’in kiran nasa ba, kamar ba zata d’aga ba, saita d’auka suka gaisa, yau hiran nasu sama-sama suka yi, hakanan taji bata son magana dashi, bayan ta gama ta kashe wayar juyowan da zatayi sai taga ba Yaya Aryan a gun, gabanta ne ya fad’i, ta fara tunanin ko ta b’ata masa raine akan d’aukar wayan, mik’ewa tayi ta hangoshi can yana wasa da ganyen wata bishiya, wurin ta k’arasa tace “Yaya Aryan” da sauri yajuyo idonsa ya kad’a ya d’anyi ja, kan ta kuma magana ya d’aura hannunsa bida leb’ensa yace 
“shiiii, kin gama wayan?” cikin yanayin rashin jin dad’i tace “eh Amma kayi hak’uri” murmushi yayi yace “hak’urin me zanyi, ai baki laifI ba, da mijinki kike waya fa to me zaisa raina ya b’aci” gabanta ne taji ya fadi dammm”, hakanan taji maganar da yayi bai mata dadI ba, tace “Yaya Aryan ba mijina bane fa kawai dai saurayina ne’ ‘murmushin yak’e yayi yace “Amma ai aure za kuyi” yana gama fad’an haka yayi gaba ya barta a tsaye, Basma ji tayi zuciyarta ya mata ba dad’i, hawaye ne ke son zubo mata, da sauri tabi bayansa tasha gabansa tace cikin shagwab’a. “Yaya hawayen zai zubo” dariya ta bashi Amma ya dake, yace me ya kawo hawaye, keda kika gama shan soyayya da mijinki” ai tuni hawayen ya soma zuba, sharr bata k’aunar Aryan 
na fad’an haka, matsawa yayi gab da ita cikin salon muryansa mai kashejiki yace 
“wlh karki kuskura hawayenki ya sauka k’asa, domin saina mugun sab’a mikl’, hawayan Basma mai daraja ne a gun yayanta Aryan.” Da sauri ya tara hannunsa biyu yace duk lokacin da kikejin kuka koda bama tare ki rik’e kukan, sai mun had’u kiyi shi akan hannu na, domin in maida shi cikina”. Murmushi tayi tace 
“tom na bari Amma saika daina cemin Yaya Shureym shine Mijina” dariya yayi sosai yace “dama a kan shi zaki min asaran hawayanki tom karki k’ara” yatsansa yasa ya lakuto hawayenta ya sanya a baki yasha, saida ya raba fuskan da hawaye kana yace “muje gida”. 
Sun kama hanyan zuwa gida, Basma tace 
“Yaya Aryan wlh da za’a barni dana kwana a gidan ku” Murmushi yayi yace 
“saboda me zaki kwana mana a gida?” 
“saboda kawai in tashi inga Yaya Aryan, in nayi kuka ya shanye min hawayena” dariya yayi sosai yace “tom bazan k’ara sha ba, kuma mun b’ata” fuskar tausayi tayi tace 
“wlh bamu b’ata ba, muna nan a tare, Yayana ba fad’a” duk suka kwashe da dariya. Cikin farin ciki da nishad’i suka isa gida, a wannan rana kamar karsu rabu ko wanne yanajin kewar d’an Uwansa. 
Tun daga wannan rana Yaya Aryan da Basma suka d’inke, rana d’ai-d’ai ne basa fita wurin shak’atawa. Aryan ya kama aiki gadan-gadan wanda a sanadin zuwansa company ya k’ara hab’aka, Deeja kuma tana ta zuwa makaranta, a yanzu soyayya take sosai da Yaya Ahmad a waya, wani lokacin yakan zo hira, Basma ta rako shi, itama dan su sha hira da Yaya Aryan. 
Umma da Yaya Aryan sun san soyayyan Yaya Ahmad da Deeja, abinda ke basu tsoro shine, kar gaba iyayen su Basma suk’i yarda ya aureta, domin su talaka ne, Yaya Ahmad ya gyarawa su Deeja gida, anyi fenti an gyara gidan yayi kyau, an zuba musu sabon furniture’s. Yaya Aryan ya siyan musu kaya da komai na abincin, da kud’in albashinsa na farko dana biyu, yanzu ko sun fita da Basma shi yake musu siyayya, ya sauya waya ya mai dama Basma nata. Shak‘uwa mai k’arfi ya shiga tsakaninsu, Basma ba tada abokin hira sai Yaya Aryan, video call, charts da kuma zuwa wurin shak’atawa, duk tare suke komai, gaba d’aya ta sauyawa Yaya Shureym, wayansa da kyar take d’agawa, shima da yake yanada wacce yake so sai ya daina damuwa da ita, dama shi abinda yasa ya rik’e wuta, k0 zai cusa mata son shi ya samu yana rage zafi da ita. 
Bayan wata uku Basma da Yaya Aryan lamarinsu ya wuce tunanin kowa, basu tab’a furtawa juna kalmar So ba, Amma kuma idanun su, sassan jikinsu,jini, b’argo, da tsoka sun gama zama d’aya, sun tabbatar da in ba d’aya ba rayuwa, amma duk da haka zuciyansu yak’i ya basu damar yarda da abida jikinsu ke fad’a musu. Yau ya kama Lahadi, Yaya Aryan da Basma suna zaune bisa dadduma a wurin shak‘atawa, hira suke na nishad’i, wayar Basma ya d’auki k’ara, cikin rashin damuwa ba tare da ta duba mai kiran ba saita d‘auka tare da sanya hands free, muryan Yaya Shureym taji yace 
“My Basma nazo yanzu ance kin flta kina ina ne? ni fa yau nazo muyita ta k’ara, gaba d’aya kin sauyamin kin shareni, kin barni da missing d’inki, Basma ina cike da shauk’inki mai yawa, dan Allah Basma ki bani had’in kai ko da sau d’aya ne muyi rayuwa, wlh bazan bari kowa ya sani ba, kuma kinga Aure za muyi, inma kina tsoro muyi a k‘asar nan saimu fita England muje can mu huta” Tsoro, fargaba, damuwa ne suka ziyarci Basma, wani zafafan hawaye ke fita a idonta,jikinta ya d’auki rawa, sam bata zaci abinda zai ce mata ba kenan har tabar wayan a hands free, Yaya Aryan mik’ewa Yayi da sauri ya fige wayan ya bugata da k’asa, komai na waya ya tarwatse, Basma toshe kunne tayi saboda k’aran fashewan wayan, Yaya Aryan sai huci yake kamar wani zaki, sanya takalmi yayi ya fara tafiya, ya rasa ina zai sanya ransa yaji sanyi, ya d’anyi nisa a tafIyan ya shiga cikin mutane, da gudu Basma ta ruga ta rungumeshi ta baya tana kuka, tace “Yaya Aryan wlh ban tab’a yin wani Abu ba, Yaya Shureym ya sha kawo min farmaki da irin wannan maganar amma nak’i amincewa da k’udurinsa, wlh tun lokacin ya fara flta a raina ni sam bana Sonsa” Aryan ya b’abb’are hannunta daga jikinsa, ya juyo da ita gabanshi ya tsinketa da kyakkyawan Mari guda biyu, nan da nan hankalin mutane ya dawo gunsu, Ya matsa gab da ita yace “Basma kalli ido na ki gayamin abinda kika gani a ciki yanzu” idonta na zubda hawaye ta dafe kumatunta tace “Yaya Aryan kayi hak’uri wlh ban aikata komai ba” cikin fushi da fad’a ya daka mata tsawa yace “Basma me kika gani a idona ki gayamin” tace “idonka yayi ja” yace “Basma kukan zuciyana ne ya bayyana a idona, kina son ki kasheni ko” ya k’arasa maganar muryanshi na rawa, ido ta zaro waje tace “Yaya Aryan ni bazan kasheka ba” lumshe ido yayi ya bud’e, cikin kasalalliyan murya da rauni yace “Basma ina sonki, ina k’aunarki” idonsa ne ya kawo kwalla yana gabda zubowa, sai Basma ta tara hannunta tace cikin kuka “Yaya Aryan nima ina sonka, ina k’aunarka, kaine rayuwata, karka min asaran hawayenka, wanda ban tab’a ganinsa ya fitaba sai yau, ka gau-gauta mayar min da sauran ka adana min su, sai lokacin farin ciki ka flddamin su” sai hawayen ya d’iga a hannunta, bakinta takai ta shanye su, hannunsa ta kama tana jansa suna tafiya, Yaya Aryan binta yayi da kallon mamaki, gaba d’aya Basma ta bashi mamaki da maganarta. Mutunan dake gurin sai suka fara tafa musu, lallai sun bada salo da kowa yayi sha’awarsu, haka suka barwurin su ko ajikinsu, kowa na fad’an albarkacin bakinsa. Bayan sun kama hanyan gida Yaya Aryan yace ta samu guri tayi parking za suyi magana, bata masa musu ba ta samu guri tayi parking, yace “Basma ina so ki sani tun ranar dana fara tozali dake da kika tofamin miyau, wani Abu ya d’arsu a zuciyana akanki, a da ina tsammanin k’iyayya ne, sai daga bata na gane ashe So 
ne, ban tab’a jin d’an d’anon So akan wata mace ba, sai akanki Basma, dan Allah Basma ki kulamin da kanki da rayuwanki, domin kece rayuwata“ Farin ciki ne ya lullub‘e Basma, yau ta gasgata abinda gan-gan jikinta yake gaya mata akan Yaya Aryan, tace cikin jin kunya “Yaya Aryan karka damu, insha Allah zan kula maka da kaina da kuma mutunci na, kai ne rayuwata nima, kai kad’ai nake gani a idona na kasance cikin farin ciki, dan Allah ka rik’e min Amanar zuciyata, domin kaine mutum na farko da ya bud’e shafukan so da K’auna a ciki, kuma har abada kai ne mutum na farko kuma na k’arshe ba na biyunka” Murmushi yayi yace 
“Kinsani farin ciki Murmushi, amma fa ina da kishi, sai ki san yanda za kiyi da Shureym” murmushi tayi tace “my Aryan karka damu zan gayawa ya Ahmad komai”. Cikin farin ciki suka k’arasa gida, yau Yaya Aryan ji yake ya sauke wani abu mai nauyi a zuciyansa, haka ma Basma yanzu ta tabbatar Aryan nata ne. ‘Da dare’ 
Basma ta tafi wurin Yaya Ahmad ta sameshi yana aiki a system d’insa, sai ta gaishe shi, kana ta samu guri ta zauna tace “Yaya Ahmad nazo muyi magana ne” cikin kulawa yace ina jinki Basma” gyara zama tayi ta soma gaya masa duk abinda Yaya Shureym ke gaya mata, hankalinsa yayi matuk’ar tashi, nan ya shiga niman number Shureym, amma bai shiga ba, cikin yanayi na damuwa ya shiga yi mata fad’a akan meyasa bata gaya da wuri ba, fad’a da nasiha yayi mata sosai kana yace 
“ina ganin zan gayawa su Momy a sanya bikin kawai ayi kowa ya huta” da sauri Basma ta kalli Yaya Ahmad bakinta har yana rawa tace “Yaya Ahmad wlh bana sonsa bazan aureshi ba na tsaneshi” ta k’arasa maganar cikin damuwa… 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *