ZABIN SAMHA CHAPTER 6

 ZABIN SAMHA CHAPTER 6

Karan karfen dataji ya sauka a kasa ne yasa Samha ta bude idanunta. Ganin abunda yake faruwa a gabanta ne yasa ta kara zaro idanu.

Sabah ta gani ya cakume kwalar Zack sai faman zabga mishi naushi yakeyi ta ko ina yana fadin “Bakada hankali ne Zack? Kasheta kakeso kayi ne ko me? Toh idan daman kana rike dani ne a zuciyarka to ka fito filli ka tunkareni ba wai ka biyo takanta ba”. Sabah ya karasa maganar yana cigaba da kai mishi duka da naushi ta ko ina.

Zack dayaji duka, azaba iya azaba ya bude baki a wahale ya soma fadin ” Aliyah ta taso tun muna yara tana dawainiya da sonka har zuwa yanzu amma kai ko ajikinka. Meyasa bazaka sota bane eh?”

“So kake na sota saboda inajin tausayinta ne ko meye?! Ana so dole ne wai?!” Sabah ya tambayeshi a tsawace.

“Kai kadai Aliyah takeso, ka tausayamata ka sota ko da kadan ne”.

“Toh baza’a sota din ba. Kai har waye da zaka bude baki ka fadamun abunda ya kamata naso? Me ka sani game da so?”. Sabah ya tambayeshi yana zaro mishi idanunsa da suka kankance saboda tsabar masifa da tashin hankali.

Cikin zafin nama da karfin hali zack ya mike ya tura Sabah ya kai mishi naushi a ciki yana fadin ” kaima me ka sani a game da so?! Babu wanda ka taba so a rayuwar ka Sabah, don haka kaima babu abunda ka sani a game da so” zack ya fada yana kara kaiwa sabah naushi a ciki.

“Kai kuma a garin ku haka ake nunawa mutum so? Bakada hankali”. Wani irin wawan naushi Sabah ya kai mishi a fuska, har sai da yaji wani irin duhu ya rufeshi ya fadi a kasa, Sabah bai tsaya nan ba haka yabi takanshi ya dinga zuba mishi ruwan naushi ta ko ina. Zack sai mutsu mutsun azaba yakeyi ya kasa kwatan kansa.

Samha dake tsaye cikin ruwan tana kallon abunda ke faruwa a gabanta, hankalinta a tashe ta soma fadin ” Dan Allah ya isa hakan ku bar wanan fadan da kukeyi”.

Sabah ko ta kanta bai bi ba haka ya dinga dukan Zack. Juyowa yayi ya hango karfen da Zack ya riko yashe a kasa. Idanunsa ne suke rufe, zuciya ya dibeshi ya mike daga kan Zack yaje inda karfen yake yashe a kasa ya dauko ya sake nufo inda zack yake kwance a kasa, yana zuwa yayi saitin kanshi zai buga mishi karfen.

Samha na ganin abunda ke shirin faruwa wani irin bugawa kirjinta yayi bata san sanda ta karaso a guje ba tazo ta juya baya ta rufu akan Zack tana kokarin kareshi.

Sabah har ya dago da karfen zai bugawa Zack, sai ganin Samha yayi a gabansa tana kokarin kare Zack, cak ya tsaya ya dakatar da abunda yake shirin yi. Ruwa na zubowa ta ko ina a jikinsa ya tsaya yana kallonta.

A hankali Samha ta dago tana dubansa, kanta ta girgiza mishi alamun kar yayi haka, ta soma fadin ” Sabah karka yi haka,don idan ka aikata hakan bazai taba haifar da da’ mai ido ba, nasan ka sarai bazaka taba yafewa kanka ba idan hakan ya faru. Kaji please Sabah”.

Sabah shiru yayi yana processing kalamanta, daga bisani ya jefar da karfen a kasa. Hanu yasa ya dagota daga inda take tsugune ya juyo da ita yana fuskantar Zack ya soma fadin “Zack wallahi wallahi kaji nayi maka rantsuwar musulmi ko, idan na sake ganin ka tunkare Samha da niyan taba koda gashin jikinta ne, toh sai nayi maka mumunar ila, don haka daga yau sai yau, ka fita daga harkanta, don idan kayi wani abu da har ya taba lafiyanta bazan taba yafe maka ba”.

Yana gama fadin haka ya juya ya soma tafiya hanunsa rike da Samha wace taketa faman waigowa cike da damuwa tana duban Zack dake kwanace a kasa ruwa nata faman dukansa.

Bayan sunyi nisa wani irin razananen kara Zack ya sake yana zubda hawayen nadama . Aliyah ce ta karaso ta tadda shi a kwancen itama hawaye ne ke zubowa bisa kuncinta ta tsaya tana kallonshi.

Sabah da Samha har sunyi nisa suna tafiya still Sabah yana rike da ita, Samha ta kira sunanshi a hankali tana dubansa “Sabah?……”

Sabah shiru yayi bai ce komai ba daga bisani ya soma fadin “Dazun saura kadan na ji miki ciwo, ban san ya akayi hakan ta faru ba”.

Samha ta sunkuyar da kanta sa’anan tace ” karka damu, babu abunda ya sameni ai”.

Sabah ne ya tsaya ya juyo yana kallonta sa’anan ya bata fuska yace ” kina abu kamar wace takeda karfi, kina tunanin da badin na rike kaina ba ai da na raba wanan katan kan naki gida biyu”

Samha shiru tayi bata ce komai ba sa’anan ta soma magana cikin sanyi murya ” Banaso naga kun jiwa junanku ciwo ne” ta karasa maganar ta dago tana dubansa.

Sabah shiru yayi idanunsa suka soma haska masa yanda ya daga karfen zai bugawa Zack da kuma yanda tazo ta rufu akansa. Shiru yayi cikin zurfin tunani daga bisani ya sake rukon daya mata a hanu ya soma tafiyarsa ya barta tsaye a wajen.

“Sabah….” samha ta kira sunansa cikin dagin murya. “Ina kuma zaka?”

Sabah bai juyo ba ya bata ansa da ” Gida mana, zan kaiki ki canza kayan jikinki, kinga duk a jike kike.” Yana gama fadin haka ya cigaba da tafiyarsa.

Har ya danyi nisa da tafiya, Sabah ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” gwanda ma ki kawar da wanan tunanin da kikeyi don babu abunda zai faru”.

Yana gama fadin haka ya sakar mata murmushin na nasa mai tsuma zuciya sa’anan ya kara gaba ya tafi ya barta tsaye a wajen.

Samha harara ta watsa wa bayanshi sa’anan ta soma binshi har zuwa inda yayi parking motarsa, suka shiga tare yaja. Straight gidansu Samha suka nufa, mai gadi ya bude musu gate suka shiga. Zuwa lokacin ruwan saman ya danyi sauki da zuba.

Suna shiga parlourn, lami kadai suka tadda tana dan aiki a kitchen, suka gaisa Samha ta haura sama zuwa dakinta taje ta canza kaya, Sabah ya nemi wuri ya zauna a parlourn.

Bafi minti biyar ba sai ga Samha ta sauko kasa hanunta rike da hand towel tazo ta mika masa tace ya dan samu ya goge jikinshi da sumar kansa daya jike. Sabah bai ce komai ba ya karba towel din.

Samha ta mike ta shiga kitchen ta hado musu shayi mai kauri da zafi a cup ta shigo ta ajiye a centre table dake parlourn sa’anan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantarshi.

“Sabah ya baka goge jikin naka ba, kar sanyi fa ya kama ka”. Samha ta fada tana dubansa, Sabah shiru yayi bai ce mata komai ba.

“Toh ga shayi nan na hado, sai ka samu kasha”. Nan ma banza yayi da ita bai dago ya dubeta ba.

Samha ta dan tabe baki sa’anan tace “Sabah, ko dai har yanzu kana fushi akan abunda ya faru ne”.

Sabah ko juyowa baiyi ba ya kalleta balle ma ya bata ansa, hanu yasa ya dauko kofin shayin dake gabansa ya kawo daidai saitin bakinta. Samha murmushi ta dan sake har ta mika hanu zata karba, sai kuma taga ya dauke kofin ya kai bakinsa ya soma shan kayansa.

Harara Samha ta watsa mishi tana turo baki, shikam ko ajikinsa ya cigaba da kurban shayinsa. Sai daya kurba san ransa sa’anan ya bude baki ya soma fadin “Bakiji tsoro ba?”

“Tsoron me?” Ta tambayeshi tana dubansa.

“Zack, bakiji tsoron abunda zai miki ba dazun?”

Samha shiru tayi sa’anan ta girgiza kai tana fadin ” Tunanin wanan bai zo mun ba, nidai tsorona da fatana a lokacin, bai wuce karku jiwa junanku ciwo ba”.

“A haba, da gaske kike kenan” sabah ya fada mata yana hararta.

