ZABI NA CHAPTER 15 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 15 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

One month Later+

Tuni dai Iyayen Sufyan sun je gidan su Layla anyi magana ta fahimtar juna.. Sun tattauna a game da yaran su sannan sun aminta da juna.

Bincike dai iya gwargwado anyi kuma komai lafiya lau.

An sa lokacin biki wata biyu wanda a yanzu haka saura wata daya. Mama dai har yanzu bata amince da maganar Sufyan ba.. dayake dai Layla ta dawo daga rakiyar ta ko sauraronta ma bata yi.

Su Ibrahim dai ko da suka dawo hutun su na sati uku sossai suka yi blending da Sufyan.. suna son shi sossai kamar yadda shima yake son su. Ko da zasu koma school sai da yayi musu shopping na kayan ciye-ciye masu yawan gaske.

Abin mamaki a yanzu Layla ta gyara tsakanin ta da Umma.. sossai take bata girman ta kamar yadda tayi deserving. Haka tana yawan zuwa wurinta neman shawara. Hakan yana bata ma Mama rai amma kuma babu yadda ta iya domin kuwa ta kula sam Layla ta daina biye mata.

Abinda dai Layla ta kasa yi shine neman sulhu da su Ameera.. ba wai ta riqe su a zuciya bane amma haka kawai tana jin nauyin kalolin rashin mutuncin da tayi musu a baya.. sossai take jin kunyar su. Kai hatta wayar da Ameera ta bata kyauta watannin baya ta kasa yi mata godiya.. Ko a makaranta idan sun hadu bata iya kallon ta balle suyi magana.. Ameera tried to talk to her several times amma Layla sai tana kaucewa..

Ameera ta fahimci Layla ta gyara hali and she is super happy for her.. ta sani cewar tana jin nauyin ta kamar yadda take jin nauyin Zayd.. ta kula she wants to keep some distance between them for now.. afterall, bayan dukkan abinda ya faru dama zai yi wuya komai ya dawo normal a lokaci daya… she believes time will heal everything.2

♤♤♤♤♤♤

SUFYAN ABUBAKAR BICCI RESIDENCE

UNGUWAN SARKI

Zaune suke a falon shi tare da abokin shi mai suna Ammar Bello Nasidi.

Asali dai sun dade basu hadu da abokin nashi ba domin kuwa shi yana zaune ne a qasar Germany inda yake aiki da wani construction company. Mostly sai ya samu hutu ne yake shigowa qasar don sada zumunci a wurin ‘yan uwa da abokanen arziki. Yanzu haka satin shi daya da shigowa inda ya sauka a gidan iyayen shi a Abuja.

A yanzu kuwa ya zo garin Kaduna ne don ziyartar Uncle dinshi (wato qanin baban shi) Alhaji Aliyu Nasidi. Daga nan kuma ya fara ziyartar abokanen shi da suke nan Kadunan.

“Gaskiya I am happy for you abokina.. finally you’ve moved on”

“Wallahi kuwa abokina… ban taba zaton zan samu wadda zata maye gurbin Salma ba a zuciya ta. Layla is just so spec….”

Wayar shi ce da tayi ringing ta hana shi qarasa maganar da yake yi. yana murmushi yace “speaking of the angel..  she is the one calling me”

Gani nayi ya yanke kiran sannan ya kira ta video call.3

Ammar dai yana ta murmushi… from all indication he seems to be very happy for his friend!

Ko da Layla ta amsa wayar na leqa na hango ta sanye cikin hijabi tana murmushi.

“Masoyi na ya kake??”

“I am good masoyiya ta.. ya gida?? ya kuma stress din school???”

“Alhamdulillah.. ka ci abinci dai ko??”

STORY CONTINUES BELOW

“Yes ma’am” ya fada yana murmushi.

“Allah yasa dai yau babu shift din dare.. ka zauna a gida ka huta. bana so kana stressing kanka dayawa”

Ammar wanda yake sauraron su ne yayi gyaran murya wadda ta sa Sufyan fashewa da dariya.

“Masoyi waye a tare da kai?? like you’re not alone in the house”

“Yes dear, wani long lost friend dina ne ya ziyarce ni. Sunan shi Ammar.. bari in bashi ku gaisa”

Daga nan Sufyan ya miqa ma Ammar wayar.

Ammar dai yana karbar wayar ya ga fuskar Layla sai na ga yayi pause kamar wanda ya ga ghost..

“ina na san wannan fuskar??” tambayar da yayi ma kanshi kenan.2

“Assalamu alaikum.. ina wuni” ya jiyo muryar Layla wadda ta katse mishi tunani.

Ajiyar zuciya ya saki sannan yayi murmushi yace “wa’alaikis salam.. Gimbiya muna lafiya”

“lafiya lau”

“toh madallah.. ya karatu? ya kuma shirye-shiryen biki??”

“Alhamdulillah”

“toh Allah yasa ayi a sa’a.. Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a ta gari”

“Ameen nagode sossai”

“toh bari in barki haka… ga Sufyan, sai anjima”

“sai anjima” Layla ta fada yayinda ya miqa ma abokin nashi wayar.

Gani nayi Ammar ya miqe ya wuce kicin but looking so very much confused and worried.

why??

Bayan almost five minutes ne Ammar ya dawo falon riqe da tea cup.. har a wannan lokacin Sufyan yana ta hira da Layla a waya. Labari suke yi na kayan lefe da za’a kai nan da few days…

Ammar wanda ya zauna gani nayi yana ta sipping tea dinshi yayinda ya zama lost in thought.. he is definately trying to remember a wurin da ya san Layla. One good thing about him is idan ya ga mutum sau daya baya taba manta fuskar….

Ban ankara ba na ji yace “Ya Salam.. I remember”

Abokin shi wanda yake sallama da Layla ne ya dago kai ya kalle shi cike da mamaki.

Yana kashe wayar ne yace “hey what’s up??”

Ammar dai ajiye tea cup dinshi yayi yace “Your fiance, I know her from somewhere”

“really???” Sufyan ya fada cike da qaguwa na son jin inda abokin nashi ya san ta especially idan aka yi la’akari da shi din ba mazaunin Nigeria bane.

“Ka tuno Cousin brother dina Habib da ya rasu 3 months ago??”

“Yes I do.. Allah ya jiqan shi”

“Ameen.. uhm, she used to be his girl friend”

“ah okay.. amma ai babu matsala abokina, ko akwai???”

Ammar ya miqe tsaye tare da sakin ajiyar zuciya yace “I am afraid akwai matsala babba abokina. Uhm, I really dont want to be the one to say this but I just have to”

“whoa my friend kana bani tsoro…”

“Saurare ni abokina.. the thing is gaskiya akwai wani zuwa da nayi garin nan na je gidan Habib and I saw Layla there”

“uhm.. okay, it’s still not a problem… is it??”

Gani nayi Ammar ya zauna kusa da Sufyan sannan yace “abokina.. Habib dan uwa ne kuma dukda ya rasu Allah ya gafarta mishi, he wasn’t really a good person. Habib ya kasance yana tara ‘yan mata kala-kala. Nasihar duniyan nan babu wadda ba’a yi mishi ba amma baya ji.. ta kai ga har kwanciya yana yi da su, yayi aikin alfasha da su sannan ya basu kudi..”6

STORY CONTINUES BELOW

Sufyan wanda hankalin shi ya masifar tashi ne na ga ya fara shafa kanshi da hannuwan shi guda biyu… wata ajiyar zuciya ya saki sannan yace “dont tell me cewar Layla ma tana cikin matan da yayi mu’amala da su”

“I am not sure abokina.. ni dai na san na taba ganin ta a gidanshi kuma yanayin yadda na ganta she was kinda comfortable.. now
the big problem is idan har wani abu ya taba shiga tsakanin su then na tabbatar itama tana dauke da cutar da ta kashe shi..”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. cuta??? wace cuta kuma??”

“HIV AIDS”7

“what????” Sufyan ya fada a razane yayinda ya miqe tsaye… tuni zufa ta karyo mishi ta ko ina.2

Ammar ma miqewa yayi tsaye tare da sakin ajiyar zuciya yace “Yes abokina, kusan sama da shekaru biyar kenan da Habib ya kamu da wannan cutar.. he didnt tell anyone and according to yadda ya fadi mana wai a lokacin he began seeing a doctor in Germany wanda ya dora shi akan magunguna, ka san cewar cutar tana dadewa a jikin mutum kafin ta fara yi mishi illah musamman idan kana da kudi kana kula da kanka as per doctors’ orders.. You are a doctor and you know better than I do”7

“inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” Sufyan ya dinga maimaitawa yayinda ya koma ya zauna.. Duk sanyin AC da ke kadawa a falon bai hana shi yin sharkaf da zufa ba.

“kuskuren da yayi shine yadda ya cigaba da mu’amala da yaran mutane ya dinga yada musu wannan cutar.. now idan har yayi mu’amala da Layla toh babu tantama ya sanya mata wannan cutar” Ammar ya fada yayinda ya koma ya zauna a gefen abokin nashi.

“what am I suppose to do now? wallahi abokina I really love Layla.. kenan I should give her up???” Sufyan ya fada muryar shi tana rawa.1

“Noo, not yet abokina. Kai likita ne ai.. shawarar da zan baka shine kayi inviting dinta asibiti ayi mata test.. idan har komai daidai kenan babu abinda ya shiga tsakanin su”

“Yes good plan abokina.. I will do that ASAP” ya fada with a little bit of hope.

♤♤♤♤♤♤♤

FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE

MALALI GRA

Zaune suke a cikin motar shi kamar kullum idan ya zo hira.

Sufyan dai tun jiya da suka yi maganar Layla da Abokin shi gaba daya jikin shi yayi sanyi.. ji yayi ma kamar baya da lafiya don kuwa ko ofis ya kasa zuwa.. Allah ya taimake shi dama baya da patients dayawa.. don haka the few he has sai ya kira wani colleague dinshi ya roqe shi akan ya duba mishi su. Babu abinda yake so ya ji a rayuwar nan irin a gama komai a ce she is okay!

Ni kuwa da na San tabargazar da Layla tayi a baya nace is there a chance she is okay???9

“Masoyina wai ya na ga kamar baka jin dadi.. lafiya kuwa???” Layla ta fada cike da damuwa.

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “lafiya lau masoyiya.. I am just tired ne”

“ayyah..  gaskiya yakamata ka dauki hutu. You seriously need rest”

“Yeah ai dama zan dauka lokacin bikin mu.. I wouldn’t want anything interfering in our honeymoon”

Zuciyar Layla ce ta buga a dalilin wannan kalaman na Sufyan.. Allah ya sani a duk lokacin da ta tuno yadda zai same ta sai hankalinta ya tashi.. Zai aure ta a matsayin budurwa amma kuma ba zai same ta a budurwa ba.. Dukda Layla ta samu mai gyaran jiki wadda take ta bata magungunan da zasu matseta ta sani cewar it will never be thesame..

“Masoyiya ta gobe Saturday tunda babu school zan zo mu je asibiti ayi mana wasu tests…”

Cikin rashin fahimta tace “tests masoyi??? ban gane ba.. rashin lafiya nake yi da har..”

STORY CONTINUES BELOW

“relax.. kin san yakamata idan za’ayi aure a tabbatar da lafiya.. besides its jut a formality”

For no reason sai jikin Layla yayi mugun sanyi a yanzu.. haka kawai sai ta fara ji kamar something will definately go wrong.. what is it though???

“toh shikenan masoyina.. Allah ya kai mu”

“ameen”

Daga nan dai suka cigaba da hira.. hirar da basu taba yin irinta ba domin kuwa daga shi har ita jikin su a sanyaye yake… kowa da abinda yake tunani. A haka dai suka yi sallama.

♤♤♤♤♤♤♤

5 days later

CITY-SHELTERS

ALI AKILU ROAD-KADUNA CENTRAL

Zaune yake a kujerar ofis dinshi wuraren qarfe Goma sha daya da rabi na safe yayinda yake duba wasu files a Macbook dinshi.. As usual yana yi yana sipping tea- something he can’t live without.

Wayar intercom ce tayi ringing yayinda na ga ya danna wani button.

“Yes Adriana”

“Sir, there is a man here to see you.. he goes by the name Sufyan Abubakar Bicci”

“Oh yeah.. send him in please..”

“right away sir”

Awa daya da ya wuce ne Sufyan ya kira Zayd akan yana son ganin shi and it’s very urgent.. a yadda Zayd ya ji muryar shi ya tabbatar it’s something serious don haka ne ya bashi appointment tare da reshecduling meeting din da yakamata yayi da staff dinshi zuwa bayan Zuhr.

Adriana ta qwanqwaso qofar Zayd ta bude sannan tace “please go ahead Sir”  yayinda tayi ma Sufyan nuni da ya shiga.

“thank you”

Zayd ne ya miqe tsaye yayinda Sufyan ya qaraso wurin shi suka yi musabaha.

“Please have a seat.. Ya gida ya aiki?? Zayd ya tambaye shi yayinda duk suka zauna.

“Lafiya lau.. ya naku??”

“Alhamdulillah..”

Adriana ce ta shigo riqe da tray a hannunta ta ajiye a gaban Sufyan wanda yayi mata godiya.. Murmushi tayi sannan ta fita.

“So how far what’s going on?? you sounded very worried on the phone sannan gashi yanayinka ma ya nuna hakan”

Ajiyar zuciya Sufyan ya saki sannan yace “dama ba wani abu bane, na fasa auren Layla”

“what?? calm down.. ban gane ka fasa auren Layla ba.. me ya faru?”

Anan dai Sufyan ya fara ba Zayd labarin abinda yake faruwa..

“…mun je asibitin tare da ita three days ago aka yi mana tests and today da na je asibiti shine aka bani results din…”

Gani nayi ya zaro wata takarda daga aljihun shi ya tura ma Zayd ba tare da yayi magana ba… Zayd wanda ya dauki takardar yana budewa ne yace “dont tell me she is..” bai qarasa magana bane na ji yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. she is HIV positive??”12

“…a gaskiya ina jin nauyin zuwa wurin Abba da wannan zancen shiyasa nayi tunanin in zo in same ka tunda you are practically their family and maybe you’d know how to tell him..”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. wacce irin rayuwa ce wannan??? I can’t believe this… uhm yanzu ya Abba zaiyi idan ya ji wannan?” Zayd ya fada hankalin shi a matuqar tashe.

“Wallahi nima abinda nake tunani kenan shiyasa ma bazan iya zuwa ba.. right now family house din mu zan je.. zan fadi musu cewar na fasa auren amma saboda in rufa mata asiri bazan fadi musu asalin reason din fasawan ba.. I will just cook up a story that will make things easy insha Allah”

STORY CONTINUES BELOW

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” abinda Zayd yake ta maimaitawa kenan. Gaba daya tausayin Abba ne ya rufe shi.

Ya zai yi idan ya ji wannan mummunan labarin? toh shi yanzu how is he gonna face him and tell him this bad news???

“Wallahi Allah a yau da ace cikin shege Layla tayi zan haqura in aure ta saboda ina son ta tsakani da Allah kuma na tabbatar tayi nadaman munanan Abubuwan da tayi a baya but amma ya zanyi da ita a yanzu?? I cant marry a woman carrying a deadly disease like HIV aids”

Gyaran murya Zayd yayi sannan yace “haka ne Sufyan.. Allah ma ya taimake ka da aka yi test din before marriage.. thank you very much for wanting to keep this away from your parents.. I will find a way to let Abba know insha Allah”

Sufyan ya miqe tsaye yayinda shima Zayd ya miqe suka yi musabaha..

“I wish you the very best Sufyan.. we will keep in touch”

“Nagode Zayd… Allah ya bar zumunci and please ka ba Abba haquri.. I just cant face him with this”

“you got it Sufy..”

♤♤♤♤♤♤♤♤♤

ZAYD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA

Zaune suke a kan kujerar falon shi yayinda yake rungume da ita yana ta lallashin ta.

Zayd dai ko da ya dawo gida ya sanar ma Ameera halin da ake ciki sai kawai ta birkice mishi gaba daya… Kuka ta dinga rusawa kamar wadda aka yi ma sanarwar wani nata ya mutu. Tausayin Layla ne ya cika ta..

“Yanzu shikenan Habibi babu yadda za’ayi Ya Layla ta warke??? babu wani likita a fadin duniyan nan da zai iya magance mata wannan cutar???” ta fada cikin kuka

“as far as I know Habibty, gaskiya babu.. the only thing da za’a iya yi shine a dora ta kan treatment wanda she can live long without any problem.. just that it’s very difficult for one to live peacefully knowing cewar yana dauke da cutar but I promise you habibty.. I will contact the best doctors across the world with regards to her treatment and I will support her financially no matter the cost insha Allah”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” ta fada yayinda ta fashe da sabon kuka.

Yana shafa cikin ta yace “please Habibty stop crying.. kin ga ba ke kadai bace. you are pregnant and the doctor has asked that you dont stress yourself… remember??”

“Habibi how can I stop crying? duk laifi na ne”

“how is it your fault??”

“A lokacin da na dinga yi mata nasiha maybe if I had pushed her harder duk wannan bazai faru ba..”

“hell no Habibty, every one is responsible for his or her own destiny.. Layla chose her path and it’s not your fault so please dont blame yourself for what she has done to herself..”

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya cigaba da fadin “Ni matsala na ma shine yadda Abba zai karbi labarin.. ban san ta ina zan fara yi mishi wannan zancen ba”

♤♤♤♤♤♤♤

FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE

MALALI GRA

Zaune suke gaba dayan su a babban falon Abba yayinda suka yi shiru suna sauraron Zayd wanda shima ya kasa magana.

Ameera wadda take zaune kusa da Umma sai share hawaye take yi yayinda duk suka zama confused.

Ita kanta Layla wadda take zaune kusa da Mama jikin ta a sanyaye yake.

Tayi mamakin jin an ce Zayd yana da magana da su duka ‘yan gidan harda ita.

“Zayd ka tara mu tun dazu sannan kayi shiru ka kasa magana… Ga Ameera tana ta share hawaye. Na tambaye ku abinda yake faruwa kun qi kuyi mana bayani.. Shin meye dalilin ka na tara mu a nan din??”

STORY CONTINUES BELOW

Gyaran murya Zayd yayi sannan yace “Uhm.. Abba dama akan maganar Layla ne..”

“Layla kuma?? me tayi???” Mama tayi tambaya kai tsaye.

Layla kuwa a yanzu jikinta ya qara yin mugun sanyi jin an ambaci sunan ta… what has she done??

“Muna jin ka” Abba ya fada

Zaro takardar hannun shi yayi sannan yace “dama Sufyan ne ya same ni a office dina yace ya fasa auren Layla”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” Gaba dayan su suka dinga maimaitawa amma fa banda Mama wadda da alama labarin yayi mata dadi.1

Layla kuwa sa hannu tayi a kai ta shiga rusa kuka.

“wai ban gane ba.. wani laifin tayi mishi ko kuwa???” Abba yayi tambaya confusedly yayinda ya juya ya kalli Layla yace “me kika yi mishi??? hala uwarki ta hure miki kunne kika wulaqanta shi ko??”

“wallahi Abba babu abinda nayi mishi..” ta fada tana kuka.

“Abba the problem is this..” Zayd ya fada tare da miqa mishi test result din.

“The thing is Sufyan ya kai Layla asibiti suka yi tests.. unfortunately nata ya fito HIV positive” Zayd ya qarasa fada in a low tone..

“what??? Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” Layla ta fada yayinda ta miqe tsaye dafe da qirji.. gaba daya jikinta rawa yake yi.

Abba kuwa gani nayi ya dafe qirjin shi yayinda ya qura ma takardar idanuwa.. Mama da Umma kuwa da basu gane abinda ake nufi ba sai faman tambaya suke yi.

“Layla??? tana dauke da cutar qanjamau???” Abba ya fada

Wani uban tsalle Mama ta daka yayinda ta dafe qirji tana fadin “na shiga uku ni Hindatu… cutar qanjamau?? ai wallahi qarya ne.. sharri za’a yi ma ‘ya ta”

Umma dai salati ta shiga yi.

Gani nayi hawaye sun fara bin fuskar Abba yayinda yayi folding test result din ya ajiye a gefe ya miqe.. Da sauri Zayd ma ya miqe domin kuwa ya riga yayi sensing akwai matsala.

Aikuwa Abba yana taka qafar shi sai kawai jiri ya kwashe shi.. Allah ya taimaka Zayd yana kusa da shi ya riqe shi.

Tuni Abba ya suma..

Umma da Ameera suka yi kan shi suna salati. Zayd ya fita da gudu don kiran masu aikin gidan su taimaka a dauki Abba a sa shi a mota don zuwa asibiti.

Ita kuwa Layla duqewa tayi qasa tana rusa kuka.. kukan da bata taba yin irin shi ba..

Mama kuwa surutai na banza na ji tana yi wanda ban gane kan su ba… da alama dai she is in shock ne.

2 days later

Kwana biyu kenan da aka kwantar da Abba a Garkuwa Hospital. Abba dai a dalilin shocking news din da ya ji jinin shi ya hau.. A yanzu haka yana under close watch na likitoci saboda ba’a so a samu any slight problem that could lead to a heart attack.5

Zayd ya so a fitar da shi qasar Saudiyya amma likitocin suka hana a dalilin taimakon gaggawa da yake buqata.. dukda haka an tsayar akan idan ya zama stable za’a fitar da shi din domin kuwa shi Zayd din ya fi ganin quality na aikin likitocin qasar shi.5

Cikin ikon Allah kuwa washegarin ranar da aka kawo shi asibitin ya farfado.. abin mamaki shine ko da ya farfado he didnt panic instead ya nemi su bashi Al-qur’ani mai girma ya dinga karantawa yana samun sauqi a zuciyar shi.

Bai yi maganar Layla ba haka suma babu wanda yayi mishi.. Daga karatun Al-qur’ani da yake yi sai kuma bacci.. dayake akwai maganin bacci da ake bashi a medication dinshi in order to calm him down.

Tun ranar da wannan al’amari ya faru Mama da Layla basu zo asibitin ba..

Su Ammi sun zo sun duba shi… Abokanen Abba na unguwa da wurin aiki ma duk sun zo.

Zara da Mustapha ma throughout suna asibitin.

Su Ibrahim dai suna school don haka ba’a sanar da su abinda ya faru ba..

Wani ikon Allah babu wanda ya san abinda ya faru.. Hatta su Ammi basu sani ba. Kawai dai ciwo ne Allah ya saukar mishi.. a haka aka bar zancen.

A bangaren Layla kuwa tana can gida cikin tsananin tashin hankali.. tun daga ranar da baqin labarin nan ya dirar mata ta birkice.. tsawon kwanakin nan biyu ta kasa cin komai.. Ruwan ma a wurin alwala take sha.. cikin kwana biyun duk ta fige ta rame ta lalace kamar ba ita ba. Ko bacci sace ta yake yi wanda bata dadewa take tashi.. tayi kuka ta gaji, salloli kuwa yin su take yi kamar babu gobe.. roqon Allah gafara take yi babu sassautawa.. Layla tayi yunqurin kashe kanta sau dayawa amma sai ta kasa.. ta sani cewar musulinci bai goyi bayan Suicide ba, ta sani cewar babban laifi ne ka kashe kanka a addinin mu.. abinda ya zama mata wajibi shine roqon gafara a wurin Allah. Gaba daya ta tsangwami kanta da kanta.. Yanzu shikenan rayuwarta ta lalace har abada.. Cutar AIDS zata kashe ta.. duk kyan ta ya tashi a banza tunda tana dauke da cutar da babu wanda zai amince ya kusance ta.. shikenan komai nata ya zo qarshe.7

It’s obvious qarfin addu’o’in da take yi su suke keeping dinta strong.. ni kaina har mamaki nake yi na yadda ban ganta kwance ba a kan gadon asibiti.. Lallai abu ya kai inda ya kai!

Mama dai tun daga ranar da suka ji wannan mummunan labarin bata zauna ba.. hada ‘yan kudaden hannunta tayi ta fita don neman magani. Duk qawayenta da take tunanin zata samu biyan buqat
a ta wurin su ta je amma babu nasara.. da zarar ta sanar da su abinda yake faruwa sai su ja gefe suna yi mata fada akan yadda tayi sake ta bari son abin duniya ya ingiza ‘yarta ta kamu da cutar banza.. akwai ma qawayen da suka gargade ta akan ta ja baya da Layla kar ma ta kamu da cutar yayinda wasu suka fara qyamatarta kamar ma ita ce mai dauke da cutar..5

Haka dai ta dawo hankali a tashe babu solution.. abin mamaki kuwa shawarar da qawayen nata suka bata akan ta ja baya da Layla yayi tasiri a cikin zuciyarta domin kuwa tunda ta dawo ko hanyar dakin Layla ta kasa zuwa balle ta nemi ganinta…5

STORY CONTINUES BELOW

Tsawon kwanaki biyu basu sa juna a ido ba.. this is the time da yakamata ta kasance tare da ‘yarta, ta janyo ta a jiki tunda dai aikin gama ya gama babu yadda zasuyi amma inaaa.. instead sai ta nisance ta, bata san halin da take ciki ba, a raye ko a mace???9

☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!

FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE

MALALI GRA

Wuraren qarfe takwas da rabi na safe Layla ta fito daga dakinta wanda tana tafe tana dafa bango saboda wani mugun jiri da yake kwasar ta.. Gaba daya ta canza cikin qanqanin lokaci, ta birkice kamar wadda ta shekara batada lafiya.

Gani nayi ta nufi hanyar kicin yayinda take dafe da cikinta.. da alama dai yunwa take ji.

Nikuwa nace dole ta ji yunwa.. kwana uku babu ci.. banda ruwa da take sha wurin alwala ai da saidai a fitar da gawarta.

Aikuwa tana shiga kicin din ta nufi fridge ta bude ta dauki ayaba da apple… Nan da nan na ga ta cinye apple daya da ayaba uku.

Daga nan kuma wurin kayan tea ta nufa ta hada shayi mai kaurin gaske wanda tana yi jikinta har rawa yakeyi..

Gani nayi ta zauna a qasa kan tiles tana sha..

Shan tea din take yi amma sam baya mata dadi.. kai gaba daya babu abinda yake yi mata dadi a duniya.. jin ta take yi kamar ba ita ba..

Masu karatu just imagine the situation she is in right now!!

Tana daf da shanye tea din ne Mama ta shigo kicin din.. da farko bata ga Layla ba sai da ta kawo daf da ita sannan ta ganta..

Wani uban tsalle ta daka yayinda ta ja baya dafe da qirjinta tace “me kike yi a nan???”

Muryar ta tana rawa tace “tea nake sha”

Mama wadda ta qara matsawa nesa kadan tace “ai na gani… idan kin gama sha ki fitar da kofin waje”2

“waje?? meyasa??” Layla ta fada yayinda hawaye suka fara wanke mata fuska.

Gani nayi ta miqe ta cigaba da fadin “Yanzu mama qyama ta kike yi?? saboda na kamu da cutar qanjamau??” idan kowa zai guje ni a duniyan nan ai ke bai kamata ki guje ni ba.. banda wannan ma, kin manta ke kika sa ni a halin da nake ciki??”2

“Ni??? Ni Layla??? ni nace ki je ki kwanta da namiji ki aikata Zina ki kwaso cuta???”2

Layla dai kuka ne ya ci qarfin ta yayinda take mamakin kalaman Mama.. Tabbas bata ce mata ta aikata Zina ba.. infact right now she can’t even blame anyone tunda she is responsible for everything that is happening… da ace ta bijire wa munanan shawarwarin da ta dinga bata all these wouldn’t have happened..

“ni dai tsakani da Allah wannan cutar da kika kwaso matsala ce babba.. bazai yiwu kina amfani da abubuwa nima ina amfani da su ba.. don haka zan ware miki kayan amfanin ki daban sannan…”

Layla wadda take kallon Mama cike da tsananin mamaki sai kuka take yi… Gani nayi ta juya jiki a sanyaye ta fita daga kicin din.

Ita kanta mama sai da jikinta yayi sanyi toh amma kuma ita ya zata yi.. Allah ya sani tsoron cutar take yi.. yanzu haka tunani take yi na yadda zasu cigaba da zama tare a a gida daya..4

STORY CONTINUES BELOW

Ni kuwa nace kut… rayuwa kenan!!

Layla tana shiga dakinta ta fada kan gado tana ta kuka. Ji nayi tace “Na shiga uku, Yanzu kenan Mama qyama ta take yi?? uwar da ta haife ni?? idan har tana qyama ta kenan kowa ma gudu na zai yi??? ta ya zan cigaba da rayuwa knowing cewa ni da kaina na tsangwami kai na?? ga Abba kwance a gadon asibiti babu lafiya kuma duk a dalilina, ga masoyina Sufyan ya rabu da ni, gashi kowa a gidan ya sani cewar ina da cutar qanjamau.. it’s only a matter of time before su Ibrahim ma zasu sani.. toh wai meye amfanin zamana a gidan nan?? meye amfanin zamana a garin Kaduna??”3

Gani nayi ta miqe ta shiga dressing room tayi shirin wanka.. Ko minti goma bata yi ba na ga ta fito daga bathroom. Ina kallonta ko mai bata shafa ba.. turaruka kawai ta fesa sannan ta koma dressing room ta bude wadrobe dinta ta ciro inner wears da wata doguwar riga ta material ta sanya.

Wani akwati na trolley dan madaidaici ta janyo sannan ta koma wurin wadrobe din ta fara ciro kayanta tana zubawa… Da alama dai she is going somewhere ne

Ni kuwa nace ina zata je???

Bayan ta cika trolley din ne ta rufe ta sannan ta dawo dakin janye da shi ta ajiye a gefe.

Wayarta ta dauko sannan ta shiga contact.. ina tsaye a gefe na ga tayi dialing lambar Haleema sannan ta sa wayar a kunne.

“Leema kina ina ne???”

A dayan bangaren Haleema tace “wallahi gani nan na shirya zuwa Abuja.. akwai wani new catch dina ne da zan bi because yace he is gonna be free this weekend… and you know what that means for me ko?? yanzu haka yana waje yana jira na” ta qarasa har tana dariya.

“Please wait for me… zan bi ku”6

“what??? ke da kika ce mun kin tuba?? remember fa ranar har wulaqanta ni kuka yi ke da su Yussy don na fadi gaskiya besides ina shi sabon masoyin naki yake??”

“Ki bar wannan zancen Leema… something serious happened” ta fada yayinda hawaye suka fara bin fuskarta.. sai da tayi composing kanta sannan tace “ina zan same ki yanzu??”

“idan dai kina so sai mu biyo gidan ku mu dauke ki, ya kika gani???”

“toh shikenan”

Ni kuwa nace ‘oh shit, from frying pan to fire’

Bayan sunyi sallama ne na ga ta zauna zaman jiran Haleema.

Ko minti goma sha biyar ba’a yi ba kuwa Haleema ta kirata ta sanar da ita cewar suna bakin gate din gidan su. Aikuwa nan da nan ta miqe ta yafa gyale ta dauki hand bag sannan ta janyo trolley dinta.

A lokacin da ta fito Mama tana dakinta don haka bata ji fitar ta ba… dama dai itama Laylar bata bi ta kanta ba because she knows from what transpired between them a while ago ta riga ta gane matsayinta a wurinta.

Aikuwa tana fitowa wajen gate dinsu ta ga wata dalleliyar Range rover baqa.. Haleema ta sauke glass ta leqo tana kallonta cike da mamaki tace “qawa ta.. ya na ga kin rame ne?? kin yi ciwo ne kika zabge haka??”

Mamallakin motar wanda ya ga security riqe da trolley din Layla ne ya fito yayinda ya bude boot security din ya sanya a ciki.

Mutumin dai tunda ya fito daga motar ya kalli Layla bai sake dauke idanuwan shi daga kanta ba.. har ya bude boot din ya rufe ita yake kallo.

STORY CONTINUES BELOW

“Its a long story, ki bari idan muka isa muka kebe zan baki labari” Layla wadda take tsaye jikin qofar Haleema ta fada ahankali.

Bata ankara ba ta ji ance “bisimillah gimbiya.. “

Tana juyowa ta gan shi tsaye ya bude mata qofa yana jira ta shiga.

“Nagode” Layla ta fada yayinda ta shiga gidan baya jiki a sanyaye.

Security ne yace “Anty ki gaishe da Alhaji.. Allah ya bashi lafiya”

Shi duk a tunanin shi asibiti zata je wurin Abba wanda kayan shi ne a cikin trolley zata kai mishi.

Bayan ya rufe qofar Layla ya zagaya ya shiga ne ya tayar da motar suka hau hanya.

“Ina kwana, sorry bamu gaisa ba” Layla ta fada tana kallon mutumin wanda yake ta satar kallonta ta madubi.

“Lafiya lau gimb
iya”

Haleema wadda take murmushi tace “Kamar yadda na fadi maka she is my friend Layla..” ta dan waigo tace “Layla wannan sunan shi Tukur amma ana ce mishi Teekay”

Layla dai murmushi kawai tayi yayinda shi Tukur din yace “nice to meet you beautiful”

Layla bata kai ga amsawa ba Haleema tace “ai na ga tunda ka ganta ka zuzuce.. I am sure akwai magana”

Dariya yayi yace “ai magana tana hannun ki sarauniya.. da zaki amince in hada ku biyu..”2

“I dont mind at all.. idan dai zaka iya da mu ai shikenan” ta juyo ta kalli Layla tace “ko ba haka ba qawa ta??”

Layla wadda bata san me ke yi mata dadi ba a duniya ta qaqalo murmushi ba tare da tace komai ba… da alama ma bata ji me suka ce ba

Sun dauki hanyar Abuja yayinda Tukur da Haleema suke ta hira ne na ji Haleema tace “wallahi yau na ji jikina duk wani iri.. Kamar bani da lafiya”

Tukur yace “nima kusan haka wallahi…” ya shafa fuskarta tare da fadin “but I am sure idan mun isa ABJ zamu warware.. saboda i am sure kin tanadar mun kayan dadi kamar yadda na tanadar miki da ke da qawar ki” ya qarasa fada yayinda ya saukar da hannun shi bisa boobs dinta harda matsawa wanda ya sanya Haleema tayi ‘yar qara suna dariya.

Layla dai gaba daya bata sauraron su ma.. Hankalinta yayi mugun nisa na tunanin halin da take ciki.

☆☆☆☆☆☆☆☆

FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE

MALALI GRA.

Abba ne kishingide bisa doguwar kujera ta babban falon shi yayinda Umma take bashi fruit salad yana sha.

Minti talatin da tafiyar Layla ne suka dawo.. Abba dai ba wai likita yayi niyyan discharging dinshi bane amma a dalilin ya dame su cewar ya gaji da zaman asibitin ne ya sanya aka sallame shi.. Yanzu haka ma banda medication din da aka bashi, a kullum likitan zai dinga bin shi har gida yana duba jikin shi a kullum sau biyu.

Tunda Abba ya kwanta a asibiti Umma take tare da shi.. Ita kuwa Ameera a dalilin halin da take ciki bata kwana amma tana yini a asibitin. Babu yadda Zayd bai yi da Umma akan ta je gida ta huta ba so he can take the shift amma sam ta qi. Kayan da zata buqata ma Ameera ce ta koma gida ta kwaso mata.. Dayake dai sashen Mama da na Umma suna separate building ne duk zuwa gidan da Ameera take yi idan tayi abinda zata yi takan je sashen su Mama tayi ta qwanqwasa qofar su amma ayi banza da ita. She only go there to check on Layla domin kuwa ta sani cewar tana cikin one of the most difficult, if not the most difficult phase of her life.

STORY CONTINUES BELOW

Zayd ne a tsaye kusa da one of the windows na gidan yana magana da Bilal a waya yayinda Ameera ta fito daga dakin Abba tana fadin “Abba na hada maka ruwan wankan”

Abba wanda ya dan yi murmushi ne yace “thank you my daughter, Allah yayi miki albarka”

Tana murmushi itama tace “ameen Abba”

Umma wadda ta ajiye bowl na fruit salad din a kan side table ne tace “toh mu je in taimaka maka”

Abba ya miqe suka wuce dakin shi.

Zayd wanda yake tsaye yana magana a waya ne na ga ya juyo ya kalli Ameera wadda itama take kallon shi… Murmushi yayi sannan ya daga mata hannu yayi mata nuni da ta zo wurin shi..

Da sauri ta nufi wurin shi ta shige jikin shi suka rungume juna..

Suna a hakan har ya gama magana da Bilal a wayar..

tsawon minti uku suna maqale da juna ba tare da sun ce ma juna komai ba..

“Habibi”

“Na’am”

“thank you very much for every thing you have done for me and my family.. I can never repay you for all..”

“sssssshhhhh… Habibty please stop”

Yayi breaking hug din sannan yayi cupping fuskarta da hannuwan shi biyu yace “samun ki a matsayin matar aure alone is a blessing.. you are the best thing that has ever happened to me”

Gani nayi ta saki murmushin jin dadi yayinda ya sakar mata light kiss a baki sannan ya saki fuskarta ya tsugunna a gaban ta ya shafa cikinta yace “ga wasu special gifts nan kuma coming soon. Ya salaam.. I swear I am a lucky guy” ya fada yana dariya.

Ameera wadda take shafa gashin kanshi tana dariya itama tace “ai ni ce lucky one din Habibi”

“then I guess we are both lucky Habibty” ya fada yayinda ya miqe tsaye yana kallon agogon hannun shi.

“Habibty zan leqa ofis.. I have a meeting plus ina da wasu ayyuka da zanyi.. Please take care of Abba and incase of anything don’t hesitate to call me kin ji?”

“Okay Habibi.. but ya maganar da mukayi?? don Allah ka sa baki.. ka san fa tunda ka ga Abba yayi shiru bai ce komai ba akwai matsala..”

“kar ki damu Habibty, idan na dawo zanyi mishi magana.. Insha Allah komai zai daidaita”

“toh Habibi.. I will go and check on Ya Layla nima.. I can’t even imagine irin halin da take ciki yanzu”

Zayd yayi mata kiss a kumatu yace “everything will be fine Habibty.. please relax and don’t stress yourself… I will take care of everything”

Kafin tayi magana ne wayar Abba da take kan centre Ottoman na falon ta fara ringing. Ameera ce ta nufi wurin wayar ta dauka..

Gani nayi tana kallon fuskar wayar cike da mamaki…

“Layla???” ta fada yayinda ta kalli Zayd wanda yayi mata nuni akan ta amsa

Tana amsawa kuwa tace “Ya Lay…” bata qarasa ba na ji tayi shiru sannan kuma tace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” tare da sakin wayar.

Da sauri Zayd ya qarasa wurin Ameera yana fadin “Habibty lafiya???” yayinda ya duqa ya dauki wayar tare da kamo ta ya rungume because firgicewar da tayi ya bashi tsoro sossai.

“Hello.. who is this??” daga nan shima na ga yayi shiru yana sauraron abinda ake fadi mishi, ga Ameera maqale a jikinshi tana ta rusa kuka babu sassautawa..

Gani nayi ya kashe wayar ya jefar akan kujera yayinda ya dinga shafa bayan Ameera alamar lallashi amma fa ya kasa fadin komai..

A daidai nan ne Umma ta shigo falon ta gan su a wannan halin..

A rude tace “lafiya?? me ya faru??”

Jiki a sanyaye Zayd yace “Layla ce tayi hatsari a kan hanyar Abuja…”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. ba dai ta rasu ba????”4 Years Later!!

RIXOS THE PALM DUBAI HOTEL AND SUITES

PALM JUMEIRAH-DUBAI

Zaune yake a kan daya daga cikin kujerun lounge na lafiyayyen suite din da suke sauka a duk lokacin da suka zo qasar.+

Dayake kamfanin Zayd yana daya daga cikin wadanda suka yi project na wannan hotel din sun ware mishi special executive suite wanda ya zama kamar nashi ne.. they did this in order to show gratitude for what his company has done for them.

Riqe yake da wayar shi yana typing message wanda ban samu daman ganin abinda message din ya qunsa ba.

Sanye yake cikin wandon three quarter na sweatpant baqi da baqar polo T-shirt. Da na kalle shi da kyau sai na ga kamar ya qara zama yaro..

and I am like after 4 years??? chai…

Gashin kan nan nashi na larabawa wanda ya sha gyara ya kwanta sai qyalli yake yi.. gashin fuskar shi on point as usual.. in all dai he looked very handsome.

Ameera ce ta fito daga daki sanye cikin doguwar Jallabiya baqa mai masifar kyau.. da gani ka san wannan jallabiyar ba ta yara bace sannan budget din talakawa bazai dauko irin ta daga shago ba. Ni kuwa da na kalli Ameera da kyau sai na ga ta masifar canzawa.. tayi haske ta qara qiba-irin qibar nan mai sa mutum yayi kyau. Tsabar hutu da fatar Ameera ta ji har wani qyalli take yi kamar wata mai laulayin ciki.2

Qamshin turaren ta da ya hadu da nashi ne ya bada wani yanayi mai dadin gaske.. ni kuwa nace Lallai naira tana aiki a wurin wadannan mutane.5

Gani nayi ya miqe tsaye da sauri tare da ware hannuwan shi.. ita kuwa qarasowa tayi da sauri ta shige yayinda yayi hugging dinta very tight.

“You know I love you to the moon and back right?”

“I know Habibi.. I love you too.. very much”

Yana murmushi yayi breaking hug din tare da kallonta daga sama har qasa yace “Masha Allah Ameeran Zayd.. kinyi kyau sossai da har na fara tunanin yawan mutanen da zasu kalle mun ke” ya qarasa fadi yana gyara mata gyalen da ta yafa a kanta.

“Toh Habibi mu fasa fitar mana.. ni dama baka fadi mun inda zamu je ba kuma ma I swear I dont even feel like going out”

Girgiza kai yayi yace “nah, it’s very important that we go Habibty plus idan mun je zaki ga koma menene”

Murmushi kawai tayi tace “shikenan Habibi.. where are our angels ban ji motsin su ba.. ko ba tare zamu je bane??”

Ameera dai shekaru uku da rabi da suka wuce ne ta haifi yaran ta ‘yan biyu Mata kyawawa sannan farare sol masu kama da baban su sak.. Amna da Aira sun shigo duniya da qafar dama domin kuwa bala’in farin jini gare su.. so cute and adorable!! Yanzu haka shekarun su Uku da rabi.. tuni sun fara zuwa wata makaranta mai tsadan gaske da kyau a nan cikin garin Kaduna..6

“kar ki damu da su, Su Maheera sun zo sun tafi da su..”

“What?? su Maheera suna Dubai? yaushe suka zo ban sani ba???” Tayi mishi wani irin kallo sannan ta cigaba da fadin “Oya start talking, na san akwai abinda kake boye mun.. what have you planned this time around??? ka dai san ban iya reacting to surprises ba ko?? especially the ones coming from you”

STORY CONTINUES BELOW

Yana dariya ya ja hannun ta tare da fadin “nothing big my love.. let’s go, we are wasting time”

Haka ta bi shi suka fita.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ARMANI PAVILLION

BURJ KHALIFAH

Zaune suke a qayataccen Pavillion din wanda ya hadu iya haduwa yayinda suke ta ciye-ciye da shaye-shaye.. wannan wurin dai yana tsakar garden na hotel din yayinda ake hangen Dubai Fountain wanda yayi providing wani spectacular and entertaining backdrop.. mai karatu wannan wurin dai wuri ne na masu hannu da shuni domin kuwa you will only be comfortable if you are sophiticatedly dressed.

Wasu fararen yara na gani suna ta kai da komowa suna wasa.. A cikin su dai na gane Ridwan, Riyaz da Baby eesh yaran Zaheera sai kuma na ga wasu kyawawan ‘yan biyu farare sol masu kama da Zayd don haka ne na tabbatar Aira da Amna ne.. yaran gwanin ban sha’awa duk inda suka gifta ana ta kallon su.

Da na juya ne na hango wasu samari guda hudu zaune a kujerun su suna ta hira yayinda suke ta ciye-ciye abin su.. ina matsawa kusa da su kuwa na ga ashe su Ibrahim ne.. dukkan su sun qara girma sun goge sun zana big boys sunyi kyau sossai… Masha Allah!!

Da na matsa kuma na ga wani table dauke da Zarah da mijinta Mustapha, Zaheera da Mijinta Sadiq sai kuma Maheera da Meher.. Dukkan su dai gwanin ban sha’awa. Gani nayi wata riqe da Baby wanda bai wuce wata biyar ba ta nufi wurin Zarah ta miqa mata shi… Babu shakka babyn Zarah ne sannan wadda ta miqa mata shi bazata wuce Nanny dinshi ba.

Na juya kan wani table din kuma sai na hango Abbu, Ammi, Umma da Abba a zazzaune cikin shiga ta alfarma.. Ni kuwa nace lallai abun babba ne tunda harda dattijai ma sun hallara.6

Wani table din da na hango kuma wasu kyawawan Fulani ne mata da maza.. babu shakka close relatives din Ammi ne..

Sai kuma wani table din na hango wasu larabawa su ma din dai da gani na san mutanen Abbu ne na Saudiya.

Da na juya kuma sai da na zaro idanuwa a dalilin ganin su Anty Khadija (Qannen Abba) harda mazajen su.. gaba dayan su sun canza sun qara kyau kamar fa ba su ba.

Ni kuwa nace lallai Zayd yayi qoqari sossai wurin inganta rayuwar inlaws din shi gaba dayan su.. Masha Allah!

Wata na hango a tsaye nesa da su tana waya yayinda ta juya bayanta.. ina tafe zan je wurinta don in ga ko wacece na ji an sa ihu ana tafi..

Ko da na juyo kuwa sai na ga Zayd da Ameera suna shigowa Pavillion din yayinda fuskar Ameera tayi displaying tsananin mamaki na yawan mutanen da ta gani..

“what’s happening???” Ameera ta fada ahankali.

Da sauri ta qarasa wurin su Zarah da su Zaheera suna ta rungume juna suna gaisawa yayinda Zayd ya nufi wurin abokin shi Mustapha..

Daga kai da Ameera tayi ta hango su Umma sai ta sa ihu yayinda ta ruga wurin su.. haka aka dinga yi mata dariya.

Ni kuwa ganin haka ne na tabbatar lallai sun dade basu hadu ba..

Daga nan fa ta dinga bin tables din kowa tana ta gaisawa da su.. ‘Yan biyun nata kuwa tunda suka  ganta suke ta bin ta.. duk inda ta daga qafa nan suke sauke nasu.. they kept following her trail kamar tails… Its evident suna bala’in son Uwar tasu ne.

A lokacin da Ameera take tsaye a table din su Ibrahim suna gaisawa ne ta jiyo muryar Zayd ta ear-mic yayinda yake fadin “May I have every one’s attention please”

Daga nan fa hankulan kowa suka koma kan Zayd.. Ameera wadda take tsaye itama ta juyo tana kallon shi yayinda take admiring how cute he looked.. duk qure gayun da baqin nasu suka yi gaba dayan su babu wanda yayi kyan da Zayd yayi (ni kuwa nace ba dole ba.. tunda mijin ki ne) Gashi shi din ba gayu yayi ba tunda dai sanye yake cikin qananan kaya… Qananan kayan ma na zaman gida.. Ya fito so simple kamar wanda ya fito yawon shan iska.

STORY CONTINUES BELOW

“Uhm ina yi ma kowa godiya na amsa gayyatan zuwa wannan taron da kuka yi within this short notice.. I really appreciate! na sani cewar kun san dalilin da ya sanya nayi gayyatar but well, I have something to say.. something that na san kowa ya sani but I feel I need to say it again.. infact I could keep repeating it over and over again till the day I die”

Gaba daya aka fashe da dariya.

Yana murmushi na ga ya kalli Ameera wadda take tsaye nesa da inda yake sannan yace “Habibty please come here..”

Tana murmushi ta fara approaching dinshi yayinda yace “Kyakyawan Zabin da nayi a iya tsawon rayuwa na shine auren Ameera.. a tare da ita na samu dukkan natsuwa, na samu dukkan soyayya, na samu dukkan kulawa, na samu mata mai riqon addini mai hankali, sannan ‘ya’ya na sun samu uwa ta gari”

Ameera wadda ta cika da kunya gani nayi ta sa hannu ta rufe fuskarta briefly tare da girgiza kai.. A lokacin da ta qaraso wurin shi kuwa hannu ya miqa mata yayinda ya janyo ta jikinshi ya rungume tare da fadin “A kullum ina gode ma Allah da ya bani Ameera a matsayin mata sannan Uwar ‘ya’ya na”

Yayi breaking hug din sannan ya kalle ta cikin ido.. itama shi take kallo yayinda kunyar iyayen su ya cika ta.. Zayd surely knows how to embarrass her.. da ta san zai yi mata haka da tayi cooking up wani story da zai hana ta fitowa..

“Habibty, I love you very much. Ke ce ZABI NA a koda yaushe.. even for a second ban taba regretting zabar ki a matsayin mata na ba.. you are the best thing that has ever happened to me… I actually may not have the right words to express you how I feel about you and how blessed I am that you came into my life. I just want to let you know that I love you with everything I’ve got and can’t imagine a life without you”

Manyan baqin nasu ne na ji suna fadin “awwwnn… masha Allah.. wow….” da sauran su

Ita kuwa Ameera tana murmushin jin dadi ta huro mishi kisses tare da fadin “thank you Habibi and I love you too..”

Gani nayi Bilal ya matso wurin su riqe da wani dan qaramin cute box na Zobe tare da budewa.. aikuwa yana budewa wani lafiyayyen diamond ring ya haske mun fuska..

Ya Salaam.. ban taba ganin Zobe mai kyan wannan ba.. very simple and
unique… Its a custom-made, a very expensive one. infact wannan zoben ya ba millioyin naira baya.

Zayd ne ya ciro Zoben tare da duqawa har qasa kamar dai yadda turawa suke yi sannan ya kamo hannun Ameera.. Gani nayi ya zare daya daga cikin Zobunan zinarin da suke yatsun ta ya hada da dayan.. Hakan kuwa ya ba mutane dariya sossai. Ita kanta Ameera dariya take yi… Ya za’ayi zobe biyu su zauna a yatsa daya???

Diamond ring dinshi ya Zura mata a vacant yatsar tare da fadin “Dear Habibty, Please Marry me again and never leave my side. Dagaske bazan iya rayuwa babu ke ba.. You are the love of my life and I cant imagine living in this world without you”

Da sauri Ameera ta duqo tare da birkita gashin kanshi tana murmushi tace “Hey handsome, I will marry you over and over again.. Ameera taka ce har abada. I love you so very much too.. more than life itself”5

Gaba daya mutanen da suke wurin kuwa suka dinga tafi.. hatta iyayen su were so happy to see how very much their children love each other. Umma har hawaye na farin ciki tayi ganin irin soyayya da kulawar da ‘yarta take samu a wurin mijinta.

Zayd wanda ya miqe tsaye ya rungume Ameera ta gefe ne yace “one more thing my love”

Ameera tace “what???”

Gani nayi yayi pointing at dogon ginin burj khalifah yace “there… I bought you a flat on the 20th floor of this building as our wedding anniversary gift to you..”

Zaro idanuwa Ameera tayi wanda kafin tayi magana suka ga wani haske ya bayyana a sama daidai saitin 20th floor din burj Khalifa..

wani 3D reflection suka gani na rubutu kamar haka “Happy wedding anniversary to us Habibty.. I love you to the moon and back”2

STORY CONTINUES BELOW

Daga nan kuwa Fireworks suka dinga tashi stylishly wanda ya birge matuqa.. It was such a beautiful sight to behold, abun dai gwanin ban sha’awa.

Ameera wadda take cikin shock na suprise gift din da Zayd ya bata ne na ga ta janyo shi da sauri ta rungume shi tare da fashewa da kuka yayinda gaba daya dangi aka dinga sanya albarka ana ya yabawa…

Maganar gaskiya ita ce Zayd yana da kudi na fitar hankali sannan yana kyautata ma iyalin shi to the core, hatta far relatives dinsu suna amfana matuqa da arzikin shi (both from his side and Ameera’s) not to mention bayin Allah talakawa da yake taimaka wa. Yanzu haka ya kashe millions of naira in order to get the apartment for Ameera..

Over these years Dubai has become like a second country for them.. basu shige wata basu je qasar ba saboda Ameera tana bala’in son zaman qasar… As usual her every wish is his command shiyasa whenever they are both free sai kawai suyi tafiyarsu can su huta… Kai hatta ‘yan biyu a Dubai aka haife su.

wannan kenan!

Ameera dai da qyar ta natsu ta daina kuka yayinda ta shiga yi ma Zayd addu’o’i iri-iri.. tun yana amsawa da ‘ameen’ har ya koma yana ta kwasar dariya saboda she kept wishing him every good thing there is on earth and the hereafter without realizing cewar tana ta repeating..

A haka ne dangi suka dinga zuwa wurin su suna ta yi mata congrats tare da yi musu fatan alkhairi..

A daidai lokacin da dangin Abbu na Saudiya suke congratulating din Ameera ne na jiyo wata familiar voice daga baya…

“Congratulations Sis..”

Juyowan da nayi kuwa na hango ta yayinda na cika da mamaki.. Wa nake gani???

“Ya Salam.. Sis ashe kin zo???”

Ni dai ware idanuwa nayi don tabbatar da wadda na gani a tsaye…

LAYLA??? How????3

“Yes sis” ta fada yayinda itama take murmushi.

Masu Karatu ga Layla na gani.. Babu shakka itace wadda na hango dazu tana magana a waya wadda ban samu daman ganin fuskarta ba.. Sanye take cikin wata doguwar flowery material gown yayinda ta nade kanta da wani gyale matching color with the material. Layla ta dan yi duhu kadan amma kuma kyan nan nata yana nan, bata qara qiba ba but ta dan rame…

Da sauri Ameera ta matsa wurinta suka yi hugging juna very tight yayinda na ji Ameera tana fadin “how are you Ya Layla??”

“I am fine Ameera… Alhamdulillah”

Ameera tayi saurin breaking hug din sannan tace “How is Ya Anwar????”

Bata rai tayi sannan tace “he should be fine”

Ameera tayi murmushi tace “hmmm.. Ya Layla not fair”

Layla wadda da alama bata son zancen Anwar din ce tace “yeah well please dont start with your lectures, I am really happy for you.. Allah ya sanya alkhairi  ya cigaba da sa albarka a auren ku.. Allah kuma ya kawo yan hudu at a time”

Ameera ta zaro idanuwa tace “what??? ‘yan hudu Ya Layla?? ashe zan baki guda uku kyauta kenan”

Layla ta fashe da dariya tace “inyi ya da su?”

Ameera tana dariya tace “but hey you look good, Masha Allah..”

Layla ta dan ja ma Ameera kumatu tace “…all thanks to you and your husband Ameera.. I really can’t thank you enough for what you guys are doing for me… Allah ya saka muku da alkhairi”

Ni kuwa nace me sukayi mata???

“haba dai Sis, idan bamu yi miki ba wa zamuyi wa???” ta kamo hannun Layla tace “na san baku gaisa ba.. zo mu je ku gaisa”

Daga nan suka nufi wurin da Zayd yake tare da abokin shi Mustapha.. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *