YAR SHUGABA CHAPTER 13

YAR SHUGABA 
CHAPTER 13
Hankalin Yaya Ahmad yayi matuk’ar tashi, cikin kulawa yace “haba Aryan ya, kake abu kamar k’aramin yaro, nace maka Basma tana barci inta farka zansa ta kiraka” ajiyan zuciya Aryan yayi yace cikin damuwa, “to shikenan nagode” nan suka yi sallama ya kashe wayar. Basma ta farka da misalin k’arfe biyu na rana, Kaka Ma’u ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya marasa nauyi, sallan Azahar ta gabatar kana aka kawo mata abinci, Kaka Ma’u ce ta matsa mata taci, loma uku tayi da kyar kana ta sha ruwa tace ta k’oshi, mik’ewa tayi kamar an tsikareta tace wa Kaka Ma’u tana zuwa sai ta fice, tayi sa’a falon ba kowa haka ta sanya takalmi ta flto haraban gidan, motocin gidan sun ragu da alama sun tafi raka su mai Martaba ne airport, hanyar k’ofar fita tayi tana waige-waige kamar mara gaskiya, masu gadi suka hanata fita, saita fara musu masifa akan su bata hanya ta wuce, ganin ta cije ne yasa suka bata hanya tawuce, tana shirin fita taga Yaya Ahmad zaune bisa wani dakali daga gefe ashe duk yana jin hayaniyansu, tsayawa tayi cak ta kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya mik’e yazo gabanta ya tsaya cike da tuhuma yace 
“Basma bakyajin magana, ina zaki bayan an hanaku fita, ya kike so ki zama mara biyayya ne” fashe masa da kuka tayi, girgiza kai yayi ya kama hannunta suka koma cikin gidan, part d’in su ya wuce da ita ya zaunarda ita a gefen sa ya kira sunanta a nutse “Basma kin ga abinda rashin ji ya haifar miki, naso ace haka bai faru ba, dana tsaya miki 
tsayin daka akan baki auri Shureym ba a baki wanda kike so, Basma meyasa kika aje tarbiyanki kika nima lalacewa haka, bayan kinyi saukar Al‘Qur’ani har sau biyu, kina da sani akan littafai Addini sosai, a takaice in aka baki aji zaki iya rik’ewa a matsayin Malama, ya a kayi kika shagala da duniya haka Basma?” “ 
Jikinta ne yayi sanyi sosai ta kuma b’arkewa da kuka tace Yaya wlh mun riga munyi kuskure, kuma wannan rayuwar a England muka koyoshi, insha Allah bazamu sake ba mun tuba, ni dai ka taimakeni karka bari a aura min Yaya Shureym wlh bana sonsa, kafi kowa sanin waye Shureym bai cancanta ya zama mijina ba” ajiyan zuciya yayi yace 
“na sani Basma amma Abba ya riga ya yanke hukunci, ni shawara ta gareki shine ki masa biyayya sai Allah ya sauk’ak’a miki lamarin” “To Yaya kamin Addu’a, amma da son Aryan zan mutu” Tsaki yayi baice komai ba wayarta ya d’auka yayi dailing number Aryan, bugu d’aya ya d’aga, sai ya mik’a mata ta kara a kunne, a cikin damuwa Aryan yace”My Basma kina lafiya kuwa?” kuka ta saki wanda hakan yayi dai-dai da k’ara rikicewansa, cikin damuwa yace “meya faru gayamin mana ko so kike nima nayi kukan”. Tuni Yaya Ahmad ya bata wurin domin ya gaji da jin kukan nata, Basma ta shiga bashi labarin komai bata b’oye ba, ai zunbur ya mik’e a tsorace yace 
“Basma shikenan kinyi sanadin rabuwanmu, shikanan kin jawo mana damuwa mara yankewa” ya k’arasa maganar cikin rawar murya, Basma sai ta k’ara tsinkewa da sabon kuka, Aryan kashe wayar yayi gaba d’aya, Basma taita dialing number akashe, a flrgice ta mik’e ta fita da gudu, Yaya Ahmad yana waje, ganin ta a guje yasa ya bita a guje, wurin gate ta nufa, masu gadi suka tare ta, kuka take da magiya akan su barta ta fita, amma suka k’i bari har Yaya Ahmad ya cimma su. 
Kama hannunta yayi gam yana janta, ihu sa saka tana tirjiya, ihun ta ne ya dawo da duk hankulan mutanan gidan duk suka fito a guje, da yake sun dawo daga rakiyan, kam su k’arasa cikin gidan sosai Basma tayi wani ihu saita langwab’e, a razane Yaya Ahmad ya juyo yaga idanunta sun kafe ta suma,jikinsa na b’ari ya d’auketa tsak ya shiga cikin gida da gudu, a hanya yaci karo dasu momy, nan ya kewaye su ya wuce da ita part d’in president, a falon ya ajeta duk suka shigo ko wanne ya rufa a kanta, Ammi ne keta kiran sunanta amma shuru, da gudu Meena ta kawo ruwa aka yayyafa mata, lumshe ido tayI’ tare da sauke ajiyan zuciya mai k’arfi, President da kansa yazo ya d’auketa cak ya haye da ita sama, ya kuma yi gargad’in kar wanda ya biyoshi, a zata yayi akan gadonsa ya d’auki wayansa ya kira likitansu. 
Baifi rafin awa ba sai gashi, ya haura sama ya dubata, allurai yayi mata a ciki harda na barci, yayi wa Abba bayanin “damuwa ce ya haifar mata da suma, yanzu nayi mata alluran barci domin kwakwalwanta ya huta” nan Abba ya mishi kyauta ya fice yana godiya. Su Ammi duk suna falon sun kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya zauna jugum yace “Ammi dan Allah kusa baki ajenye maganar Auren nan, lamarin Basma ya fara bani tsoro” Ammi tace “nima abinda na gama tunani kenan, amma kasan Abbanku baya sauya magana in yayi” Momy ce tace “uhum nikam ina bayan Abbanku, aure kuma da Shureym ba fashi” tana gama fad’an haka ta mik’e tace 
“Husnah zo muje na had‘a miki turarukanki kan ki tafI” Cikin sanyin jiki da damuwa Anty Husnah tabi bayanta cike da tausayawa ‘yar uwanta. Sai bayan Sallan Isha’i ta farka, Abba da kansa ya kira Ammi tazo tayiwa Basma wanka ta shiryata, Abinci ta bata da kanta, da kyar take iya cin kad’an, bayan sun natsa Abba ya kira su Meena dasu Momy, dasu Yaya Ahmad duk suka had’u a falon sa, ya soma magana “na taraku a nan ne domin in kuma jaddada muka akan zancen Auren ku, saboda wasu dalilai mun k’ara kwanakin bikin zuwa bayan wata Uku, lokacin Basma ta samu lafiya sosai, Meena tasha maganin Islamic akan kwayoyin da tasha, ke kuma Leema ki samu yin istibra’i ” Leema saita sunkuyar da kai k’asa, cike da dana sani, yanzu kowa yasan ita fasik’a ce wa iyazu billah, maganar zuci takeyi hawaye na zuba a kuncinta. Abba yakai dubansa ga Basma data rakub’e gefe d’aya kusa da Ammi yace “ke kuma Basma ina so ki sani tun da muka haifeki, ban tab’a saki abu kin k’i yimin ba, to ina niman alfarma a gunki a matsayina na mahaiflnki, kiyi hak’uri kiyi min biyayya insha Allah zakiyi nasara a rayuwanki, Basma ke mai biyayya ce a garemu, akwai abubuwa dana auna na tabbatar da yin aurenki ga Shureym shine dai-dai, zumunci ba abun wasa bane, dan haka ki sanyawa ranki salama ki tabbatar min da nine mahaifinki kuma na isa dana saki Abu kiyi min”,,,,,,,Kuka ta soma yi amma mara sauti, tashin hakanli ta shiga, domin yau ta riga ta sadak’ar an rabata da Aryan, kwantawa tayi a jikin Ammi tace cikin kuka mai karya zuciya 
“Abba ina son Aryan ne wlh shi nake so, burina in muku biyayya,Abba kamin komai a rayuwata, k’arshe na sab’a muku, na aje tarbiyyan da kuka bani na soma yin wata rayuwa mara tushe, mai dinbin dana sani aciki, nagodewa Allah da kune kuka ganni da idonku, na tabbatar da labari aka baku baza ku yarda ba, saboda kun bani dukkan yardanku, Abba saboda haka na hak’ura da soyayyar Aryan, amma ku sani zan auri Shureym bisa ga biyayya a gareku ne, domin in cire muku rad’ad’in sab’a muku da nayi, Na amince zan auri Shureym, Aryan ka yafemin” Sai ta k’arasa maganar da wani matsanan cin kuka, da gudu ta mik’e tabar falon, ta nufi d’akin Abba,ta fad’a gado tana rera kuka mai tsuma zuciya. 
Gaba d’aya illahirin mutanan falon jikinsu yayi sanyi, hatta Abba ya tausayawa ‘yarsa abin sonsa, sunyi shuru ko wanne da irin abin da yake sak’awa a ransa, sautin kukansu Meena da Leema ne ke tashi a falon, Kaka Ma’u ce tace “ni kam wannan lamari yana bani mamaki, waye wannan Aryan d’in da yake son raba zumunci” Yaya Ahmad ne yace cikin wasan kaka 
“ke kuma tsoguwa ina ruwanki, ana Abu na yara kin tsomo baki, sai ki mana shuru” Abba ne ya masa dak’uwa yace 
“kai ungo naka uwata kake cewa hakan” su Ammi duk suka yi murmushi, nan take fara’ansu ya dawo, damuwan da suke ciki ya ragu, Abba yace 
“Ahmad ina so gobe in Allah ya kaimu ka tattaro min dukkan takardu da makullan abubuwan da Basma ta mallaka” Cikin ladabi yace “to Abba insha Allah zanyi, Allah ya kaimu” Nan Abba ya sallami kowa, Momy ce mai girki Abba ya cewa Ammi, ta wuce da Basma d’akinta, ta bata kyakkyawan tsaro saboda karta fita cikin dare ba’a sani ba. Shureym bayan sun isa Kano, ya samu Maminsa ya matsa mata akan shifa lallai sai an aura masa Basma in ba haka ba akwai Matsala, Hajiya Sa’a tayi murmushi tace masa “Ka kwantar da hankalinka, aurenka da Basma kamar anyi an gama, ita d’in banza harta isa tace bazata aureka ba, zanje in samu Mai Martaba na k’ara hura masa wuta akan lamarin” dariya yayi na farin ciki yace “to Mami ya maganar aurena da Safeena? Kinsan fa so nake a fara d’aurawa da ita kan na Basma” tace “Karka damu cikin satin nan zan had’aka da sarkin gida da wasu, domin suyi jagoranci aurenka da Safeena, a cikin sirri za,ayi ba tare da kowa ya sani ba, kaga sai a d’aura muku aure kam bikin su Basma da wata guda, ka ajeta a gidan gonarka, da an d’aura aurenku da Basma ku tarkata ku wuce America, bazaku dawo ba sai ka kammala komai da shekara guda, kaga lokacin komai yayi dai-dai” dariya yayi harda tafawa yace “Gaskiya Mami kin gama min komai in kika min haka, zanyi murna sosai” tunowa da yanda Basma ta nuna masa tsantsar kiyayya yayi, yasa ya cije leb’e yayi wani shu’umin murmushi. 
‘Bayan kwana biyu‘ Aryan ya lalace yayi duhu, hankalin Umma ya tashi sosai dan kwanan sa biyu ko k’ofar gida baya iya zuwa, sallah ma a gida yake yi, baya iya cin komai sai abu mai ruwa, sai yawan barci. Deeja ce take sanarwa Yaya Ahmad halinda suke ciki domin sam Yaya Aryan yak’i yarda suje asibity kuma yace shi lafiyansa kalau, Ahmad ya shirya yazo, ya samu Umma ya sanar mata abin da ke faruwa game da Basma da Aryan, bai b’oye mata komai ba, hankalin Umma ya tashi sosai ta tausaya musu, dama tasan za ayi haka, Deeja d’aki ta shiga ta fara kuka, Yaya Ahmad ya sanar mata da zuwan iyayensa nan da ranar Juma’a akan maganar auren Deeja, Umma ta sanya albarka tayi murna koba komai hakan ya rage mata damuwa, nan ya shiga wurin Aryan da kyar ya shawo kanshi suka tafi asibity tare. Likita ya duba shi ya rubata masa magani da allurai, haka akai treatment d’insa, Yaya Ahmad yayi masa siyayyan kayan ciye-ciye, kana ya dawo dashi gida, ya yiwa Umma sallama ya tafl. 
‘Bayan wata guda’ Bikinsu Basma saura wata biyu, Yaya Aryan ya ware yaci gaba da zuwa aikinsa, sai dai yanzu miskilanci ya k’aru, baya magana saiya kama dole, baya cin abinci sosai duk ya rame yayi fari, Umma tayi mita da lallashi harta gaji ta kyaleshi, kullun dare baya iya barci sai yayi kuka sosai, kana yayi Nafila ya rok’i Allah kan ya sassauta masa akan lamarin. 
