YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 25 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 25 BY HARUNA USMAN

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Yanzu al’amari fa ya sake Kazancewa, Sarkin aljanu Sham’una a nasa bangaren sai murmushe aljanu ya ke yi kamar yana murmusar soyayyar gyada, babu ko Shakka ya isa Kasaitaccen jarumi, saboda sadaukantakarsa duk inda ya fuskanta sai a dare a ba shi wuri. Shi ne da kansa ya ke bi da gudu yana kamowa yana kashewa, amma ba dai a tarbe shi ba. A’a, Sarkin aljanu Sham’una ya wuce haka a wurin gama-garin aljanu.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Ran nan sai Karajin mazaje kake ji da hargowa, da ma ko fadan mutane ne yaya, ballantana kuma na aljanu har ma da manyan jaruman sarakuna irin Sham’una da Ifritu?

A takaice dai kwanaki ashirin da daya da aka yi ana ta gwabzawa kafin a rabu don hutawa da kuma sake shiri, kumaa cikin kwanakin nan daidai da rana daya Bangaren Sarkin aljanu Sham’una bai taba samun nasara baa kan daya bangaren. Tsananin yawansu ne kawai ya sa ba a saurin gane irin nasarar da ake samu a kansu, sai dai ko in an kwatanta yawan gawarwakin kowane bangare tukuna.

Bayan an dan natsa ana hutawa sai shi jarumin aljanin nan wanda har yanzu ba a san kowane ne ba ya zo wa Idrisu da wata irin riga da wando da takalmi ya ce masa, “Ya kai Idrisu amshi wadannan kaya ka saka a jikinka kafin a ci gaba da yaki.”

Jarumi Idrisu ya karba tare da tambaya, “To su kuma wadannan kaya mene ne labarinsu da kuma hikimar sanya su? Kai hasali ma kai kanka mene ne labarinka?”

Jarumin saurayi ya ce, “Ya kai Idrisu, labarina dai ka bar shi sai in Allah Ya taimake mu mun kammala yaki, amma labarin sutura da na ba ka shi ne, kaya ne na kare tartsatsi da kuma zafin wuta, don mu aljanu

ZAMU TASHI 

in yaki ya yi yaki, to mukan juya yin amfani da wuta, kuma babu shakka ka san cewa jama’ar Sham’una sun ji jiki sun wahala, Karshe nan gaba kadan ka ga sun fara yin amfani da wuta.”

Idrisu ya yi godiya, kuma zuciyarsa ta natsu a kan amfani da wadannan tufafi.

Wannan saurayin aljani ya ci gaba da sanar da Idrisu cewa, “Akwai fa babbar gwagwarmaya a gabanmu, don har yanzu muguwar tsohuwar aljanar nan shaidanunta ba su fara yaki ba tukuna, ko da yake ba wai muna jin tsoron mayaKanta ba ne, a’a, duk da cewa mun san akwai tsananin wahalarwa saboda irin Kwarewa da siddabarunsu, amma duk da sauki in an kwatanta su da wasu mayu su dari biyu da take da su, wasu jajayen iblisai ne wadanda gaba daya mun hakikance cewa babu abin da zai iya kama su sai dai takobinka kadai.”

Jarumi Idrisu dan Hamidu ya ce masa, “To tun da haka ne wadannan ku bar ni da su kawai, in Allah Ya yarda za mu sami rinjaye a kansu.” Ya dauki suturun wuta da aka ba shi ya saa jikinsa.

Babu dadewa da faruwar wannan lamari sai ga jama’‘ar Sarki Sham’‘una sun sake kawo hari, aka ci gaba da gwabzawa, kawunan mazaje sai zuba suke yi kamar ana kakkabar yalwatacciyar itaciyar Www.bankinhausanovels.com.ng mangwaro.

Sham‘una yana can gefe sai kayar da mazaje ya ke yi babu KakKautawa, ya yanke shawarar Kokarin rage yawan mayakan Bangaren abokan gaba ne tukuna don su ma jama’‘arsa su ga cewa ba su kadai aka fi kashewa ba, wato maimakon ya.bata lokacinsa wurin fuskantar manyan jaruman yaKkin, a’a wadannan yace sai daga baya tukuna. Ko kuma in Bakayalu ta fito ta gama masa da su.

Wannan hari da jama’ar Sham’una suka sake kawowa sai da aka yi kwanaki hudu ana karawa, a rana ta biyar sai aka rika jin dirin takawar mayaka na fitowa daga cikin gari.

Aljana Bakayalu ce da tawagarta.

Ga aljanunta nan jejjere, kowane launi Kungiyarsu daban, bakake da koraye da sauransu. Jeri na shidasu ne jajayen mayun iblisan nan su dari biyu, kumasu ne ke dauke da kujerar aljana Bakayalun wadda take kai a zaune rike da wata Katuwar bakar tukunya ta tsafi.

‘Tsohuwar aljana fa ta duba da kyau ta lura da yadda aka tsara yaKin, sai ta umurci rundunar farko ta aljanu dubu dari biyu da aukawa. Abinka da Kwararru sai nan na nan salon yaKin ya sauya, Bangaren su Idrisu suka fara shan bakar wahala, amma haka Sarki Ifritu da wancan saurayin jarumin

Www.bankinhausanovels.com.ng ke kewayawa filin daga suna ihu suna Kara karfafa wa mayaKansu guiwa a kan cewa ajure, nasara tana kusa.

Aiki ya Karu a kan maza, Idrisu da Sarki Ifritu da wancan jarumin dole suka Kara Kaimi wurin rufar wa musamman wadannan aljanu na Bakayalu wadanda ke murtsuke aljanu kamar suna wasan yara. Cikin wasu ‘yan sa’o’i wadanda ba su wuce bakwai ba sai ga shi wancan runduna ta farko ta Bakayalu sai dai tarihi, don kuwa an gama dasu.

Wannan al’amari ba Kankanin Kara karfafa guiwar jama’ar Bangaren su jarumi Idrisu ya yi ba, suka ji wani sabon Karfi ya shigar musu, saboda haka ko lokacin da aljana Bakayalu ta sako daya rundunar ba su tsorata ba, sai aka ci gaba da gwabzawa kawai, kuma irin yankar Kaunar da aka yi musu a baya ba su yarda an sake yi musu irinta ba.

Lokacin da runduna ta uku na bangaren Bakayalu ta tunkaro cike da wani irin fushi sai jarumi Idrisu ya ja wata babbar tawaga ta aljanu da gaggawa suka nufi bangaren dama, shi kuma Sarki Ifritu da ya fahimcei abin da ake nufi sai ya janye wata tawagar da gaggawa suka nufi hagu, kuma kafin a hade da abokan gaba tuni wadanda suka yi dama da wadanda suka yi hagu din suka yi wa wancan runduna ta jama’ar Bakayalu zobe suka sa su a tsakiya suka hau su da kisa babu

Www.bankinhausanovels.com.ng kakkautawa, shi kuma wancan matashin aljani abokin su Idrisu ya dirar musu ta tsakiya.

Yaki fa ya kankama yadda ya kamata, a haka dai cikin kwanaki tara da fara artabu da mayakan aljana Bakayalu sai ga shi an cinye mata rundunoni hudu, kuma ba tare da Bata lokaci ba runduna ta biyar ta shigo, wadanda daga su fa sai jajayen mayun nan wadanda har yanzu aljanar ke kan girkawa, sunajiran lokacin shigarsu ya yi.

Shigar runduna ta biyar fa sai yaki ya koma na feshin wuta, da kuma jefa mulmulen wuta, bayan sun kammala sai kuma aka shiga gwabzawa gaba da gaba, yaki ya yi Kamari, sai da aka yi kwana_ hudu ana gwabzawa da wannan runduna. A rana ta biyar Bangaren su Idrisu suka sami nasara, abin kamar a labari.

Kaka-tsara-kaka, yanzu fa abin da ya rage wa aljana Bakayalu na jarumai sai dai mayun aljanunta kawai, kuma babu shakka lokacin shigarsu fagen daga ya yi, saboda haka sai bangaren Sham’una ya ba da umurni ga mayakansa da ke cikin filicewa gaba dayansu, har shi kansa Sham’una din su janye, don jajaye za su shigo.

Dalili kuwa shi ne, ita Bakayalu a irin girka da

tsafin da ta yi wa wadannan shaidanu, da zarar suka

Www.bankinhausanovels.com.ng shiga fagen fama, to duk abin da ke cikin filin halaka shi kawai za su yi, ko mene ne kuma kowane ne, to da zarar sun kammala sai ta sake yin amfani da tsafin don sake mallake su, fitinarsu ta koma karkashin ikonta.

Ganin mayakan Sham’una suna janyewa daga fagen fama suna komawa baya har da shi kansa uban gayyar, da kuma lura da cewa wadancan jajayen iblisan sun fara tunkarowa zuwa cikin fagen fama, sai Idrisu ya tuna da bayanin da wancan matashin jarumi ya yi masa game da wadannan mayun aljanu, sai ya fahimci cewa lallai akwai makircin da aka shirya, saboda haka sai Idrisu ya rika yekuwa cikin wata murya mai Karfi yana umurtar Sarki Ifritu da wancan jarumin su janye gaba dayansu su da jama’arsu, har ma ya ke cewa, “Ku juya… na ce ku tsere.”

Abin dai kamar tatsuniya, cikin dan Kankanin lokaci sai ga filin babu kowa sai jarumi Idrisu kadai, su kuma jajayen aljanun nan, mayu sun yiwo tsinke gare shi.

Haka Idrisu ya yi ta fafatawa da su, kuma duk irin maitarsu sun yi amma ina, Allah Bai yarda sun cutar da shi ba, da suka kammala siddabarunsu irin na mayu sai suka nufo shi don ayi ta ta kare.

Tuntuni abin dada maya ke ta jira ke nan. Ya sa takobi ya yi ta datsa jikkunansu bibbiyu, ta

Www.bankinhausanovels.com.ng yadda sai da abin ya ba kowa mamaki, har ita kanta Bakayalu, wato irin yadda takobin wannan jarumi dan Adam ke yi musu muguwar Barna. Da zarar ya sari jan aljani sai kawai ka ga wata irin wuta ta kama shi ta cinye kurmus. Kai a takaice dai babu ko daya da ya rage.

Bayan ya kammala da su bai yi wata-wata ba sai ya dum fari inda manyan aljanun nan suke su da kakarsu Bakayalu ya yi wata irin dirar mikiya da sara baki daya a tsakiyarsu, abinka da wanda ya tunzura.

Rashin sa’ar da aka samu shi ne, duk da Kokarin kaucewa da jaruman aljanun nan suka yi sai da takobin jarumin ya ratsa tsakanin hannayen wani jarumin aljani da ke dauke da wani gefe na kujerar da Bakayalu ke kai, sarar ta datse hannayen har ta sami wani sashe na kujerar. Haka dole wancan jarumin yana ji yana gani ya rabu da hannayensa kamar yadda gefen kujerar da ya ke rike da shi shi ma ya gutsure.

Bakayalu ta sulmuyo, amma kafin ta fadi Kasa sai ga shi ta dire riKe da tukunyar tsafinta a hannu. Ta dunKula hannu ta kai wa jarumi Idrisu wani bugu, shi kuwa sai ya sa fadin takobinsa ya kare, ji kake yi tatsatsatsa… wuta ta tashi ta yi sama, amma abin mamaki a wurin aljana Bakayalu maimakon wannan takobi ya narke a dalilin haduwarsa da tsafataccen

Www.bankinhausanovels.com.ng hannunta, sai ga shi ko lanKwashewa bai yi ba, kafin ka ce haka jarumanta sun rufar wa Idrisu aka ci gaba da gwabzawa ita kuma ta samu ta janye zuwa bayan fage.

Yanzu kam Bakayalu ta hakikance cewa akwai magana game da wannan takobi na jarumi Idrisu dan Hamidu, saboda haka sai ta ruga zuwa gidanta cikin sauri kuma a fusace, tun kafin ta shiga sai ta fara kwalla wa jikanyarta aljana Dailanu kira. Nufinta shi ne ta fada mata gaskiya game da al’amarin fita da bakin littafi wanda asirin rayuwarsu ke ciki, don yanzu ta gama hakikance cewa Dailanun ce ta fita da littafin, to lallai ne ta zo yanzu ta fada mata gaskiya sannan ta kashe ta, in ma dai ba ta fada mata gaskiyar ba dai ta yanke shawarar halaka ta.

Shigarta dakin Dailanu sai ta tarar ba ta nan, amma kuma ga rubutacciyar takarda a kan shimfida. Kuma tabbas rubutun Dailanu ne,

*Zuwa ga shugabar matsafa Bakayalu. Babu sauran bukatar ci gaba da wahalar neman wanda ya dauka tare da fita da bakin littafin . da sirrin rayuwarku ke ciki, ni ce jikarki Dailanu na fita da shi zuwa ga mutanen kirki wadanda suka yi amfani da shi suka assasa yadda za a

Www.bankinhausanovels.com.ng kwato wa al’umma ‘yancinsu. daga mulkin kama-karya da zaluncin da ke Bakayalu tare da jikanki la’ananne Sham‘una ku ka dulmuya su ciki, ba aljanu ba ba mutane ba, ku biyu kadai! Haba

Shigata cikin addinin Islama ne ya sa na kara fahimtar irin dulmuyar da al‘umma da ki ka dauki dumbin shekaru kina yi, dubi irin yadda zaluncinki bai bar hatta ‘ya’yan da kika haifa ba, musamman mahaifina da kika kashe ba kan wani kwakkwaran dalili ba

Shawarata a gare ki ita ce har zuwa yanzu da ki ke karanta wannan takarda kina da sauran dama guda daya ta samun tsira ke da azzalumin jikanki barawon ‘yan mata ‘ya‘yan mutane, damar kuwa ita ce ku bar bautar tsafi da wuta da rana, ku gaggauta musulunta, in kuwa ba haka ba, to ina yi muku albishir din cewa ku taku ta kare, kuma ko lahira ba na fata Allah Ya hada fuskata da ‘yan wuta

Ni ce dai jikarki, Dailanu ‘yar Kailanu-” Tsananin mamaki na irin wannan ba zata ya sa nan take aljana Bakayalu a karo na farko a tarihin rayuwarta ta yanke jiki ta sume har na wasu ‘yan

Www.bankinhausanovels.com.ng dakikoki. Tana farfadowa sai ta yi wata irin Kara wadda duk aljanin da ke makwabtaka da wurin sai da ya tsorata, sannan ta sa barorinta suka kira mata Sham’‘una daga fagen fama, yana zuwa sai ta mika masa takarda ya karanta.

Yau Bakayalu ce take tambayar sa, “To yanzu kana ganin mene ne abin yi?”

Sai Sham’una ya ce mata, “Ya shugabata, yanzu dai lokacin yaki ne, kusan babu abin da za mu iya yi game da wannan yarinya, amma ina ba ki hakuri da kuma alkawarin cewa duk inda ta shiga a cikin duniya ko wajenta bayan yaki zan kamo ta in taune ta da bakina da ranta kina kallo.”

Bakayalu ta nisa sannan ta ce, “Yanzu abin da zaa yi bari in shiga cikin kayan tsafina mu je mu ga yadda zaayida wannan yaro dan Adam mai tsaurin kai.”

Wasu irin jajayen kaya ne, kai daga gani a lokacin da ta sa su ka san an yi shirin sharri.

Yanzu dai yaki ya dan sassauta, aljanun Sarki Sham’una sun fahimci cewa shugabanninsu ba sa cikin fagen, wanda hakan ya taimaka kwarai wurin sa mayakansu su dan janye jiki. Ko kadan bangaren su jarumi Idrisu,ba su matsa ba, don tuni suke jiran irin wannan dama don sararawa. Kowa kuma yanzu yana ji a jikinsa cewa in

Www.bankinhausanovels.com.ng Bakayalu ta tashi fitowa, to abin ba zai yi kyau ba,

don tabbas za ta zo ne da gaurayen makirci da

mugunta gaba daya, sai dai kawai Allah Ya kiyaye. Can kuwa sai aka hango su.

Ga Bakayalu nan a gaba tana jagorantar tafiyar, jikanta Sham’una yana biye a baya da sauran wasu dakaru masu yawan gaske, Sarki Ifritu ya yi wuf ya sungumi gwalminsa zai nufi inda suke, sai Idrisu ya sa hannu ya dafa kafadarsa yana mai cewa, “Allah Ya dade da ran Sarki wannan fada ba naka ba ne, ka bar ni da muguwar tsohuwar nan, don _ tsatsubetsatsubenta suna da yawa, kuma ka san cewa Sarki Sham’‘una ba ya mutuwa in ba an kashe ta gaba daya ba a gangar jiki da kuma ruhi.”

Sarki Ifritu dai bai kammala fahimtar abin da jarumi Idrisu ke nufi da cewa sai an kasheta a gangar jiki da ruhi ba, amma kasancewar babu lokaci bai tambaya ba sai kawai ya amince ya koma baya din ya bar Idrisu don ya kammala kintsawa.

~ Kafin dan Hamidu ya kammala addu’o’in da ya ke yi don fuskantar wannan tsohuwar iblishiya, abin mamaki sai kawai ga dokinsa Jagora a guje ya nufo shi, yana gudu yana haniniya tare da harbin iska kamar bai taba jin Karfi da lafiya ba a rayuwarsa irin ma ranar.

Www.bankinhausanovels.com.ng Wani irin farin ciki da murna suka lullube jarumi Idrisu, ganin cewa dokinsa da ya dade babu lafiya ga shi yau ya ji sauki kuma ma kamar ya fi shi zakuwar haduwa da abokan gaba, ai nan take Idrisu ya dauke sirdin dokin da ke kan dardumar da ya ke ta yaki a kanta ya dora wa doki abinsa, ya nade dardumar tashin ya saKala a kurciyar sirdi. Doki yana jin an hau “shi sai ya yi wani irin rimi ya dire, ya daga kafafuwan baya ya harbi iska sannan ya zabura ya nufi inda su Bakayalu suke. Aka hade a tsakiya, su biyu kadai, jarumi Idrisu dan > Hamidu da tsohuwar aljana Bakayalu.

ALJANA Bakayalu ta ce masa, “Kai dan Adam! Me kake bukata ne haka kake ta kashe mana jama’a babu dalili?”

Jarumi Idrisu ya amsa mata cewa, “Ranki kawai nake son dauka, ke da azzalumin jikanki Sham’‘una saboda irin mugun zalunci da kuka dade kuna yi.” Cikin fushi sai ta ce masa, “Kai Karamin alhaki! Ka san da wadda kake magana kuwa? Nice kakar aljanu, nice sharri, ni ce mugunta gaba daya, na kashe aljanu da mutanen da babu wanda ya san adadinsu, wadanda suka fi ka jarunta da tsageranci. Ba a taba nasara a kaina ba kuma ba zaa taba yi ba…”

Idrisu ya katseta, “Ke dakata! Yi gaggawar janye wadannan kalmomin cewa ba za a taba ba, don ina yi miki albishir din cewa lokacin ne ma ya zo yanzu. La’ananniyar tsohuwa kawai wadda rayuwarta ba ta da wani amfani sai cutarwa.”

Da Bakayalu ta ji irin wannan magana da mutum

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *