YAYANA NE COMPLETE
Gidan Majid acike yake da yan barka kowa se kallon babyn yake ana Allah yaraya amma me jego tayi shiru daga gefen gado take zaune dakaganta kaga me damuwa da alama ma kuka tayi ga dan karamin akwati agabanta kayan baby kala hudu nata kuma kala biyu,
Jitayi an riko hannunta datayi tagumin dashi,yayartace asama’u janta tayi har dakin yaranta kafin tafara magana,
Haba badi’a duk abinda zakiyi kibari se an watse kiyi abinki sekin nunawa mutane kina cikin wani hali,
Cikin muryar kuka tace Yaya dole inyi kuka abin yafara isata majid fa ba talaka bane amma kiga wulakancin dayai mana nibama kaina nake jiyewa ba dan jinjirinnan dabesan komai ba haka zetaso yabi layin yayyensa dasuke cikin ukubar rayuwa kamar ba gidan ubansu ba kinsani bantaba magana ba bantaba nuna damuwata akan duk abinda yakemin shida mahaifiyar saba da kuruciyata zasusa hawan jini yakamani,
Dukda dahaka badi’a hakurinnan shi zakici gaba dayi kodan yaranki suyi koyi dake kuma komai na rayuwa me wucewa ne kiga kala biyunnan dayai miki wallahi sedan wane da wane hakama na yaron wasu kalar designers ne dabantaba ganin suba kuma daga gani masu tsada ne kicigaba da rungumar kaddarar ki kinji,
Shikenan Yaya inaga bawata walima da zamuyi kawai dai ayi snaks dakayan rabo nasiyo bucket dozen takwas masu marfi anyi sticker da hoton yaron sukadai gareni kudin zobo ne danaketarawa,
Allah yasa musu albarka zamuyi snacks din nida Yaya muktar farida kuma tayi memo tace zatayi fried rice da kunun aya su Hajiya kuma zamu Tara wani Abu mubasu suhada gara,
Yaya na gode sosae Allah yabar zumunci kuma su Hajiya subar zancen gara ai wayanda za ayiwa ba kirki garesuba,
Kedai babu ruwanki susukace zasu iya,
Shikenan Allah yataimaka,
Dakyar tayi bacci ranar saboda masifar mijinta ga yaronta da azabar kuka tarasa inda zata sa kanta,
Ranar suna yaro yaci suna jabir dakyar ta riqe kukan datakeji har en biki suka watse wani yankwanannen rago ya yanka kamar ma jaririne befi wata huduba da iyayenta sunsan kalr wulakancin da ake mata dasun kashe auren batason mijinta yasaketa saboda tanason sa matsalarsa kawai rashin son haihuwa ne,
Washe gari tagama gyaran gidan yaran su uku sunyi makaranta biyune kusa da ita se jaririnta jabir biyun basu isa akaisu makaranta ba kuma tasan babansu baze kaisuba shiyasa takeso kafin su isa zuwa makarantar ta tanadi wani Abu dantasakasu makaranta medan kudi kodan rayuwarsu ta inganta,
Sallamr mahaifiyarsa taji Hajiya rabi azahiri ta tsorata sanin duk zuwan Hajiya rabi to da cin mutunci take zuwa,
Gaisheta tayi ta amsa ciki ciki mama kizauna mana,
Bazama nazo yiba inabanda nuna isa dankun rainani yaushe zaku aikamin danama kamar abinda na roka toga tsiyarku nan nakawo muku banaso wannan abin zanraba nida en uwana,
Hajiya kiyi hakuri ragon ne bayida girma,
Ohh sannu munafuka wato duk abinda Dana yake miki bakya gani harkin raina girman ragon to wallahi bari yadawo kicenasa ina nemansa senaji idan shine yake daure miki gindi kina wannan iskancin kuma ga namanan idan ba akarominba kuriqe tsiyarku,
Dama badi’a bame magana ceba hakan yasata shiga kitchen ta kawso sauran naman tahada mata tamiqa mata tana bata hakuri,
Babu godiya ta karbe sema kara raina naman datayi tatafi tana fadin bafi’a duk ta kwashe tabawa en uwanta dan munafurci,
Komawa tayi tazauna tamakasa yin kuka kallon jabir take dayketa tsotson mamanta amma bakomai aciki sbd bakinciki tunjiya takasa cin komai ga yaron bashida madara tana tsoron taba abincin data ajiyewa yaranta suzo suci basu koshiba dan tasan ubansu baze bada kudin cefane dasu ba,
Ahaka jabir yagaji yayi bacci sauran yaranma duk sunyi bacci shnifidesu tayi tafito daniyyar wanke wanke Sega majid yashigo,
Binta yayi damugun kallo ko amsa sannu dazuwan datake masa beyiba,
Ledar data gani ahannunsa taje zata karba Dakatar Da ita yayi yabude ledar yanuna mata,
Kinganusu nan kayan miya ne kuma wallahi nakwana biyu ne daga seke se abdulrahim karki sake kibawa wayannan Yayan naki jeka inbiki haihuwar rurrutsa,
Muryarta na rawa tace…,
Allah kabamu hakuri da juriya azaman duniya
Ameen.
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari na)*
_labari da rubutawa_ _sophieG_
_A very heart touching story 2017_
*bismillahir rahamanir rahim*
_ina rokon ubangiji Allah dayabani ikon farawa lafiya da kammalawa lafiya yasa mu amfana da darussan dake tattare acikin littafin_
_sadaukarwa ga dukan masoyana_
Page 1
Gidan Majid acike yake da yan barka kowa se kallon babyn yake ana Allah yaraya amma me jego tayi shiru daga gefen gado take zaune dakaganta kaga me damuwa da alama ma kuka tayi ga dan karamin akwati agabanta kayan baby kala hudu nata kuma kala biyu,
Jitayi an riko hannunta datayi tagumin dashi,yayartace asama’u janta tayi har dakin yaranta kafin tafara magana,
Haba badi’a duk abinda zakiyi kibari se an watse kiyi abinki sekin nunawa mutane kina cikin wani hali,
Cikin muryar kuka tace Yaya dole inyi kuka abin yafara isata majid fa ba talaka bane amma kiga wulakancin dayai mana nibama kaina nake jiyewa ba dan jinjirinnan dabesan komai ba haka zetaso yabi layin yayyensa dasuke cikin ukubar rayuwa kamar ba gidan ubansu ba kinsani bantaba magana ba bantaba nuna damuwata akan duk abinda yakemin shida mahaifiyar saba da kuruciyata zasusa hawan jini yakamani,
Dukda dahaka badi’a hakurinnan shi zakici gaba dayi kodan yaranki suyi koyi dake kuma komai na rayuwa me wucewa ne kiga kala biyunnan dayai miki wallahi sedan wane da wane hakama na yaron wasu kalar designers ne dabantaba ganin suba kuma daga gani masu tsada ne kicigaba da rungumar kaddarar ki kinji,
Shikenan Yaya inaga bawata walima da zamuyi kawai dai ayi snaks dakayan rabo nasiyo bucket dozen takwas masu marfi anyi sticker da hoton yaron sukadai gareni kudin zobo ne danaketarawa,
Allah yasa musu albarka zamuyi snacks din nida Yaya muktar farida kuma tayi memo tace zatayi fried rice da kunun aya su Hajiya kuma zamu Tara wani Abu mubasu suhada gara,
Yaya na gode sosae Allah yabar zumunci kuma su Hajiya subar zancen gara ai wayanda za ayiwa ba kirki garesuba,
Kedai babu ruwanki susukace zasu iya,
Shikenan Allah yataimaka,
Dakyar tayi bacci ranar saboda masifar mijinta ga yaronta da azabar kuka tarasa inda zata sa kanta,
Ranar suna yaro yaci suna jabir dakyar ta riqe kukan datakeji har en biki suka watse wani yankwanannen rago ya yanka kamar ma jaririne befi wata huduba da iyayenta sunsan kalr wulakancin da ake mata dasun kashe auren batason mijinta yasaketa saboda tanason sa matsalarsa kawai rashin son haihuwa ne,
Washe gari tagama gyaran gidan yaran su uku sunyi makaranta biyune kusa da ita se jaririnta jabir biyun basu isa akaisu makaranta ba kuma tasan babansu baze kaisuba shiyasa takeso kafin su isa zuwa makarantar ta tanadi wani Abu dantasakasu makaranta medan kudi kodan rayuwarsu ta inganta,
Sallamr mahaifiyarsa taji Hajiya rabi azahiri ta tsorata sanin duk zuwan Hajiya rabi to da cin mutunci take zuwa,
Gaisheta tayi ta amsa ciki ciki mama kizauna mana,
Bazama nazo yiba inabanda nuna isa dankun rainani yaushe zaku aikamin danama kamar abinda na roka toga tsiyarku nan nakawo muku banaso wannan abin zanraba nida en uwana,
Hajiya kiyi hakuri ragon ne bayida girma,
Ohh sannu munafuka wato duk abinda Dana yake miki bakya gani harkin raina girman ragon to wallahi bari yadawo kicenasa ina nemansa senaji idan shine yake daure miki gindi kina wannan iskancin kuma ga namanan idan ba akarominba kuriqe tsiyarku,
Dama badi’a bame magana ceba hakan yasata shiga kitchen ta kawso sauran naman tahada mata tamiqa mata tana bata hakuri,
Babu godiya ta karbe sema kara raina naman datayi tatafi tana fadin bafi’a duk ta kwashe tabawa en uwanta dan munafurci,
Komawa tayi tazauna tamakasa yin kuka kallon jabir take dayketa tsotson mamanta amma bakomai aciki sbd bakinciki tunjiya takasa cin komai ga yaron bashida madara tana tsoron taba abincin data ajiyewa yaranta suzo suci basu koshiba dan tasan ubansu baze bada kudin cefane dasu ba,
Ahaka jabir yagaji yayi bacci sauran yaranma duk sunyi bacci shnifidesu tayi tafito daniyyar wanke wanke Sega majid yashigo,
Binta yayi damugun kallo ko amsa sannu dazuwan datake masa beyiba,
Ledar data gani ahannunsa taje zata karba Dakatar Da ita yayi yabude ledar yanuna mata,
Kinganusu nan kayan miya ne kuma wallahi nakwana biyu ne daga seke se abdulrahim karki sake kibawa wayannan Yayan naki jeka inbiki haihuwar rurrutsa,
Muryarta na rawa tace…,
Allah kabamu hakuri da juriya azaman duniya
Ameen.
Feeyah😍
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari na)*
*N!$@ online writers*
_written by sophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin nakune ummeejay,ummeekhaleel,zeenaseer,husaina ubandiya,Sha’awa ibrahim,jidda(dota),shukrah,adama maifata,bilkisu,meera Dan fodio,ddss. Nagode sosae da addu’arku agareni Allah yabar zumunci ameen_
Page 2
Yanzu don Allah majid haka zamu cigaba da rayuwa Yayan cikinka nefa amma ace abincin dazasuci yana musu wuya agidan ubansu,
Magana take kamar zatayi kuka,
To naji malama bazan basu abinciba se randa naga dama kintashi kin haifo yaya jeka inbika saboda kawai ki karyemin tattalin arziki don kinga Allah yasamin hannu to babu ruwana dacinsuko shansu ai seda nanuna miki banida muradin ki haife cikin dukansu bayan abdurrahim kika ki Dan haka dole kece zakiyi dawainiya dasu babu ruwana,
Bata cika sonyin maganaba balle wannan maganar Mara dadi datakejinta
Daga bakin mutumin daba jahiliba Dan boko me tarin dukiya amma se bala’i da makon masifa,
Kije ki hadamin ruwan wanka munada meeting yau akasuwa,
Batace dashi komaiba tabi hanyar dakinsa bayan tahada mai ruwan wankan tazauna zaman jiranshi yafito,
Kallonta yayi bayan yafito yace,
Lafiya dai badee’a?
Don Allah jabir zaka siyowa madara naringa hada mishi da ita,
Saboda? Yatambaye ta yana shafamai a hannunsa,
Shiru tayi tana nazari kafin tace,
Saboda ni banasamun isasshen abincin dazanci har ruwan nonon sukawo su isheshi wuni daya,
Bari kiji babu ruwna da jabir nabaki abinci kici banason tsegumi don kisani tunyanxu yashiga layin su abduljabbar,
Takasa cewa komai Dan takaici idan tayarda taci abincin saboda jabir to sukuma su abduljabbar mezasu CI dama abincinta take basu itakuma idan anyi cinikin zobo setasan yadda zatayi taci takara musu,
Dakinta tashi ga tazauna bakin gado tana kallon yayanta tana kuka,
Kuyi hakuri *y’ay’ana*nasani wantarana zanyi *alfahari*daku zancigaba da Neman nakaina don na inganta rayuwarku saboda babanku bashida niyyar sakamin hannu a lamarinku,
Dahaka rayuwarsu taci gaba yau dadi gobe wuya ga yaran duk halinta suka gado basu cika magana ba haka suketa Jan hanji ga ramarsu tarashin wadata tafara bayyana badi’a ma duk tayi zuru zuru damuwa tayi mata yawa takasa sanar da mahaifanta ko babban yayansu besan Halin datake cikiba Yaya asama’u kadai tasani itama kusan halin su daya da badee’a zurfin ciki yayi musu yawa,
Suna zaune jugum ta kammala abincin rana ta hada da nata Dana abdurrahim kallon abincin take abdurrahim,abduljabbar,abdulkadir,abdul’aziz, abincin baze ishesu ba ga jabir yafara cin abinci gashi duk yarame kwanaki yai rashin lafiya amma ko kudin adaidaita sahun zuwa asibiti bebasu ba,
Tazaunar dasu duka harsun faraci Sega majid yashigo,
Sallallamin dayakene yasata dago tana kallonsa,
Yanzu badee’a cin amanata kike kisatar min abinci kiba yayanki sannan kuma ki hadasu da dana salon kar yakoshi?
Nikam bansatar maka abinciba nawa dana abdurrahim na hada musu,
Ina ruwana dayaranki kibasu naki daban mana suci karki sake kikara hadamin su da yarona inaso yaci yakoshi maza zoki raba musu,
Majid don Allah karmu raba kan yayanmu,
Nace kixo kiraba musu abincinan tun raina be baci ba,
Kamar zatayi kuka haka taraba musu abincin nasu abduljabbar befi suyi loma shida shida ba yakare,
Ta dago tana kallonsa da fuska a maraice hannunta kawai yaja yana fadin,
Abdurrahim kaci abinci sosae kaji,
Yaran suka bisu da kallo har suka bacema ganinsu,
Abdurrahim yakoma kusada en uwansa sunaci atare har aka cinye nasu yadauko nasa sukaci atare har jabir ma dayake rarrafe,
Bangaren su badi’a kuwa a Palo ya tsaya yacire rigarsa dagashi se singlet da dogon wandon shadda akan kafafuwansa yazaunar da ita yada kallon bakaken lips d’inta dasuka sha lipstick sunata kyalli ga sky blue din jallabiya takama jikinta tayi mata kyau,
Kinyi kyau badee’a,
Batama jinshi hankalinta yatafi tunanin yayanta ko sun koshi,
Dan kwalin kanta taji yazame yana kara rungumeta ajikinsa,
Watoshi bashida damuwa ko ga yayansu can yunwa zata halaka su batasan lokacin da kuka ya kwace mata ba kamar wata jaririya,
Majid kuwa dama ya kwaso jarabarsa bema saurari kukan datakeba seda ya sauketa,
Taso tahanashi sekuma tayi tunani hukuncinta agurin Allah gakuma tsoron karta kwashi wani cikin dan jiya tafara sallah kuma tasan yanayinta,
Dakinta takoma tasamu yaran a apalo dikansu sunyi bacci gyara musu kwanciyarsu tayi tashi ga uwar dakin,
Bayan kwana biyu tashirya zuwa gidansu tagaida su Hajiya ta kwana biyu batajeba,
Yace ta shirya yakaita taji dadi sosae,
Ke dawayannann yaran orututu da otonyo zaki,
Eh ta amsa tana kallonsa,
Bazasu shigarmin motaba dama da abdurrahim kadai zaki se wannan jabir din dasena dan matse nakaiki,
Dasu duka zani danbansan wazan barwa suba kasan kuma sunyi kankanta abarsu sukadai agida kabarshi kawai zan hau napep,
Kallonta yake cikeda masifa,
Ke kinma fasa tafiyar senagani inkece kike iko dakanki nizaki gaywa wannan banzar maga…….,
Bata jira yakarasa maganarba tana yaranta suka shiga gida,
Shirunta yana masa ciwo danhaka yabita yana balbaleta da fada amma har yakaraci surutunsa batacemasa uffan ba cikida takaicin abinda taimasa yabar gidan.
*kwanaki a wani group wata takawo topic akan cikin biyunnan wanne ne zaka zaba*
*1 uwar miji bata sonkine*
*2 mijin ki baya sonkine*
*kowa yafadi albarkacin bakinsa but ni awurina banason kodaya acikin biyunnan sbd in uwar miji batasonki to maganar jin dadi bata tasoba karshema sekun rabu hakama idan mijin bayasonki karma kikawo maganar kwanciyar hankali a gidan sedai idan Allah ne yayi ikonsa*
*Allah ya dubemu da idon rahma*ameen
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari na)*
_by sophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Sha’awa Ibrahim_
Page 3
Abdulmajid kasim asalinsu en garin sokoto ne akaramar hukumar kware duka en uwansu suna kware mahaifinsa ne kadai yke zama a sokoto shikadaine gun mahaifiyarsa shiyasa yake sheke ayarsa yadda yakeso,
Badi’a kintabbatar ba matsala banaso adawo ana dana sanin wannan auren naku,
Babanta ne yasata agaba yana tambayarta don yasan Halin uwar majid batada kirki kokadan,
Abba babu matsala insha Allah,
Banaso kibari sonda kike masa yasa kikasa ganin laifinsa kije kikara tunani nabaki kwana biyu,
Tashi tayi cike da kunya tashi ga daki,
Bayan kwana biyu abba yasake tambayarta ta shaidamasa da babu matsala,
Tana tsananin son sa hakane shima agurinsa yahanata sauraren kowane saurayi inko yaga abu basetace tanaso ba komai aka kawo musu a kasuwa indai namata ne dazasu siyar seya kawo mata amma abbansu betaba bari ta karba ba sedai yakoma dasu ya ajiye,
Yayyenta zama sukayi akayi maganar auren muktar yace abarta tunda tana sonsa shima yanasonta,
Bayan kwana biyu iyayen majid suka turo an saka ranar bikin wata me shigowa,
Lokacin bikin yaxo akayishi cikin kwanciyar hankali gidan amarya yayi kyau komai daidai irin na mutane masu wadata,
Bayan wata biyu da auren badee’a tafara laulayi sunje asibiti aka tabbatar musu datana dauke da ciki wata biyu sunyi murna sosae kamar su fadawa duniya,
Gata da kulawa ba amagana har mahaifiyarsa ttanaji da cikin tun daga gidanta take zuwa takaimata kayan kwadayi,
Shikansa majid idan yafita aiki ko kasuwa seyazo saubiyar kafin lokacin tashinsu office ko kuma kasuwa yayi,
Asibitin da yayarta take aiki acan take zuwa awo,
Tayi masa zancen komawa makaranta yanuna mata bashida ra’ayin komawarta makaranta be rage tada komaiba kuma yafiso kullum yana tareda ita,
Ba ayi yarjejeniyar cewa zebarta tayi karatuba kafin auren dan haka besamu matsala daga gunta ko iyayenta ba se aka share batun,
Cikinta yashiga watan haihuwa zuwa lokacin komai ashirye yake kayan babyn dasuka Tara sukansu basusan adadinsu ba siya kawai suke suna ajiyewa,
Ranar da badee’a ta tashi da naquda da safe a gigice sukayi asibiti hankalin majid duk atashe yakasa kiran kowa yafada suna asibiti,
Ko awa daya ba ayi dazuwan suba Allah yasauki badi’a lafiya tasamu da namiji murna gurin abdulmajid ba amagana anan yakira mamansa yafada mata kafin asallamesu asibiti tacika da dangi,
Ranar suna kuwa anyi barin kudi abinci a ko’ina yaro yaci suna abdurrahim sedai ace Allah yaraya abdurrahim,
Mahaifiyarsa ta umarcesa daya dawo gidanta har badi’a tayi arba’in tadawo dan babu kyau mutun yana kwana shikadai agida,
Bemusa mata ba yayi yadda tace sedai kwana kadai ke kaishi gidan kullum yana gurin badi’a da babynsu,
Ganin haka abbansu yace ranar data cika kwana arba’in takoma gidanta bayason wannan zaryan da mijinta keyi masa agida,
Ana gobe zata koma majid yafito da safe yashiga dakin mamansa,
Umma nafita zamuje asibiti da badi’a,
Batada lafiyane tatambayesa,
A a za adorata kan maganin family planning ne,
Family me?ta tambayesa tana miqewa tsaye,
Planning umma,
Bakuda hankali wallahi kunyi kadan kaikadai na Haifa inaso naga gida yacika da yara babu wani planning banyarda daga haihuwar da daya zaku wani ce planning kusake tunani bada yawun bakinaba,
Umma ai ba wani abubane kuma bawai munce abdulrahim kadai ne zamu Haifa ba,
Banason iskanci kanajina kodan kaga duk abinda kake ina daure ma gindi?tobanda wannan zancen sena Daura zanina naje har gidansu badi’a nayi rashin mutunci,
A a umma base anyi hakaba kiyi hakuri,
Dayafi dai tafada tana zama tacigaba da mita,
Fita yayi yana tunanin yadda zeyi da wannan zencen.
*duk kalar jin dadin dakake arayuwar duniya dazarar katuna da mutuwa zakaji jindadin yaragu amma masu imani ne kadai ke tuna mutuwa maras a imani kuwa harkarsu tqduniya kadai sukasa Agaba wannan babban kuskurene duk yadda kayi niyyar aikata mummunan aiki katunada mutuwa hakan zesa katuna haduwarka da ubangijinka mezakacemasa ranar tonon asiri? Zakaji tsoron wannan ranar dataimakon Allah sekaga kakasa aikata wannan aikin Allah kasa mudace ameen*
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari na)*
_by SophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Anty badee social_
Page 5
Baby meyake damun badee’a ne naga ta rame kuma fuskarta da alamun akwai damuwa kuma gasu Abdul kamar yayan riqo suma duk sun rame,
Mijin yaya asma’u ne ke tambayar ta Dan lokacin daze fita ya hadu da badee’a zata shigo anan yalura da ramewarta yadda idonta sukayi zuruzuru,
Shiru tayi nadan lokaci tana tunanin tafada masa koze taimakawa kanwar ta ta,
Kiran sunanta yayi kafintadawo daga duniyar tunanin data shiga,
Mahmoud badee’a nacikin damuwa uwar miji da mijin sunsata atsakiya suna gasa mata gyada a tafin hannu,haihuwa take babu tsari uwar mijin tayi rantsuwa bazatayi family planning ba shikuma mijin bayason wannan haihuwar datake babu kai babu gindi duk cikin yayannan babu shekara biyu a tsakaninsu yanzu halin da ake ciki tundaga kan abduljabbar har jabir itake cida su yace wallahi tunda take haifarsu kamar awaki baze dauki nauyin komai nasuba danshi baze yadda tacinye masa tattalin arziki itada yayanta ba,
Shiru yayi yana jinjina jahilci dakauyanci irin Na abdulmajid,
Baby yanxu su Hajiya basu dauki wani mataki ba aka zuba masa ido yana wahalar da yar mutane?
A’a itace bataso afada musu basusan halindatake ciki ba Dan tunfarko basuso aurenba saboda sunsan uwarsa batada kirki batasan girman kowa ba,ganin badee’a tadage shitakeso yasa suka barta ta aureshi dakunya kuma yanxo daje kai kararsa gurinsu, ga yahanata komawa makaranta kuma babu wata sana’a mekyau dazata kawo kudi zobo takeyi lokacin sanyi ba asiya sosai sbd babu k’ishi tausayinta nake konamiji ya yakara da ciyadda mutun uku bare mace, kuma har yanzu tace tanason abinta,
Dariya yayi yace so hana ganin laifi ai
Uhmm narasa abinda take tsinta agurinsa wallahi,
Allah ya sauwaqe gobe sekishirya dasafe kafin kitafi gurin aiki zanbaki sako ki kaimata,
Ameen tace murna fall aranta datasan mijinta ze taimaka wa yar uwarta batareda wani tunaniba aida tuni tasanar dashi, godiya tayi masa dukda batasan mezaiyiwa badee’ar ba,
Washe gari motarsa yabata yace sakon yana ciki se kuma kudi yabata kuma tacigaba da hakuri insha Allah zata ga ribar yinsa,
A palonta tasamesu abdulrahim kadai yaje makaranta,
Bayan sungaisa Yaya tace
Yanaga yaran basuje makaranta ba?
Babu abincin dazan basu sutafi dashi kuma lesson suke se 3:00 suke tashi kinga ko bazan turasu haka ba da idan banida abinda zan basu nakan Debi nashi idan nasamu nabiya to yan zuma koshinkafa yadaina kawo buhu awo yake duk bayan kwana biyu,
Hmmm shikenan Mahmoud ne yabani sako nakawo miki mijinki dai bayanan ko?
Bayanan ta amsa tana kallonta,
Hanyar fita tadosa tana cewa kizo mu kwaso kayan,
Abu biyu take ji axuciyarta murna kuma da takaici yadda mijin yayarta ytaimaketa haka amma mijinta abin kaunarta yakasa taimakonta,
Kayan abinci ne masu Dan yawa balaifi sekuma kudi dabansan konawa bane,
Yaya asma’u tace sekuma nawa taimakon duk abinda ake so amakarantarsu kifada min insha Allah zan taimaka kafin muga yadda za ayi achanja musu makaranta,
Cikeda murna tayi godiya kuma zatazo har gida tayiwa mahmoud godiya,
Tundaga wannan lokacin mijin asma’u yake taimakonta dukda watarana takan tashi cikin rashi mijinta kuwa besan meke gudana ba yana ganinta dai tarage damuwa da al’amuransa amma acikin zuciyarta itakadai tasan damuwar datakeda game da abdulmajid,
Kwana biyunnan bata jin kanta daidai fargaba take Allah yasa ba abinda take zargi bane,jiya batayi bacci ba zazzabi takeji ajikinta yadda gabanta ke faduwa yahanata bacci,
Yau kusan sati daya kenan tana fama duk abinda zataci baya zama tayanke shawarar kiran Yaya asama’u,
Kinga bari idan nataso daga aiki Zanbiyo da abin awon ciki mugani kibar kuka,
Yaya asma’u tace bayan tagama sauraren badi’a data kirata awaya,
Karfe uku agidan tayimata,
Karbi badee shiga kiyo fitsari anan inkin gama ki kirani nazo,
Wani kalar dokawa da zuciyarta tayi lokacin da Asmau tafada mata ciki ne da ita,
Yaya muxubar dashi wallahi bazan iya ba wahalar tayimin yawa,
Kice kintuba badeea wasu sunacan suna Neman haihuwar kamar zasuyi hauka amma basu samuba kigodewa Allah tunda rabon wannan yazo zaki haifeshi sedai idan kin haihu zamu dauki mataki kuma kifadawa mijinki kinadauke da cikinsa karki boye masa komai,
Shikenan Yaya nagode Allah yabar zumunci tafada hawaye nabin kuncinta,
Bayan tafiyar asma’u tazauna tayi koka har bata gajiba ba abinda ke daga mata hankali irin….
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
*Abu nabiyu dayake janyowa mutun bakin jini shine wulakanci sekaga wani ba abinda yake burge shi irin yawulakanta dan adam,ko dabba kake wulakantawa zata nisance ka balle kuma mutun me hankali,idan kana wulakantarwa sekowa yaguje ka bawanda yakeson kusantarka*.
*kutuna ita zuciya tanason Wanda yake kyautata mata kuma tanakin Wanda yake musguna mata saboda haka mukiyaye*
Page 7
11:36pm abinci take bawa jabir dukda yadda yake nuna baya so amma dole zatabashi yaci koda ze Harar ne magani takeso tabashi inyai bacci se taje gun jarababben ubansa,
Yadanci kadan paracetamol tasake bashi ko zazzabin ze sauka tasamu yayi bacci,
Babu jimawa kuwa bacci ya dauke shi,doguwar rigar bacci tasaka ta zauna yiwa yaranta addua, muryarsa taji yana cewa,
Kinyi rantsuwa senayi miki kira nabiyu zakizo ko?,
Batace dashi kokaiba seda tagama yimusu addua,hannunsa takama sukabar dakin dan bataso yadaga murya yatashi jabir,
Shikadai yai kidansa kuma shikadai yai rawarsa,
Kallonta yayi ta lumshe idonta tana hutawa,
Wannan wani sabon salone badee?
Tagano sarai meyake nufi amma bata tankasa ba sema shigewa bayi tayi tabarshi dabaki asake,
Rigarta tamayar jikinta takwanta dan jiri ma takeji,
Shima wankan yayo yahawo gadon cike da masifa azuciyarta tace bari kayi masiifa me dalili,
Yabude bakinsa zeyi magana tace,
Inada ciki!
Ci me?
Yatambaya yana miqewa zaune,
Ciki bansan wata nawa bane amma zekai wata uku,
Waike bakida hankali ne bakya gajiya da haihuwa ne?
Dani da kai se aga Mara hankali,
Yasan gaskiya tafada dan haka yayi kasa da murya,
Wai badee babu yadda zakiyi ki abinnan ko dole seda family planning ake wannan din?
Zaune ta tashi sbd abin yamatukar bata mamaki,
Kadaina jarabar nan shine family planning bayan na asibiti kabari se sanda kaji kanason asake haifama da ko ya nabiyu Wanda zakaciyar kakaisu makaranta dakanka kadauko su sukuma sauran shegu ne,
Fuska yahade,
Badee ni kike gaywa magana?,
Banason damuwa Abdul kasan condition dina yanzu ina bukatar Hutu,
Kwata kwata yakasa bacci duk laifin hajiyata ne wallahi,
Washe gari har yaran suka tafi makaranta jabir yana bacci se karfe goma yatashi da zazzabi ga kansa ya dan kumbura,hankalinta yatashi Sosae addu’a take Allah yabashi lafiya, (nace ameen)
Wasa wasa karamin Abu ya zama babba dan ciwon jabir se gaba gaba yake kansa yayi wani irin kumburi mahaifiyarsa duk ta gigice,
Abdul jabir fa balafiya kalli yadda kansa ya kumbura,
Uhm nagani Allah yabashi lafiya,yana gama fadar haka yajuya ze fita dasauri takarasa kusa dashi tana rokonsa yakaisu asibiti dafarko soyai yashare ta sbd yau yanada abubuwan dazeyi kuma kudi zasu shigo amma ganin ta zauna kasa tana kuka yasa yace tazo sutafi,
Dole aka kwantar dasu amma bill kodaya babu Wanda abdulmajid yabiya acewarsa yarontane intaga dama tabiya,
Dan Allah abdulmajid kayi hakuri kaceci rayuwar danka kaji ance ma se anmasa aiki,
Karki kara cewa dana danki dai tunfarko seda nafada miki kiyarda azubar dashi kika ki kuma seda nafada miki duk dan dakika Haifa bayan abdulrahim toki shiryawa dawaiyarsa,
Dagowa tayi tana kallonsa kafin tamaida dubanta ga mutanen gurin kusan dukansu suke kallo cigaba yayi da surutansa cikin daga murya,
Yaya gasunan jeka inbika ko shekara takwas ba ayi da aurenmu ba amma Yaya biyar gana shida nan kan hanya mace babu control kana tabata se ciki gida Yakoma kamar makarantar naziri (tik’ek’en jahili),
Juyawa kawai tayi tanufi dakin da aka kwantar da jabir kukanma yaki zuwa seyau take danasanin auren abdul bata taba tunanin jahilcinsa yakai hakaba,
A gida kuwa yaran sundawo se kuka suke basuga mamansu ba abdul nacikin daki yafito yadaka musu tsawa atake suka hadiye kukan,
Anacikin haka Sega mahaifiyarsa tazo unguwar barka shine tabiyo gidan,
Bataga uwar yaran ba ta tambaye sa yafada mata suna asibiti tattara kan yaran tayi tace dasu zata tafi har kaninsu yaji sauki sudawo gida,
Har bayan kwana biyu gidan su ba asaniba seda Yaya asam’u takirata take fada mata suna asibiti da jabir,
Yaya tayi mata fada sosae dan bata fada ba har ankwana biyu,
Alokacin kuwa badee zaune kawai take tana jira taga abinda Allah zeyi.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you baby nurse(fatima zarah)_ ILYSM
*Abu na uku dayake janyowa mutun bakin jini shine munafurci*
*munafiki betaba farin jini ba, munafiki annobane idan ana zaune dashi babu abinda yakeso irin yaga ya tarwatse zaman*
*munafurci yana kunshe da abubuwa ne guda uku*
*abubuwannan guda uku idan mutun yakasance acikin daya dagacikinsu to yatabbata munafikine*
*na daya shine duk yadda zefada magana to baze fadi gaskiya ba cikin kaso Dari bazaka samu kaso daya dayakasance gaskiya ba acikin maganarsa wannan shine makaryaci zakuga daga yazo za afara sulalewa saboda ansan indai yazauna ya ringa zuba karya kenan and the worst part of zama makaryaci shine duk yadda yazo da gaskiya baza’a taba yarda ba koda kuwa ze hadiye Qur’an yana kashin ayoyi ne baza’a yarda ba saboda kasaba zama kana sharara karya watarana zaka iya zuwa kayi magana akan abinda kai ko waninka yake bukatar taimako alokacin amma kowa seyai buris dakai saboda bakada gaskiya kunga kuma tun anan ansamu matsala kenan*
*munafurci babbar cutace don Allah mukiyaye*
Page 8
Yaya asma’u ta firgita sosae dan ganin yadda kan jabir yakumbura sosae se kuka yake batun atada shi zaune bema tasoba ga uwarsa ma akwance wani kalar jiri take gani idan ta miqe gani take dama takoma hagu (abin tausayi),
Dasauri anty asma’u takira yayansu mukhtar tafada masa halin da ake ciki ba bata lokaci ya iso asibitin,
Yayi mata fada sosae ganin yadda jikin yaron yayi tsanani amma ace har kwana biyu bata fada ba,
Hakuri tabasu wallahi ita batasan mema zatayiba abubuwa sunmata yawa itama batada lafiya,
Yanzu ina baban sa? Ya mukhtar yatambaya,
Tun ranar damukazo ko awaya bekara kiran mu ba kuma yace kar akara tambayarsa koda kudin maganine aranar ma bebiya kudin komai ba yayi tafiyarsa,
Magana take tana kuka da alama ma batasan maganar nafita ba ganin yadda idonta suke a rufe,
Bari kuga naje naga Dr daga baya mayi maganar yaronnan yanajin jiki idan aiki za aimasa senakira babansa muji yadda za ayai yana gama fadar haka yafita daga dakin,
Shiru tayi tana kallon yadda jabir yakura mata ido ko k’iftawa bayayi ahankali ta riko hannunsa kara riqe hannun yayi yana lumshe idonsa bayan dan lokaci taji yasauke ajiyar zuciya kuma ya dan saki riqon dayayiwa hannunta, gyara masa kwanciyarsa tayi dan yaji dadin baccin,
Asma’u nagefe tana kallonta atake taji zufa nakaryo mata,
Mukhtar ne da Dr suka shigo dakin ze duba jikin jabir susaka lokacin da za aimasa aiki,
Yaya asama’u tana gefe tanajira taga yadda Dr zeyi bayan yagama bincikensa,
Dagowa yayi yna kallon badee dan yasan itace uwarsa besan taya zefara fada mata jabir ya rasu ba se kawai yaja hannun mukhtar suka fito,
Se hakuri yace yana kallon mukhtar,
Allah yajikan sa yasa me ceto ne wannan yaron yafi 30mnt darasuwa kuyi hakuri yana gama fadar haka yajuya dan ganin yadda mukhtar ya qame,
Dake wayayi yashiga dakin kokallonsu bebiye ba yashiga nado jabir acikin zani yamaida kallonsa ga badee,
Ku tattaro kayannann mutafi gida,
Dasauri tadago tana kallonsa atake tagano jabir mutuwa yayi ganin yadda mukhtar yarufesa ruf har fuska da zani,
Batasan lokacinda takai jikin bangoba dakarfi ta rufe idonta kafin tabudesu atake idonta sukayi ja kuka takeso tayi amma yaki zuwa,
Asmau ce tashi ga hada kayan cikin karfin hali tanason yaron sosae amma yakamata ace akwai Wanda ze karfafawa badee gwiwa kodan lafiyarta da abinda ke cikinta,
Har yanzu tana gurin takurawa kofar da mukhtar yabi yafita da gawar jabir ido,
Hannunta Asmau taja suka fita binta kawai take batama ganin gabanta,
Yaron ya kwanta mata sosae azuciya tanasonsa yanada sanyin hali tasaba dashi shine Abokin hirarta,
Yasan yasaka hannunsa yana share mata hawayen fuskarta duk lokacin dayaga tana kuka se lokacin taji hawaye masu zafi sun zubo mata batayi kokarin hanasu zubowa ba,
Tanaso sucigaba dazubowa kozataji sanyi azuciyarta.
_kuyi hakuri da wannan wallahi yau se a slow nasamu deepcut ne dan yatsata_ILVY oll.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin naki ne anty bilkisu (maman nu’aym)_
*kada mudauki rayuwar duniya abakin komai domin ba komai bace*
*Arayuwar duniya mutun uku ne sukafi kowane mutun bakin jini*
*mutun nafarko shine mutun me girman kai yanajin kansa so high idan yashiga mutane seya ringa d’age d’age yanajin yafi kowa,to wannan mutun zakuga kowa bayason haduwa dashi domin zuciya tafison Wanda yake kyautata mata semu kiyaye wannan idan munshiga mutane semu kyautata mu’amalar mudasu saboda mutane Rahama ne*
*Allah yabamu hakuri Ameen*
Page 6
Yaran dukansu suna makaranta daga ita se jabir suna zaune a corridor yana ta wasan sa miqewa tayi tashiga daki dan jin karar wayarta,
Bata fito ba seda tagama wayar dasauri tadaga labule tana fitowa danjin karar wani abu,
Tsayawa tayi tana kallon abdulmajid kafin ta maida dubanta ga jabir dayake kuka haryana shidewa ga gefen fuskarsa yayija harya soma kumbura dauke idonta tayi daga kallonsa takarasa kusada abdulmajid tanayimasa sannu dazuwa cikin karaji yafra magana,
Banason sannu dazuwanki munafuka nahanaki zama dayaranki duk inda nake ajiye kayana amma dan wulakanci shine zakibar wannan yaron yataba min takalmi yau dasafe nabawa me shoeshiner ya gogesu kalli yadda danki yasaka musu kura bayan hakama kinsan ko nawa nasiye su?,
Kallonsa kawai take kafin tamaida dubanta ga takalmin babu alamar kura kokuma antabasu,
Wanine yataboshi awaje shaine yazo yasauke hannunsa kan dan bawan Allah kobadan komaiba kodan yarintarsa ze masa uzuri,
Batace komai ba tasamu guri ta zauna kallon jabir din take da wahala tasakashi bacci gashi balafiya gareshiba yauma da zazzabi yatashi,
Bin bayansa tayi da kallo yadda ya daki kofar dakinsa yashige tabe baki tayi,
Azuciyarta tace yau nayi niyyan fadamaka ina dauke da cikinka Na shida amma naga kanka Na hayaki batason hayaniya yau shiyasa zanbari harka huce komai zakayi sekayi,
Adaki kuwa mamakin hali irin na badee yake ko yaki ake bisa kanta inbataso tankawa ba bazata tanka ba shikuma abinda ya tsana kenan yafiso tabiye mai suyita yi amma betaba samun haka ba,
Fama take da kanta gakuma jabir yatashi da zazzabi me zafi dan ko zama yakasayi se mak’alk’aleta yake dakyar tasamu tashirya yayyensa suka tafi islamiyya,
Paracetamol tabashi na yara Allah yataimaketa akwai shi goyashi tayi tashi ga kitchen dukda tanajin badadi jiri takeji gakuma zafin jikinta yana haduwa da nasa seta ringajin wani iri,
A daddafe tasamu ta kammala abincin takoma daki ta kwnatarda jabir dayayi bacci,
Se bayan isha tasamu kanta yaran duk sunyi bacci saboda wahalar wuni amakaranta,
Kallon fuskqr jabir dake gefenta take shatin yatsun babansa da ya kwandara masa mari dazu gasunan radorado wurin ya kumbura tausayinsa yakamata batasan lokacin da hawaye ya zubo mataba dasauri tasaka hannunta ta goge hawayen fuskarta jin abdulmajid ya kwallah mata kira tashi tayi kafin ta amsa da muryarta can ciki,
Yawwa badee nace abdulrahim yaci abinci kuwa naji shiru kamar yayi bacci,
Gyada masa kai kawai tayi danjitake bazata iya magana ba,
Bakida bakin da zaki amsamin ne?
Eh yaci tayi maganar dan batason hayaniya,
Janyota yayi jikinsa yana tambayarta,inafatan kema kinci?
Eh tace tadora da fadin,
Kayi hakuri yau bazan kwana adakinka ba saboda jabir bayida lafiya tunsafe yake fama da zazzabi,
Nikuma ina bukatar ki,
Yafada yana harde hannayensa akirji yazuba mata idanuwansa,
Kauda kanta tayi gefe dan batason irin wannan kallon kafin tace,
Kasani bazan bar yarana sukadai adakiba kuma daya cikinsu babu lafiya ze iya tashi cikin dare shisa nace kayi hakuri yau kadai,
Banyaddaba inkuma kin yadda ki kwana cikin tsinuwar Allah da mala’iku ne karkizo,(wai kuti ke cewa kaza k’azama)
Kayadda nazo dashi dakinka? Ta tambayesa cikeda gajiya da maganar,
Banyadda ba nafada mini,
Yafada tareda ficewa daga wurin yana barinta atsaye,
Takasa koda motsi dangaskiya bazata iya barin dantaba ga bayida lafiya.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
Assalamu alaikum
Dafatan munyi azumi da sallah lpy? Allah yakarbi ibadunmu ameen.
Inajiran goron sallah na 😎.
Page 9
Badee’a tayi lkuka harta gode Allah sotake taga laifin mijinta nakin kulawa da lalurar data sami dansa har yakai ga ajalinsa,
Majid mugune Dabadan se lkcn mutun yayi yake mutuwa ba da ta dauki kaddarar mutuwar jabir rankatakaf ta rataya awuyan majid sekuma wannan yaci karo da abu biyu sonda takeyiwa mijinnata dakuma albarkacin yayan dake tsakaninsu,
Bangaren majid kuwa mutuwar ta dan tabashi sbd betaba kawowa yaron mutuwa ba gashi badi’a ko kallonsa batayi tunjiya bayan dawowarsu daga asibiti dyasani yake dabe kula yaronba lkcn dayake bukatar taimako kobadan kasancewar sa dansa ba kodan mahaifiyar yaron dayake matukar so tawani bangaren kuwa abincin da yan tsirarrun mutane masu zaman amsar gaisuwa en uwansa da nata keci shine yakeji kamar naman jikin sa ake cira gani yake kamar tattalin arzikinsa suke cinyewa gsky akwai matsala baze iya yin wani yunkuri na hana zaman ba amma yana ftan daga Gobe arufe zaman makokin (wannan ko dai Dan iska ne🤔),
Dahaka rayuwa take tafiya har akayyi wata biyu da rasuwar jabir babu abinda ya sauya a al’amarin majid da gidansa badia wahala take ga wannan karon batayi sa’ar cikin ba yana bata wahala sosae sana’ar da take bakullum takeyi ba yaranta duk sun fita hayyacinsu,
Yauma kamar kullum ta tashi se a hankali dakyar ta hadawa mijin breakfast yafita aiki ga yunwa Dan kadan tahada danata bayawa Dan haka yaran kawai sukaci tace zata jira abincin rana lkcn cikinta yana wata shida kenan,
Bayan azahar yadawo gida yasameta kwance a korido zazzabi yahanata sukuni ga jiri,
Yaya asma’u ta taso daga aiki tace zatazo taduba kanwarta tundaga waje take sallama bataji an amsaba,
Maganar majid taji yasa ta tsya awaje,
Zma yayi kusa da ita en mata abani abinci na debo yunwa garinnan rana tayi yawa,
Don Allah kayi hakuri wallahi yau banajin dadi banyi girki ba,
Miqewa kawai yayi ya soma fada,
Dan bakyajin dadi sena zauna da yunwa kullum seki lafe kice ba lpy amma kin iya yin sna’ar ki seni zaki zalunta kibarni da yunwa? To wallahi kinyi kadan yanzunnan kitashi kidafamin abinci inajiranki Dan Nagano nema kike kizama muguwa,
Batason masifar nan shiyasa ta miqe zuwa kitchen tasan idan ba girkamasa tayiba masifa zetayi,
Yaya asma’u wni abune ya tsya mata awuya zuciarta tadau zafi Tajuya tabar gidan dole sudau mataki baze yiyu sunaji suna gani a kashe musu er uwa ba tafiya take tana kwalla sbd tausayin kanwarta mijinta takira tafada masa tana hanyar zuwa gdn ya mukhtar zasuyi magana ne yasan batada yawo Dan haka ya amince,
Tayi Sa’a yayan yana gida yadawo da wuri tazauna ta labarta masa komai datasani tun bayan haihuwar abdulrahim har zuwa yau,
Yayi masifa kamar ze cinyeta danme tayi shiru seyanzu tafada masa yabashi hakuri yace tawuce gida zeyi tunanin me zasuyi,
Washe gari tunda sassafe yaje gidansu yazauna da iyayensa cikin kwamciyar hankali yafadamusu yadda sukayi da Yaya asama’u yakuma cekarsu daga hankalinsu baba yashirya ranar asabar zasuje gidan dole sudau mataki mahaifiyarsu har kuka tayi sbd tausayin erta da halin datake ciki,
Sunyi sa’ar samun majid a gida Dan sammako suka yi idonsa zuru zuru domin be taba ganin alhaji a gidan ba sama sama suka gaisa Yaya mukhtar yanemi akira masu badi’a Gabanta yayi mummunan faduwa dataji lbrn babanta ne da kawunta se Yaya mukhtar harda asama’u aka zo,
Tass suka zube masa sunsan halin da badi’a takeci Wanda sune shida mahaifiyarsa suka sanyata ciki atake ya kidime zufa yafara karyo masa,
Alhaji ne yafara magana
Abdul bana bukatar sulhu Sakar min yata zakayi yanzu base anjimaba sbd itama haifarta akayi ba jaka nakawo maka ba kuma tanada gata gaba da baya kuma inaso kasani Yaya dakake cewa bakaso naka ne kokaki kokaso Dan kasanima yanzu idan zamu tafi iya kadai zan dauka nabar maka yayanka shima wannan cikin wallahi daze yiyu nabar ma ka shi baze taka kafarsa gidana ba sekaje can kasamu wacce batason Yaya irinka ka aura,
Seyanzu yasan yana cikin tashin hankali Dan harya fara hango rayuwarsa babu badeea ya hango rashin kwanciyar hankali tsintsarsa aciki yatafi duniyar tunani kukan badee ne yadawo dashi,
Ta kama kafar alhaji,
Baba don Allah kayi hakuri karka rabani da yayana da mijina wallahi inasonsu kubarni dasu kodan tarbiyar yayana,
Garama kidaina rokona bazan juri ana wulakanta ki ina kallo ba kobana raye bazan yadda ba,
Baba wallahi inkuka rabani da majid zan iya mutuwa wallahi inason uban yayana ,idonta yarufe da soyayyar mijinta bata gani bata hango abinda magabatan ta ke hango mata duk baba har aransa baso yake yarabata damijinta Ba yaso ace tabashi hadinkai ya hora majid amma takawo cikas,
Akaro na uku baba yasa ke umurtarta data tattaro kayanta kuma bayaso tadauko yaro ko daya acikinsu abdul ,
Idonta arufe tana kuka tace baba kayi hakuri bazan iya barin yayana ba nasani wata rana zasu zama ABIN ALFAHARINA don Allah kutausayamin Ku hango abinda nake hangowa,
Zuciyar baba takawo wuya mikewa kawai yayi yace duk abinda yataso koyasameki ko yayanki karki sake kinemeni bejira su kawuba yafi ta,
Yaa mukhtar yamiqe shima idonsa yayi ja sosae zefita tariqo kafarsa tana roqonsa tana kuka kokallonta beyiba sbd tawulkanta su aganinsa yajira tasake masa kafa yasakai yafi ta kawukam yaga kowa yafi ta shimexeyi seyabi bayansu,
Gun asama’u taje zata fara mata magiya ta daga mta hannu tana miqewa tsaye kafin tace ba kinzabi mijinki akanmu ba aiseki zauna gashinan kuma kisa aranki bakida er uwa asama’u aduniya tana gama fdar haka tafita.
Kuka sosae badeea take batasan INA zata sakantaba en uwan datake takama dasu sungujeta harda mahaifinta .A gaskiya ta matukar bashi tausayi musamman dayaga tana kuka sosae kuma yasan tanada hakuri fiye da tunanin sa tabar iyayenta da en uwanta ta zabeshi yana fatan kada wannan yazama babban kuskure da zatayi arayuwar ta sedai fa yarannan nata idan yagansu jiyake kamar ya sheqesu sunyi masa yawa dayaso kada yayan su suwuce biyu haka amma ummansa takawo matsala na rashin son tsarin haihuwa…..
Jin an riqo masa kafa yasashi dagowa yana kallon yadda take kuka kafin tfara magna,
Abdulmajid don Allah katausaya min da yaranmu kar rayuwar mu tashiga garari kasani auren soyayya mukayi abinda kake mana be dace ba koba don komai ba haqqinmu ne daya rataya awuyanka ka kula mu,
Wannan haqin data ambata shiyasa shi jin haushi Dan haka tausayinta daya faraji yasoma gushewa,
Abdul nasan bakason yarannan sbd bakaso haihuwarsu ba ammakasani yayanka ne kataimake ni koda da abincin dazasuci ne don Allah ba….
Numfashinta sama sama yake har idonta yafara kafewa kafin yayi wani yunkuri tazube agurin,
A rikice ya sungumeta yana zuwa kofar fita da korido yaga su Abdul awajen take karamin cikinsu yasa kuka ya rasa yadda zeyi dasu dole yasa ka su agaba sukaje asibiti,
Takaici ya isheshi ganin yadda suka cika masa mota kamar wata nursery skul bus,bayan sun isa ya cewa abdulrahim ya kakula karyabari sufita daga motar kuma karsu taba komai aciki,
Bayan awa biyu likita yagama dubata harta farfado tana kwance yana gefenta se Harar ta yake,
Muryarta harta soma dashewa tace abdulmajid,
Cikin jin haushi yace menene?
Talura da yanayinsa batasan meyasa yakehakaba yanzu, a hankali tace kataimake ni da yayana don Allah hawayene masu zafi suka zubo mata,
Naji zanyi tunani Kuma menene harda suma? Nace zan sakeki ne kokuma nayi sakin ?
Bakasan yanakeji ba shiyasa iyayena fa suka gujeni,
To ba ganiba ai inakusa yanzu gashi kinjamin nakashe kudi dayawa kuma ga kudin wankin mota wayannan yayan naki duk sun batamin mota ke kin cika rigima wallahi kinjmin hasara yau kudinnan wani Abu daze kawo kudi nasoyi dasu,
Idan tanabiyewa majid seciwon zuciya ya kasheta,
Majid a sallamemu mukoma gida banason asibitinnan,
Fita yayi yadawo da Dr aka dubuta yabata magunguna kafin ya sallamesu,
Bayan kwana biyu bata chanja zaniba dn majid baya wuni a gidan Sam balle Taji inada maganarsu ta kwana se ranar data ristashi tun asuba take tambayarsa kan maganar babu yadda zeyi koba komai tbar iyayenta sbd shi,
Kiringa dafa abinci dasu ama wallahi kar naga abinci anraga ko an zubar ina ganin haka za asamu matsala bani key din store,
Damamaki take kallonsa mezakayi dashi? Ina ruwanki ki bani key nizan ringa dibar kayan abincin dakaina yawan danakeso,
Bataso tayi gardama yace yafasa ta samu ya yarda Dan haka ta miqa masa yayi yadda yakeso fatnta dai Allah yasa yabasu Wanda ze ishesu zata ragewa kanta damuwa sbd batada kowa kusa yanzu Dan jiyama takira kanwarta farida awaya taimata rashin kunya kamar ba kanwarta ba,
A can gidansuma Hajiya Taji kwana biyu ba lbrn yasukayi da badee’a Dan haka seta tambayi abbansu yadda ya amsa mata yasa takama kanta Dan cewa yayi intanason knta da arxiki karta kuma yimasa zancen badee kuma bebata izinin nemanta ba,
Dahaka rayuwarsu tacigaba da tafiya duk ranar da yaga dama seya basu kadan koyaki dawowa dawuri balle yabasu na rana wahala suke itada yaran Dan yanzu makaranta me kawai be chanjawa Abdul rahim ba amma bakin jinin yayanta a idonsa yajawa abdulrahim haushi baya samun abinci sesanda baban yadawo yadebo musu daga store kafin tagama girkawa itada yaran sun tagayyara musamman ita datakeda ciki gashi yakai wata takwas yayi girma naban mamaki kana ganin ta kaga damuwa cikin kadai ke girma kodan kumburin damasu tsohon ciki sukeyi ita batayi komai yinsa kawai take bata wanidamu da sana’ar taba sbd duk ranar datayi wani abinci kafin yadawo dakudin ze haukacemata yace yadaina ciar dasu shagonsa yayi kasa ma sbd ciyarda yaranta dayake shiyasa duk yadda tatara kudin sedai tayi tanadinsu tayiwa yyanta lalurar makaranta, kona asibiti,
Tana zaune a korido itada yaranta Dan yau babu islamiya yunwa natacinsu har karfe hudu da rabi be dawoba Sega sallamarsa yashigo ta amsa masa tana hamdalan dawowarsa,
Hada ido sukayi Taji gabanta yafadi kwata kwata batason abin yanzu ga yunwa tanaji su abdul bame iya kwakkwaran motsi sbd yunwa,
Majid don Allah kabari nabawa yarannan abinci tukunna,ohhh yaranki sunfini kenan inace nine me bada abincin? Tona fasa sekinzo muntafi inbazakiba seki nemi abinda yayanki zasuci,semi zauna da tsinuwar Allah data mala’iku (besan Allah ba se anan)
Dakyar tamiqe tana dafa bango ta cewa abdulrahim kaje da kannenka palona kucigaba da kallon cartoon yanzu zan dawo damurnarsu suka wuce itaam taigaba gogan yabi bayan ta,
Dakyar tayi sallah magriba sbd tsananin gajiya,yana kwance tace Abdul muje kabani abincin na dafa mana,kibari nahuta mana Nagaji baccima nakeji,daga haka yagyara kwanciyarsa,
Ranar dai se 9 sukaci abinci yaranma har sun fara bacci ta tashesu tabasu kafin taci nata ta kwnta,
Ranar alhamis dasafe bayan tadwo daga awo tace bari ta leqa gidan su kafin taje gdnsu majid daukar yaranta ta tsaida adaidaita tashiga gdn gabanta ne yafadi ganin baban su zaune tunkan taaraso yasamata stop,
Kifitar min daga gida kuma kar kafarki tayi tunanin sake dawo min gida bude baki tayi zatayi magana yace bana bukatar jin komai daga gareki kikoma gun yayanki da mijinki masoyanki kuma kifita da Sauri,
Tana kuka tabar gidan ga ciki dakyar take takawa tayi danasanin abinda tayi dma tayarda ta bisu a ranar daga baya ta lallabasu ta dawo gdn mijinta,
Har ta isa gidan su majid kuka take kafin tasamu kakarsu ta lakadawa Abdul’aziz duka yamata banna,
To muna fuka…..
Nagaji😳anty badee🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfaharina)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
This page goes to u my sister,my frnd anty shukra(Zainab yakasai)ILY.
Page 11
Daga bakin kofar ta tsaya tana sauraren kalar cin zarafin da Hajiya ke yimata yau tasaba zuwa gidan Hajiya tayimata wulakancin da bata zato amma nayau yafi kona mata rai,
Ki karaso mana kiga kalar bannar da danki yaimin Nagano dalilinki nakawo minsu duk lkcn dazakije asibiti sbd kawai ki takurawa rayuwata Dan kinga bana hanasu abinci bakyaso kiga cigabana dani kike kishi Dan Dana yana kula dani to wallahi daga zan dau mataki zo ki kwashi yayanki kubarmin gida tun bankaraa daukar zafiba na illata daya daga cikinsu,
Batareda ta musa ba cikin karfin hali ta dauki abduljabbar daketa kuka yasha duka ta gargada sauran tayiamata se anjima memakon ta amsa se cewa tayi,
Aikam dai dole atafi mace ba control daga antaba ta seciki ke bakya gajiya da haihuwa ne kiketa zubo Yaya haka kamar wata akuya?,
Idan ta tsaya sauraren wannan zancen tsaf naquda zata kamata Wanda ze iyasakata haihuwa akan hanya kirjinta taji yayi nauyi sosae,
Adaidaita ta Tara duka kudin hannunta dasuka saura 90 naira ne da bata biyo gdnsu bane kudin ze isa akaita gd me adaidaitan dayaji kudin data ambata se kallonta yayi sheqeqe, amma malama ina ganin bakida hankali ko? Yoke konace kikawo kudin nakaiki zaki shiga? Ga Yaya rututu? Nikam ba bakin uwa gareniba,shiru tayi tana kallonsa kafin daga baya yaitafiyarsa hakan yasa taja hannun sauran suka fara tafiya akafa seda sukayi nisa sosae ta tari wani adaidaitan dayake sunci Rabin tsfiyar yasa yadaukesu,
Wai Hajiya haryanzu bamu iso bane? Eh seka wuce wannan sabon masallacin kadan, ashar ya lailayo bejira tayi magana ba yace kibani kudina malama ki sauka irinkune basason ganin cigaban mu kinsan har nan zan kawo ki baki tsaya yimin bayani ba,kudinsa tamiqa masa dn tasan yau in batayi ahankaliba zuciyarta fashewa zatayi,
Dakyar taga sun isa gida da zuwanta tasamu abdulmajid yana gida batabi ta kansaba tashige dakinta wanka tayi tayiwa yaranta suka kwanta,
Yaran duk sunyi bacci sbd gajiya itakam takasa baccin ma tunani take EDD dinta saura kwana biyar sotake ta sauke cikin nan sbd ya isheta sosae ba kadan ba bata taba yin ciki me kwatankwacin rigima irin wannan ba fatanta dai Allah yasauketa lpy dole tfara shan magani tsarin haihuwa aboye sbd tagaji sosae ga yayan bawani gata garesuba ita kanta tarasa nata gatan,murmushin dyaafi kuka ciwo tayi tace a fili yaushe rayuwata zata dawo daidai kamar ta sauran mutane?nasani abune me wahala asamu wata me irin matsalata arayuwa uwar miji da miji sun sakani a tsakiya sun dauran laifin dabanawa ba sunkasa gano laifin daga garesu ne shi mijin bayason haihuwa yanaso nayi family planning uwar mijin tana son jikokai tahana ayi family planning gashi yanzu tasoma goyan bayan danta bayan dakomai yagama lalacemin, hawayeni suka zubo daga idonta amma abin mamaki hawayene masu sanyi kuma daidai lkcn babyn dake cikin ta yayi kicking ahankali tashafa cikin tasa hannu daya tana goge hawayen fuskarta,
Sallamar majid yasa tadawo daga tunanin datake se cewa yayi badee zokiga wani Abu yana gama fadar yafita rigarta tadauko tasaka tabi bayan sa A gefen gado tasameshi dasaurinta takarasa yazauna gefensa sbd kafafuwanta dasu kayi tsami sbd tafiyar kasa,
Gani me Zan gani Abu abdulrahim? Bata ga komaiba illa jin bakinsa kan nata😳,
Bayan lafawar komai tashiga sheqa amai batasan dalili ba, gefen gadon ta kwanta tanajin mararta nadan ciwo shiru tayi kafin tafarajin abin yana Neman yafi karfin ta,
Batayi zaton abin zekai haka ba segata adurqushe dakyar ta ke numfashi,ganinta awannan yana yin yasashi rikicewa yafara tambayarta menene?
Abdul muje asibiti inaga haihuwace,
Haihuwa ya maimaita,kuma a asibiti? Nibazan iya Da wannan kashe kudinba ki kira Yaya asama’u mana,
Batasan me zataceba kada tayi magana ya tunzura,a wahale tace don Allah majid kakaini asibiti kasani Yaya bazata zo ba don Allah karna mutu bakasan me nakeji ba,
Dakyar suka isa asibiti bayan ankarbeta yawuceda yaran yakaisu Inda Hajiya seda ya lallabata ta karbesu,
Kusan awa uku tana fama kafin tahaihu tasamu baby girl yarinyar wata kalar katuwa Dan seda akai mata sbd girman babyn,
Wallahi badi’a Nagano babu abinda yake burgeki irin kiga tattalin arzikina ya dakushe kalli bill dinda akayomin fa? Sekisann yadda zakiyi dashi yafada yana jifanta da papern,
Binbayansa tayi dakallo seda tadaina ganinsa kafin tadawo da kallonta kan nurse dinda ke dakin tazo cire mata cannula juyawa tayi tana ajiye babyn agefe tafara kuka,
Matar zatayi sa’an Yaya asama’u durqusawa tayi ta dauki papern tafita,
Batasan iya adadin lkcn data dauka tana kukaba seji tayi andafata ta dago tana kallon matar,
Matar ta sakar mata murmushi,
Hajiya badi’a ansallameku sbd keda babynki kunanan lpy Dan haka seki tashi kitafi gida ana bukatar gadonnan,
Shiru tayi tana tunanin bata fito dawayanta ba Waze kaita gida ga babyn ko kayan sawa batada su adankwalinta aka nado ta,
Kitashi mutafi zan saukeki gida tundazu dutyna yakare ganin kina wahala yasa ban tafiba najira har naga me Allah zeyi kiyarda dani bazan cutar dakeba sunana Zainab Muhammad,
Godiya sosae tayi mata har zata fita daga motar Zainab tace, dafa tan kinada me kula dake naga tafiyama dakyar kikeyi,
Babu kowa nikadaice se yayana kuma duk mazane kanana,
Batareda ta amsataab tajanyo waya da alama mijinta takira tana Neman izinin zata taimakawa wata baiwar Allah a gidan ta kuma be hanataba,
Turus tayi tana kallon….
Nayi kokari yau tun asuba nake typing😜🙈
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: *Y’AY’ANA (Abin alfaharina)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
Abinda duk ka tsarawa rayuwarka ba shine tsarinka ba domin tunkan kazo duniya Allah yagama tsara yadda rayuwarka zata kasance tun ranar da aka haifeka har zuwa ranar dazaka koma garesa, duk abinda kaga Allah yayimaka shine daidai dakai semuyi imani da kaddara me kyau ko Mara kyau wanda yayi haka shine cikakken musulmi kuma me imani,ina rokon Allah da ya tabbatar mana da alkhairi arayuwar mu ameen.
Anty badee wannan shafin nakine kekadai kaunar dake tsakanin mu ta dabance ina rokon Allah yabarmu tare yakuma bawa ustaz lafiya ameen.❤
Page 12
Turus tayi tana kallon su Abdulrahim su kadai awaje ga kofar korido abude da alama babansu yananan dasaurinta cikin karfin hali takarasa kuSadasu,
Abdulrahim mekukeyi anan?
Hajiya ce takawomu wai fita zatayi bakowa a gidan bamu gankiba munata kuka babanmu yadawo yabude gida shine yace nazo mukwanta muyi bacci amma karsu Abdul’aziz sushigo zasu damemu shine nace banajin bacci yai fushi yace inmuka shigo seya zanemu kuma munajin tsoro,
Yakarashe maganar yana kuka batasan lkcn data janyosu jikin ta ba tafashe dakuka yaran ganin uwarsu nakuka se hankalinsu yatashi suka biye mata,
Zainab dake kallon su ta lura daga yaran har mamansu sunada damuwa sosae kusa dasu ta matsa tace maman baby kina bukatar wanka ki huta ki ajiye damuwarki gefe yanzu kinga magriba ta kusa inaso in koma gida dawuri tun safe nafito,
Murmushi nadole badee tayi tace kiyi hakuri nabarki a tsaye,
Bakomai ai,
Ruwa tahada mata tai wanka tahada mata tea tasha seyaba kyaun gidan take talura mijin ne bashi da hali amma gdnsa ya tsaru ta tabbata gidan ta baze fi wannan ba duk dukiyar mijinta da baban ta kuma ga alama mijin Dan gayune sbd talura kamar sbd fenti yayi kamar ba yara a gidan,
To maman baby se abawa baby abincin ta tunda ke kin koshi,
Murmushi kawai tayi taakrbi babyn takalleta sosae sekuma ta share hawayen dasuka zubo mata tana cigaba da kallon yarinyar ahankali tace,
Barkarki dashigowa duniya me tattare da abubuwa naban takaici abubuwa naban tausayi abubuwa na jin dadi, kuma ina miki barka dashigowa gidan babanki dabaya kaunarki baya maraba dake barka da zuwa hannun mamanki me cike da kaunarki Barka da zuwa hannun yayyenki masu sonki insha Allah ina adduar Allah yabaki juriya da hakurin zama wannan gidan mecike da bakinciki ina miki Barka……
Zainab ta rufe mata baki da hannunta, haba maman baby kada bacin rai yasaki furta abinda ba shikenan ba ki yadda wannan rayuwar taki d yayanki kaddara ce kuma kiyi imani da ita kikasance me hakuri kuma irin hakurinda baya karewa kinji,
Gyada mata kai kawai tayi tace kitashi anty Zainab kitafi gida dare nayi kilama kin barwa megidanki hidimar yara,
Murmushi me ciwo Zainab tayi tace megidana ba shida matsala koda zan kwana nanne kuma banida yara koda ya,
Ganin yadda badee kekallonta yasa tace kibari gobe zan dawo idan na dawo Zan baki lbari bani numbernki zankiraki kiga tawa sekiyi savin idan da Marsala ki kirani, bayan fitarta badee taga transfer na Dari biyar tayi murna sosae sekuma tayi shiru tunawa da kotakira ba daga wa zatayiba data ta siya tabude watsapp dinta kai tsaye tanemo sunan yaya asama’u tatura mata massage kamar haka…
As salamu alaiki
Yaya Allah yasaukeni lpy yau nasamu baby girl kitaimakemu koda da addua ne kadai na gode.
Tatura mata hoton babyn gatanan dake take kama har bakinku iri dayane.
Kwanciya tagyara musu kafin tashiga tunanin abdulmajid yana gidan amma bezo yadubasu ba hakan yasa tanufi dakin sa dauke da babyn,dasallamarta tashiga dakin zaune ta samesa yana signing wasu takaddu, zaunawa tayi kusa dashi tayi shiru,
Ya akayi? Yatambayeta yana cigaba da aikinsa,
Yarka nakawo maka naga ko daukarta bakayi ba,banida bukatar daukarta naganta ahannunki ai,
Bata karayin magana ba tayi shiru kusan mintuna goma sha Biyar kafinnyadago yakalleta se idonsa suka sauka kan babyn dake ta sharar bacci abinta,
Ka taimakeni Abdul koda hudubane kayi mata kasamata duk sunan dakakeso don Allah tafada cikin rawar murya,
Shiru yayi yafafda kogin nazari,yakamata yashare mata hawayenta kardamuwa taimata yawa ga babyn data Haifa kyakkyawa yaji yarinyar tashiga ransa fiyeda abdulrahim dole yaimata suna da sunan dayafiso aduniya,
Taga kamar ba shida niyyar yin abinda ta roqa seji tayi ya sunkuci yarinyar yana murmushi harda bisimillah,
Bayan yagama abinda yadace yamiqa mata babyn yace sunan ta LUBNA(I’m in love with this name❤),
Murmushi ne ya kwace mata lkn data tuno hirar dasu kayi auren su saura sati biyu,
Baby badee wane suna kikafiso asawa yarki ko danki? Idan nahaifi namiji nafiso asamishi abdulrahim ko abubakar sadeeq inkuma macece nafison Fatima ko safiyya🙈 ,
Murmushi yayi yace nikuma nafison sunan babana Abdul’aziz idan macece nafison Lubna❤,
Kai amma baby bantaba jin sunan ba idan nasamu baby girl zakasamata Fatima tabiyun kuma sekasa Lubna din ko?,
Badee kije ki kwanta kingaji yafda yana mikar da ita,
Wani kalar dadi taji daysa dole seda tayi hugging dinsa sosae irin sosae dinnan 😂😍
Wanna page din Na gobe ne lol. Luv u oll😘
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine meela adeel(meelolo mekan giginya😂😜).
Page 13
Shifa ko period take becika son cin abincin data girkaba sbd kyankyami kawai dai ta iya girki ne,
Badee meye haka kisakeni mana bakyajin karninda kike keda babyn😣,shiyasafa banason haihuwar nan karnin nono da jini duk su dame mutun dauki babyn ki kutafi se dasafe,
Tasani sarai bawai don yanason babyn yasa mata sunaba kawai dai yanada wata manufa ne talura da yadda yake kallon yarinyar ko abdulrahim baya kallo haka,
Bayan fitar ta daga dakin yasoma tunani, akwai matsala babba indai ba umma ce ttaadawa en uwansu Na kwareba baze fada musu haihuwarnan ba kauyawa suzo su cika masa gida acinye mai abinci subata mai gida,
A bangaren yaya asama’u kuma tana zaune tana tunanin halin da er uwarta take ciki kila yanzu tanachan da cikinnan yasata agaba ba lpy ga yara,tsaki tayi bayan tuno yadda badee tayi agaban mijin tanuna ta mato akansa dole yaji dadin kara wulakanta ta kuma tawatsa musu kasa a ido amatsayinsu na en uwanta da mahaifanta, wayarta ta janyo tanaso tadaina tunanin badee tashiga WhatsApp da sauri tannufi number ganin anturo hoto kodai hotonsu ne tafada afili har zata wuce se kuma ta dawo,
Sosae take kallon hoton har batason kyafta idonta, masha Allah tafada tana shafa screen din wayarta ga yarinyar kyakkyawa me kamada ita amma babu halin kulawa da ita bazata taba shiryawa d badee ba se lkcn databar gidan Abdul majid sbd jityi ko sunansa batason tunawa balle taji wani yafade shi hartakai ga ganin mesunan,
Amma setayi kokarin ganin zuciyarta tahanata zuwa ganin babyn karta ruguza komai,
Washe gari Zainab tana off nakwana biyu hakan yasa ta kammala komai Na gidanta bayan ta sallami mijinta yatafi aiki ta shirya komai tanufi gidan badee, a korido ta sameta tana bacci tun a tsakar gida take sallama bataji an amsaba, Allah sarki ta fada a fili,gdn angyarashi komai tsaf tayi wanka tayiwa babyn sunata bacci abinsu ga alama ma yaran basa gidan,
Farkawa tayi idonta sekan Zainab da sauri tatashi zaune,lahh Anty yaushe kika shigo? Inata baccin gajiya nasha aiki,
Ainaga alama kam keda kikeda Dinki ajikinki meye naki Na wannan urban aikin,
To idan nabarshi Waze yimin? Banidakowa akusa,
Baganiba inji Zainab tana murmushi, bani babyn a huda mata kunne kafin tagama sanin zafin jikinta,
Bayan angama huda mata kunnen Zainab ta tattara nutsuwarta ta fuskanci badee,
Inaso kibani labrinki kumabawai don inason sanin sirrinki bane sedan inaso Na taimaka miki,
Ahankali tabata labarin rayuwrta Wanda taji zata iya fada,kuka take kamar ranta ze fita Anty Zainab narasa kowa da komai nikadai nasan me nakeji azuciyata idan da soyayyar mijina kadai ta zaunar dani gidanan datuni Na tsufa gidanmu inaso abbana yafahimci abinda nake gudu dayasa ban bishiba kiga yayana gasunan duka mazane babban shekarr shi shida wazan barwa su? Wazemin tarbiyarsu? Kakarsu data hanani yin planning yanzu tabi bayan danta batasonsu kokadan duk lkcn Dana kaimata su dukansu take kamar jakai kiga danta bashida tarbiya kokadan babu abinda yasawa gaba irin Neman kudi abincin dazamuci wuya yake mana inba yanzu daya yadda yake bani komai dakansa ba dukda dagishiri dazansa amiya shine yake debarmin adadin dayakeso kuma idan abincin beyi dadiba ya balbaleni da masifa, Allah yasoni hawan jini bekamaniba kigafa duka en uwana sun gujeni inason ganin mahaifiyata amma banida iko,haihuwa nayi amma bayanke dani bawanda yataba ganin babyn bakuma alamar za azomin barka yayata Dana tura mata hoton babyn ko reply Na Allah yaraya batayimin ba abdulmajid yajanyomin bakin jini agurin en uwana😭,
Dakyar Zainab tasamu ta rarrasheta,ki godewa Allah badee kin samu haihuwar shekarata goma sha uku da aure ko bari bantabayiba dagani har mijina lpyr my qlw babu yadda zanyi inason mijina bazan iya rabuwa dashiba nasan yanason haihuwa amma betaba chanjamin fuska ba ganin idan bansashi yayi aureba awaje abokanansa kokuma mahaifiyarsa zata sashi yayi auren kuma akwai en zuga inagudun su zugashi yajuyamin baya ganin nayi shekara bakwai ba haihuwa nace yakaro aure kila za adace matar ta haihu, yacemin shi bashida ra’ayin mata biyu nikadai yakeso zezauna dani saboda Allah kuma ga yayan yayyensa nan aisun ishemu har kararsa nakai gdnmu babanmu yakirashi amma zancen dayane baze iya karo aureba nikadai yakeso haihuwa ta Allah ce koda yakaro auren idan Allah besa yanada Rabin haihuwa ba bazetaba samun taba,
Badee inason yara sosae shiyasa nace zan koma makaranta nayi skul of nursing bayan nakammala degree Na seban nema aiki dashiba najira har nzama nurse nasan zanyita ganin yara a asibiti,
Yanzu matsalar danake fuskanta itace mamansa tasoma sauyamin bakamar da ba,yaranki sun burgeni sosae kuma Na tausayawa rayuwarki shekarunki sunyiwa damuwarki kadan,
Kema abin atausaya miki ne Anty idan haihuwar alkhairi CE agareki Allah yabaki,nikaina inaganin idan nakara shekaru biyu awannan halin to matsalolina kasheni zasuyi bansan wazan tunkara zuciyata tayi sanyiba damuwa tamin yawa bama kaina nake jiyewa ba yayana rkar rayuwarsu ta gurbace ina iyakar kokarina nagrayuwarsu ta inganta Anty don Allah kitaimakeni da maganin planning bawai nagaji da haihuwar bane inaso ne nadan huta har wayannan yaransu kara girma nasan insha Allah watarana zanyi alfahari dasu,
Amma kekam anyi sakarar mace sauna kuma Allah wadaran wannan mugun halin naki yanzu matar dabaki saniba kika zauna kina zubewa sirrinki?,
Basusan dazuwan hajiyaba sejin muryarta suakyi,gaban badee ba karamin faduwa yayi ba.
Nikaina nafirgita amma nadake sbd jarumta😎
En uwa semun hadu wani lkcn🏃🏻♀
[7/5, 8:08 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Anty billy❤
Page 14
Kekuma munafuka kinzo zaki hure mata kunne ko? Tun wuri ki kwashi kafafuwanki kibar gidannan irinkune sarakan zuga kinzo kikashe mata aure,
Zainab batace komai ba tamiqe tana murmushi,badee se anjima kinji nagode sosae,badee kam ba bakin magana se hawaye zuciyarta kuna take sosae anwulakanta mata bakuwa batasan yazatayi ba,
Bayan fitar Zainab hajiya takaaraso ta zauna itada wata fitsararriyar mata da alama daga kware tazo se kallon gidan take tana yatsina fuska irin kallon datakewa badee yayi kamada harara,
Munzo ganin jaririyane tunda ban isa akaimin itaba ninazo ganin ta dakaina,
Kiyi hakuri umma wallahi yau nakeda niyar idan yadawo daga office mukawo miki ita,
Harseda aka kwana? Aitunjiya yakamata akaimin ita amma dayake ban isaba seda ninabiyota dakaina safara’u karbomin ita nagani natofeta da addu’oin tsari tunba asa tabi sahun yayyenta ba yaranann dakike gani basa kaunata insunganni kamar sunga azara’ilu(wayannan mutanen basuda alkibla ko kadan inace ita take hantararsu harda duka?🤔).
Arnyi mata huduba ne?
Kanta akasa tace eh yayi mata jiya dadaddare yace sunanta Lubna,
Yadda hajiya ta zaro ido seka zata cewa akayi sunan babyn shegiya,
Yanzu sabon salo aka samu baza anemi shawarataba akasawa yarinyar suna? Lallai akwai abinda kikayiwa Abdul wannan karon dole Na tashi tsaye karki rabani dashi, da alaamr mamaki take kallon umman (metake nufi?),
Eh kikalleni dakyau bakar munafuka wacce tazabi namiji akan iyayenta aiba abinda bazata iyayiba,
Safara’u dake gefe tace wai dama mama wannance matar yaya Abdul? Eh itacefa kingantanan kamar diyar roko wannn aise zaman hakri tashi mutafi Allah yaraya tunda kinyi son ranki,
Nan wurin ta zauna ta hsarbi kukanta harta koshi kafin ta janyo wayarta tayi Kiran Zainab kalar hakurin databaa harseda yaso kular da Zainab din Anty kiyi hakuri kuma ban fasason maganin ba inda yadda zaki taimakeni kikawo min don Allah,
Babu komai kibari se jininki yadauke zansan yadda zanyi kuma akulamin da Lubna sosae kinji,
Insha Allah nagode sosae se anjima,
Har ranar suna babu wani chanji agurin majid danshi yace bayason taron suna dakyar yana share gumi yayanka rago daya ranar sunan bawani abin azo agani sukayiba sukadaine agidan daga yaranta se en uwansa daga kware basu wuce su shida suma banda habaici ba abinda suke mata agidan itadai iyakacinta dasu ido da aka shigo da naman kadan ta diba tamiqa musu sauran sukaiwa hajiyarsa batason fitina,
Daga haka rayuwarsu take babu wani ci gaba jiya iyau kalar ramar datayi kadai ya isa yanuna tana cikin damuwa gun Zainab kadai take samun taimako shima Zainab ta daina zuwa gidan sbd haukar da majid yai musu wai be yadda da itaba,
Yanzu lubna tana wata bakwai kome take taji muryar babanta zata rufe ido kota fara kuka lokuta dayawa yakeson daukarta amma bata taba yadda dashiba inkaga dariyarta to gun yayyenta ne ko mamanta,
Ba ita kadaiba har manyan tsoron babansu suke abdulrahim ne kadai yakedan jin sanyi tagefensa kuma har yanzu sunanan da yunwarsu abinci ba lallaine yake basu Wanda ze ishesu ba maganar aci nama batamazo kusaba sedai shi yasiyo yashige daki yaci abinsa badee batada halin Tara kudin sana’arta tasiyamusu abin marmari idan tayi ranar setayi regretting ga uban jaraba musamman yanzu dayaga andau lkci bataace ciki gareta ba se abin nasa yaakra kaimi,
Kuka kuwa yazama abincinta babban bakincikinta bewuce rasa en uwanta datayi ba har gidan yaya muktar ta tafi amma ko kallonta beyiba gashi tanason ganin mahaifiyarta amma abin yafaskara,
Tura abincin kawai take badon tanajin dadinsa ba sedon ganin Lubna tana rama sbd rashin samun isashen abinci damuwarta ta tashafi diyar bayan ta kammala dura abincin tasawa Lubna nono abaki harta kama sekuma ta gantsara mata cizo dasauri ya yakiceta tace,
Yaushe kika zama muguwa harda cizo haka kallon uwar tayi tabingire da dariya su abdulrahim suka kama mata sunata dariya batasan lkcn da dariyar ta kwacemata b tace Amma yarannan sedai nace Allah yashirya minku 😂😂.
[7/8, 2:15 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
A rayuwata ta duniya babu abinda Na tsana irin wulakanci wallahi ko wanda muka fito ciki daya yaimin wulakanci yanzunnan senayi sahur dashi nadau azumin shiga harkarsa Na tabbata babu writer dinda take yin yadda nakeyi wata sekiyi mata magana setai kwana biyu ta amsa shima se idan taga damar amsaki ne amma ni kowa yazo jikin nabari nake kulashi dankar ace nai wulakanci amma dukda haka ban tsallake ba seyanzu nagano abinda yasa ake cewa writers Nada jijjidakai🤔.
Akace shiru shiru……?😕.
Page 15
BAYAN SHEKARA 5
Tun lokacin da safara’u ta zo gidan bayan anhaifi Lubna tamaida gidan digan zuwa ba’a wata daya batazo sokoto ba kuma tana zuwa se gidan Abdulmajid take sauka intazo kwarkwasa da iyayi bawanda badee bata gani ga yaran tayita hantarar su duk lkcn da tazo basa sakewa,
Kusan sau uku ana kawo kudin aurenta setace ta fasa kuma hajiyar majid ke daure mata gindi acewarta da ayi taki zama gwanda kar ayi tunda tace yanzu tfasa dole akyaleta babanta kuma Na kamar hoto haka yake,
A haka har Lubna tai shekara biyar babu wani chanji duk yadda badee tayi Dan ta shirya d en uwanta da mahaifanta Abu yakiya amma dukda haka batayi kasa a gwiwa ba haka ta shirya taje gidan kasancewar yaran duk suntafi makaranta,
Mukhtar tasamu akofar gidan yafito tunkafin takaraso yafara magana,
Kin tabbatar kinbaro gidan mijin nakine Dan wallahi matsaawar bakin baro gidansa bane karki kara zuwa nemanmu,
Don Allah yaya kasaurareni kutausayamin kodan yaya na bazan iya barinsu ba don….saukar Marin da taji ne ya katse ta,
Tun wuri ki kama kanki kibar kofar gidannan wallahi,
Ko abinda majid ke mata betaba bata mata rai irin haka ba ita da gidan ubanta idan shine bayason ganin ta bazataje gidansa ba amma sbd me ze hanata sasantawa da iyayenta suma da laifinsu kusan shekara nawa basu taba nemanta ba amma daga yau tadau Alukawarin bazata kara nemansuba sedai idan sune suka nemeta,
Tfiya take dakafa harta isa gida sbd yadda zuciyarta kekuna bazata iya magana ba ko sallama batayiba ta shiga gidan wunin ranar akwance tayishi dakyar tasamu ta daidaita kkanta,
Kwata kwata abinda yake damun majid be wuce yadda Lubna ke kin yadda dashi ga besan ya akayiba yakesonta sosae ba tun tana karama sosae yakesn daukarta amma yana zuwa kusa da ita zata kwalla ihu yanzu kuma datake tafiya kowasa take daga tagansa take guduwa ko yadda take ganin yayyenta nayi idan yadawo baba sannu da zuwa ita idan yadawo kokallonsa batayi guduwa ma take,
Ikon Allah kawai take kallo yadda majid ya Dora tsararren gini daga gefe tanamamaki sosae,
Yauma kamar kullum yagama sauke mata jarabarsa take tambayarsa ko en haya zesaka asabon ginin,
Babu ruwanki banason tambayoyi ki zubamin ido kiga yadda zanyi komai sekin sanine,
Shiru tayi batace komaiba,
Shima bangarensa mamaki make shekara biyar bawani mataki bawani ciki amma dai shiyafison haka Dan wani haushi yakeji idan yashigo gidan yagansu gasunan bi da bi,
Tunda ta tashi yau takejin gabanta na faduwa addua kawai take hartadan samu sassauci bayan isha karfe tarada hartadan gota taji shigowar motoci bata kawo komai arantaba tana zaune seji tayi anata rangada guda sekawai ganin mutane tayi a palonta da mace agaba tarufe fuska da mayafi,
Shiru kawai tayi tana saurarensu badan tana fahimtar me suke fada ba,
Wata tsohuwa er kili bibi tace to badee’a ga amarya nan munkawo bawai munbaki amanarta bane sedan mufada miki kikama kanki sannan tafi karfin asiri yadda kikaso kiyiwa majidu manta uwa Allah be yadda ba yakubutar dashi to wannan ma tamiki yawa sedai kiyiwa wasu bakar muna fuka,wata mata dake gefe ta takalleta sheqeqe tace,uhm kuga mace har mace amma se mugun hali ko kula damiji ba a iyaba duk Wanda yasan majid da baze yadda shine yanzu ba ga haihuwar kamar tunkiya keko er soyayyar nan da miji damata ke kwasa bakyayi sbd kincika gida da yaya kamar gidan reno gasunan jeka inbika to yanzu dai ga wacce zata kula dashi nan munkawo se kibi ahankali,
Kukan ma kin zuwa yayi har suka gama cin zarafin su suka fita bata Ankara ba,
Batun majid yashigo bema tasoba yadda taga dare haka taga rana, ita kanta batasan metake tunaniba, washe gari ta shirya yara taturasu islamiya tun karfe takwas tana nan zaune a apalo Sega majid,
Rana ta farko dataji bata kaunar abinda zesa ta kalli fuskar majid batason ganinsa gaba data,
Nace ki hada mana abinkari kinsan amarya ga gajiyar biki ga gajiyar jiya,har yakaraci surutunsa ko kallonsa batayi ba,
Seda yazo saubiyu kafin tasamu bakin magana,
Majid menai maka Dana cancanci wulakanci irin wannan?koda ace mata uku zaka auro baynni yakamata kafadamin bazan taba hanakaba balle nace zan tashi hankalina akanka dan nasani yanzu banida wani gurbi azuciyarka bawai kawai INA zaune azomin da amaryarkaba ko musulunci be lamunci hakaba anya majid zaka iya da haqqina kuwa?zancen nagirka muku breakfast bema taso ba inace bauta tazoyi? Tunda tayi ta jiya dadare aitafara kenan Dan haka seta fito da kanta tayi girkin ninayi nawa tundazu kuma nagaji duk abinda zakayi bazan hanaka ba akwai ranar kin dillanci,
Tabarshi tsaye agurin tunda yake bata taba gayamai magana ba seyau dole yadauki mataki.
Babu yadda zasuyi dole amarya tafito tayi girki a gefanta dakyar ya lallasheta tafito wai ita tagaji,
Badee bata gane wacce amaryaba Seda takwana biyu tafito rakiyar miji badee taganta wato safara’u aka San yadda akayi aka Liqa mai.
Kuyi hakuri da wannan yau dakyar Anty bily tabarni nayi wannan😏
[7/10, 2:02 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine Sha’awa Ibrahim(wai yaushe zaki cigaba mana da safiyyah ne? Wasu harsun manta dashi🤔).
Abin duniya ya ishi badee tarasa inda zata saka kanta majid seda yai sati biyu dakin amarya ko raba musu kwana beyiba tun tana zuwa dakinsa takwnta zaman jiran zuwansa harta dena Dan yatattara yakoma dakin amarya yanzu amaryar tafi wata a gidan amma kokallon gefen ta bayayi sedai ta hango fitarshi shikadai kokuma da amarya babu yadda zatayi sedai tasha kukanta ta koshi,
Yau abdulrahim ya tashi ta ciwon kai ko makaranta bejeba, kaje gun babanku kila ya saurareka danni konaje ba kulani zeyiba, jiki a sanyaye ya yafara tafiya yana tunanin yadda zeyi ko jiya dayaje korosa suka yi wai yashigo da kazaman takalminsa alhali babu komai a palon se wasu kalar kujeru da ba mahadi ma Dana mamansa kuma palon ko shara babu amarya an iya gyaran jiki amma ba a iya gyaran muhalli ba,
Tun kafin ya kwankwasa kofar aka bude babansa yagani cikin shirin zuwa office,
Baba ina kwana?,lpy lau ya akayine? Kudin magani nazo kabani kaina keciwo,waikai yaushe zakuyi lpy kuda uwarku?kullum cikin matsala?Kodai ita ta turoka da gangan baakayi kamada Mara lpy ba,hannunsa yasa yazaro nera goma gashi kasiya paracetamol kasha,karba kawai yayi yana mamakin yadda yabashi nera goma kokunya babu, yakasa tafiya se kallon kudin yake maganar safara tadawo dashi daga tunanin dya tfi,
Strong ya maganar kudin damukayi bakace komai bafa se shirin fitarka kake kuma nafada ma yau ankeso natura mata,irin yadda take maganar kamar zatayi kuka tana kara shigewa jikinsa shikam Dan yaro kallonsu kawai yake,
Sweety kinsan bazan hanaki ba kibari bazan dadeba zandawo sena Ciro daga banki,Na wane kudin ma kikace?
Dubu hamsin dabiyar ne, OK sena dawo maza kikoma daki wannan kyau haka ina kishin yadda bishiyar nan yazo take kallonki, Seda taimasa bye bye sannan tashige ciki baban ma gaba yayi sukabar abdulrahim tsaye agurin,
Koda yaje yakaimata kudin bakin ciki yahanata magana, sekaje kasiya maganin yafi kaita zama daciwon kai gashi kun kusa fara exam (yana jss1),
Shigowarsa gida kenan yasami Lubna tana wasarta tunda ga nesa yatsaya yana kallonta sosae take burgeshi bayason taganshi tagudu Dan baya tuna ranar da suka hada ido ta tsaya kokuma taimasa magana,
Jikawai tayi an dagata sama Seda tatsorata ta kwalla kara,
Lubnatyn baba ninefa yafada yana juyo da Ita,
Cikin hausarta dabata gama fita tace nika sauke ni kaiba babana bane kuma ni sunana Lubna,
Meyasa kikace niba babanki bane? Yadda take ihu seya sauketa yasa shi ajiyeta agabansa,
Kawata ramla kullum ina ganin babanta yakawota da mashin dinsa kuma yazo daukarta amma ni sedai mamana ta rakani da kafa ita tana sona,
Yadda take maganar babu alamun tsoro kokuma shakka atareda ita cikin idonsa take kallonsa tana fadamai abinda ke ranta,yajima tsaye yana kallonta wasanta tacigaba tana jira yazo ze tabata tabballa dagudu sbd tga yadda ko takalmansa su Abdul suka taba yana jibgarsu abdulrahim kadai yake dagawa kafa,
Tana zaune a palo tana goge kayan yaran gasunan dayawa da alama tajima tana gugar,
Kalli tarin tulin kayan yara nan amma duk sun soma kodewa abdulrahim kayan ma sunsoma yimasa kadan bansan yazanyiba ubansu bashida kula kalli yadda yaimasa wulakanci kwanaki maganin nera goma haryaushe yaro zefadama bashida lpy kabashi kudi awulakance? Nidai Allah yataimkeni da yarannan dole nasan….
Matsalarki kenan rashin godiyar Allah duk abinda nake miki keda yayanki bakya gani dankinga nadan sassauta miki ko?,
Azahiri yakona mata rai sosae hakan yasa taso gasa masa magana se wata zuciyar tace ta kyaleshi,
To Allah dai yakawomin me sharemin hawayena kwata kwata banida damuwa safara’u ta kiyaye komai akaina amma ke duk ranar Dana rabeki sekin bata min rai seki zauna dakeda yayanki kukarata kuma daga yau karki kara turamana yaranki suna damunmu dannasan da gayya kikeyi,
Wannan karon idan tayi shiru ya shammace ta shiyasa ta shirya fadamai magana amma kuka yazo mata ga bakin cikin kishiya miji yawulakanta ta agabanta,
Abdul ni inada damuwa sosae nakeda Ita,harkanada bakin budewa kace ina samaka damuwa kasani kalar damuwar danake ciki babu adadinta kuma kaida mahaifiyarka ne sila,
Mahaifiyata tafita abaknki,yaushe zata fita majid kaima se idan kaki gaskiyane Hajiya itace silar komai sonkai yamuku yawa kanku kadai kuka sani bakwa tunanin halin dazan shiga ko yarannan shiyasa kukayi wasa da rayuwata yadda kuke so kun rabani dakowa nayi mamaki dahar yanzu bakin cikin dakukasamin kaida Hajiya….
Tasss taji saukar mari,badee rainin haka yakai tsakanina dake? Zankuwa dauki mummunan mataki akanki wallahi,
Betaba dukantaba seyanzu da yasamu jarababbiya irinsa duk kalar rashin kunyar dayake yiwa hajiyar seyanzu yasan yahana a galaifinta,
Bakin cikin dakuka samin be kasheniba shine harda duka majid?babu komai rayuwa ce kuma Allah yana nan yana kallo danshi ba azzalumin sarki bane akwai ranar kin dillanci ranar da zanyi alfahari da y’ay’ana kuma lokacin nayi maka nisa nisanda gani kusa dakai…..sekuma tai shiru basena karasaba inda rai da lafiya zaka ganewa idonka,
Lubna tashigo tagudunta mama kidaina kuka kema wannan baya sonki ko kamar yadda baya sona nida su yaya abdulrahim ko?dazu Na fada masa ai kuma kice yadaina shigo miki daki tunda baya sonki,
Hawayen idonta tagoge tanajan hannun Lubna,zokiga yadda ake guga domin kikoya ki hutar dani watarana,har lokacin yana tsaye kuma Lubna batabar zancenba sosae tagyara zamanta tace,
Ki kyaleshi mama muma BAMA SONSHI tafada tana kallon cikin idonsa,
Sosae yafirgita dajin kalamanta,wannan kodai aljanu gareta yafada azuciyarshi yalura wannan ba kamar uwarta da yayyenta takeba.
🤔🤔🤔 (akwai matsala kenan),
Kuyi hakuri dajina shiru kwana biyu nima ba ason raina nake hakaba.nagode
[7/12, 10:01 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Wannan shafin nakine maryam Yusuf Ina miki fatan Alkhairi arayuwarki❤
Page 16
Baby nikam wai bazakaje kwana dakin maman Lubna ba? Tunda fa nazo baka taba kwana dakin ta ba,
Zaune ya tashi yana kallonta,bakiga yadda ta Tara yaya ba yaza ayi nakwana dakinta?,
Amma dai kasan babu dadi kar ace nice nahanaka kaje koda yaune kadai ne,
Nifa jarabar nan tata ce bazan iya da itaba kuma dayara zamu kwana adaki?
Ai kanada daki kuje can mana,seda yadan yi shiru kafin yamiqe yana kwasar wayarsa yarufe system dinsa,seda safe yafada fuskarsa a hade,
A zahiri bayason ma kallon fuskar badee amma azuciyarsa yana azabtuwa darashinta besan meyake damunsaba ga wani tsanar yaran maza daya tunkaroshi jiyake kamar yakamasu yaita jibga sekuma tsoron Lubna dayake wani kalar Abu yake hangowa a idonta dabesan komeye ba amma komenene yatabbatar da me girma ne,
Tsaf tayi shirin kwanciya tagyara yaran ta abdulrahim da abdul’azeez sune manya ta bude musu dakin dake cikin palonta daban ta gyara musu dukda bashida wani girma amma baze matsesu ba lkc yayi daza araba musu makwanci,kullum seta saka su sunshare dakin sbd batason kazanta kokadan,
Sauran yaran kanana tayi musu shimfida adakinta bayan takaisu sunyi fitsari,
Ita takwanta da Lubna akan gado suna hiransu Dan Lubna badai surutu ba har bacci yadauke ta tana jikin mamanta,
Ke kisame ni adakina inajiranki,shinen kawai abinda ya iya fada yafice,
Bin bayansa tayi da kallo,wannan mutumen wani show zekara hadawa bari naje naji dame yazo yau,
Daga kofa ta tsaya tace malam gani,kikaraso mana keda za ataimaka kin wani tsaya daga kofa,
Kamar ya?wane irin taimako?,
Dallah malama kikaraso jarrabar bata isheki bane da kika tsaya acan kina iyayi,
Ahankali takaraso cikin dakin,dani dakai waye jarababbe?kai naji ma inada jarabbar amma daga yau nayafe indai ta gefena ne Allah yabani hakuri,
Tnangama fadar haka ta kama hanyar fita daga dakin zuciyarta Na wani irin kuna tayi abinda bata taba yiba Allah ka gafarta min wato ma nizai taimakawa ko ai wallahi yanzu bakina yabude,
Lokacin dayake kallon fuskarta seyaji kamar yaimata mugun bugu seta dauke wuta, amma tana juyawa yaji babu abinda yake muradi kamarta,kardai dagaske matarnan tafiya zatayi be ankaraba yaji ta bude kofar da azama yadamqota yadawo da ita bayaso yaji abinda yakeji idan yakalli fuskarta dasauri ya kaisu gado bayan yakashe wutar dakin duk iya kokarin ta takwace takasa shiyasa tabarwa Allah amma bada son ranta ba,
Kuka take harda sheshsheka rabonta dajin haka tun haduwarsu ta biyu wannan mugunta yai mata kuma se Allah yasaka mata tundai ai daga baya tahakura bata hanashiba shine ze mata wannan aikin,
Malama seki samu damar tashi kike wani kukan munafurci kamar wata amarya nikitashi kifice tun bankasa jurar kukan nan naki ba na doddokeki anan gurin,
Zaninta tadaura tasa hijab dinta kafin tamiqe tsaye dole ta jure wannan zafin tasani baze jimaba ze tafi haihuwa bakwai aiba wasa bane zafin mutuwa kadai yarage taji,
Allah sarki nida nakeda danda yabawa shekara goma baya ni ake duka yanzu kuma akan gaskiyata nake ko abdulrahim yawuce duka akan wasu kanannan laifuka balle nida nahaifeshi Amma zankara fada maka Allah yana gani kuma namiqa dukkan lamurana da damuwata agareshi zeyimin magani kuma seya sakamin nida yayana,
Bata jira jin mezece ba tafita,
Kallonta yake tafiyarta ta chanja dagangan yaimata haka sbd tabarshi shiyake kidansa shiyake rawar sa kokadan beji tausayinta ba amma fa he’s more than satisfied badeee capital A ce, lol
Ruwan zafi sosae tayyi wanka dasu kafin yakai yaranta masu fitsari sukayi tagyara musu kwanciya,
Kusan makara sukayi yaran ko wanka basu samuba suka tafi makaranta,
Abangaren safara’u kuwa wani dadi taji domin tasamu yin abinda malam yace ba ita take zuwa mahaifiyarta ke zuwa seta karbo mata mugun abu ,
Wannan karon yace kasan gadonta gefen damijin ke kwanciya anan zata yi rami ta binne laya,
Haka kuwa tayi ta daga katifa tayi yanda yace,murna take seyanda tayi dashi kafin taje kan yayansa,
Dayamma suna zazzauna ita dayaranta tana yiwa Lubna homework se ga Abdul ya shigo bayan safara’u tagama zugo shi,
Baby Dan Allah ka karbomin Lubna mana nasan kanada iko akanta kadaici yamin yawa yadda nakesonka haka nakeson yayanka sedai su ko gaiaheni basayi,
Cikeda kissa take magaanr tana gwadawa ne taga aikinta yayi,
En matan baby kwantar da hankalinki koyanzu kikeson Lubna tadawo gunki zata dawo barikiga ina Zuwa,
Malama hadomin kayan Lubna zata zauna hannun safara’u zaman kadaici yai mata yawa,
Tasani sarai Lubna bazata taba yadda ba setace,gatanan mana idan tayarda nimeye nawa aciki ammafa seka tambayeta idan bataso bazaka takurata ba,
Sosae yaji haushi, ai umurni ne Dan haka baseda yaddar taba,
Lubana najin haka takoma jikin uwarta, mama kice yakyaleni nafison muringa kwana dake bazan bi waccenba tayi nuni da kofar dakin safara’u,
Tana kuka yana janta tana tirjewa dayaga tacika taurinkai seya fara dukanta kamar wata babba ita kanta ta tsorata dole tahakura tabishi itadai maman kallonsa kawai take,
Tananan zaune segashi yashigo yana huci kamar wani zaki,
Zaki hadomin kaynne kokema se kinji bugu,kinmaida yarinya bata jin magana har ubanta yace tayi Abu takiyi wallahi .zakija Na illatata,
Shiru yai ganin tamikomai jakar kayan yakarba yawuce azuciyarta tace lallai maza azzalumai ne betaba sanin shi ubnta bane seyau, nasan dole zata dawo indai Lubna ce,
To ensamari kuzo kubiya karatu kuka tsaya cirko cirko kuna kallona,
Abangaren safara’u kuwa tsalle take tana murna lallai abin indai hakane cikin kankanin lkc zata tarwatsa gidan dama ta tsani lubnar nan me ido kamar an soya wake,
Lubna kuwa akasan tile daya jefar da ita anan ta gama kukanta bacci ya sureta sukayi gabas😂
Kuyi hakuri u know fiyya is always lazy🙈
[7/13, 4:33 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
This page goes to all the active members of taskar billy galadanchi #one love❤ you made my day😂😂.
Page 17
Ni yarinyar nan bansan halin wa tayo ba shegen taurin kai , haryanzu fadan be gadi karewa ba kenan,
Koda yayi taurinkai bekamata ka doketa irin haka ba kasan raba da da uwa se Allah baby,
Kekikasan wannan ko uwarsu taimin irin haka ba Abu bane me wahala aguna nai mata duka ba,
Naji dai nikam banason duka kalli yadda kasamin yarinya bacci akasan tile haka aise sanyi yakamata,daukar Lubna tayi takaita dakinta har kan gado,
Lubna anji jiki har lkcn kwanciyar su bata farka ba,dayan dakin safara’u takaita Dan bazasu kwana daki daya ba sedai tabar kofa bude koda ta tashi,
Ina Lubna ne?yatambaya lkcn dayake shirin kwanciya,
Tana can dakin amma nabar kofa abude koda ta tashi kasan babukyau kwana da yaro daki daya,
Bece komaiba ya kwanta,
Cikin dare Lubna ta tashi tana kuka tayi kofar Palo kuka take tana dukan kofar,
Mama zoki tafi dani dakin ki banason nan bazan kwana ba mama kizo kidaukeni karya kuma dukana,
Tsawa ya daka mata,ke maza kikoma kikwanta kona kara zaneki wallahi,
Nace maka nafiso nakwana wurin mamana banason nan dakin,sena kuma dukannaki kenan,bata kaunar ataba lpyr jikinta shiyasa tafara tafiya ahankali suna biye da ita takwanta kan gado tana kuka ahankali,safara’u ke shafa bayanta don munafurci hartakoma yin bacci,
Da asuba safara’u taiwa dakin tsinke bayan sun gama sallah,tasamu Lubna akwance idonta arufe ruwa ta debo ta daga Lubna ta zuba kafin tamayar da ita yadda take,
Baby wai dama yarinyar can tana fitsarin kwance ne?,ban taba jin dakin dakin mamanta yana warin fitsari ba gsky batama yi inndai tayi yau iskanci ne kawai kuma sena zaneta,
Sedai kar akuma kam kuma meyawa tayi banmasan yazanyi ba amma duka bashine magani bari natasheta naimata wanka,
Yana tafe tana bin bayansa nidai karka daketa baby banason duka,
Aidole tgane kurenta da gangan tayishi sbd kokadan mamanta bata shiri da fitsarin kwance,
Lubna tana kwance sejin duka tayi afirgice ta tashi tana kuka,wayyo Allah Na menayi ?nibanyi komaiba ake dukana?,mamaki yakama shi yadda kokadan bakinta baya mutuwa,
Dan iskanci shine zakiyi fitsari akwance air bakya yiwa uwarki zaki gane indai haka zakyi muzuba nidake,
Seda yaimata duka da sleepers yakyaleta acikin kukan yaji tanamagana tana kallon safara’u dake gefe tana murmushin jin dadi,
Ai malaminmu a islamiyya yace zalunci babu kyau Wanda yayi kuma se Allah yasa shi cikin wutar jihannama yakonashi,😭
Jan hannun safara’u kawai yayi suka fita daga dakin,
Anan taci Ku kanta ta koshi hartagaji tayi shiru tana tunanin mamanta,
Abangaren badee kuwa dakyar tai bacci lkcn datakejin kukan Lubna kuwa itama seda tayi kukan Tace ,Ya Allah kana ganin abinda bayinka suke mana ya Allah kataimake mu😭,
Lubna tashi ayiwanka lkc atafiya karki letti a a makaranta,
Batareda tayi magana ba ta miqe,bayan tayimata wankan tashiryata cikin uniform tabata tea kadan tasha tace takoshi,
En matan baby naje naga mamana🙄tafada tan kallon safara’u,
Cike da mamaki takalleta kafin tagyara mata ba Anty zaki kirani ba en matan baby ba kinajina kokuma nasa babanki yazaneki,
Ai haka naji ya kiraki dazu,kiyi shiru kije gun mamanki tabaki lunch box Dinki nibanzan iya girki yanzuba kice tasaka miki abincin data girka,
dagudun ta tafita,
Tana zaune seji tai anrungumeta sosae murmushin jin dadi tayi dantasan lubnarta ce,
Mama shine jiya bakizo kin kwaceniba yaudasafe matarnan tasaya zaneni wai nayi fitsari akwance kumafa itace tazuba ruwa agurin,
Kiyi hakuri muje narakaki makaranta,uhm tace kiban abincin dazanje dashi ita bazata iya girkiba wai,ai yananan nahadamiki,
Cike dafarinciki ta rakata ta dawo,
Bayan tadawo daga makaranta ta hadu da babanta a harabar gidan sauri sauri take tafiya Dan bataso ma yai mata magana kuma yau bazata kwana gun wannan antyn ba,
Lubna ta,yfda yana tahowa kusa da ita yakarbi lunchbox dinta yanabudewa Ita dai batayi magana ba,
Iyye Lubna er gayu yau da Irish akaje makaranta lallai sabuwar mamanki naji dake,
Mamana ce tabani ba wannan antynba,nikam bani abina nakara sa cinyewa,
Gani kawai tayi yawuce fuuu bayan yamiqa mata lunchbox dinta,
A tsakar gida yasameta tana wanke wake yau alala take Sha’awa ,kaudin meye naki nabawa Lubna abincin zuwa makaranta iye kobakya jina,ita taturota wai nabata abincin,karya ne bakar munafuka nakara ganin kinmin irin wannan kaudin kiga,
Wai majid yaushe lubnar tazama yarka inace duk kabarni da lalurar su tomeye naka natada jijiyoyin wuya kana nufin zaka fara nunamin iko akan ya….
Marin dayai matane yasa t yinshiru,
Lubna takaraso kusa dasu tace, mama mubar gidannan tunda dukanmu yake mukoma gidan babanki dakike bani labari,
Bata amsata ba tashige dakinta tana kuka me ban tausayi harseda taji kanta ta yafara ciwo kafin tahakura,
Nayi danasanin rashin binka babana gashinan kungujeni dalilin haka rayuwata tana cikin tsaka mewuya nadauki soyayyar miji data yaya gashi tana wahalar dani banida mafaka dole senan gidan majid idan nafita bansan inda zan dosaba waxe karbeni da yaya haka kuma bazan iyabarinsu ba rayuwarasu ta lalace, Allah ka kara bani hakuri da juriya Ameen Lubna dake gefenta tashare mata hawayen fadar ameen dukda bata fahimci komaiba.
Feeyah tayi kokari yau💃🏻💃🏻💃🏻
Wai wannan wane irin iskanci ne Lubna kitson ma kice bakiso?haka za abarki dakai kamar mahaukaciya?,
Ni bance banason kitso ba Na mamana nakeso wannan bata iyaba kuma da zafi,tafada tana kara sautin kukan Ta,
Wane irin zafi zaki zauna ne kosena jibgeki yadda muka saba?,nikam banaso zanje gun mamana tayimin nata babu zafi,
Haushi ya kamashi yasa takalmi yaimata duka safara’u ta matseta cikeda mugunta ta taimata kitson kuma batama iyaba (kunsan kitson Dan koyo yafi komai zafi haka maman nu’aym taimin lkcn datakeso ta iya kitso ina gudu tana kamoni sun rankwashi ba abinda banshaba😂),
Badee Na zaune korido tana jiyo kukan Lubna babu yadda zatayi mamaki take yadda tanaji tana gani ana so arabata da yarta,
Uban waye yashafamin maiko ajikin fenti? Ko kallonsa batayi ba yadda yazo yana mata ihu akai,wai bakwa jinane? Nace uban waye acikin Ku yashafamin maiko ajikin fenti?,
Miqewa tai tafita daga cikin yaran takoma gefe,wani mugun kallo daya bita dashi tai kamar batasan me yakeba,
Ke kuma meye nakomawa gefe?,cikeda rashin kula tace, naji kace ubanwaye shiyasa nadawo gefe kazagesu su kadai Dan ni bazaka zagi ubana ba,
Sosae yaji haushi shiyasa Yakoma kan yaran kafin yadawo kanta,
Bazaku fadaba kuka zubomin ido kamar Na uwarku? Shiru yaran sukayi dama gasu ba magana sukeyiba,haushi yaturnuqeshi,
Takan abdulrahim yafara yaimasa duka sosae kafin yajanyo abduljabbar badai sokuke Ku lalatamin fentiba kunkwaso mungun halin uwarku ko? Itadai tana tsaye tana kallon ikon Allah yana zuwa kan abdulazeez yaruga ya kankame uwarsa,mama kibashi hakuri bani bane karya dake ni don Allah,
Tayi mamaki sosae ganin yadda majid yayo kansa ze dake shi,
Dakata malam badai dukansa za kayi ba yazo jikin uwarsa? Toko mutuwa na kunyar idon mahaifi Dan haka bazaka dake shi agabana ba seka kara gaba idan ka hadu dashi awaje koyankashi zakayi gaka gashi,
Ke har kinada bakin magana matar databar iyayenta tabi namiji mezata yi taburge mijin kuma mace kamar akuya se haihuwa aure ko shekara Tara beyiba haihuwa bakwai Dan ma Allah yataimake ni daya ya rasu,
Sosae zancensa yataba kahon zuciyar ta amma tadake tagano majid danyaga tana masa shiru ne,majid bansan ka zama Dan dauduba seyau seka bari waccen uwar daka tafadi wannan bakaiba,kuma zancen haihuwa dakake fada da nice kai tun dakaga ina kwasar cikin seka daina raba ta kaga basena kwashi cikin ba,jabir kuma ina rokon Allah yasa me cetona ne tunba yauba nasan bakayi bakin cikin mutuwarsa babu abinda yake bata min rai irin nabude idona naganka agabana waikaine uban yayana,
Batajira yabata amsaba tai shigewarta daki jitake inama tanada wurin zuwa daba abinda ze hanata barin gidan majid,
Bangaren Lubna kuwa taci kuka harta gode Allah,
Tana zaune agefe tana kallon safara’u dake kallo tace,
Anty don Allah ki bude min kofa naje inyi wasa,
Wasar uwarki?kice wurin iyayi da Gulma zaki tunda anriga ankoya miki shegen iyayi kamar ba er shekara biyar ba,
Mamana tace Gulma bakyau kuma bata koyamin ba Dan Wanda yake Gulma dashida me zalunci duk wuta za a saka su kuma wutar Allah zafi gareta,
Cike da yarinta take maganar kuma iya gaskiyarta take fada,
Dallah daga can babu inda zaki dauko tsintsiya kisharemin palonnan tun shekaranjiya kikejin kasa da datti idan kintaka amma dayake kinyo gadon kazanta bakisan koda wasa kice zaki share ba,
Mamana tace zata koyamin shara amma sena kara girma idan nakai girman abdulkadir,
To ni bazan jiraba maza jekidauko tsintsiya tunban jibgekiba wallahi,
Ganin dagaske take yasata shiga kitchen tadauko,kwata kwata batasan me takeyiba idanma taga abin wasa seta ajiye sharar se taji safara’u ta yimata tsawa kafin tacigaba,
Anty nagama inje inyi wasan?tafada tana leqen fuskar safara’u,
Kitchen zamu shiga har girki zaki koya,tafada tana jan hannun ta suka shiga kitchen,
Anty mamana tace zata koyamin girki amma sena kara girma don Allah kibarni inga mamana,takarasa maganar tana kuka,
Babu inda zaki,tunkafin tarufe bakin ta Lubna tafara ihun kuka tayi juyin duniya taki yin shiru, karshe dai ta kyaleta tace zamu hadu dake,
Washe gari Lubna tana bacci dukan da majid ya sabayi mata yatasheta ga baccin yamata dadi Dan kwana tai kuka ita se wurin mamanta zata kwana,
A firgice tamiqe zaune tafara kuka,indai bazaki daina mana fitsari akwance ba wallahi na dinga jibgarki kenan,
Dagudu tafito daga dakin taci Sa’a kofar abude se part din mamanta ta sameta tana shara kafin ta ankara majid ya damqota yahau dukanta tun tana iya kuka har ta kasa itadai badee se kallon ikon Allah take yadda yahaukace yana dukan Lubna kamar yasamu wata babba koda ace babba ce mace bata cancanci irin wannan dukan ba balle Lubna dabatasan komai ba,
Ganin daya yi tazube akasa ko numfashi batayi yasa yadaina dukanta yafara Dane tabarmar kunya da hauka,
Zoki kama yarki gatanan tasuma kinkoya mata munafurci komai setace ke tahanamu bacci ta hanamu hutawa wallahi wata rana sena illata ta kuma tana farfadowa kidawo da ita gun safara’u,
Idonta dasuka chanja kala ta dago tana kallonsa dasu,
Wallahi majid indai kaga Lubna takoma gun waccen algungumar matar taka to bana doron duniya kadaina wannan tunanin kuma kacigaba dadukansu haka ranar daka kashe daya sekayi sunan ka kashe danka na tabbata zakayi bugun gaba dahakan,
Harta juya zata shiga daki bayan ta dauki Lubna tajuyo,
Kacewa safara’u ta hado min kayan diyata Dan bazan bari takoma ba.
Don Allah kuyi hakuri darashin jina kwana biyu nima badason raina hakan yafaruba,ina fata zakuyimin uzuri?🤗😍❤
[7/17, 8:23 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakune matan gidan homel&SophieG novel group nagode Allah yabar kauna ameen.
Page 19
Tsaya wa yai agurin kamar andasa shi Zuciyarsa namasa zafi jiya ke kamar yaje yaita dukanta seta daina numfashi,wato shi zata gayawa magana irin haka?Ashe garada datake kyaleshi akan yanzu datake maida masa da magana?lallai dole yasan yadda zeyi da ita inbahakaba renin zewuce wuri idan takama ko korarta ne yai itada yayanta dole yayi sbd yanzu babu abinda ya tsana irin ganin su,gajiya yai da tsayuwa yawuce yana hura hanci,(daga baya kenan),
Dakyar tasamo kan Lubna ta farfado tun lkcn kuma take kuka tana rarrashinta har tagaji tadaina ta zubawa sarautar Allah ido,
Nidai kaje kadawo da Lubna ta,tafada tana tunzuro baki,ki kyalesu nifa koson ganin yarinyar banayi wallahi wani Abu nakeji inasonta sosae azuciyata amma banaso naganta kodan tanada taurin kaine,
Bakaramin dadi tajiba Dan dama haka takeso,shikenan tunda uwarta tanunamin ita tahaifeta,
Kiyi hakuri kinji en matan baby,zomu kwanta kardamuwa tahnaki bacci,
Washe gari Sunday bayan fitan majid yatafi kasuwa safara’u tafito Neman fada, badee nawanke uniform din yaran bayan sun tafi islamiya Lubna CE kadai a gdn ganin har yanzu tana wasu en firgice firgice yasa bata turata islamiyan ba,
Sannu bakar munafuka to kin karbo yarki sae me?,
Nakarbo yata sekuma shikenan babu yadda za ayi Dan bakukukamin naqudarta ba dazan zauna inakallo ana jibgarta kamar jaka sekijira idan kinhaifi naki kibashi yadaka yadda yakeso badai nawaba,
Angaya miki kowa irinki ne?kamar wata dabba kikesta sako yaya,Toni ba jahila bace senagama gurje amarcina koda zan haihu balle ni wannan baya cikin tsarin rayuwata, haihuwa bakwai ashekarun dabasukai gomaba gida yakoma kamar gidan Reno,
Babu jahili dayawuce Wanda yake tsarawa kansa abinda ba Allah ne yatsara masa ba kuma haihuwa baiwace ki jira ranar dazakiso ganin yayanki amma lkcn yakure miki Niba shashasha bce inada aikin yi idan kin gama surutunki sekin kara gaba,
Allah yawadaran naka ya lalace ni ina zaune da iyayena lpy Nafi wacce tazabi tabi namiji akan iyayenta kuma Na mijin ma batada daraja a idonsa amma dai wallahi anji kunya,takarashe maganar tana karkade kugu,
Kekika damu da wani miji ninan zaman yayana nake bazan yadda nabarwa ballagaza irinki suba Dan bazafin haihuwa kika saniba kuma banso kikoya musu muguwar tarbiyar da tsohuwarki takoya miki tunda har tsohonki bata bariba yanaji yana gani ana abinda ba daidaiba amma be iya magana nikuwa iyayena zaunensu suke qlw,
Sallamar majid suka jiyo yadawo kila koyai mantuwa ne,
Take safara’u tafara birgima,wayyo ni Allah Na shiga uku na lalace,
Aidasauri yazo yarungumeta yana jin Ku kanta har zuciyarsa,
Lollipop dina ya akayi ne?,
Matarka kemin gorin haihuwa kuma harda marina tayi kilama kunnena yadaina ji,
Babu wani bincike yahau dukan badee,ai gara ita akanki inaga sena illataki zaki gane kuskurenki abin naki yawuceni haryakai kan baby na to wallahi kindebo da yawa,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Abdul dukan babbar mace Ashe lalacin naka yakai haka kuma agaban yarta?
Hajiyarsa ce tazo dubasu sbd majid yafi karfin wata beleqa gidan ta ba,
Shiru yayi yana kallonta azahiri ya tsorata daganinta amma akan enmatan baby babu abinda baze iyayi ba,
Kalleni dakyau munafuki sekazo muzauna naji dalilinka nadukan matar ka sannan katanadai hujjoji kwarara dazaka fadamin narashin zuwa kaduba lpyta na stawon wannan lokacin,
Haryabi baynta seyaji muryar safara’u tace,
Baby kazo kamin tausa kuma kasan kace idan kadawo zamuyi magana fa,ta fada cikeda shagwaba tana rausayar dakai kamar karamar yarinya,ai kawai sebinbayanta yayi yama manta da kiran uwarsa,
Bema damu da Kiran datake masa ba yacigaba datafiyarsa,
Hajiya da abinya girgizata kawai tashige part din badee itama tabi bayanta dalubna ahannunta taana goge hawayenta,
Tana kuka ta labartawa Hajiya komai damarsu daya baya hanasu abinci sedai ba isashshe ba,
Yanzu badee kina wannan halin baki taba fadamin ba?Hajiya naga yai nisane bayajin kira,
Aiseki fadamin yanzu wayake biyan kudin makarantarsu?abdulrahim kadai yake biyawa shima yacireshi daga makarantar kudi sauran ninake kukutawa,
Sosae tajinjina al’amarin tabawa badee hakuri tace gobe zata dawo dantasan ba abar majid hakaba amma dalaifinsa,
Dasauri Lubna tace,Hajiya inaganin wani bakin Abu mekamada mage a dakin Anty safara’u akasan gadonta,
Take gaban badee yafadi sbd sosae take tsoron al’amarin Lubna yanzu.
🤗🤗🤗🤗
[7/18, 10:32 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
*ban taba tunanin rubutu ze zama sanadiyar hadu wata da masu kaunata ba burina be wuce na Isar dasaqon danake son isarwa ba kuma ya amfanar,
*Bawannan ne Na farko dana farajin hakaba amma wannan karon senaji ni daban kamar ba safiyya ba,natsinci kaina cikin tsananin nishadi dajindadi,
*wani lokacin kusancinka damutun bashine zesa kushaku ba,
*A rayuwa sewanda baka taba saniba kuma baka taba ganiba seyai maka rana irin wacce baka zato,
*base mutun yafada maka yana kaunarka ba azaman tare kaida kanka zaka fahimci hakan,akace kukan kurciya gamai hankali bayanine,
*ina rokon Allah yabar kaunar dake tsakaninmu Fatima(baby nurse)Allah yasa munada rabon ganin juna Ameen,
Kiyarda dani wani lokacin senayi kamar nahaukace idan natuna yadda kike min banaso nadaina tuna wasu abubuwan sosae nakejin dadi😍,
Daga karshedai wannan shafin nakine ke kadai fatima (baby nurse).
Page 20
Lubna na hanaki irin wannan surutun kosokike muyi fada?,
A’a banaso muyi fada,fada babu kyau kamar yadda kuke da babyn Anty safara’u har yana dukan ki,yarinta afili take maganar,
Badee ta runtse idonta batason yarinyar nan tacika surutu irin haka gashi tagano Sam Lubna batayo halin ta ba batasan taboye abinda keranta ba kuma bata shakkar fada ko agaban waye, sanin idan takara kwabarta wata kwabar zata kumayi yasa taimata shiru,
Hajiya ma kallon lubanr take aranta tace,majid yayi gudun haihuwa gashi be tsallaketaba,be tsallake zuwan Lubna dunaniyaba kuma be tsallake tonuwar asirinsa ba,idan batayi tantamaba yarinyar nan bazata rasa mutanen boyeba,ta tuna lokacin da margayi megidanta yake bata labari tun bayan aurensu lokackn bata jima datarewa ba,duk inda mugun Abu yake mugayen iskokai ne,wani mugun sammu ne,ko kuma maye hankalinsa baya taba kwanciya da wurin, takuma tabbatar dahakan saboda abubuwan dasukayita faruwa kafin rasuwarsa,
Badee bari natafi segoben idansu Abdul sun dawo kigaishemin dasu(daga baya kenan),
Tou Allah yakaimu Hajiya Allah yakara girma, ta amsa da ameen,
Lubna gashi asiyamiki bobon zuwa makaranta,
Tana murna taakrbi kudin harda godiya,badee kam mamaki ne yakamata ganin yadda Hajiya keson jansu ajiki yanzu kometake nufi da hakan?Allah masani sedai yayi kokarin kawarda mamakinta har gate taraka hajiyar taleqa titi abinda tajima batayi ba taga mutane dadama suna harkokinsu ajiyar zuciya tasauke kafin tace kowa da bukin zuciyarsa Allah kaimana sassauci,ameen inji Lubna dake biye da ita,
Hajiya kam kwana tayi tunani Sam bata zaton er uwarta tayi mata haka sedai idan safara’u ce me mugun hali idan hakaneko zatakai karar safara’u gun mahaifiyarta domin ataka mata birki sbd bazata yadda tanaji tana gani arabata da danta ba,wani gefe na zuciyarta kuma mamakin kalar hakurin da badee take,arayuwarta bata tunanin akwai mace irin badee haka kamar ma uwarta ta gado sbd itama batada magana sosae ba kuma haka kawai ake gano damuwarta ba,
Allah sarki badi’a kusan shekaru fiye dagoma kina kwasar takaaici nakasa gano kina son dana tsakani da Allah ammani dafarko baniyyata na tagayyara rayuwarkiba,
Toshi wancan shashasahn batasan ma ta Ina zata soma da lamarinsaba,
Asubar fari ta shirya tayiwa gidan majid tsinke,
Sauri Sauri yake tafiya kamar wanda aka aiko masa uwarsa batada lpy,
Kai Abdulmajid INA zaka?,
Hajiya wani guri nayi yanzu zan dawo,
Kazo nima sauri nake kware zaniyau idan mungama magana seka tafi koda birnin sin ne,
Wayyo Hajiya kijirani safara’u ce ta aikeni tace inyi sauri, yafada yana kara speed,
Lahaula walaquwati illah billah tafada tana tafa hannayenta,majid haka aka shanyeka?mace kakewa wannan azarbabin?nashiga uku ni jikar mallam🤔,(uhm kya gama sallallaminki kikarasa ciki majid ai bashida duwawun zama tunda en Matan baby ta aikeshi),
Hakuri sosae tabawa badee kamar ba hajiyar da badee tasaniba har seda badee tace,don Allah Hajiya kidaina bani wannan hakurin kuma aike uwace sedai muyi fatan Allah yasa mugama da iyayenmu lpy,
Ameen ta amsa,badi’a ya maganar iyayenki kuma,
Ai Hajiya kidaina batunsu idan har suna sona zasu nemeni nayita zuwa basu hakuri basu saurareniba Dan haka nabarwa Allah komai inajira ne yayi ikonsa,
Sosae Hajiya taji tausayin badee taquduri niyyar taimaka mata da yayannnan nata datake bugun gaba dasu kuma tana fatan suzama ABIN ALFAHARINTA,
Abinda hajiyar zata iya nataimako tayi ciki harda yiwa mazan dinkin sallah dake tafe sekuma harkar karatunsu insha Allah zata taimaka Dan itama bawani abin kirki garetaba sbd mugun maqo irin na majid,
Tafito rakiyarta hajiyar tace bari naje dakin waccen isashshiyar nagaisheta tunda ni bazatazo tagaisheniba,
Nikam wai yakumbo meye haka?safara’u tafada dayake haka suke kiranta Dan haka taji en gidansu nakiranta,
Ai dole zaki tambayeni kuma kisani kin bani kunya Wallahi,
A’a toni menai miki tunda sanyin safiyarnan zaki bugamin kofa inabacci kintasheni kuma ki tsiramin masifa,kujimin fitinanniyar tsohuwa,
Tabdi jam ni Hajiya rabi diyar muhammadu jikar maryama da mallan,
Wai menene haka aketa hayaniya en matan baby,majid ya tambaya yana leqo kansa ta kasan hannun safara’u,
Hajiyace kemin fada babu gaira babu dalili,tafada tana hararan badee da hajiyar,
Ko uwarki baztamin haaka ba kuma yanzu can nayi naji ko ita tasaki kiyi min haka karamar Mara kunya kawai,
Aiko safara’u tasa kuka Yakoma ciki tana diddira kafafuwanta daqasa,
Hajiya meye haka kinga kimsaka min ita kuka ko yanzu dakyar zansamu kanta,kekuma munafuka kike kallona ko?zamu had…
Kafin yakarasa yaji safara’u na kara sautin kukan ta air arikice yabibayanta yaran rufo kofar,
Hajiya kam baki ya mutu se kawai taakama hanyar fita,bata wani jimaba ta is a kware,
Yo ke yakumbo aikinsan kahaifi da ne baka haifi halinsaba sedai muyi ta hakuri da addua,
Maman safara’u tafada bayan tagama sauraren korafin Hajiya,(korafi bekarbu ba hajiya😜)
Hajiya taji haushi ganin er uwarta bata basa zancen muhimmanciba hakan yasata baro garin babu shiri,
Bari mu leqa bangaren yaya asama’u,
A palonta takee zaune ta tasa hoton Lubna agaba tana kallo zuwa yanzu tanaso taji halinda er uwarta take ciki amma shiru ba labari,mamansu har kuka tayi wa asama’u kan tashawo kan mukhtar badee tadawo gida amma abin yafaskara baban suko shima yanaso yaji halinda take ciki amma besan yazeyiba seyanzu yagano yayi katobara daya yarda yahakura lkcn datazo nakarshe segashi yanzu ko labarinta yadaina ji,
Mijin yaya asama’u ma yayi fushi d ita akan maganar badee danyaita binta suhakura tamai kafiya yanzu tayi lallashin duniya yake gun mukhtar yaki harta tadaina masa zancen sedai taita kallon hoton Lubna datakai akacira daga wayarta akayomata na kati akayo enlarging dinsa takafa a palonta.
Safara’u kinji wai yakumbo tazomin nan dashirme,
Maman safara’u ke maganan awaya,
Mama kyaleta ni sonake har ita agamamin da ita kawai Dan naga tanaso takawowa shirin mu cikas,
Murmushi naga tayi tana sauke wayar daga kunnenta.
Luv u oll❤
[7/20, 8:45 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
happy birthday Anty billy Allah yakaro shekaru masu albarka ameen.
Masu Neman yayana daga farko suna biyoni private suyi hakuri don Allah idan sunji shiru u know I’m lazy wahalar marking nakeji🙈.
Page 21
A’a mama ni banason asakashi yahanasu abinci sonake asakashi yadasa musu bakin cikinda suna kallon abincin ma amma cinsa yagagaresu daga uwarta sa har badee da yayanta sonake rayuwarsu ta tagayyara harsesun gudu da kafafunsu kinga idan anyi haka semufara da uban gayyar,
Safara’u ke waya da mahaifiyarta,
Toke safara’u bakyaganin abin zedau lokaci?
Babu wani daukar lokaci ai ance idan masara taji wuta ita dakanta zata fada,
Nida sonayi ko muce yasako musu ciwo nadan wani lokaci harse ransu yabar jikin su wallahi jinake kamar sumutu yanzu wannan uwar dukiyar tadawo hannun mu,
A’a baza ayi hakaba aise ayi saurin ganomu,idan wuya tai wuya tsaf zaki nemesu kirasa,yadda kikeji haka nakeji wallahi Dan majid din maqon masifa ne dashi koyanzu senayi dagaske nake samun wani Abu hannun sa Wanda na aiko miki satowa nayi yatambata nace kila ya zubar ne yaita mita, yanzu dai kije kicemasa akara sako masa tsanarsu har uwar yaji bayason ganinta,
To shikenan sekin jini,
Dahaka sukai sallama nikaina seda na tsorata (anya wai badee bazata mutu ba🤔abin yaimata yawa),
BAYAN WASU SHEKARU
Tundaga Wannan lokacin babu abinda Abdulmajid yasawa gaba irin Neman kudi, yatara dukiyar da shikansa besan adadin taba,
Yayansa,uwarsa da matar sa badee bemasan da zaman suba sesuyi satidaya basu ganshi ba,
Abincin dasuke ci yadamqawa safara’u se abinda taga dama take basu ,
Uwarsa tayi yawo harta gaji dole tahakura addua kawai take masa yanzu sosae take wahala,
Duka kuma sedai idan majid be hadu da daya daga cikin yaran ba har abdulrahim daya zama saurayi yanzu bewuce duka awurinsaba yo ko uwarsa ta tunzurashi se yaimata duka,
Lubna ce kadai matsalarsu yanzu,tazama budurwa wani kalar kyau ne da ita har tafi wacce tayo kyau,bata tsoron sa shida matar sa kokadan indai tana kusa bawan da ya isa yataba uwarta yanzu zaunenta take gida batada matsala dan tagama secondary skul tace kozataci gaba bayanzu se islamiya datake zuwa,kuma tana koyon dinki awurin wata makociyarsu amma da Dan tafiya tsakaninnan,
Yauma kamar kullum tafito zataje gidan datake koyon Dinki ta iso kusada wata qatuwar bishiya abinda takeji yafara tasomata wani kalar tashi gashin jikinta yake kullum tana so takarasa Dan tasan bakaramin abubane wannan koma menene amma setaji abin yana kara yawa,
Afili tace nakusa fara avoiding hanyar nan,
Lokacin da ta dawo tasamu safara’u na surfawa badee rashin mutunci ita kuma tatsaya kallonta kamar hoto,
Wai mama meyasa kike kyale matarnan tana surfa miki ruwan rashin mutunci kina kallon wallahi ki jibgeta seta fita hayyacinta,
Lubna kinsan na hanaki irin wannan ko idan baki dainaba nizan jibgeki bakyajin manya na magana sekin sako bakinki,
Kiyi hakuri mama manyan naga girma ya Riga hankalinsu zuwa,kuma wallahi dabadan duk abinda kayi se anmaka ba babu abinda ze hanani gurzar bakin wata yau,
Shiru badee tayi Dan tasan yanzu idan ta takurata da fada zata hau bori tajiwa kanta ciwo,shine abinda yake damun Lubna idan ranta yabaci shikenan seta fara nose bleeding daga an tabata seta ringa buga kanta duk inda tasamu se anmata ruqiyya kuma dakyar take dawowa daidai,
Safara’u ta buga tsaki, mayun banza ke bakida daraja awurin miji kuma kinkafe kinki tafiya shekara da shekaru kokwana dakin ki bayayi amma kin nace saboda kwadayin abin duniya kinga babu cigaba kinki tafiya ko ina kikai jarrabar ki oho, kodayake ma inkin tafi babu gidan zuwa iyaye sun yafeki sbd anzabi abin duniya akansu shiyasa aka cika gida da yaya sedai Haryanzu babu alamun fidda uwa balle akaiga riba mtswwwwww(ai dasauri najanye fuskar badee nace wannn tsinin baki haka duk wurin tsaki ne karki tsokanewa baby badee ido😂),
Safara’u kenan Aiduk Wanda yayi zagi akasuwa yasan da Wanda yake, tana gama fadar haka tashige daki Dan jin ana kiran sallahr magrib,
Lubna dake tsaye tace, maye dai yasan inda yake kuma kema daknki nan gaba zaki tantance maye acikin mu,kuma wallahi kurwan mu our sedai shi zakiyi wa megidan mu munriqe Allah dankinsani wallahi har hanjinki inagani sedai ina jiran naga ranar da reshe ze juye da mujiyane kuma kaikayi zekoman kan masheqiya, itama binbayan mamanta tayi,
Cike da takaici takoma gefenta lallai yakamata tadau mataki akan Lubna, amma tayaya?ga Hajiya ma itake rage musu wani zafin shiyasa sukeyin kamar basuda damuwa gashi tafara ganin alamun nasara arayuwa Dan abdulrahim da abduljabbar suna kusada kammala degree dinsu ga Abdul’aziz ma yana 100level,abdulqadir da lubna kadaine basu samu admission ba, kuma duka mazan ba azaune sukeba kowannensu yanada sana’arsa ta hannu,
Dole na riqe takuna Lubna nashirin ruguzamin komai,
Kamar wani zaki haka yashigo dakin badee daya fi wata be leqoba yaka yaringa ihun kiranta dasauri tafito gabantanafaduwa dan tasan ba alkairi ke kawo shiba,
Ban hanaki yiwa enmatan baby gorin haihuwa ba,
Shiru tayi tana sauke idonta kasa,
Hakan yatunzurashi bazata daina yimasa shiru ba kenan shifayarasa abinda yahana shi sakinta ko kuma korarta itada yayanta ya tsani ganin su,
Kyakkyawan mari yadauketa dashi,dasauri Lubna tafito tanajanta gefe,
Metai maka? Tafada muryarta da alamun kuka,
Zaki kaucene kosena jimiki ciwo,badee tace, Lubna banason irin haka kije kicigaba da aikinki,
Mama kidaina bata yawun bakin ki babu Wanda ya isa ya wulakantaki ina kusa,
Saukar mari taji hakan yasata tsaya wa tana kallon majid sekuma jini yafara fita daga hancinta.
Ku yarda dani idan aka kirani Anty wani dadi nakeji senaji nazama wata babba,irin anty Sophie ina wuni ya typing😎 wayyo dadi sanaji kamar nabawa wacce takirani Anty sweet🍬,
Inkinaso kiga yadda murna ke lullubeni kicemin baby Sophie 🤔 ranar sekin goyani kuma da zani😂.
LUV U ALL❤
[7/21, 5:49 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
*Wani Abu se rayuwa lokacin dakake dariya lokacin wani ke kuka,lokacin dakake ta kamar kanada lpy lokacin waninacan yana shan wahalar ciwo,haka a kullum aka haihuwa haka kuma kullum ake mutuwa😭,
*yayinda kake takama da tarin dukiya wani yana can yana tunanin ina ze samu abinda zeci yanzu anjima bema San ya zeyi ba, don Allah kada mu jira se munsamu dayawa zamu bayar, Dari biyun daka fi karfin ta koda a kullum irinsu zasu fadi daga jikinka bazakama lura ba itace zata saka rayuwar wani cikin nishadi da jin dadi na wuni daya,
*nera goman dazaka bawa wani bawan Allah baka saniba ranar gobe kiyama kilama itace zata zama cikon mizaninka Na shiga aljanna,
Ya Allah kabamu badon murama ba sedan mukasance masu jinkai da taimakon en uwanmu Allah ka kara rufamana asiri duniya da lahira ameen thumma ameen,
Page 22
Daga hannun sa yai ze mareta badee ta janyeta,
Haba majid yanzunnan idan ta birkice ni zaka bari da ita kuma kasan yadda take don Allah kai tafiyarka karka tadomin rigima,
Wallahi ban haifi danda ze fifita uwarsa akainaba ni zaki nunawa soyayyar uwa har za kice bazan yimata hukunci ba,gorin haihuwa za tayiwa matata wayasanima ko duk cikin datake samu yana zubewa kece sila,ni nafara zarginki ma wallahi bakar munafuka dole nai bincike akan ki Dan nafara gano take takenki kuma wallahi duk nakara jin anmata gorin haihuwa sena illataki mutanen banza mutanen wofi,
Majid kadai San inda mutanen banza suke Dan kana tareda su,ni wallahi nafi karfin nayiwa kishiya wani mugun Abu wai dan karta haihu,ta haihu mana gatanan ga gidan da mijin,inda saniyar gaba tasha ruwa wallahi anan ta bayan ta zata sha,ba dai kabawa Neman kudi muhimmaci ba akan bautar Allah da kiyaye dokokinsa badai kayi watsi da tarin tulin haqqoqin mu dake kanka ba?to wallahi ka shirya ranar da Allah ze damqeka ranar da zakayi kidanka kuma kayi rawarka,
Haryayi niyar fita yaji ta ambaci haqqi se yadawo ya kama hannunta, dama Riga da zanin jikin sunmata kyau Dan haka yakauda idonsa daga cikin nata dama haka kesa yaji ya tsaneta,
Sekicemin haqqinki kikeso abaki jarrabar ta motsa kenan to ai ba kiyi magana da wuriba,
Nidai bahaka nake nufi ba kasakemin hannuna inada aikin yi,
Taji tsoro sbd tajima batasha maganiba Dan ganin yana Neman share shekara be nemeta ba to ita yanzu yama zatayi?Lubna dake kan Ku jira zaune ta kalla da alama ma bata hayyacinta,
Janta dayayi dakarfine yasa tadago tana kallonsa dasauri yadauke kansa danbayaso abinda yai niyya yaruguje, dakin sa dabaya tuna rabonsa dayashiga ba ya tura kofar, yayi mamaki sosae ganin dakin agyare da alama anadan kula dashi sedai yadanyi kura,
Waike wane irin wulakanci ne wannan?se kibarni inata…..sekuma yai shiru yana kyacci hadida girgiza kansa,
Seda ta Daura zaninta tace,inaso ne nanuna maka yanzu bakina ya bude kuma kasani niba zaman ka nakeba zaman yayana nake zancen jaraba kuma kaika koyamin kuma nadaina yi Na barka da abinka banida damuwa dakai,ka kiyayi ranar dazaka nememo karasa kuma daga yau in ka kwaso yayan jarabarka ga en matan baby can always available karka kara zuwa gurina balle katadamin hankali Dana yayana,
Baki asake yake kallonta, gsky zata kwafsamai domin tafi safara’u akomai amma besan meyasa yake jin kamar yakasheta ba inya ganta dukda inya tuna yadda tacika mai gida ransa yana baci, to wai duk ina soyayyar danake mata?(yadda naji kamar nabuge bakin dan air),
Miqewa yai yashiga bayi yayo wanka badee kuma dakinta takoma,
Tasami Lubna adaki tana jera kayansu a wardrobe batako kalli inda takeba tawuce toilet gani take kamar duk Lubna ta fahimci komai,
Ita kuma bin maman tayi da kallo hartashige toilet,murmushi kawai tayi afili tace inama waccen matar zata barku kuzauna lpy?,
Safara’u taga shigarsa bangaren badee amma tayi jiran fitowarsa har tagaji be fito ba,
Meya tsaya yi ohh ni safara’u, daga karshe dai tahakura tazauna tunanin yadda zatayi da lubna,
Lubna ta dawo daga islamiya da safe around 12:15 a gate tasami wani manna’u daya manne mata yasan lkcn datake dawowa daga islamiya Dan haka anan take samun sa tayi kora harta gaji,
Yi tayi kamar batasan da zaman sa awurinba Dan haka yai saurin shan gabanta, haba lubna ta kisaurareni koda minti biyarne,
Malam banida lokacin ka Inada abinyi kabani hanya,
Tana gama fadar haka tabi gefensa zata wuce seya riqo hijabinta daqarfi ta kwace tana masa mugun kallo Dan haka Yakama kansa,
Tana shiga tai wanka ta Dora musu abincin rana fara damai har sun saba kullum shinkafa ba miya sedai mai da gishiri sharrin safara’u ne wannan,
Tafito tsakar gida dibar ruwa taga safara’u da majid sun gito da alama seyanzu zefita ko kallonsa batayi ba tacigaba da aikinta,
Ke lubna baki iya gaisuwa bane?majid yatambayeta ganin da koba komai tana gaisheshi,
Batako dago ta kallesu ba,
Yaushe zata gaishemu kuwa yarinya ta girma taga kirjinta ya cika takai daidai dakowa aure takeso,
Ita tafada miki tana son aure?
Dazu naganta dawani harda riqe mata hijab aiko nace sena fada maka kaga inbaka yardaba ga shaida,
Tanuna masa hoto awayarta, sbd tasan wannan saura yin wata rana tanaganinsa yana tare Lubna sedai bata taba kula shiba Allah yasa burinta yacika a aurar da Lubna auren dole Wanda bazata taba jin dadiba yadda uwarta take ayanxu (safara’u kin manta dadi da wuya babu Wanda ze dawwama),
Nikam da lubna ta lalace ai gara ka aurar da ita nikam inason ta kuma ai da nakowane, yadda take maganar dukse yaji ya yadda da ita amma wannn hoton ya harzuqashi,
Kusa da lubnar yatafi,yanzu kinzabi kizubarmin da girma da mutunci akan ki fadamin kina son aure namiki?,
Ni bancewa kowa inason aureba kuma bantaba yin iskanci ba kaima kasani banaboye abinda ke raina matukar inada gaskiya,
Karya kikeyi kinkoyo munafurci gun uwarki Dan haaka dole nadauki mataki dole na aurar dake akan kijanyomin abin fada kihanani shiga mutane,
Itakam cigaba tayi da aikin ta tana tabe baki Dan bata bawa zancen muhimmanci ba,
Safara’u dake gefe tayi wani murmushi alamun jin dadi aranta tace, dole akarawa malam kudi Aikinsa nakyau(kuji Dan Allah majid ba bincike hujjar dabata hujjaba yahau kai yazauna),
Anty Sophie
Baby Sophie luv u buhu buhu❤
[7/22, 7:42 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Bance dole se kowa ta karanta littafina ba,babu abinda ze bakanta min rai irin mutun fiye da dari su karanta littafina amma basu wa’azantu da abinda ke cikiba, su karanta littafina batareda sundauki darrussan dake ciki ba,koda mutun daya yakaranta littafin kuma yadauki wa’azi da darasin dake ciki to zanfi alfahari da hakan kuma nayi bugun gaba dashi ako’ina,ba don in burge kokuma in Tara tarin masoya nakeyi ba inayine saboda Allah.
23
Mama Wannan gashin naki dani nakeda shi dole mane na saka mai relaxer kigafa yadda yakeda uban yawa gashi seyaita nannadewa,
Lubna dakewa badee kalaba take fadar haka,
Kuma ahaka dakika ganshi bantaba saka masa relaxer ba ko bayan aurena ba yadda babanku beyiba nace bazan saba karyazo ya lalace min irin na Fareeda Dan gashinmu iri daya da ita wai ita batason shi ahaka taje tana saka relaxer aiko duk ya kakkarye,tafada tana dariya,
Itama lubna murmushi tayi tace inaso naga kanwar nan taki amma nafiso nafara ganin yaya asama’u Dan yadda kike ban labarin ta,
Hmmm,Ashe kinada jira lubna adadin shekarunki aduniya shine adadin shekarun da suka guje ni, inaso naga mahaifiyata amma banida hali nasan ita tanaso taganni idan su basa sona fatana dai Allah yasa suna cikin koshin lafiya,
Ni fa mama nayi mamakin yadda kika ki binsu kika tsaya gun Wannan mutumin nifa ina danasanin shine mahaifina wallahi Sam Sam banso yakasance u….
Lubna yakamata zuwa yanzu kifahimci abinda nake kokarin nuna miki a kullum, eh naji ke yarinya ce amma duk yarinyar data kusa shekaru a shirin a duniya yakamata tagano abinda ake kokarin nuna mata,
Yau inaso ki tsaya ki saurareni dakyau idan da a can baya ina fada miki magana atakaice to yanzu Zn miki bayani sbd kina bukatar sani Dan ke macece watarana kina gidan aurenki,
Lubna idan akace miki aure to magana ce da babu wasa acikin ta magana CE me girma kuma aruyuwar duniya wuya ko dadi babu Wanda ze dauwama kamar yadda rayuwar mu bazata dauwama a duniya ba,
Eh Allah ya hallatta saki amma koshi bayasonsa beside inason babanku sosae lokacin dough yanada laifi babba ma dan bekamata yabarni da dawainiyar yayansaba Dan bayason haihuwa, kuma tarbiyar yaya yakamata ace sunsameta ne daga gurin mahaifiyarsu,
Lubna kinsan duk abinda babanku yake yi ada dasa hannun mahaifyarsa?idan natafi nabarku Waze kula min daku dukda lkcn ba ahaifekiba nasan abune me wahala idan narabuda babanku subarminke sanin kanki ne banason hayaniya Allah ne kadai yakawoni gidannan, lubna inason kusamu tarbiya mekyau idan nabarku wahala kawai zakuyi kiga yanzu da ace bananan ya auro safara’u duk tarbiyr data doraku akai ita zakubi which bana tunani zaku samu tarbiya ta gari,
Yadda kikejin anacewa uwa uwace to haka ma uba ,iyaye dakika gani ba’acanza su duk yadda sukakai ga lalacewa dole ne abasu girman su na iyaye Dan haka inaso ki kiyaye harshen ki akansa kodan yadda kike ganin su Abdul sunayi kinji,(yanada kyau muringa nusar da yayan mu irin wannan),
Bayan haka lubna akwai hakuri a rayuwar duniya bakitabajin Wanda yakeda hakuri ya wulakanta ba Dan haka idan baki dashi tun yanzu kikoya ina fatan wannan rayuwar damuke ciki mu gaggauta barinta Allah yatabbatar mana da alkhairi yakuma baki miji nagari,
Ameen ta amsa tana rufe fuskarta dadukan tafin hannayenta,
Murmushi kawai badee tayi tanajin son yayanta fiye datunanin me karatu,
Babuko sallama yafado dakin yana kiran sunan lubna fitowa tayi tana kokarin rufe zip din rigar ta,
Gani ta fada bayan tafito,yawwa sako hijab Dinki ga bako kinyi awaje sunansa Mubarak Dan gidan wani abokin kasuwanci nane Dan naga kinfara kula maza yanuna kina son aurene dan haka gara na aurar dake akan kizubarmin da mutunci,
To baba ni banfa cemaka inason aure ba,takarashe maganar tana turo baki,
Koma dai menene kije yana waje,fita yayi daga dakin,
Hmm wallahi se yatafi da kafafunsa haka kawai,
A tsaye ta same shi yajingina da motarsa taimasa sallama shiru be amsa ba,
Seji tai yace wooo wannan mezafin ce,dasauri takalleshi da alama besan maganar a fili yaiba,
Tab….wannan ko gaisawa bazata bari yayiba taga alamar riqaqqen Dan iska ne wato yama gano me zafi ce hmm,
Ban baka damar yin magana ba inaso kasaurareni dakyau kaji,
Dafarko dai tundaga ganin ka danayi baka kwantamin ba in fact u’r not my type karkabari abata ma lokaci idan aure kakeso kaje kanemi daidai kai, ina fatan zaka fadawa Wanda yaturo ka baka dace dani ba? Nagode,
Baki asake yake kallonta harta bacema ganin sa,lallaima yarinyar nan dama haka take batada mutunci to wallahi dole nasan yadda zanyi tazo hannuna nazata mesaukin kaice na wawusheta nabar kasar gaba daya🤔,
Yaukam dukansu yaran suna gida Dan haka suka zauna palon mamansu sunata hira Sega majid yashigo dukansu suka gaidashi be amsaba segun lubna ya tsaya beyi wata wataba ya kifa mata mari afirgice ta miqe,
Ni zaki maida karamin mutun,naturo yaro gurinki ki walakanta shi dankina takama da rashin mutunci?,
Nifa nagansa ne beminba shiyasa nafada mai gaskiya dankar na wahalar dashi,
Ni nace miki se Wanda kikeso zaki aura?Wanda nakeso naturo miki kuma dole kiyi yadda nakeso,
Wallahi ni banason sa nagwammace na mutu akan na auri wannan Dan iskan,
Chajan dake gefe ya zaro yahau dukanta, ko uwarki ba ta isa ina magana tana magana ba balle ke kuma gidannan idan ana kaunar zaman lafiya dole ayi yadda nakeso,
Sunso su kyaleshi amma abdulrahim yaga hankalin baban baya jikinsa da haka dasauri ya kwaceta yana boyeta bayansa dama yana cike da haushin baban,
Ya’isa haka baba tadaku sosae kalla har jini ya soma fita,inace kuma kasan yanayinda take ciki?kuma ajirata takawo Wanda takeso bawai akakaba mata Dan iska ba,
Abdulrahim har dakai kakoyi rashin kunyar?inace kaima kasan halina Dan haka miqomin itanan,
Basuyi auneba suka soma jin ihun safara’u, labe take musu Dan taga yadda zasuyi,Ashe lubna taganta kuma dama majid ya tabo abubuwan,
Dakyar da bala’i aka kwaci safara’u a jaka tabar part din badee sbd ta daku,majid kuwa kokarin dukan lubna ya soma yi sedai abinda yagani ya matukar firgitashi duk yadda suke fada beyizaton abin yakai hakaba,
Ka gani ko majid?yanzu a tsaye zamu kwana wallahi jiwa kanta ciwo zatayi abdulrahim kukama min ita karta kashe kanta.
Anty Sophie ta gode😎
[7/23, 8:34 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Jidda (dota) & umzeey Allah yanunamin aurenku in kwashi Shoki ameen❤.
To kardai kuyi min fada yadda kuka saba Dan nahade Ku a page daya😏.
Page 24
Wani kalar faduwa tayi da seda hankalinsu yatashi sun tsaya suna kallonta kowa yakasa isa inda take, daganan kuma bata kara motsiba,
Ko mutuwa zakiyi sedai ki mutu akaiwa Mubarak gawarki aljanin jikin ki ma yaci ubansa,dakici gaba da borin kiga inban saka muciya ko tabarya na bugeki ba bakar munafuka,
Fuuu yafita kamar ze tashi sama (kadai tafi zuwa gashin jikin enmatan baby😡),
Abdulrahim ya kwashe ta ya kaita dakin mamansu abduljabbar yai mata addua ajiyar zuciya tasauke sekuma ta gyara kwanciyarta se bacci,
Zama sukayi adakin suna maida zancen,
Abdulrahim yace,mama waime baba yake nufi damu ne kusan shekara goma bamuda maraba da babu a gidannan sedai idan yana Neman amfani damune musamman lubna,
Numfashi badee tasauke,Abdul nima bansaniba amma nasan duk kalar hakurin danake yakusa kaini maqura,sundauki karan tsana sundorawa lubna karkaji mamakin safara’u ce tazugo shi in kuma ba hakaba to yanada wata manufa,
Abduljabbar yace ,lallai kam dole dabiyu yabijiro da Wannan zancen haka kawai ya dauko mata zancen aure ba batareda wata manufa ba,
Abdul’aziz yamiqe yana cewa karfa kuji mamakin saboda kudi ne zebada ita Dan babu abinda baba yasawa gaba irin Neman kudi,
Abdulqadir yayi murmushi yace, idan dagaske auren yakeson yimata bayaso tazubarmai da mutunci meyasa bazece ta kawo mijin dakanta ba?wallahi idan ya takurata bataso wannan Mubarak din zamuyi wa duka seya fita hayyacinsa,
Bance kudaki Dan mutane ba amma dai kome zakuyi indai zakukarbowa kanwar Ku yancinta ne kuyi amma karku illata yaran mutane,
Abdulrahim yatashi tsaye yana fadin Hajiya zamu fadawa kawai,
Yome hajiyar ta isa tayi banda tsufa daya tasomata ma,ga baba bayajin maganarta ko kadan, inji aabduljabbar,
Aiko wallahi barmasa gidan zamuyi Dan baze kashemu daranmu ba, fadar abdulqadir,
Abdul’aziz yace wallahi kuwa dama bamuda wani amfani a gidannan sedai kawai yana amsa sunan ubanmu ne,
Kuyi tunani dai dukanku bayara bane koba komai ubankune kuma shiyake cidamu,
Mama kidaina zancen abinci,muntaba ci mun koshi ne? Ana ganin mu anga yunwa kullum cikin cin fara damai kekanki kina marmarin cinnama amma kinfi sati ko takardarsa baki ganiba, duk abinda muke samu a sana’ar damuke tabawa aharkar makaranta yake karewa,inji abdulrahim yadda yake maganar abin yakai shi maqura kenan,
Kusani dai duk lalacewar gidan uba gara ace kunadashi kuma inaso kudan masa uzuri dukda wasu abubuwan dason ransa yake yi amma bayinkansa bane, kuma idan munbar gidan ina kukeso mutafi?kunsandai banida inda zan kaiku ko?
Abdul’aziz yace mu babu ruwan mu dashi danki zamuyi danhaka mujira muga mezeyi ,in zancen gidane ai akwai gidan Hajiya daki semun zaba danhaka ki kwantar da hankalinki,
Shiru kawai tamusu Dan taga alamar ba abinda yashafesu da mahaifin nasu,
Kukan lubna ne yasa duka suka maida hankalinsu gareta,
Yaya kubani ruwa don Allah karku dauko a cup nafison nacikin bucket Jinake kamar Na shekara bansha ruwa ba,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, yaukuma da shan ruwa abubuwan suka zo?
Abdulrahim yadebo ruwa a cup ya tofa adduo’i aciki yabata ko sauke hannun sa beyiba yaga ta ajiye kofin yaleqa yaga bakomai aciki kallonta yai yaga ta lumshe idonta,
Dariya Abdul’aziz yai yace wannan mutanen na lubna inaga daga birnin sin suke kuma da alama kasa suke zuwa wannan shan ruwa haka sekace garin kwaki😂
Dariya sukayi dukansu kafin suyiwa maman sallama suka nufi dakin su,
Washe gari koda suka tashi hannun lubna ya kumbura sosae da alama taji ciwo ne lkcn data fadi, dakyar suka ga gari yayi haske danse kuka take,
Dole tace su Abdul sukaita gidan me gyara targade a duba hannun Dan babansu baya nan bazata fita ba izinin sa ba,
Mama kikamamin nasa Riga,inji lubna,
Meye kuma sekin canja kaya kayanma na bacci?
Mama sababbi ne fa kuma kinga Wando ne banaso naje anajan hannun ina tsalle Allah tsaf zan hankade zanennan, amma kinga inwando ne nayi wulli yadda raina yakeso,
Sosae badee tai dariya tace Allah ya shirye ki lubna
Ameen tace bayan sun gama saka rigar,
Da shigarsu zauren gidan taga wani hadadden saurayi da wata matashiyar mata agefe da alamamatarsa ce Dan ga cikinan jikinta zekai wata biyar se matsar kwalla take tana kallon kafarta data kumbura,se sannu matashin ke mata,
Lokacin da akazo Jan kafar ihu take tana lailayo ashar, shi kuma se sannu yake mata kiyi ahankali karkiji wa baby ciwo,
Seda akazo daure kafar tayi shiru tana kallon mijin nata daya shagala wurin kallon cute face din lubna,
Hawaye take ahankali ganin yadda wannan matar ke ihu kila da zafi sosae,
Me dorin yacewa su Abdul bisimillah,bayani sukai masa faduwa tayi kan hannun kafin safe yakumbura yana mata zafi,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un tafada lkcnda akafara Jan hannun, Dan matashin saurayinnan se kallon yadda take damqe hannun nakusa da ita take tana kuka ahankali dukseyaji ta burgeshi,
Wani uban tsalle tayi lkcn da akasa abin daurewar ya tsuke sosae, dukansu seda sukayi dariya,kekuma ki tsaya mana karki batamin aiki,
Bayan angama haryanzu mata damijinna zaune da alama wani Abu suke jira,
Tunda suka shigo talura yana kallonta har suka fice, jyuowa tai taga haryanzu ita yake kallo suna hada ido se yasakar mata murmushi Dan kallon matar sa tayi se taga ta ware mata yatsunta guda biyar ta motsa labbanta alamar Uwar ki?
Zaro ido tai sosae sekuma tayi saurin dauke idonta tacigaba da tafiya da sauri sauri Dan su Abdul sunyi gaba.
Anty Sophie na fatan yauba korafin yayi kadan? 🤗
[7/28, 3:03 PM] Babee Feeya: [7/26, 12:40 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine yar uwa rabin jiki billy galadanchi❤
Page 25
Daganan gidan Hajiya suka wuce dama Abdul’aziz ne kawai se abdulrahim suka kaita suna zuwa suka samu hajiyar azaune tsakar gida ita kadai da kofin koko agabanta da sauri lubna ta karasa gaban hajiyar tana murmushi,
Hajiya barka da hutawa,barka dai kanwar maza yakuke ya mamanku?
Lpy lau suka amsa,
Kokon dake gaban ta lubna tadan kurba tace haji wai anya ba kwakwa a kokon nan jinake ina wani lulawa,
Dariya sukayi dukansu Hajiya tace kikarasa shanyewa naga alamar ko karyawa bakiyiba,
Wlhy kuwa Hajiya kamar kinsani,
Meyasameki a hannu?
Jiya na fadi Ashe naji ciwo seyau dasafe natashi hannun yakumbura shine aka gyara,
Nan abdulrahim ya zazzage mata abin da yafaru,
Tabdijam…idan aure yakeson yimata aiseyace ta fito damiji, towaima yaushe yasan Ku yayansa ne dahar zenuna isa akanku?
Kunga Ku tashi Ku tafi zuwa sabogoginku kubarmin ita nan nayi wanka naje gidan kobayanan zan jira shi Nagano take takensa iskanci ne danhaka wallahi dole na dauki mataki danyaga nazuba masa ido ne shiyasa iskancinsa ke ta’azzara harni zekawowa batun banza,
Shiru sukayi suna saurarenta dasuka masifarta bamekarewa bace suka barmata gidan,
Wanka kawai tayi komai bata shafa ba tasaka kayanta suka nufi gdan majid,
Suna tafiya kafin su samu adaidaita tana faman mita,
Yaushe zanyadda atura yarinya gdn mijin da bataso, daya aka kare ma da auren soyayyar balle Wanda babu ko digonso acikinsa,ga yaron fandararre wallahi dasake,
Har suka samu adaidaitan suka isa gdn surutu take har tsoro tabawa lubna ,wannan mita har ina er tsohuwa?
Batakobi takan lubnar ba ta shiga gidan dakin safara’u tafara zuwa taringa buga kofa amma bata bude ba dole tahakura tayi bangaren badee,
A kwance suka sameta Palo tayi shiru tana tunanin abin duniya,
Gaisawa sukayi da Hajiya ta kawomata Dan waken datayi yau dashi suka karya kuma dashi zasuyi abincin rana,
Kai amma er nan kin kyauta dama inajin yunwa da babu komai acikina tunjiya se ruwan kunu,
Allah sarki Hajiya yakika zauna da yunwa kunu aiba ya rike ciki?,
Badi babu komai gidan se farar shinkafa komai babu, er wannan yarinyar dake gurina shekaranjiya uwarta tazo ta dauke ta wai aure zasu mata banida Dan aika ga su Abdul ma sunkwana biyu basujemin ba,
Zaro ido badee tayi tace, Hajiya zama ke kadai a gida babu dadi ko zaki tafi da lubna ne?,
Bazan je da iyaba kema ai kina bukatarta sedai inkosu Abdul dayansu ze koma can,amma lubna kam kodan Wannan munafukar matar ta majid bazan daga da itaba Dan nasan koba komai tana tare miki wani abin,
Hakane kuma bari abdulrahim yazo muji seya fadi Wanda zekoma candin Allah yakauda bacin rana kar wani Abu yataso bakowa kusa,
Uhm,ke dalilin zuwana gidannan abdulrahim yacemin wai aure majid zewa lubna kuma batason mijin?
Eh haka yazo jiya yana fada Dan ma yaturo yaron nibansan me lubnar tace mai ba shine yaje yahado majid din yazo nan yaimata duka ciwon ta yamutsafa shine kikaga taji ciwo a hannun,
To ana auren dole ne kuma idan aure zemata seya bata damar kawo mijin datake so,
Inji Hajiya,
Hmmm,yaushe zeyi haka tunda zugoshi akayi saboda ba akaunar ganin farin cikin mu,
Kardai kicemin safara’u ce ta zugoshi?,
Itace fa hajiya kuma wallahi nasan dabiyu yayi haka baze rasa wata manufa akan wannan ba tunda baban yaronma abokin kasuwancin sa ne,
Aiko yadebo ruwan bala’i Dan wallahi bazata sabuba baridai yadawo yau inanan inajiransa,mukayi rashin mutuncima ba gaira ba dalili balle antabo mu?(yau antuna da baya kenan hajiya),
Bayan azahar safara’u tatafi part din bade tana zuwa ta tabe baki,
Tsohuwa sarkin jaraba anzo?toyau dai koda mekikazo keda munafukar matar danki dabatada maraba da sharar gidannan awurinsa inada yadda zanyi daku domin Dan naki atafin hannuna yake,
Badee dai shiru tayi Dan ita batason tashin hankali sedai tasani Hajiya ba kyaleta zatayi ba,tunkafin tagama tunanin tajiyo muryar hajiyar,
Yo safara’u akwai munafukin dayakaiki keda uwarki?anyi muku inuwa amma kuna saka Wanda yakaiku inuwa rana?karki manta taimakonki nayifa keda uwarki Dan nazata son Allah da annabi kike wa majid Ashe ba haka bane Dan abin hannunsa ne ya tsokale muku ido,
Tawani gefen bana ganin laifinku sbd shine yabaku dama babu abinda yasawa gaba seneman kudi shiyasa kuka samu damar rufe masa ido yana tunanin kune masoyansa kukasa ya guji uwar data kawo shi duniya,yabar mace guda daya dadaukar dawainiyar yayansa harsu biyar,
Idan kin lura mumunkama Allah shiyasa muka zamemiki kadangaren bakin tulu,danke kina er bakin ciki zakije ki zugoshi ya aurar da yarsa gawani can Dan iska wato haka kikeso kiga rayuwar bayin Allah cikin mugun yanayi bakisan shi Allah ba azzalumin sarki bane danhaka munanan dubunki zata cika,
Kuma wallahi yau koda bala’i da masifa da rashin mutunci babu Wanda ya isa ya aurar da lubna ga wanda bataso kuma inanan inajiran shi majid din dakike ta kamar ke kike juyashi,
Shegiya mekar kama dabakar zuciya,
Duk abinda zakice kice danki dai a hannuna yake kuma yau zakiga yadda miji ke tsallake umurnin uwarsa yabi na matar sa,
Majid yadawo jinhayaniya bangaren badee yasa shi tafiya can yana fadin
Allah yasa ba enmatan baby aka taba ba,(kuji Dan iska),
Aiko safara’u tana hango babbar rigarsa na cika da isaka ta daka tsalle tafadi kasa,
Wayyo Allah wayyo nikaina namutu na lalace Na shiga uku na,
A gigice ya isa yamiqar da ita yana tambayar menene,
Wai Hajiya ce tazo shine nazo ingaisheta sukafara zagina itada badee’a wai nafita karna shafa musu tsiya kuma dannace lubna tazo ta tayani fito dakayan wanki shine sukemin gorin haihuwa wama yasani koni ke zubar da cikin danake samu lubna bazatajeba karna koyamata bin bokaye da malaman tsibbu Dana saba bi Nida uw…
Ransa yakai kololuwar baci yasan uwarsa bazata dakuba danhaka yaikan badee dake tsaye cike da tsoro tana firfito da ido dama irin haka take gudu shiyasa duk yadda safara’u keson suyi fada bata biye mata saboda duk laifin duniyarnan hukuncinsa duka ne ita da yayanta duk basu wuce hakan ba,
Marin daya gaura matane yasata dawowa daga tunanin datake atake kanta dake ciwo yasara mata dafe kan tayi tana zama ahankali take kuka,
Hajiya takoma gabansa takwada mai mari har yadaga hannunsa sekuma ya sauke hannun,
Wannan abin safara’u taso yakasance tasan daya daki uwarsa lallai daga uwar har badee’a da yayanta barin gidan zasuyi sekuma Allah yadauki mataki akan majid da kansa batareda tasha wahalar kawar dashiba,
Ashe kai karamin Dan iska ne tunda bazaka iya rama marin da uwarka tamakaba?,
Duk ba wannan yakawo ni ba inaso kasani wannan auren dazakiyiwa lubna babu shi banason nasakejin batun yatashi,
Kasan halina sarai Abdulmajid idan tayi nasarar rufemaka ido har kake tsallake bin umurnin uwarka tayi nasarar sawa ka mance da matar ka baiwar Allah uwar yayanka to nasan batayi nasarar kawar ma da memories dinka na daba wallahi tallahi kaji na rantse zandawo Hajiya Rabin daka sani ada kuma ba karamar barna zamu aikata ba kaji na fada maka kuma mu zuba ni dakai shege ka fasa,
Sosae maganganunta suka shigeshi har yadanyi sanyi yana hada ido da safara’u ya birkice,
Yarinya y’atace kuma na bada ita Dan haka koduk duniyarnan zata taru akaina babu Wanda ya is a yasa na chanja maganata danhaka nanda sati daya za ayi komai agama kuma wani acikinku yayi trying something stupid kuga yadda zan tada hankalin kowa agidannan,
Fuuu kamar zetashi sama yafita,
Lubna ta sulale akasa tana kuka sosae harda sheshsheka,
Badee ma haka ta kalli Hajiya,
Yaushe zamuji dadin rayuwarmu ?Hajiya zuciyata nauyi take min abubuwa dayawa marasa dadi take dauke dasu,kikalli yarana koda sundauko jin dadi nawuni daya dole se an wargaza musu shi bansan me safara’u take nufi damuba,
Sosae Hajiya take tausayinsu,seda ta lallashe su sukayi shiru tace zata tafi se dayadaga cikin yaran yazo,kuma duk abinda yataso su aika mata Dan daga yau bazata kuma yin shiru ba dan tagano badee kamar doluwa ce komai akemata bakin nan gum kamar ruwa yaci shirwa,
Seda ta sakata a adaidaita kafin tajuya gida tana tunanin yadda za asaka wa rayuwar erta kunci tun tana yarinya.
(Ashe akwai Dan karamin yaki a gdn majid).
Don Allah fans kuyi hakuri dajina shiru kwana biyunnan banji dadi bane shiyasa nagode❤,
Bansan me mutane sukeso su saniba amma dayawa suke tambaya na wai billy galadanchi yayata ce wasu har private suke bina,to ga amsarku nan,
Anty Bilkisu yayata ce the same father the same mother ita nake bi☺
[7/28, 1:48 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja’afar novel group
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusher fans club
Feedo novels,Wannan shafin nakune ina godiya sosae da kwarin gwiwar dakuke bani inajin dadi sosae Allah yabiyaku❤ameen.
Page 26
[7/29, 1:13 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja’afar novels
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusha fans club, nagode sosae da kwarin gwiwar dakuke bani Allah biyaku da mafificin alkhairi ameen.
Page 26
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba domin majid ya haukace hagaga shirin biki yake dukda ba ayi komaiba yace Daura aure kawai za’ayi,
Sosae suka shiga firgici bakamar lubna Dan dayazo baban yatursasata dole tafita a motarsa ta same shi,
Sauke glass yayi ganin ta tsaya tana kumbura Fuska,
Madam shigo mana kika tsaya awaje,
Shiru ko motsi batayi ba yaita magana ta kyale shi,
Inba zaki shigo ba zan kira baba Wallahi, Dan murguda baki tayi tashiga motar tana jin takaicinsa sosae tasan idan tayi rashin kunya yanzu majid yaji kan mamanta ze sauke kuma batason abinda zetaba badee danma kwanakinnan tana ganin ta se a slow ko baccin kirki batayi,
Zama tayi tabar kafafuwanta awaje tajuya masa baya,kishigo mana kinsa AC yanata bin iska yace yana kallon bayanta,
Babu abinda na tsana irin kallon fuskarka, na tabbata ashekarar nan baza asamu Wanda zeyi kalar danasanin dazakayiba idan kayi gangancin bari aka Daura auren nan,
Hango majid tayi yasa dasauri tasakafafuwanta tana rufo kofar,
Murmushi yayi yajuyo sosae yana kallon fuskar ta dake a tamke kamar an aiko mata Manzon mutuwa,
Dan matsowa yayi ganin majid yashige gida yana Dora hannunsa kan shafaffen cikinta me aka sawa cikinnan?
Dagowa tai dasauri ta kalleshi da idanunta dasuka soma chanja kala zuwa ja,
Kadauke hannunka daga jikina kuma karka kara wannan kuskuren,
Jikinki aina wane kwana nawa yarage?daga nadan Dora hannuna abinda zan mulka son r…
Mari ta wanka mai shine sanadin tsayawar sauran kalamansa,
Dan iska la’ananne wallahi ka gaggauta fadawa mutanen nan kafasa auren nan Dan zakayi danasani fiye da tunanika,
Fitowa tayi tashigewarta gida tana zuwa tabawa badee labari atake badee taji batada lpy,
Addua kawai tasa agaba Allah yakawo musu mafita,
Washe gari koda suka tashi majid yakawo wani shirgegen kato wai gadin lubna zeyi karta fita,
Duk basu tabbatar da abinba seda suka ga lallai fa auren zemata haryaraba invitation card duk masifar Hajiya al’amura sun tsaya,
Kuka lubna take kamar ranta ze fita yanzu gobe za auramata mijin dabataso,
Yayyanta duka suka zauna adakin mamansu suna jajanta all al’amarin ganin kawai sukayi abdulrahim yafita bababu jimawa segashi yadawo,
Wardrobe dinsu ya warware wata katuwar jaka yahau zuba kayan su lubna aciki,
Saboda bacin rai har inner wears seda ya zuba a ciki se kallonsa suke,kusan duka kayan su ya kwashe dama kayan bawani yawa garesuba,
Badee tace abdulrahim mekake shirin yi?
Gidan zamu bari Wallahi bazaku kwana gidannan ba harmuma,
Yajuyo yana kallon kannensa yace,Ku shirya fada zamuyi megadin can ymzamuyiwa dukan tsiya,
Abdul’aziz ya kwashe da dariya kai yaya idan kakaimu can Waze bamu abinci,?
Allah zebamu kamar yadda yasaba bamu,
Kutashi mu tafi,aidasauri lubna ta tashi Dan duk wata hanya dazata sa afasa aauren sonta take,
Suna zuwa gate megadin yataso yana kallon lubna,
Ke koma megida yace kar abarki ko gate ki l….
Kyakkyawan naushi yasamu daga Abdul’aziz sauran suka riqe shi,
Kabarta ta fita inkayi gardama jikinka yayi tsami,inji abduljabbar,
Itadai badee wani dadi takeji ganin yadda yayan ta suka soma zama abin ALFAHARINTA,
Abdul’aziz yaja hannunta Dana lubna suka sasu a adaidaita yakaisu gdn hajiya,
Zuwa yai yace kusakeshi kuzo mubi bayan su gobe zamuzo adebi kayan shimfiida Dan babu makwanci a gidan,
Me gadi kam bakinsa yatoshe daya sha haushi,shima Barin gidan zeyi dama anbashi Rabin kudinsa,
Hajiya har kuka tayi data gansu rayuwar majid nacikin hadari batasan ta ina zata faraba yanzu sunbarmai gidan Siya cinye shida safara’u,
Majid da safara’u dasukaje kware sun dawo suka samu bangaren badee a rufe ga megadi baya nan dakinsa ma bakomai,
Sosae suka firgita ganin har suna shirin kwanciya basu dawo ba, safara’u takafe mai kafafuwa baze iya zuwa gidan hajiyarsa ba seya tuna can kadai su keda mafaka hankalinsa ya Dan kwanta,
Wani kalar nishadi safara’u takeji yanzu tarabashi dakowa saura dukiyar sa dama Dan ita kadai take tare dashi burinta Dana mahaifiyarta yakusa cika,
Danhaka ta zage damtse taiwa majid tarba me kyau yau,
Washe gari yakira baban Mubarak yace amarya tagudu tunjiya yake nemanta babu labari,
Yanzu alhaji kasan yarinarnan bataso zata tursasata?nidai ko anganota yarona yafasa danbanason tashin hankali,
Be jira majid yamasa bayaniba yakashe wayarsa.
Daga nan auren ya lalace,
Saura kuma muji yadda safara’u zatayi da babyn ta.
Rayuwa tayi musu dadi a gidan hajiya domin basuda wata damuwa sosae su Abdul ke kula da gidan dakyar ne zasu wuni su kwana dayunwa tun safe suke fita idan babu makaranta inbasu bar abinda za aciba Dayansu ke dawowa yakawo sana’ar su gyaran waya ne kuma suna siyan wacce ba sabuwa ba su kuma siyar Dan haka basuda matsala sosae suke fahimtar juna koda sun samu sabani,yanzu hakama sun siyawa lubna keken Dinki datafara koyo kuma tana Dan kokari dukda bata kware sosae ba kuma en unguwar basu sansuba sosae sedai ma mutanen hajiya ne dake kusa sosae suna mutunci shiyasa suke kawo dinkin,lubna ma daga ankawo style taga me wahala ne take cewa ki chanja me sauki kokuma ki kai wani gurin karna bata miki,dinkin yara idan tayi seyafi kyau doguwar Riga kamar akanti kika siyo,zaman banza ya kare,
Bangaren majid kuwa sati daya da tafiyar su badee abubuwa suka soma sauyawa kwata kwata hankalinsa ba akwance yakeba duk tunaninsa yakoma kan badee da yayanta ya kama hanyar gidan hajiya har besan iyakaba amma seya kasa zuwa daya matsa dabi hanyar sedai yaga tarin traffic dabesan daga inda yafito ba harseyagaji ya sauya hanya damuwar tai masa dawa har rama yayi,
Safara’u tazama gagarumar me mulkar gida se yadda takeso za ayi kwata kwata yanzu bata zama gidan en aiki tadebo ta zuba tafita lokacin da takeso tadawo lkcn dataga dama idan yayi magana seta balbaleshi da masifar kamar uwarsa karshema shine zebata hakuri,
Mamana ta kaina kinga abinda nace yana shirin tabbata ko?sannu sannu bata hana zuwa….
Sedai adade ba akaiba er gaban goshi,
Kusan shekara goma shabiyar muna fama seyanzu hakarmu ke shirin cimma ruwa,kai amma fa munsha jira,
Safara’u da mahaifiyarta ke magana Dan har kware taje sbd yanzu da motarta da driver intafara yawo se indai mai yakare mata,
Yaya asama’u yau takudura aranta duk yadda za ayi seta shiga gidannan tagano kanwar ta seyanzu take hango kalar da girman kuskuren dasuka yi ido a rufe,tashafe sati biyu tana yawon hanyar gidan kowani daga cikin su badee da yayanta ne tagani kozataji sassauci aranta,
Mamaki sosae yakamata ganin bangaren badee’a arufe sedai hankalinta yadan kwanta dan taga sabon apartment daya sha gyara kila kuwa badeen ce aciki dasauri takarasa tana buga kofar,
Kallon mamaki takewa matar data fito tana wani yauki ga kiba duk ta hade ta zama shapeless,
Lafiya dai kika bugamin kofa na bude kuma kin kuramin ido?
Hmm…tasauke ajiyar zuciya,Dan Allah nanne gidan Abdulmajid me mata badi’a?
Ita safara’u se yanzuma ta lura da matar tana kama da badee’a sedai da matar da lubna kamar an tsaga kara ko ince tamkar yaya asama’u tayi kaki,
Eh nanne amma yanxu nice matar sa badee’a bata gidan yau kimanin wata biyu data gudu itada yayanta annemesu an rasa danhaka seki kara gaba kuje zuwa nemanta,takarashe maganar tana yatsina fuska,
Idon yaya asama’u yacika da hawaye,daga ganin Wannan matar ta majid er bariki ce ta karshe kokuma tantiriyar Mara kunya duk yadda akayi masifartace ta ishi badee’a yasa tabar gidan,
Muryarta araunane tace sakinta majid din yayi?,
Bakiji nace guduwa tayiba?be saketaba mugun halinta de yasa tagudu wayasanima ko yawon barbada ta tafi?,
Ran yaya asama’u yabaci sosae danhaka juyowa kawai tayi tana goge kwallar fuskarta basuga ta zamaba dole su tashi tsaye Neman er uwarsu tabar gidan miji karta fada mugun hannu kokuma mummunan yanayi itada yayanta,
Zama tayi a mota tayi kuka harta gode Allah tana Dora duka laifin akanta ma koda su baba sunyi fushi da ita yakamata ace sun saurareta ita macece kuma tasan kalar abubuwan da ita badee take facing kuma ma akan gaskiyarta take me raba da da uwa irin haka se Allah balle ace tabar su gdn da agaban idonta ma basuda wata daraja kuma ace tabar su to hannunwa?Waze mata tarbiyarsu?soyayya ta shafe komai dukda zata iya hakuri amma yakamata ace sun mata uzuri,
Ganin babu sarki se Allah yasa ta share hawayenta tan tunanin gunwa ma zata fara zuwa?yaya mukhtar kam baze saurareta ba,
Gidan farida tayanke zataje dukda faridan batada mutunci amma dole zuwa yanzu tanemi er uwarta Dan koba komai tana sonta,
Bangaren badee kuwa hankalinta kwance sedai jin kusancinta da iyayenta yasa taji duk hankalinta yakoma can dan unguwarsu daya da hajiya sedai layi ne ba daya ba sedai kuma babu wani nisa a tsakaninsu,tafara tuno moment dinsu da en uwanta,
Afili tace koyaya su ummu suke nasan dai sunanan araye, inaso naga farida nasan itama zuwa yanzu yayanta sun girma,
Allah kadawo da hankalin en uwana da iyayena Agareni, ameen inji lubna dake tsaye tana kallonta.
Kuyi hakuri da wannan don Allah banida lafiya kuma dakyar nayi typing sena samu ya goge,Tnx😍
[7/31, 9:11 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you my everlasting momma Zainab inuwa #aka Anty sis👌🏻,may Allah’s noor be wit u now and forever😍.
Page 28
Sosae badee takejin batada lafiya zuciyarta ke mata ciwo tafi 2weeks ahaka sedai bata fadawa kowa ba,
Batasan tana kaunar mijinta ba seyanzu, yanzu dayai mata nisa,badan faricikin y’ay’ana ta ba bazata baro gidanba kodan giftawarsa datake gani yana rage mata damuwa dayawa duk wayannan abubuwan dayayi daga auren safara’u zuwa yanzu bata Dora laifin akansa sedai akan safara’u aganinta duk ba acikin hankalinsa yake aikata hakan ba,
Sosae take jin tanason ta kusantu da mijinta amma yayi mata nisa irin nisanda batasan lokacin da zasu sake haduwa ba tadade bata ji irin wannan yanayin ba ga ciwon da zuciyarta yana dad’uwa batason fada ne kada hankalinsu yatashi,
Addu’a take Allah yakawo mata saukin wannan ciwon kodan taga iyayenta taji sanyi kuma tanaso taga farin cikin y’ay’anta,kuma dole idan tanaso taji sauki a zuciyarta to seta cire Abdulmajid aranta Wanda take hango dinbin aiki agabanta,
Washe gari tunda sassafe takejin babu dadi jikinta har rawa yakeyi har gurin sha biyu tana kwance hajiya batanan ta tafi kware da Abdul’aziz zata karbo amfanin gonarsu lubna ce kadai a gidan itama yau aiki take tun asuba take wanki kayanta na badee Dana hajiya se 11:30 tagama se kawai tayi wanka ta Dora abincin rana dakin tashiga tadan kwanta tahuta kafin ruwan shinkafar data Dora yatafasa,saukar numfashin mamanta taji yana fita ba daidai ba dasauri takarasa kusa da ita,
Mama menene?bakida lpy ne?amsa ko daya badee bata bataba illa hannunta data riqo tana dumtseshi sosae saboda ciwon datakeji a zuciyarta,
Dasauri badee ta fito waje a daburce,dakinsu Abdul tanufa sekuma ta tuno bakodayansu a gidan ga hadari har anfara yayyafi hijab dinta kawai ta dauka ta kwaso uwar tata dakyar take tafiya,
Babu kowa akan hanyar balle tayi tunanin zasu samu abin hawa,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un kawai take maimaitawa a lokacin kuma aka tsuge da ruwa,
Afili tace shine amfanin waya dayanzu nakira yaya Abdulrahim,
Tsayuwa ta gagari badee Dan haka tasulale akasa ta kwanta bata damu da yanda ruwa ke dukanta ba ko magana takasayi lubna take tunani Dan tasan mura bata mata da kyau,
Wata bakar mota ta hango kirar Benz baka tana tafiya slow saboda ruwan da ake,
Mus’ab dake tafiya yana danna wayarsa soyake yaji ya lafiyar matar sa dukda yasan koya kira rashin mutunci zatayi masa amma a condition dinta yakamata ace yasan yadda take dukda bejima da baro gidan ba dago kansa yayi yaga er yarinya budurwa tana tsaidashi ga mutun yana gani yashe akasa Dan haka yai saurin yin parking daga gefe yafito da sauri,
Ke lafiya meyake faruwa?
Dakyar take magana numfashinta nayin sama sama tace,
Mama na kataimakeni zata mutu don Allah,
Hanzarin kwasar badee yayi yasakata abayan mota dasauri lubna tashiga bayan tana rungumo mamanta dake ta juyi ajikinta,
Baze iyayin gudu da motar ba sbd ruwan da ake ga asibitin dayakeso yakaisu dadan nisa domin a can yake aiki yanaso yadubata Dan ga alama tanajin jiki kuma yagansu lyk they are helpless,
Bayan sun isa asibtin yafito dasauri yadauki badee ya nufi emergency lubna na biye dashi abaya tana sharar kwalla, yakai kofar da ze shiga wayarsa ta fara Neman agaji,
Gado yasamu a gefe ya Dora ta kafin yadaga wayar ganin sunan mahaifiyar matarsa,
Sannu isashshe yanzu kabar matar ka a gd naquda ta kamata munzo asibiti baka nan danhaka duk inda kake kazo muna labour room,
Wani Dr yahadasu dashi Dan duk yarikice yanufi gun matarsa,
Bayan mintuna goma da shiga da badee Sega Dr din yafito yamiqawa lubna wata paper yai mata kwatancen chemist,kiyi sauri kikawo muna bukatarsu yanzu,
Kallon paper take taga tarin abubuwan bukata batada ko kobo take hawaye suka fara zubowa da idonta kusa da chemist din taje tazauna akasa,
Mus’ab kuwa kafin yakarasa labour room har matar sa ta sauka, shiga yai yasamu ana gyara su sedai babyn kamar tazo da mura Dan haka dasauri yasauka siyan magani,
Dasaurinsa yakarasa kusa da lubna shiya manta ma dayazo dawata saboda murnan babyn sa da tazo atake kuma yatuno da fuskar lubna aransa yace itace wacce naketa burin Allah yasa ke hadani da ita Alhmdllh,
Baiwar Allah ya akayi?mekike yi anan?,
Cikin Muryarta data soma dashewa tace,abubuwan buqata zan siya kuma ban fito da kudi ba don Allah kataimaka ka aramin kudin,
Amsar takardar yayi yasiya abubuwan dasauri har ya juya ya hango matar sa da mahaifiyarta suna zuwa yanayin fuskarsu yasa jikinsa yayi sanyi,
Karbi inji matar sa me suna jameela tana miqa masa babyn,
Kasa amsa yayi yatsaya yana kallonta yana marairaice fuska,
Kasani nafada maka daga ranar Dana haife maka danka ko yarka zamana dakai yakare kuma bazan taba shayar ma da itaba danhaka gatanan tafada tana ajiye babyn a kasa,
Lubna dake kallon ikon Allah tayi saurin zuwa ta dauke babyn daga kasa,
Don Allah jameela ki taimaka kishayar da ita konawa kikeso zan baki,
Batareda ta amsashiba tajuya itada uwarta dake zugata suka fice,
Kallon lubna kawai yayi yace mutafi aduba jikin mama,
Yadda yayi duk setaji tausayinsa,
Ki tsaya anan zan dubata sedai karki bari ta kwashi sanyi,
Gyada masa kai kawai tayi tana kallon babyn datayi bacci a hannunta,
Bangaren jameela kuwa a zuciyarta tana jin soyayyar yarta sosae sedai abinda mahaifiyarta tafada mata bazesa ta iya kula da yarinyar ba.
😂😂wasu Na cewa wahalar tayiwa badee yawa yakamata tafara jin dadi yanzu Dan Allah kuyi hakuri kubari yatafi yadda na tsarashi I promise u a very happy ending insha Allah har Dan luv za a tabo ammafa niban iyaba saboda banayi😜
[8/1, 11:09 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Masu karatu sekunyi hakuri dani Dan sosae nake mistake agurin sunayen yarannan danasan zasu rikitar dani haka daban saka suba amma zanyi kokarin ganin Na kiyaye nagode.
Page 29
Komai jiki asanyaye yake yinsa haryagama duba badee tayi bacci yasa akai kaita daki annex Shiga dakin yasamu lubna azaune ta Goya babyn dake bacci da alama yarinyar batada rigima,
Kawo ta nakai ta gida idan da wata matsala seki kirani,yafada yana tsaya wa bayanta Dan ta kwance zanin goyon,
Banida waya itama mama batada waya shiyasa kaga ina Neman taimako kasancewar duk yayyena basa kusa,mun gode sosae Allah yasaka da mafificin alkhairi kudin ka kaga gidan mu adaidai inda kadaukomu zuwa next week insha Allah zanyi kokarin hada maka kazo ka karba,
Kallonta kawai yake yadda take magana cike da manyance seduk yaji ta burgeshi dama tun lokacin yake rokon Allah yasa ke hada su, murmushi yai mata kafin yace zandawo zuwa anjima idan ma dasauki sosae za asallame ku,
A hanya tunani yake Waze bawa yarinyar nan reno mahaifiyar sa bata gani ga kanwarsa akwance komai se an mata ba magana sedai ido kawai larai ke kula dasu duka ayyuka sun mata yawa amma bashida yadda zeyi yanzu dole ze gwada zuwa lallashin jameela kokuma yasamu wata wacce zata kula masa da ita ,amma zeyi matukar bakin ciki idan er ta girma a hannun me Reno zefi kyau ta girma a hannun mamanta,
Huci yafitar daga bakin sa me zafi yana shafa fuskarsa da duka hannayensa bayason hayaniya kokadan segashi rayuwar sa tazo da kaddara me tarin yawa damuwa Na nema tayi masa yawa,
Bayan la’asar su hajiya suka dawo sunsamu babu kowa agidan kuma ga gidan abude basu yi tunanin komai ba suka zauna zaman jiran dawowarsu kila basu yi nisa ba,
Wasa wasa har kusan magrib basu dawoba Dan haka suka fito kofar gidan Abdul’aziz yakira abdulrahim yafada masa su lubna basa gidan a rikice yadawo,
Hajiya tashishshiga makota nakusa dasu amma sunce basu shigo ba hankalinsu yakara tashi sunanan tsaye akakira sallah danhaka suka shiga gidan suyi sallah,
Bangaren badee kuwa kusan magrib dinnan ta farka garau taji jikinta danhaka tace a sallamesu dakyar lubna ta rarrasheta tabari suyi sallah,
Mus’ab yadawo asibitin Dan yaduba jikin wayannan mutanen dabesan kosuwayeba soyake hankalinsa yakoma gu daya irin yadda hankalinnasa ya karkasu bayaso yanaso yai focusing akan damuwa daya,
Azaune yasamesu har kasa ya durkusa yagaisheda badee yamata yajiki ta amsa tana cewa, naji sauki don Allah a taimaka asallamemu mukoma gida bawanda yasan inda muke kar hankalin su yatashi,
Mama bakyajin komai ne yanzu?
Babu abinda nakeji mungode sosae Allah yabiyaka yaimaka albarka,
Ameen ya amsa yana murmushi, fita yayi babu jimawa yadawo da paper hannunta da ledar magani ahannunsa,
A kofar gidan suka sami su Abdul cirko cirko suna jimami fitowa sukayi nan lubna tai musu bayanin shine yataimake su sosae suka masa godiya daga baya sukabi badee Lubna kuma yake mata bayanin yadda badee zatasha maganin,
Har yajuya ze tafi yajiyo muryar lubna tana magana,
Yanada kyau muyi hakuri dakomai da ze riskemu a rayuwar duniya dolene ajarabcemu Dan dolene a gwada imaninmu wannan jarrabawace ta duniya idan muka cinyeta zamu ga daidai idan kaddara tazo mana semu karbeta da hannu bibbiyu mekyauce kokuma sabanin haka nalura kamar kanada damuwa kuma yau naga daya da idona ina rokon Allah daya raya babyn nan akan tafarkin addinin musulunci yakuma albarkaci rayuwar ta,duk yadda rayuwa tazo maka sekayi godiya ga Allah domin idan kaji ta wasu sekaga taka bama komai bace, idan ka koma gida ka shafa min kanta don Allah,
Takarashe maganar muryarta na rawa da alamun kuka takeso tayi,
Duk abinda hakuri be bayarba rashinsa baze bayarba,dabana hakuri dabansan iya cutukan dazasu sameni ba damuwa taimin yawa inaso tarage min kozansamu sassauci,
Ina rokon Allah daya kawo maka mafita,baka fadamin sunanka ba,
Sunana Mus’ab Muhammad Sharif, nikuma sunana lubna Abdulmajid tafada tana murmushi shima murmushin yayi kafin yai mata sallama yawuce,
Yarinyar tashiga zuciyarsa sosae dole yanemi kusanci da ita amma tayaya?
Bari nasan yadda zanyi damatsalolin gabana kafin nakama wannan tunda nasan gidansu kuma bamuda nisa sosae hankalina akwance yake kusan unguwar mu daya ma,
Bangaren majid kuwa komai ya gagareshi albashinsa se yadda tayi dashi idan anyo cinikin kasuwa da kasonta aciki ita kanta batasan iya adadin dukiyar data Tara ba,
Hajiya nifa plan dina yanzu bewuce asakomai ciwo ba ahankali Wanda zegagara yin komai se yakai stage dinda shikanshi yagaji da duniyar sena kwashi dukiyoyina nabarshi banida matsala,
Eh kuma shawarar ki tayi Dan haka kibari wani satin kizo muje dakanki ayi maganar kuma kizo dakudi sosae domin aikin yayi saurin ci,
To shikenan hajiya sekin jini,(wa’iyazubillah Allah ka kallemu da idon Rahama ameen),
Yaya asama’u ta fadawa farida yadda sukayi da safara’u yaya asama’u bamuga zamaba tashi mutafi dole munemeta muje gida a fadawa su alhaji don Allah,
Sun samu ummansu da alhaji suka zayyane musu komai atake ummansu tafashe da kuka,
Dama irin wannan ranar nake so tazo….
Masoya littafin matsayina anty billy tace nabaku hakuri dajinta shiru kwana biyu insha Allah gobe ko jibi zakuji ta,mun gode ❤
[8/2, 5:05 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
Na
SophieG
A very heart touching story 2017
Idan nabaku wannan shafin banyi laifi ba haka kawai na tuna da abubuwa dayawa nasan kuma zaku tuna kuma zaku gane me nake nufi,Ummeejay,Ummeekay,zeenasir,bellzahra,husaena ubandiya(in-law),ummi rilwan(matar big bro),Sha’awa,dizuwa and fatima (matar nu’aym)pls let’s reunite😍😭.
Page 30
Na dade inajiran wannan ranar,ranar dazaku zo kuna kukan rashin er uwarku nayi tunanin kunada hankali sena iske sabanin haka,
Tajuya kallonta gun alhaji,
Alhaji badee’a er kace kanada damar yanke mata hukunci akan kowane laifi amma wannan yayi tsauri,kayan ke mata hukuncin rabata da duka en uwanta batareda kayi tunanin wane hali ni uwarta zan shiga ba fiye da shekara ashirin bansata a idona ba kuma nayi shiru ban maka zancen ba kaima ka yimin shiru,
Asama’u kekikafi kowa shaquwa da Badee amma wannan karon kika rufe idonki kika watsar da ita kukan me kikeyi yanzu?,
Farida kekika yiwa badee rashin mutunci harkikeda bakin zuwa kina fada to yanzu bakin cikin me kike?,
Dukanku kunada aure kuma kunason mazajenku meyasa kuke so ita tabaro mijinta awaccen lokacin anya kuwa kunsan darajar soyayya?kukasan metake angowa idan tarabuda mijinta? Babu wani yanayi na rayuwar duniya dayaze dawwama farinciki ne kokuma sabanin haka,kunsan zafin haihuwa kunsan zafin rabuwa da yayaye to akan me zakuga laifinta Dan taki baro yayanta tabiyo ku?gunwa kukeso tabaro su hajiyar Abdul wacce batabawa dancikinta tarbiya mekyauba balle Dan wani?,
To daga yau kar Wanda yasake kulani acikin Ku harse kunganomin yata kuma Ku tabbatar da tana cikin yanayi me kyau harkai alhaji domin Kaine silar komai dakaida mukhtar da tsoron cikin ta tazo amma ya kwada mata mari yakoreta itada gidan ubanta,
Daki tashige tabar su jiki amace Shiru sukayi suna hango girman laifinsu gashi uwarsu tayi fushi dasu ahaka suka bar gidan,alhaji ma yadade jikinsa asanyaye matar sa bata taba daga muryarta akansa ba segashi yau tana fada masa magana kanta a tsaye dole yatafi Neman yarsa me cike da hakuri da kawaici,
mukhtar ma dayaji labarin abinda ummansu tace hankalinsa yatashi yayi yawon gidan majid har yagaji amma bayasamunsa a gida,a haka suka shafe sati biyu babu wani labari,
Bayan sallah la’asar lubna tafito domin siyan kayan Dinki sedai me shagon dake layinsu baya nan danhaka ta karasa layin dake gaba dasu kadan kamar ranar dazasuzo taga shagon da ake siyarda kayan dinki,
Tundaga nesa alhaji ya hango ta yana tsaye a kofar gidan abin duniya ya isheshi sosae yake kallonta wallahi wannan yarinyar kamarta da asama’u ta shahara badan asama’u tazama babbar maceba babu abinda zehana shi cewa itace kuma yayan asama’u babu wacce takamo hanyar haskefatar wannan yarinyar, koda yawo daga tunani beganta ba,to kodai aljanace?
A a wannan mutunce yaba kanshi amsa, tabar ma yashimfida ko Allah zesa tasake biyowa,
Lubna data siyo abinda zata siyo takamo hanyar komawa gida seji tayi an rungumeta tabaya,dasauri tajuya cikeda tsoro waye Wannan,
Ramla kawarta tagani batasan lokacin datace,wayyo dadi kashe ni ramla yaushe kuka dawo?
Aimunjima da dawowa naje gidanku akace kuntashi daga nan ina kuka koma ne?
Wancen Layin nasama,
Gidan hajiyarku kenan?kicema muna kusa muma nan muka dawo sedai mu daga farkon layin muke,
Dadi yakama lubna bakinta yaki ruhuwa se ganin sukayi mota ta tsaya gefen su,
Ahh yaya Mus’ab daga ina haka?,
Daga gida mana ga gidanmu can,yaimata nuni dawani gida mekyau irin gidan masuji da naira,
Allah sarki,
Mekikazo yi anan?,
Kayan Dinki nazo siya sekuma na hadu da kawata muka bige da hira,
OK muje nasaukeki gida dama inaso naga jikin mama,
Aitaji sauki sosae,Baku gaisa da kwataba sunanta ramla,
Gaisawa sukayi kafin su shiga motar ramla suka fara kaiwa gida kafin sukarasa gidansu lubna,
Har cikin gidan takaishi yagaisa da sumama da hajiya yadan zauna kafin yai musu sallama lubna tarako shi dama tanaso ta tambayeshi,
Ina fatan mahaifiyar baby ta dawo?,
Bata dawoba na buga dambu taliya taki dawowa so nakarbi wannan kaddarar ahaka akayi suna bawani taro yanzu ina fafutukar Neman me reno nakasa samu,
Subhuhanallahi tace sekuma tayi shiru kafin tayi saurin juyawa cikin gida tana fadin ina zuwa,
Paper ta samu da Biro takawomai,
Samun numbernka anjima zan kiraka yanzu inada aiki akaina kuma gobe nakeso nagama idan yaya yadawo zan ari wayarsa nakiraka,
Murmushin jin dadi yayi asaukake yasamu yadda zekusanto kansa da ita, rubuta mata yayi kafin yamata sallama,
Tana Dinki tanabawa mamanta da abdulrahim labarin Mus’ab seda takai gun datake son fada musu buqatarta ta ajiye dinkin ta fuskance su,
Mama na fada miki duk Wanda yakeso yaga bacin raina yatabaki zannunamasa halina koshi wanene haka kuma duk Wanda ya farantamiki nikuma da izinin Allah sena taimakeshi sedai in abin yafi karfina,sosae nake tausayawa bawan Allahn nan matar sa tabar mai jin jira kutaima kubani izinin zuwa tun safe zuwa yamma nai masa renon yarinyar nan don Allah,
Ajiyar zuciya abdulrahim yasauke yace,lubna bawai naki ta taki bane domin yana bukatar taimakon sedai kisani ke macece bekamata abarki asakeba kullum kina hanya and haka kawai bakomai a tsakaninku bazamu barki kije gidansa ki zauna ba dama dai ace zeringa kawo yarinyar ne da bazamuki ba,
Yaya mahaifiyarsa da kanwarsa nanan fa kuma sunada me aiki sedai abubuwa sun mata yawa kuma idan kalura shikanshi damuwa ta lullubeshi,
Akwai haka kuma seki tambayeshi idan ya yadda,
Yawwa yaya nagode sosae Allah yataimake mu,
Ameen kawai yace yana fita daga dakin,
Wai mutuminnan kodai sonki yake lubna?inji badee,
Lahhh mama rufani kisayani,kedaganin wannan mutumin kinsan yafi karfi na kawai dai yanada kirki ne,
Badeee kallonta kawai take tana murmushi.
Banan yakamata na tsaya ba amma wallahi nagaji😩❤.
[8/5, 2:52 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Anty Sophie yauba y’ay’ana?
Anty Sophie y’ay’ana shiru kwana biyu,
Anty Sophie munajira fa😀
Baby Sophie ina badee?
Baby Sophie muna missing lubna fa
Anty Sophie nifa inajira naga yadda safara’u zatayi da majid.
Duk wacce tasan tace haka to su suka sakani typing yau sbd haka wannan shafin nasune sukadai😍 anty Sophie, baby Sophie nagodiya😘.
Page 31
Tundaga sallamarta yagano itace domin sosae muryarta sosae take San yaya zuciyarsa amsawa yayi yana gyara zamansa bayan sun gaisa tace,
Am yaya majid dama nace zancen wacce zatayi renon baby ne shine nace idan ba asamu ba kuma babu damuwa insha Allah zanyi,
Jin zancen yayi daga sama Dan haka yayi saurin miqewa yana cewa gani nan zuwa,
A’a tsaya mana yanzu dare yayi amma idan ka amince gobe ma zan fara zuwa kuma bawai zaka biyani bane kawai zanyi ne saboda Allah sanadin taimakon dakayimin nida mahaifiyata,
Wani dadi yakeji sosae magana ma kasa yi yayi sedai jitayi kawai yace alhmdllh,
Yaya kayi shiru ko akwai Matsala ne?,
Dasauri yace A’a wallahi babu komai na gode sosae gobe dakai na zanzo nadaukeki,
To Allah yakaimu amma baka fadamin sunan y’ar tawaba,
Murmushi me sauti yayi yace sunanta Fatima amma dai ninafi kiranta da baby,
To Allah yaraya mana baby Fatima ameen yace kafin sukayi sallama,
Dagudu takoma dakin su tasamu badee nagoge mata kayan da tadinka dazu dama haka suke sesun goge Dan dinkin zefi kwanta wa yayi kyau,
Mama yaya Mus’ab ya yadda kuma yace dakansa zezo yadauke ni sedai mama zaki bimu kiga gidan?
Meyakaini ni badeeyatu Allah dai ya kiyaye insha Allah baze cutar dake ba,
Mama don Allah kibini muje kiga gdn zakuma gaisa da mamansa kinji,
Ganin ta marairaice fuska yasa badee tace to shikenan amma bazan zauna ba dawowa zanyi, aidama mama bazaki zauna ba,
To Allah yakaimu lubna se kije ki karasawa indo dinkin ta Dan yanzu dinkin zesami gibi tunda bakya zama,
Wallahi kuwa mama ai hannu yarage kawai nasa se zip gara na kashe darennan nadinka mata kayanta naji anacewa batada mutunci kar tazo tayimin RM(inji anty badee) wallahi na gurji bakin yarinya,
Bazama tayi miki ba Dan naga alamar ke Sam bakya gudun fitina,
Shiru tayi tana cigaba da dinkinta,
Washe gari karfe 8:15 am a gidan tayiwa majid sbd zumudi ganinma yayi Daren yai masa tsayi har cikin gidan yashiga shi dai yana jinjina tsaftar su,
Yaya nace zamuje da mamana su gaisa ta hajiyarka kuma zataga gidan,
Babu damuwa yace yana murmushi,
Ta kofar gidan su badee aka bi kasancewar layinsu daya sedai akwai Dan nisa a tsakanin gdnsu Dana su Mus’ab,
Sosae badee ta kurawa kofar gidan ido Sega alhaji yafito yana shimfida tabarma, sosae take kallon sa yananan yadda yake sedai alamun tsufa ya bayyana sosae ajikin sa ai dole ya kwana biyu,
Alhaji kuma zaman cikin gidan baya masa dadi Dan ummansu badee bata wani kula shi iyakacinta da shi gaisuwa se gabatar masa da abinci ko magana yaimata a daqile take amsa shi abin yadameshi yarasa hanyar samun badee se addua yake,
Tunda suka shiga gidan tsikar jikin lubna ke tashi tana jin hankalinta na miqewa daurewa kawai take har suka shiga palon gidan yai musu iso dakin hajiya,
Dasauri lubna tai baya danji tai kanta ya masifar sarawa,badee tayi saurin kallon ta,
Lubna meye haka?
Mama bazan iya shiga dakin nan ba,
Mus’ab yai saurin dawowa da baya yace,
Meyasa?
Yaya Mus’ab kayi hakuri Ku bincika dakinnan ina Palo inajiranku,
Kallon badee yayi yace,
Mama kokingane me take nufi?
Um…tanada matsalar iskane idan kaga tayi haka to taji a jikinta akwai abinda ya shafi asiri,tsibbo,da sihiri nagane haka ne tun tana karama hankalinta baya taba kwanciya a wurin ina baka shawarar kanemo mataimaka aduba dakin nan dagidannan dakyau,
Mutuwar tsaye yayi yana tunani to su Waze musu wani asiri agidn kuma wa suka tsarewa wani abu?shi sema yanzu yake tuno abubuwa da dama,
Mama bari nakira larai tadawo da hajiya Palo zan dauko safna megadi ya tayani muduba hankalina yatashi,
Babu matsala tace tana juyawa,
Sunanan zaune Sega larai riqeda hannun hajiya takuma goyo baby dasauri lubna takarasa ta na karbar baby bayan sun zauna suka shiga gaisawa da hajiya dama tasan da zuwansu,
Kukane ya kwacewa lubna ganin kyakkyawar budurwa akwance komai se an mata babu baki bakafa balle hannu se idanu kawai tana kallon mutane, Allah sarki batasan hawaba batasan sauka ba ankwantar da ita haqiqa duk yadda kake ganin rayuwar ka tayi tsanani ka godewa Allah domin akwai wayanda tasu tafi taka wuya da wahala,
Goya babyn tayi daketa bacci dayake batada rigima kokadan, zuwa tai tana kallon safna taimata murmushi tace sannunki,gyada mata kai kawai safna tayi tana kura mata ido,
Hajiya tace maman lubna mungode sosae Allah yabiyaki da gidan aljanna Mus’ab yamin bayanin komai mungode,
Babu komai hajiya muma godiyar mukazo yi,murmushi kawai hajiyar tayi,
Mus’ab yazo da wasu maza su biyu zasu shiga dakin hajiyar lubna tace,
Kufara binciken tun a bakin kofa idan takama har tile din dakin a bambare baruwanku da gado ko wardrobe naji a jikina wannan abin yajima adakin gadon kuma bazefi shekara biyu ko ukuba,
Ya jinjina wahalar dazasuyi Dan tile din bana yanzu bane sesun sha wahalar daga shi,
Katifar suka soma dagawa suka cire komai najikin gadon basuga alamar komai ba secan idon Mus’ab ya sauka kan wani tile dabe zauna sosae kamar sauran ba seya tuna lokacin da za adaura gadon,
Ranka yadade ga wani tile mun gani be zauna sosae ba kuma munfara Daura gadon,
Musbahu tile din akasan gadon yake?
Eh,
To indai kun fara aikin kubarshi kawai baze zama matsala ba tunda akasan gadone,
Dasauri yakarasa ya daga tile din wani kalar Abu yagani kamar randar ruwa er karama bakikirin ga takarda a jikinta andaura da zare bismillah yayi yadauko tafito palon yana cewa mazn suci gaba da dubawa,
Kuga abinda naciro yace yana nunawa badee dasauri tamiqe takarba sukayi waje Dan tasan idan lubna ta gani birkicewa zatayi.
Washhh anty Sophie tagaji😰
[8/5, 3:45 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 32
Mus’ab menene Ku fadamin kuna ina tana kokarin tashi larai tayi saurin maidata zaune hajiya ki zauna suna zuwa kinji babu komai, wannan larai tamusu halacci batada matsala kuma tana tausaya musu,
Suna zuwa waje badee tai bisimilla hadi da adduar neman tsari daga muggayen aljanu da mutane,
Papern jiki tasoma cirewa ta bude rubutu ne na Hausa anyishi kasa sama dakyar ta iya hada kalmomin makaranta
Sunan wata tagani arubuce da manyan haruffa ankuma bada yadda za akarya asirin ta hanyar kona wayannan abubuwan idan wacce akayi wa ta chanja ra’ayinta na kar yawa,
Tana gama karantawa Mus’ab yai saurin zuwa yadauki fetur da ashana suka kona abin seda yazama toka kafin suka koma cikin gidan,
Muryan Hajiya sukaji Tana cewa innalillahi wa inna ilaihirraji’un larai haske nake gani suna shiga tana faduwa asume,
Dasauri sukayi kanta badee tace mus’abu kakira wani malamin idan akwai shi nan kusa atake ya kirashi kasancewar basuda nisa segashi yazo cikin mintuna a shirin,
Addua yai mata sosae sekuma bacci yadauketa yace abarta tahuta kafin yatafi suka bashi lbrn yadda akayi yajinjina al’amarin sunanan en mazannan biyu suka fito megadi yace,
Alhaji mun matso wardrobe gaba sedai munga alamar anfasa gini dasauri ya dauki hammer suka shiga dakin daidai wurin yafasa Sega laya guda biyu sun fado,
Dauka yayi da bismillah yafito palo yanuna musu atake malam yace akona a palon yadora kan tile yasa kero da ashana yakona,
Seji sukayi safna tace maaama😳,
Kuka kawai Mus’ab yasa wato duk wannan wahalar da mahaifiyarsa da kanwarsa keyi fiyeda shekaru goma Ashe wanine yakunsa musu Ashe haduwarsa da lubna alkhairi ce atake yaji wani sonta yakaru azuciyarsa,
Juyawa yayi yana kallonta daniyyar yimata murmushi seya ganta a dunkule ko motsi batayi, dasauri yayi gunta hakan yajanyo hankalin su malam yakoma gunsu,
Badee takarasa tadaga zaune se ganin jini tayi yana fita ta hancinta innalillahi wa’inna ilaihirraji’un tafurta, batason ganin nose bleeding dinnan Dan yanzu setajiyawa kanta ciwo,
Bayani taiwa malam ganin alamun kansa yakulle ruwa yace abashi a Kofi yai Addis aciki dakansa ya matse bakin yadura mata ahankali jikinta yafara saki se sauke ajiyar zuciya take,
Alhmdllh bayan kwana biyu lubna na zuwa gidan yanzuma ita kewa baby wanka larai takoya mata kuma hajiya tadan soma gani ba sosae ba safna ma tafara zama sedai bata jimawa azaunen kuma bata magana sosae amma duk malam ya basu magani suna sha dakuma addu’o’i majid yarasa inda ze Dora lubna sbd shukin sonta daya kamashi ga son babyn sa datake sosae take kula da ita yauma yaji dadi sosae yaga ta dinkawa baby riguna guda biyu sunyi kyau ta gwada mata se surutu take mata kamar Tana gane me take cewa yarinyar ko se dariya take kwasa,
Adakin hajiya suke zaune suna hira hajiya tana jinjina wannan lamarin,
Lubna tai murmushi tace nifa Momy Sam bana mamakin wannan abin naga abubuwa da dama arayuwata masu kamada wannan babana yakasance mutum Wanda bayason haihuwa dukda wadatarda Allah yaimasa ya watsar damu bamusan meye kulawa daga bangaren uba ba muntaso cikin tagayyarar rayuwa mamanmu itace komai namu se mahaifiyar babanmu dake taimaka mata daga baya kuma ya auro wata er uwarsa daganan komai yakara lalacewa bin malamai dabokaye take tanaso ta hallakamu muda babanmu mudai Allah ykaremu sbd munriqeshi kuma mundogara dashi sedai babanmu tasamu sa’arshi be riqe ibada kamar yadda yariqe Neman kudiba yanada dukiyar dabesan adadin ta ba akowace kasuwa dake garin nan yanada shaguna akalla biyar ko shida ana haka yakawomin miji mugun miji Wanda yakasance shedani Na karshe munyi kokarin ganin hakan bata kasanceba amma abin yacitura se kawai muka hada kayanmu mukabar gidan yanzu haka muna gidan hajiyarsa kuma har yau betaba zuwa nemanmu ba muma bamu koma Neman sa ba,
Sosae Momy ta tausaya musu tace yanzu haka kuka baroshi da muguwar mata idan ta kassarashi fa?
Komai tayimai Momy shiyaso yawulakanta mu fiye da zato bezo nemnanmu ba muna bazamu nemeshi ba,
Kiyi shiru kawai lubna ke yarinya ce,safna dake gefe tana saurarensu tayi dariya da muryarta slow slow tace Momy kibarta su sukasan rayuwar dasuka yi dashi, kiyi shiru kema safna bakisan komai na rayuwa ba,murmushi kawai tayi bata saba magana me tsayiba wannan datayi setaji duk ta gaji,
Ke nifa Momy Allah kadai yasan iya adadin bala’in da matar nan ke kullawa dayanzu kila ta kassaramu,
Tafada tan dariya suma dariyar sukayi,
Yauma suna zaune a Palo suna hutawa Dan lubna Goya baby tayi sukaje motsa jiki da safna dan tafara tafiya,
Mus’ab yashigo yabasu wayoyi masu kyau kirar Gioni A1 safna se murna take lubna kam sake baki tayi ina ita INA Wannan zankadediyar wayar daurewa tayi taimasa godiya tace to aini yaya bansan yadda zanyi dawayar ba ko kira ban iyayiba,
Zama yai yadan koya mata masu sauki yace takoyawa safna fita zeyi,aiko tasamu abinyi baby tasha pics ba adadi,
Bari mu leqa majid,
Kwance nasameshi yana ko bayida lpy ne oho,
Safara’u kinsan dai ina bukatarki ko dakinacewa sena baki kudi yanzu kuma kona baki kudin bakya karba kitaimakeni karna mutu kinsabamun da abinnan karki gujeni yanzu pls,
Kallon uku saura kwata taimasa tace kaikam ka boni da jaraba namiji kullum cikin buqata sekace doki?kaibaka gajiyane?nikam wallahi nagaji bakada lpynma sekayi jaraba?tobari kaji inada abinyi yau basussukan danake bi zanje karbowa kuma kila bazan dawo yauba Dan daganan har kebbi da zamfara zani ban kuma CE ga ranar dazan dawoba sedai kawai kaganni,
Shiru yayi yana kallonta taja mayafinta taita tafiya,
Ahankali hawaye ke zubo masa kila wani bala’i ne ke shirin samun sa sbd jiyake kafafuwnsa duk sun soma sakewa ga wani nayi da qirjinsa yaimasa,badee ce tazo masa arai dasauri yatashi zaune sauri sauri yashirya yazari key din mota,
Hanyar gdn hajiya yakama amma ga mamkinsa akasuwa ya gakansa se kawai yasamu wuri yai parking yadafe kansa da yai masa nauyi da hannayensa.
Nidai INA bayan safara’u yadda takecin uban majid yamin daidai😎
[8/7, 5:31 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you anty billy❤
Page 33
Mama kiyimana addua Allah yasa ayi nasar samun aikin nan kinsan Dan tsohon governor din garin nan muna mutunci sosae yanzu da muka gama service yace mukawo takardunmu nida abduljabbar insha Allah babansa zesama mana aiki,abdulrahim yafada yana murmushi,
Tun yaushe Abdul?shine bansaniba seyau?,
Jiyanefa nabashi nazata abduljabbar ya fada miki,
A a nikam,Allah yatabbatar mana da alkhairi,
Ameen ya amsa yana miqewa,
Bari na dubo lubna lafiya har yanzu bata dawo ba akwai mamaki Dan bata saba kaiwa hakan ba,
Daka kyauta kuwa amma kada kayi mamakin tana tareda majnun dinta ne?
Tsayawa yayi yana cewa,wa kenan?,
Mus’ab mana aini tuni naganosu inata so nafada maka kasata agaba ta fada ma gaskiya amma bansamu lokaci ba,
Ummm lallai ma lubnar nan nita maida bi can kenan?,nafa tambayeta Dan kar afara surutu tace min itafa bakomai mutunci kawai suke dashi haka takejinsa kamar ni,
Hmm yanzu kam asiri yatonu seka fadamata ka gano Dan asan abinyi,
Lallai kam yace yana fita,
Dakafa yataka yazo daidai gidansu badee ya hango ta goye da baby da waya akunnenta Mus’ab na gefenta yayinda safna ke tafiya daga gefe ita kadai,
Ke gani nazo gidanku bakya nan,wai ke bakyajin kunya kinje kin tare a gidansu saurayi?,inji ramla da wannan shine zuwanta nabiyu gdnsu lubna amma batanan,
Dariya lubna tayi tana kallon Mus’ab da shima ita yake kallo bakin nan kamar me tallar Maclean,
Eh din ai gidanmu ne,meye kike nemana?,
Hajjaju Dinki nakawo miki kuma express ne,
Wazaki kawowa Dinki express?,
Ke dalla banason iskanci gasunan nabarwa mama anjima zan dawo bikin kanwar mijina za ayi shine seyau yakawomin kayan danya raina ni,
To masifatu naji sekinzo, bata jira ta amsaba ta katse wayar Dan ganin abdulrahim ya iso kusa dasu,
Bayan sun gaisa da Mus’ab yace wannan kanwar tamu nafito dubawa ganin bata saba kaiwa warhaka bata dawowa,
Gaskiya kam,wallahi baby ce batajin dadi taki yadda dakowa sekuka take yanzu ma nace don Allah tatafi da ita har taji sauki,
Aiba komai danan dacan duk dayan….
Juyowa yai jin ana gaidashi safna yagani,
Ahh kanwar mu ansamu sauki kenan harda yawo?,
Murmushi kawai tayi tajuya, shima murmushi yayi yana cewa seku koma ko kar dare yayi tunda gani ma karasa gidan tare,
To shikenan inji Mus’ab yaiwa lubna sallama yanaji kamar karsu rabu itama haka take ji amma bayadda za suyi (bansan yaushe wannan luv ya kullu har yakai wannan stage din ba)
Salamu alaikum
Wa’alaikumussalam abdulrahim ya amsa yana kallon tsohonnan dake tsaye idonsa yayi ja sosae ga hawaye kwance acikin idon sa,
Dan Allah idan babu damuwa zanso kuzo mukarasa gidana inason zanyi magana daku ne don Allah badon halina ba,
Abdulrahim yakalli Mus’ab dabasu Riga sun tafiba,alama yaimasa dakai subi tsohon,
Har tsakar gida yakaisu amma kowa bakinsa dauke da addua akan tabarma suka zauna,
Na Dade ina ganin wannan tana wucewa tanan sosae jikina kebani ita jini nace amma saboda girman laifina yasa banida karfin halin tunkararta naimata magana seyau Dana ganku atare nakasa jure abinda nakeji don Allah Kuyafe min Ku nunamin mahaifiyarku inaso naganta kafin nabar duniya,
Dukansu baki asake suke kallonsa meye hujjarsa idan sudin jininsa ne amma ita lubna tagane meyake nufi sedai tayi shiru tanaso taji yafada da bakinsa,
Nasan kanku ya daureko?,
Insha Allah Ku yayan badee’a ne idan banyi kuskureba Kaine abduljabbar ko kuma abdulrahim saboda kune manya a yayanta wannan kuma naji labari sunanta lubna kece karama acikinsu naganeki ne saboda tsakanin kama dakike yi da yayar mahaifiyarki asama’u,
Arayuwata bantaba ganin mutun me zurfin ciki ba irin maman mu, Ashe muna kusa da iyayenta bata taba nuna mana ba Dan tasan zamu iya zuwa,
Dasauri umma ta fito daga daki tana kallonsu karasawa tai kusada lubna tana shafa fuskarta se hawaye tarasa Na menene na bakincin rasa yarta datayine duk wannan shekarun kokuma na farin cikin ganin jikokanta ne dakuma jiyo kamshin erta dake kokarin kusantota,
Ganin hawaye afuskar umma yasa bade yin murmushi ta juya tana kallon su Abdul,
Yaya kuganemin wannan tsohuwar wai kuka take,tafada tana murmushi kafin tajuya gun alhaji tace,
Dan tsoho angona mekake bawa kishiya ta ne datake da hawaye a idonta har yanzu?
Basusan lokacin da dariya ta subuce musu ba, da alama jikar tasu me barkwanci ce,
Abdulrahim yace kunaso mukawo muku itane kokuma zakuje dakanku Ku ganta,
Eh kuje kukawo mana ita inji umma,
Dasauri lubna tace a’a yaya baza ayi haka ba zamu kasan mama Nada ciwon zuciya so zamu bita a hankaline,
Alhaji mamana ta cemin bazata taba nemankuba indai kuna sonta dolene Ku nemeta dakanku danhaka inaga Ku fara tura yayyen nata da kannenta su gwada lallashinta I’d an ta sauko dakanta zatazo da ganku amma fa kunada aiki ja agabanku kunsan ance wanda baya fushi duk ranar dayayi to saukar sa abune me wahala,
Abdulrahim ya akayi kanwar ka tafika wayo?inji umma,
Tadai fini sanin halin mama ne,
Dariya sukayi suduka kafin suyi musu sallama Dan magriba ta gabato,
Ranar umma kasa bacci tayi saboda murna itada Allah bayan er tsohuwar soyayyar su sukayi nafila domin nuna godiya da jin dadi ga Allah.
Naso ganin yadda tsofaffi ke soyayya🤣🤣🤣nikadai Dana fadi abin senaji shi bambarakwai🏃🏻♀🤣
[8/9, 1:30 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Sadaukarwa ga daukacin masoyana fatan alkhairi agareku Allah yabar soda kauna❤
Page 34
Alhmdllh abdulrahim yasamu aiki shida abduljabbar, abdulrahim a federal inland revenue shida abokinnasa dayai masa hanya abduljabbar kuwa abangaren health ne,(👃🏻najiyo kamshin yarannan zasu zama young billionaires),
Ranar jumu’a ne da sassafe aka turo masa ta email Abduljabbar se Monday nasa yashigo sunyi murna kamar zasu zuba ruwa akasa susha se hamdala suke,
Aranar kuma 10:00 am tana zaune itada lubna da baby dake zaune tanata wasanta,
Lubna shikenan kin karbe musu yarinya?nifa banason shishshigi Dan kinga sun sake damu haka sosae zaki kwaso musu yarinya kwana da kwanaki kinsanfa halin mutane balle ma babu dangin iya babu na baba,
Mama ki kwantar da hankalinki sunada kirki sosae kuma nifa bani nace zanzo da itaba itace ta maqale min babanta yace nazo da ita kuma tausayinta nakeji karma dai idan natuna yadda uwarta ta ajiye ta akasa cikin asibiti ko sau daya batasan dumin jikin uwarta ba,
Um Allah yakyauta bari intashi yau dambu nakeson ci,
Nikuma drinks zansiyo yau baki zanyi kawayena zasu zo tafada tana murmushi kafin tasaka hijab ta dauki baby,
Ke kam ina kikaga kawayen?,
Sababbi nayi umma idan sunzo zaki gansu,daganan tafice tasiyo su exotic da five alive,
Su mama da hajiya anbaje an zubo dambu dayaji zogale se tururi yake kowa da plate dinsa hajiya se afawa ake ana yabon dan danonsa,
Badee dai se murmushi take batace komaiba, sallama sukajiyo daga waje hajiya ta amsa tanacewa kosuwaye sukaraso gamunan,
Da sauri badee tamiqe hawaye cike da idonta tama kasa magana,da sassarfa suka karasa gabanta sekuma suka zube akasa suna kuka kamar ransu ze fita dakyar asama’u tayi karfin halin riqo hannunta,
Badee’a bamuda bakin rokon ki amma kisani mun gane kuskuren mu don Allah kiyi hakuri kitausaya mana,
Farida ta karbe, yaya badee kikarbi tubanmu Dan Allah da darajar umma munyi ta Neman ki gdnki munje babu adadi amma bakya nan kuma bama ganin mijinki umma tayi fushi samu ko kallon mu batayi dagamu har alhaji,
Shiru tayi tana hawaye to ita me zatayi da kin amin cewa dasu bayan Allah ne amshi adduarta wannan abin farincikine agurin ta en uwanta gatanta sun dawo gareta atake taji 70% na damuwarta yakau,
Jin tayi shiru kusan minti biyar yasa yaya asama’u miqewa tace,nasan abune me wahala kiyafe mana da wuri amma munbaki lkc kiyi tunani kuma bazamu ga laifin ba domin laifin mu me girmane,
Ganin sunjuya yasa tayi azamar janyosu ta rungumesu ta saki wani kuka me sauti tana cewa,
Yaya bakuda laifi nice me babban laifi kunnuna minso kunso kufitar dani acikin wahalar rayuwa Amma so yarufe min ido nayi babban kuskure wahalar Dana sha bansan dame zan kwatantamuku ba bamusan meye dadin rayuwaba har seda takai ga mun gudu daga gidan,yaya Allah ne ya karbi addua ta yadawo min daku yadawo min da gatana yaza ayi na butulce masa,
Lubna dake jikin kofa tana kallon su tasulale kasa tana murmushi hawaye na zuba daga idonta tanajin wani sanyi na ratsata babu abinda yafiye mata ganin farincikin mahaifiyarta,
Badee yaya mukhtar na waje fa tare mukazo,
Ku shigo dashi mana kunbarshi Awaje,
Kai atakaicedai ranar ta shirya da en uwanta suka ringa neman gafararta aka kawo musu abinci da lemu sukaci se santi suke har yaya mukhtar daya zama magidanci dole yasaki jikinsa amma sosae yake kallon badee tarame sedan haske datayi dama ita ba fara bace sosae amma ba baka bace,
Su abdulrahim duk sundawo suka iske abin farinciki, yaya asama’u tace duk kuzo nizan fada muku sunayenku domin kowannenku nasan fuskarsa,
Sosae sukayi mamakin ganin batayi kuskure wurin fadar sunayen suba tazo kan lubna tace kekuma kanwar maza ke photo copy nace sak dukda bantaba ganinkiba amma nasan sunki kece lubna,
Dasauri lubna tafada jikinta tana dariya harda hawayen jin dadi tace dama haka dangi suke?
Ranar da qafa suka taka har gidansu badee,
Ummansu ta rungumeta tana kukan farinciki daganan komai yawuce se kallon gidan badee take komai ya sauya yasha fenti da tile ko ina se kyalli yake kamar gidan wata amarya,
Bari na Dan leqo majid,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un nafada ina ja dabaya ganin mutum yashe akan gado yarame kamar Wanda tunda aka haifeshi yake asibiti kai kamarma an tonoshi daga rami bayako motsi se ido dake yawo se wari yake ga jikinsa babu alamar yaji ciwo balle nace ciwon ne sanadin warin,
Inanan ina sharar kwalla Sega hajiya safara’u se kamshi take tashigo dakin,
Yabude bakinsa zeyi magana kawai se jini kamar yana amai kusan sau uku yana attempting yai magana amma jini dake fita ya hanashi,
Hehehe,waikai baka gajiya da magana ne sokake jinin ka yakare? To zuwa nai namaka wanka domin warinnan naka yana takurani,
Gani nayi ta saka hand gloves tajanyoshi kasa kafin ta karkatashi ta kwantar dashi kasa tajashi har tsakar gida tacire zanin gadon tabayar akai shara se kuma tajona tiyo jikin famfo takunna kamar me wankin mota haka taringa fesamai ruwa numfashinsa nayin samasama,
Kayan jikinsa tacire tabi jikinsa daruwan kafin ta sakamai jallabiya tamaida shi daki bayan tasa inno me aikin ta tagyara dakin.
Kuka sosae nake majid yazaama abin tausayi kamar bashiba gashinan awulakance😭😭😭
A birthday isn’t complete without wishes.here is mine for a scintillating year ahead,happy birthday meena parrot.
Page 35
Gidan su badee a cike yake kamar ana wani biki koda na leka yayan gidan ne suduka da jikokai se murna suke lubna na tsakiyar cousins dinta harda masu aure wayanda suka girmeta se sauran sa’annin da yayansu wani sanyi takeji a ranta,
Abduljabbar kam idonsa nakan juwairiyya diyar yaya asama’u itama da naga alamar taga saurayi me kyau daji da gayu daganandai naga yaimata signal sun fita wajen gidan,
Badeee kuwa bacci take irin Wanda harta manta rabonta da shi akan gadon ummansu su Fareeda ko se gadin ta suke lokaci zuwa lokaci umma ke leqowa kutasheta taci abinci farida tace umma kibarta harta tashi daga ganin baccin yaimata dadi,yanzuma zuwa tai taga anyi azahar bata tashiba tasameta azaune tana murmushi su asama’u na mata tsiyar wai tazo sha nono gun umma shine ta bige da Bacci, miqewa kawai tayi tsaye tace muyi sallah mana yunwa nakeji,
Muryar umma sukajiyo tana cewa yawwa dama kenazo natayar wannan bacci haka kuma bakici abinci ba sunhana natashe ki,
Ai umma yanzu natashi sallah zamuyi muci abinci,
Bayan sungama cin abinci suka hallara a palon alhaji yakara bawa badee hakuri sosae daga nan tabasu lbrn rayuwar da sukayi,
Se palon yakoma kamar gidan mutuwa sbd kowa kuka yake se alhaji kadai dayake kallonsu yana murmushi ganin yadda suka rungume juna suna kuka,
To kuyi shiru haka tausayin ya isa tunda gasunan da rai da lpy,
Abduljabbar yace Dan Tsoho don Allah naga amaryar ka kuma ta kwanta min arai ko zaka bani?,
Juwairiya datasan ita yake nufi dagudu ta fita daga palon suka bita da kallo suna dariya,
Abdulrahim ya harareshi yace waikai meyasa bakada kunya ne shikenan daga ganin yarinya,
Badee tace baruwanka kabar min y’ay’ana aini abin farin cikina ne wannan hadin zan hada kuma zeyi kyau,
Yaya mukhtar yai murmushi yace kai abdulrahim dawonan kusa daani inma kanada wacce kakeso ka fadamin ko yar sarkin garin nan ce se inda karfina yakare,
Yana Sosa keya yace dama kanwar mijin lubna ce,
Dukansu suka maida dubansu ga lubna data zaro ido tana dafe kirji,
Yaya asama’u tace yaushe kuka aurar min da y’a ban saniba?,
Lubna tace bafa gaskiya ya fadaba,
Badee tace amma dai kinsan nasan soyayya kuke keda Mus’ab ko?,
Dagudu tafita tana cewa kai mama nidai bance haka ba,
Farida tace to ni wa kuka barmin duk kun kwashe y’ay’an,
Kamar hadin baki abdulkadir da Abdul’aziz suka karasa kusa da ita suna cewa gani mama,
Dariya tayi tace kinga nasamu twins dina ko?,
Alhaji yace to Ku tashi kubani wuri inhuta,
Lubna tana daki zaune itada juwairiyya,laila diyar farida,da jalila kusan dukansu sa’anni ne se rahama dake gefe tana fama da tsohon ciki haihuwa tabiyu kenan zatayi wayar lubna tayi kara tana dubawa taga Mus’ab ne dasauri ta daga,
Baban baby ya akayi?,
Tambaya ta ma kike yau tunda kin hadu da en uwanki shikenan kin manta da miji kuma,
Ni na isa in manta da Rabin raina?kana raina kawai dai tundazu muna tare ne kasan dole hankalina yadauku kayi hakuri kaji habibi,
Rahama tadan tabo lubna,to rasa kunya seki bawa kanki excuse ko kifita can waje in kinga dama ma daga soyayyar seki soye,
Miqewa kawai tayi tana cewa sory sister’s,
Daganan kuma suka sha soyayya,
Atakaice dai ranar cikin nishadi suka wuni,
Bayan kwanaki su Abdul suka fara fita aiki yayinda abdulkadir yake final year dinsa shi kuma Abdul’aziz yafara zuwa har sun fara karatu sedai fatan Allah yabasu sa’a,
Badee taji damuwarta ta ragu sosae sedai bayan lafawar komai hankalinta yakoma gun mijinta sotake kawai ta ganshi ko hankalinta ze kwanta tanaji a jikinta kamar yana cikin wani hali,
Wannan karon kuka nake kamar anmin mutuwa Dan ganin majid a tsakar gida kwance duk yafita hayyacinsa sakamakon safara’u data janyoshi tsakar gida zatayi mai wanka yanda ta saba Sega waya ankirata a gaggauce tafita tabarshinan tana cewa jirani zandawo kuma rufe gd zan Dan inno batann,
Anan tabarshi tun ba rana har tazo ta cimmasa nan gashi ko motsi be iyayi se magana yake jini na fita a bakinsa,
Nalura duk lkcn dayake son yin magana sejini yaringa fita abakinsa hakan nanufin anrufe masa bakin ne,
Saurarar sa nayi naji meyake cewa se jinayi yana cewa badi’a,
Akace ko karema yanada rana balle mutum kuma komai Nada lkc yadda komai yake da farko haka yake da karshe yau ina badeen dayake hanawa abinci?yau ina badeen dayake tauyewa haqqi?ina badeen dayabari da Sha’awa bayan yariga yasaba mata da yanayinsa idan bame hakuri bace da tsoron Allah dayanzu ta afkawa halaka,
Wannan tunanin yake yana kuka sosae yana haka Sega safara’u ta dawo haka tawankesa awulakance tajashi tamaidashi daki Sega ta da tarin takardu,
Kai inkana son samun salama ka saka hannu kan wannan takardun karka damu darashin aikin hannunka indai signing zaka mun hannun zeyi aiki,
Kallon papern yayi taga ta gidansace dake sama road gidan daya Dade da ginawa abdulrahim lumshe idonsa kawai yayi baze taba signing wannan ba yafi bukatar mutuwarsa akan hakan,
Kanta ta dafe kusan sati daya kenan yaki signing dinsu dole takoma gun malam,
Ga mahaifiyarta ba lafiya batamasan metakeyi ba batasan wake kantaba
Mayafinta taja tabar gidan gaba daya,
Duk yadda tayi damajid abin yacitura gashi yanzu taji Sha’awa ta addabeta mijinta baze iyayin komai ba,wani alhaji takira kafin ta tattara majid takai shi dakin megadi daga shi se tabarma,
Akace kowa yabar gida gida yabarshi to hakane a gurin sa yabar dangi da iyayensa suma sunbarshi babu menemansa balle yasan halin dayake ciki.
Asia m inuwa sefa kunyi hakuri da lazy writer momma na CE ta shagwaba ni kuma kar kibari tajiki kina cemin lazy Dan bataso atakuramin 😉
Meena parrot nayi late ko?sory baby.
[8/12, 11:56 AM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 36
Kuka yakeso yayi irin dakarfinnan kozeji sanyi amma gani yake idan yayi jininsa ze qare,ahankali hawaye ke sauka daga idonshi addua yake azuci Allah yakawomai dauki,(ina sharar kwalla nima nace ameen😭),
Zuwa yanzu kam badee takasa jurewa bacci ma gagarar ta yake idan tatuna da majid tadora duka laifin akanta meye nata nabaro gdnma tabaroshi da matarda batada imani kokadan a zuciyarta itakam komawa gidanta zatayi koba komai idan tana ganinsa hankalita ze kwanta dama ba korarta yaiba,
Miqewa tai tadauro alwala tayi nafila raka’a biyu da addu’o’i kamar yadda ta saba inta kasa bacci,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,lubna tafada tana zabura dasauri badee tazo kusa da ita,ke menene?,
Mama mafarkin baba nai wai ya rasu,sosae gaban badee yake dokawa tadaure tace kwanta kicigaba da baccin ki,
Mama muje mudubashi,kikwanta nace bakisan dare bane idan gari ya waye zamuje,
Dakyar ta samu lubna tai bacci washe gari tunda sassafe lubna ruwa kawai tadafa wai asha tea fita zasuyi,
Ke ina zaku tunda sassafe dazakibamu tea kawai kintaba ganin munsha tea?inji abdulrahim,
Ai hardaku zamu baba zamuje dubowa,
Babu inda zamu harku ma yana gama fadar haka yashiga daki inda mama Da hajiya,
Eh shi zamuje dubawa tunda shima mutun ne dazakazo ka tsaya min akai kana tambaya ta sekace ubana idan kai bazaka ba bazance dole sekaje ba amma nida lubna zamuje Dan naga alamar kanwar ka tafika hankali sbd tasan darajar ubanta,
Guri yasamu yazauna ganin yadda tadau zafi, mama bawai bansan darajar sa bane abinda yaimana ne bangama hucewa ba kuma banaso muje Wannan matar tasa ta cutar damu don Allah kiyi hakuri,
Shikenan mu mun tafi tafada tana miqewa tsaye, zanbiku nima inji hajiya,
A a yizamanki keda kefama da ciwon kafa kizauna aiba jimawa zamuyiba,
Su abdulrahim suka hau mashin lubna kuma suka tsaya jiran adaidaita bayan sun samu sunatafe wayarta tafara ringing baban baby tagani,bayan sun gaisa yace kina inane naji kamar iska da karar ababen hawa,
Eh muna kan hanya nida mama zamuje can gidanmu dubo baba,bani address din gidan mana nakwana biyu ban ganki ba ga baby tana kuka wai se mama take kiramin,kwatancen gidan taimasa kafin suyi sallama,
Wai nikam wannan bawa akwai kazanta kuji yadda wari ya baibaye gate din nan daka doso kamar ka amaye hanjinka,tab..bari na wankeshi tun ba ayi zaton gawa na ajiye ba.injiw safara’u data dawo daga gantalinta,
Anan tajanyo shi kan tarbarma ta jona tiyo tafara shekamai ruwan,
Su badee kam suna zuwa ba wata wata suka shigo gidan dukansu mutuwar tsaye sukayi suna kallon safara’u dake ta sheqawa bawan Allah ruwa hankali kwance,
Lubna data gano baban sune awulakance haka tai kukan kura ta shaqo wuyan safara’u takaita kasa dakyar abdulrahim ya bambare ta zuwa lokacin har tasoma fitar mata da jini ita kanta lubna tsabar bala’i da safara’u ta shuka a gidan hankalinta ya bar jikinta seda Abdul’aziz yafita gate da ita sekuka take,
Badee kam kan mijin tai tadagoshi batadamu da kazantar dake jikinsa ba,
Majid don Allah katashi ka yimin magana me matar nan tai maka?duk acikin kuka take maganar,
Abdul kukaimin shi cikin gida,abdulrahim yadorashi akafada yawuce dashi toilet din tsakar gida yakai shi kafin yashiga dakin safara’u yadauko sabulu da soso yakawo wa badee,
Ka dauko min kayanshi kaduba adakinta da sauri yakoma dakin yadauko kayan gasunan ajere amma ambarshi cikin muguwar jallabiya,
Sunanta yake kira ahankali jini nafita bakinsa dasauri tarufe mai baki kayi shiru kar jininka yakare,
Sosae ta wankesa ta saka masa kayan abdulrahim yadauko yadawo dashi harabar gidan karkashin bishiya kan tabarma,
Mus’ab yakaraso dasauri Yana tambaya meyasa meta,dasauri taja hannun su ta nuna musu wannan katon dutsen,yaya kudaga shi akwai wani Abu agurin,
Da addua abakinsu suka karasa wurin layune sunfi dozen awurin,Mus’ab yace siyo kalanzir da ashana mukona,
Haka kuwa sukayi suka kona duka,Abdul’aziz yace muje ciki mana,
Abduljabbar kitchen yashiga yasamo wuka yadawo yahau bishiya yakaryo itace masu kauri yadawo inda yabar ta abdulqadir ya tsareta se muzurai take,
Yace ke inkina bukatar kanki da lafiya to ki dauke masa wannan wahalar kuma duk inda kikasan kinsaka wani mugun Abu ciki da wajen gidannan kifada mu toneshi ko wallahi mujibgeki mun jibgi banza,
Shiru tayi tana kallonsa,
Au ba zakiyi magana ba?
Abdul kuzo mufara aiki inaga seta soma jin maza zata fada,
Dasauri tana kuka tace wallahi zanfada,
Badee kam tanacan rungume da mijinta tana kallon ikon Allah se en kananun hawaye da take,
Rana dubu ta barawo rana daya tak tame kaya.
[8/13, 5:35 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Na sadaukar da wannan shafin ga en gidan Sophie G fatan alkhairi agareku.ILYSM❤
Page 37
Nidai ban binne komai a gidannan ba wallahi ciwo ne Allah ya Daura masa banida sa hannu aci….
Kyakkyawan mari abdulrahim yadauketa dashi yakara mata wani dabayan hannu,
Abduljabbar bani itacen nan inaga sena saka jikin ta yaitsami,batayi auneba taji sun soma rangada mata itacen,
Abdulrahim banda duka inji badee,
Mama idan kinajin tausayinta ne seki tashi kikoma cikin gida koki fita waje babu Wanda ze hanamu jibgarta indai bata fada mana gaskiya ba,
Shiru tayi Dan bata taba ganin zuciyarsa irinta yauba,
Azuciyar safara’u kuwa cewa take sedai Ku kasheni bazan fadaba,
Shiru tayi tana kallon su babu alamar zatayi magana,
Aiko suka shiga dukanta kamar ankama barawon daya addabi unguwa,
Zaki fadane kose mun kakkaryaki?
Ganin dagaske suke yasata cewa zan fada wallahi zanfada,akasan zuciyarta tunanin sharadin da bokansu yabasu take tace shikenan tawa takare,
Nan tashiga nuna musu harseda suka tsorata babu inda bata binne mugun Abu a gidanba layu sunfi akirga har wani Abu dabasusan meye ba hardasu rayyyayyen maciji dakunama akwanrya aka Daura wa laya aka binne lkcn da suka hako su daga ramen bayan dakin badee seda suka tsorata Dan macijin sakunamar ba cewa sukayi b’it,hmm
Aiko majid jiyaye kamar andaukemai katon dutse aka jinsa yake wani sabo hannayensa dakomai Na jikinsa suka shiga kakkarwa nan take ya sume agurin dasauri majid yaje mota zedauki waya yakira malam se ganin badee yayi tana bawa baby abinci yana zuwa ta kwadamai harara,
Kabar yarinya ita kadai amota koda nazo tana kuka idan aka sacemin itafa?,
Sory baby bari mugama da wannan matsalar tukunna,
Malam yazo yaduba shi yabashi addua da magani da yardar Allah zedawo daidai,
Ruga gida kadaukomin key din part dina tafada tana kallon Abdul’aziz dasauri yaje yakawo ta bude dakin zanin gadon kadai tayaye aka kwantar da majid,
Safara’u kuwa dakinta suka turata suka kulle bayan sun karbe wayanta ,
Hajiya tazuba ido har tagaji basu dawoba danhaka tamiqe tarufe gidan tana fitowa ta hadu da yayan anty asama’u maza su uku abubakar,Ibrahim da muhsin sunzo gaisheda badee,
Ai batanan sunje can gidan haryanzu basu dawoba yanzuma bayansu zanbi,
To hajiya muje mu sauke ki daganan ma semu gaishe ta mubata sako kuma,
Hajiya tunda taga majid take ihun kuka tanawa tsinewa safara’u dakyar aka samu tai shiru nan en samarin sukayi waje suna bawa su abubakar labarin dukan dasuka yiwa safara’u da abinda suka gani danma har sun kona da sun nuna musu,
Badee kindawo dakinki kikula da mijinki nikuma zankoma da lubna Dan ban iya zama nikadai har mijinki yaji sauki ko,
Kunya sosae takama badee tace uhm kawai tana kaida kai,
Lubna kamar tayi kuka tabi hajiya itafa bata taba bacci ba ajikin mamanta ba Dan haka take bakin cikin bin hajiya tunda suka isa kokallon Mus’ab da baby batyiba tashige gidan tana kumbura fuska bece komaiba yawuce gida saukinsa daya baby bacci take,
Yo lubna Dan anrabaki da uwarki sekizo kinamin kumbure kumbure?to idan kinyi aure senagani koda uwarta ki zaki tafi zoki dora mana tuwo,
lubna kuka taringayi da dare tana kiran mama seda abdulrahim ya rarrasheta kafin tayi shiru tayi bacci,
Majid be farka ba se washe gari tunda ya hada ido da badee yafashe da kuka,
Badee’a don Allah kiyafemin nasan na yimiki babban laifi amma don Allah ki gafartamin gashinan tun ba aje ko ina ba nagane kuskurena,
Yi tayi kamar bata jishi ba ta kauda kanta tana goge kwalla wani sabon sonsa take jin yana tsarata kamar taje ta rungumeshi,
Dakyar ya rarrafa ya rungumeta yana bata hakuri dakyar tajuyo,
Yawuce majid bakada lpy ka kwanta ko zaka iya tashi kayi wanka kayi sallah,
Eh yace yanajinjina hakuri da juriya irin na badee ita takama masa yayi wanka tana kakkauda kai,
Badee’a ina y’ay’ana?
Wani kallo tai masa cike da mamaki,
Cikeda gayya tace dama kanada yaya ne?,
Sosae gabansa yafadi azuciyarsa yace kodai bata hakura bane?.
Wayyo Allah na gaji😩
[8/14, 11:51 AM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 38
Badee’a don Allah kiyi hakuri wallahi nima ba asonraina nake muku haka ba duk yadda naso in kyautata muku se insamu kaina dakasa yin haka,daganan kuma seya sakuka yana kara bata hakuri,
Itafa yasoma bata kunya danhaka ta janye idonta daga nasa tace,
Meye haka kakeyi kamar wani yaro?Dan Allah nidai kabari,ta miqe tana cewa ni Allah ma yasa yarannan suyi hankalin kawomin kayana da abinci nasomajin yunwa,
Jikinsa ba karfi amma haka yamiqe dasauri bari nasiyo miki masa IET,
A’a bari muka zuwa 10 inbasuzoba zanje dakaina nasiyo kaikam yaushe zaka iya fita aiseka fadi ahanya,
Rufe bakinta keda wuya sukajiyo sallamar yaran a palon badee suka tsaya Sega su sunfi to dasauri lubna taje gun mamanta,
Mama ina kwana?kina lafiya? Babu abinda ke damunki dai ko?,
Badee kam kallonta kawai take yadda idonta suka kumbura daga ganin ta kuka tayi,
Majid idonsa suka cika da kwalla,Allah sarki dayanzu yayansa sunyo kansa amma ji karamar ma kota kansa batayi ba lafiyar mamanta kawai take tambaya,
Bazaku gaisheda babanku bane?,
Kusa dashi suka karasa sunayimasa yajiki,
Ya amsa yana zubar dahawaye durqusawa yai ze nemi ga farar su dasauri suka rigashi,
Baba plssss rungumesu yai yana kuka suma sunayi,
Ihu lubna tasa tafadi kasa tana birgima cikeda tsoro suka juyo suna kallonta kafin badee tace ke meye haka sekace wata ta goye?,
Mama bakiga sunrufeshi ba Niko ganin sa ma banyi ba,
Mtsww to shine zaki samana ihu haka?inji abduljabbar,
Dakansa yakarasa kusa da ita yadago ta Ku kyale min lubna ta ai gaskiya tafada yakarashe maganar yana murmushi,
Dukansu sukayi murmushi daganan suka zauna cin abinci,
Shiru babu motsin safara’u badee tace su bude ta ko lafiya shirun yayi yawa kuma abata abinci itama ai mutun ce kamar su,
Safara’u kam nacan reshe yajuye da mujiya se muzurai take tunda ta tashi daga bacci takasa koda motsa Dan yatsanta ne kuka kawai take tana Dana sanin biyewa mahaifiyarta datayi yanzu gashi bataga lpyrta kuma bataga dukiyarda tazo ci Dan sun karbe komai har kudin dake account dinta sun tursasata tatura su account din majid domin dama ba nata bane,
Sosae badee’a ta tausaya mata majid yace sukira bakanike ya duba lafiyar motocinsa zasu maida safara’u kware inda mahaifiyarta,
Haka kuwa akayi dukda badee bataso tafiyarba amma babu yadda zatayi haka suka hada kayan safara suka miqata kware babanta yai kuka kamar ransa ze fita dakyar suka rarrasheshi dganan majid yabawa safara’u takardar ta saki biyu babanta yace kayimin daidai Dan haka ke Hajiya tunda kindan samu sauki seki cigaba da girban abinda kika shuka gashinan tun ba aje ko ina ba kinfara gani dama Na fadamiki inasane daduk abinda kuke kuma Allah baze kyalekuba koda dabba kika cutar balle Dan Adam rai yakai hamsin Wanda kika saka cikin mawuyacin hali saboda biyan bukatarku ta banza,hmm
Daganan suka dawo sokoto gidansu badee suka fara zuwa majid yanemi ga farar su suka yafe mai suka karayimai nasiha sosae yai godia,
Umma tace badee’a zo inason magana dake,
Ke kina ganin babu matsala ko?banason abinda zekara cutar min dake,
Umma babu wata matsala kibari idan hankali ya kwanta zanbaki labari yadda zakifi gamsuwa,
To shikenan Allah yayi muku albarka,
Ameen,
Part din safara’u majid yasa aka kwashe mata kayanta kaf aka tura mata kware,
Part dinsa suka koma yasa aka gyara gidan yai kyau,yaje dasu Abdul kasuwa suka ga shagunan kasancewar baya nan yasa shagon duk arufe yaran sa sungaji sun rufe sun gudu da Dan cinikin dasu kayi,
Office ma yaje yai reporting abinda yafaru kuma yana bukatar Hutu yakara warwarewa,
Wai!duniya sabuwa Dan har hajiya aka dauko ta dawo gidan danta da zama lubna ko da dakinta kullum zatayi bacci setayi kuka wai an rabata da mamanta,
En uwan badee da yayansu wuni guda suka yiwa badee agidanta abinci har seda suka gaji daganinsa lubna Dan ba’asaba ba taci abinci har babu iyaka ranar seda taikiba ta musamman,
Badee tafito daga wanka sotake ta kwanta tahuta tasha yawo har tagaji,
Tana tsaye gaban mirror taji an rungumeta,majid mai zan shafa fa,
Bana bukatar jikin ki da mai,yahade bakinsu,dasauri tazare bakinta tace,
Lahhh meye haka sekace yaro?
Nafi Abdulrahim jin luv da kuruciya daganan sukayi gado,
Ai a 200 nabaro dakin ina dafe kirji wannan luv haka sekace meela da adeel😉
[8/15, 12:58 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 39
Bayan awa uku nadan leqa don in gani ko akwai wani rahoto dazan dauko,lahaula wata sabuwar soyayyar dagani yasa nayiwa kaina kiyamullaili nabar gidan gaba daya sedai zuwa gobe daidai komai ya lafa😉
Washe gari seda nai wanka nai sallahn asuba ko kwalliya ban tsaya yiba nakama hanyar domin da kafa zani babu kudin adaidaita kuma nakafe kai dafata sena dauko muku rahotonnan saboda nacika alkawarin Dana dauka,
Bansamu isaba se karfe takwas harda rabi,
Majid kasa ke ni mana intashi kofa sallah bamuyi ba kalli yadda rana tafito,
Dasauri yamiqe zaune yana murtsike ido,
Subhuhanallahi Ashe munmakara haka ya’akayi,
Ka tambayeni ya akayi bayan Kaine ka hanamu bacci,
Munacin lokaci tashi muyi wanka,
Kadaiyi ninayi dakina,tattara kayanta tayi tabar masa dakin sefaman murmushi yake seyaimin kamar wani ango,
Zaune tasami lubna fuska shabe shabe da hawaye,
Ke meye haka kika zauna kina kuka?,
Bake bace kinsan bamu kwana tareba kuma baki fito ba seyanzu kuma ni inaso inganki,se wani sabon kuka,
Waike yaushe kika lalace da wannan shagwabar?inace aure zakiyi?shikenan kuma sekice danmun saba kwana tare yanzu bazaki kwana ba seda ni?kinada aiki ja agaban ki maza tashi kiyi shara da moping,
Tashi tayi tana turo baki tafice daga dakin ta share ko ina har tazo dakin badee ta sameta zaune kan sallaya,
Zama tayi tana jiranta harta shafa adduarta,
Mama wai sallar me kikayi yanzu?
Kingama shara da moping din?,a’a nadaiyi shara nan dakin zanshare senayi moping,
Shine kika zauna tambayar abinda be shafeki ba?to ki tabbatar kafin nagama hada breakfast kin kammala shara Da moping,
Hmm,kawai tace tacigaba da aikinta,
Tana zaune adakin badee tana game awaya Sega kiran Mus’ab,
Ummm uhm uhm nikam na shiga uku kabar sona tafada tana kukan shagwaba,
Kekam yaushe kika sangarce haka komai shagwaba?,bakaibane kusan awa ukufa yanzu baka kiraniba,hmm yi hakuri nidai yanzu baba na nan zanzo ingaisheshi ne,
Eh yananan befara fitaba tukun,OK to gani nan zuwa,
Majid anzama baba yazauna shida Mus’ab se labari suke ya yaba da hankalinsa sosae kuma yaimasa godiya akan taimakon daya yiwa su badee,
Babu komai baba ai yiwa Kaine dama nazo ne neman izinin zuwa gurin lubna kafin naturo magabata na ayi magana tunda naga insha Allah komai ya daidaita,
Babu komai Mus’ab insha Allah zaka iya cigaba Dazuwa,
Sosae yayi godiya kafin yaimasa sallama yafito a harabr gidan suka sha hirar soyayyar su kafin yawuce,
Bayan sati biyu Mus’ab yaje gidan yayan mamansa dakuma kanin babansa Wanda yaje babu Wanda be zubda kwalla ba acikin su sbd watsi dasu kayi da zumunci suka ringa Neman gafarar sa yafada musu cewar dama za aje nema masa aure ne ranar asabar me zuwa iyayenta suka bashi yaturo,
Ranar Saturday akayi magana kuma an bawa Mus’ab lubna,majid sukaje gurin iyayen juwairiyya nemawa Abduljabbar aurenta sekuma safnar abdulrahim wacce bansan lokacin da suka dinke ba seganin majid nayi da sauran mutane sunje gidan dayamma alhmdllh komai yatafi yadda akeso sedai majid yace se ayi hakuri da auren se bayan sundawo aikin hajji shida iyalansa,
Ai lubna dataji labari dagudu taje ta rungume babanta tana murna wani sanyi majid yake ji azuciyarsa yace wai dama Ashe haka yaya suke jiyake kamar ya hadiye su,
Baby kinji baba wai sekunje hajji kindawo nifa nagaji na matsu wallahi senan da wata uku fa,
Kadaina kirana dasunan yata kuma bangane ka gaji ba ka matsu dame?,
Naganki matsayin matata mana bakisan yadda nakeji bane idan nace inason ki sosae senaji kalaman sunyi kadan,
Uhm kayi hakuri kaji Dan samari kamar gobe ne insha Allah,
To Allah yakaimu lokacin da rai da lafiya,anjima zan kawo miki baba Dan safna zataje gidan kawu kwana biyu kafin ta dawo,
Aikam dai wallahi nayi kewarta ina zuba ido,
To shikenan en mata na se anjima.
Soyayya ruwance inkasha sekaba masoyi nima nasha naba nawa masoyin😉
Kamar yadda meenar parrot kebawa masoyinta abdul😜
[8/16, 11:57 AM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera IbrahimY’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera Ibrahim wannan shafin nakine dalilin kyautar dakika min jiya har mafarkinnayi nasiya miki mota😎 Allah yabar soda kauna ameen.
Page 40
Alhamdulillah su lubna andawo daga makka se shirin biki ake domin saura sati biyu adaura aure majid bakin nan yaki ruhuwa ze aurar da yayansa su uku sejinknsa yake daban kamar ba shiba,
Hello ramla banason wulakanci tun dazu nake kiranki kinki dauka,
Dalla kirabu dani da abinda yake damuna dama yau nake da niyyar zuwa hargida infada miki salim ya takura seda aka matso da date din bikinmu kusa bayan tafiyarku jibi za afara bikin ga ankonki nan nasiyo miki shi zanzo nakawo miki bansan kozaki samu zuwaba tunda kema ankusa bikinki,kawai seta fashe da kuka,
Ke kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa bari gani nan zuwa gidannaku kuma biki aidole dani za’ayi koda kuwa ankaini yaune akafara bikin washe gari senazo bare ma akwai sati daya a tsakani,
Ajiyar zuciya ramla tasauke,to shikenan amaryar Mus’ab sekinzo,
Yawwa matar salim,
Ranar Saturday saura sati daya bikin su lubna kuma aranar aka miqawa salim matar sa ramla sedai fatan asha amarci lafiya,
Majid dakansa yatura abduljabbar kware yakai wa goggonsu invitation arabawa dangi Dan hajiya tayi rantsuwa lubna bazata kuma fitaba se an fara biki,
Takowane bangare se shirye shirye ake safna ma se gyara ake sha juwairiyya yaya asama’u tace ta tattaro tadawo inda lubna susha gyaran tare dakyar ta samu tazo wai ita kunyar badee takeji koda tazoma tana dakin lubna babu abinda ke fitar da ita idan badee tazo kawo wani Dan abin gyara da gudu take shigewa toilet sbd kunya yauma suna zaune da sassafe badee ta shigo da Dan hadinta a kofuna da sauri riyya ta miqe zata gudu,
Inkika sake kika shiga bayinnan wallahi sena ranqwasheki uban wa kike kunya anan?tsaf zan zaneki danni ba wuce duka kuka yi agurina ba maza zoki karba ki shnye ina gani Dan nafara zargin zubarwa kike,
Lubna tace nikam mama bani idan wannan me dadin ne kuma wannan Dan karamin kofin baze isheni ba,
Sannu kekuma rasa kunya,tunzuro baki tayi,
Ahankali juwairiyya tazo takarba tazauna tana sha a hankali harta shanye,
Badee na fita juwairiyya tacewa lubna waike baki gaji da waynann abubuwan bane da ake dirka mana nifa nafara jin yanayi kumama nikam banaso suyi yawa naje ya hallakani a banza,
Wane irin hallakawa sekace baya sonki Nikam wannan kazar ne bazan tabaci ba bakiga ba akawomana ba?ninace karsu wahalar dakansu wallahi gara wannn kodan dadin sa zaksha,
Juwairiyya tayi dariya kawai Dan ita mamakin lubna take yadda bata iya boye abinda keranta,
Biki kam anshashi har angode Allah ranar Saturday da safe aka Daura aure da dare misalin karfe Tara aka miqa kowacce dakinta bayan sun sha nasiha lubna kam ita aka kai karshe Dan maqalewa tai jikin badee tana kuka itafa seyanzu da za akaita tagane tafa bar gidan kenan danhaka taringa kuka seda majid yazo ya rarrasheta tana rungume jikinsa yakaita mota,
Hmm lubna amarya.
Abdulrahim kam da abduljabbar basu yi wata wataba suka angwance daganan suka kwashi baccin su me dadi,
Bangaren Mus’ab da lubna kuwa rarrashinta kadai seda suka kai karfe dayan dare kafin suyi alwala suyi sallah dacin kaza seda yadaukesu awa daya,
Wayyo yaya bacci nakeji,tab..yace wannan karatun dolene yau kibari idan kingama dauka sekiyi baccin kinji daganan al’amura suka chanja (dama ni bana tsayawa daukar irin wannan rahoton saboda dalilai danhaka nafito najamusu kofar sedai fatan Allah yabada zuri’a Dayyaba ameen),
Washe gari misalin 10:12 am tafarka dasauri ta tashi zata miqe,
Wayyo Allah na tace takomawa zaune,shikenan yakassarani mama kizo kigani ban iya tafiya tasa kuka,
Gogan cikin bacci yajyo kukan lubna dasauri yatashi,
My lady ya akayi?sannu kinji,bari na hada miki ruwa namiki wanka,
Banda kuka da shagwaba tana kara narkewa babu abinda take,
Bayan sunyi sallah yace,my lady Kindaina jin zafin?,
Juya fuskarta tai gefe tana jin kunya tace um um,zo induba kose anyi Dinki ne?,
Nikam ka kyaleni jikina duk ciwo yake kuma bacci nakeji,
To ki kwanta bari naje nasiyo miki magani kinji,
Abdulrahim kam yarasa inda ze tsoma kansa Dan dadi ko motsi safna tayi seyace sannu,
Wani Abu dayake ban dariya shine koda naje abduljabbar da juwairiyya kunyar juna suke ji sunkasa hada ido,
Yaya asama’u ita tai abincin aka kai musu suka ci,
Lubna na zaune a Palo Sega kiran safna awayarta,
Matar yaya,inji lubna
Matar yaya Mara imani,
Yayanki daine bashida imani muryata seda tadaina fita,
Dan bakiga abinda yayanki yaimin bane ke ko tafiya ban iyayi fa,
To uban waye yake iya tafiyan dalla daga chan ni se anjima maganama wuya take min,
Sosae safna tai dariya kafin suyi sallama.
Dana sani na tsaya najiyo ihun Lubna koda shine nayo recording amma nextym video zanyi Basenasha wahalar typing ba 😉
[8/16, 8:35 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 41
Bayan wata daya da en kwanaki lubna ta soma laulayi duk abinda taci seta Harar yauma zaune suke itada Mus’ab da yamma ya karbo mata tuwo gun momynsu,
My lady pls tashi kidanci koda loma goma ne kinji,
Nikam kabarni idan naci amai zanyi,ba zakiyi Amai ba kina ci zanmiki alluran daze hanaki Amai,
Dakyar yasamu tadanci yaimata allura yace tadan kwanta kafin yaje masallaci yadawo tasamai kuka dakyar ya rarrasheta tabarshi yafita gashi ta hana ya fadawa kowa tunjiya ta rikice,
Sallar magrib kadai tayi agurin tafara Amai tanayi tana kuka ahaka tayi kokari ta gyara gurin,
Sallahr isha’i ma azaune tayi saboda jiri take ji tana gamawa sewani aman gabadaya ta gama galabaita kuka kawai take ahaka Mus’ab ya zo yasameta abokinsa yakira yataimake sa yakawomai ruwa da magani baze iya fitaba zesaka mata drip din agida,
Mus’ab gara ka kawota asibiti kawai tunda batada lpy sosae bekamata ka ajiye ta gidaba Dan kana takamar kai likita ne tana bukatar kulawa sosae amma fa shawara ce,
To shikenan Ibrahim gamunan zuwa Dan wallahi ko magana bata iyayi nagode,
Shege Mus’ab sharp shooter haka fa ka yiwa jamila kaikam bakasan dadin amarciba,
Kujimin Dan iska dallah nidai gani nan zuwa banza kawai,
Suna zuwa akayi admitting dinta akaimata komai daya kamata tasamu bacci,
Se washe gari yakira gidansu yafada hankalin badee sosae yatashi tafada wa majid tare sukazo lubna na bacci majid be jima ba yawuce kafin yamma asibiti en uwa duk sunzo dubiya zuwa lokacin ta farka amma takicin komai ita tsoro takeji,
Safna,juwairiyya, Rahama da babynta,laila da ramla duk suna dakin badee taje gida tayo wanka,
Safna tace,waikukam bakuda uzuri harkun abinnan?, tayani fada inji juwairiyya duk kwazaban yayanki dai ba asamu rabo ba,
Ita dai kallonsu kawai take batajin zata biye musu amma Wallahi tanajin sauki duk seta fige su Dan seta rama,
Se dariya suke suna kiranta me hazaqa aiko taji bazata iya hakuri ba majid na zuwa tasoma narkewa a jikinsa tanace wa,
Wayyo My man yunwa nakeji,ko inbaki abincine zaki gwada ci ne?,nikam ba zanyi Amai ba?,insha Allahu bazakiyiba, miqewa yai yadebo tuwo kadan a plate ya leqa toilet ya wanke hannunsa yadawo yazauna yanajanyota jikinsa,
Su safna anzata abin Na kallo ne kawai sesukaga yafara bata tuwo abaki tanaci tana kukan shagwaba ahankali suka silale waje suna fita se dariya juwairiyya tace kai amma wallahi lubna er iskace kukaga yadda tabamu kunya fa,
Safna tace aitayi maganin tsiyar damuke mata,
Seda tai sati daya a asibiti tadanji sauki ta matsa aka sallameta,
Wanka tai taci abinci ta kwanta Dan dare yayi Mus’ab ma wanka yayi suka ya kwanta yana janyota jikinsa,
Cikin dare yaji kamar lema akasan su dasauri yatashi yakunna wuta,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, jini duk agadon lubna se baccin ta take Tashin ta yashiga yi tashinta yai daidai da murdawan maranta dasauri taduba jikinta ihu ta kwalla shikenan se suma jinin kuma kamar ankunna famfo sekara zuba yake kwasar ta kawai yayi sukayi asibiti,
Zama nai akasa na ringa ihu INA gun jin kuka nashiga uku har na hangomu ranar suna munacin rengem😭🙆🏻,
Kafinma su isa cikin yafita dafe kansa yayi kamar zeyi kuka se Ibrahim ne yai kokarin tsayar mata da bleeding din tasamu bacci se kusan la’asar ta farka sekuma ciwon Mara haka taringa wahala kuka kawai take tana juyi tasha injection kamar me amma bawani chanji,
La’ilaha illallahu yarnan haka kike wahala?wannan cikin ya gwada miki boni sannu kinji inji hajiya se kuka tana kamawa lubna,
Har kusan magrib Abu yakici yakicinyewa,
Ji tayi tagaji da gadon ma kasa takeso ta kwanta batasan lokacin da ta fizge cannula din hannunta ba ta fado kasa ta kwanta tana kiran mama,
Mama Dan Allah kitaimakeni marata jinake kamar zata fita baba kutaimakeni wallahi mutuwa zanyi,
Mus’ab ji yayi kuka yazo masa amma yadannne kmata yai yamaidata gadon yasa auduga yana danne gurin data cire cannula din sbd jini dake fita,
Sannu lubna kidaina wannan ihun kina addua kinji?,
Wayyo Mus’ab kaceci rayuwata incikinnan ne ke min haka Dan Allah kuciremin shi inba hakaba shine ajalina,
Bashi bane yi hakuri kinji bari Ibrahim yakawo allura insha Allah daga anmiki ita zakiji sauki,
Mus’ab nagaji da alluran nan kuciremin cikinnan don Allah,
Majid ne yashigo yariko hannun ta lubna kiyi shiru kiyi addua ba ihuba kinji kuma kidaina zancen aciremiki ciki kinji?,
Baba harda kai baka sona?yaushe kabar sona?don Allah kutausaya min bakusan me nakeji ba wallahi jinake kamar zan mutu,
Abdulrahim dake gefe yaji hawaye Na kokarin zubo masa da sauri yajuya yai waje yana kuka kamar yaro baze juri ganin er uwarsa hakaba yana jin sonta fiye da tunanin me karatu,
Mama kema kinbar sona?to kice sucire mun cikinnan nasan ke kinaso na,
Na lura lubna bata hayyacinta danhaka dasauri nabar dakin inata kuka kuma nace sena fadawa mamana😫😩.
[8/17, 6:18 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 42
Shiru ta lafe jikin Mus’ab ahankali bacci ya kwashe ta tana sauke ajiyar zuciya,
Washe gari garau ta tatashi sedai Dan abinda baza arasaba kafin yamma ta wartsake se shagwaba take zubawa,
Kwana daya ta kara aka sallameta badee ta wuce da ita gida seda tadan kwana biyu gidan badee tace mijinta yazo yadauketa takoma gidanta suna zuwa Momy tace takoma part dinta seta kara samun sauki wannan wahala haka aidole tahuta sosae,
Sega lubna tana kasa dakai yanzu kunyar Momy akeji,
Subhuhanallahi yaya meya sami safnar?,ohh harkun dawo gida?OK to insha Allah inanan zuwa yau idan Abu Zara yadawo,ahh haba aisena zo karma kace a’a akwai ma zancen danake so muyi da safnar,to shikenan Allah ya inganta mana,
Tab…su safna angama yimin tsiya Ashe ta kwasa,hmm
Aikin ta tacigaba dayi tana goye da baby,
Baban baby kagama cin abincin nan dasauri muje dubo safna wai batajin dadi,
Meyake damunta?kwazabar Ku kedamunta mana ciki ne da ita amma ba serious ne ba ciwon kawai kasala ne,
Safna dama haka en gdnku suke?kema bakida dangana daga zuwa har kinyi wannan,
Er iska baznji haushi ba ai nasan ramawa kike,
Dariya sukayi daganan suka shiga hira har dare lubna ta koma gida,
After two month lubna ta sake kwasar wani sedai wannan daga bayyanarsa ya fita tasha wahala kamar wancen Dan haka tana Dawowa gida bayan kwana biyu tana zaune gefen gado Majid na shirin fita office tace,
Dan Allah nikam yau idan zaka dawo kadawomin da maganin planning mana,
Maganin planning? Waye zesha?yakamata taje asibiti kafin tafara sha,yafada yana yagyara belt dinsa,
Nice zansha fa kaima kasan yakamata na huta koda shekara dayane?,
Waike meyasa kike Abu kamar bakida hankali?kawai Dan kinsamu miscarriage sau biyu sekice zakiyi planning? To wallahi ban yadda ba kuma idan kikayi aboye bazan taba yafemiki ba,
Ai dole kace haka tunda bakaine kasha wahalar Dana shaba,
Koma dai menene inkinaso musami matsala dake to ki gwada yin abinda kikace wallahi me rabani dake se Allah shashancin banza,
Sosae ranta yabaci Dan haka tace, ni wallahi senayi inba haka ba sedai in bar maka gidanka bazan zauna inna dauki ciki yana wahalar dani kuma inma yafita sena wahala ba kuma ace bazan dauki mataki ba ai hutawa nace zanyi ba cewa nai bazan kara dauka ba,
Wannan maganar da jahili yaita bazanyi mamaki ba amma kisani kekam kinban mamaki kuma Dan Allah karki fasa,
To shikenan zakaga jahilci kuwa,
Fuuuu ta fice kayan ta ta hada tabar gidan yadda zuciyarta tazo wuya,
Yana kallonta ta hau adaidaita ransa abace yanufi wurin aiki,
Lubna meye haka daga INa haka kika kwaso kaya?,
Mama Mus’ab ne,meyai miki?,wai Dan nace zanyi planning shine yarufeni da fada kuma yana fadamin bakaken maganganu,
Lubna shine kikayo yaji?,Tass..ta sauke mata mari kafin tacire sleepers din kafarta tashiga dukanta,
Ashe bakida hankali,dakika zo nan uban me zanmiki,maza dauki mayafinki kibarmin gida babu ubanda ze rakaki ni haka kikaga nayi wace kalar wahalar ce ban shaba da bazaki kwaikwaiyo da halinaba kiyi hakuri billahillazi idan kika kuma yin yaji kikazomin nan sena kusa illataki balle wannan banzan dalilin naki dabe taka kara ya karya ba,
Lubna da tuni tasoma nose bleeding tabi hanya babu mayafi se dankwali kawai akanta,
Mus’ab jiyai baze iya hakura ba bari yabi bayanta yana kokarin shiga yaci karo da ita zata fito badee na bayanta da mayafinta ahannu tana kiranta amma ko juyowa bataiba,
Riqeta yai sosae amma dakarfi ta kwace dganan tashiga buga kanta duk inda tasamu dakyar ya riqeta ya lalubo numbern malam ya kirashi yazo addua yaimata se bacci,
Mus’ab tashi kaje gurin aikinka kaji bayan azahar daidai tafarka sekazo ka kwashe ta Dan bazata kwanarmin agida ba,
Godiya yai yafita daga gidan yana cewa dole Na kiyaye bacin ran lubna wannan bala’i haka dabadan nazo ba haka zata fita ana kallemin jikinta,
Koda yadawo daukarta har suka isa gidan ko kallon sa bataiba bata fasa bashi abinci ba haka tashiga kitchen tadafa abinci me rai da lafiya,
Da dare taje gun momy,lubna lafiya jiya bakizo kin karbi baby ba kuma da safe bakizo ba mun gaisa nace ko lpy larai ta dubomin tace bakwanan,
Eh Wallahi bacci ya kwasheni jiya se 11 nafarka shiyasa banzo ba kuma d sassafe naje gida banjima da dawowa ba,
To lafiya daiko,lpy lau fa kawai dai naje ne,
To shikenan babyn nacan tana bacci tagama rigimar Neman ki,
Ai dole tawuni ta kwana bataga uwarta ba bari nadauki abita mutafi nayi missin shagwabarta,
Momy tai dariya kawai tana jin dadin yadda lubna ke kula da baby.
[8/18, 8:59 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 43
Wanka tayi tayiwa baby duk yana zaune amma ko kallonsa batayi ba secin magani take,
Kwanciyarta tayi bayan ta musu addua tashafe jikinsu da ita ganin haka yasashi cire jallabiyar jikinsa ya hau gadon ahankali yadauke baby yakaita gefe yamaye grubinta jikin lubna jin tadan matsa baya yasa yagano idonta biyu danhaka yafara laluben kalmomin da ze rarrasheta,
My lady don Allah kiyi hakuri dukda nasan inada gaskiya akan abinda kike shirin yi kiyi hakuri mu cigaba da rokon Allah insha Allah daga kinkara daukar wani cikin zamu dauki matakin da idan Allah yataimaka baze fita ba amma don Allah ki fahimceni inason naga Dana ko yata daga gareki kitaimaka muyiwa babynmu kani ko kanwa kinji,
Allah nagode maka daka azurtani damiji me sanyin hali nice nai masa laifi amma shine yake bani hakuri Allah ka bamu zaman lafiya dahakuri Allah ka kauda shedan a tsakaninmu,
A hankali tafara kuka tana kara shiga jikinsa,don Allah kayi hakuri kayafe min daga muryata danai akanka dakuma fita danayi bada izininka ba,
Ohhh nahakura maman baby kinsan banason kuka musamman naki muyi bacci kinji,daganan nikam nadawo gidan babana na rungume nawa sweetheart din (pillow😩) dakyar nai bacci,
Washe gari yanata sauri ze fita yayi letti sun fito kenan tayo masa rakiya Sega wata mata da zumbulelen hijab tsayawa sukayi suna kallonta harta karaso kusada su,
Durqusawa tai gabansu tafara rero kuka,Mus’ab don girman Allah kayi hakuri abinda nai maka kagafarta min don Allah Badon halinaba wallahi rudin shedanne da zuga daga wurin Momy gashi ta rabani da mijina da yata mafi soyuwa agareni wallahi ba laifina bane,
To da farko dai na yafemiki domin Allah ma munai masa laifi kuma ya gafarta mana amma kisani tunda nake ba aimin abinda ya batamin rai ya tabo zuciyata irin wannan ba,Dan haka gaskiya tsakani da Allah bazan iya kara zaman aure dakeba ina rokar miki Allah daya baki wani mijin Wanda yafini ga yarinya ta nan Allah da ikonsa ya rayamin ita cikin koshin lafiya,
Allah ya isa taringa jerawa Momy aranta kafin daga baya ta share hawaynta,ta miqa hannu ta karbi baby sosae takejin sonta na ratsata hakika tayi wauta da rashin hankali data yarda ta wofintar da rayuwar er ta tun tana cikin tsumman goyo,
Don Allah ka yimin alfarma daya inaso adan ringa kaimin yarinyar nan koda na awa dayane domin na ringa ganin ta,
Dama Waze raba da da mahaifi?zata ringa zuwa ganin ki bakida wannan matsalar,godiya tai musu kafin tashiga bangaren Momy itama taneme gafararta akan rashin kunyar da taimata,
Anan kuwa tagafar tamata takama gabanta,
Kishiyar Momy wacce itace silar faruwar duk wani mummunan abu agidan tazo tana Neman gafara ganin yadda Allah yai da ita yasa suka gafarta mata bakinta kadai ke aiki banda shi babu wani Abu mnajikinta dayakeda amfani,
Da room freshener na ahannu nashiga dakin da safara’u take amma se kamshinsa ya hade da mummunan warin dake tashi adakin akwance nasameta kan tabarma,
Yo waike kukan ubanme kikewa mutane duk kinbi kin suna daki da azababben wari wannan warin Allah ya agajeni karya kasheni sbd masifa munyi yawon asibiti har mun gaji amma babu wani ci gaba duk Dan abinda natara ya kare gurin neman magani wallahi bar ganin ki kwance zan wanwanka miki mari bakar munafuka,
Mahaifiyarta ke wannan masifan ta miqe a dudduqe takarasa dakinta Dan tuni tamaida safara’u dakin ajiye shirgi acewaeta bazata juri wannan warinba,
Baban safara’u ne yabiyo se shiga gidan a hankali yajiyo muryarta tanakiransa saboda tausayinta dayake ji yasashi shiga dakin yana toshe hanci,
Baba don Allah kakiramin su badee’a in roke su gafara ko zan samu sassauci,
Hawayensa ya share yace Allah yasa zasu yafe miki nima tabarma nazo dauka domin su majid din sunshgo gari yace badee tana tafe itada lubna sunzo ganin gida,
Aidasauri tace kataimakeni ka kiramin su inrokesu ko Allah zesa su yafemin domin na cutar dasu,
Majid kam warinta yagama isarsa kuma bayajin ze iya yafe mata danhaka yajuyard fuskarsa gefe,
Cikin muryar kuka da tsantsan tsoro badee tace nayafemiki safara’u Allah yayaemiki wannan lalurar majid don Allah kayafe mata bakaga halin da take cikina,
Tunawa yai duk laifin dayaiwa badee batareda ta tsaya wani tuna niba tayafemasa kuma yaiwa Allah laifuka da dama yana Neman gafarar sa meze hana yafewa wannan matar kila sanadiyar haka shima Allah yayafe masa,
Babu komai mun yafe miki Allah ubangiji yatakaita wahala,
Yana gama fadar haka yai waje,anan badee tai musu Dan ihsani kuma ta roki inna da ataimakawa safara’u da wanka lubna kam jikinta duk amace yake kalli wannan matar katuwa ji yadda takoma batada maraba da kwarangol,
Allah ka gafarta mana zunubanmu wayanda muka aikata da gangan da wayanda bamusan mun aikata ba
[8/19, 1:38 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 44
Hello yaya abdulrahim ina wuni,
Lafiya lau sisi yajikin ki?,
Naji sauki sosae gashi ma ina shirin zuwa muku wuni yau,
Kin cika yawo kuma gashi lafiyar ma bata isheki ba to yau bama nan,
Kuna ina yaya,tafada muryarta kamar zatayi kuka,
Muna asibiti safna ta sauka dama shinakira nafada miki,
Wani ihu datayi seda tasauke wayar daga kunnensa,
Tsaya mana hajiya,
Yaya me muka samu?,
Baby boy,
Aiko ganinan zuwa dama a shirye nake,
Bata jira ya amsaba ta katse wayar,
My man tashi muje asibiti safna ta sauka munsamu baby boy,
Alhmdllh, amma kidaina wannan tsalle tsallen karki mana wata barnar,
Murmushi kawai tayi tace bari naje Na fadawa Momy kilama zata bimu takaiga jika,
Dariya kawai yayi yabi bayanta,
Bayan ansallamesu abdulrahim yayo gidansa da ita badee takirashi awaya,
Nace kamayarda safna gida acan zatafi samun kulawa lubna tace kayi can gidanka da ita,
Yanzu mama seta koma gida?harfa se bayan kwana arba’in,
To rashin kunya zaka yimin?,kokuma shawarar ka nanema?,
A’a yace murya a sanyaye,to kamaida ita gida zatafi samun kulawa,
Badan ransa yasoba yai yadda badee tace,
Yanzu cikin lubna yana wata hudu kenan,
Yau ake suna kasancewar gidan za ayi suna yasa en uwa zuwa suka tare part din lubna tunda sassafe zasuyi aiki,
Ta fito zata fada musu ga abinda za ayi Mus’ab yajnyeta daki sunyi jira har sun gaji Dan haka suka fara gyara kayan miya,
Ke Zainab tunda ke gidan yayanki ne danje ki kwankwasa musu rana keyi fa ga mutane sun fara zuwa amma ba agama abinci ba,
Zainab diyar kawunsa ce zuwa tai ta kwankwasa kofar lubna na zaune gefen gado da hand dryer hannunta tana busarda gashinta Mus’ab kuwa yana tsaye yana Daura agogo tsintsiyar hannun sa tace waye? Zainab ce wai anty juwairiyya tace kifito rana nayi basusan meza afara ba,
Zainab ki shigo bana jinki,itakam tsaye tai jikin kofar taki shiga Mus’ab yagama shirin sa yai mata sallama ze fita taimasa Allah yakiyaye ,
Kishiga mana Zainab kika tsaya anan,shiga tai duk kunya ta isheta tace,
Yaya lubna aiki fa mukeda kikazo kika zaunan nan tundazu,
Laifin yayanki ne meyasa baki masa fada ba seni zakizo kinawa Turin baki nidalla mikomin doguwar rigata cikin wardrobe dinnan tafarko daga sama zaki ganta nasa mutafi karku cini gaya babu miya,
Dariya Zainab tayi tace to kiyi sauri,
Atakaice dai sunan yayi dadi yaro yaci suna abubakar sadeeq Allah yaraya mana,
Ramla ma ta haihu tasamu baby girl sunanta Aisha juwairiyyan abduljabbar ma ba abarta abayaba seda ta suntulu yarta mace kamar lubna tayi kaki,nan abduljabbar yaiwa badee’a takwara suna kiranta mami,
Lubna kadai ta rage ta sauke nata Dan har ta koma gida saboda kumburi babu abinda take iyayi se salla shima dakyar tana numfarfashi har ta gama badee bata bari tai komai kullum tana kwance,
Lubna tana zaune wayar badee na gefenta taga yaya asama’u Na kiranta miqewa tai dakyar tayi hanyar palon majid da wayar a hannunta,
Majid na zaune kan doguwar kujera badee tayi pillow da kafafuwansa da alama ma bacci take dasauri lubna ta juya zata fita majid yace,
Daughter zo mana ko jikin ne?,
A’a baba wayar mamace ake kira shine nakawo mata ta ajiye wayar kan center table tafita da murmushi a fuskar ta,
Se sukan la’asar badee ta farka da sauri ta miqe saune,
Haba majid meyasa kabarni inata bacci haka?gashi nace yau dambu zamuci komai ban shirya ba,
Hmm gadai wayar ki lubna ta kawo yaya asama’u nakira,
Zaro.ido tai tace lubna taganmu a haka?,eh mana amma wayar kawai ta ajiye ta fita,
Aiduk laifinka ne seda nace zanje daki nakwanta kace nai kwanciyata anan yanzu gashi kaja ta ganmu duk kunya ta kama ni,
Dariya kawai yayi yace ji yadda kikayi da fuska kamar wata yarinya nidai kije ki matsa mata kafafuwanta naga sun kumbura,
Wallahi haka suke kullum ko jiya seda najira tai bacci nima nayi segumi take duk sanyin dakin tausayinta nakeji bata taba jin dadin cikiba,
Nima ina tausaya mata ganin kotafiya dakyar take yi amma ai takusa sauke wa Allah dai yasauketa lpy,
Ameen bari inje indubata,
Washe gari tunda ta tashi sallar asuba take jin abubuwa amma dai ta daure har gari yayi haske,
Dafa gadon tayi zata miqe ta kasa jin yadda bayanta ya riqe tace washhh,dasauri badee ta taso,lubna ko abinne?,
A’a bayana ne kawai naji yariqe,😳kuma kikace a’a?, ina wayar ki nakira Abdulqadir yakaimu asibiti,shiru tayi zufa naqaryo mata,pillow badee ta daga tadauko wayar dasauri takira abdulqadir jikinsa har rawa yake daga masallaci yadawo gida dasauri,
Lubna kiyi kokari ki tashi muje mota mana,
Mama wallahi kodaga nafara bazan iya yiba,to bari nakira abdulqadir Yakama min ke,kusan karo sukayi tace zoka kamamin wai bazata iya tafiyaba,
Yana zuwa ya sureta se mota se cije baki take tana runtse ido sosae,
Dasauri aka karasa da ita labour room Sega Mus’ab kamar ze tashi sama yashige dakin,
Har karfe goma na safe babu wani labari,ta wahala iya wahala saboda girman babyn se kusan karfe goma sha biyu ta haifi namiji ni narasa dawa yaron ke kama gashinan babba kamar insace ingudu.
Rawa naringa yi ina murnar zamusha biki sedai wani Abu Dana tuna yasa jikina yai sanyi😔
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017.
Second to d last page
Page 45
Baka tafi kabarni ba gashinan ankawo wata tsohuwa secin zalina take,inji lubna dake waya da Mus’ab,
Metai miki?,yatambayeta da muryar murmushi,
Muna fa zuwa ko zama banyi ba mama tasa tamin wanka daruwa me azabar zafi,
To kiyi hakuri taimakonki take ina baby,
Yanacan hannun mama tana shirya shi shima anmai wanka shima naji se tsala ihu yake,
To kije ki rarrashe shi mana,ta zaro ido tace rufani ka sayani kar kasa mama ta fige ni dama tana cewa banida kunya,
Dan kinrarrashi danki shine bakida kunya?,eh mana kaibakada labari ne dama ba Dan fari bane bari inci abinci zan baka labari yunwa nakeji,
To bye luv u,luv u too my man,
Dakin badee suke zazzaune duka matan sa’anninta Sega badee tashigo da baby karbi lubna bashi nono yaronma yanada dangana tunda yazo duniya benemi abinci ba se bacci yake,
Karbar sa tayi tana kallon su safna kasa kasa itafa akwai matsala yaza’ayima shekara da shekaru tana boyon Abu yau kawai bainan nasi ace taciro shi kowa yagani hijab ta janyo tasa ta tura babyn ciki,
Ke meye haka?inji badee,
Mama nikam wallahi banaso suganmin jikina,
Yo naji wani shashncin banza jama’a Ku tayani gani ko a tarihi bantaba jin wannan labarin ba,
Aiko mesu safna zasuyi ba dariyaba,
Ke zaki ciro mamman kibashi yadaina mana kuka kokuwa senazo naciro dakaina?,
Toni ban iyaba,dada kika kunshe cikin hijab mezakiyi?,tana masifa tanuna mata aiko yana kamawa ta fizge tana ihu,
Wallahi lubna watan cin ubanki ne yakusa kamawa Dan marinki zanyi zaki kamane yadai tsallar masa a fuska kose yayi kuraje?,
Wallahi mama zafi bakiji ba daya kama,ai kowa da haka ya saba ki kama dalla malama yaro yunwa yakeji shayarwa yazama wani jidali kuma,
Sudai su riyya se dariya suke,lubna kuwa harda Dan kwallanta ita anganemata jiki kuma gashi tanajin zafi,
Nikam murna kawai nake yaune suna danhaka nace sena yanki en biki Kure adaka zanyi nadauko kayan sallana a kasan akwati domin yaune suna,
Inacikin shiri cikin Dan ubansun lace dina sega momma na (Zainab inuwa #antysis) tashigo cikin shirin ta nace mama wannan wankanfa inazuwa?,
Tare zamuje Dan bazan yadda kije kina tsokanar meela ba kuma gakida Dan iskan kwadayi,duk inda raina yake seda yabaci dn bazan manta ba bikin jawaheer ma haka taimin seda nasha ranqwashe ko babbar tusa hanani tayi,
Haka nagama shiri ina ta turin baki harna shiga mota muka tafi ban daina fushi ba Dan nasan ba zanci rengem ba yau,
Tun gate na hango meela dasauri na dauke kaina araina nace mummuna kawai kamar ba er gidanmu ba,
Mamaki ne ya cika ni lokacin Dana hango ayarin en gidan Sophie G kowa tadau wanka sunkame akan kujerun roba se hankadar mutane suke,
Can Na hango su anty billyn Abdul,cute Zara,maman Nana,anty badee social,baby nurse daga gefe se yagar naman rago suke aiko idona nakansu se hadiyar yawu nake,kyakkyawan rankwashi naji senaci uban makiyanki bikin nan bazamu jima ba Dan bazaki sani kunya abinda kikeyi ko sultan bayayi kwadayi kamar mayya,
Nidai se zare ido nake nasan banida gaskiya meela tabiyo gefen mu tace andai ji kunya kwadayayya kawai,nace wallahi zamu hadu yanzu Dan kinga mamane kinsan bazata bari muyi fada anan ba,
Biki yai biki se shagali ake mama takasa ta tsare haka naita kumburi ga ankawomana abinci ta nama anhanani ci dole na dangana atakaice dai banji dadin bikinba,
Gaisawa kawai nayi da en gidan ZBI mama tasani agaba mukayi gida bayan anbiyomu dakayan bikin anan nema naji sunan yaro Muhammad,
Har mukaje gida bakina kamar zetabo bango,haba sweetheart zokiji banason wannan fushin yi hakuri banaso kina fada da meela yayarki ce kingani kuma kwadayi bakyau kinji kidaina,
To mama insha Allah nabari daga yau,yawwa er albarka Allah yanunamin aurenki,ai a 360 nabar palon ina rufe fuska naji kunya amma akasan zuciyata se ameen nake cewa😉,
Allah ya raya mana muhammadu ameen.
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y’AY’ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017.
LAST PAGE
Inaso Ku saurareni dakyau kunga yadda rayuwa ta zame mana inaso Ku dauki rayuwar duniya abakin aure Ku masu mata kuriqe matayenku da kyau kuriqesu irin riqon dazakuyiwa kanku yayayenku Ku kasance masu kula da rayuwarsu da tarbiyarsu lubna kekadaice mace kiriqe mijinki dakyau kikula da tarbiyar yayanki kiyi yadda kikaga inayi sirrin mijinki shine babban abinda zaki boye lubna kinji labarina kuma kingani da idonki don Allah Ku taimaka Ku kasance masu riqe amana kuma kusani kune ABIN ALFAHARI NA,
Nan sukayi murna kowa zuciyarsu fess majid dake jikin kofa yashigo yana cewa,
Madalla da samun mata irinki madalla da samun uwar yaya irinki badee’a hakika nima Y’AY’ANA ABIN ALFAHARI NA ne,
Murmushi sukayi sukace madallah da samun iyaye kamarku muma muna alfahari daku,
Allah yai muku Albarka yasa mugama daduniya lafiya,ameen muka amsa harnima.
ALHAMDULILLAHI
Anan na tattaro alqalamina