Samha bata damu ba, tasa hannu ta janyo towel din data kawo mishi, ta bude sa’anan ta soma goge masa lalausar sumar dake kwance bisa kansa dashi

Sabah bai hanata ya bari ta cigaba da goge masa ruwan. Bude baki yayi ya soma fadin ” Naji dadi daya kasance kina wurin, don daba din ke ba, ban san me zan masa ba” ya karasa maganar cike da jin haushi, ya kwace towel din da take goge masa kansa dashi ya jefar kan kujera sa’anan ya mike yaje ya tsaya wajan window fuskarsa dauke da damuwa ya cigaba da fadin “share kawai, don’t mind me,kawai ina jin haushin kaina ne akan abunda ya faru”.

Samha tana zaune ta kura masa ido tana kallon yanda duk yabi ya shiga cikin damuwa. Nan ta soma tuno da kalaman Amjad inda yake fadin cewa Sabah yanada kaifin tunani da hankali sosai don, baya iya juriyan yaga mutum cikin matsala ya kyale, hasali ma sai dai ya daura wa kansa laifi ya toye wa kansa farin ciki don kawai yaga ya faranta maka. Wani irin sonsa ne da tausayinsa ya soma karuwa cikin zuciyarta, ta cigaba da kallonsa.

Bangaren su zack kuwa, bayan barinsu Sabah wajen, jiki duk yayi tsami ya mike zuciyarsa cike da nadamar abunda yayi. Hawaye ne masu zafi suka cigaba da gangaro masa. Yana dagowa sukayi ido biyu da Aliyah wace fake tsaye tana kallonshi hawaye masu zafi suna zubo mata. Wani irin tausayin kanta da tausayin zack dinne ya mamaye zuciyarta.

Ta karaso ta tsaya inda yake kanta a sunkuye tana zubda hawaye cike da nadamar abubuwan data dinga aikatawa.

Dagowa tayi tana duban Zack sa’anan ta soma magana cikin sheshekar kuka.  “Zack bakada hankali, Meyasa zaka aikata hakan Zack eh? Meyasa kayi haka?! Ta karasa maganar tana rushewa da wani irin kuka.

Zack i’ina ya soma yi yama rasa mai zai ce mata. Aliyah ta dan lafar da kukan nata sa’anan ta cigaba da fadin ” A da ina yiwa Samha kallon wawiya wace bata waye ba saboda yanayin da take yin abubuwa da kuma halayenta. Yan’mata masu irin halayenta kwata kwata bana shiru dasu don irinsu haushi suke bani amma sai kum na gani ba haka bane. Samha batada kusanci dani amma bakaga yanda ta dinga mun fada rananar ba data gano abunda nayi don naja hankalin Sabah zuwa gareni, sai ta dinga mun fada kama wace ta damu dani, kamar wata yar’uwarta. Samha tanada zuciya mai kyau Zack” Aliyah ta fada ta sake rushewa da wani kukan.

Zack shiru yayi yana sauraronta nan ya tuno da abunda Samha tayi dazun, duk da dai yazo da niyan yaga bayanta ne amma hakan bai hanata zuwa ta taimaka mishi ba alokacin da Sabah ya dago karfen zai buga mishi. Wani irin sabuwar nadama ce ta soma ziyarta zuciyarsa, yana danan sanin abunda ya aikata, bude baki yayi ya soma fadin ” a gaskiya Samha batada matsala don hankalinta da tunaninta daban yake, gashi tanada saurin yafiya, batada ruko sam a zuciyarta”.

Aliyah ce ta cigaba da fadi hawaye nata faman gangaro mata “A duk lokacin danaga Samha Zack, sai na dinga ganin muni na, sai na dinga ganin kwata kwata ban cancanci soyayyar Sabah ba”.

“Karki ce haka Aliyah, ki daina…”

Aliyah bata saurareshi ba ta cigaba da fadin ” A zahiri ina nunawa cewa na tsaneta ne amma can kasan zuciyata ina kwadayi da kishin halayenta ne kawai, saboda nasan bawai kyawawan halayenta ne suka janyo Sabah gareta ba a’a ina kishi ne saboda yanda take mu’amala da kowa tsakaninta da Allah, bata sa komai a ranta.”

Zack ya kamo hanunta ya soma magana a hankali yana fadin “Aliyah kisani kema kinada kyau da kuma naki kyawawan halayen, ni nasan da hakan”.

Aliyah ta dago tana dubansa da jajayen idanunta tace “Ban gane ba Zack, mai kake nufi?”

“Gaskiya Samha ta fada miki ranan, daga yau karki sake jiwa kanki rauni ko makamancin haka akan kinaso ki jawo hankalin Sabah gareki. Aliyah idan baki so kanki ba, taya zaki nunawa wani so? Ki fara da kanki tukuna. Ni kuma na miki alkawari zan shayar dake irin son da baki taba gani ba Aliyah.”

Wani irin hawaye ne masu zafi suka cigaba da gangarowa Aliyah tana sauraran kalaman Zack. Kalaman data jima tana jira taji daga bakin Sabah yana furta mata amma gashi yau’ wani ne daban yake furta mata. Shiru tayi tana sauraronsa tana zubda hawaye, Shi kuwa ya cigaba da bata baki yana kokarin kwantar mata da hankali.

Bangaren su Samha kuwa, kurawa Sabah ido tayi ta cigaba da kallonsa daga bisani ta mike daga inda take zaune ta soma takowa inda yake tsaye, ta juyo tana fuskantarshi sa’anan ta bude baki tace “Sabah, kai kam kanada farin jini kaga kowa yana sonka”.

Sabah ya juyo yana dubanta sa’anan yace “Me kika ce?”

“Bance komai ba” ta fada tana kokarin juyawa ta bar wurin.

Sabah yasa hanun ya janyota yana fadin “Dawo nan ina zaki? Ai Najiki sarai abunda kika fadi. Kince kowa na sona, su waye kowan?” Ya karasa maganar yana matsota kusa dashi.

Mutsu mutsu ta farayi tana kokarin kwatar kanta. Sabah yace “karki ma fara, don sai kin gaya mun su waye kowan da suke sona tukuna”.Samha murmushin yake ta sake, ganin da gaske yake bazai kyaleta ba yasa ta soma lissafo mishi sunayen mutane “kaga akwai Zack, ga kuma Aliyah” sai kuma tayi shiru tana dubansa.

Sabah ya girgiza mata kansa sa’anan yace “mutane biyu ne kacal kowa?

“Eh toh kaga ga shinoh, Abba, da kuma Abbanka” samha ta karasa maganr tana masa kirge da hanunta.

“Saura mutum daya” ya fada yana kafeta da kyawawan idanunsa.

Samha ta bishi da kallo kirjinta ne ya fara bugu. Lalausar murmushi ya sakar mata wanda yasa dimple dinsa suka lotsa ya sake bayanar da ainin baiwar kyau da Allah yayi masa.

“Kin gama kirgen da hanun damanki, amma har yanzu banji kin lissafo suna guda daya ba, sai ki cigaba dana hagun, ina so naji waenada suke sona a nan”

Samha shiru tayi tana kallonsa da dara daran idanunta cike da karfin hali yaga ta daga hanun nata sama ta soma fadin ” Harda ni ma, Samha itama tana son Sabah!” ta karasa maganar tana runtse idanunta gam

Sabah baki ya sake yana kallonta cike da mamakin kalamanta don bai taba zaton zata bude baki ta fada mishi haka ba, bai san sanda dariya ta kubuce masa yanda yaga taci serious da idanunta a rufe.

Jin dariyan daya soma yi ne yasa Samha ta bude idanunta taga sai faman dariya yake mata “wallahi kin ban dariya, ban taba ganin mutum ya daga hannu don ya fadi haka ba” ya karasa maganar yana rike cikinsa yana dariya.

Samha tayi kicin kicin da fuska ta soma turo masa dan karamin bakinta tana fadin “Shine zaka dinga mun dariya, dana sani ma da ban fada ba” ta karasa maganar tana watsa mishi harara ta soma kokarin sauke hanunta kasa.

Sabah yana ganin zata ajiye hanunta, yayi sauri yasa hanunsa ya cafke, a hankali ya soma gangaro da yatsun sa har yazo ya hade da tafin hanunta ya rike gam, yana kallon cikin kwayar idanunta.

Samha wani irin yarr taji a jikinta ta dago tana duban hanunsu daya hade wuri daya sa’anan ta dawo da dubanta gareshi, kallonta yakeyi kyawawan idanunsa na fito da wani irin sirri na daban cike da tarrin sonta, ya lumshe su a hankali ya sake budesu ya zube cikin nata. Wani irin murmushi Samha ta sakar masa, tana kallon handsome face dinsa mai mugun tafiy da imaninta a duk sanda ta kalleshi, zuciyarta fal da farin ciki ta cigaba da kallonsa tana murmushi, Sabah shima murmushin ya sakar mata ya sake matso ta kusa dashi ta fada bisa fafadar kirjinsa, yana shakkar daddar kamshin jiknta sa’anan ya rada mata cikin kunne a hankali “kanwata, naji dadin wanan kalaman naki, don sun sani farin ciki. Your like makes me the happiest”. Ya karasa maganar cike da farin ciki, Samha murmushin jin dadi ta sake tana ajiyar zuciya.

Washe garin ranar ta kasance weekend basuda lectures, Samha tana zaune a dakinta tare dasu Khady da Amina waenda suka kawo mata ziyara don tunda ta kirasu a waya ta soma zayane musu yanda abubuwa suka kaya tsakaninta da Sabah suka ce sai sun zo har gida zasu ji labarin da kyau, don wanan ba labarin waya bane.

Samha zaune take a bakin gado tayi zurfi cikin tunani, babu abunda take tunani in banda Sabah da kuma kalamansa na jiya, wani irin feelings ne taji yana kara taso mata game dashi, nan take kuma taji tana missing dinshi.

Khady dake zaune kan carpet ta jingina da jikin gadon tana faman latsa wayarta ta dago ta dubi Samha wace gabadaya hankalinta baya tare dasu,  ta dawo da dubanta ga Amina suka hada ido sa’anan suka girgiza kansu a tare suna kallon Samha. Khady ta mike tazo ta zauna kusa da Samha a gado tana fadin “Kawata wanan murmushin da kike ta faman yi ke kadai fa?”

“Wai duk tunanin Sabah dine ko me?” Amina itama ta jefo mata nata tambayar tana kashe mata ido daya.

Samha gabadaya ji tayi kunya ya rufeta ta kasa cewa komai sai faman mutsu mustu takeyi kamar wace batada gaskiya.

Khady “tace Samha ya haka, mun kwaso jiki munzo dan mu sha labari kuma sai ki fara haka. Haba karki mana haka mana.”

Haka Amina da khady suka sa’ta a gaba sai data zaiyane musu komai tass suka zaro idanu suna kallonta cike da tuhuma.

“Samha anya kuwa?” Amina ta jefo mata tambayar. Samha tasa hanu ta rufe fuskarta dashi tana fadin

“Wlh ban san meyasa ba, a duk sanda nake tare da Sabah bana iya controlling feelings dina akanshi. Ni dai in har zai amshi soyayyata a gareshi toh banida sauran wata damuwa”

Khady da Amina suka tabe baki suna sauraronta. Nan kuma Samha ta tuno da Aliyah da kuma irin tarrin son da takewa Sabah, jikinta ne yayi sanyi ta cigaba da fadin ” wasu zasu bada zuciyarsu ga wanda suke kauna amma son nasu zai zamto koshin wahala don wanan da suke mikawa zuciyar nasu, bai ma damu da sunayi ba” Samha ta karasa maganar tana sunkuyar da kanta kasa.

Khady ce tazo ta dafe kafadarta tana fadin ” toh ai Samha, ba kowa bane yake samun yanda yakeso a rayuwa ba, so karki damu da wanan, kibi zuciyarki da abunda takeso kinji kawata”.

“Haka ne Samha ki kwantar da hankalinki kibi abunda zuciyarki takeso. Karki kawo batun wasu a ranki.” Amina ta fada tana sakar mata murmushi.

Shiru sukayi daga bisani Khady ta bude baki ta soma fadin “yauwa kunsan me zamuyi yanzu? Ku matso kuji”.

Haka suka matso kusa da khady ta rada musu a kunne. Cike da murna da zumudi suka fito daga dakin suka sauka kasa zuwa kitchen. Daman Anty fanneh bata nan sun fita tare da lami tunda safe, ta rakata zuwa kasuwar Balogun. Nan suka fada kitchen Samha ta soma fito musu da abubuwan hade haden cake din da zasuyi, bayan ta gama fito dasu tare suka hada kai suka soma kwaba cake din, Samha wace tayi tankaden flawa din duk tabi ta bata fuskarta da jikinta da garin flower, suna gama kwabawa suka raba gida uku suka juye a cikin pans daban daban sa’anan suka saka a cikin oven sukayi setting din timer.

Nan suka koma wurin dining suka fara zaman jiran cake din ta nuna, sun shafi kusan minti arba’in suna jiran timer din ya buga don Samha har ta soma gyangyadi kamar wace batayi bacci daren jiya ba, karan timer dinne ya farkar da ita, su khady suka shiga kitchen din da sauri suka bude oven din suna duba cake dinsu, sai da suka tabbatar da ta nuna tukuna suka fito da cake din suka jera kan dining table. Amina ta kurawa cakes din ido sa’anan tace “yanzu in banda Samha bamuda masoyin da zamu bawa cake dinan”

Khady ce ta bude baki ta bata ansa da ” ni inada”.

Amina da Samha suka juyo suna dubanta sa’anan suka fada a tare “kinada? Toh waye saurayin naki da bamu sani ba”.

Khady tadan susa kai sa’anan tace ” eh toh masoyi ai ba sai lallai saurayi ba, ai zai iya kasancewa aboki shima”.

“Amina tace hakane”. Haka suka tattara, Samha ta kai nata cake din cikin fridge ta ajiye da niyan tafiya dashi school ranar monday tabawa Sabah. Haka suka koma daki suka cigaba da hiransu ba’a jima ba su khadie sukace zasu wuce gida. Haka sukayi sallama suka tafi.

Ranar litinin da Safe bayan an gama lectures, Samha ta ciro cake din datayi packaging dinsa zata bawa Sabah daga cikin jakarta ta kama hanya zuwa department dinsu Sabah cike da dokin ganinsa.

Tana isa restroom din ta tadda shi zaune shi kadai, gani tayi ya saka face mask ya rufe fuskanshi.

Hankalinta a tashe ta karaso inda yake ta soma fadin “Sabah, mura kakeyi ne?”

Sabah ya dago yana dubanta sa’nan ya bata ansa da “eh ai duk ke kika jawo”.

Samha shiru tayi tana dubansa sa’anan tace ” amma ya kake ji yanzu? Da sauki muran?”

Sabah bai ce mata komai ba ya dago yatsan sa daya yana mata alamun data matso taji. Samha ta ajiye cake din data ruko a gefe sa’anan ta matso ta sunkuyo dab dashi, Sabah yana ganin ta matso nan dan nan ya cire Mask din daya rufe fuskarsa dashi ya kamo wuyanta ya soma mata tarrin karya a fuska. Samha ihu tasa ta soma kokarin kwatar kanta.

Sabah ya dakatar da tarrin yana fadin “Ance wai idan ka yadda mura, kafi saurin warkewa don haka bari na baki, tunda duk kece kika jawo na samu muran”.

Samha ta bige hanunsa daga rikon daya mata tana watsa masa harara ta soma fadin “wlh ka cika mugunta, shine zaka kama mun tarri a fuska?”

“Toh meya kawo ki nan?” Ya jeho mata tambayar.

Samha ta dauko cake din ta soma fadin “Daman munyi cake ne a gida kuma ya rage shine nace bari na kawo maka.”

“Au toh yanzu cake dinma ragowa za’a kawo mun?”

“A’a ba haka nake nufi ba, ka…….”

Sabah bai bari ta karasa maganar nata ba ya katseta da ” yanzu ina fama da wanan muran shine zaki kawo mun cake? taya kikeso na hadiya abu mai zaki da wanan muran? Ah lallai kam kanwata, kin iya kula da mara lafiya”. Ya karasa maganar yana jefo mata hararar wasa.

Samha jikinta ne ya soma yin sanyi da kalamansa bata ankara ba taji an fuzge cake din daga hanunta, juyawa tayi taga shinoh rike da cake din yana fadin “wow, amma Samha Allah ya miki albarka don na jima ina kwadayin cin cake.”

Abba ne shima ya bulo from nowhere ya fuzge cake din daga hanun shinoh yana fadin ” Dallah mallam kawo cake dinan, daman yunwa nakeji, lemu mai sanyi kawai zan nema na hada dashi.

Abbah ma bai ankara ba yaji Sabah ya fuzge cake din daga hanunsa yana fadin “ku bani cake dinan, za’a samu wanda zai ci” yana gama fadin haka ya mike ya soma tafiya zai bar musu restroom din.

Abba da shinoh ne suka bi bayanshi suna fadin ” Haba SB, yanzu sai kasa cake dinan a gaba ka cinye kai kadai, bazaka dan tsam mana ba?”

Sabah yayi banza dasu ya cigaba da tafiya su shinoh suka cigaba da binshi suna mishi magiya daya tsam musu cake din.

Samha cike da takaici ta bisu da kallo har suka bace mata daga gani. Tayi kicin kicin ta bata fuska itama ta fita ta bar cikin restroom din, tafiya takeyi tana kunkuni akan halayen Sabah, wato yanzu an sake dawowa gidan jiya kenan, duk karfin halin data tattara ta fada mishi cewa tana sonshi ranar ya watsar, ya dawo kamar yanda yake a da, saima abun daya karu yanzu. Cike da takaicin halayensa ta koma department dinsu.

Bangaren su Amjad kuwa, zaune yake cikin gym yayi zurfi cikin tunani sai ga Khadija nan ta shigo ta karaso inda yake zaune tayi mishi sallama hannunta rike da dan karamin kwalin cake. Amjad ya ansa sallamar ya dago yana dubanta.

Khadija tadan sakar masa murmushi sa’anan tace “Daman ni dasu Samha ne mukayi cake, shine na maka guda daya nace bari na kawo maka”. Ta karasa maganar tana mika masa kwalin cake din.

Amjad ya kalli kwallin sa’anan yace “ai yau ba birthday dina bane”.

Khady ta bata fuska sa’anan tace “Sai lallai ranar birthday tukuna ake cin cake?”

Amjad yayi ajiyar zuciya sa’anan yace “A’a ba haka nake nufi ba, kawai dai ban damu da kayan zaki bane”.

Ganin ta sake bata fuska ne yasa ya gyara kalamansa yana fadin “a’a ina nufin… nasan wanan zaiyi dadi.”

Harara ta dinga watsa mishi tana turo baki. Babu shiri ya karba cake din daga hanunta yana mata godiya bata ce mishi kala ba a kule ta juya ta tafi ta barshi a wurin yana tsaye rike da cake din a hanunsa.

Wuri ya nema ya zauna ya kurawa cake din ido, yana zaune a haka yayi zurfi cikin tunani yana kallon cake din kamar daga sama yaji muryan Samha tana fadin “wanan cake din….”

Amjad yana ganinta cikin sauri ya soma kokarin boye cake din yana fadin “babu komai”.

Samha wace ta rigada ta ganshi ta karaso tana tambayarsa “khady ce ta baka wanan cake din?”

I’ina da kame kame ya soma yi yana kokarin yi mata bayani. Samha dariya tayi sa’anan tace ” wai daman kai da Khady kuna? Akwai wani abu tsakanin ku ne?”

Amjad yayi saurin katseta da “a’a ba haka bane, it’s not what you think”.

“Toh menene? Gaya mun”. Samha ta karasa maganar tana masa dariya cike da zolaya.

“Tukuna”. Amjad ya fada mata ya kasa hada ido da ita.

“Ka fada mun mana Amjad, meye tukuna?”

“Eh toh har yanzu we’ve not figured it out, kuma ina son wanan maganar ya zamana tsakanina dake ne Samha. Karki bari taji”.

Samha tayi shiru tana dubansa, Amjad ya cigaba da fadin “Abunda kikaga yasa nace hake, nida ita har yanzu bamu tabbatar da abunda muke ji game sa junan mu bane shiyasa”.

Shiru sukayi kowa da nasa tunanin, kamar daga sama sukaji an jefo kwallo, kwallon bata tsaya ko ina ba sai cikin cake din da Amjad yake rike dashi. Tare suka dago shida Samha, nan suka hango Oga Sabah tsaye a gefe ya kafesu da ido yana kallonsu.Cikin zafin nama Amjad ya mike daga inda yake zaune don yasan da gangan Sabah ya jefo musu ball din.

Sabah yana ganin ya mike ya kawar da kansa gefe yana fadin “mayar da wukar, mura nakeyi kuma hanuna ne ya kubuce na wurga ya zo nan”.

Amjad cike da masifa ya soma fadin ” Bakada lafiya meye na buga kwallo, bazaka je ka zauna kaga yanda ake bugawa ba, sai lallai ka buga?!”

Sabah bai bashi ansa ba, idanunsa ne suka sauka kan cake din daya gama rugujewa a hanun Amjad sa’anan ya dawo da dubansa ga Samha, wani irin kishi ne ya rufeshi bai san sanda ya soma fadin ” Toh sai meye don a ruguza maka cake din, nima ai tayi mun nawa cake din. Zan iya baka wanan”. Ya karasa maganar yana watsa mishi harara.

Samha tana jin abunda ya fada nan da nan ta cafke tace ” toh ai bani na bashi cake din ba, khady ce ta bashi”.

Nan da nan Sabah ya zaro ido don a tunaninsa shima Amjad din tayi masa cake din ne ta kawo masa.

Cike da mamaki Amjad ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” kinyi wa Sabah cake?”

Samha zaro idanu tayi tana kallonsa. Shima Sabah kawar da kansa gefe yayi ya kasa hada ido da Amjad.

Amjad ya matso dab dashi yana kai mishi dukan wasa ” wai tsaya tukuna, ba dai kishi nake gani cikin kwayar idanunka ba, kishi kakeyi don kana tunanin Samha ta bani cake?” Amjad ya karasa maganar yana masa dariya.

“Haba Sabah, ban sanka da haka ba”. Ya fada yana cigaba da masa dariya.

Sabah kunya ne ya lulubeshi, dayaga dariyar da Amjad yake masa yaki tsayawa yasa ya cire mask din dake fuskarsa ya fara mishi tari a fuska shima.

Amjad nan da nan ya kauce ya bata fuska yana fadin ” Meye haka?”

“Oho ba’a sani ba” yana gama fadin haka yaja tsaki ya tafi ya barsu a wajen. Samha da Amjad suka bi bayanshi da kallo.

Samha girgiza kai kawai tayi don inda sabo yanzu ta rigada ta Saba da halin Sabah.

Misalin karfe hudu Samha ta fito daga last lectures dinta kenan, sai ga Aliyah nan tazo, idanunta duk sun shiga ciki har wata yar’ rama tayi, fuskan nata a yau babu make up, sai ta zama kamar wata mara lafiya. Aliyah ta tsaya tana kallon Samha da shanyanyun idanunta daga bisani ta bude baki tace “Samha ina so na danyi magana dake idan bazaki damu muje cafeteria”.

Samha bata ce mata komai ba haka tabi bayanta suka je cafeteria suka nemi wuri suka zauna. Bayan sun zauna shiru ne ya dan ziyarce su daga bisani Aliyah ta dago tana duban Samha wace ta kura mata ido tayi shiru tana kallonta, Aliyah ta soma fadin ” Samha ba komai bane yasa na nema ganinki illa dana baki hakuri akan abunda Zack ya miki, nasan abunda ya aikata yanada muni, bai cancanciyafiya daga gareki ba, amma dukda haka Samha karki tsaneshi, ni yakamata ki tsana ba shi ba don nasan ni kaina nayi miki laifufuka da dama a baya amma yanzu cike nake da nadmar aikata su. Kiyi hakuri”. Aliyah ta fada tana sunkuyar da kanta kasa.

Samha cike da mamaki take binta da kallo don bata taba tunanin Aliyah zata kawo kanta tana bata hakuri haka ba, nan kuma tausayin Aliyan ya rufeta, Samha ta bude baki ta soma fadin ” karki damu Aliyah babu komai, komai ya wuce insha Allah. Kuma I understand how you feel da shi zack dinma har kanshi, kawai hanya daya bi don ya samo miki farin cikinki ne bai kamata ba, amma banga laifinsa ba, don so babu abunda baya sa mutum yayi”.

Aliyah tayi shiru tana dubanta sa’anan ta cigaba da fadin ” Shekara bakwai, samha tsawan shekara bakwai kenan na taso ina dawainiya da son Sabah, inason Sabah tamkar raina, kuma har yanzu banjin akwai abunda zai sa naji na daina sonsa, zan cigaba don son Sabah har sai ran dana  ji na daina numfashi a doron kasan nan” Aliyah ta karasa maganar tana rushewa da wani irin kuka.

Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Samha, itama kwalla ne suka cika mata idanu. Cikin sauri ta bude jakarta ta ciro yar’ karamar hanki ta matso kusa da Aliyah ta mika mata, Aliyah ta karba ta soma goge hawayenta, daga bisani ta dawo da dubanta ga Samha taga itama hawayen takeyi. Harara ta dan watsa wa Samha sa’anan tace “kukan me kuma kikeyi?”+

Samha ta dan saki murmushi bata ce mata komai ba tana kallonta.

Aliyah cigaba tayi da kuka nata tana share hawaye da hanki. samha cike da tausayi ta sake matsowa kusa da ita ta soma rarashinta.

Bangaren su sabah kuwa, zack ne ya shigo cikin department dinsu rataye da jaka a bayansa, yana isa dab da ajinsu inda sukeyin lectures yaja ya tsaya, don tun faruwar abun yake shakkan zuwa inda su Sabah suke don bai san da wani ido zai kalle Sabah ba.

Tsayawa yayi shiru yayi zurfi cikin tunani yanda zai shiga cikin ajin. Kamar daga sama yaji muryan Sabah yana fadin ” ka shiga ciki mana, kaja ka tsaya a waje”.

Cikin sauri ya waiga yaga Sabah tsaye a bayanshi yana kallonsa, kyawawan idanunsa kadai zaka iya hangowa farare tass dasu, don ya rufe sauran fuskarsa da mask.

Zack ya soma susa kansa, gabadaya sai ya dinga jin wani iri ya kasa hada ido da Sabah.

Sabah ya kalleshi yace ” au tsanar ya kai ga haka kenan, ko kallo na ma bazaka iyayi ba, kwana biyu kenan kanata gudun mu”.

Zack yayi shiru bai ce komai ba sai waware ido yaketa faman yi. Sabah ya tako ya matso har inda zack yake tsaye yasa hannu ya dafe kafardarsa ya cigaba da fadin ” tunda ni Sabah ban san yanda ake son muntum ba , ban kuma san menene so ba, ai…..”

Zack yayi saurin katseshi da “Ya kake magana haka SB, kaima kasan bazan taba tsanar ka ba”.

Sabah ya sa hannu ya zagaye wuyan Zack yana rugume dashi ya cigba da fadin “Hmm zack kenan, mutum mai irin halina sai ku shekara dashi baka san meke tafe dashi ba, zai iya saka tunanin cewa bai damu ba, don irin mu bamu nuna damuwar a filli”.

Sabah yana gama fadin haka, ya yanke jiki ya fadi.

Cike da tashin hankali Zack ya ruko shi yana “SB! Sabah!…. dan Allah ka tashi”. Amma ina Sabah an riga da an tafi.

Hankalin Zack a tashe yasoma ihu da azo a taimaka mishi, nan students sukayi ca akansu, aka rufu akan Sabah. Nan da nan Zack ya ciro waya ya soma kiran gidansu Sabah, hankalin Alhaji muazzam a tashe ya soma tambayar zack abunda ya sameshi, zack yace Zazzabi ne ya rufeshi don jikinshi yayi zafi sosai. Alhaji muazzam yace toh yanzu zai sa a turo da mota a daukeshi, gashi baya garin yayi tafiya zuwa abuja nan da nan Ya kira dr fahad family doctor dinsu, yace mishi yaje gida yanzu yanzu nan danshi babu lafiya yaje ya dubashi. Babu shiri Dr fahad ya bar abunda yakeyi ya soma shirin zuwa gidansu Sabah. Alhaji muazzam hankalinsa kasa kwanciya yayi, nan ya bar abunda yakeyi, yasa aka mishi booking flight na zuwa lagos.

Zack yana tsaye hankalinshi a tashe motan gidansu Sabah ya iso akayi parking, driver din ya fito da sauri aka saka Sabah cikin mota, driver din yaja ya tafi dashi.

Amjad yazo wucewa yaga an saka Sabah cikin mota, nan ya hango Zack ya karaso yana tambayarsa ” Zack, meya faru? Meya same Sabah?”

Zack hankali a tashe ya soma fadin ” zazzabi ne na mura, ina jin ya zama mishi high fever ne zafin jikinshi kuma ya hau ya sumar dashi. Na kira gidan nasu shine aka zo aka daukeshi”.

Nan da nan amjad ya ciro waya yana fadin ” bari na kira Samha na fada mata don nasan bata sani ba”.

Cikin hanzari Zack ya dakatar dashi yana fadin “a’a karka ma soma, don Sabah ba zai so hakan ba”.

Amjad ya dubeshi sa’anan yace “Duk da bashi da lafiyan ma sai ya nuna karfin hali?”.

Zack yace “eh toh kasan halin Sabah din sarai, baya son mutane suga weakness dinsa”.

“Harda waenda yakeso? Sai ya boye musu?” Amjad ya jefo mishi tambayar.

Zack yayi shiru ya kasa bashi ansa. Amjad ya girgiza masa kansa sa’anan yace “Ai ba haka Zack, kowa yana bukatan wanda yakeso a kusa dashi a duk sanda ya shiga cikin wani hali”. Yana gama fadin haka ya bude wayansa ya soma neman Samha a layinta.

Bangaren gidansu Sabah kuwa, har ya farfado dr fahad yazo ya dubashi ya bashi alura da magunguna yace, fever ne kawai ke damunsa, ya samu ya danyi bacci ya huta, zai lafa. Ya sake mishi alura wanda zai sakashi bacci sa’anan yace zai tafi zuwa anjima zai sake zuwa ya dubashi. Ya mishi sallama ya tafi.

Sabah har yayi nisa da baccin sa, kamar a mafarki ya soma ji ana buga kararawar shigowa parlourn babu gagautawa. Daga bisani aka koma bubuga kofar da karfi, Sabah wani irin tsaki yaja ya bude idanunsa, don wani irin sara yaji kansa ya soma masa.  Dayaga bubugwan bana lafiya bane kuma baza daina ba yasa ya yaye bargon daya luluba dashi ya sauki daga kan gadon, yayi hanyar kofa ya bude ya sauka kasa zuwa parlourn

“Wai dallah waye ne haka, ina zuwa mana”. Ya fada yana kokarin bude kofar, yana budewa Samha ta shigo ciki a rikice, fuskarta babu walwala ta tsaya tana dubansa.

Sabah yana ganinta ya dafe kai yana fadin “Amma zack Allah ya mishi katon baki na surutu, wato sai daya fada miki kenan”. Ya fada yana kawar da kansa gefe.

Samha harara ta watsa mishi ta soma tambayarsa ” ya zafin jikin naka yanzu? Kasha magani kuwa?”

Sabah yace “oh Allah”

“Kasha maganin?!” Samha ta sake tambayeshi a dan tsawace don tasan shi sarai da karfin hali sai yaki shan magani.

“Ban sha ba”. Ya fada cike da rashin damuwa.

Samha tace “Ban san meye matsalarka ba Sabah, shekaranka nawa yanzu, har yanzu baka iya kula da kanka, taho muje kasha maganin”. Ta fada tana turashi kamar wani karamin yaro, kai kace uwa da danta ne, haka suka soma haurawa matakala zuwa dakinsa.

Suna shiga ya hau kan gado ya kwanta, Samha ta taba jikinshi daji still da zafi. Mikewa tayi ta shiga bayi ta debo ruwa ta tsoma yar’ karamim towel a ciki ta sake dawowa cikin dakin da zaune a gefen gadon.

“Cire riganka” ta fada mishi kai tsaye.

Sabah ya dago yana dubanta sa’anan yace ” Meye haka? Likita fa yazo ya dubani”.

“Eh na sani amma har yanzu jikin naka akwai zafi, idan na goge maka da wanan ruwan, zai lafa”.

“Karki wani wahalar da kanki, zafin ya soma sauka”. Ya fada mata yana kawar da kansa gefe.

Samha bata saurareshi ba, ta ciro towel din daga cikin ruwa ta matse ta soma goge  masa fuska dashi, shiru yayi yana kallonta.

Samha ta zabga mishi harara sa’anan tace “meyasa baka fada cewa bakada lafiya ba, har sai daka bari ciwon ya kai ka kasa? Kasan yanda hankalina ya tashi kuwa, gabadaya duk na bi na rude, a guje na bar school saura kadan ma mota ta bigeni duk saboda na shiga damuwa akanka!”

“Okay, okay, naji calm down, ki rage murya mana karki kara mun ciwon kai”.

Samha tayi shiru tana dubansa, kwalla ne suka soma ciko mata idanu tana kokarin matse su ta cigaba da fadin “wani sa’in sai in dinga ji kamar banida wata amfani a wajenka, ace bakada lafiya amma bazaka iya bude baki ka fada mun ba, ko babu komai tsakanina da kai, ai ni kanwarka ce”.

Sabah juyowa yayi yana dubanta sa’anan ya mike ya kamo hanunta da take faman goge masa fuska dashi ya matso da fuskarsa dab da nata ya soma magana a hankali muryarsa can kasa kasa  “kinada amfani mana kanwata, kuma ina bukatan naga kina murmushin akoda yaushe” ya karasa maganar yana shafo gefen fuskarta.

Samha shiru tayi tana dubansa ” kiyi mun dariya nagani”. Ya fada mata.

Samha ta bata fuska sa’anan tace “ai ba zan iya dariya ba hakan nan”. Ta karasa maganar tana turo masa dan karamin bakinta.

“Amma kin iya yi wa Amjad dariya. Ni din ne bazaki mun ba”.

Samha ta zaro ido tana fadin “yaushe? kuma a ina kaga nakewa Amjad dariya?”.

“Yau dinan mana, danaga kinata faman masa dariya sai da jinina ya haura”.

Samha ta sukyar da kanta tana murmushi. “Au Wato kina nufin ni bazan iya saka ki dariya ba kenan? Shikenan.” Ya fada ya koma ya kwanta yana turo karamin pink lips dinsa.

“A’a fah, ba haka bane”. Ta soma kokarin masa bayani, ya katseta ya dago yana fadin ” wayo Allah kaina, ko fever nan zai sake dawowa ne?” Ya karasa maganar yana dafe gefen kansa.

Samha kirkiro dariya tayi ta soma yi. Sabah ya sake rikon dayayi wa kansa ya juyo yana dubanta sa’anan yace “oya kiyi dariya inji”.

“Yanzu fa na gama yi”. Ta fada tana dubansa.

“Wanan ai ba dariya bace, bakiyi sa kamar  yanda naji kinayi wa Amjad ba”.

Yana gama fadin haka, idanunsa ne suka sauka kan karamin bakinta, ya kurawa soft lips dinta ido, gani tayi yasa duka hanunsa biyu ya tallafo fuskarta, ya soma matsowa dab da ita ya manna lips dinsa akan nata yana mata soft kiss a baki.

Samha lumshe idanunta tayi, wani irin feelings ne taji yana taso mata daya hada bakinsu wuri daya.

Sai daya mata kiss na kusan minti biyu sa’anan ya dago yana dubanta, ta bude idanunta a hankali ta zubesu su cikin nashi. Murmushi kawai ya sakar mata yana kallonta.

Nan da nan kuma yaga ta bata fuska ta zaro idanunta tana fadin ” na shiga uku, sabah meye haka? Kissing dina fa Kayi”.

Sabah ya daga mata gira daya bai ce komai ba ya cigaba da kallonta.

“Ko na kara ne?” Taji ya jefo mata tambayarSamha bata bashi ansa ba, ta zira harshenta ta dan laso lips dinta na kasa, sai taji zaki kamar na cake.

Ta juyo tana dubansa sa’anan tace ” ya naji kana tasting kamar cake?”

Bai bata ansar tambayarta ba yace “ki jira next stage din, sai na samu lafiya tukuna” Sabah ya fada yana kashe mata ido daya.

Data gano inda zancen nasa ya dosa, bata san sanda tasa ihu ba tana rufe kunnenta ba, ta fita ta bar masa dakin. Shikam Sabah, dariya ya bita dashi, yana girgiza kansa.

Samha sai faman kunkuni takeyi tana magana can kasan ranta, ” rana daya bazai wuce ba da bai sakani jin haushi, ko takaici ko kuka ba”. Ta karasa maganar tana jan tsaki.

Tana isa dab da dining ta hango ragowar cake din data bashi cikin plate alamun yaci ya rage. Ranta ne taji ya danyi mata sanyi ta karaso ta dauki daya daga cikin fruits din dake saman cake din tasa a baki ta soma ci. Tana gamawa ta haura sama zuwa dakin da Alhaji muazzam ya bata yace nata ne, tana shiga ciki wani irin nauyi taji jikinta na mata, nan da nan ta fada kan gado ta soma bacci.

Sai zuwa yama missalin karfe biyar ta farka, ta fada bayi ta wanke fuskarta sa’ana ta fito daga dakin ta soma saukowa kasa zuwa parlour, abunda ta hango ne yasa ta dakata ta tsaya tana kallonsu.

Sabah ta gani sanye cikin kayan sanyi, blue sweater, da kuma bargo ya lulube kasan jikinsa dashi, yayi kicin kicin da fuska ya bata rai, ga Alhaji muazzam a gabansa rike da kwanu daya dama masa quacker oat a ciki sai fama yake dashi daya bude baki ya karba kamar wani karamin yaro. Sabah sai faman kakaucewa yakeyi yaqi karba.

Alhaji muazzam ya sake debo oat din ya kawo cokalin daidai bakin Sabah yana fadin “Haba baby boy, bude baki mana kasha ko da kadan ne, kaji please. Ban sanka da kunya haka ba fa”.

Sabah ji yayi kamar ya kwala ihu don takaici, Samha ta dan labe a bayan step tana kallonsu, tana kokarin rike dariyan da yake neman kubuce mata.

Ganin Sabah yaki tanka masa yasa ya ajiye cokalin yana fadin ” menene kuma baby boy? Ina jin bakada lafiya fa na yanke na bar duk abunda nakeyi na dawo. Kayi hakuri nima ba’ason raina bane nake tafiya ina barinka kai kadai ba, don haka yanzu gani na dawo gida, karka ji komai. Oya ahh, bude baki ka karba”. Ya fada yana kokarin kara tura masa cokalin oat din a baki.

Sabah ya sake bata rai kamar hadari ya taso ya soma fadin ” Abbah wai dan Allah meye haka, ni ka kyaleni, ciwo na zai karu” ya fada yana kawar da kansa gefe.

“Haba Sabah, please open up”. Alhaji muazzam ya cigaba da masa magiya.

“Wayyo Allah! Abbah dan Allah mana, nace bazan sha ba”.

“Please Sabah…”

Samha dataga abun nasu bana karewa bane yasa ta karaso inda suke tazo suka gaisa da Alhaji muazzam, daga bisani ta fada mishi zata wuce gida tunda jikin Sabah ya danyi sauki.

Alhaji muazzam ya juyo ya soma bata hakuri yana fadin ” kiyi hakuri Samha, na barki da jinyan Sabah. Bansan taya zan fara miki godiya ba.”

Samha murmushi kawai ta sake tana fadin ” Babu komai Abbah”

Wani irin kallo Sabah yake binsu dashi bai ce komai ba. Alhaji muazzam ya ajiye kwanun oat din ya juyo yana fuskantar Samha sa’anan yace ” Samha nagode sosai, kuma ina farin ciki da Sabah ya sameki a matsayin kanwarsa.”  Yana gama fadin haka, wayarsa ta soma ringing ya tashi ya bar musu wajen dan ya ansa kiran.

Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Samha dajin kalaman Alhaji muazzam tayi shiru tana tunani, ” kayi hakuri Abbah, ban jin zan iya zama irin wanan kanwar da kake hango wa Sabah”  ta fada can kasan ranta, tana tuno da abunda ya faru dazun a dakinsa. Kiss din dayayi mata ne ya soma mata yawo a ka, ta sunkuyar da kanta kasa.

From nowhere taji Sabah yasa hannu ya janyota ta fada bisa faffadan kirjinsa, fuskarsa ya matso dab da nata ya soma fadin ” tunanin me kikeyi? Ko kina tunanin yanda zakiyi improving kiss dinmu ne?” Ya tambayeta yana daga mata gira daya.

“Sake ni, waya fada maka abunda nake tunani kenan” ta fada tana watsa mishi harara.

Sabah shiru yayi yana kallonta, itama ta kura mishi ido tana kallon kyakyawar fuskarsa. Lalausar Murmushi ya sakar mata yana kara matso da fuskarshi dab da nata. Gabadaya scent din jikinsa mai dadin kamshi ya mamaye ta, Samha ta lumshe idanunta tana jiran taji saukan soft lips dinsa kan nata, har ya kai bakinsa dab da nata, wayarsa daya ajiye akan dining ta soma ringing ta katse su.

Samha ta bude idanunta ta zubesu cikin nashi tana kallonsa.

“Jeki daga”. Ya fada mata yana kallon cikin kwayar idanunta.

“Ni kuma? Wayarka ce fa.” Ta fada mishi

“Atoh ni kikeso na tashi naje na daga? Banida lafiya fa”.

Samha ta mike tana kunkuni ta karasa wajen dining din taje ta dauko wayar ta daga tana hello, shiru taji ba’ayi magana ba daga bisani aka kashe. Ta dago wayar daga kunnenta tana fadin “kodai wrong number ne?”

Haka ta dawo ta fada mishi, nan ma ta tarar da Alhaji muazzam ya gama wayarsa ya dawo parlour, ta fada mishi zata wuce gida, yace toh shikenan ta gaishe mishi da Amminta. Nan yasa daya daga cikin drivers dinsa da sukai ta gida.

Washe gari bayan lectures, Samha tana gym as usual tana faman aikinta na team manager. Tsugune take tana kwashe kwallon da aka gama buga ball dasu tana zuba su cikin basket.

Kamar daga sama taji muryan Aliyah na fadin “wai ke har yanzu bazaki daina wanan aikin na baiwa ba?”

Samha ta waigo cikin sauri tana dubanta.

“Menene kina mamakin ganina ne? Ko bai kamata na sake zuwa nan bane”. Ta jefo mata tambayar tana murmushi.

Samha ta sake baki tana kallonta sa’anan tace “a’a ba haka bane”

“Toh menene? naga kina mun wani irin kallo kamar kinada wani abu cikin zuciyanki. Kodai Sabah ya gaji dake ne ya kyale?”

“A’a muna nan tare har yanzu”.

“Oh haba? Ni kuma ina nan inata dokin wanan ranan tazo”.

“Samha ta murguda mata baki tana watsa mata harara ta juya ta cigaba da abunda takeyi.

Aliyah murmushi kawai tayi tace “Bari nazo na tayaki babbar yaya” haka ta karaso inda Samha take tsugune tasa hannu tana tayata kwasan ball din.

Sabah yazo wucewa kenan ya gansu tare, ya tsaya curuss yana kallonsu don abun yayi mugun bashi mamaki. “Yaushe kuka zama best friends?” Ya jefo musu tambayar yana karasowa inda suke.

Aliyah tana jin muryar Sabah wani irin faduwar gaba ne ya ziyarce zuciyarta amma tayi kokari ta dane ta kirkiro murmushi a fuskarta tana fadin ” ai yanzu Samha kawata ce sosai, ko ba haka ba babbar yaya?” Ta karasa maganar tana kallon Samha tana murmushi.

Samha murmushin yake ta kirkiro a fuskarta, amma can kasar ranta tana fadin “Anya kuwa?”

Suna cikin haka sai ga Zack nan ya shigo cikin sauri yazo ya tadda Sabah yana fadin

“SB, zo muyi practice. Na san ka samu karfin jiki yanzu”.

Aliyah najin haka ta mike tsaye cikin sauri ta soma yiwa Zack fada tana fadin ” wai kai Zack bazaka taba barin Sabah ya huta bane? Kai kenan kullum kana makale dashi, haba” ta fada tana watsa mishi harara cikin wasa.

Zack ya dubi Sabah yace ” SB, wai dan Allah da gaske na cika like maka?” Ya karasa maganar yana dafe kirji.

Sabah dariya kawai yayi bai ce komai ba, Aliyah ma dariya ta soma yi ta matso kusa da zack tana fadin ” ka tsaya na cire maka abu a kai” haka ta sa hanu ta cire mishi abunda ya fada cikin gashinsa. Nan suka cigaba da wasa da dariya tsakaninsu babu wata sauran fada.

Samha tana zaune can gefe tana kallonsu, can wayarta ta soma ringing ta ciro daga jakarta, khady ce ke kiranta, ta kara wayar a kunnanta. Khady ta soma tambayarta inda take tanason ta rakata kasuwa idan sun gama lectures na rana tana son ta danyi shopping. Samha tace mata toh shikenan.

Bayan sun gama lectures haka suka wuce kasuwa suka shiga wata boutique sai faman zagaye sukeyi a ciki don sun kusan hour daya da wani abu Khady ta kasa gama siyayya.

Samha ta dubeta a gajiye ta soma fadin ” wai dan Allah khady baki gama wanan siyayyen bane? Tun dazu fa muke ta abu daya?”

Khady ta dubeta ta soma fadin ” wai Samha fa takalmi nake nema da zaiyi matching da wanan kayan don gobe za’ayi ta takare, yaqi za’ayi wlh ko ni ko shi”.

“Ban gane ba, kedawa zakuyita ta kare?” Samha ta jefo mata tambayar.

“Amjad mana, wai har yau nidashi mun gagara fita, sai dai musa rana a daga. Na gaji gaskiya bazai yu’ ba, gobe za’ayita ta kare.” Ta karasa maganar tana murguda baki.

Samha ta dubeta tace “toh fa, lallai kam”.

“Eh mana shiyasa kikaga dole gobe nayi kwaliyata na kece raini, inaso nayi masa kyau sosai”.

Samha dariya ta soma yi tana fadin ” hakane kawata, gwanda kiyi kwaliyya ki fito sosai yanda idan ya kalle ki bazai yi marmarin ya sake kallon wata ba”.

Cike da murna suka tafa suka cigaba da dube dube ko khady zata samu takalmin dazaiyi matching da kayanta, can idanunta suka sauka kan wata hadadiyar high heels, cikin sauri khady ta karasa ta sunkuya ta dauko kafa daya tana duban takalmin.

“Samha, wlh sune, Allah ya nuna mun su, wanan takalmin dasu zanyi yaqin badal gobe”.

Samha ta kalli takalman taga sunyi tsini dayawa ta tabe baki. Khady bata damu ba ta nema wuri ta zauna ta cire takalmin dake kafanta ta soma kokarin gwada sababin. Haka tayi tayi, da kyar takalmin ya shiga kafarta.

Samha ta dube ta tace “khady wanan takalmin ba size dinki bane ba fa”.

Khady ta juyo tana duban mai shagon sa’anan ta soma tambayarta ko akwai baban size . Mai shagon ta soma bata hakuri tace wlh shikenan musu, babu wata babban size.

Khady bata daddara ba haka ta kwasa takalman ta biya kudi, ko cirewa bata yi a kafanta ba suka soma tafiya.

Samha ta dubeta tace “Wai khady takalman nan sun miki kadan mana, meyasa kika nace kika siya.”

Khady wace take tafiya da kyar tace “wlh Samha ina ganin takalman nan naji sun kwanta mun don jikina na bani cewa idanna sanya su, zan samu nasara a yakin da zanyi gobe. Shiyasa ma kikaga na sanya su tun yanzu don na samu su bude kafun zuwa gobe”

Samha shiru tayi tana tunanin dama ita da Sabah zasu samu su fita haka, data ji dadi. Tana cikin wanan tunanin khady ta taba ta tana fadi “Samha ba amminki bace nake ganina wancan shagon?”

Samha ta dago cikin sauri ta hango Anty fanneh cikin wani shago da ake siyar da wasu haddadun Abaya. Nan suka karasa suka je suka sameta a cikin shagon, Bayan sun gaisa khady tayi musu sallama ta tafi ta barsu. Samha ta nema wuri ta zauna cikin shagon don ta san siyayar ammin nata sai a hankali don tasha rakota kasuwa sai su jima tana zaban kaya. One by one Anty fanneh ta dinga ciro abaya kala kala tana gwadawa tana tambayar Samha ko sunyi kyau, don gobe sunada outing da zasuyi tare da Alhaji muazzam. Samha ta zabga uban tagumi tana kallon mahaifiyarta da take yin abu kamar wata yar’ budurwa data samu saurayi.

Samha ta girgiza kai cike da tausayin kanta don gashi har Ammi itama za’a fita da ita amma ita ko oho, Sabah bai ma san tana yi ba.

Anty fanneh data ga mind din Samha baya tare da ita yasa ma ta daina tambayarta ko kayan sunyi, ta tabe baki ta cigaba da zabon kayanta da kanta.Washe gari da safe Alhaji Muazzam ya sauko kasa ya tarar da Sabah zaune a parlour yana kishingide a kan kujera yana buga game a wayarsa, Alhaji muazzam ya dubeshi yace ” Baby boy, ka shirya yau zamu fita outing”.

Sabah shiru yayi kamar bai ji shi ba “Sabah ko baka ji abunda nace bane? Cewa nayi ka shirya yau zamu fita tare dasu Samha da Aminta”.

Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa’anan yace “Gaskiya Abbah nikam bazani ba, kuyi tafiyar ku kawai”.

“Haba baby boy, na yau kadai ne fa”.

“Wai Abbah idan zaku fita mun dinga binku kenan sai kace wasu yara kanana. Kai da ita ku fita mana abinku. Ai ba sai mun biku ba”. Ya fada yana cigaba da buga game dinsa a waya.

Alhaji muazzam ya sauke ajiyar zuciya ya zo ya zauna kusa dashi ya soma rarashi yana bashi baki har ya samu ya lalabashi ya amince amma yace daga yau bazai kara binsu ko ina ba. Alhaji muazzam ya amince yace babu matsala. Shi kanshi Sabah ya fada ne kawai amma can kasan zuciyarsa yasan saboda Samha zataje ne shiyasa ya sauko ya amince zai bisu ba wani abu ba.

Bangaren gidansu Samha itama Anty fanneh ta sa Samha a gaba tace sai lallai ta bisu fitan da zasuyi, tace tunda dan’ta Sabah ma zai bisu bataga abunda zai hana itama Samha fita dasu ba.

Ba’a jima ba suka gama shiri, Alhaji muazzam ya fito ga bodyguards dinshi na biye dashi, Sabah yana ganinsu yaki kememe yace indai dasu za’aje ya fasa tafiyan. Alhaji muazzam yace toh shikenan, ya dakatar dasu yace ba sai sun bisu ba, shi zaiyi tukin ma da kansa. Watar katuwar bakar SUV ce mai shegen tsada da kyau Alhaji muazzam yaja suka bar gidan. Ko dasuka isa gidansu Samha, Samha da Amminta ne suka fito suka tadda su, Kuma sunyi kyau sosai.

Sabah yana ganin Samha wani irin bugu yaji kirjinsa ya soma yi kamar ko da yaushe a duk sanda ya daura idanunsa a kanta, don tayi mishi kyau sosai, amma ya danne ya kau da kansa gefe yayi kamar bai ganta ba, Samha ta bude kofar seat din baya ta shiga ta zauna. Itama Anty fanneh ta shiga gidan gaba. Sabah ne ya gaisheta sama samah, ta juyo cike da farin ciki ta ansa gaisuwan nasa. Haka suka dau hanya tamkar family guda abun sha’awa suka soma tafiya. Familyn yan’ gayu kenan.

Suna cikin motan, Samha sai faman satan kallon Sabah takeyi da gefen idannunta, shi kam shiru yayi cikin zurfin tunani bazaka ma ce yana cikin motar ba.

Alhaji muazzam ya dubi Sabah daya hada fuska ta mudibin gaba ya soma fadin “yau wace rana zamu fita tare da Sabah. Sabah amusement park fa zamu, banga kana murna ba”.

Sabah shiru yayi ko tanka mishi baiyi ba, Anty fanneh dariya kawai tayi, Alhaji muazzam ya juyo yana duban Samha sa’anan yace “kefa Samha? Da fatan Ammi bata takura miki na fitowa yau ba?”.

Samha murmushin karfin hali kawai ta kirkiro don gabadaya a takure take a back seat dinan, ga Sabah daya mata banza tamkar wasu kurame haka suke zaune a bayan.

” Babu komai Abbah, ai nima na jima banje Amusement park ba. nasan it’ll be fun idan muka je”.

Alhaji muazzam yaji dadin abunda ta fadi yace ” toh ai shikenn, yayi kyau daman ina tunanin ko zaki fita da kawayenki ko wani abu tunda yau public holiday ne babu lectures.”

Anty fanneh ce tari saurin capkewa tana fadin ” Ai Samha bata fita ko ina, ita fa daga makaranta sai gida. Gata kuma da kokarin aiki don bakaga aikin data taya ni dashi a gida jiya ba. Ai ita kam bata damu da fita ba, shiyasa ma na matsa mata nace sai lallai ta biyo mu”.+

Sabah dariya ya soma yi a gefe yana fadin “Allah sarki wata dai tana fama da rayuwar kadaici”. Haka ya dinga waka yana mata dariya kasa kasa. Samha tayi kicin kicin da fuska tana turo baki.

A haka suka karasa randle avenue na cikin Apapa GRA suka shiga park din wanda yake dauke da dunbin jama’a kasancewar ranar public holiday kuma yawanci sun kawo yaransu da iyalensu don su shakata.

Anty Fanneh ta dubi wurin taga ya canza mata sosai don rabonta da park din tun Samha na karama suna kawota da ita da marigayi mai gidanta. Tare suka karasa cikin park din suka siya tickets na shiga. Suna shiga ciki nan Samha ta soma murna saboda wurin yayi sosai ga su roller coasters, horse ride, merry go round, pirate ship da sauransu, mutane sai faman hawa sukeyi wasu na dariya cike da nishadi wasu kuma suna ihu don tsoro.

Sabah ne ya dubi Samha yaga sai faman washe baki takeyi tana fadin cewa zata hau duka lilon dake wurin. Harara ya watsa mata yace ” Meye haka kinata wani kaudi sai kace wata yar karamar yarinya yar’ shekara bakwai. Baki taba hawa lilon park bane ko meye?”

Samha bata damu da maganganusa ba ta bashi ansa da ” lokacin ina karama, Abuiy yana yawan kawoni, kuma sai ya bari na da’ na ko wani lilo a nan tukuna zamu wuce gida”.

“Toh ai gaki gasu sai kije ki da’ana. Ni nayi nan, zanje na nema inda ake siyar da coffee nasha”. Yana gama fadin haka ya kara gaba ya tafi ya barta a wajen. Samha ta marairaice fuska tabi bayanshi da wani irin kallo kamar zatayi kuka.

“Sabah!” ta soma kwada mishi kira amma ko juyowa baiyi ba ya cigaba da tafiyarsa. Su Alhaji muazzam da Ammi ne suka juyo suka ganshi yana tafiya.

Alhaji muazzam yazo cikin sauri ya karaso inda Samha take tsaye, zai fara bata baki don ya kwantar mata da hankali kenan sai ga Anty fanneh ta karaso tana fadin “ku rabu dashi kawai, kasan yara musamman matashi saurayi kamar sa basu cika son zuwa irairen wuraren nan ba, kawai don babu yanda ya iya ne shiyasa ya biyo mu. Samha zo mu tafi kawai zai zo ya same mu daga baya”. Anty fanneh ta fada tana kokarin jan Samha su bar wajen, samha wace gabadaya hanlinta na kan Sabah daya tafi ya barsu ta juyo jiki a sanyaye ta soma binsu. Gaban wata katuwar roller coaster suka je suka tsaya. Anty fanneh tace shi zasu fara hawa, Alhaji Muazzam yace anya kuwa zata iya, ya tambayeta yana mata dariya.

Suna tsaye from nowhere wani yaro karami wanda bazai wuce shekara biyar ba yazo da gudu yana guje gujensa, bai hankara ba yazo ya buge Anty fanneh. Cikin sauri mahaifiyar yaron tazo ta dauke shi tana basu hakuri, Anty fanneh tace ai babu komai da’ na kowa ne. Matar ta kara basu hakuri ta dauki danta tayi gaba. Alhaji muazzam shiru yayi yana kallonsu har yaron da mahaifiyarsa suka bace musu daga gani, daga bisani ya bude baki ya soma fadin ” Yara suna son Amusement park, tamkar Aljannar duniya suke ganin nan wajen”.

Shiru yayi ya san nesa sa’anan ya cigaba da fadin ” Tunda muke ban taba kawo Sabah nan wurin ba, wanan shine karo na farko”.

Anty fanneh ta dago cike da mamaki tana dubansa. Bai tsaya nan ba ya cigaba da fadin ” lokacin yana karami, sai nayita sa mishi rai ince idan na samu lokaci zan kawo shi amma ban taba cika alkawarina ba. Yawanci abubuwa daya kamata na dinga masa a matsayina na uba, bana mishi saboda bana samun lokaci. Sabah ya taso shi kadai amma kafun na ankara sai na lura da baby boy dina ya girma ya zama mutum wanda ba sai ya jira an masa ba, baya depending akan kowa, shi kadai yake abubuwansa da kansa. Ko ma meye yake damunsa bazaki taba ji ya bude baki ya fada maka ba, da kanshi zaiyi solving matsalarsa abun har ya kaiga bai ma san yanda ake relying akan wani ba”.

Samha tana tsaye tana jinsu, jikinta ne yayi mugun sanyi, data lura sunyi zurfi cikin maganarsu hankalinsu baya kanta, yasa ta juya a hankali ta dau hanyar da Sabah yayi ta soma bin bayansa.

Daidai wajen wata rumfa inda ake sayar da kayan motsa baki ta hangoshi yana zaune yayi zurfi cikin tunani, wani karamin yaro ne yazo wucewa yayi tuntube ya fadi a kasa, Nan da nan Sabah ya farga ya mika hannu zai taimakawa ya yaron, Samha ta karaso a hankali tazo ta tsaya a gabansa, Sabah ya dago ya ganta, shiru yayi yana kallonta, itama binshi da kallo takeyi jiki a sanyaye tana fadi can kasan ranta “karka damu Sabah, abubuwan dakayi missing lokacin kana yaro zan tayaka dawowa dasu. Murmushi tadan sakar masa ta mishi alamun daya tashi su tafi, babu musu Sabah ya mike suka soma tafiya tare.

Bangaren su Khady da Amjad kuwa, yau ce ranar yakin badal din da khady taketa kirari, wani irin kwaliyya tayi mai bala’in kyau, sanye take da takalman data siya a jiyan gashi sunyi mata kadan da kyar take tafiya dasu amma bata hakura ba haka ta dinga lalabawa har ta fito kofan gidansu ta sameshi, koda suka hadu da Amjad ma tsayawa yayi yana kallonta don ta tafi da imaninsa sosai. Ya fada mata tayi kyau, murmushi ta sake ta ce mishi ta gode. Haka suka shiga cikin motarsa yaja suka tafi, suna kan hanya, Amjad ya juyo ya dubeta sa’anan ya soma tambayarta inda take so suje.

Tace duk inda ya kaisu is okay with her. Amjad yace to bari suje ikeja city mall, tunda akwai cinema da wurin shakattwa sosai a mall din, haka Amjad yayi driving sukaje har ikeja, ko da suka shiga cikin mall din, khady da kyar take iya tafiya saboda takalmin data saka, suna cikin tafiya takalmin ya harde ta tayi tangal tangal kamar zata fadi, Amjad yayi saurin kamota, nan ya nema daya daga cikin kujerun shakkatawa dake cikin mall din ya zaunar da ita yana mata sannu.

Khady ta cire takalmin ta soma matse matsen kafafunta da sukayi ja har sun soma kumburi saboda matsan da suka sha cikin takalmin. Amjad ya dubi kafan sai ya fahimce abunda ke faruwa, ya mike yace mata yana zuwa, bai jira yaji mai zata ce ba ya tafi ya barta zaune a wajen, nan ya fara dube dube a cikin mall din ko zaiga shagon da ake siyar da takalma.

Khady na zaune shiru shiru har kusan mintin goma sha biyar bata ji duriyar Amjad ba, cike da damuwa ta mike ta soma dube dube cikin mall din ko zata ganshi. Kamar daga sama taji ana kiran sunanta ” khadija! Khadija”

Khady ta waigo cikin sauri, fuskar da bata taba zaton zata kara ganinsa ba ta gani tsaye a gabanta. Fuskar tsohon saurayinta ne Alamin. Wani irin harara ta watsa mishi sa’anan ta juya mishi baya tayi kamar bata ganshi ba.

Alamin ya karaso inda take yazo ya tsaya a gabanta yana fadin ” Haba khady, kwana da kwaniki banji duriyarki ba, ko na kira layinki ma baya shiga, koya shiga ma baki daga kirana? Kin shareni kin manta dani? Me yayi zafi haka khady? Nine fa Alamin naki”. Ya karasa maganar yana mararice mata fuska.

From nowhere sai ga Amjad nan ya bullo ya tsaya a bayansu, duk maganganun da Alamin ya gama fadi karap a kunnensa.

Wani irin kallo khady ta watsawa Alamin sa’anan ta soma rufeshi da masifa ” wai kai Alamin har kanada bakin da zaka zo ka tunkareni kana fadamun wanan shirmen. Wato ka manta da yaudarar da cin Amanta daka dingayi a baya? Ko dayake ba laifinka bane laifi na…..”

Sai kuma ta tsaya ta yanke maganar da take sonyi don ganin Amjad tsaye a gefenta yana kallonta.

Bata tsaya wata wata ba taje ta tsaya inda Amjad yake ta cigaba da fadin “kaga ma bari nayi introducing dinka wanan shine saurayina sunanshi Amjad.”.

Ta fada mishi tana nuna Amjad. Daga bisani ta cigaba da fadin “Toh yanzu ya? ka sake samun wace zaka ci amanarta ka yaudareta ko har yanzu shiru?” ta watso mishi tambayar tana hararansa.

Shiru Alamin yayi yana musu wani irin kallo ita da Amjad din. Amjad ma shiru yayi bai ce komai ba. khady taja hanun Amjad tana fadin “kaga kyaleshi, taho mu tafi”. Haka ta ja shi suka tafi suka bar Alamin tsaye a wajen yana binsu da wani irin kallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *