YARIMA MUS’AB CHAPTER 1

YARIMA MUS’AB CHAPTER 1

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tsaye suke ko wacce sanye da uniform mai launin ruwan madara (Milk colour) da kuma kore wanda bai turu sosai ba (Army green) riga da wando sai kuma hijab wanda kadan ya wuce kirjin su(ga musulmai kenan yayin da sauran kabilun zaka bambance su ta hanyar rashin hijab din)…… Dalibai kenan a makarantar ta GIWO SCIENCE ACADEMY dake hanyar barin gari in ka nufi Ningi (wato Kano Road) cikin garin na Bauchin Yakubu…..+

Tsaye a layin Assembly suna sauraren bayanin Principal din nasu cikin harshen turanci ko wacce ta kasa kunne tana sauraran shi in ka dauke dalibai guda biyu dake ta tadin su babu abinda ya dame su tsawa ya daka musu “Zainab nd Saudah! stop this nonsense” turo baki dayar tayi cike da rashin tarbiyya take ‘yan harare hararen ta.

Gama assembly keda wuya ko wacce ta shige ajinsu domin daukan darussa. Mafi yawancin daliban sun hada group ne as usual suna tattaunawa kan abinda Principal yace wato na zuwan d’an sarkin garin makarantar tasu domin Bautar kasan shi (National Youth Service Corps. NYSC) wanda ya zabi yayi a wannan makarantar. Kowa cike yake da zumudi da kuma son ganin shi in ka dauke dalibai guda biyu dake zaune da littafi a gabansu suna dubawa hankali kwance yayin da daga kofar ajin kuma aka shigo yarinyar dai ta dazu ce wacce akaiwa fada lkcn assembly tana taku d’aid’ai har zuwa gaban board din gaba dayansu suka maida hankali gareta tana murmushi take duban kowacce cikinsu kana ta bude baki cikin harshen turanci dai har ila yau (wanda doka ce hakan magana da turanci during classes idan kuka koma hostels sai kuyi yarenku kasancewar makarantar ta boarding ce) ta fara magana “Albishirinku students” daliban da mafi yawansu ‘yan korenta ne suka fara “sai Xieey tamu muna sauraren ki” ta sake murmusawa “shin kuwa kunsan waye zai zo yau?” bata jira cewarsu ba taci gaba “to ba kowa bane face YARIMA MUS’AB dake shirin zama mijina da zarar nayi candy” suka dau tafi da ihu “yeeeey sai Xieey Allah dai ya nuna mana prince dinki” daga musu hannu tayi tare da fadin “saboda haka kowacce cikinku ta kiyaye kar ta sake in kamata da laifin cin amanata in ba haka ba…..” ta jinjina kai tare da wucewa wajen zamanta

Daya daga cikin ‘yan Matan nan ne masu karatu naga tayi murmushi tare da girgiza kai taci gaba da sauraren Kawar ta wacce ke yi mata bayanin wani Topic da bata gane ba……

K’amshin turaren shi ne ya fara aiko musu da bayanin isowar shi wajen kafin ya sako kafa cikin takun shi na jaruman mazaje cike da kuzari bakin shi kuma dauke da sallama gabaki dayansu suka mike tsaye “Gud morning Sir!” suka furta a tare daya bayan daya yake kallonsu kafin ya furta “Morning u can seat down” kowa ya nemi waje ya zauna “Maa Sha Allah” shine abinda naji daya daga cikin ‘yan matan ta furta a hankali nan ya fara gabatar musu da kanshi tare da sanar dasu cewar zai dauke su darasin Chemistry nan take naga wannan yarinyar ta fadada fara’ar ta da alamu wani abun ne yayi mata dadi.

Tambayoyi ya fara jifansu dashi nan take ajin akayi tsit ko motsi baka ji sai chan naga ta daga hannu (na kasa gano muku sunan ta fa readers) ta mike yace “can I know ur name first?(zan iya sanin sunan ki?” ta gyada kai “My name is Hafsat Hasheem Hussain” sannan ta fara mishi bayani dalla2 har zuwa karshe kafin ta koma ta zauna “give her a round of applause class (Ku tafa mata)” raf! raf! raf! Suka tafa don sunsan itace kawai zata iya bada amsa yadda ya dace a cikin su nan ya cigaba da tambayoyi itama ta gefenta ta daga hannu ya daga ta tare da tambayar sunan ta “My name is Hafsat Abubakar Lamido” Nuno ta yayi da yatsa tare da furta “Abbah Sadeeq?” ta gyada mishi kai tana murmushi shima murmushin yayi daga bisani ta bada amsa ta zauna duk wasu tambayoyi shi bayan Hafsat wacce ‘yan ajin ke kira Lamido to fa kaf yarinyar da ya kira da 3ple H a zuciar shi itace ta amsa sosai ta burge shi sedai abinda ya bashi mamaki fuskar ta daure tamau take amsa tambayoyin babu ko ‘yar fara’ar nan….. (Kuji min bako da shisshigi ko miye matsalar shi da dariarta oho).

Idan aka koma ‘bangaren Xieey wato Zainab Ahmad Waxiri kuwa ran ta a dagule yake duk a sanadin murmushin da yayi wa Lamido (to pha).

Tafe suke sun fito daga class kasancewar upstairs suke ‘yan SS 3 suna saukowa wajen shiru bb kowa don duk ‘yan ajin sun nufi dinning cin abinci sai fa su da suka tsaya karisa wani abin+

Suna gab da fita daga wajen sai ga Sir Mus’ab (sunan da suke kiranshi) ya fito daga Library suka matsa da sauri suna gaida shi yayi murmushi yana kallon Lamido “ke amman baki da kirki Yayan naki yazo amman bazaki ko kulani ba ko dan irin a nuna an sannin nan?” tayi dariya “to Yaya ai naga kai baka sanni bane shiyasa ni kuma….” “Ke kuma me? baki son raini ko kar in ce ban ganeki ba” ta sake murmusawa (wanda hakan na lura dabi’arta ce) sannan tace “No kawai banso kamin yadda naga kayi wa Xieey ne” dan tabe baki yayi “au wai wancan gantalalliyar yarinyar? harda wani tattaro kawayenta ita ala dole ta sanni, I totally disliked her wlh” wannan karon dariya tayi sannan ta tambayeshi ya su Ummi (wato mahaifiyarshi) ya amsa da “suna nan lafia, ni saida naji sunan ki ma na tuna tana ta maimaita min diyarta na makarantar nan har sako ta bani fa wai lallai in nemeki in baki” ta murmusa “Allah sarki Ummi nah nagode kwarai daman nasan tafi kowa sona a kaf garin Bauchi” yayi dariya

Tsaki taja kasa2 domin ta fara gajiya da wannan tsayuwar Lamido ta juyo “Sorry Besty na barki tsaye” harara ta banka mata bata dai ce komi ba “Yaya bari mu wuce kaga mutumiyar tawa ta shaka nasan matsalar ta yunwa ce bata iya jurar ta” kallonta yayi “Ayyah to muje in taka muku ko” suka jera suna tafia hankali kwance suna ‘yar hirar su tamkar sun saba (Hafsat da Mus’ab) ita Kam 3ple H bata ko cewa ci kanku har suka isa dinning din

Zaro idanu tayi don ganin babu ko dan ajinsu daya a wajen shikenan time dinsu ya kare (tsarin Schl din shine ko wanne Class da lkcn cin abincin su, kuma yana cika zasu fice dole ko baka gama ba shiyasa Teachers ma basu rikesu da zarar lokacin yayi ake barin kowa ya fito) juyowa tayi ta kalli Lamido da alamar ya zanyi? Idanun ta har sun ciko da kwalla itama Hafsat din jikinta duk a sanyaye sanin yanayin Kawar tata bata juriyar yunwa yanzu sai ta kasa tafia

Tambayar su yayi ko lafia? Hafsat tace “wlh Yaya time ya kure kuma daman ni na bata mana lokaci a Class still kuma mun tsaya magana ita kuma Besty yunwa take ji” ya kalle ta har ta bashi tausayi yace “to ynx me zata samu taci kafin in dawo?” “Akwai cookies da Fanta a hostel bari mu karisa” cewar Hafsat Lamido. Yace “okay kuje ina zuwa ynx” ya maida kallon shi ga 3ple H wacce har ta fara tafia a hankali kamar mai tausayin kasa wanda da alamu yunwar ce don ya lura macece mai zafin nama bata da sanyin jiki “Sorry Sister kinji laifi na ne” karo na farko da tayi murmushi tun farkon ganin shi da ita sannan ta girgiza mishi kai alamar babu komi tayi gaba. “Maa Sha Allah” shine abinda ya furta a kasan zuciyar shi sbd ganin yadda murmushin ya bala’in mata kyau kasancewar tana da dimples ga kuma wushiryar da ya kara bayyana kyaunta a fili ya dafe zuciyar shi yana fadin oh Allah na samo ta! (A rayuwar Mus’ab yana maseefar son mace me dimples yana matukar burgeshi) abin mamaki readers shima fa yana da dimples din…(uhm tabe baki, cigaba da typing)

Suna zaune a ta bayan hostels dinsu tana rike da robar fanta ya karaso wajen dauke da murmushi zama yayi kan ciyawan dake gabanta ya tankwashe kafafu “sannu acici ya jikin naki?” turo baki tayi “ni dai ba acici bace ba kuma lafiata lau” wayarshi ta katse shi daga maganar da yake shirin yi taji yana kwatanta wajen da suke wani mutum ne ya taho dauke da Leda mai tambarin Dudu pharmacy yana sanye da bakaken suit fuskar nan tasha bakar shade ya risina tare da mika mishi da alama daya daga cikin guards dinshi ne

Bude ledar yayi ya Ciro musu takeaway guda hudu sai ice creams,Hollandia yoghurt da kuma Burger kallon Lamido yayi “Sis samo mana plate don ni na tsani cin abinci cikin takeaway” taje ta dauko plates guda biyu da cokala uku harara ya watsa mata ya juye biyu cikin plate daya ya saka cokulan yana fadin “Bismillan Ku ‘yan mata” hararan abincin 3ple H tayi a ranta tana fadin wannan mutumin kanshi na motsi kawai sai in kama cin abinci dashi? Kamar ko yaji yace “Sis bata sanar dake haka akeyi a gidan mu ba ko? Kuma ni gaskia na saba nd also ni fa mijin Bestyn ki ne kuma Yayan ta to miye?” Kama kai Hafsat tayi “Yaya ina kaji wannan zance? Wato daga dawowar ka har Ummi sun sanar dakai ko?” Yayi murmushi “to miye tunda suna so ai dole mu musu biyayya ni har na amince sedai ke idan baki son mummuna” ya fada yana daga gira ta mai hararan wasa tana fara cin abincin Hafsat Hasheem tayi saurin dauke plate din “ai wlh baki isa ba daman shine angon ko ki sanar min?” Ta kai mata duka “to ai gashi kinji so bamu abinci acici kawai” shima yana marairaice “Besty ki bamu mana yunwa fa” ya fada a shagwabe kamar yaro ta noke kafada alamun naki “plead” ta fada tana musu gwalo “please” yace sannan ta ajiye suka fara cin……….

Xieey dake tsaye a inda ta makale tana kallonsu wanda tun zuwansu wajen aka kai mata gulmar ta fashe da kuka tana fadan wlhy baku isa ba Abbah na zan fadawa dole in sami abunda nake so ko mey zai faru……

Kuka sosai Xieey takeyi ta kama hanyar ofishin principal don bata jin zata iya hakura yau din nan
Nocking tayi bata jira ya bata izini ba ta afka ciki ganin ita ne ya girgiza kai cike da takaicin rayuwa irin ta ‘ya’yan manya Sam babu tarbiyya babu ko gaisuwa ta fara magana “Sir ka kira min Daddy na yanzu please” baiyi magana bai sai wayar da ya tura mata cikin gaggawa tayi saka lambarshi don bata da lokacin duba contact ta kira babu jimawa aka dauka domin Dad din yana ganin kiran yasan ita ce yadda yake masifar kaunar ta kasancewar ita kadai ya haifa mace cikin kuka tace “Daddy help me please” hankali tashe jin kukan ta ya furta “me ya faru Momy nah waye ya tabaki fada min duk fadin garin nan” cigaba tayi da kukan tana fadin “nidai Dad zan dawo gida please ka aiko a daukeni YARIMA ne” cikin lallabi yake bata hakuri har dai ya samu ta sassauta kukan nata “to fada min me Yayi miki daga zuwanshi makarantar” “nikam a’a Dad kawai nafi so muyi maganar gani gaka” ta fada cikin shagwaba “to kiyi hkr kinji idan kukayi hutun mid term zan aiko a dauke ki kinji Mama nah” a haka ya lallashe ta ta koma hostels badan taso ba.
+
A yayin da MUS’AB ke chan gurin su Hafsat suna ta nishad’in su don zuwa yanzu 3ple H itama ta sake dashi sai raha suke (nikam ina mamakin wannan dan Sarkin da sam babu ji da kai da kuma miskilanci irin na sarauta a tare dashi). yana daria yace “wai ni Hafsatou black meysa kike son Fanta ne? don zaman mu anan kinsha Fanta uku” ta harare shi cikin sigar wasa “Allah ni Angon Besty ka daina yaushe nasha uku?” Ganin yadda ta turo baki suka hadu suna mata daria ta musu shiru Lamido tace “Yaya in fada maka gaskia Kaine ai baka gane ba wato fa in baka sani ba Besty fullo ce shiyasa take kaunar Fanta da burodi” zaro idanu yayi harda wani kama baki kamar mace “au daman fullo ce ai ban lura ba sbd naganta Blacky shiyasa, kice ma harda Burodi” suka sake kwashewa da daria ita kuwa ta shaka kiris take jira ta fashe ta fara magana “eh anji bak’ar ce kaima ai naga ba fari bane kuma da akeyi da Fulani Allah yasa kuma tushenku kenan sbd haka bazanji haushi ba” ta mike zata tafi suka tashi suma Lamido ta tattara plates din da sauran ledojin suna cigaba da tsokanar ta banza ta musu tayi gaba abinta.
Bayan sati biyu sukayi hutun midterm break don haka wadanda ke cikin gari suka fara shirin zuwa gida don yin kwana biyu kuma da yike alhamis da juma’a ne sai ya hadu da weekend so sai Sunday zasu dawo amman banda masu nisa don sukam babu inda zasu je cikin su harda Hafsat Blacky (nima na d’ana sunan) kasancewar ta ‘yar Gombe tun safe Lamido take mata magiyar kan tazo suje gidansu amman taki yarda Sam har MUS’AB yazo tafiya da ita tace “please Yaya ka kira min Ummi a waya mana” babu musu ya kira ta ya mika mata wayar jin Ummin ta dauka “Hello Ummi nah” murmushi tayi jin muryar Hafsat “Baby nah ya akayi ance kuna tahowa amman shiru naga har Zainab ta dawo” “eh wlh Ummi kinga Besty tak’i tahowa kuma kinga babu inda zataje shiyasa nace muzo tare amman ta k’iya” ta karashe cikin jin haushi Ummi ta murmusa “Oh Hafsatou kenan sam bata son shiga mutane bata wayar” (Ummin tasan ta ne sanadin Hafsat Lamido da yake tana zuwa mata visits) mik’a mata wayar tayi Hafsatou da ta kama kai jin ankai k’arar ta tasan dole taje ta amshi wayar tana gayar da Ummi cikin girmamawa “Haba Momma nah kuma shine zaki ki biyo ‘yar uwar taki ko baki son zuwa waje nah ne?” Ummi ta fada bayan sun gaisa 3ple H ta girgiza kai kamar tana ganin ta “a’a Ummi ba haka bane yanzu zan shirya mu taho” “yauwa ko ke fa ‘ya ta maza kuyi sauri ina Yayan naku yake?” Kallon shi tayi wanda ya zuba mata idanu tun fara wayar yana jin dadin yadda take girmama Ummin tashi sbd yana kaunar ta bai kuma hada ta da kowa ba Hafsatou ta amsa “gashi nan Ummi a bashi?” Ummi tace “a’a kice dai ya taho min daku da wuri tunda direban ya iso” to tace sukayi sallama ta mika mishi wayar tana hararan Hafsat Lamido da har ta hado mata kayanta don zumudi….
Shima hararar ta yayi “malama Blacky yadai kike hararan mata ta” murguda baki tayi “to itama wa yace takai karata gurin Ummi!” yayi daria “ai maganin mai taurin kai kenan kuma nima daga yau na gane in kikayi abu da Ummi zan dinga hada ki” ya fada yana daukan karamin akwatin kayansu zuwa mota da sauri driver ya kariso ya kar’ba ya sanya a but suka shige baya shi kuma ya shiga gabar motan direba yaja suka kama hanyar cikin gari suna d’an taba hira shi da Malam Idi yayin da Hafsat Lamido bacci ya kwashe ta daman ko baccin dare taki saboda za’aje gida 3ple H tana ta kallon gefen hanya yanda ciyayi ke tsere tana murmushi kamar ance ta dago suka hada idanu dashi ta madubi yana kallonta…………..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *