YAR SHUGABA
CHAPTER 31
‘Bayan Sallan lsha’i’ Su Yaya Ahmad sun kawo Ango Aryan, tunda suka shigo gabansa ke fad’uwa ya rasa natsuwan sa, nan su Yaya Ahmad suka yi musu d’an tunatarwa game da aure sannan suka yi musu sallama, da kyar Basma ta saki Meena sai kuka take yi, haka suka tafi tare da yi mata sallama. Yaya Aryan ya rakasu har mota saida yaga wuce wansu kana ya koma cikin falo ya zauna ya cire hulan kansa yana fifita dashi domin duk sanyin AC dake d’akin gumi yake yi, maida hulan yayi ya mik’e ya nufi d’akinsa, ruwa ya watsa tare da d’auro alwala ya sanya farar jallabiya ya fito falo, ya shiga kitchen ya d’auki plet tare da cups, hannunsa rik’e da ledoji ya nufl d’akin Basma. Ya sameta zaune gefen gado fuskarta rufe da mayafl, zama yayi kusa da ita yaji kansa ya sara mishi d’aurewa yayi ya yaye mayafin, d’ago fuskarta yayi cikin murya k’asa-k’asa yace
“Amaryata kinsha k’amshi, anya zaki rik’a barina ina fita kuwa? dan k’amshin ki kawai zai rik’a riki tani in kasa fita”.Murmushi tayi tace “anya kuwa myn?”
Murmushi yayi shima yace “Eh mana, tashi ki d’auro Alwala muyi Sallah” Cikin murmushi tace “ina da alwala ban dad’e da idar da Sallan lsha’i ba” “ok tashi mu gabatar da Nafila” ba musu ta mik’e. Sun idar da Sallan Nafila Raka’a biyu ya kama kanta ya mata Addu’a’o’i, kana suka yi Addu’a gaba d’aya suka shafa, kayan ciye-ciye ya zuba a plet d’in sannan ya zuba mata yoghurt a cup ya kai bakinta kamar ba zata amsa ba, ta bud’e bakin a hankali tana sha, haka ya ciyar da ita komai da hannunsa harsai da ta ce ta koshi kana ya rabu da ita yaci nashi
Bayan sun kammala ya kwashe kayan ya maida kitchen ya rufe ya koma d’akin ya tadda Basma ta sauya kayan barci ta kuma shiga bayi ta wanke baki, kwanciya tayi akan gadon taja bargo tana dariya k’asa-k’asa tace “Myn saida safe”Murmushi yayi yace “ok Allah ya tashe mu lafiya” sai ya zauna gefen gadon ya dafe kansa, tunani iri-iri yake yi amma ya gaza sanin ina hankalinsa ya dosa, jallabiyansa ya cire ya zagaya d’ayan side d‘in gadon ya kwanta, kansa yana ta sarawa d’auriya kawai yake yi, cikin k’ank’anin lokaci idonsa yayi jaaa, hakanan tsoro yaji ya diran masa, Addu’a ya shiga yi dan neman yardan Allah, cikin lokaci kad’an ya samu rangwame ga yanda yakeji. Jawo Basma yayi tana k’ok’arin zillewa ya d’aurata bisa kirjinshi, gam ya rik’eta sunajin bugun zuciyan juna, cikin rad’a yace mata a kunne “Rashinki yasa dare ya zame min rana bana iya barci, na shiga k’unci da damuwa, ya zanyi in misalta miki Son da nake miki ki fahimci zuciyata, my Queen kin zama b’angare na jikina bazan iya rayuwa ba ke ba”
Hawaye mai zafi yana bin idonsa kansa nayi masa tsananin ciwo, Basma ta d‘ago kanta tana kallon fuskansa, cikin kasala da damuwa tace Myn ka daina min asaran hawayenka, wannan ranar mukejira tazo, dan haka farin cikinka nake so ka nuna min a yau da mai cike da so da k‘auna”.
Hawayensa ta goge masa, rungumeta yayi tsam ajikinsa tare da sakin ajiyarzuciya. Daga nan kuma salon ya sauya, suka lula duniyar masoya, soyayya suke nunawajuna mara misaltuwa, sun gama kamuwa sosai, Aryan yana k’ok’arin kai ga biyan buk’atansa jikinsa ya soma rawa, nan da nan zazzab’i ya diran masa kansa yayi zafi kamarwuta nan take kwayan idonsa ya sauya kala yayi jaa kamar garwashin wuta, cike da tashin hankali ya ja jikinsa yana haki, Basma ta kamo hannunsa domin ta fara kamuwa dan maganin da tasha suna matuk’ar aiki ajikinta, fincike hannunsa yayi da k’arfi ya mike jallabiyansa ya maida ya koma gefen gadon ya zauna tare da dafe kai. Kuka Basma ta fashe dashi tanata juyi a kan gadon, kukanta ya k’ara tayar masa da hankali, cikin mutuwar jiki ya mik’e da nufin barin d’akin,jiri ne ya kwashe shi ya zube akan gadon yana rawar sanyi, Basma hankali ta yayi matuk’ar tashi, cikin k’arfin hali ta mik’e ta matsa kusa dashi, a can k’asan mak’oshi Aryan ke fad’in “Basma dan Allah ki matsa a kusa dani mutuwa zanyi, in kina kusanto ni azaba nakeji“ Kuka Basma ta fashe dashi da k’arfi tana fad’in “Innalillahi wa inna ilai hir rajiun .mik’ewa tayi ta shiga bayi ta d’auraye jikinta tare da yin Alwala.Al’Qur’ani ta d’auko ta zauna nesa dashi ta soma karantawa a nutse tana kuka, dafe kunnuwansa yayi bai sonjin karatun amma bai hana karatun na shiga kunnensa ba, a hankali ya soma samun natsuwa, da k’arfi ya saki ajiyan zuciya,juyowa yayi yana kallon Basma hawaye na zuba masa, daina karatun tayi ta aje Al’Qur’anin ta dawo gefensa,fuskanta d’auke da murmushi tace “Myn sannu yajikin da fatan baka jin komai yanzu k0” Murmushi ya mayar mata ya share hawayensa, mik’ewa yayi yana tangad’i, ta mik’e zata kamashi ya daga mata hannu cikin dishewan murya yace
“Kina tab‘a ni ciwon zai dawo” ido ta zaro waje tare da toshe bakinta hawaye na fita a idonta, haka ya fita zuwa d’akinsa, wanka yayi ya sauya kayan ya fad‘a gado sai barci mai nauyi ya d’auke shi. Basma zama tayi gefen gado tana kuka wiwi ba mai taimakonta, tunani barkatai take yi amma ta gaza fahimtar komai, mik’ewa tayi ta gyara shinfid’ar gadon ta kwanta, cikin
k’ank’anin lokacin barci ya d’auke ta. ‘Washe Gari’ Basu suka farka ba sai bayan k’arfe takwas na safe, cikin sauri Basma ta fad’a bayi tayi wanka tare da d’auro alwala, ta gabatarda Sallan Asuba tayi dukkan Azkar na safe kana ta tashi ta shirya cikin Riga da sket na atamfa ta d’aura d’ankwali, ba wani make-up tayi ba ta fito falo ta samu Yaya Aryan yana zaune, ta k’arasa falon ta zauna nesa dashi kanta a sunkuye ta gaishe shi, cikin fara’a ya amsa “My Queen hop kin tashi lafiya?” Laflya lau Myn, uhum yajikinka?” “da sauk’i ai na warware”
“tom masha Allah, Allah ya k’ara afuwa, amma ka tashi da wuri shine baka tashe ni ba?” “Wallahi naso tashin ki, dan harna isa k’ofar d’akin sai naji gabana na fad’uwa sai na dawo kawai” D’ago fuska tayi ido cike da hawaye tace “amma Yaya Aryan a da baka jin irin haka, meyasa yanzu haka ke faruwa?” tana zubda hawaye. ‘ Mik’ewa yayi da sauri ya kamota ta mik’e tsaye, rungumeta yayi tsam ajikinsa, take ya fara jin zafin jiki da ciwon kai, saketa yayi suna kallon juna yace Basma bansan me yake faruwa dani ba, tun bayan kwana biyu da suka wuce, duk lokacin da kika zo kusa dani ina shiga cikin mawiyacin hali, kaina ya rik’a min wani irin ciwo tamkar zan mutu,jikina kuma tamkar garwashi, a yanzu haka inajin abinda nake gaya miki a jikinsa” Zuba ma juna ido suka yi, tace
“Myn zan kira Yaya Ahmad in sanar masa domin anima maka magani” Kama hannunta yayi yace “karki gaya masa saboda kar mu tada musu hankali, yanzu dai ki cigaba damin Addu’a, zo muje mu karya tun d’azu aka aiko mana da breakfast daga gida” Hannunta ya kama gam suka wuce dinning sunci sun koshi, suna yi suna hira kamar babu wata matsala a tare dasu. Da midalin k‘arfe biyu na rana Mutane suka fara zuwa, Yaya Aryan fita yayi ya basu guri. Basma tana tare dasu Deeja a d’aki sai tsiya suke mata, murmushi kawai take yi dan ita kad’ai tasan halin da suke ciki, kamarta gaya musu amma saita fasa. haka suka yi mata yini sai dare su Yaya Ahmad suka zo suka kwashe su. Basma na gefen Aryan yana nishi sama-sama, abinda ya faru jiya shine ya kuma faruwa yau, kuka Basma take yi mara sauti, Addu’a take yi tana tofa masa, a hankali ya samu natsuwa ya hau saman gadon ya gyara kwanciyansa, yau baijin zai iya taflya ga shi bai wankejiki ba, haka barci ya d’auke shi mai nauyi. Basma tashi tayi ta wankejiki ta d’auro alwala Sallan Nafila ta gabatar tare da jero Addu’a, Allah ya kawo musu d’auki cikin matsalan su.
Nima dai na taya su da Ameen. Bayan mako biyu‘ Su Basma suna cikin wannan halin babu wani sauyi, duk sun rame sunyi haske, d’an kyau da Amare su keyi su sam ba suyi ba. haka suka shirya suka nufi gida dan su gaishe su, sun isa ko wani part sun gaishe su, President yayi tafiya dan haka basu sameshi ba.
Part d’in Yaya Ahmad suka nufa, hira suke sosai Yaya Ahmad ya kalle su yace cikin kulawa “Aryan, Basma anya babu wata matsala kuwa a tattare daku? kunga yanda kuka yi rama sai haske da kuka yi kamar wanda suka farfad’o daga ciwo” Murmushi suka yi, Yaya Aryan yace “Abokina mu da muka yi Auren soyayya ai babu wata Matsala da zai samu damuwa, kawai dai duk cikin Amarci ne muka koma haka, ko ya kika ce My Basma?” Murmushi tayi tace “sosai ma kuwa Mijina, hankalin mu kwance yake ba wata damuwa” Yaya Ahmad yace “to Alhamdulillah naga yanda kuka sauya ne lokaci guda, dole muyi zargin ko da Matsala” ‘ Yaya Aryan yace “aiko ba zamu sake zuwa ba sai munyi k’iba sosai, dan d’azu ma Ammi tirkemu tayi,wai me yake damun mu duk mun fita hayyacin mu” Dariya duk suka saka yaya Ahmad yace “Allah kuwa duk wanda ya sanku kafin aure in ya ganku yanzu sai yace kunyi rama” Deeja tace “raman ma sosai kam, kuma abin mamaki gaba d’aya suka yi raman, Allah yasa dai lafiya” Harara Yaya Aryan ya watsa mata “me kike nufi? kina nufin baki gamsu da abinda muka fad’a ba” mik’ewa tayi da sauri tana dariya tace “sosai kuwa, ai daga kai har Basma bakin ku d’aya, kuma shegen miskilanci ne daku” tana gama fad’an haka ta bar wurin da gudu dan kar Yaya Aryan ya mata hukunci. Haka suka gama yinin su sai dare suka koma gida cike da farin ciki, suna isa gida, gabansu ya fara fad’uwa sun riga sun sadak’ar yau ma abinda suka saba fuskanta ne zai faru, sun kuma kasa hak’ura dajuna, dan kullun sai Aryan yayi k’ok’arin kusantarta, amma abin yaci tura.
Yaya Ahmad yana kwance a d‘aki ya juya ya kalli Deeja sai barci take yi, tunanin su Basma ya kasa b’ace masa a zuciya “kuma ya kasa yarda da abinda suka gaya masa, yasan wannan karan Basma ba zata tab‘a gaya mishi damuwarta ba tunda tana Son Aryan, sannan kuma yasan yanda Aryan ke Son Basma bazai cutar da ita ba, to me yake damunsu su biyun? meyasa su kayi rama haka?” Tambayoyin da yakewa kansa kenan wanda ya zaga samun amsansu sai a bakin Aryan da Basma zai samu, gyara kwanciya yayi da niyyar gobe in Allah ya kaimu zai je gidan da safe yaga abinda ke faruwa ko ya matsa musu su gaya masa. Da wannan tunanin ne barci ya d’auke shi. ‘Lallai Aryan akwai wata matsala a tare da kai, ko meye ne…?’
Hmmm yau dai dasan na tarwatsa farin cikin Makaranta wannan littafin, sai dai ince kuyi min hakuri haka na tsara Iabarin, kuma ina da dalili, insha Allah za kuyi farin ciki a nan gaba. Godiya gareku masoyana da irin Addu’an ku gare ni. Ina sonku sosai irin da yawa d’innan Allah yabar zumunci