Abba ya wakilta Abokansa wajen nimawa Ahmad auren Deeja, da yake Ahmad ya sanar da Abba komai tun farkon had’uwansu, Abba ya jinjina lamarin kuma yayi farin ciki da ‘ya’yansa, da suka kasance masu tausayi da taimakon na k’asa dasu, hakanne ya k’ara bashi k’arf’ln gwiwan ya amince da Auren Ahmad da Deeja, a ransa baiji dad’in raba Basma da Aryan ba,Amma yayi alkwarin zai d’aukaka darajan Aryan yanda duniya da ‘yan uwansa zasu amfana dashi. Mak’otan su Deeja da mai anguwa sune suka amshi maganar Auren Deeja, iyayen Ahmad da sukazo Sun boye asalin Ahmad, suka sanya biki dai-dai dana su Meena, a haka suka gama taron cikin mutunci, kowa ya koma gida. Deeja farin ciki ya lullub’eta, amma inta tuno da Yaya Aryan sai damuwa ya rufeta. A haka suka fara shirye-shieyen biki, Yaya Ahmad ya sanar musu da, shifa Deeja kawai yakeso a bashi, baya buk’atar komai, hatta abincin biki Abbansu ya d’auki nauyi, dan haka kar su takurawa kansu, Umma saboda murna har kuka tayi. B’angaren Basma kuwa, lamura sun dagule mata ta lalace tayi bak’i, duk ta rame inka ganta sai ka k’ara kallonta ka tambaya anya itace Basma ‘yar kwalisa kuwa? domin duk ta flce a hayyacinta, kowa na gidan yana tausaya mata, hatta Momy tana jin tausayin ‘yarta haka yasa takejawota ajiki, tana lallashinta da maganganu masu dad’i da nasiha, yanzu Basma ta saduda ta kuma hak’ura da lamarin, burinta bai wuce ta k’ara tozali da Aryan ba suyi magana na bankwana. 
Su Meena an natsu, ana ta bata magunguna na Islamic wanda zai wanke mata dattin kwayoyin data sha. Leema kuwa Momy musamman takawo mai gyara, domin a gyarata, yanda zata dawo kamar budurwa, koda dai ta riga ta rasa budurcinta. ‘Ni kam nace anbaro shiri tun rani’ Hmm Shirye-shirye ake ta ko wani b’angare, Abuja, Kano, Kaduna, duk sunata shirye-shirye, biki ne na ‘ya’yan manya. ‘Biki saura wata guda’ 
President ya kira Ahmad suka gana dashi a d’akinsa. Yaya Ahmad ya flta da sauri domin aiwatar da ummarnin Abba. Abba ya kira Momy da Ammi, ya kira duk yaran gidan, kaka Ma’u ita ta koma Kaduna dan taf’ljin dad’in zaman can. Yaya Ahmad ya nufi gidansu Aryan, ya samu duk suna gida da yake weekend ne, Yaya Ahmad ya shiga ya zauna a shinfld’an da Deeja ta masa, suka gaisa da Umma, ya kalli Aryan ya kalli Umma yace “Umma mahaiflna ne yace inzo in tafl daku gidanmu, domin yana buk’atar ganinku, yace in baku hak’uri akan hakan, yasan shine ya kamata yazo amma bisa wasu dalilai yace da kuje ku same shi” Yaya Aryan ne yace “ok badamuwa yaushe yake son ganinmu?” “Yanzu yake son ganinku” Umma tace “to shikenan bari mu tafl” ta k’ara maganartana mik’ewa, komawa d’aki suka yi duk suka canza shiga mai kyau, suka rufe gidan suka shiga mota. “ Aryan na gaba Umma da Deeja suna kujeran baya, sun kama hanya suna tafiya, Aryan suna hira da Yaya Ahmad, tafiya sukai mai nisa, tun suna arean talakawa har suka gota arean masu hannu da shuni, Yaya Ahmad yana zullumi a zuciyansa yanda in suka san Abbansu ne Shugaba k’asa ya zasu d’auki lamarin ,Yaya Aryan ne ya katse masa tunaninsa yace “Ahmad naga mun doshi hanyar gidan Shugabab kasa ne, kasan fa ta arean akwai check point kuma ga yawan security” murmushi Yaya Ahmad yayi yace 
“eh gidanmu dole sai tanan zamu bi, karka damu” haka suka fara ratsa check point ba tare da an tare su ba, security suna d’agawa Yaya Ahmad hannu, mamaki ne ya fara cika su, basu tsinke ba saida suka ga security na bud’e musu hanya suna sarawa Yaya Ahmad, katon tangameman gate d’in fadar shugaban k’asa suka dosa, wanda kan su k’araso an bud’e musu gate, a tsorace Yaya Aryan ya kalli Ahmad bakinsa yana yawa yana nuna shi 
Hmm 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *