Yar tallah11

              *YAR TALLA*

            

              *CHAPTER11*

*ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana*
*fadar. a a  dan Allah kayi hakuri Malam kar ka kashe shi*
*Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawarsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.”
Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi’u da duka kamar Wani zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin* *hankali su suka hana Rabi’u komai saidai kare kansa da yake, sai da yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike yayi waje*
*Hayaniyar suce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana dukan Rabi’u ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta motsa*
*Rabi’u ya ruga malam ya bishi ai
Saina kashe ka la’anannan Allah, Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin gidan nan kai cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka munafukin Allah*
*Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa ‘yan zummokaransa ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, “Kasan inda dare yayi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa ka hadu da mummunan* *hatsarin da za a kasa gane ka, Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah yayi maka wanda . ya fishi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta*
*Allah ya daga maka hankali ya hana nutsuwa a duk inda kake”
Laure ta fito tana fadar, “Don Allah Malam ka shigo gida haka nan tunda dai ka kore shi kaga har ‘ mutane sun fara taruwa.*
*Malam Bala ya dawo gidan yaci gaba da ‘zazzaga masifa tamkar wanda baya cikin hankalinshi, Saude dai na kallon su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba*
*Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana neman Rabi’u can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya*
*hada kan shi da gwiwa da ‘yan kullin tsummokaransa a gaban shi.
Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake tana kiran sunan shi, Rabi’u yayi saurin dagowa yana kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da*
*hawaYe, yayi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. ‘
Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da ‘wani irin kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi’u ya samu da kyar ya iya tsaida nasa*
*kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba
tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba*
*Saude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Kiyi hakuri na san Ubangiji na sane damu ba mancewa yayi da muba, kuma shi ya san* *yanda zaiyi damu, tashin hankalina Saude a yanzu daya ne ‘ yanda zan tafi in barki ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki fuskanta bayan bana nan, bansani ba*
*Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, ‘Dole zan tafi’, dole zan bar garin nan Saude kiyi hakuri ki rungumi rayuwa a duk yanda tazo* miki kar ki yarda ki sabawa Ubangiji *a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0 kishiyar hakan. Na ‘ san insha Allahu Ubangiji ba zai bar rayuwarki ta lalace ba*
*Yasa’hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi ‘yan, dari biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya*
*raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, “Ga. wannanki riqe a hannunki kiyi amfani dasu  insha Allahu zaki rinqa samun aikena a duk inda na shiga a fadin
duniyar nan*
*Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar, “Allah ya hada fuskokin mu da alheri.”
Saude tayi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin kuka mai daga hankali*
*Don Allah kada ka tafi ka barni Yaya wallahi mutuwa zan yi idan ka tafi Wayyo Yayana!” Ta qara* *fashewa da wani gunjin kukan Rabi’u ya dafa ta yana kallon* *idanuwanta kafin yace, “Kiyi haquri Saude ni kaina ba dan naso ba zan tafi inbarkiba,da zaiyiwu da dole* *dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne tunda ke macece amma na
yi miki alkawarin duk inda nake a duniya ina tare*
*da…. Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda*
*kukan da ya kwace masa shima. Ya zame hannayenta daga jikinsa yana fadar, “In har kina sona da gaske Saude kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida nina tafi sai wata rana*
*Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar hawayen dake zuba daga idanuwanshi kamar an kunna famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka iya karfinta. Rabi’u na jin ta amma bai waiwayo ba saboda yanda yake jin zuciyarshi na*
*Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba jama’a da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda Saude ta duka bata sake tashi a gun ba, tun tana kukanta iya karfinta har muryarta ta disashe*
*Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga*
*gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana, amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana’ kuka, ba ta ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina’  tana dagowa taga Inna Laure, ta mike ta ‘ kwasa da gudu ta nufi hanyar gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ‘ Tana shiga cikin gidan ma nan ma Malam ya dora mata da nashi dukan yana zaginta tare dayi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu alamun* *tausayawa“ a fuskarta itama ta hau zaginta tana fadin*
*Yar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.”
Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu tsummokaran* *kayan ‘Yar Baba wadanda ta gama dasu ta watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada* *mata yanda zata sanya sannan ta ‘ dora mata tallar wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta fice daga gidan tana matsar kwallah.*
*Haka taje tallar ta dawo bataci komai ba, sai kukan da take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki
alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wunin ranar yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za taga* *Yayanta amma k0 mai kama dashi bata ganiba haka ta karaci yawon tallarta ta dawo da yamma likis.*
*Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman kujera ‘yar tsugunne wadda mata ke cema tayani gulma*
*suna hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da baki tana fadar*
*Kin ganta nan fa dillalliya, wane  aikatau ga wannan ai tallar ce kawai ta dace da ita*
*Dillaliya tace, “Haba dai a ganin ki dai, amma in da nice da wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai.”
Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna Laure* *cinikinta ta mike ta wuce dakinta Tana jin Inna Laure na fadar, “Hmm! Dillaliya kenan aini duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha, to shi kuwa k0 miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi don har na fara tunanin in zuba masa* *shinkafar Bera a abinci ‘yaci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe.*
*Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na ‘ga yarinyar jinin ya zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai dana shiga daki nayi ta dariyar qeta yanda naga Malam na sharar  kwalla.*
*Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo*
*diilaliya na fadin“Ke wai ba zaki saro gyada ki soya mata  ta rinqa zama kofar gida bane ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da* *daddare.” Laure ta ce “Ai k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje ‘Yar Kutungu da kaina in siyo mai kyau*
*in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata*
*Akwai ki da bada  shawara mai kyau*
*Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuiuki wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da mai lallashinta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa*
*Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata a. duniya, basu da* kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta sake rushewa da wani sabon kukan lokacin data tuna da lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan kwalliya. *
*Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan yaga ta shiga damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen nata, ga shi* *yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan za*
*Tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shiba yanzu, wala ya mutu k0 yayi rai. Shin k0 yana a wane hali yanzun ma?*
*“Wai k0 ba dake nake bane Saude kina ji ina ta faman kiran ki?”
Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi*
*Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, “’Yar iska duk uban me kike ina kiran ki kin yi min shiru?*
*Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki tana fadin.*
*“Ke dai kya kai su in kaya ne  wuce ki dora mini sanwar tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki wanke mini su.
*Saude ta yi saurin dagowa ta kalle ta, Laure ta ce, “Bakallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin isa.”*
*Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta taba yin wanki ba, don kayanta ma kala daya ne, duk wani wankin gidan Rabi’u ne ke yinsa. To ta inama zata fara?
Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan*
*ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama
aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman numfarfashi.*
*Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al’amura sun karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare.*
*Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara dagulewa  tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum a wurinta jiya tafi yau*
*Tun tafiyar Rabi’u bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan* *rashinsa wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta ta kwanta ta yi barci, qunci da* *wahalhalun rayuwa sun yi mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin rayuwar da take ciki.*
*Musamman abubuwan da ‘Yar Baba ke mata ya na  damunta, ko’dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma ‘Yar Baba na da shekara sha biyar, amma tafi Saude garman jiki, saboda ita irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan gaBoBin nanne.*
*Ita kuwa Saude ‘yar siririya ce sosai, kamar a hure ta ‘ta fadi, sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa ‘Yar Baba gajeriya ce mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da* *wadatar na shanu, ba laifi ‘ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya.*
*Yar Baba har tafi mahaifiyarta   wurin‘rashin mutunci da rashin tausayi ga gadara da ‘ rashin kunya da tsinannan surutu, kamar aku, ga shi’ Inna Laure da Malam Bala sun dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka samu yana kanta.
Shi yasa ‘Yar Baba ta tashi da* *kwalliya ‘yar gayu ce sosai, suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau.*
*Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana gabda kawowa kofar gidansu ta hango* *wata qaramar mota Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da wasu ‘yan uwa masu ‘mashin’ ma balle mota*
*Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon motar, tana zuwa daf da ita ne ta ga an bude an fito. ‘Yar Baba ce da wani saurayi suka fito daga*
*gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan ledojin nan na shopping.*
*Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side gasu daban-daban, wato wari da wari, wani yafi wani. Hakan yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya takalman duk sun sha faci da Leda.*
*Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin na fadar, ‘Wannan kuma wace ce?”*
*Yar Baba ta tabe fuska kafin ta ce “’Yar talla ce gidanmu take tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?”
Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce “A’a, haka kawai amma dai gaskiya kazama ce,  wallahi bakijiba data wuceni harzuciyata saida ta tashi. ”
Daidai nan Saude ta shige cikin* *gidan tana jin zuciyarta na mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta* *sannan ta dauki abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne ke bi yabe*
*yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna ta soma cin dumaman tuwon.*
*Yar Baba ta shigo niki~niki da ledoji  Inna Laure da ke zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar.
“Oyoyo! Ga ‘yata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka farauto mana
‘Yar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin* *mayafinta mai kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna, gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take.*
*Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala-kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace, daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na manyan mata.*
*Bakin Laure yaqi rufuwa‘ta dubi ,‘Yar Baba tana fadar, “Wannan kuma ina ki ka same shi ‘Yar Baba, dan wane ne a garin nan?”*
*Yar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace, “Wallahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi na dawo daga makaranta. Laure ta rafka guda kafin ta ce, “Da kyau ‘yata tauraruwa cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki dan anan dai haihuwa tayi rana,  Ki dai tsaya ki nutsu ki dage ki shake mana wuyan duk wanda ki*
*Kikeso inja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa daurin huhun goro*
*Yar Baba ta sa dariya tana fadar, “Kai shi yasa nake son ki Laure.” ‘
Ta mike tsaye tana fadar, “Hmm! Gaskiya wani abu na cimin tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar mini da aji a gaban samarina.*
*Laure ta zaro ido “Wace yarinyar?”
‘Yar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, ‘Yo wace ce in ban da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta wallahi data wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar matalauta.”*
*Laure ta ce, “Ai waccan mai kama da igiyar shanyar ni kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.”*
*Yar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune kamar mai rawar taBa-kaka.*
*Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu sunada bakinda ’zasu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa sanin kayanta a duniya kala uku ne suma na Laure ne data gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun wanka k0*
*na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi wanki tadiba aciki tayi wanka.*
*Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata shekaru uku kenan da suka wuce da ‘yan kwanaki. Ta mayar da ‘yar kwallar data ciko mata ido ta ci gaba da cin tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata tsaye a qahon zuciya.*
*Da ranar Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa bokitin alalarta a gaba tana kallon jama’a na ta kai wa da kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take yana faman tsangala kafa da* *shanyayyan hannunsa guda can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda ya shanye
Saude ta Kara hade fuska dan a* *duniya idan akwai wanda ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijone dan a Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani qarami. Yaro*
*Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana*
*faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta*
*dauke kanta taci gaba da kallon wani waje. Garba*
*ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. “sannu da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?” Saude ta jiyo muryar nan kamar an kunna injin*
*markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana*

*Kaiii Na tausayama rabiu Sannan Saude Na ganin rayuwa aradu Mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin cigaban wannan qayataccen labarin daga*
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *