ZABI NA CHAPTER 14 BY FADEELARH
DAYS LATER+
Tuni su Abba sun koma sabon gidan su a cikin Malali GRA. Abba dai har sai da Abbu ya sa baki a maganar sannan ya amince.
Ginin bene ne sashe uku sai boys quarters da kuma quarters na masu aiki. Abba ya dauki sashe daya, Umma ma sashe daya sai Mama da Layla suma sashe daya. Su Ibrahim kuwa suna boys quarters abin su.
Da qyar Abba ya amince ya karbi motoci biyu a cikin guda uku da Zayd ya bashi… Shi dai Zayd bai takura shi akan wannan din ba. shi kam burin shi ya cika tunda dai ya sanya sirikin nashi cikin irin rayuwar da yake so.
Gidan Abba dai ya masifar haduwa.. Gida kamar Zane saboda kyau.. Duk wani abin zamani na jin dadi akwai shi a wannan gida. mai karatu ba sai na baka labarin kyan tsari na wannan gida ba.. na barka ka cigaba da fantasizing.
Abin mamaki kuwa Mama sai washe baki take yi tana murna ta shiga daula.. haka ta dinga gayyatar qawayenta ‘yan qarya suna ta zuwa suna ganin gida.. Hatta Hajiya Suwaiba ta zo gidan, Ganin irin daular da Mama take ciki sai bata yi da-na-sanin turo barayi suka sace mata kudaden ta ba.. a cewar ta ko girgiza bazata yi ba..
Anan kuwa Mama ta ja Hajiya Suwaiba gefe ta sanar da ita yadda Layla ta gaya mata maganganu tare da juya mata baya wanda har yanzu ko kallon arziki bata yi mata balle magana ta hada su.. ta roqi Hajiya Suwaiba alfarmar ta qara tuhumar malaminta a duba lamarin Zayd tunda dai an biya shi kudin aikin shi.. Hajiya Suwaiba tayi alqawarin zata tuhume shi din.. a ranta kuwa ta ayyana bata qara zuwa gidan domin kuwa gaba daya ta hada kayan ta zata koma garin Zuru.2
A bangaren Layla kuwa tun daga ranar da ta tsage ma Mama bata qara sauraronta ba… Gaba daya ma ta daina shiga harkar Mama. Duk iya qoqarin Mama na ganin ta lallaba Layla sam ta qi bata fuska.
Hankalinta ya tashi sossai amma a dalilin alqawarin da Hajiya Suwaiba tayi mata sai ta sa a ranta wannan din na dan lokaci ne.. ta tabbatar idan Layla ta samu Zayd zata sauko.
Ita dai Umma tunda suka dawo sabon gidan su ma bata qara sanya su Mama a ido ba tunda dai kowa da sashen shi.. dayake Su Khadija (Anties din su Ameera) sun zo ganin gida sai ta zama so busy wurin kula da al’amuran su tunda dai dama wurinta suke sauka idan sun zo. Tunda suka leqa wurin Mama sau daya basu qara komawa ba sai ranan da zasu tafi sannan suka shiga suka yi mata sallama.
Har suka qarashi zaman su a gidan basu ga Layla ba.
Wannan Kenan!!
♤♤♤♤♤♤♤♤
KADUNA STATE UNIVERSITY
A yau litinin.. yau ne aka yi resuming school.
Wuraren qarfe takwas da rabi na safe Yusrah da Maryam suna zaune a Garden na kusa da department dinsu suna hira ne Layla ta iso.
Sossai suka yi mamakin ganin ta domin kuwa da bakinta ta ce bazata yi resuming ba sai semester tayi nisa.. Gwara ita ma, Haleema cewa tayi barin makarantar zata yi don ta gaji bazata iya ba.
“Layla???” Maryam ta fada cike da mamaki yayinda take kallon ta.
“Wait, wai ke ce kika yi resuming school yau?? I thought you said sai semester tayi nisa” Yusrah ta fada yayinda ta matsa mata don ta zauna.
Layla wadda ta zauna ce ta dan yi murmushi tace “I changed my mind.. na ga babu abin yi ne a gidan”
“toh wai tsaya.. kin yi ciwo ne? sai na ga kamar kin rame.. ko dai idanuwa na ne?” Maryam ta fada yayinda take qare mata kallo
STORY CONTINUES BELOW
Yusrah tace “Nope Mari, gaskiya Layla ta rame… hope dai ba tunanin ZAF bane??”
Layla dai bata fadi ma qawayen nata cewar barayi sun shiga gidan su ba.. shima sabon gidan da suka koma abinda yasa suka sani don sun kira ta a waya sun sanar da ita zasu zo shine ta fadi musu cewar sun tashi.. a lokacin ko da suka nemi address ta fadi musu amma kuma tayi musu qaryan bata nan saboda gaba daya ta kulle kanta tana nazarian rayuwarta da yadda zata cigaba.. a dalilin hakan ne ma take kashe wayarta don ma kar a matsa mata.
Layla ta saki ajiyar zuciya yayinda wasu hawaye suka ciko idanuwanta amma ta matse..
“Na dan yi zazzabi ne kwana biyu but I am fine now” ta fada cikin sanyin murya.
“haba Layla.. yanzu har zazzabi kika yi baki sanar mana ba??” Yusrah ta fada.
“Kuyi haquri.. it wasn’t that serious ai shiyasa ban fadi ba”
“Ke na ga kwana biyu ma bana ganin ki Online.. shekaran jiya ma mun kira wayan ki switched off.. kin ga fa dama we wanted to come see your new house ne”
“Kuyi haquri.. yanzu idan an tashi daga school sai mu je ko??”
“Yeah.. sounds like a good plan” Yusrah ta fada.
Wayar Layla ce tayi qara alamun text message ya shigo. Hannu ta sa a pocket din hand bag dinta ta zaro wayar.
Gani nayi Maryam da Yusrah sun kalli wayar cike da mamaki yayinda Yusrah tace “whoa.. ina kika samo S21 mutumiyas???”
Layla wadda take bude message din ce tace “Na manta ban gaya muku an sace mun waya ba shine Ameera ta aiko mun da wannan…”
“hmmm.. who would have thought Ameera zata kai wannan matsayin.. gaskiya ta kyauta” Maryam ta fada.
Yusrah ce ta dan taba ta tare da yi mata alamu akan tayi shiru don kuwa basu so tayi musu exploding.. sun sani sarai da an ambaci Zayd da Ameera an shiga uku.
Hankalin Layla wanda yake kan text message din da ya shigo wayarta ce na ga ta bata rai..
Leqawa nayi na ga rubutu kamar haka:
Hey Cutie.. hope you are good? don Allah kiyi haquri akan abinda ya faru a baya.. na so ace kin bani second chance don in gyara kuskuren da na aikata.. I swear I really love you Layla. Dama ina so in sanar da ke bani da lafiya and I will be going to Germany tonight for medical check up.. ina fatan idan na samu sauqi na dawo komai zai daidaita a tsakanin mu.. I pray we end up together once again.. and this time bazan qara taba ki ba sai bayan munyi aure. I pray you find a place in your heart to forgive me..6
Yours truly,
Habib
Ji suka yi ta gabza wani mugun tsaki yayinda ta mayar da wayar cikin jaka tace “dan iska kawai..”
Yusrah ce tace “hajiya ke da wa??”
Kafin ta amsa ne wata sabuwar latest Range Rover Evoque baqa wuluk ta faka a parking lot na department din. Gaba daya kallo ya koma kan motar. Ba sai an fadi maka ko waye ba domin kuwa plate number din motar kawai zaka kalla ka gane.
ZAF-06
Gilas din motar tint ce don haka idan ba an zuge ba ko kuma wanda yake ciki ya fito bazaka taba ganin mutum ba.
Gaba daya dai ‘yan makarantar sun ji labarin auren Ameera da Zayd don haka sun sani sarai cewar ita ce a cikin motar. Dukda kowa ya cigaba da hidimar shi hankulan su duk suna kan motar domin kuwa nobody wants to miss the opportunity of seeing ZAF idan har yana cikin motar kuma idan har zai fito din.
Zuciyar Layla ce take bugawa yayinda jikinta yayi mugun
sanyi.. Su Yusrah magana suke yi amma sam kunnuwan ta sun toshe gaba daya.
A cikin motar kuwa riqe suke da hannuwan juna suna magana.
STORY CONTINUES BELOW
“wallahi Habibty ban so kuka koma school ba yanzu.. we are suppose to be on our honeymoon a qasashen duniya fa yanzu”
tana murmushi tace “Habibi mun yi Honeymoon din a nan ai.. it’s all thesame fa. As long as muna tare it doesn’t matter where”
Bata rai yayi yace “No my angel.. dagaske it’s not thesame. Yanzu dai idan kuka yi mid-semester break zamu je so get ready. Duk wata qasar da kike so ki je zamu je insha Allah”2
Tana murmushi tace “nagode masoyina”
Hannun ta ya kai saitin bakin shi yayi mata kiss sannan tace “I will miss you”
Fashewa da dariya tayi tace “Miss kuma?? normally fa ko ina gida kana zuwa ofis.. it’s almost thesame ai”
“No Ma’am, it’s not thesame”
“how so??”
“kin ga idan kina gida as soon as I miss you I have 3 options.. One: I can call you, two: Zaki iya zuwa ofis din and 3: Zan iya dawowa gida to be with you. amma yanzu kina class all 3 options cant work out for me..”
Tana shafa hannun shi a cikin nata tace “Kayi haquri Habibi and I promise you idan bana lectures I will call you.. hopefully you will be free”
“for you I will my Angel.. you come first, thank you”
Ya matsa tare da cafko lips dinta yayi mata kiss sannan yace “I love you so much”
Fuskar shi ta shafa tace “I love you more”
Yana murmushi yace “thanks Habibty”
Daga nan ya bude qofar shi yayinda ya fito don zagayawa ya bude mata…
Aikuwa yana fitowa idanuwan kowa akan shi..
Sanye yake cikin wani navy blue yadi danqararre sannan mai laushin gaske wanda akayi ma dinkin zamani da samari ke yayi a yanzu.. Sossai kayan suka yi mishi kyau. Kan shi babu hula don haka gashin nan nashi baqi qirin na larabawa wanda ya sha gyara ya kwanta sai qyalli yake yi.. Gashin fuskar shi on point. In all dai Zayd ya fito a kyakyawan shi as always.
Hankalin shi sam baya kan mutanen da suke around.. infact bai ma san suna kallon shi ba dukda kuwa cikin style ake ta satar kallon nashi. Su Layla wadanda suke zaune within close range ma har ga Allah bai gan su ba.
Ko da ya zagaya ya bude mata gani nayi ya miqa mata hannu ta riqe sannan ta fito. As usual tana sanye cikin dogon hijabinta har qasa.
Qofar baya ya bude ya dauko hand bag dinta..
Kafin ya miqa mata ne Sameer yayi musu sallama suka amsa.
Cikin girmamawa Sameer yace ma Zayd “Ina kwana Sir”
Zayd wanda ya girgiza kai yana murmushi ya miqa mishi hannu suka yi musabaha yayinda yace “Hey why ‘Sir’?? please stop.. suna na Zayd. Ya kake?? ya karatu??”
Sameer yana murmushi yace “Alhamdulillah”
“uhm.. have we met before??” Zayd ya tambaye shi yayinda Ameera tayi saurin fadin “Habibi wannan course mate dina ne. Sunan shi Sameer.. shine wanda muka kai ka asibiti a motar shi lokacin da ka suma…”
Tun kafin ta qarasa maganar ne Zayd yace “Ya Salam..” Gani suka yi kawai ya janyo Sameer yayi hugging dinshi briefly tare da fadin “thank you very much.. you saved my life and I am grateful”
Shi dai Sameer gaba daya ma ya rude… wai yau shine ya hadu da the Famous ZAF wanda har yayi hugging dinshi sannan yana yi mishi godiya.
Da sauri yayi composing kanshi yace “ah haba dai.. its okay”
“nope it’s not okay” Zayd ya fada tare da miqa ma Ameera Jakarta yace “just a minute please”
Gani suka yi ya zagaya ya shiga motar shi.. can kuma ya leqo yace “what’s your full name??”
STORY CONTINUES BELOW
“Sameer Nazeef” ya fada yayinda yake mamakin dalilin Zayd na neman full name din nashi.
Zayd ya fito daga motar riqe da cheque da complementary card dinshi ya dawo wurin su sannan ya miqa ma Sameer din.
Hannun Sameer yana rawa ya karba yana dubawa..
A cheque of N5m..
“that’s my complementary card.. Idan ka samu lokaci ka zo company dina.. I want to give you a job offer wanda zai zama legit har lokacin da zaka gama school and the cheque is all yours.. please accept it as a token of my gratitude for what you did for me”5
Shi dai Sameer gaba daya jikin shi yayi sanyi yayinda ya kasa magana.. gani nayi ya juya ya kalli Ameera wadda itama shi take kallo tana murmushi.
Ganin lallai ya kasa magana ne tace “Its okay Sameer..”
“nagode sossai yallabai amma wallahi da ka bar kudin.. sun yi yawa ai. the job offer alone is okay” Sameer ya fada jiki a sanyaye.
“kar ka damu Sameer.. you deserve much more from me.. You saved my life and it’s a big deal”
“nagode sossai… Allah ya saka da alkhairi” ya fada cike da murna yayinda ya kalli Ameera yace “Uhm Hajiya Ameera dama HOD ce tace idan kin shigo tana neman ki..”
Ameera dai jin Sameer ya kirata Hajiya sai kawai ta fashe da dariya..
“Okay Sameer, yanzu zan je and please the name is Ameera as always”
“noted Ma’am”
Bayan ya qara yi ma Zayd godiya ne ya tafi abinshi.
Zayd ne yace “Why is the HOD looking for you? hope dai ba laifi kika yi mata ba Habibty?”
Dariya tayi tace “not at all Habibi.. ka manta cewar Habibty dinka is the class rep?? I think she wants to pass an information ne through me”
“aaah… yeah. Okay”
Wata danqareriyar Mercedes Benz latest GLE Coupe ta faka a parking lot din. Zayd yana ganin motar ne yace “ga qawar ki nan”
Cike da mamaki Ameera tace “ya akayi ka gane ita ce Habibi??”
“The car”
Ameera ta kalli motar da kyau.. tana cikin wadanda ya bata kyauta.
Zayd dai ya siyo ma Ameera motoci har guda uku ya bata kyauta wanda da qyar ta karba.. kwana hudu da suka wuce ta fara koyon tuqi.. a cikin motocin akwai Mercedez Benz sak irin wadda Zara ta zo da ita a yanzu.. Tare suka siya ma matan nasu motar domin kuwa tayi kyau sossai.. bambancin su kawai kala ne.
Zara wadda ta fito straight wurin su ta qaraso yayinda take murmushi tace “Mr and Mrs.. ina kwana Yayana”
Zayd yana murmushi yace “lafiya lau gimbiyar Musty, how you??”
“I am fine..”
“hope kina enjoying motar ki??”
“wallahi sossai… it’s the best one ever, so smooth and comfortable… Yayana ai Benz tayi wallahi”
Zayd yana dariya yace “Sossai..” Ya kalli agogon hannun shi briefly sannan yace “let me get going.. I have a meeting by ten and I need to go get ready”
Ya kalli Ameera yace “Habibty na tafi.. don’t forget to call me please”
Tana murmushi tace “I won’t Habibi.. stay safe”
“You too, bye”
Basu bar wurin ba har sai da ya tafi sannan Ameera tace ma Zara ta raka ta ofis din HOD dinsu.
STORY CONTINUES BELOW
Wani ikon Allah har Zayd ya tafi bai ga Layla da qawayen ta zaune a wurin ba.. ita kanta Ameera bata kula da su ba.. A lokacin da zasu wuce ofis din HOD din ne ma Zara ta hango su har tana fadi ma Ameeran.
Layla dai a dalilin tashin hankalin da ta shiga kifa kai tayi a gwiwarta ta dinga rusa kuka yayinda qawayen ta suke ta lallashinta.
Tabbas tayi asara.. da yanzu ita ce a matsayin Ameera.
Tsawon lokaci ta kwasa tana ta kuka wanda tun qawayen nata suna bata haquri har suka gaji suka zuba mata idanuwa. Sai da tayi mai isarta sannan ta haqura ta daina don kanta. Gaba daya fuskarta tayi jajawur.. Idanuwanta sun kumbura duk ta fita daga hayyacinta abin gwanin ban tausayi.2
Da qyar qawayenta suka lallaba ta suka shiga class.
***************
< p>Tunda su Layla suka shiga class kuwa suka ji ana ta hirar abin arzikin da Zayd yayi ma Sameer.. sai addu’o’i suke yi ma Zayd da Ameera yayinda ake ta zuzuta maganar.
Sossai abin ya taba zuciyar Layla.
Ana cikin haka ne Ameera da Zara suka shigo yayinda Ameera ta nufi podium inda lecturers suke tsayawa tayi ma ‘yan ajin sallama tare da announcing musu saqon HOD dinsu..
Gaba daya ajin aka natsu ana sauraron ta har ta gama.. Dukda dama suna respecting dinta a baya a yanzu girmamawar ta qaru.. Kai ko da ta dawo ta zauna a kujerar ta haka ‘yan ajin suka dinga zuwa wurinta suna gaisawa da ita tare da yi mata godiya na abin arzikin da Zayd yayi ma Sameer.
Kai a yau hatta lecturers da suka shigo class sun ba Ameera extra respect a dalilin sanin matsayinta a yanzu.
Layla dai yinin ranar tana fama da qaunar zuciya da tsananin ciwon kai sannan ga da-na-sanin da ya cika ta.
Dayake yau ne resumption day, ba wani lecture din arziki aka yi ba… yawanci duk Introduction ne..
Ko da aka tashi ma Ameera ta sanar da Zayd cewar Zara zata sauke ta gida don haka bata wani kira driver ba..
Ita kuwa Layla kamar yadda suka yi da su Yusra, gidan su ta kai su wanda har sai da suka kira Haleema don ji idan ita ma zata je amma tace musu tana Abuja don haka idan ta dawo zasu kai ta.
♤♤♤♤♤♤♤
3 DAYS LATER
MALAM FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE
MALALI GRA
Wuraren qarfe takwas na dare suna zaune a dinning din Abba suna dinner.
A yau din Zayd da Ameera sun zo gidan.. dayake girkin Umma ne ko da tayi musu tayin su tsaya suyi dinner babu musu suka zauna.
A qa’idance dai duk dare gaba daya gidan tare ake zama ayi dinner kamar yadda suka saba tun suna tsohon gidan su amma fa tun suna can din Mama da Layla suka daina zama ayi da su. Toh anan din ma basu zuwa… idan ranar girkin Mama ne saidai ta aika musu da abincin su dinning din Sashen Abba kamar yadda yake a tsare amma fa ita da Layla basu zuwa.
A yau din dai lafiyayyen Tuwo da miyan kuka Umma tayi.. Ga lafiyayyen man shanu da farfesun naman kaza. A gefe kuma ta hada fruit salad mai lafiya.
Zayd dai ya ji dadin abincin sossai.. ya yaba qwarai wanda har qarawa yayi.
Su Ameera da Ibrahim suka dinga yi mishi dariya na santin da yake ta bazawa yayinda Umma da Abba suka ji dadi sossai.
Bayan sun kammala suna shan fruit salad ne Zayd yayi gyaran murya yace “uhm Abba maganar makarantar su Ibrahim da muka yi.. dama ina so in sanar da kai anyi inviting dinsu interview jibi insha Allah.. so I think yakamata gobe su je Abuja”
STORY CONTINUES BELOW
Su Ibrahim dai jin haka sai suka fara murna..
Abba yana murmushi yace “Ya zanyi da kai?? mutum baka gajiya ko alama.. daga wannan sai wancan.. Allah ya kaimu”
Umma tace “ni ban ga dalilin kai su wata makarantar kwana har Abuja ba.. Yanzu ace duk makarantun cikin garin nan babu wadda zasu je sai Abuja??”
Zayd yana murmushi yace “Ba haka bane Umma.. Islamic Leadership Academy tana da kyau ne sossai, infact it’s the best Islamic oriented school in the whole of Africa.. zasu qaru sossai”
“toh Allah ya sanya albarka”
Gaba dayan su suka ce “ameen”
Ya kalli su Ibrahim yace “gobe sai ku shirya za’a zo a dauke ku a kai ku airport sai ku tafi a jet dina”3
Zaro idanuwa suka yi yayinda Aliyu yace “Ya Zayd a jirgi zamu je??”
“ofcourse bro.. zaku sauka a gidan Ammi na sai kuma jibi a kai ku interview din”
Habaaa.. cike da murna suka dinga yi ma Zayd godiya. Ita dai Ameera ta cika da farin ciki.
Babban abinda yake birge su Abba shine yadda Zayd yake kyautata ma yaran Mama (Ibrahim, Munnir da Suleiman) same way da yake kyautata ma Aliyu. ko kadan baya nuna bambanci a tsakanin su. Duba rashin mutuncin da Layla tayi mishi amma still ya gina gida ya basu sashen su a ciki da ita da uwarta.. ya loda kayan abinci a gidan suna ta ci sannan dukda ba directly yake basu kudi ba still da kudin nashi ake yi musu hidima..
Rayuwa kenan!
“Abba akwai one last issue that I wanted to discuss with you..” Zayd ya fada yayinda dukkanin su suke kallon shi suna sauraron abinda zai ce.
Abba yana murmushi yace “fadi in ji Zayd”
“Dama akwai wani abokin Abbu a Saudi Arabia.. babban likita ne shine nayi mishi maganar ciwon asthman Umma and he said idan da hali she should go and see him..”
Abba ya girgiza kai yace “kana dai nufin kayi booking mata appointment da likita ka zo kana neman amincewata ko?”
Zayd yayi murmushi sannan yace “kayi haquri Abba”
“toh banda abinka Zayd, ai ciwon nata ya kwana biyu bai tashi ba tunda ana kiyaye dokokin likita”
“dukda hakan Abba, ai gwara ta samu treatment wanda idan an dace ma bazai qara tashi ba insha Allah”
Abba dai tuni ya daina dragging da Zayd domin kuwa no matter how hard he try to, in the end sai yayi everything possible to convince him.
“yaushe ne ka shirya mata tafiyar?”
“Next week ne Abba.. da kai da ita ne zaku je” Zayd ya fada da sauri.
Anan dai Abba da Umma suka dinga sa mishi albarka suna ta yi mishi godiya.. Ameera kuwa cike take da murna.. bata taba sa ran zata auri mijin da zai kyautata ma iyayenta haka ba.. Tabbas ta gama samun komai a rayuwarta tunda ta samu miji kamar Zayd.
Ko da suka yi ma su Abba sallama su Ibrahim suka raka su har parking lot wurin motar su sannan suka yi musu sallama suka wuce sashen su cike da murna.
Ameera kuwa suna shiga mota kafin Zayd ya tayar tayi saurin matsawa ta rungume shi very tight ba tare da tace komai ba..
Yana murmushi yace “whoa.. Habibty what have I done to deserve such a sweet hug??”
“everything Habibi.. everything”
Ji yayi ta fashe da kuka tace “nagode sossai Habibi.. shukran… I am short of words wallahi Habibi.. ban san da wane baki zanyi maka godiya ba akan dukkan abubuwan da kayi mana..”
“Ssshhhh..” Yayi breaking hug din sannan ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta yace “ni da ke daya ne Habibty.. idan nayi miki wani abu kamar kaina nayi wa, haka idan nayi ma iyayenki kamar nawa nayi wa don haka please stop wasting your tears.. you know I can’t pay for them right??”
Murmushi tayi sannan ta hada bakin ta da nashi tayi mishi kiss briefly sannan ta janye.
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “that was brief Habibty.. I expected a deep one”
Tana dariya tace “ka dai san nan din gidan sirikan ka ne ko?? kar muyi abin kunya don haka kayi haquri ka kai mu gida zan baka the best one ever..”
“Promise??”
“Yeah my love”
Daga nan kuwa ya ja motar suka bar gidan suna ta hirar su ta soyayya.
♤♤♤♤♤♤♤♤Kamar dai yadda Zayd ya tsara tuni su Abba suka gama shirin su tsab suka hau jirgi sai Saudia.+
Wani ikon Allah hankalin Mama yayi masifar tashi.. ta so ace da ita a cikin tafiyar amma ina babu halin tambaya ma balle ta sa ran za’a je da ita.. haka ta dinga fama da baqin ciki. Umma ta riga ta shiga jirgi.3
Zayd dai musamman ya damqa ma Abba kudade dayawa don ya ba ma Mama da Layla.. kudin that they can use for their daily needs sannan ya qara sa an loda musu kayan abinci a gidan don dai a fita haqqin su.. Idan ka shiga store din gidan Abba zaka rantse kayan sayarwa ne saboda yawa..
Su Ibrahim kuwa dama dai interview din da suka je yi duk formality ne domin kuwa matsayin Abbu da Zayd a Nigeria ya isa ayi musu alfarma ko wacce iri ce a duk inda suka neme ta. Tuni an basu admission a Islamic Leadership Academy.
D
ayake dai dama an riga anyi resuming suma babu bata lokaci Zayd ya kammala musu komai suka tafi.. Aikuwa Mama tana kallo yaran nata suka yi mata sallama suka wuce makaranta abin su.. Zayd da Ameera ne suka raka su har Abujan.3
Su Ammi kuwa sun ji dadin ganin Ameera, Musamman ‘yan biyu. Its the first time she visited tun auren.. Ameera dai ta ga soyayya wurin dangin miji.. sai nan nan ake yi da ita, abin har mamaki yake bata.. ko da wasa bata taba mafarki irin wannan rayuwar ba.
Sai da suka yi kwana uku a Abuja sannan suka dawo a dalilin makarantar Ameera.
Kwana biyu kacal da dawowar su daga Abuja kuwa aka tafi indefinite strike a makarantar su Ameera.. Hakan kuwa ba qaramin dadi yayi ma Zayd ba domin kuwa it’s the perfect time for them to travel out of the country for their honeymoon especially because ya samu sauqin aikin shi a ‘yan kwanakin nan.
Ba tare da bata lokaci ba kuwa ya shirya musu tafiyar su shi da Ameera zuwa qasashe biyar England, Switzerland, Greece, Dubai da Saudi Arabia..4
A cewar shi duk lokacin da aka yi calling off strike din sai su sa pause su dawo idan yaso they will return and continue during mid-semester…
Sai da suka koma Abuja suka yi ma su Ammi sallama sannan suka bar qasar..
Fatan mu Allah ya dawo da su lafiya… Ameen!
♤♤♤♤♤♤♤♤
One week later!!
FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE
MALALI GRA
A yau sati daya kenan da su Ameera suka bar qasar.
Tsaye take a gaban wadrobe dinta yayinda take jera kayan ta.
Layla dai tuni ta kwashe kayanta ta kai ma tela yayi mata ‘yan dabaru a kai… Allah ya taimake ta dama yawanci kayan suna da allowance a ta ciki don haka duk wadanda suka matse ta an bude su.. haka masu manyan wuya duk an rage.. wadanda kuma ba’a iya yi musu dabara ta sallamar da su.1
Kudaden da Abba ya bata na kashewa a school kuwa masu yawa ne.. (Kudaden da ta sani sarai daga wurin Zayd suka fito) a ciki ta cire ta siya sabon atamfofi ta bayar za’a yi mata decent dinkuna masu rufe jiki sannan ta siya manyan veils different colors.. su ma irin wanda ke rufe jiki dinnan.
Tana nan tsaye ne ta ji qarar qofa.. ko bata kalla ba ta san Mama ce tunda dai daga ita sai ita a gidan..
Ba tun yau ba Mama take shigowa dakin Layla tayi ta magana har ta gama amma Layla bata ko kallonta balle ta amsa ta.. Gaba daya Layla haushin Mama take ji don kuwa ita ta sanya ta a halin da take ciki.
STORY CONTINUES BELOW
Yau da ace Zayd kawai tayi losing da sauqi.. toh amma iskancin da suka dinga yi da Habib fa?? wannan shi ya fi tsaya mata a rai.. shi ya fi tayar mata da hankali3
“Layla na ga baki ci abincin ki ba”
as usual dai bata ce mata komai ba.
Gani nayi ta zauna a gefen gado sannan tace “dama na zo ne in fadi miki akwai wata Hajiya Bara’atu qawata ce sossai, dazu ta zo gidan nan muna hira shine nake bata labarin abinda ke faruwa na game da ke da Zayd shine tace akwai wani malam a Minna ya iya aiki sossai, Tunda kin ga akwai kudade masu yawa da Abban ki ya bar mana sai…”1
“Dakata Mama” Layla ta fada cikin tsananin bacin rai tare da rufe qofar wadrobe dinta da qarfi.
“Ko da wasa kar ki qara kai sunana wurin wani Malam ko boka.. instead ki kai naki. Ni kam har ga Allah na haqura da Zayd.. a yanzu haka qoqari nake yi in ga na gyara kuskuren da nayi a baya don haka please ki qyale ni”
“Amma Layla taimakon ki fa…”
Katse ta tayi tare da fadin “taimako Mama?? ai wallahi ke kika cuci rayuwata kuma bazan taba yafe miki ba..” daga nan ta fashe da kuka tare da zamewa a qasa.
Jikin Mama yayi sanyi sossai… A duk lokacin da Layla ta furta mata wadannan kalaman sossai hankalinta yake tashi.
Gani nayi ta miqe da sauri ta nufi wurinta ta rungume ta yayinda take fadin “Kiyi haquri Layla ta.. idan dai akan wannan maganar ne bazan qara ba.. tunda kin haqura da Zayd din shikenan.. ki yafe mun kin ji??”
Layla dai ta sani cewar she cant stay long tana fushi da Mama, dukda ita ta sanya ta a wannan halin ai itama da nata laifin tunda dai da hankalinta ta amince ta fada rayuwar banza. A yanzu haka still she has no one like her.. tunda ta bata haquri she has no choice but to accept.
Layla tana share hawayen ta tace “ya zanyi Mama?? ai dole in yafe miki.. nima ina fatan Allah ya yafe mun”
“toh wane laifi kika yi da kike neman yafiya daga wurin Allah??” Mama ta tambayeta confusedly.
“Uhm.. ina nufin dukkan laifukan da nayi mishi” Layla ta fada yayinda take scolding kanta na kusan tona ma kanta asiri da tayi..3
(Kar ku manta, Mama batada masaniya akan abinda ya dinga faruwa tsakanin Habib da Layla)
A haka dai suka yi sulhu da juna yayinda suka cigaba da hirarraki na yadda zasu cigaba da rayuwa.. Har ila yau dai, Mama tana qoqarin nuna ma Layla lallai ta dage ta samu mai kudi don su kece raini suma yayinda ita Laylar ta gwada mata duk wanda ta samu idan dai mai hankali da natsuwa ne batada matsala..
Mama dai bata dauki zancen ba amma a dalilin bata so ta sake samun matsala da ita ne ya sanya tayi shiru.. amma kuwa ta qudurta a ranta lallai sai ta gyara mata tunani.
Kenan dai Mama bazata taba canza hali ba???
♤♤♤♤♤♤♤♤
5 days later!
FAROUQ ABDALLAH’S RESIDENCE
MALALI GRA
Zaune suke a dakin ta yayinda suke ta hirar bikin Maama, cousin din Yusra da za’a fara gobe.
Haleema wadda take chatting da Yusuf a WhatsApp ce na ga ta dago kai ta kalli Layla tace “Qawata kun yi magana da Habib kuwa kwanan nan?”
Cike da bacin rai Layla tace “Leema don Allah kar ki qara yi mun maganar Habib.. I told you I am done with him.. meye matsalarki ne??”
“hey calm down, the reason why i asked is na ji ance baya da lafiya yana Germany and gashi Yusuf yana gaya mun it’s very serious”
Maryam ce tace “Subhanalillah, wanne irin ciwo ne haka?”
STORY CONTINUES BELOW
Haleema tace “wallahi ban sani ba.. I asked Yusuf and he isn’t giving me a straightforward answer”1
“toh fa.. amma dai Layla yakamata ki kira shi tunda dai anyi zaman mutunci.. I am still wondering what he might have done to you da kika rufe shi gaba daya” cewar Yusrah.
Maryam ce tace “gaskiya fa.. atleast na ga dai dukda Zayd ya taka shi a wurin arziki shima dai babu laifi.. ko banza with him zaki rage zafi tunda dai ke dama arziki is the main priority a wurin ki”
“that was before.. not anymore” Layla ta fada cike da jin zafin abinda Maryam ta fada.
toh amma she is right ai tunda dai haka tayi presenting kanta.. no be so???3
Haleema ce tace “Layla a gaskiya yakamata ace kin yafe ma Habib.. you guys had a great time together. Wallahi tun ranar da kika gan shi da Fiddy bai qara mu’amala da wata mace ba.. he promised it will continue to be just you alone… besides what you guys did was not really a big deal since auren ki zai yi kuma…”1
bata qarasa magana ba tayi saurin yin shiru don kuwa ta kusa kwafsawa..
Yusrah ce tace “ban gane mu’amala ba??? and what did they do???” da sauri ta kalli Layla ta cigaba da fadin “Qawa were you having sex with Habib???”
Layla wadda gaba daya jikinta yayi sanyi kasa dago kai tayi balle ta kalle su..
Haleema wadda ta gane ta kwafsa ce tace “Layla please I am sorry.. I didnt mean to..”
“you didn’t mean to expose what you guys have been doing?? kenan dagaske iskanci kuka dinga yi babu aure a tsakanin ku?? Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” Yusra ta fada cike da disappointment.
Layla wadda tuni ta fashe da kuka ce tac
e “wallahi sharrin shaidan ne kuma nayi nadamar abinda nayi.. how I wish I could turn back the hands of time but I just can’t”2
Gaba dayan su dai shiru suka yi yayinda Maryam da Yusrah suka yi displaying tsananin shock..
Haleema ce tace “Look Layla.. wannan din fa ba wani babban laifi bane.. kissan kai kika yi??”
“haba Leema, instead of kiyi regretting abinda kike yi kamar yadda Layla tayi amma kina nema ki qara dulmiya ta???” Maryam ta fada cike da bacin rai.
“Abeg jor leave me… it’s a free world, allow me to live however way I want”3
Yusrah tace “I’m sure ma ke kika jefa ta cikin wannan harkar..”
“qaramar yarinya ce ita marar wayau?? ba kudi take so ba?? abeg jor.. this is no time for blame game.. she already did what she did kuma ta samu abinda take so don haka duk wannan kukan munafincin na daga baya ne”
Ta miqe tare da daukar Jakarta tace “ni kam ina da appointment nan da minti talatin.. gwara in tafi kar inyi latti. Sai mun hadu a gidan su Maama gobe”
Bin ta suka yi da ido cike da mamaki har ta fita..
Daga Maryam har Yusrah ma kasa lallashin Layla suka yi don kuwa hankalin su yayi matuqar tashi.. basu taba sa ran duk bude idon Layla zata biye ma namiji yayi lalata da ita ba alhalin babu aure a tsakanin su.
Maryam ce tace “gaskiya na tausaya miki Layla.. kin yi asarar masoyin asali Zayd sannan kin yi asarar virginity dinki to some stupid guy.. Ga kuma laifin da kika aikata ma mahaliccin ki.. Ya salaam”
Yusrah ce ta matsa kusa da ita ta riqo hannun ta sannan tace “Ki daina kuka Layla. tabbas abinda kika aikata kuskure ne babba.. irin kuskuren da bazaki taba iya gyara shi ba. Yanzu dai kawai ki cigaba da neman yafiyar Allah.. kiyi ta istigifari. Kuma ki sani cewar duk mijin da zaki aura dole ne zai gane he is not your first.. I just hope and pray you find an understanding person that can forgive you”
STORY CONTINUES BELOW
Haka dai suka cigaba da lallashinta tare da fadi mata kalamai masu sanyaya rai.. A yau ta tabbatar lallai Yusrah da Maryam qawayen arziki ne.. if only she mingled with them more than she did with Haleema, things would have been different.. But then it’s to late to cry now.. Yeah???
♤♤♤♤♤♤♤♤
CEREMONIAL CANOPY
EVENT CENTRE
A yau ranar dinner din Maama.. Wuri dai ya cika da mutane.. Duk inda ka waiga zaka ga manyan masu kudi maza da mata.
A yau din kwana uku kenan da aka fara bikin.. tunda aka fara kuwa Layla bata samu ta je ba a dalilin qunci da ta shiga tun ranar da Haleema ta tona musu asirin abinda suka dinga yi da Habib.
A yau din ma dai ta fito ne saboda kar Yusrah ta ji haushi domin kuwa tana ta yi mata qorafi since the past 3 days.
Zaune take a can wani corner yayinda take ta kallon mutane suna kai da komowa… Da ganin yanayin ta ka san she is not okay. Sanye take cikin decent dinki na ankon Maama din. Dukda damuwar da take ciki kuwa tayi kyau sossai..
Kun san Layla dama first class ce wurin kyau!
Su Yusrah da Maryam wanted her to join them in entertaining the guests as part of ‘yan uwan amarya amma ta qi.
Haleema dama tunda wani guy ya janye ta suka yi gefe suna ta hirar su.
Zaune yake a wani corner na hall din tare da abokanen shi suna ta hira.. A zahiri dai yana zaune tare da abokanen shi amma gaba daya hankalin shi baya tare da su..
Kallonta yake ta yi da yadda tayi isolating kanta.. he has been staring at her for almost thirty minutes yayinda yake ta kula da duk wani motsin ta..
Gaba daya ta gama birge shi.. Daga yanayin kayan jikinta zuwa natsuwar ta..1
Gani nayi ya miqe yayinda yace “Guys, ina zuwa don Allah”
Daya daga cikin abokanen nasu ne yace “Sufy ina zaka je??”
“I’ll be back..” ya fada sannan ya wuce.
**************
“Assalamu alaiki Gimbiya”
Layla wadda take zaune ta jiyo muryar shi daga sama.
Da sauri ta dago kai ta kalle shi tare da fadin “wa’alaikas salam”
“Da fatan Gimbiyar zata bani wurin zama..” ya fada yana murmushi.
“please have a seat” ta fada tare da nuna mishi kujera.
Gani nayi ya ja kujera ya zauna yayinda yace “nagode da karramawar ki gimbiya”
Layla tayi murmushi ba tare da tace komai ba.
“Ni sunana Sufyan Abubakar Bicci.. I am from Kano state. Actually, ina tare da abokane na ne a can side din shine na hango ki nace bari in zo mu gaisa”
“Allah sarki.. nagode” Layla ta fada.
“toh ya sunan ki?”
“ooh sorry.. My name is Layla Farouq, nima ‘yar Kano ce”
“Whoa ashe garin mu daya! nice to meet you Layla.. da fatan zaki bani dama in shiga zuciyarki because as soon as I saw you, love at first sight happened”
Zuciyar Layla ce ta buga da jin kalaman shi..
Tabbas Sufyan looks 100% okay.. da ganin shi yana da hankali da natsuwa, he looked well-to-do sannan yana da kyau babu laifi.. Baqi ne shi ba fari ba but dukda hakan zaka iya saka shi a sahun handsome dudes.
Matsalarta a yanzu shine idan magana tayi nisa har ta kai su ga aure ya gano cewar ta sayar da budurcin ta tun kafin ta shiga gidan shi fa? Lallai fa an zo wurin.. irin abinda ake gudu kenan, it’s part of the reason for her regret.. Yanzu ya zata yi??
“Gimbiya na san kina buqatar lokaci.. babu matsala… Zan baki lokaci kiyi nazari. Yanzu dai alfarma daya nake nema a wurin ki.. please can I have your contact??”
Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “there is no problem” yayinda ta fadi mishi lambar wayarta…
Nan da nan yayi saving sannan ya kira ta don ta samu tashi lambar.. Itama tayi saving.
“are you here on behalf of the bride or groom??” ya tambaye ta.
“the bride.. cousin sister din qawata ce”
“oh.. Allah sarki. Ni I am here on behalf of the groom, family friends dinmu ne”
Kafin tayi magana ne Haleema ta qaraso wurinta cikin tsananin tashin hankali… jikinta har rawa yake yi.
“lafiya??” Layla ta tambayeta.
Ba tare da Haleema ta kalli Sufyan ba ta janyo hannun Layla tana fadin “please come with me..”
A rude Layla ta miqe ta kalli Sufyan tace “excuse me please”
Bata tsaya sauraron shi ba ta bi Haleema yayinda take tambayar ta abinda ke faruwa..
Kai tsaye Haleema ta janyo Layla suka fito harabar hall din yayinda take ta sauke numfashi.. Sai a wannan lokacin ne Layla ta kula da hawayen da suka wanke ma Haleema fuska.
“Leema what happened, na ga kina kuka… anyi rasuwa ne??”
Daga mata kai tayi alamar ‘eh’
Jiki a sanyaye Layla tace “who???”
“Ha-bib…”Two Month later!!
It’s exactly 2 month da rasuwar Habib…
A ranar da Haleema ta sanar da Layla rasuwar kuwa hankalinta yayi masifar tashi..
Babu shakka Habib ya lalata mata rayuwa, babu shakka duk duniya yana cikin wadanda ta tsana, tabbas ta yanke duk wata alaqa da take tsakanin su amma hakan bai hana ta ji mutuwar shi ba.. ko babu komai akwai tausayi na musulinci..
Hatta Mama ta ji mutuwar Habib domin kuwa ko babu komai sun ci dukiyar shi dukda barayi sun raba su da 70% of it.
Abinda ya fi bada mamaki kuwa shine har yau babu wanda ya san ainihin ciwon da ya kashe shi.. Duk nacin Haleema na son sani a wurin Yusuf ta kasa… Ya gwada mata shima bai sani ba amma ga dukkanin alamu ya sani, abinda ya daure mata kai shine yadda baya so ya fadi..
Shi kanshi Yusuf din yayi sanyi sossai tun bayan rasuwar abokin nashi.
.. abin mamaki iskancin da suka saba yi da Haleema ma ya janye gaba daya.. Dayake yana bala’in son Haleema bai rabu da ita ba amma dai a kullum zancen shi bai wuce na maganar auren su ba… ita kuwa Haleema ba shirin auren tayi ba don haka kullum tana cikin yawo mishi da hankali..
Layla dai tuni ta fara soyayya da Sufyan..
Sufyan Abubkar Bicci dai Asalin shi mutumin Kano ne kamar yadda na fadi muku. Babban likita ne a Giwa Hospital da ke cikin garin Kaduna.. Yanzu haka shekarun shi talatin da uku a duniya.. Sufyan dai ya taba yin aure amma Allah yayi ma matar rasuwa wurin haihuwa.. Allah ya dauki ranta da abinda ke cikin ta. Shekaru biyu kenan da matar shi ta rasu, Tsawon shekaru biyun nan bai samu macen da zata cike mishi gurbin ta ba sai wata biyu da suka wuce da ya hadu da Layla..
Layla dai ta shiga ran Sufyan sossai… ita kanta ta tabbatar yana sonta tsakani da Allah. Tun tana noqewa har ta saki jiki suka fara soyayya.. Soyayya mai tsabta ba irin wadda tayi da Habib ba a baya. Ya ba Layla labarin rayuwar shi A-Z, bai boye mata komai ba a game da shi domin kuwa da gaske yake yi ba wasa ba… A bangaren ta kuwa ba komai ta fadi mishi ba domin kuwa tana gudun kar abinda suka fara ginawa ya wargaje..3
Toh amma tambaya anan ita ce.. is it the right thing to do???🤔2
Sufyan dai yana da arzikin shi daidai gwargwado.. Haka yana kyautata ma Layla sossai. Katin waya, Kayan ciye-ciye, kayan sawa da sauran su babu laifi yana bata.
A yanzu haka jira kawai yake yi Abba ya dawo don ya gabatar da kanshi.. as it is, baya so a dauki lokaci mai tsawo wurin maganar auren su domin kuwa he is all set…
Mama dai ta san Sufyan yana zuwa, Ya shiga har gida ya gaishe ta ma.. Ita kam har ga Allah bai yi mata ba don kuwa ta kula ba mai tarin arziki bane kamar Habib balle kuma Zayd.. ita har yanzu tana akan bakan ta na lallai ‘yar ta mai kudi zata aura. Har zaunar da Layla tayi ta umurce ta akan ta cigaba da neman mijin aure mai arziki amma ba Sufyan ba.. Ita dai Layla amsa ta kawai tayi. Tuni ta riga ta dawo daga rakiyar Mama.. Tayi alqawari bazata qara bari ta bata mata rayuwa ba kamar yadda tayi a baya.. A yanzu kam jira kawai take yi Abba ya dawo a fara maganar auren su ta bar gidan ma ta huta.4
Wannan Kenan!!
♤♤♤♤♤♤♤
Weeks later!!
ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA
Zaune take a kan kujerar falon shi yayinda yake kwance a kan cinyar ta. Kallon TV suke yi suna hira.. suna yi tana wasa da gashin kanshi wanda ta san yana jin dadin hakan sossai.
STORY CONTINUES BELOW
Zayd da Ameera dai jiya suka dawo. Sai da suka sauka a Abuja suka yi kwana biyu sannan suka dawo gida. Kamar yadda suka yi planning zuwa qasashe biyar tabbas sun je.. Ameera kuwa babu qarya ta bude ido. tayi yawo sannan sun gurji soyayya tare da mijinta.. sun mori rayuwar su. Gaba daya ta canza tayi kyau ta qara haske sannan ta yi ‘yar qiba.. Da ka kalle ta zaka san hutu ya ratsa jikinta.. Ta zama babbar yarinya..!
A lokacin da suka je qasar Switzerland ne Zara da Mustapha suka je suma… Dayake Zara bata taba zuwa Switzerland ba shiyasa suka yi planning su hadu a can din… they had a beautiful time together as friends and couples.. sunyi enjoying rayuwar su sossai.
Daga Switzerland din ne suka wuce Saudiya inda suka yi Umrah harda su Abba.
Umma ta ga likitan ta.. kamar yadda Zayd ya fadi musu cewar zata samu kulawa sossai tabbas ta samu.. ta samu treatment mai kyau..
Daga Umma har Abba sun huta suma.. Dama dai the idea na tafiyar don su huta din ne..
Umma tayi mamakin ganin yadda Ameera ta masifar canzawa.. idan ka ganta zaka rantse ciki gareta amma gaskiyar zancen a wannan lokacin shine babu komai sai tsabar hutu.
Sun yi planning dawowa Nigeria gaba dayan su a tare amma kuma sai aka kira Zayd ana neman attention dinshi a Dubai don haka dole suka wuce Dubai din shi da matar shi yayinda su Abba suka tattara suka dawo Nigeria dukda su Mustapha.
Zuwan su Dubai ne suka yi discovering cewar Ameera tana da ciki a dalilin wani zazzabi da tayi.
Aikuwa daga shi har ita sunyi murna marar misaltuwa.. Tuni labari ya isa wurin iyayen su da abokanen arziki.. su ma sun cika da murna.. finally Umma da Ammi zasu ga grand child dinsu…
Allah ya taimaki Ameera cikin nata baya bata matsala ko kadan.. asali ma banda Zayd da kullum yana maqale da ita yana labarin cikin har ga Allah mantawa take yi cewar tana da shi.
A dalilin cikin kuwa ko bayan da ya gama abinda yake yi a Dubai din sai suka yi zaman su a can.. a cewar shi weather din garin is good for her and the baby.
Yanzu haka dalilin dawowar su don an sanar cewar an janye yajin aiki na makarantar su Ameera ne shiyasa.. banda don wannan da sunyi zaman su a can..
Saukar su Abuja kuwa Ammi sai nan-nan take yi da Ameera.. motsi kadan sai ta tambaye ta me take so ko kuma ina yake yi mata ciwo.. she treated her like a princess domin kuwa komai yi mata ake yi ko kadan Ammi bata bari tayi komai. Su Maheera ma haka suka dinga tarairayarta.. Har makarantar su Ibrahim sun je sunyi visiting dinsu.. sossai suka yi murna. Abin mamaki Ameera sai gani tayi yaran sun canza gaba daya sunyi kyau.. da gani ka san suna samun kula ta musamman. A lokacin ma saura kwana uku su fara jarabawa wanda idan sun kammala zasu dawo gida hutu.
Wayar Zayd ce tayi ringing yayinda na ga ya janyo ta yana dubawa…
Abba ne…
Da sauri yayi picking call din cikin girmamawa ya gaishe shi. Bayan Abba ya amsa ne yace “dama akwai wanda yake neman Layla ne zai zo gaishe ni gobe da daddare.. toh abokanena na wurin aiki yawanci duk sun tafi seminar, abokina Malam Zakari yayi tafiya sannan Malam Isah makwabci na anyi mishi rasuwa shine nace bari in ji tunda na ga gobe Saturday idan kana da lokaci ka zo..”
Tun kafin Abba ya qarasa magana ne yace “Babu matsala Abba zan zo..”
Daga nan suka dan taba hira sannan suka yi sallama.
Ameera wadda take maqale a jikin shi ce tace “wai me ya faru? na ji kana fadin zaka je gidan..”
“Your sister’s suitor.. zai je ganin Abba gobe shine yace in zo so that we can receive him…”
STORY CONTINUES BELOW
Cike da murna Ameera tace “whoa.. that’s good news, I am happy for her gaskiya. Allah ya sanya alkhairi”3
“Ameen”
♤♤♤♤♤♡♡
Washegari!
FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE
MALALI GRA
Abba ne zaune a kan three-seater kujera yayinda Zayd yake zaune a kan single-seater.
Sufyan yana zaune a qasa tare da abokin shi mai suna Faisal.
Kamar dai yadda suka shirya a yau din Sufyan ya zo tare da abokin shi don gabatar da kanshi a wurin Abba.
Tuni dai sun gama introduction din da suka kamata yayinda Abba ya cigaba da yi mishi tambayoyi yana amsawa..
Zayd dai yayi mamakin ganin Sufyan a matsayin wanda Layla ta zaba.. shi fa duk a tunanin shi Habib zai gani tunda dai tare ya taba ganin su wanda har kiss suna yi da juna.. what happened? kenan sun gama cin duniyar su ta watsar da shi shine ta dawo ma Sufyan?? toh amma from his looks da tarihin shi da ya basu ba mai mugun arziki bane kamar irin wanda ya san Layla tana nema.. Har ga Allah Sufyan ya bashi tausayi domin kuwa da ya san kalar macen da yake son aure da tuni ya kauce.. But again yayi tunanin for her to leave a rich kid like Habib sannan ta dawo ma Sufyan it’s possible ta gyara hali ne… well, if that’s the case then a big congratulations to her..
“Abba dama ina so in nemi izini akan in turo manya don a fara maganar aure saboda dama munyi magana da ita Layla akan ina so ayi auren da wuri shine tace batada matsala but the
final say has to come from you”
Abba wanda ya yaba qwarai da halayen Sufyan ne yace “eh toh don ta wannan din babu damuwa.. a bangaren mu dai zamuyi bincike and while we are at it zaka iya turo manyan naka sai a fara magana”
Ya kalli Zayd yace “ko ya ka gani??”
“Yes Abba, it’s in order ai… Allah ya sanya alkhairi”
Gaba dayan su suka ce ‘ameen’
A haka dai suka shiga hira sossai kamar ba sirikai ba.. tun Sufyan da Faisal suna kamewa har suka saki jiki suka sha hira..
Yawanci hirar duk ta abubuwan da ke faruwa ne a qasa..
Sufyan dai ya san labarin Zayd amma bai taba ganin shi ba sai yau din.. a tunanin shi zai yi girman kai da ji-ji da kai a dalilin status din shi a qasar nan amma sai ya fahimci sam ba haka bane… asali ma they found him to be a jovial, down to earth and humble human being.
Tuni suka yi bonding da juna wanda a qarshe ma har exchanging lambobin waya suka yi..
A haka dai su Sufyan suka yi musu sallama tare da yin godiya na irin karbar da aka yi musu da kuma damar da aka basu na su turo manyan su.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Zaune suke a falon Abba bayan tafiyar Zayd yayinda yayi musu bayanin yadda suka yi da Sufyan.
Umma wadda tayi ma Layla murna ce tace “masha Allah, Allah ya sanya alkhairi Layla”
Layla wadda a yanzu take girmama Umma ce tace “nagode sossai Umma”
Mama tayi tsaki tace “ni dai gaskiya yaron nan bai yi mun ba..”
Cike da mamaki dukkan su suke kallon ta.
“Kamar ya bai yi miki ba?? yana da wani aibu ne wanda kika sani da bamu sani ba?” Abba ya tambaye ta cike da curiosity.
“toh gani nayi kamar shima maneji yake yi da rayuwar shi.. zai iya riqe mata a hakan??” ta fada kai tsaye.
STORY CONTINUES BELOW
Umma dai bata yi mamakin jin wannan kalaman ba daga bakin Mama domin kuwa kowa ya san halinta.. mai arziki kawai take so a rayuwarta. ita ta ma yi mamakin yadda suka dawo ta ji wai Layla ta tsayar da mijin aure. A yanzu da Abba ya gama basu labarin Sufyan kuwa ta tabbatar yarinyar tayi hankali.. ta dawo daga rakiyar uwarta.
“Wato Hindatu har yanzu baki yi hankali ba ko??? har yanzu baki canza wannan mugun halin naki ba ko?? shin abinda ya faru a baya bai zame miki ishara ba?? kin manta lokacin da kika dinga wulaqanta Zayd kika ziga yarinyar nan ta wulaqanta shi har ya koma ma Ameera daga baya al’amarin shi ya bayyana??? wannan din bai isa ya zama darasi a wurin ki ba??” Abba ya fada yana mai tir da halin ta.
“Ni fa Abban yara baku fahimce ni ba.. a wannan zamanin bazai yiwu yadda ake fama da matsalolin rayuwa ka dauki ‘yarka ka kai ta gidan da zata wahala…”
“Mama.. Ya isa haka. Wallahi bana son abinda kike yi.. ni babu ruwana da kalar arzikin Sufyan.. daidai gwargwado yana da halin shi.. he is well to do tunda dai babban likita ne kuma yana da gidan shi na kanshi da motocin shi. toh me zan buqata bayan wannan?? Ni kam har ga Allah ina son shi tsakani da Allah kuma ina fatan idan Abba yayi bincike akan shi aka gano baya da wata matsala muyi aure” Layla ta fada ranta a bace sannan ta miqe ta kalli su Abba tace “Sai da safen ku” ta wuce sashen su.
Gaba dayan su shiru suka yi suna mamaki. Lallai Layla ta gyara hali, who would have thought so???
Mama dai dauke wuta tayi yayinda tayi kamar wadda ruwa ya cinye.. ta rasa yadda aka yi Layla ta canza gaba daya. ita tana qoqarin samar mata hanyar da zata ji dadi a rayuwa tana botsarewa.2
“toh kin dai ji daga bakin yarinya.. don haka idan yaro bayada wata matsala zan bashi auren ‘ya ta. Idan kin ga dama ki sa musu albarka idan kuma baki dama ba shikenan, wannan ya rage naki”
Mama dai jikinta a sanyaye ta miqe ta wuce sashen ta yayinda ta bar su Abba suna mamakin hali irin nata.1
♤♤♤♤♤♤♤
ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA
Wuraren qarfe Goma da rabi na dare ya shigo gidan. Kai tsaye ya wuce sashen shi don kuwa ya tabbatar gimbiyar shi tana can.
Aikuwa yana shiga babban falon shi ya ganta kwance a kan kujera..
Sanye take cikin wata gajerar baby doll nightie tana latsa wayarta..
Qamshin turaren shi da ta ji ne ya sanya ta dago kai ta gan shi a tsaye yana qare mata kallo..
Tana murmushi tace “Welcome Habibi.. how did it go??”
Da sauri ya tsugunna a gaban ta tare da sakar mata kisses tun daga bakinta har zuwa cikinta yace “great..”
“Masha Allah, gaskiya nayi ma Ya Layla murna sossai”
Zayd wanda yake shafa cikinta ne yace “how are our little ones doing??”
Zayd da Ameera dai tun ba’ayi ultrasound scan an tabbatar musu cewar twins zasu haifa ba tuni sun ba kan su hope.. suna ji a jikin su lallai twins ne zasu haifa.
“they are fine.. kawai dai munyi missing dinka ne..” ta fada yayinda ta tashi zaune.
“Nima nayi missing dinku”
Gani nayi ya zauna a gefen ta kan kujera yayinda ta haye bisa cinyar shi ta kwanta a jikin shi kamar mage.
“ka ci abinci??”
“Yes my love, Umma ta bani abinci”
“so tell me about mijin Ya Layla??? Abba ya bada green light??? is it that same guy that visits her in school??”
“Nope….”
Daga nan ya fara bata labarin Sufyan da kuma yadda ya gwada yana so ayi auren da wuri.. blah blah blah!!!