YAR SHUGABA
CHAPTER 27
Wuri ya k’awatu sosai, b’angaren iyaye Maza daban tare da abokan Abba, sai iyaye Mata b’angare su daban tare da k’awayensu, yara Maza da Mata suma duk b’angarensu daban, sunata ciye-ciyen kayan kwalan da mak’ulashe, mota ce ta shigo gidan duk hankalinsu ya koma wurin ganin kosu waye a motan,Aryan ne ya fito ya doshi b’angare su Abba, risinawa
yayi ya gaishesu, Dady dai yanata kallonsa, Aryan yace “Amm Abba damajiya naje Gombe na d’auko Kakanni na iyayen Umman mu, to shine suka ce na kawo su ku gaisa tare da tayaku murnan dawowar Basma” cike da farin ciki Mai Martaba yace “Masha Allah, jeka tawo dasu, sannunsu da zuwa” Abba yace “Umman ku fa?” yace”tana tare dasu a cikin mota”
“madallah su k’araso ciki”. Aryan ya wuce wurin Motan ya bud’e musu, Malam Baffa ne ya soma fitowa sai Inna, dama suke mazaunin baya, sai kuma Umma ta fito daga mazaunin gaba, Suka jero, Yaya Aryan yana gabansu, Dady ya zabura ya mik’e a rud’e, saboda ganin abinda baiyi tsammani ba a rayuwansa, barin kujeransa ne yayi ya fara tafiya ba tare da ya sani ba, su Abba suka bishi da kallo da kuma kalon inda yake kallo, Dady ya dafe kansa da hannu biyu yana ambaton Allah, wani k’ara ya saki sai ya yankejiki ya fad’i, cike da tashin hankali su Abba da yaran suka rufa a kanshi. Meena ce ta fara kuka tana fad’in Dady, Dady, Dady, su Umma sun kasa k‘arasowa saboda abin ya tayar musu da hankali sam basu gane shi ba. Cikin sauri suka d’auke shi sai a sibiti, zan iya cewa dukan mutanan wannan taro suka dunguwa zuwa asibiti, emergency aka shiga dashi, likitoci uku suka rufa a kansa, cikin wani na’ura suka sanya shi suna ta aikin bincike, Abba ya musu bayani yanda abin ya faru, sun fahimci matsalan daga kanshi ne, sai da suka d’auki awa guda a kansa suna aiki. Daga wajen emergency d’in cike yake da Family d’insu, su Abba sai kaiwa da komawa suke yi, su Leema dasu Basma sai kuka suke, Ummi ma ta kasa dauriya kuka take kashirb’an, su Momy na lallashinta, Abba ne ya juyo yace “yanzu fa Ibrahim Addu’a yake buk’ata ba kuka ba, dan Allah kuyi shuru muji da guda d’aya”. Likitoci sun flto daga d’akin, su Abba da Mai Manaba, sai Alhaji Gana Abokin Abba suka tare su, Doctor Jabir ne yace
“Yallab’ai muje office, nayi muku bayani” haka suka bi bayansu. Duk suka samu guri suka zauna, Dr Jabirya kalle su yace
“Yallab’ai bincikenmu ya nuna cewa Gomna Ibrahim ya tab’a samun loosing memory, to yanzu akwai abinda ya gani da yasa ya dawo dashi hankalinsa, munyi masa allurai da gwaje-gwaje wanda in ya farka zai dawo hayyacinsa gaba d’aya, kuma rayuwan da yake ciki yanzu ba zai manta ba, zai cigaba da rayuwansa kamar yanda ya saba, wancen tunanin daya rasa shine ya dawo kwakwalwansa” Abba yace “Alhamdulillahi, yanzu zai kai k’arfe nawa kafin ya tashi?” Dr Jabir yayi murmushi yace zai d’auki lokaci kan ya farka, amma ba matsala bane” “to Masha Allah, Allah ya bashi lafiya” duk suka amsa da “Ameen” Dr Jabiryace “yanzu nasa an canza masa d’aki na summan, kuma za’a iya shiga a duba shi amma dan Allah banda hayaniya, domin bama so a tashe shi, munfi so ya tashi da kanshi” Mai Martaba yace “bakomai insha Allah za’a kiyaye” nan suka yiwa Doctor godiya suka fito. Da sauri su Yaya Ahmad dasu Ammi suka tare su Abba, dan jin me yake damun Dady, cikin natsuwa Abba yace “Alhamdulillahi ya farfad’o sai dai ya samu barci, da zaran ya farka komai zai yi dai-dai, sai dai likita yayi gargad’i banda hayaniya, Hajiya Fatima ku shiga a nutse ku duba shi, Yaranma duk ku shiga, sai ku fito su Ahmad su maidaku gida” Ammi tace “to shikenan, Allah ya bashi lafiya” duk suka amsa da “Ameen”.
Haka suka shiga d’akin a nutsu bayan sun gama duba shi suka fito, su Yaya Ahmad suka wuce da matan zuka gida, su Umma ma dasu Baffa Yaya Aryan ya maidasu gida ya dawo. Nan aka k‘ara security a asibitin, su Yaya Ahmad suna zaune a wajen d’akin, su Abba kuma suna zaune a ciki, sai Addu’a suke tofa masa. A nan suka yi Sallan Magrib da isha’i, har zuwa lokacin Dady bai farka ba, damuwa ne ya soma ziyartan su kusan awa hud’u har lokacin bai farka ba, Abba ya kuma yiwa Doctor complaining, Dr Jabir ya k’ara basu hak’uri, ya tabbatar musu da zai farka karsu damu. Har misalin sha biyun dare Dady bai farka ba, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Yaya Shureym, Yaya Adam, Yaya Aryan, Abba, Mai Martaba duk a asibiti suka kwana, Alhaji Gana ya wuce gida shi da sauran Abokan Abba. A can gida kuma Matan hankalinsu a tashe suka kwana.
Washe ga ri‘ Da misalin k’arfe goma na safe Dr Jabir ya shigo duba Dady, duk su Abba suna gefe a zaune, Dr Jabirya duba drip d’in dake mak’ale a hannun Dady, a hankali Dady ya sauke ajiyan zuciya, ya soma bud’e ido tamkar wanda ke tsoron haske harya bud’e duka, Addu’a ya
shiga karantawa, murmushi Dr Jabir yayi, Dady ya mayar masa da murmushi yace
“Baffana” dan fuskan Baffa ke masa gizo a idonsa, da sauri Abba ya mik’e ya isa baki gadon ya kama hannun Dady yace “Alhamdulillahi, Alhamdulillahi,Alhamdulillahi, Mai Martaba Ibrahim ya farka” Cikin muryan mara lafiya Dady yace “Ina Baffana suke? ko basu na gani ba d’azun” cikin rashin fahimta Abba yace “suwa kake magana akai?” murmushi Dady yayi ya kalle Mai Martaba yace
“ku kira min Aryan domin ya kawo min Innata da Baffana, da kuma k’anwata Aishatu, kuce masa su tawo tare da d’an Uwana Aliyu” cike da mamaki Mai Martaba ya kalli Abba yace “inna fahimci Ibrahim yana magana akan bak’in da Aryan ya shigo dasu ne jiya, Allahu Akbar Allah Mai iko, kaji wani abin Al’ajabi, ban tab’a tunanin Ibrahim zai dawo hayyacinsa ba, kusan shekaru sama da talatin kenan”
Abba murna da farin ciki ya hanashi magana, hamdala da tasbihi yake wa Allah, wayansa ya ciro ya kira Ahmad yace
“Ahmad maza kaje gidansu Aryan, ka tawo dasu gaba d’ayansu ka kaisu gida, gamu nan likita zai bamu sallama zamu koma gida” Yaya Ahmad zaiyi magana yace
“Ahmad yanzu ba lokacin bayani bane, maza ka tafl ka aiwatar da abinda na saka”
Dr Jabir yayi dariya yace “wato yallab‘ai kasan sallama zan baku” cike da farin ciki Abba yace “kwarai kuwa me zamu jira, bamu sallama da sauran magunguna su Naufal su tawo dasu, mu kaga tafiyar mu” sai ya tallabo Dady yace “ “D’an Uwana sauko kaga mu wuce gida, ka samu kayi wanka kaci abinci ka rama Sallolin da ake binka, sai mu zauna Family Meeting yau ka gana da iyayenka” Cikin farin ciki Dady
ya sauko yana murmushi, haka suka kai shi har mota suka tafi gida,. Su Yaya Shureym suka amsa magungunan Dady, sannan suka wuce gida. Gidan ya hargitse da Murnan dawowan su Dady, direct part d’in president suka wuce a can duk suka kimtsa suka ci abinci, Dady ya rama sallolinsa Magrib, lsha’i da kuma Sallan Asubahi. Duk sun had’u a falon Abba suna zaune, sai yajiki suke masa, Ummi sai murna miji ya farka, Meena kuwa baki har kunne dasu Basma, falo ya cika suda iyalensu suna ta hira da barkwanci cikin nishadi da farin cikin, sallaman su Yaya Aryan ne ya katse hiran nasu, Yaya Ahmad dasu Umma suna biye a baya, wuri aka basu suka zauna Dady ne ya mik‘e ya isa in dasu Malam suka zauna, ya durkusa ya had’a hannunsa biyu, Baffa ido ya zaro ya shiga murza idonsa, lallai wannan Ibrahima Khalil ne, an ya ko dai gizo nake gani?” kallon Inna yayi ya cigaba da cewa
“wai Ameena kina ganin abinda nake gani kuwa, wannan kamar Ibrahim d’in mu?
kamannin fuskansu d’aya, sai dai shi mun masa sanin lokacin da yake k’arami ne”
Inna tace “kwarai kuwa Malam nima abinda na gani kenan” falon yayi tsit suna kallon su, Dady yace cikin kuka Inna, Baffa, Ibrahim d’in kune ku daina tantama, ina Yaya Aliyu ina Aisha k’anwata?” Ai gaba d’aya falon sai tsoro ya shigesu, Kaka Ma’u ta taso ta dafa kafadan Dady ta kalli Abba tace “Muktar ko dai fad’uwan da Ibrahim yayi ya samu matsala a kansa ne?” Murmushi Abba yayi yace “lafiyansa kalau, Allah ya dawo masa da hankalinsa ne, kuma wa’innan Kakannin su Aryan ne kuma sune iyayensa, ganin su da yayi jiya ne ya haifar masa da fad’uwa har yayi dogon suma, hakan ne yayi sanadin dawowan tunaninsa na tun lokacin da yana k’arami da Alhajinmu ya bigeshi ya rasa tunaninshi” Gaba d’aya falon sun girgiza da zancen Abba, amma banda Abba da Mai Martaba sai Hajiya Kaka, sune kad’ai suka San wannan abin, saura duk sun d’auki Dady d’an uwansu ne na jini. Falon ya cika da kabbara tare da yiwa Allah tasbihi, Malam da inna kuka suka sanya, Umma ma haka su Ammi ne suka taso suka shiga basu baki, Aryan mamaki ya cika shi ya shiga zancen zuci “dama ashe Dady Babansu Meena shine Yayan Umma wanda ya b’ata tun yana k’arami, tasha gaya musu, wani lokacin har kuka take yi suna lallashinta” Khadija ce ta taso ta fad’a jikin Dady ta shiga kuka sosai cikin kuka tace “Dady dama kai Abbanmu ne bamu sani ba, Abbanmu ya rasu shekaru kusan bakwai da suka wuce” K’ank’ameta yayi ajikinsa yace “Innalillahi wa inna ilaihur rajiun, Baffa wannan ‘ya’yan Aliyu ne ashe? Yaya Aliyu ya rasu? ina Matarsa take?” Malam ya share hawayensa ya nuna masa Umma yace “had’in zumunci muka yi musu da k’anwarka Aisha, wancen Yaro Aryan shine babban d’ansu sai Khadija ga tanan itace k’arama, Aliyu ya rasu da kewarka sosai, wani lokacin da girmansa ma kuka yake yi yana jimamin rashin ka, kullun zancenmu ko ka mutu ko kana raye, bamu tab’a tsammanin zamu sake had’uwa da kai ba” Sai ya k’arasa maganan yana fidda kwalla, da sauri Dady ya janye Deeja daga jikinsa ya isa wurin Umma, kama hannunta yayi ya kaita tsakiyan falon yace ‘ “kunga k’anwata Uwa d’aya Uba d’aya muke, na tafl na barsu tsawon shekaru, yanzu gashi Allah ya had’amu, abin mamaki da ikon Allah ashe itace Mahaifiyarsu Aryan, bamu tab‘a had’uwa ba” ya waigo ya kalleta yace
“Aisha kece haka? ashe Yaya Aliyu ya rasu” kuka Umma ta sanya, saboda nan take zafin mutuwan Mijinta ya taso mata, Dady ya maidata mazauninta. Abba ne ya mik’e ya kama hannun Dady yace “baka rasa Aliyu ba tunda gani a tare da kai, zoka zauna ka kwantarda hankalinka, wannan kukan da kuke ya isa haka, Farin ciki ya kamata muyi da godewa Allah bisa wannan Al’amari” Dady baima Abba musu ba ya bishi suka zauna, falon yayi shuru sai sasshekan kukan Deeja ke tashi da Umma, su Basma ma kukan suke dan jin wannan bak’on Al’amari, Su Yaya Ahmad tsoron Allah ya hanasu magana,Yaya Aryan kuwa sai ajiyan zuciya yake yi, idununsa sunyi jaaa hawaye yana bin kunshinsa.
Hmm