YAR SHUGABA
CHAPTER 7
Basma da Deeja suna tafe a hankali a cikin mota, Basma ta kalli Deeja tace “Deeja dan Allah ina son ki bani tarihinku a tak’aice in ba damuwa” murmushi Deeja tayi tace “ba damuwa Anty Basma” nan ta fara bata labarinsu tas a takaice, har suka isa Asibiti
zancen suke yi, Basma tana girgiza kai alaman tausayawa sosai. Bayan sun isa Asibiti, suka tadda Yaya Ahmad a office d’insa, ya duba Deeja ya k’ara bata wasu maganin kana ya sallamsu yace “an gama ba zata k‘ara dawowa ba” Basma ce tace
“ok Yaya godiya muke” murmushi yayi mata yace a cikin harshen yaran barebari, “Basma, Khadija tana da kyau, k0 kin lura da haka kuwa?” da murmushi a fuskanta ta mayar masa cikin yare, “sosai ma kuwa, haka Yayanta yake kuma yama fita kyau, ita tafl kama da Ummansu” murmushi yayi yace cikin sigar wasa “to kina ganin inna zab’eta tayi?” zaro ido tayi waje tace
“Yaya talakawa ne fa, amma kana ganin su Ammi zasu yarda?” dariya yayi sosai yace “mai zai hana suk’i yarda, damu dasu duk d’aya muke a gurin Allah, face wanda yafi wani imani, kawai ke zaki wayar da ita sosai ta zama kamar yanda kika waye, sannan zan sata a makaranta tayi karatu, kinga ai shikenan ba mai hanani aurenta” murmushi tayi tace “hakane Yaya Ahmad, ni ai wallahi ka sani farin ciki sosai, dama kuwa kasan abin da nake shiri kenan na maidata makaranta” dariya yayi yace “to na rigaki buk’atar samun Ladan” itama dariya tayi tace “yauwa Yaya Ahmad, ya za ayi ka samar ma Yayanta aiki a company Abbanmu, yana da diploma a computer science, kaga in an d’aukeshi sai ya koma karatunsa, yayi digree da masters, kuma yana aiki ana biyansa salary mai kyau” murmushi yayi yace “shawara mai kyau, kinga mun taimake su, tunda suna cikin buk’atan haka, kuma dama amfanin Arzikin kenan, in ka samu ka bama na k’asa da kai, zansa ma a k’ara yiwa unguwarsu titi, zamu d’auki matasan unguwan marasa k’arfi mu sanya su a makaranta, dan naga unguwar akwai mabuk’ata sosai” tace “da kyau Yaya Ahmad, wannan shawaran yayi, Allah ya bamu ikon yi” yace “Ameen” duk wannan hiran cikin yaransu na barebari suke yi, Deeja tayi shuru tana saurarensu amma bata fahimtar me suke cewa, computer science d’in da Basma tace, shine ya bata damar
fahimtar k‘ila hiran da sukayi da ita ne, take gaya masa. Mik‘ewa Basma tayi tace
“Yaya bari mu tafi” murmushi yayi yace a cikin harshen labaraci “ki kulamin da Matata, karki sake ki gaya mata ba yanzu ba tukun, kuma ina so ki b’oye musu asalinmu, saboda su samu damar sakin jiki damu” murmushi tayi tace itma cikin yaren”ai Yaya bazan fad’a ba, zance musu Mom d’nmu da Dad basa k’asarnan suna Canada, muke Nigeria da sauran family d’inmu, kuma gidan hutuna shine gidan iyayenmu, kaga bazasu gane ba” Cikin harshen turanci yace “good girl” tana dariya suka fita, Deeja dai jinsu takeyi, tad’an so ta fahimci hiran amma bata gane ba saboda batajin barbanci sai kalmomi kad’an take iya tsinta. Suna tafe a hanya suna hira a yanzu Deeja ta saki jiki sosai da Basma, koda suna kusan sa’a amma akwai girmamawa na musamman da Deeja kewa Basma, Basma tace
“Deeja zamu shiga kasuwa siyayya” tace “to Anty Allah ya kaimu lafiya”. Sunje Babban shago na saida kayan kanti, side d’in maza suka fara shiga, riga da wando ta siya kala biyar k’ananun kaya, sai manyan kaya shadda da material na maza kala biyar d’inkakku, sai su singilet da gajeran wando guda biyar-biyar, sai takalmi kala hud’u, huda kala biyu, da kuma turare masu k’amshi har kala Hud’u, sai a gogo kala biyu. Aka sanya kowanne ajaka, ta bada kud’i aka sanya musu a mota Suka shiga side d’in mata nanma kaya ta sanya Deeja ta zaba kananu da kuma Iesshi da atamfa, hatta gyale, takalma da d’an kunne duk ta siya mata, sannan ta siyawa Umma nata kayan kala uku da mayafi,takalmida d’an kunne da sarka, harda turare, Siyayya suka yi sosai kana suka wuce gida. Suna isa suka fara shiga da kaya, Umma ai bud’e baki tayi tana kallon kayan cike da mamaki, saida suka shigo dashi tas, Basma ta ware na Yaya Aryan tace “Deeja ina d’akin Yaya Aryan yake?” Deeja tace “shine can da yake kallonki” tace “d’akin abude yake?” “Eh a bud’e yake kullun” Umma kallonta take kawai ta kasa magana, Basma ta nufi d’akin ta bud’e, ba laifi d’akin ba wari yana k’amshin turaren wuta na tsinke, sai dai d’akin akwai datti da tarkacen kaya, aiko shiga tayi ta bud’e k’ofar, ta fara kauda kaya kana ta samu tsintsiya ta share d’akin, har wani gumi ta had’a abinda ba’a saba yiba, Deeja tazo zata tayata tace ta barshi itama zata iya, tana gama sharan ta kakkab‘e zanin katifar ta gyara kana tazo ta kwashi kayan data siya masa ta aje gefe guda, ta flto tana sharce zufa, Umma
ne tace “Sannu da k’ok’ari Basma Allah ya miki albarka, ya baki miji nagari, yasa ki gama da duniya lafiya” ta k’arasa maganar tana matsar kwalla, Murmushi Basma tayi ta k’arasa kusa da Umma, zama tayi gefenta a kan tabarma tace “Umma na d’aukeki Uwa a gareni, duk abin da na muku na yiwa kaina ne domin Uwata nayi mawa, kuma Umma meye amfanin kud’in da za’a tara a aje ba’a yi taimako dashi ba, ki d’auka tamkar ke kika haifeni Umma, domin Allah ya riga ya had’amu, iyayena basa nan suna k’asar waje dagani sai Yaya na Ahmad da kuma sauran danginmu, lokaci-lokaci suke zuwa nan domin mu munk’i zama dasu, munfi son zama a k’asarmu, Umma iyayenmu suna bamu kud’in wanda bamu san me zamu yi dashi ba saboda yawansu, kinga kuwa
danna bayar wa Alumman Annabi bamu Fad’i ba” Da murmushi a fuskan Umma tace “kwarai kuwa Allah ya saka da alkhairi” Ameen Umma, kuma nayi magana da Yaya na yace zai mai da Khadija makaranta, yace in gaya muku kaf’ln yazo” Umma cike da farin ciki mara misaltuwa ta rungume Basma, Deeja kuwa tsalle tayi ta dawo kusa da Basma, godiya ta shiga zuba mata sosai tamkar ta biya mata saudiya. Haka sukaita murna suna zuba mata godiya, Basma ta d’auko takadda ajakarta ta shiga rubuta short note, ta bama Yaya Aryan hak’uri akan abinda tayi masa. Tana gama rubutawa ta mik’e ta je ta sanya letter a cikin d’aya daga cikin jakukunan kayan data siya masa, kana ta fito ta d’auki Jakarta tayiwa su Umma sallama, Umma har k’ofar gida ta rakota tana shi mata da albarka tare da addua, Deeja kuwa har mota taraka ta. Basma na isa gida wanka ta yi ta dad’e cikin ruwan zafi tana gasa jiki domin yau ta kwaso gajiya, tana fitowa ta shirya ta wuce part d’in Momynta, ta same ta zaune bisa dadduma ta idar da sallan La’asar, zuwa tayi ta kwanta ajikinta cike da shagwab’a tace “Momy kin jini shuru yau baki nime ni ba?” murmushi tayi tace ai kwanakin nan naga kamar kinyi hankali ne, kodan basu Leema ne k’ila” dariya tayi tace “kai Momy, dama can ma haka nake, hala su Na’im suna islamiya?” “eh suna can, wai ke kuwa yaushe rabon da naga kina karatun al’Qur’ani?” murmushi tayi tace “Momy ina karantawa bayan sallan Magrib da kuma in zan kwanta barci, a wata sau biyu nake saukewa fa” “Masha Allah haka nake so ki rik’a kula da ibadarki sosai” “tom Momy zan kula insha Allah, Momy dama ina son muyi magana akan yarinyar dana bige rannan, sunan ta Khadija” nan ta shiga bama Momy labarinsu kaf da kuma abubuwan da tayi musu, da ma taimakon da take shirin yi musu ita da Yaya Ahmad, Murmushi Momy tayi na farin ciki tace
“Basma ban tab’a tunanin kinyi hankali irin haka ba sai yau, wannan abu da kike yi ‘tunani ne mai kyau, nima zan bada tawa gudun mawar akai, sai muyi tarayya a cikin Ladan gaba d’aya, zanga Ahmad saimu tattauna akan gyaran unguwar da taimakon mutanan unguwar, Allah ya bamu ikon yi da iklasi” tace “Ameen Momy, kin amince in cigaba da taimaka musu kenan?” “sosai kuwa na amince, ai in dai wannan ne sai inda k’arfi na ya k’are wajen baki goyen baya, kuma mun taimaka wa Abbanku ne, tunda shike Mulkar k‘asatar nan” “hakane Momy” kamar zata gayawa Momy k’udirin Yaya Ahmad akan Deeja saita fasa, saboda ta d’aukar masa alkhawari akan bazata gayawa kowa ba. Haka suka cigaba da hira na ‘Ya da Uwa har barci ya d’auke Basma, Momy kuma ta cigaba da lazumi, sai gabda sallan Magrib ta tasheta, sannan duk suka nufi d’aki.
Yaya Aryan ya dawo da yamma lis,ya samu Umma tana tuka tuwo, ya gaisheta kana ya nufi d’akinsa, yana tura k’ofa ya shiga yaga daki fes an gyara, bai k’ara tsinkewa ba saida ya hango jakukuna a gefe, da sauri yajuyo ya kalli Umma yace
“Umma waya shigan min d’aki kuma jakukunar waye a ciki?” Murmushi tayi tace
“ka shiga ka duba akwai sak’on bayani a ciki” Deeja ce tayi tsaraf tace “Yaya Aryan kayanka ne da” bata k’arasa ba Umma tayi mata dakuwa tace “yi min shuru a wurin nan, ya shiga ya gani mana da kansa, ya tsaya yana tambaya”jikinsa a sanyaye ya koma d’akin, zama yayi dirshen a ledan d’akin, ya shiga bude kayan dake jakukunan d’aya bayan d’aya, harya isajakan da huluna da agogo ke ciki, yana ciro hula sai letter ya fad‘o, da sauri ya aje hulan ya shiga bud’e letter, gyara zama yayi ya soma karantawa kamar haka ‘Assalamu Alaikum’ “‘Yaya Aryan nasan zaka yi mamakin ganin sak’o na, da farko ina mai baka hak’uri akan duk abin da na yi maka kwanaki, hak’ik’a nayi kuskure, kuma naji kunya d’azu sosai, saboda bansan kaine Yayan Deeja ba. “‘Yaya Aryan wannan kayan naka ne, a matsayina na k’anwarka na siya maka, karka d’aukesu a matsayin na raina maka ne, wallahi nayi maka dan Allah ne, domin a yanzu ka zama Yaya a gareni.“
“‘Dan Allah kar kace ba zaka sanya kayan ba, domin in kayi amfani dasu, hakan ne zai nuna min ka yafemin akan abinda ya faru tsakanin mu, kuma ka d’aukeni k’anwarka. Hakan zai sanya ni farin ciki sosai Yaya Aryan.“ ‘Kanwarka Basma Bulama.‘ Nagode.
Wani irin yanayi Yaya Aryan ya tsinci kansa a ciki, komawa yayi ya d’aura kansa bisa katifa, ya kuma karanta sak’on, yayi ta maimaitawa kusan sau biyar, mamaki ne ya cika shi, zuciyarsa yana harbawa a hankali,ji yayi duk kasala ya rufeshi, lumshe idonsa yayi ya shiga tariyo abinda ya faru a tsakaninsu, nan take yaji ta burgeshi yanda take nuna isa kamar wata “YAR SHUGABA‘ salonta ya bashi mamaki yanda tayi saurin sakowa ta bashi hak’uri, sai yaji zuciyarsa ya wanke babu sauranjin haushinta da yake yi, hakanan ya tsinci kanshi da k’ara son ganin ta, yana kissima ya salon zai sauya tunda yanzu sun shirya ba fad’a, murmushi yayi wanda ya k’ara bayyana kyawunsa, a bayyane yace
“nima naso na baki hak’uri, saboda irin k’ok’arin da kika yi akan Deeja, baki cancanci mari a guna ba Basma, kawai dai munyi abun a cikin rashin sani ne, dukda ke kika fara tsokana ta, amma duk da haka zanja aji, domin ki gane ni d’in Namijin gaske ne” Dariya yayi wanda ya bayyana fararen hak‘oransa, ya tashi zaune ya k’ara duba kayan, duk sun kwanta masa arai, godiya yayi ma Allah, kana ya mai da kayan mazauninsu ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallan Magrib.
Hmm