YARIMA MUS’AB CHAPTER 3
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi kokari kwarai wajen ganin yayi yaki da damuwar shi da safe ya isa bangaren Abbah ya gaidashi kamar yadda ya saba idan har yana gidan sedai sama² ya amsa mishi ba yadda ya saba ba murmushi yayi na gefen baki domin yasan makircin waccan matar ce don yana da yakinin ita ce ta zuga Abbahn nashi kan maganar daren jiya..+
Mikewa yayi ya nufi bangaren Ummi da sallama ya shiga suna zaune a falon tare da ita suna ta fira wanda rabi ta makarantar su ce bayan ya gaida ta suma suka gaidashi Hafsa ce ta fara gaidashi “Gud morning Yaya” ya amsa da “Mrng Wifeey” cikin yanayin shi na tsokana zaro idanu tayi kafin ta rufe fuska alamun taji kunya shikam dariya ma ta bashi Hafsatou cikin kulawa tace “Barka da safiya Yaya” murmushi yayi yana kallonta yace “Barka dai
Bestyn mu hope kin tashi qlau” a takaice ta amsa da “lafia lau” nan Ummi tace “to maza masu lattin tashi tunda dai kun makara mukam munyi Breakfast sai Ku tashi maza kuje kuyi anjima kuje ku duba Maryama da jiki don bata ji dadi ba” amsawa sukayi da to suka nufi wajen cin abincin shi da Hafsatou tambayar shi tayi mai zaici yace “duk abinda zaki ci zuba mana” ta zuba musu sannan ta hada musu tea suka fara karyawan cikin nutsuwa take komi yayin da shi kuma duk abinda yake idanun shi suna kanta Ummi na ankare dasu daga inda take zaune “Fatan dai kayi bacci baka saka damuwa ba cikin ranka” Hafsatou ta fada ba tare da ta kalle shi ba “ni kuwa a duniya mai zai hanani bacci tunda kina cikin gidan nan” bakin shi ya furta ba tare da yayi zato ba
Kallonshi tayi da alamun tambaya yayi saurin saita zancen shi wajen fadin “eh mana daman ai rashin fahimta nayi wa zancen amman tunda kika nuna min yadda abin yake tuni na gane kinga ko babu abinda zai hana inyi bacci” ta harare shi domin tasan ba gaskia bane amman duk da haka ta kyale shi ganin taki cewa komi ya dubeta “Anya ko Blacky kinyi bacci kodai tunani na ya hanaki sukuni ne? fada min” zaro ido tayi kardai mutumin nan ya hango jirgin ta yau ta boni duk yadda take yaki da zuciyarta wajen ganin ta hana ta son abinda take ganin ya haramta gareta amman sanda ya gane, ita kam zuciyarta batai mata adalci ba
Amman cikin karfin hali irin nata ta gallamai harara tare da nuna Hafsa tana fadin “kai Malam gata can fa kar santin abinci yasa ka mance da wadda kake tare” shi kuwa da daman tsokanar ta yake don har ga Allah bai fahimci komi a tare da ita ba yace “ke ‘yan mata ai naga Bestyn ki ce so indai da gaske kuke da amincin naku ba sai kawae ku rokeni in hadaku ba hankali ku kwance” ta mike tana fadin “a kai kasuwa nikam domin duk mijin da Besty ta aura tamkar ya haramta ne agareni beside ma ni mai zanyi da mai mata har biyu kuma gaka baki wuluk” ta karasa maganar cikin dariya shi kuwa gabanshi saida ya fadi domin ya razana da jin kalamanta ya mike da gudu ta wuce daki tana mishi gwalo ganin ya biyota ya girgiza kai “Zaki fito ne ai bani kike kira Baki wuluk ba kin manta kwalta ne ni” ya wuce zuwa wajen su Ummi wacce duk abinda suke tana kallon su a ranta tace “yau na shigesu yaran nan ga dukkan alamu sun kamu da soyayyar junan su ya zanyi in ya furta domin tabbas nasan YARIMA sarai baya boye maitar shi”
A fili kuwa dariya tayi tana fadin “ai ramako da azaba nan ka Saka ta gaba da fadin Blacky don kawae yau ta rama”
Hafsa tace “ai kam dai daman Besty bata barin bashi wlhy duk abinda akai mata sai ta rama shiyasa a Schl su Xieey suke ragar min wani abun don suna tsoronta ba karamin aikinta bane ta kamasu ta jibga kuma babu yadda suka iya”
Ummi taji wani abu ya darsu cikin ranta amman ta yaya hakan zai yuwu kuwa? MUS’AB yace “ke kuma daman tsayuwa kike kina kallon su kenan amman dai bakici sunan ki ba don ko Granny bata daukar raini lkcn da take ‘yan mata a kauyen su, a hakan zaki zauna ta dinga rainaki kenan idan na aure kun?”
Remote Ummi ta lalubo ta jefa mishi ya kauce yana dariya “Sannu mai Ido ba dan ciki wato Uwar tawa kake bada labarin lkcn da take budurwa ina ka san hakan?” Cikin dariya yace “to Ummi ba Abbah Sadeeq bane yake bani lbr”
“To naji Zubairu je ka shirya kuje maza ku dubo Addar taku ni banson shiririta irin taka” ya fice yana murmushi abinshi Hafsa ta maida duban ta kan Ummi tana neman Karin bayanin zance shi na idan ya auresu ita da Xieey? Nan Ummi ta kora mata bayanin yadda akayi jiya tana bacci hankalin ta bai wani tashi ba sbd daman bata daura wa kanta kishi ba domin tasan gidan sarauta ba’a cika zama da mace daya ba to amman tana tsoron yadda zata kaya tsakanin su da Xieey wata zuciyar tace to ba ga Hafsatou ba ai zata tsare miki koma miye, wata Zuciar ta sake fadin to tare zaku zauna kenan idan kinyi auren ai itama komawa garinsu zatayi tayi nata auren nan hankalinta ya dan tashi tunawa da tayi cewar ba gari daya ma suke ba ynx ya zatayi? Can wata shawarar ta fado mata to ki roki Yaya Mus’ab mana ya aureku tare ba shikenan ba kuyi zamanku gida daya
Murmushi tayi jin shawarar da zuciyarta ta bata ta mike tana fadin “Ummi bari in shirya kar Yaya ya fito”
Ummi ta bita da kallo tana jinjina sanyin hali irin na diyar ta a ranta tace ko ya zata kaya idan dukkanin su suka fahimci Auta yana son Hafsatou oho fatan ta dai Allah ya kawo musu abin cikin sauki domin tasan tabbas sai ya furta….Shiryawa sukayi Lamido cikin atamfa riga da skirt ita kuma Hafsatou cikin doguwar Riga tayi rolling mayafin shi suka fito nan suka iskeshi har ya shirya cikin manyan kaya har da hula
Wannan ne karonta na farko da ganin shi cikin shigar manyan kaya sai ta tsaya kawai tana kallon shi ba karamin kyau yayi mata ba shima idanu ya zuba mata duk da cewa ba wani kwalliya tayi ba amman tayi kyau sosae, Murmushi Hafsa tayi ganin irin kallon da suke yiwa Junan su sun manta a inda suke dan gyaran murya Ummi tayi da sauri Hafsat ta kauda kai yayin da shi kuma Mus’ab ya sauke ajiyar zucia tare da juyawa cike da kunya ganin Ummi ta kamashi yana kallon H³ ya nufi kofa yana fadin “Ummi sai mun dawo” tayi murmushi ganin yaki kallon ta “to Auta ku gaidasu Allah ya tsare” nan suma suka mata sallama tare da bin bayan shi.+
Parking lot na bangaren Ummi suka nufa inda yake tsaye yana jiransu ya zuba hannuwa a aljihu yana kallon su duka biyun Allah kadai yasan abinda yake kissimawa cikin ranshi
Driver ne ya matso kusa dashi tare da rusunawa cike da girmamawa domin ya hanasu durkusa masa yana fadin “Yallabai zamu fita ne?” Mus’ab ya murmusa “Eh Mlm Sule amman kayi zaman ka ba nisa zamuyi ba” gyada kai yayi tare da komawa wajen zamanshi yana fadin a dawo lafia
Wata Bakar mota ya nufa yana budewa H³ ta shige baya yayin da Lamido ta shiga gidan gaba ya tada motar suka fice daga fada suka nufi Gida Dubu gidan Aunty Maryama Wacce Mus’ab ke bi.
Sosai tsarin gidan ya burge H³ musamman yadda taga falon babu wasu tarkace very classic bayan sun zauna Mai aikinta Zubaida ta kawo musu ruwa tare da gaidasu Mus’ab yana tsokanar ta da cewa “a’a wai nikam Zuby har ynx kina nan to yaushe zamuje L/K musha bikin ne? Tayi dariya Aunty Maryama dake fitowa daga dakin ta ta furta “ai basai kunje LK ba da Dan gida za’ayi” ta karisa tana zama gefen H³ wacce ke kallon Yarima dake ta dariya ta lura yana da matukar saukin Kai fiye da tunanin ta sai Kara burgeta yake.
Gira ya daga wa Aunty yana jiran karin bayani tace “eh ai Mlm Sule direban Ummi ke sonta ai har yaje gida anyi magana” jinjina Kai yyi yana fadin “a gaskia na tayaki murna don Akwai shi da nutsuwa Allah yasa ayi damu” da gudu Zuby ta shige Kitchen suna mata dariya
Nan suka gaidata ta dafa kafadun H³ “Kawar Little Kakus yau kinxo mana ziyara kenan” murmushi Hafsat tayi tana wasa da Kafar Yaron Aunty dake hannun ta Ajmal dake ta leqen fuskar ta yana wangale baki ta mika masa hanu ya kuwa zo
Lamido ta ce “wai lallai Besty kin ciri tuta domin Ajmali ko ni bai yarda dani”
Maman shi tace “fadi gaskia dai Kakus kodai kina mishi mugunta ne” suka yi dariya nan suka cigaba da hiran su
Hafsat gwanar son yara tuni ta goya Ajmal suka shiga Kitchen taya Zuby aiki sai tsiya lamido take mata tana bada Lbrn lkcn da aka kawo Zuby bata iya komi ba sai kauyanci Hafsat sai dariya take..
Basu bar gidan Aunty ba sai wajen la’asar nan ma ba gida ya kaisu ba saida suka zaga gari sosai kafin suka iso gidan..
Yau Ummi ce a bangaren Abbu sbd haka ganin bata bangaren suka nufi site dinsa domin su gaidashi nan suka dan jima yana jansu da hirar makarantar su kafin da zaici abinci suka masa sallama suka koma bangaren Ummi duka su ukun nan suka fara kallo suna dan taba hira a tsakar falon yau Akayi serving abinci suka ci H³ kam ko cokali 5 batayi ba ta koma gefe sam ya lura bata son cin abinci da yawa
“Ke Blacky ance baki juriyar yunwa amman bakison cin abinci sam”
Tayi narai² da fuska “Yallabai ni ka daina cemin Blacky gaskia ko in fada ma Ammi na”
Zaro idanu yayi kamar Mai tsoro “yi hkr Baby abin bekai nan ba so kike Ammi ta hukunta ni”
“eh dai a daina kuma ai duk bakinmu daya naga”
Dariya suka yi ita dai Lamido kallon diramar su take suna sakata nishadi tana kuma kissimawa a ranta cewa rayuwa dasu shine cikar farin cikin ta
Ranar Saturday da safe suna bacci aka taada su wai su shirya su fito Yarima na jiransu a mota babu musu sukayi yadda aka sanar dasu
STORY CONTINUES BELOW
Kaya Kala daya suka saka dogayen riguna Peach wanda Ummi takai musu last visit tsarabar Dubai nan sukayi kyau tubarkallah a gaggauce suka gaida Ummi sbd sai horn Yarima yake suka mata sallama tace Allah ya тѕare
Cikin mota suka tadda shi Lamido tayi saurin shigewa baya nan H³ ma tayi niyyar binta hararan da ya watsa mata yasa bb shiri ta bude gefensa ta shiga “Gud Morning Yaya” Hafsa ta fada
“Morning wify hw was ur night?”
Tayi murmushi jin yaqi daina fadin wify “Alhamdulillah”
H³ ma ta gaidashi “Sir an tashi lafia”
“Lafia lau Mai kan kwakwa” ya fada cikin sigar tsokana
Hade rai tayi “ai nikam I can’t wait mu gama schl ma wlhy sai kaga wacce zaka tsokana”
Murmushi yayi ya juya wajen Hafsa “Wify zamu bar Besty ta koma Gombe ko mu riketa a nan?”
“Yaya kawai mu riketa nima zanfi jin dadi wlh” ta fada har cikin zuciyar ta kuma hakan ne
“Yauwa to Acici sai ayi shirin zama Nanny da kuma aikin wanke² da shara”
“Allah ya kiyaye ku nemi Maid tun dare bai muku ba”
Hanyar da taga sun dauka ne suna shirin barin garin yasa ta kalle shi “Yaya Ina zamuje ne”
“Ke ni banson tmby ki jira zaki gani ai”
Bata sake tmby ba tace “Yaya please a tsaya wlhy bacci bai isheni ba kuka tadani don Allah Besty dawo nan”
Fita Hafsa tayi babu musu ita ta koma baya ta kwanta abinta suka cigaba da tafia..
1hr 48mins ya kaisu cikin Gombe tmbyr Lamido yayi ko tasan sunan Unguwar su nan ta fada masa ya tsaida motar ya fita Dan achaba ya tsare “Malam don Allah zaka shiga gaba ne ka kaimu Unguwa uku wajen gidan uban bala”
“Okay muje” cewar dan achaban
Mintuna kadan suka iso Hafsat dake bacci Lamido ta taso fitowa tayi tana mitssike idanu tare da kare ma wajen kallo kamar a mafarki ta ganta a kofar gidan su da sauri ta kallesu ya gyada mata kai ai wani uban tsalle ta daka bata san sanda ta rungume Yarima ba tana fadin “Thank u Prince”
Murmushi yayi mata Hafsa dake kallonsu itama ta murmusa tana jin dadin ganin aminiyarta cikin farin ciki da sauri kuma H³ ta dago cike da kunya ta kama hannun Besty suka shige gidan da Sallama
Gidan dan madaidaici ne dai² talaka amma tsaf yake ko ina babu datti da gudu Blacky tayi cikin wani daki tana fadin “Ammi na gani nazo”
Ammi dake sallar walaha tayi saurin sallamewa tana mamakin ganin Hafsat da safen nan “ke fa Mami baki girma wlhy ynx babu ko sallama sai ihu kuma ma wai lafia kuwa na ganki,ina fatan ba wani abin kikayi ba suka koroki ba?”
“Haba Ammi daga zuwata bb ko sannu”
“To ai naga ba lkcn hutu bane kuma nasan halinki da Jan magana”
“Toh ni lafia klau hutun Midterm muke” ta fita tare da jawo hannun Hafsa
“Ammi ki canka wace wannan?”
Ammi tayi murmushi “ni da diyata sai na chanka? to naji Hafsatu ce”
Da sauri Lamido ta durkusa tana gaidata cikin fara’a ta amsa tana fadin “daga makarantar kuke ne ynx?”
Hafsa tace “a’a daga gida Yayan mu ne ma y kawo mu yana waje”
Rankwashi ammi tayi wa Hafsat “ke kam anyi ja’ira ynx kuna tafe da bako kika barshi waje kinxo sai zuba kike to maza tashi ki shigo dashi”
Kafin ta rufe baki ma yara sun fara shigowa da kaya daga wajen sa
Hafsat da ta tsani a taba lafiar kanta har idanunta sun ciko ta fice tana zumbura baki zuwa wajen Yarima dake cikin Mota yana faman kallon unguwar
Ganin ta nufo shi ya bude mata motar “ya akayi ne Blacky kike bata rai?”
Cikin sigar shagwaba ta saki hawayen nata “ba Ammi bace ta rankwashe ni”
Janyo hanunta yayi zuwa cikin motan ta zauna ya fara share mata hawayen “to laifin me kikayi?”
“Wai ai bana jin magana haka fa tace daga zuwana kuma wai na barka a waje”
Murmushi yayi yace “ayya sorry ashe akaina ne to yi hkr Baby na”
Kallonsa tayi jin ya kirata da Baby ya kashe mata ido da sauri ta fice a motar tana dafe kirji “ka shigo inji Ammi”
Fitowa yayi ya rufe motar tana gaba yana binta a baya har cikin gidan
Falon Ammi ta shigar dashi wanda suke zaune ita da Hafsa suna tadi yayin da Hafsa ke shan kunu da kosan dake gaban ta hankali kwance
“Besty shine ba jira ko wato abin wariyar launin fata ne”
Daria sukayi Ammi ta dago domin su gaisa zumbur ta mike tsaye shima kallon ta yake gabanshi na dukan tara²…..Tabbas tasan wannan fuskar haka take rayawa cikin ranta amman ta kasa tuna a ina ne nan dai ta koma a sanyaye ta zauna shima Yarima zama yayi a tsakar dakin suka gaisa tamkar sun san juna take tambayar shi mutan gida da aiyuka tare da masa godia.+
Haka nan matar ta burgeshi yaji farat daya yana kaunarta sannan ynx ya gano inda Hafsat ta dauko Kyau sedai Ammi ta fita Haske itama tana da dimples kamar su daya da da Hafsat din
Kunun shima ya zuba yana sha domin duk basu karya ba suka taho suna dan taba hira bayan sun gama ne tace “Mami ki tashi ke da Hafsa ku shiga gidan Baffan ki Ku gaidasu
Hade fuska tayi domin sam ta tsani shiga gidan sbd abinda suke mata amman babu halin taki don babu musu tsakanin ta da Ammi wannan shine tarbiyyar da tayi musu
Yana lura da yadda take famar bata rai sai yabi bayansu yana fadin “Ammi bari nima in zaga Unguwar taku sbd nan gaba kar in manta hanya”
“To a dawo lafia” itama ta mike ta shiga kitchen don daura musu abincin rana
Jikin mota ya tsaya yana kallon su suka shiga wani gida nan kusa da nasu gidan
Da sallama dauke abakinsu suka shiga “Assalamu Alaikum” sun fada yakai sau uku kafin wata mace ta leqo daga daki tana fadin “wai waye ne da hantsin nan yake cika mana gida da kuwwa” ganin su Hafsa yasa ta wani cune fuska gata daman ba wani fasali ne da ita ba tamkar dai kawata Minauwal (Lol)
“Maman Fati ina kwana” Hafsat ta fada a dan dakile
“Eh lallai dole wato rashin kunyar da kika koyo kenan?”
Ita kam Hafsa ikon Allah take kallo daga shigowa taga an fara masifa ko sallamar su ba’a amsa ba
“Wai Lami kedawa kike ta hayaniya ne da safen nan” sukaji muryar namiji yana fada daga daki
“Yo nida ‘yar wajen wancan tsintacciyar magen mana tazo tana min halin fitsarar da ta saba mana”
Da hanzari yaran gidan suka fito suna kallon su cike da wulakanci shima Baffan fitowa yayi
Da sauri suka durkusa suna gaidashi amman bai bi takan gaisuwar ba ya yamutse fuska “ke mai ya kawo ki gida naga ba hutu ake ba ko wani abin maganar kika jawo mana”
Ta girgiza Kai “a’a Baffa hutun Midterm ake kuma ma yau zamu koma”
“Oho sbd ga mai kudin banxa in banda rashin hnkali ki taso tun daga Bauchi zuwa nan kuma ki koma yau yaushe ma aka fara hakan naga baki taba zuwa hutun midterm ba” ya cigaba da masifa babuji ba gani
“A’a fa Baffa Malamin mu ne Yayan wannan ya kawo mu” tana nuna Hafsa
Gyada Kai yake kamar kadangare “Oh lallai iskanci kika koma da Malamai kenan ko?”
Tuni ta fara hawaye tana girgiza kai
“to tashi ki fice min a gida tambadaddiya ina dab da cireki cikin zuri’a ta”
Da sauri tayi hanyar waje tana zubar da hawaye tasan halin Baffa Auwalu amman batasan har zai fara mata zaton bin maza ba Hafsa sai bata hkr take domin ita abin ya daure mata Kai duk da cewa ba yau ta saba ganin kiyayya irin wannan ba don gidan Kakannin su haka suke musu
Yana hango fitowar su lkcn yana zaune cikin mota kafarshi a waje suna dab da karasowa kusa dashi sukaci karo da wani saurayi kana ganinsa kaga kalar ‘yan kalare gashin nan babu kyan gani har sun gota shi ya dawo yasha gabansu
“Ke Mami Dan uwarki baki iya gaisuwa bane?” Ya fada yana wani ciccijewa
Murguda baki tayi “to ni yaushe na ganka”
Wani ashar ya maka “ke ni sa’an ubanki ne kk min rashin kunya” ya daga hannu da niyar Kai mata Mari sai yaji an rike hanunsa ta baya
“Haba Malam da girmanka dukan mace” Yarima ya fada yana kokarin danne bacin ransa
Abunka da kwarjinin Sarauta sai Kamalu ya kasa musa masa ya sauke hanu yayi tafiyar shi ganin kukan da takeyi ya janyo hanunta zuwa mota suka shiga Hafsa na biye dasu itama hawayen take
Hankali tashe yake tmbyr ta me ya faru nan taci gaba da kukan da kyar ya lallashe ta suka shiga gida daman Ammi tasan za’a rina bata ko tambayi dalili ba ta zuba musu jallop din taliya sukaci kafin yaje yayi sallar azahar
Kwanciya Hafsa tayi sai bacci suna ta hira Yayan ta ya dawo daga Shago da tsalle ta suka rungume juna tana fadin “I miss u Yaya Sadiq dina”
Murmushi yayi yana Jan hancin ta cike da farin ciki sosai hannu ya mika ma Yarima suka gaisa zasu kai sa’anni dashi yana cin abinci suna hira da ya gama yayi wanka Hafsat sai binshi take duk inda yasa kafa
Yarima yace “Blacky ki barshi mana ya huta”
Tace “yauwa Ammi ai kinga kullum haka yake cemin Blacky”
Tayi daria “ai kunfi kusa ke dashi”
Ya mata gwalo yana jan hanun Sadiq “Aboki na muje ka nuna min garin naku please”
Itama ta rike dayan hannun Sadiq tace “lallai ji wani wayau ka kwace min Ammi shima Yayan kwace min shi zakayi?”
“Kai habibty ai babu mai rabamu kawai yawo zan kaishi me kikeso in kawo miki”
Ta gane wayo yake son mata amman tayi shiru alaman tunani kafin tayi tsalle “Yaya Ice cream din Havila please ni da Besty”
“Au tare kuka zo?”
“Eh Yaya tana bacci a dakin Ammi na”
“Okay sai mun dawo maa gaisa da ita” inji Sadiq suka fita
Itama kwanciya tayi domin baccin..