YAR SHUGABA CHAPTER 19

YAR SHUGABA
CHAPTER 19
‘Nigeria“ 
Abba sun sauka laflya cikin dare, ya shaida masu Momy Basma na gaishesu ba wata Matsala. Yaya Naufal ya labaratawa Yaya Ahmad duk abinda ya faru, damuwa ne ya ziyarceshi yace “anya kuwa Shureym na kula da Basma?” Yaya Naufal yace 
“yana kula da ita a yanda muka gani, kuma ai in da da matsala zata gayawa Abba” murmushi kawai Yaya Ahmad yayi a ransa yace “ban yarda ba dole zanyi bincike akai, dan Basma tana da zurfin ciki, ni kad’ai take gayawa damuwanta ko Momy” a fili kuma yace “hakane, to Allah ya bata lafiya ya k’ara musu zaman lafia” “Ameen” Yaya Naufal yace, kana ya wuce part d’inshi. Kasar Monaco’ 
Aryan yayi nisa cikin karatunsa, a yanzu hankalinsa ya kwanta, sai dai haryanzu bai maida jikinsa ba, yana waya dasu Umma da Khadija sai Yaya Ahmad, yanzu ya daina kashe wayansa kullun tana kunne, har yanzu bai dawo cikin walwala ba, baya dariya sai dai yak’e kuma shima saiya d’auro, murmushi ne kawai ya kanyi time to time. Wata rana yana makaranta ya fito daga aji yana tafiya, karo yaci da wata ta tawo a guje bata lura dashi ba, d’agowa tayi cike da tsoro, cikin harshen turanci tace “yi hak’uri wlh ban kula bane” gyad’a mata kai kawai yayi sai ya rab’eta ya wuce, binsa tayi da kallo cike da tunani barkatai, 
“iya had’uwa wannan guy d’in ya had’u, ko dan wani kasa ne oho? Gaskiya bazan bari ya kub’ucemin ba, dan na kamu da sonsa, kuma shine dai-dai tsarina” Abinda take fad’a a ranta kenan, da gudu ta bi bayanshi, bata san sunanshi ba gashi ya tsere mata, duk da haka bata hak’uri ba, ta cigaba da bin bayansa da gudu ta cimmasa, gabansa ta sha, sai ta tsaya cike da yin nishi tace 
“Yi hak’uri na tsaidaka, sunana Jidda Bukar, ni ‘yar Nigeria ce katsina state, muna zama a Abuja, nazo nan karatu ne, in ba zaka damu ba ko zan san daga ina kake? dan kayi min zubin d’an k’asar India” 
Murmushi yayi a takaice yace cikin harshen turanci “sunana Aryan Aliyu, Dan k’asar Nigeria” ido ta zaro tace “wow ashe k’asarmu d’aya, wlh gani nayi ba kayi kama da ‘yan Nigeria ba, amma nayi murna sosai, cewa nayi bari na biyo ka saboda naga Kana da sauk’in kai, in ba damuwa ko zamu kulla abota” ransa ne ya b’aci, amma saiya dake cikin rashin sakin fuska yace “nagode, amma ba zai yuwu ba kawai, in dai mun had’u sai mu rik‘a gaisawa” yana gama fad’an haka ya wuce, binsa tacigaba da yi tare da yi masa magayi akan suyi exchangen number, tsayawa yayi zuciyarsa na tafasa cikin masifa yace 
“ya isa dan Allah, kiyi hak’uri ina da mata, pls ki fita a harkata, sai wani bina kike kamar naci miki bashi” jikinta ne yayi sanyi bata k’ara furta komai ba sai ta juya ta fara tafiya, tausayi ta bashi sai ya dakatar da ita yace Jidda kiyi hak’uri ban cika son ana takura min bane” juyowa tayi idonta ya cika da kwalla tace “ba komai na fahimceka” Numbern shi ya karanta mata, kana suka yi sallama. Ta wuce cike da murna shi kuma ya tafi cike da tunanin Basma,ji yake kamar yaci amananta, wani b’angare na zuciyansa yace “bakaci amana ba, itama ai tanacan tare da mijinta” runtse idonsa yayi hawaye mai zafi ya fito masa,ji yayi komai ya dawo mishi sabo, zazzab’i ne ya rufeshi, sai ya tafi gida cike da matsananciyar damuwa. Tun daga wannan ranar Jidda ta mak’alewa Aryan, Sam baya son abinda take masa,yana k’ok’arin janye mata amma sai k’ara shige masa take, ita burinta bai wuce ta samu zuciyar Aryan, ko bazai aureta ba tunda yace yana da mata, zata amince masa su tab‘a rayuwa k0 kad’an ne, domin tana fama da sha‘awansa. Aryan yana gida a kwance da yamma, sai yaji anyi masa knocking, tashi yayi ya tafi ya bud’e, mamaki ne ya rufe shi ganin Jidda ce, murmushi tayi masa sai tabi gefensa ta shige d’akin, binta yayi da kallon yana mamakin yanda akayi tasan gidansa, cikin nuna k0 rashin damuwa Jidda ta cire mayafinta ta zauna a kan kujera mai mazaunin mutum d’aya,komawa yayi ya zauna kujeran dayake fuskantarta tace Nasan kayi mamakin yanda akayi na gano gidanka ko, kasan ance mai son d‘an tsuntsun shike binsa da jifa, Aryan wlh ina sonka amma kak’i bani gurbi a zuciyarka” Aryan d’aure fuska yayi yace “Jidda nafiso ki bar alak’anmu da abota kawai, domin bana tunanin zaki samu gurbi a raina, dan na riga na bada soyayyata ga wata” Hawaye ne ya cika mata ido tace “pls Aryan, ni wlh ko kaina kace in baka a shirye nake” mik’ewa tayi tajuya a gabansa ta cigaba da cewa “Kalli surata da kyau, ina da duk abinda mace take dashi ajikinta wanda namiji zai mora, dan Allah ka yarda dani in zama mai d‘ebe maka kewa, koda baka sona in har ka yarda min da haka zanyi murna” Aryan cikin b’acin rai ya mik’e ya nuna mata hanyar waje yace “Jidda na tsaneki na tsani mata masu irin halinki, ki sani har ki mutu ba zaki samu yanda kike so ba domin nafi k’arfin iskancinki, kuma ki sani Ni ba kalar ki bane, ki gaugauta cireni a cikin jinsin mutanan da kikasani” jiki na rawa ta mik’e zata bashi hak’uri, cikin tsawa ya dakatar da ita “Nace ki fita” da sauri ta kwashi kayanta tana mai jin haushin kanta, rufe k’ofarsa yayi tare da sauke ajiyan zuciya, Addua yayi da k’ara niman tsari ga irin wannan matan. Tunanin Basma ya shiga yi, “Yarinya ce mai natsuwa, duk wayewarta a kame take, ga kud’i dajin dad’i na rayuwa amma akwai tarbiyya mai kyau, har abada yanajin ba zai samu mace kamarta ba” hawaye 
ne ya zubo mashi yace a fili”Basma har abada ina sonki, babu macen da zan aura ta kai matsayinki, nasan haduwata dake wani jarabawa ne a rayuwana, Allah ya rabamu ina tsananin sonki, Allah ka bani 
wacce zata share min hawaye na”. “_Aryan nima na tayaka da cewa “Ameen”. Masu karatun bari mu koma k’asarAmerica mu 
ga wainar da Suke toyawa._ ‘Bayan wata guda’ Basma ta warware, zamansu kuma yana nan zaman doya da manja, da dad’i ba dad’i, kadaran kadahan, Basma yau tasha Riga da wando English wears, saita d’auko gyale tayi rolin iya kyau tayi, jaka ta d‘auka ta fito falo, Safeena ta tarar tana shan fruit, Safeena tace cikin tsokanar fad’a “Ayawo yau kuma shigan yan iska kikeji?” Basma bata tanka mata ba, illa tsaki da taja ta fice, Safeena ta ce 
yar rainin wayo, zaki had’u da Shureym shine dai dai da iskamcin ki”. Basma na fita taxi ta shiga ta wuce inda suke had’uwa da Bilal, ta sameshi yana jiranta, kallonta yake cike da soyayya yace “Basma kinyi kyau sosai” murmushi tayi tace “nagode muje ko” wurin shak’atawa suka wuce, suna tafe suna hira, Bilal yace 
Basma yaushe zaki kaini gidan ku na gaida da Iyayenki, nifa da gaske sonki nake kuma aurenki zanyi, dan har na fara magana da Ammi na” Murmushi tayi tace 
“ni iyaye na suna Nigeria, yanzu da Yaya na muke a nan k‘asar, kuma ina so ka sani gaskiya ina da aure” ai bata k’arasa maganar ba yajuyo a zabure yace “pls my Basma ki daina fad’an wannan maganar imma wasa kike” murmushi tayi tace “Bilal da gaske nake, Mijina dai baya tare dani yana k’asarmu” tab’oye masa hakan saboda bata son yasan komai nata, cike da damuwa ya samu guri yayi parking yace “meyasa kike wasa da aure, Basma na tabbata ke mace ce mai ilimin addini, meyasa bakya amfani dashi, yanzu kusan 1month da had’uwarmu, sauk’in abin ma tun farko kink’i Amincewa dani muyi soyayya, kin ce ke kin d’ukeni brother d’inki ne, dama nike kid’ana da rawa, da tun farko kin gaya min kina da aure da alak’anmu batayi nisa ba, ko kuma da nasan yanda zan fuskance ki, amma ba damuwa naji dad’i da kika gayamin gaskiya, zan koyawa kaina hak’uri da soyayanki, sai mu cigaba da zumunci” 
Murmushi tayi tace “nagode da tunatarwa, insha Allah zan gyara muje ko” “yanzu ina muka nifa?” murmushi tayi tace 
“muje wurin wasa da mota ko?” dariya yayi yace “OK my Friend” dariya tayi tace 
abotan harya fara aiki kenan” murmushi kawai yayi ya tada mota suka cigaba da tafiya. Sai k’arfe bakwai na dare Basma ta dawo daga wurin wasan mota, Bilal ya sauketa a k’ofar gida, hakan yayi dai-dai da cillowar motan Yaya Shureym, ita kuma tana d’aga ma Bilal hannu harya wuce, sannan ta shiga gida. Ta samu Safeena zaune sai d’irkan abinci take, tsaki Basma taja tace “Mutum baida aikin yi sai ya zauna yaita d’irkan abinci kamar jaka, wai dole ita mai ciki” Murmushi Safeena tayi bata ce komai ba domin ta riga ta had’a mata bomb mai kwacenta yau a gun Shureym sai Allah. Safeena ta gayawa Shureym daya dawo, k’arya da gaskiya akan fitan da Basma take yawan yi da kuma mummunar shiga, ransa yayi matuk’ar b’aci, fita yayi nimanta wuraren shak’atawa ko zai ganta a can, amma haka ya karad’e yawan nimanta bai ganta ba, dawowansa kenan yanzu daya hangota tana d’agawa wani hannu, ransa ya k’ara b’aci sosai kishi ya rufe masa ido, da sauri ya shiga gidan yayi parking. Falo ya shiga da sauri ya soma kwalawa Basma kira, da sauri ta flto tana fad’in dan Allah karka fasa min kunne, sai wani kwala min kira kake, sai kace tsohon makawo” a zuciye ya bud’e baki zaiyi magana, sai ga Bilal ya kwad’a sallama ya shigo falon, Basma saida gabanta ya tad’i, amma saita dake tace cikin Fara‘a “Friend hala nayi mantuwa k0?” murmushi yayi yace “kin manta da ice cream d’inki kina sauri” “ayya wlh ban kula ba, nagode kuwa sosai” Shureym ai sakin bakin yayi yana kallon ikwan Allah, cikin harshen turanci Bilal yace masa “ina yini big brother” Shureym ya amsa a tak’aice, sai ya fice da sauri. Yaya Shureym zama yayi akan kushim yana cizon leb’ensa, gaba d’aya kishi ya rufe masa ido. Harwani d’aci bakinsa yake masa saboda b’acin rai, Basma tana ganin ya zauna bai ce mata komai ba, sai kawai ta shige d’aki.Shureym ya d’aga wayarsa ya kira Dadyn Kaduna, Gobna Ibrahim, suka gaisa Dady yace “Shureym ya Basma da fatan kuna lafiya?” cikin k’unan rai yace “Dady Basma tana cin Amanta, fita take yi tana hurd’a da wasu maza a waje, yau tun rana ta fita sai yanzu ta dawo, kuma Dady wani saurayinta ne ya kawota gida, yanzu yabar falon mu” a razane Dady ya mik’e yana fad’in “Inalillahi wa inna ilai hir raji’un, Basman ce ta zama haka, to maza ku shirya gobe-goben nan ku tawo Nigeria, zan kira family meeting gaba d’aya zamu had’u a Abuja duka, kayi 
hak’uri kaji Shureym karka ce mata komai” sai suka yi sallama. Dady ya fara kai koma a falo sai salati yake, Ummin Meena dake zaune itama ta mik’e a tsorace tana tambayarsa “Alhaji lafiya?” kallonta yayi bai ce komai ba, ya shiga niman number Mai Martarba Sarkin Kano, suka gaisa, sai ya shaida masa akwai family meeting a Abuja gobe in Allah ya kaimu, nan suka yi sallama. ya d’aga waya ya kira President, shima haka ya shaida masa kamar yanda suka yi da Mai Martaba, President cikin mamaki yace Ibrahim lafiya dai k0?” cikin murmushi yak’e yace “Lafiya Kalau sai in munzo zaka ji komai insha Allah” da haka suka yi sallama. Dady ya koma ya zauna, itama Ummi ta zauna, ya shiga gaya mata Abinda Shureym yace masa, cikin salati Ummi tace “wlh k’arya yake yi, ba dai Basman mu ba, sai dai in sharri zai mata, dan ba haka muka tarbiyyantar da ita ba” 
Cikin b’acin rai Dady yace “karki shaideta domin d’an yau ba a iya masa, kuma ai ba tare dasu muke zama ba, hasali ma ba gari d’aya muke ba, Basma zata iya komai tunda dama bason Shureym take ba” sai jikin Ummi yayi sanyi ta shiga nazarin maganar Dady… 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *