ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH
Washegari!!+
ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA
Kwance take a kan gadon dakin shi wuraren qarfe Goma da rabi na safe tana bacci.. wayarta da take ringing (Video call) ce ta tashe ta daga baccin.. Ko da ta duba gani nayi tayi murmushi yayinda ta gyara kwanciyarta tayi answering..
A yau din dai tun da safe Zayd ya tafi ofis a dalilin zai yi wani brief meeting da wasu clients da suka zo daga Sokoto..
Shi ya hada musu breakfast suka ci sannan ya wuce.. Gaba daya ya shagwaba Ameera, komai shine yake yi mata. Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ta koma kan gado ta kwanta don ta samu enough sleep and rest.2
Wuraren qarfe tara da rabi suka gama meeting din a nan office dinshi ya sallame su.. tun daga nan kuwa ya kasa yin komai.. gaba daya tunanin shi ya koma kan Ameera. A rayuwar shi bai taba sa ran mace zata birkita mishi qwalwa ba haka, bai taba sa ran akwai lokacin da zai ji baya iya yin aikin shi da yake so with passion ba tare da ya ji muryar wata mace ba..
Yayi yunqurin kiran ta countless times amma yayi tunanin qila bata tashi ba.. a haka har qarfe Goma da rabi tayi and ganin cewar bazai iya jurewa bane ya kira ta.
“Habibi”
Zayd wanda yake kallonta yana murmushi yace “Habibty sorry I woke you up.. tunda na gama meeting dina nake so in kira ki sai nayi tunanin baki tashi ba, yanzu ma I thought kin tashi ne shiyasa..”
“ssssshhhh.. it’s okay my love, ka fi komai muhimmanci a rayuwa ta. tell me, ya ofis??”
Resting bayan shi yayi a executive chair dinshi yace “boring Habibty, gani nan ina ta missing dinki, na kasa yin komai..”
fashewa tayi da dariya yayinda ta tashi zaune tace “subhanalillah.. toh yanzu ya za’a yi??”
Kai tsaye yace “ki zo..”
Zaro idanuwa tayi tace “inyi maka me Habibi??”
“I just want to feel your presence.. please come. I promise you bazamu dade ba zamu koma gida kin ji??”
Turo baki tayi tace “Wallahi Habibi ka cika rigima.. ka dai san tun jiya na fadi maka mai kitso na zata zo tayi mun ko?”
“kar ki damu zanyi miki.. Kira ta ki ce tayi zamanta”
Zaro idanuwa tayi ta fashe da dariya tace “ban gane zaka yi mun ba.. ka iya ne??”
“ban iya ba amma zanyi browsing in gani.. I am sure babu wahala.. don Allah tashi kiyi wanka ki zo.. ina jiran ki”
“Huh.. toh na ji, gani nan zuwa kuma dagaske sai kayi mun kitso idan muka dawo.. deal??”
“deal Habibty.. sai kin zo. I love you” ya huro mata kisses yayinda ta sa hannu ta cafko su tana murmushi itama tace “I love you more my love”
Bayan sunyi sallama ne ta sauka daga kan gadon ta shiga dressing room dinshi tayi shirin wanka.
Dama dai tun jiya ya kwaso mata kayanta dayawa ya jera mata a wadrobe dinshi.. a cewar shi dakin shi ya zama nata.
☆☆☆☆☆☆☆☆
CITY-SHELTERS
ALI AKILU ROAD KADUNA CENTRAL
STORY CONTINUES BELOW
Wuraren qarfe Goma sha daya da minti arba’in da biyar Ameera ta iso kamfanin.. Driver ne ya kawo ta a cikin wata dalleliyar Range Rover evoque sabuwa gal.
Customised Plate number na motar ce ta tabbatar ma securities din cewar daga gidan ogan nasu ne..
Driver yana fakawa a porch na entrance ne securities suka rugo a guje don kawo gaisuwa.
Ameera wadda take zaune a cikin motar kuwa tana ta hira da qawarta Zarah a waya wadda take ta tsokanar ta akan ta bi miji ofis saboda naci da tsabar soyayya yayinda take ta qoqarin defending kanta..
Bayan ta gama wayar ne ta ga mutane a tsaye kusa da motar.. ta sa hannu zata bude ta ji anyi saurin budewa..
Ko da ta fito sai gani tayi suna ta duqawa yayinda suke ta gaishe ta kowa yana so a ji muryar shi.. Ita gaba daya ma ta rude ta kasa amsa su
Ikon Allah, wai yau ita Ameera ce mutane suke ta rawan jiki wurin gaishe ta.. who would have thought so??
Babu shiri ta dinga amsawa kanta a duqe yayinda take a rude.. da sun san how confused she is a wannan lokacin da sun haqura da gaisuwar sun qyale ta..
Dago kan da tayi ne ta hango Bilal tsaye a bakin entrance din yana murmushi..
Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin “thank God I see a familiar face..”
Shima dai cikin girmamawa a matsayinta na matar ogan shi ya qaraso wurinta yace “sannu da zuwa Madam, he told me you were coming.. this way please”
Murmushi tayi tace “thank you”
Aikuwa suna shiga kamfanin ma’aikata suka fara tasowa da sauri suna gaishe ta harda russunawa..
Kar ku manta Hotunan Ameera sun zagaye social media don haka babu wanda bai gane ta ba..
Ita dai har ga Allah bata son haka, gaba dayan su sun girme ta but they keep bowing down kamar ita ce mai kamfanin.. A rude ta dinga amsawa yayinda take ta murmushin dole..
Bata samu sauqi ba sai da suka isa wurin lift (executive lift meant for the CEO) ya bude suka shiga.
Haka ta wuce ta bar ma’aikata suna ta maganarta yayinda suke yaba simplicity dinta.
A cikin lift din ne ta saki ajiyar zuciya tare da fadin “what a relief”
Bilal ya fashe da dariya yace “kar ki damu, you will get use to this.. it will be just double in Lagos and maybe triple in Abuja..”
Kafin ya rufe bakin shi tace “what?? please Nooo, I cant deal with this..”
A daidai nan ne lift din ta bude kanta alamar sun iso yayinda yake ta yi mata dariya..
Adriana wadda take zaune a kujerar ta kuwa ganin Ameera ne tayi saurin miqewa ta russuna tare da fadin “Good morning Madam”
Ameera ta kalli Bilal in a low tone tace “not again..”
Girgiza kai yayi yana murmushi shima in a low tone din yace “sorry ma’am”
Ameera tana murmushi tace “good morning Miss. Adriana”
(She saw her name tag on her table)
“Can I see your boss??” Ameera ta tambaye ta wanda hakan ya sa suka fashe da dariya ita da Bilal.
Adriana dai ta kula neman magana Ameera take yi.. ita ta isa ta hana ta shiga ganin mijinta ne??
Kai tsaye tace “please go right ahead Ma’am”
“thank you” Ameera ta fada yayinda Bilal wanda yake dariya yace “toh ni bari in koma, dama fita zanyi sai na dawo”
“sai ka dawo.. nagode sossai”
STORY CONTINUES BELOW
☆☆☆☆☆☆☆
Zayd yana zaune a kan kujerar shi riqe da wayar shi.. a yadda ya qura ma wayar idanuwa zaka rantse wani abu yake yi nan kuwa hotunan Ameera ne ya sa a gaba yana kallo.. hotunan da yayi snapping dinta jiya a lokacin da take tsaye gaban aquarium.
Qwanqwaso qofar tayi ta shigo tare da fadin “Assalam Habibi”
Zuciyar shi ce tayi sanyi a dalilin ganin Ameerar shi.. matar
shi wadda ta dagula mishi lissafi gaba daya..
Da sauri ya miqe yana murmushi yace “wa’alaikis salam Habibty..” ya ware hannun shi yayinda ta ruga tare da jefar da hand bag dinta ta shige jikin shi ta maqale kamar wata mage..
Yana shaqar qamshin ta mai dadi ne yace “Habibty kin yi kyau sossai”
Murmushi tayi tace “nagode Habibi”
Sanye take cikin rigar Jallabiya baqa sannan ta nada gyalen a kanta.. Da ganin wannan jallabiyar ka san ta ja kudi domin kuwa ta hadu iya haduwa sannan ta dace da Ameera sossai.. tana cikin wadanda aka sanya mata a kayan lefen ta..
Sunyi kusan minti uku rungume da juna sannan yayi breaking hug din ya janyo ta wurin kujerar shi ya zauna sannan ya zaunar da ita a kan cinyar shi.
Tana shafa sajen shi tace “toh gani na zo.. hope komai ya zama normal yanzu??”
Girgiza kai yayi alamar a’a
“kuma dai?? toh me kake so??” ta tambaye shi kamar yadda ake yi ma yara irin cikin sigar lallashi dinnan yayinda take birkita gashin kanshi wanda hakan yake yi mishi dadi don kuwa har lumshe idanuwa yake yi..
“I want a hot and passionate kiss Habibty, irin wanda kika yi mun da zan zo ofis dazu.. shine zai yi reviving qwalwa na.. yanzu haka ji nake yi kamar an toshe mun ita”3
Ameera wadda ta fashe da dariya sossai Zayd yake bata mamaki.. wai dama haka yake da rigima? a da fa tayi mishi kallon babu ruwan shi ashe ashe shima Oga ne..
“ka samu Habibi.. I love kissing you”
Daga nan kuwa ta hade bakin ta da nashi ta shiga aika mishi da hot kiss kamar yadda ya buqata.. sai da suka yi mai isar su sannan suka saurara.
“thank You” ya fada with a sigh of relief
“anything for my cute husband” ta fada tare da Jan kumatun shi wanda har sai da yace “ouuchh”
Tana dariya ta juya ta dauki Mug na tea dinshi tayi sipping sannan tace “ofis dinka yayi kyau sossai Habibi.. da fa kullum idan ina wucewa sai inyi ta kallon ginin ina mamakin yadda aka yi using glass aka yi gini mai tsawo sannan mutane na zama a ciki..”
Fashewa yayi da dariya yace “and here you are inside it as the owner..”
“Wife of the owner dai..”
Girgiza kai yayi yace “duk wani abu da na mallaka a duniyan nan naki ne Habibty.. this office is yours my love”
Tana murmushi tace “ni kai kadai nake so ka zama nawa Habibi.. ina bala’in son ka”4
“ni naki ne Habibty, I love you very much too”
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Bilal ya fito ya shiga motar shi qirar latest Audi sabuwa gal sai walqiya take yi.. yana shirin yin reverse ne na ga ya tsaya yayinda yayi saurin kallon side mirror da kyau a dalilin hango ta da yayi..
Layla???3
Gani nayi ya juya da sauri don ya tabbatar da lallai ita din ce..
tabbas ita ce!
STORY CONTINUES BELOW
“what the hell is she doing here??” ya tambayi kanshi yayinda na ga yana kallonta ta madubi har ta shige cikin kamfanin.
Har ya bude qofa zai fito sai kuma na ga yayi saurin going against it yayinda yayi janyo wayar shi yana murmushi.3
Wata lamba yayi dialing wanda aka yi answering instantly.
“hello Marilyn.. this is Bilal, there is a girl in front of you requesting to see the CEO please let her through..”2
Bayan ya kashe wayar ne na ga yana dialing wata lambar yayinda yace “zaki gane baki da wayau.. useless gold digger”
Reverse yayi ya fice abinshi yayinda yake jira ayi answering call din da yayi placing..
Ni kuwa nace anya Bilal ka kyauta da kace a barta ta shiga kuwa?? lallai kwallin Malam yana daf da yin aikin shi..8
☆☆☆☆☆☆☆☆
Marilyn daya daga cikin receptionist ta kamfanin wadda ta gama magana da Bilal ta intercom dinta ce ta ajiye yayinda ta kalli Layla wadda take tsaye tana kallonta.
“uhm sorry, I am here again to see Mr Zayd..” Layla ta fada hoping yau din za’a barta ta gan shi.
Ga mamakinta kuwa sai ta ji Marilyn tace “Go to the 5th floor and you will receive further directives from there”
Layla dai shiru tayi na seconds yayinda ta cika da mamaki.. kwana nawa kenan tana zuwa neman shi ana yi mata wulaqanci amma kuma yau haka kawai aka bata go ahead??? could it be her lucky day??
“thank you” ta fada yayinda ta nufi daya daga cikin lifts din da ta ga mutane suna shiga..
Layla dai anyi directing dinta har wurin Adriana wadda bata dade da yin waya da Bilal ba.. kamar dai yadda ya umurci Marilyn haka yayi ma Adriana amma this time ya sa ta kira Zayd ta sanar da shi zuwan Layla.. he is sure he will let her in, well atleast he is hoping so!3
Ameera tana nan zaune akan cinyar shi yayinda suke ta hirar su ta soyayya.
Wayar intercom dinshi ce tayi ringing yayinda yayi answering.
“What???” ya danyi shiru yana kallon Ameera sannan kuma yace “okay Adriana, let her in”
Tun kafin ya ajiye wayar ne Ameera ta yunqura zata tashi yayinda yayi saurin riqe ta yace “ina zaki je?”
“ba na ji kayi baquwa ba? I shouldn’t be sitting here while..”
“Sssshhh.. ba baquwa bace Habibty, its your sister Layla”
Tun kafin ya rufe bakin shi ne tace “what??” yayinda wani mugun kishi ya taso mata.
“me take yi a office dinnan?? wai dama…”
Hugging dinta yayi very tight sannan yace “hey relax my love, kin riga kin sani cewar ko Mata sun qare a duniya bazan taba daukar Layla ba.. she disgusts me.. Ameera you are my queen daga nan duniya har gidan Aljannah insha Allah.. daga ke na rufe qofa don kuwa babu wani abinda nake nema wanda baki da shi.. I love you very much”
Wani irin sanyi ta ji a zuciyarta..
Yayi breaking hug din da yayi mata sannan yace “come here.. give me a kiss”
Aikuwa da sauri ta hada bakinta da nashi ta fara kissing dinshi..
A daidai nan ne Layla ta shigo ofis din..
Zuciyarta ce ta buga a dalilin abinda idanuwanta suka gano mata.. Dukda bata ga ko wacece ba ta tabbatar Ameera ce because her small figure says it all..
Qarar qofar da Layla ta rufe ce ta dawo da su yayinda suka juyo suna kallonta..
Layla wadda qirjinta yake ta zafi yayinda qafafuwan ta suka yi mugun sanyi da qyar ta qarasa shigowa tana kallon su kamar yadda su ma suke kallon ta.
STORY CONTINUES BELOW
Sanye take cikin dinkin doguwar riga ta fitted gown wadda ta kama ta sossai.. Gaba daya shape dinta ya fito.. with a deep neck as usual revealing part of her boobs. Bata daura dan kwalin atamfar ba sai ta yafa dan qaramin gyale a kanta wanda ya bayyanar da dogon gashin ta… fuskarta dauke da make-up.
Zuciyar Ameera sai tafasa take yi ganin yanayin shigar ta.. wato ta biyo shi office don tayi seducing dinshi!
“Ina wuni Zayd..”
Zayd dai gaba daya ma haushin kanshi yake ji da har ya bata lokacin shi akan Layla a baya.. tambayar kanshi yayi meye abun so a wurin ta? how can he even marry someone with this level of exposure??
Ji suka yi yayi tsaki tare da kawar da kanshi.. Ameera ce tayi saurin kallon shi.. ta kula gaba daya fuskar shi ta canza zuwa kalar rashin mutunci.
Ita dai Layla bata damu ba.. tunda dai ta samu ganin shi an gama.. Mission dinta shine ta tabbatar ya kalle ta cikin ido yadda kwallin da ta shafa da sunan shi zai yi aiki.2
Aikuwa zama tayi a kan kujera ta sa mishi idanuwa babu ko qyaftawa… kallon da ya bala’in ba Ameera haushi.
“me kike yi anan??” ya tambaye ta yayinda ya kalle ta straight in the eyes.
ghen ghen ghen…3
Zuciyarta tana
bugawa yayinda ta tsorata da irin kallon da yake yi mata.. banda don kwallin da ta sanya wanda take so su hada idanuwa da ta bar ofis din a guje because she already sensed trouble..
“na zo in baka haquri ne..”
“haquri akan me?? you made your choice and I hold no grudge Layla so..”
“if you dont.. meysa kake wulaqanta ni??”
Ita dai Ameera tana zaune tana sauraron ikon Allah.. me Layla take nufi kenan??
“….A gaskiya tun farko ka sani cewar ni bana son ka amma dukda haka ka nace mun.. tabbas kai kyakyawa ne, ka iya soyayya amma kuma bakada kudi.. A duniyan nan kudi suna da matuqar amfani a rayuwar dan Adam domin kuwa da su ake yin komai.. A yau ka duba ka gani, idan ka aure ni a wane irin gida zaka ajiye ni?? Ciki da falo??? me zan ci??? tuwon masara da miyan kuka??? me zan sa?? atamfar roba-roba??? a me zaka kai ni unguwa??? tsohon mashin dinka??? me zaka bani??? SOYAYAYA cikin TALAUCI?? a’a wallahi bazan iya ba.. bazan tashi a maneji in fada ma talauci ba don haka kayi haquri ka nemi daidai da kai don wallahi na fi qarfin ka ta ko’ina…” Zayd ya qarasa maganar yana kallonta cikin ido
Ni kuwa nace uhm uhm Zayd.. hattara da kwallin Malam!!
Ameera ta zaro idanuwa tana kallon Layla cike da mamakin wadannan kalaman.. was that actually what she told him the other day???
Layla wadda jikinta har rawa yake yi saboda mugun da-na-sani da tayi ce ta duqar da kanta cike da kunya..
“those were your exact words to me Layla and kamar yadda kika bani shawara, nayi amfani da ita.. na samu perfect lady wadda take daidai da ni, she is right here with me”
Ya ja kumatun Ameera yana murmushi yace “Ita ce ZABI NA.. the most beautiful thing I ever had in my life.. My soulmate. She is irreplaceable in my heart..”
Yayi mata kiss a kumatu ya cigaba da fadin “..Ba da zuciya kawai nake son ta ba, da raina nake son ta.. She is my everything and I can’t live without her”
Ameera wadda ta cika da farin ciki sai da ta saki ajiyar zuciya yayinda ta runtse idanuwanta ta bude tana murmushi…
Kiss tayi mishi a kan kumatun shi tare da birkita gashin kanshi tace “thank you Habibi.. I love you, soo very much”
Murmushi yayi mata sannan ya juya ya kalli Layla wadda hawaye suka fara wanke ma fuska yace “it’s time for you to go.. gwara ki tafi da qafafuwan ki kafin in sa a fitar mun da ke because you are seriously invading our privacy”
Layla dai jin haka sai ta miqe jiki yana rawa ta fice domin kuwa a wannan lokacin ji tayi numfashinta yana neman daukewa… Ba’a taba wulaqanta ta ba a duniya irin yau.
Tambaya take yi ma kanta shin Kwallin da ta sanya bai yi amfani ba kenan ko me??5
Adriana dai sai ganin Layla tayi tana ta bin bango yayinda take zubar da hawaye.. Sossai ta cika da mamaki amma tayi watsi da ita.. da alama dai ba mutumiyar arziki bace shiyasa ma har Bilal ya kira ya bada directives akanta.. it was more like he planned for this to happen and haka kawai sai ta tsinci kanta cikin farin ciki da hakan ya faru.
A haka dai da qyar ta bi bango ta shiga lift din.. Kuka take yi na fitar hankali. Gaba daya sai kallonta ake yi har ta fita daga kamfanin.. the most embarrassing moment of her life.GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI+
Kwance take a kan gadon Mama tana ta rusa kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.
Layla dai da qyar ta iso gida bayan ta baro kamfanin Zayd. Babu abinda yake kai da komowa a qwalwarta sai kalan wulaqancin da Zayd yayi mata..
Mama wadda take zaune tayi tagumi mamaki ne ya hana ta magana..
“toh wai ban gane ba.. kenan kwallin malamin bai yi aiki bane ko me??? ko dai bai kalli cikin idanuwan naki bane?”
“wallahi Mama ya kalli cikin idanuwana.. idan kika ga irin kallon da yayi mun ma sai kin tausaya mun.. Zaune fa na ganta a bisa cinyar shi suna ta sumbatar juma kamar zasu cinye juna.. Yanzu fisabilillah ta ina wannan baqar banzar ta dace da shi?? Na shiga uku yanzu shikenan Ameera ta cuce ni a rayuwa..” Layla ta fada tana kuka.2
Mama wadda kanta yake a kulle ta mirgina ta janyo wayarta tana fadin “aikuwa bari in kira Hajiya Suwaiba, ya za’a yi in sakar mata kudi har naira dubu dari tara sannan ace ba’a samu yadda ake so ba.. ai wannan ma zancen banza ne”
Bayan ta latsa lambar Hajiya Suwaiba ne tayi answering.. Mama ta sanya wayar a speakerphone yadda Layla zata ji.
“Hajiya Hindatu muna lafiya??”
“Hajiya Suwaiba ai babu zancen gaisuwa.. Ga yarinya ta yi ido hudu da yaro amma babu abinda ta samu sai wulaqanci, me ke faruwa ne??”
Shiru suka ji ta dan yi sannan tayi gyaran murya tace “ban gane wulaqanci ba.. in ce dai ta kira sunan shi sau uku kafin ta shafa kwallin??”
Cikin muryar kuka Layla tace “wallahi na kira sunan shi sau uku kamar yadda kika fada”
“Layla ki daina kuka.. dama na manta ban sanar muku ba.. Malamin yace akwai wadanda jinin su yake da qarfi don haka suna yin kwana biyu zuwa uku kafin maganin yayi tasiri akan su.. ina kyautata zaton wannan din yana da jini mai qarfi ne, idan har kin tabbatar kunyi ido hudu da shi mu jira nan da kwana ukun ina mai tabbatar miki cewar zai biyo ki har gida..”
“haba, yanzu na ji batu Hajiya Suwaiba.. ina nan har na fara tunanin kudaden da aka kashe ace babu sakamako mai kyau ai abu bai yi ba” cewar Mama wadda harda sakin murmushi.
“ai kar ki ji komai Hajiya Hindatu.. magani dai yana nan zai yi aikin shi”
A haka dai suka cigaba da hirar su yayinda hankalin Layla ya dan kwanta..3
☆☆☆☆☆☆☆
GIDAN HAJIYA SUWAIBA
BADARAWA
Zaune take a falonta tare da qawar ta Hajiya Barira a lokacin da take waya da Mama.
Bayan sunyi sallama ne ta gyara zama tare da kallon Hajiya Barira tace “yau na shiga uku na ci kudin cizo.. aikuwa akwai matsala”
“ke kuwa wace matsala tunda dai kin riga kin gama da su.. ai kawai dagewa zakiyi akan lallai yarinyar bata yi amfani da kwallin kamar yadda ya kamata ba shiyasa aikin bai yiwu ba..” Hajiya Barira ta fada tana murmushi.
“ai baki sani ba.. Hajiya Hindatu muguwar taqadara ce.. wallahi idan nayi sake zata iya wulaqanta ni a dalilin wadannan kudade da na danne..”
Asali dai Hajiya Suwaiba ko da ta je gaban malaminta a garin Hadeja tayi mishi bayanin komai da abinda ake buqata.. ko da ya bubuga qasar shi ya duba ya gani ya fadi mata gaskiyar lamarin.. Gaskiyan lamarin kuwa shine babu wanda zai iya raba auren Ameera da Zayd, idan kuwa mutum yayi qoqarin raba su toh zai shiga babban matsala a rayuwa idan har bai rasa ran shi ba don haka yace bazai taba sa hannun shi a abinda ya fi qarfin shi ba kuma ya ba Hajiya Suwaiba shawara akan ta cire hannunta a lamarin domin kuwa ita kanta bazata gama lafiya ba balle those that are directly involved. Dayake ta riga ta shaqi kudade a hannun Hajiya Suwaiba sai ta ga bazata iya mayar mata da su ba musamman ganin yadda ta debo mata kudin daga qatuwar Ghana-must-go wadda ta tabbatar mata da tana da su dayawa kenan..8
STORY CONTINUES BELOW
Ko da ta dawo ta rasa yadda zata yi shine ta nemi shawarar Hajiya Barira.. and they came up with the plan that’s in action presently wanda da alama qaryar su ta kusa tashi..4
“toh ya wancan maganar tamu?? ai ina tunanin kawai mu aiwatar da komai kafin kwana ukun saboda idan har suka shiga tashin hankali bazasu tuna da zancen yaron ba.. ko ya kike gani??”
Hajiya Suwaiba ta fashe da dariya tace “aikuwa haka za’ayi Hajiya Barira.. Yanzu wane yara yakamata suyi mana aikin??? kin dai san bazamu dauko ‘yan unguwa ba tunda Malali da Badarawa ai babu nisa.. kar a zo ayi saurin gano su”
“Kar ki d
amu Hajiya Suwaiba.. akwai yara da zan dauko daga Hayin Rigasa, ‘yan iska ne na gaske.. kwanaki ma sunyi mun wani aiki kuma na ji dadin shi sossai.. Ke kam kawai ki shirya gobe mu je in yaso sai kiyi musu bayanin komai.. ko ya kika ce?”
“ai haka za’a yi Hajiya Barira.. Allah ya kaimu goben”
toh fa… what are they planning???8
☆☆☆☆☆☆☆☆
A bangaren su Ameera kuwa ko da suka koma gida dai Zancen kitso ya bi ruwa.
Da farko Zayd ya duba a YouTube don ya koya kamar yadda ya fada amma ko alama bai fahimci komai ba.. Ganin lallai bazai iya bane ya dinga roqon Ameera akan tayi haquri ita kuma ta qi.. haka ta dinga dragging wanda shi yana lallashi ita kuma tana tirjewa.. ita din ma da wasa tayi mishi don kuwa ta sani sarai dama bazai iya ba.. A taqaice dai sai da ya kai gwiwowin shi qasa yana roqo sannan ta haqura..
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
2 days Later
GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI
Tun ranar da Hajiya Suwaiba ta tabbatar musu da lallai su jira nan da kwana uku zasu ga aikin malaminta Layla take cikin zullumi.. Gaba daya ko baccin kirki bata samu a ‘yan kwanakin saboda tsananin tashin hankalin da take ciki..
Yanayin da ta ga su Ameera a ranar da ta je kamfanin shi da kuma kalaman da ya fadi mata ya tabbatar mata da lallai ba da wasa yake son Ameera ba, haka tabbas ya auri Ameera ne ba don ya rama abinda tayi mishi ba.. Bata manta irin kallon da yayi mata ba, gaba daya babu digon soyayyarta a idanuwan Zayd.. Tabbas tayi babban kuskure, a yanzu Zayd ya fi qarfin ta nesa ba kusa ba..
Lallai idan har maganin Malam bai yi aiki ba dole ta samu wata hanyar fitar da Ameera daga rayuwar Zayd.. toh wacce hanya zata bi???
Wuraren qarfe Goma na dare tana Kwance a kan gadon dakin da ya kasance nata da Ameera a da yayinda take ta tunani kala-kala.
Wayarta ce tayi ringing.. ko da ta duba sunan qawarta ta gani
Yusrah.
“Ke Layla me ya faru ne kin boye kwana biyu?”
Layla wadda ta gyara kwanciyarta ce tace “hmm.. wallahi Yussy bana jin dadi ne”
“Ki kwantar da hankalinki ki manta da ZAF, tunda dai Ameera yake a aure a yanzu kin sani cewar you stand no chance with him.. plus labarin da kika bamu na wulaqancin da kika yi mishi was terrible.. just move on and continue with your Habib. ko dayake kuma baku shirya ba gashi kin qi ki fadi mana ainihin abinda ya hada ku”
Jin sunan Habib ne ya sa zuciyarta ta buga.. Allah ya sani tayi regretting haduwa da Habib da dukkanin abinda suka aikata.. A dalilin shi ne tayi missing opportunity na zama wife of one of the young billionaire a qasar nan.. a dalilin shi she isn’t a virgin anymore..2
“Yussy don Allah ki daina yi mun maganar Habib kuma maganar Zayd bazan taba haqura da shi ba sai inda qarfi na ya qare”2
“hmmm.. toh shikenan qawata. Ni dama fa na kira ki ne in fadi miki cewar an kawo ankon bikin Maama, zan kai ma tailor din naki gobe kamar yadda kika ce..”
STORY CONTINUES BELOW
“okay toh.. thanks”
“tunda baki gayyace mu na Ameera ba ni na gayyace ki na cousin dina” Yusrah ta fada cikin tsokana.
Maama dai wata cousin din Yusrah ce zata yi aure shine Yusrah ta gayyaci qawayen nata.. asali dai anko kala uku aka fitar wanda ya kama naira dubu saba’in da biyar.. Layla ta biya kudin ankon shine zata kai ma tailor dinta kamar yadda ta buqata..
“Na shiga uku da ke Yussy.. bikin Ameera da aka daura aure bamu sani ba.. tana kwance a gadon asibiti aka daura auren saboda tsabar bala’i.. ai wallahi da nasan za’a daura auren da sai na lalata shi….”
Daga nan fa ta dinga zabga masifa Yusrah tana ta lallashinta har tana regretting dauko maganar.. Da qyar ta sassauta yayinda suka dan taba hirar makaranta da za’a yi resuming next week wanda ita Layla ta gwada bazata koma ba sai semester tayi nisa..
Ko da suka yi sallama zuciyarta sai zafi take yi tana tafasa.. Ban ankara ba na ga ta fashe da kuka.. Kuka sossai kamar wadda zata mutu.. Sai da tayi mai isan ta sannan ta natsu… harda wani dan zazzabi ya rufe ta.
A taqaice dai Layla bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Da asuba Umma ta fito daga kewayen dakin Abba inda ta dauro alwala. A yau din girkinta ne don haka a dakin Abba ta kwana.
A wannan lokacin Abba da su Ibrahim sun tafi masallaci… asali dai tunda yaran suka yi wayau ya fara jan su zuwa sallan asuba don su Saba domin kuwa dama ita take yi ma mutane wahalar zuwa..
Umma ta kabbara Sallarta ne ta ji motsi a tsakar gidan.. alamun tafiya na mutane ta dinga ji.. A haka dai ta cigaba da sallarta har ta idar..
Tana zaune tana dhikr ne ta jiyo ihun Mama da Layla yayinda ta ji maganganun qarten maza.. A firgice ta miqe tsaye tana addu’o’i yayinda ta ruga a guje ta fita.
Gabanta ne yayi mummunan faduwa a lokacin da ta shigo falon.. ta tarar da wasu jibga jibgan maza har guda uku riqe da bindigogi, Layla tana duqe a qasa tana ta kuka yayinda ta jiyo hayaniyar wasu a dakin Mama..
Barayi ne suka shigo gidan!!
“samu wuri ki durqusa ko in bige ki..” daya daga cikin su ya fada cikin tsawa.
Jikin Umma na rawa ta durqusa kusa da Layla wadda take ta kuka.. Ita dai Umma ganin wayar Layla tayi da Sarqoqinta zube a gaban daya daga cikin su.
Bata ankara ba ta ga Mama ta fito tana kuka yayinda wasu qarten Mazan suke biye da ita.. Daya yana riqe da bindiga, dayan kuma yana riqe da Ghana-must-go da kuma wasu sarqoqin.
Ingiza Mama suka yi ta fado wurin su Layla wanda har sai da qugunta ya amsa.. Babu abinda take yi banda kuka yayinda take ta kallon Ghana-must-go din kudin su..
“ita kuma wannan fa??” daya ya tambaya yana nuna Umma.
“Yanzu ta fito daga dakin can..”
“tashi mu je ki dauko mana dukiyar ki..” Umma wadda ta bi ta rikice dukda ta san batada komai jikinta yana rawa ta tashi ta nufi dakinta yayinda biyu daga cikin su suka bi ta..
Bayan dan lokaci sai suka fito da sauri yayinda daya yace “wannan talaka ce oga.. batada komai”
“toh ai tunda mun samu a wurin waccan ku zo mu tafi kafin a taso daga masallaci..”
Layla dai tuni numfashinta yana neman daukewa ganin za’a tafi da wayarta da kudin su..
Mama wadda ta kalli Ogan su ce yace “Don Allah kuyi haquri ku bani jakar nan…”
“idan baki rufe mun baki ba sai na fasa kan ki..” ya fada yana nuna ta da hancin bindiga.
Aikuwa babu shiri ta yi shiru yayinda jikinta yake ta rawa..
Haka suna kuka suna kallo qarten mazan suka fita da dukiyarsu..
Suna fita kuwa na ga Layla tana birgima tana ihu yayinda Mama ta dafe kai tana ta kuka tace “mun shiga uku mun lalace.. shikenan sun gama da mu…”
Umma wadda take ta kuka sai haquri take basu akan kayan su da aka sace.. a tunanin ta kayan sawa ne a ciki.
Abinda bata sani ba kuwa kudade ne a ciki..
Gani tayi Mama ta tashi ta bi bayan barayin a guje tana ihu kamar mahaukaciya.. Layla kuwa tana nan kwance a qasa kamar wadda ta mutu.
Umma dai miqewa tayi ta bi bayan Mama don ta taro ta.. a yadda ta rude kuwa idan an qyale ta zata iya bin titi.
Aikuwa Mama tana daf da gate ne su Abba suka shigo gidan hankali a tashe..
Bayan sun tashi masallaci ne labari ya zo musu shine suka garzayo tare da neighbors dinsu Malam Zakari, Malam Yunusa da Malam Sa’idu.
Su Ibrahim sai kuka suke yi ganin yadda Mama ta bi ta haukace.
“don Allah ku karbo mana dukiyar mu da suka dauka.. na shiga uku ni Hindatu” Mama tana fadi tana ta kuka
yayinda take qoqarin fita.8
Abba wanda ya riqo ta ne yake fadin “haba Maman Layla.. ki natsu mana. Ai tunda suka bar ku da rai da lafiyar ku sai ku gode ma Allah.. me suka dauka??”
Mama dai kuka take rusawa yayinda jikinta yake ta rawa.. Ta ya zata fadi musu jakar kudi ce suka dauka??
Gani suka yi ta juya a guje ta koma cikin gida yayinda su Ibrahim suka bi bayan ta.
Umma wadda take tsaye tana hawaye ce ta fara basu labarin abinda ya faru.. ta dai sanar da su cewar sun dauki jaka wanda ta sa ran cewar kayan sawa ne a ciki…
A nan dai su Malam Zakari da iyalin su wadanda suka fiffito daga baya suka jajanta abinda ya faru yayinda su Abba suka dinga yi musu godiya..
Haka suka tafi suna ta maimaita zancen.. kowa yana ta mamakin yadda basu shiga gidan kowa ba sai na Malam Farouq Abdallah.. sun danganta hakan da qila don ‘yar shi Ameera tana auren mai arziki ne shiyasa..
A lokacin da su Abba suka shiga falo suka tarar da wani sabon tashin hankali..
Layla kwance bata numfashi, da alama ta suma ne yayinda Mama take ta jijjiga ta tana kuka.. Su Ibrahim ma suna nan sun zagaye su suna ta kuka..
Babu shiri Abba ya fita don neman mota a kai ta asibiti..ZAYD AHMAD FADOUL RESIDENCE
UNGUWAN RIMI+
Wuraren qarfe takwas da rabi na safe ne suka fito daga bathroom din dakin shi manne da juna..
Sanye yake cikin bathrobe dinshi yayinda take daure da dan qaramin towel fari sol.. da alama dai wanka suka yi..
Tura ta yayi jikin bango yayinda yake ta baza mata kisses ta ko ina.. Ameera dai gaba daya jikinta ya saki. Allah ya sani bala’in son Zayd take yi.. idan yana romancing dinta wani mugun dadi da farin ciki ne yake ziyartar ta..
Bata ankara ba ta ji ya daga ta cak ya nufi gadon shi ya kwantar da ita..
“Habibi please.. ka manta ofis zaka je??” ta fada muryar ta qasa-qasa
“kin fi ofis din muhimmanci Habibty.. the only thing that makes me happy is you…” ya fada yayinda yake bin ko ina na jikinta da kisses.
Ameera wadda take cike da farin ciki ce ta rungume shi very tight yace “I love you, I love you, I love..” bata qarasa magana ba na ji tace “oouch” yayinda kuma ta fashe da dariya.
Zayd dai ya jefa su duniyar da suke masifar so.. duniyar da take sanya su nishadi.. wadda idan suka shiga ko kadan basu so su fito..
Sun yi nisa a cikin wannan duniyar ne wayar Ameera ta fara ringing.. dukkan su sun ji amma dayake basu so komai ya katse musu jin dadin su sai suka watsar..
A ringing na hudu ne Zayd ya miqar da hannu ya janyo wayar tare da dubawa.. Ganin sunan Umma ne ya sauka daga kanta ya koma gefe tare da miqa mata..
“Umma ce..” ya fada yayinda ya sauke numfashi.
Ameera wadda ta karbi wayar itama numfashi ta sauke tare da gyara muryarta sannan tayi answering.
“Hello Umma ina kwana”
Murmushi tayi ta kalli Zayd wanda shima ita yake kallo tace “ba bacci nake yi ba Umma.. bana kusa da wayar ne”
A wannan lokacin ne Zayd ya janyo Duvet ya rufa mata yayinda ya janyo robe dinshi yana sakawa.
Ameera wadda ta tashi zaune dafe da Duvet din a qirjinta ce tace “Subhanalillah… ya akayi haka Umma?? Ya jikin Ya Layla??”
Zayd dai kallonta kawai yake yi yana jira ta gama wayar ya ji me ya faru…
“Gamu nan zuwa Umma..” daga nan ta kashe.
“Habibty what happened???”
“barayi ne suka shiga gida da asuba..”
Hankalin shi a tashe yace “Subhanalillah.. are they all okay??”
“Yes they are but Ya Layla ce ta suma, suna asibiti..” ta fada yayinda jikinta yake rawa.. tuni idanuwan ta sun cika da ruwa.
Kafin yayi magana ne ya ga ta miqe dafe da Duvet a jikinta tace “don Allah Habibi mu je asibitin mu duba ta..”
Zayd dai shiru yayi yana kallonta.. ya za’ayi ya je asibiti duba Layla?? is Ameera okay??10
Kamar ta san me yake tunani sai tace “We are not just going there to see her ai.. Umma da Abba ma suna asibitin..”
♤♤♤♤♤♤♤♤
GARKUWA HOSPITAL
SULTAN ROAD
Umma ce zaune a waiting room na dakin da aka kwantar da Layla tare da matar Malam Zakari (makwabtan su) suna labarin abinda ya faru.
STORY CONTINUES BELOW
Ko da aka kawo Layla asibiti dai an samu ta farfado, likita ya sanar da su shock na abinda ya faru ne ya dake ta amma komai lafiya don kuwa zuwa yamma zai sallame ta.
A wannan lokacin Abba yana waje tare da Malam Zakari suna tattaunawa.
Ameera ce ta shigo waiting room din hankalinta a tashe.. sama-sama suka gaisa da matar Malam Zakari sannan ta qarasa wurin Umma ta zauna a gefen ta tace “Umma ya jikin nata?”
A yadda ta bi ta rude zaka rantse da ita da Layla sun wani mugun shaquwa ne.
“Da sauqi Ameera.. likitan ma yace zuwa anjima zai sallame ta’
“zan iya ganin ta yanzu?”
Shiru Umma ta dan yi sannan tace “eh toh.. Mama ma tana ciki”
Miqewa tayi tace “bari in shiga in ganta..”
********
Zaune take a bisa gadon dakin yayinda ta jingina bayan ta a bango.. hawaye ne suke ta bin fuskarta babu sassauci.
Mama wadda take zaune kan kujera daf da gadon ce tace “wallahi ba qaramar wauta muka yi ba da muka bar kudaden nan a gida.. da mun sani kinyi Rigista a banki sai mu kai su can.. yanzu shikenan wadannan tsinannun sun taqaita mu..”3
Ita dai Layla a yanzu jikinta yayi matuqar sanyi.. Lissafi kawai take yi na halin da take ciki da kuma yadda rayuwata zata kasance. Tuni ta fara da-na-sanin abubuwan da ta aikata a rayuwa wanda duk laifin Mama ne.
A daidai lokacin ne Ameera ta iso bakin qofar dakin.. tana budewa cikin sallama ta jiyo muryar Layla cikin kuka tana fadin “ni kam da sun bar min wayata ma da na rage zafi… yanzu ta ina zan fara siyan waya??”
Sallamar Ameera ce ta sanya suka dago kai suka gan ta tsaye tana kallon su.
Daga Mama har Layla babu wadda ta iya amsa sallamar.
Gani sukayi ta canza gaba daya cikin ‘yan kwanaki… kai har kyau tayi. A yanzu ma sai suna mamakin yadda basu taba kula cewar tana da kyau ba.. gashi dai tana nan a baqar ta amma kuma sai qyalli take yi.. gaba daya ta cika dakin da qamshin designer turaren ta mai dadin gaske.
“Ina kwana Mama”
Wata muguwar harara Mama ta danna mata sannan ta kawar da kai ba tare da ta amsa ba.
Ameera dai tayi zaton hakan.. Bata damu ba ta qarasa shiga yayinda ta kalli Layla wadda duk ta bi ta zabge, ga fuskarta da ta kumbura tayi ja.
“Ya Layla ya jikin ki??”
Layla dai kasa magana tayi.. Zuba ma Ameera idanuwa kawai tayi yayinda take cike da da-na-sani. she would have been in her shoes right now!!
Mama wadda ta cika da baqin ciki ce tayi tsaki sannan tace “sannu baqar munafuka. Kin zo gulma ko?? kina farin ciki akan abinda ya same mu… toh ki sani, wallahi zaman ki da Zayd yana daf da qarewa don haka..”
Layla ce tayi saurin kallon Mama tace “Don Allah ki yi shiru.. kai na yana ciwo” daga nan ta zame ta kwanta tare da juya musu bayan ta.
Kalaman Layla a wannan lokacin kuwa sai da suka sa jikin Mama yayi sanyi.. akan wane dalili Layla zata dakatar da ita bayan duk a dalilinta take fadi ma Ameera maganganun da take yi???
Ameera ta saki ajiyar zuciya ta kalli Mama tace “Allah ya kiyaye gaba Mama, Allah kuma ya ba Ya Layla lafiya”
Daga nan kuwa ta juya ta fita abinta yayinda ta jiyo Mama tana ta zage-zage.3
☆☆☆☆☆☆
Ameera dai ko da ta fito fuskarta bata nuna kom
ai ba..
Ta tarar da Abba, Umma da Zayd zaune suna magana wanda da alama Abba baya son maganar da ake yi domin kuwa fuskar shi a murtuke take.
STORY CONTINUES BELOW
“Yauwa Habibty, please come and help me talk to Abba” Zayd ya fada yayinda ya nuna mata kujerar da take kusa da shi”
Da sauri ta qarasa ta zauna.
“Uhm muna magana ne akan abinda ya faru shine na bada shawarar su Abba su bar gidan da suke su koma Malali GRA inda akwai security”
Gani nayi Ameera ta kalli Abba da sauri.. tabbas ta sani cewar Abba bazai amince da wannan ba tunda kuwa dama harda irin wadannan abubuwan ya sanya baya so yana relating da masu arziki.. baya so mutane su dinga gani kamar ya aura ma mai arziki ‘yar shi ne don kwadayi da son abin duniya.
“Kamar yadda na fadi maka Abba, dama akwai gidan da na gina tun lokacin da nake tare da Layla kuma wallahi dama na gina shi ne da sunan ka.. ko lokacin da bamu daidaita da Layla ba I still wanted to give it to you because da sunan ka na gina shi and it belonged to you and fortunately I ended up with Ameera and…”
“Zayd kayi haquri ka bar wannan maganar don Allah..” suka jiyo muryar Abba..
Ameera ce tace “Please Abba kayi haquri ku koma can din.. wallahi hankalin mu zai fi kwanciya da hakan. Ka ga tunda irin haka ta fara faruwa bamu san me zai iya biyo baya ba..”
“exactly Abba.. Dukda mun san Allah ne mai karewa but atleast kamar yadda Habibty ta fada.. hankalin mu zai fi kwanciya idan kuna can din”
Wannan karon dai Abba shiru yayi bai ce musu komai ba.
For the first time Umma tayi gyaran murya tace “Abban yara ina gani don Zayd ya baka kyautan gida a matsayin shi na sirikin ka ai ba wani abu bane.. kayi haquri ka amince… ai yanzu an riga an zama daya”
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “toh shikenan zanyi shawara”
Zayd yayi murmushi tare da fadin “Yauwa Abba.. thank you so much”
Daga nan suka shiga hira.
Abbu ya kira Abba a waya yayi mishi jaje… Haka Ammi da Zaheera ma sun kira Umma sun yi mata jaje.
Zayd dai bai nemi shiga duba Layla ba.. Haka kuma su Umma basu ce ya shiga ba.. Sanin abinda ya faru da kuma tension din da ke tsakanin su ma ya tabbatar musu da lallai it’s not a good idea.
A dalilin kiran Zayd da aka yi a waya ana neman shi a ofis ne yayi ma su Abba sallama yayinda ya sanar da su zai turo driver da mota incase za’a buqata. Ko da Abba ya gwada mishi baza su buqaci komai ba tunda anjima za’a sallami Layla still Zayd yayi insisting.
Haka nan dai Abba ya amince… Allah ya sani bai taba ganin mutum mai naci irin Zayd ba.
************
Tsaye suke a wurin motar shi yayinda suke riqe da hannuwan juna.
Zayd wanda yake ta kallonta ne yace “Allah ya sani ina son ki Habibty..” tana murmushi tace “nima bala’in sonka nake Habibi”
Lumshe idanuwa yayi ya bude yana murmushi yace “a tunaninki Abba zai amince..” tun kafin ya gama magana tace “kar ka damu zai amince.. he wouldn’t have told you he’d think about it idan har ba zai amince ba… trust me”
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “thank God”
Ya bude motar shi zai shiga yayinda yace “bari in je ofis dinnan dai Habibty.. I am sure sun gaji da jira.. lateness wasn’t in my character before I married you…”2
“what??? kana nufin ni nake sa ka zuwa latti?? ka manta kullum kai ne…”
Juyowa yayi ya toshe bakin ta yana murmushi yace “it’s still your fault my love.. you are irresistible.. ko kadan bana so inyi nisa da ke shiyasa nake zuwa latti”
STORY CONTINUES BELOW
Janyota yayi jikinshi yace “I love you so much Habibty” ya duqo saitin fuskarta yayi mata kiss a baki.
A rude tace “Habibi.. this is a public place fa…”
“So what?? aren’t you my wife??”
Tana murmushi tace “har gidan aljannah insha Allah”
“insha Allah Habibty”2
Ya juya ya shiga mota ya zauna ne Ameera tace “yauwa Habibi please I have a request”
“Please go ahead Habibty”
“uhm dama ina so ne in siya ma Ya Layla sabuwar waya tunda an sace nata..”
“okay”
Ameera dai tayi mamakin jin response dinshi.. A tunanin ta bazai amince ba tunda Layla ce amma kuma ta tuna labarin da Zaheera ta bata wanda ya tabbatar mata da lallai Zayd baya rama sharri da sharri.. kawai dai idan ya cire ka daga chapter na rayuwar shi then you are out!
“Zan sa a kawo anjima… anything else??”
Murmushi Ameera tayi sannan tace “I love you too” tare da kashe mishi ido daya.
Kisses yayi mata blowing yana murmushi yace “take care of yourself”
“I will” sannan ta rufe mishi qofar motar ta koma cikin asibitin shi kuma ya ja motar shi.
♤♤♤♤♤♤♤
GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI
Da yamma Layla tana kwance a kan gadon dakin Mama cikin bargo yayinda take tunanin rayuwarta da ta Ameera.. awa daya kenan da driver din Zayd ya dawo da su gida a dalilin sallamar ta da aka yi daga asibiti.
Gani nayi ta sa hannu ta share hawayen da ke gangarowa daga idanuwan ta.
Mama ce ta shigo dakin riqe da plate na abinci.. da ka ganta ka san tana cikin damuwa sossai domin kuwa duk tayi sanyi.
Qarasowa tayi kusa da Layla tace “ki tashi ki ci abincin sai ki sha magani Layla”
Ba tare da tace komai ba ta tashi zaune ta karbi plate din ta dauki cokali tana jujuya abincin.
Mama ta zauna a bakin gadon ne suka ji an kwankwaso qofar.
Ibrahim ne da Suleiman suka shigo riqe da manyan ledoji sai wata ‘yar qarama.
Ko da Suleiman Suleiman ajiye ma hannun shi gani nayi ya fice da sauri.. da alama wasu kayan zai kwaso.
Ibrahim Wanda shima ya ajiye manyan ledojin hannun shi ya qarasa wurin su direct ya miqa ma Layla qaramar ledar yace “Ya Layla dama Direban gidan ya Ameera ne ya kawo kayan da kuma wannan wai a baki inji ta..”
Tun kafin ya qarasa magana ne Mama ta fizge ledar tana shirin jefarwa tace “lallai ma ‘yar iskar yarinyar nan.. wato tana so ta nuna mana tayi arziki ta fi qarfin mu shine zata..”
Ko kafin ta qarasa magana Layla ta karbi ledar hannun Mama ta bude. Jikinta yana rawa ta ciro kwalin sabuwar wayar Samsung qirar Galaxy S21 yayinda ta kalli Ibrahim tace “nagode Ibrahim.. You can go”4
Ibrahim ya cika da mamaki sossai domin kuwa yau ce rana ta farko da Layla tayi mishi godiya.. sannan abin mamaki Ameera ta aiko mata da saqo ta karba… Lallai duniya ta fara sa ta bisa hanya da alama.
Suleiman ne ya qara shigowa da wasu manyan ledojin ya ajiye yayinda suka fita tare da Ibrahim.
Bayan fitar yaran ne na ga Mama ta sa ma Layla idanuwa cike da mamaki.
“wai ban gane ba.. kina nufin karba zakiyi??”
“na ma karba Mama.. idan ban karba ba ina zan samu wata? bani da komai sannan bani da wani wanda zai bani.. kin kuwa san nawa wannan wayar take??”
“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. me nake ji daga bakin ki Layla? kina nufin…”
“ina nufin daga yau bazan qara daukar duk wata muguwar shawarar da kike bani ba.. duk laifin ki ne..”7
Mama wadda ta cika da mamaki tace “ke lafiyarki kuwa???”
Layla ta fashe da kuka sannan ta ture plate din abincinta har ya fadi qasa ya fashe sannan ta miqe tsaye riqe da kwalin wayarta ta cigaba da fadin “duk ke kika sanya ni a cikin halin da nake.. a yau da baki bani muguwar shawara ba da ni ce a gidan Zayd, da ni ce matar shi.. Gaba daya kin bata mun rayuwa.. bani da komai”
Mama wadda ta miq
e tana qoqarin riqe hannun Layla ce tace “haba ‘ya ta.. kiyi haquri…”
Fizgewa Layla tayi tare da fadin “kar ki qara taba ni.. a yau nayi da-na-sanin kasancewar ki mahaifiyata, nayi nadamar abubuwan da nayi a baya, Allah ya isa tsakani na da ke kuma bazan taba yafe miki ba”
Juyawa tayi a guje ta bar dakin yayinda Mama tayi tsaye kamar wadda ruwa ya cinye ta.6
♤♤♤♤♤♤♤