ZAFIN RABO CHAPTER 10 BY SAKIEYY
Bata tashi daga barci ba sai 10, tana farkawa tayi hanyar bathroom d’inta ta tsara wankan ta sannan ta fito, tayi shiriya cikan wata doguwar riga navy blue and pink ta material ta saka mayafi sannan tayi duk wani abunda ya zaman mata aladarta ta fito daga d’akin, amma sai da ta tabbata bata ji d’uriyar kamal ba, kitchen ta fara zuwa dan samar wa cikinta abunda zata ci, d’aura ma kanta tea tayi sannan ta d’auki bread tayi sandwich, sai da abincin ta yayi taci sananan ta k’ara dawowa kitchen d’in ta shiga dube dube, store d’in mak’il yake da kayan abinci da drinks ba abunda babu, tana bud’e fridge shima a cik’e taga su fruits, da vegetables da snacks da wasu drinks d’in, tana bud’e freezer itama tagan ta cikin da nama, su kaza su kayan ciki da dai suaran su, duk basu fara k’ank’ara ba alamun ba’a dad’e da zuba su ba, fitowa tayi da kayan cikin da kaji guda biyu ta ajiye a gefa, sannan ta shiga gyara su, sai da ta gyara su tsab sannan ta d’ora kayan cikin ta bar kajin a madanbaci, sannan ta fita daga kitchen d’in.
+
A hankali sakeena ta taka ta shiga d’akin kamal, tana shiga d’akin k’amshin turaren mad dad’in kamshi ya dake ta a hanci, share wa tayi ta fara duba d’akin, ganan yarda d’akin yake kawai ta girgiza kanta, haka ta shiga gyara mishi d’aki, ta canza mishi bedsheet, ta wanke mishi band’aki, ta shiga closet d’inshi ta gyara abunda zata gyara, kayan shi na dati ta saka a laundry basket, kan kice me d’akin yayi k’al dashi sannan sakeena ta fito, parlor ta k’ara gyarawa shima ta gama tayi d’ayan side d’in da bud’e d’aki d’aya ta gyara shi sosai shima ta wanke toilet, ta shimfid’a bedsheet shima daman ba komi akan gadon, sai da ta tabbata d’akin yayi k’al sannan shima ta fito da gyara parlor d’in saboda bata sani ba ko k’annan nashi zasuyi amfani dashi, sai da sakeena taga gidan ta yayi k’al kamar zaka zuba ruwa a k’asa kasha sannan ta koma kitchen, nan da fara yanke yanke yanken abunda zata iyayi da d’ora abubuwa da suk’e dad’ewa kan su dahu, ka ganta ta ta fita daga hayyacin ta aiki kawai take durk’a dan tunda ta tashi bata zauna ba, sai jin horn tayi, gabanta ne ya fad’i ta zata ka’annan nashi ne suka zo, d’aga idanunta tayi kan agogo taga hud’u da rabi, har lokaci ya jaa haka bama ta sani ba, fitowa tayi ta koma parlor dan ta l’eka, tana l’ekawa ta ji hankalinta ya kwanta, kamal ne ya fito daga mota, yana sanya cikin suit black, hannunshi ruk’e da wata briefcase, wata harara ta daka mishi ta window d’in tare da jan wani mugun tsaki, ta komawa hanyar kitchen,
“Ai kin banza, ya saka duk na wani rud’e na zata k’annan shi ne zasu shigo su ganni a haka”
Duk ta fad’i a ranta tana mita, haka ta koma kitchen ta cigaba da girkin ta, anyi kusan awa d’aya tun dawowar kamal, bata k’ara jin d’uriyar shi ba, sai jin knocking tayi, kan ta amsa an bud’e k’ofar, maida idanunta tayi wurin taga kamal a tsaye, ji tayi munfashinta yayi sama bata san daga ina ba kawai ganin shin da tayi da had’a idon da sukayi, yana sanye cikin manyan kaya yadin gray kana ganinshi kasan mai tsada ne hula na kanshi, ga turaren shi da duk ya mamaye gidan, haka ta bishi da kallo, bata san me ya saka ba,
“Nazo na gaya miki yanzu zanje na d’auko su, suna garin nan ma tun safe, so nan da magrib insha Allah zamu dawo”
Yana maganar yana duba agogan shi, sakeena da har lokacin kallon shi take ta kasa d’auke idanunta maganar shi ce ta dawo ta ita, tayi sauran maida idanunta wurin juya brown spaghettin da take, bata amsa shi ba, har ya k’araci tsyauwar shi ya fita, yana fita tayi wata ajiyar zuciya, ta fara tambayar kanta me ya saka tayi ta binshi da kallo, ta fi minti biyar tana ma kanta tambayar da ta kasa bama kanta amsa can kuma ta juya ta cigaba da aikinta, minti talatin duk ta kamala girkin da zatayi, ta shiga zubawa a flask tana kaiwa dining table, sai da ta tsara komi tsab ta koma kitchen ta fara dirk’ar wanke wanke, ita ta manta rabon da tayi irin wannan aikin, minti talatin shima ya d’auke ta ta gama tare da gyra kitchen d’in tsab, sannan ta d’auko ta kunna turaran wuta ko ina a gidan har d’akin kamal, da side d’in da k’anan shi zasu sauka, tana duba agogo taga shida da rabi, sauri tayi ta ajiye kaskon turaren wutan akan center tabla a parlor sannan tayi d’akinta da sauri dan tasan a kowane lokaci zasu iya shigowa, sai da ta kulle d’akinta da muk’ulli sannan ta fad’a bathroom ta tsala wankan ta, fito, a niste ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa, d’inkin yayi kyau, ta sakama fuskar ta hoda ta kwalli da d’an lipgloss, ta d’auko mayafi dan ya shiga da kayan ta d’ora akan ta bayan ta d’aura d’ankwali, ta feshe jikinta da turare sannan ta fito, tayi mamaki da bata ga koma a parlor ba dan yanzu har bakwai ta wuci alamun basu iso ba, k’ara kunna wani turaran wutan tayi ta shiga sakawa a ko wane lungu na gidan, tana cikin haka taji k’arar horn, sauri tayi ta leka ta window ta ga mai gadi na shirin bud’e gate, a hankali ta ja baya ta koma kitchen ta kulle, gabanta wani irin fad’uwa yake, sai ta d’an sami nustuwa sannan ta fito, ta ajiye kaskon hannunta a gefe, sannan tayi hanyar k’ofar parlor da ake ta dannan doorbell, murmushin yak’e ta saka a fuskar ta sannan ta bud’e k’ofar bayan tayi ajiyar zuciya.
STORY CONTINUES BELOW
Kyawawun k’annanshi, farare sol ta gane a tsaye dukan su na cikin bak’ar abaya, murmushi ta sakar musu tare da musu sannu da zuwa da basu wuri su wuce, suna wucewa da dubi kamal wanda yake a tsaye, manyan idanunshi kaf akanta, ko k’ifta su bayayi wata harara ta daka mishi ta juya zata bisu ciki, sai ji tayi ya jawo ta jikinshi, k’anshin turaren shi ya k’ara dakar mata hanci, a hankali taji wannan deep voice din tashi a kunan ta,
“Kin manta, yi zamuyi kamar ba wata matsala a tsakanin mu”
Wata ajiyar zuciyar tayi, a haka ta kyale shi, tana jikin shi har suka koma parlor, suna shiga ta gansu a tsaye a tsakiyar parlor d’in, murmushi ta musu, suma d’in murmushi na d’auke akan fuskar su, ga mamakin ta sai gani tayi k’aramar tayo kanta da sauri ta rungume,
“Finally, yau naga yayata da idanuna”
Yarda kausar tayi maganar sai da ta bana koma dariya a parlor d’in harta sakeena, sun dad’e a rungume sai can taji an kwace ta daga jikin kausar, tana d’aga idanunta suka had’a ido da kamal,
“Ya isa haka kausar kada ki, b’alla mun ita”
Yarda yayi maganar da wani irin salon shi, ga idanunshi basu bar kanta ba, hannunshi sak’ale akan k’ugunta, suara k’iris ta mishi wata harara, kawai sai gani tayi ya matso, bata ankra ba sai jin lips d’inshi tayi akan kumatun ta ya sumbata, tsigar jikinta wani tashi tayi saura k’iris ta kwace bada ban kamal ya mata wani mugun rik’o ba, a haka da kyar ta dake tayi murmushi yak’e sannan ta maida idanunta kan k’annan shi, da suke musu wani irin kallo alamun suna burge su, sakeena wata harara tayi a cikin ranta, sannan ta fara cewa
“Muje na kaiku d’akin da zaku sauka ko,”
Tana maganar ta kwace daga jikin kamal da k’arfi sannan tayi wurin babar ta karb’i akwatin ta, ta fara takawa d’ayan side d’in, tana ji babbar ta fara ce mata dan Allah da barshi zata jaa abun ta, ita kuwa sakeena tace mata bakomi a haka har suka isa guest bedroom d’in, suna shiga wan
i dad’in kamshi ya cika d’akin ga sanyin ac, sakeena ta samu ta ajiye mata akwatin a gefan gado sanan ta juya ta maida hankalinta kansu, fuskarta d’auke da murmushi,
“In kun gama abunda zakuyi, ku zo parlor abinci na nan na jiran ku”
D’aga mata kai sukayi, murmushi ta k’ra musu ta fita daga d’akin tare da jawo musu k’ofa, tana fitowa parlor taga kamal a zaune akan kujera, ya cira hular kanshi tv a kunne, wani mugun kallo tayi mishi sannan ta koma kitchen, fruit salad da zob’on da ta saka a fridge ta d’auka ta dawo dasu kan dinning sannan ta koma ta k’ara kunnan farfesun kayan cikin, sai da yayi ta zuba a wani katon plastic bowl sannan ta fito shima ta ajiye akan dinning a daidai lokacin k’annan shi suka fito,
“Sannu, mun saka ki aiki ko”
Kamila ta fad’i a yayain da ta k’araso dining area d’in ita da kausar murmushi na d’auke akan fuskar su, zata amsa kenan sai jin bayan ta tayi ya daki wani fad’ed’an k’irji gaba d’ayan ta ta shige, kamshin turaren shi ne ya sanar da ita ba kowa bane in ba kamal ba, numfashin shi taji da muryarshi taje a wurin wuyan ta,
“Eh mana, kun saka nun baby na aiki, gaba d’aya kun gajiyar mun da ita”
A wani hankali yayi maganar tare da k’ara rungumota da manna ta ajikin shi, kunya ce ta kama sakeena, wai dan Allah me matsalar shi ne, ko lafiyar auran su k’alau bai kamata ya dunk’a mata haka ba a gaban k’ananshi balle yanzu da dukan su ba abunda suka tsana irin junan su, a hankali ta cire hannanyrn shi daga kan cikinta ta juyo ta kai idanunta kanshi, shima d’in ita yake kallo, manyan idanunshi sunyi wani narai narai dasu, sai ki rantse da Allah akwai soyayya mai k’arfi tsakanin su,
“Lallai kamal, you are a very good actor”
Ta fad’i a ranta yayin da azahiri ta maida kallonta kan kausar da kamila, wanda fuskar su har lokacin akwai murmushi a cikin ta, hannunta na cikin na kamal saboda yak’i sakin ta tayi musu nuni da su zauna, tana gani sun zauna akan kujerar dining table d’in, ta maida kallon harara ta kanshi, wanda har lokacin bai d’auke idanunshi daga kanta ba, a hankali ta fara mosta bakin ta yarda k’anan nashi baza su ji ba ta fad’i,
“Ka sake mun hannu”
Tana gani ya girgiza kanshi, sakeena itama girgiza kanta tayi, zata saka hannunta ta kwace ya ruga ta, k’ara matsowa kusa da ita yayi, sannan ya kai bakinshi kan kunanta, ya rad’a mata a hankali,
“Zan sake ki, amma sai kin yarda zaki bani abinci a baki”10
Da mugun sauri ta fusge daga jikin shi, wani irin abu taji ya taho tunda kaf’arta har tsakiyr kanta da yayi maganar, harara dai ta k’ara daka mishi, shi kuma fuskar shi d’auke da murmushin mugunta, sauri tayi ta maida hankalinta kan su kausar ko sunga mai ya faru, taga hankalin su baya wurin suna hira, hamdala tayi tare dayin wurin su zatai serving d’insu, sai ganin kamila tayi ta mik’e,
“Ai ki sami wuri ki zauna, zanyi serving d’in kada ki k’ara wahalar da kanki”
Wani dad’i taji ya mamaye ta, gaskiya y’an gidan su basu da matsala ita kuwa bata san inda kamal yaje ya samu wannan mugun halin nashi ba dan ko kamil kirkin shi yayi yawa,
“Bakomi Allah, ku ne da gajiya tunda ku kuka yi tafiya dan haka koma ki zauna na k’arashe lada na”
Muryarta d’auke da murmushi, k’ara ganin kausar tayi ta mik’e tayi kanta, hannunta ta rungumo,
“In batun lada ne muma ki barmu mu samu sobada haka ki zauna k’afafuwan ki suma su huta, ki bari mu taya ki”
Kausar ta fad’i yayin da ta zaunar da sakeena a kan kujera, sannan ta juya ta koma wurin yayarta, sakeena kuma binsu tayi da kallo da murmushi, dan taji sun bal’in kwanta mata a rai, jin zaman da tayi akan kujerar kusa da ita ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin ta, manyan idanun kamal akanta, hankalinshi gaba d’aya shima fuskar shi d’auke da murmushin muguntar nan nashi, sai da gaban sakeena ya fad’i, dan tasan wata muguntar yake shirin aikatawa.
a ita, kallan shi take, kallan da baya dauk’e da komi sai tsan tsan k’iyayya,
da kikayi”