ZAFIN RABO CHAPTER 6 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 6 BY SAKIEYY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ita kuma ta kasa gane lamarin gaba ki d’ayan shi, me ya saka yayi mata abinda yayi mata, ita da ba abinda ya tab’a had’a ta dashi, duka duka yau ce rana ta biyu da ta fara ganin shi, sai d’azu ma ta tuna ashe fuskar shi ita ce wacce ta gani a gaban cilantro ranan nan, wani irin fad’uwa gabanta yake tunda ta iso garin kano, ga yarda taga mijinta na yi mata, it tasan ba haka akeyi ba ranar farkon aure, tasan ba santa yake ba dan had’a su akayi, ta wani b’angaran ta gane b’accin ranshi dan itama basan auran take ba, amma ya kamata yayi mata abunda yayi mata? Tana ganin bata cancanci haka ba, ita wallahi mutuk’ar tsoron shi take ji, duk bakinta yau ta neme shi ta rasa ta kasa mayar mishi da murtani, in ka ganta ta canza a d’an awani kawai, dukan ta a birkice take, bayan ja wur da idanunta sukayi tsabar kuka, jin tab’a tan da akayi ne ya saka ta saurin dawowa daga tunanin ta,1

“Nace muje ko”

Datijuwar ce tayi mata magana, sakeena kuwa ta tsaya wa tayi ta zuba mata ido, dan bata gane suje ba, ta bita suje ina?, ina ma wai ya kawota ya ajiye ta ne?, ji tayi bari kawai ta bud’e bakinta ta tambaye ta,

“Ina zumu je?? Wacece ke?”

Haka ta had’a tambayoyin tayi mata duk a lokaci d’aya gani tayi matar ta kyalkyale da dariya,

“Me kike ci na baka ne zuba, ai in kike bini zaki gane ma kanki”

Ganin yarda bata yi magrib ba ga har isha ta far shawo kai, tace ma mata da su je, duk a ganinta matar bata wuce y’ar uwar shi ba, haka ta bi bayan matar har suka shiga cikin gidan, compound d’in gidan ba wani mai girma bane, haka har suka isa parlor, shima parlor din saisai saisai yake ba wani abu mai tsada a ciki kawai kujeru ne sai tv da take a jikin bango, y’an matan da ta gani a wurin tabi da kallo, ko waccen su hankalin ta nakan tv d’in wurin, sakeena a hankali ta furta sannun ku, a ganinta y’ayan matan ne, ba wacce ta amsa ta dukda duk sun juyo yanzu suna kallon ta, sai mutum d’aya itama ma ba ita tayiwa magana ba,

“Sisi wace kuma wannan?”

Ko yarda taji tayi maganar tasan yarinyar bata da tarbiya, abun ne ya d’an bata mamaki, taya y’a zata wa uwarta magana haka,

“Me ya saka kike tambayar ta, daga ganinta ai kinsan bak’uwar ta ce”

D’ayar wacce take zaune akan 3 seater wacce da kad’an da d’ara wacce ta fara magana ta fad’i, ga dai su mata masha Allah amma tarbiya sai a hankali, iyayen da basa zama suyi ma y’ayan su tarbiya na bata mamaki,

“Kwayi mun tambayoyin ku anjima, yanzu dai, Hadi tashi ki kaita d’akin ku ta d’an watsa ruwa, in kin fito na muku bayani”

Wace aka kira da hadi ta mik’e, itace wace tun shigowar ta bata yi magana ba, haka ta fara yin gaba bata ce ma sakeena komi ba, ita kuwa da taga haka ta bita, sai da suka shiga wani d’aki, katifa ce a k’asan dakin sai akwatina a gefe, tsayawa tabi d’akin da kallo duk yaji jiki,

“Ga band’akin”

Hadi na gama fad’a tare da nuna mata band’akin ta fita ta bata wuri, ita kuwa sakeena binta tayi da kallo, sai can kuma ta juya ta fara rage kayanta tare da fad’awa ban d’aki.

Ba wani wankan da tayi dan mai zai kaita ita da ba zama tazo yi ba, tasan anjima kad’an zaizo d’aukan ta, ita kuwa taga k’arfin halin matar da tace ta watsa ruwa a jikinta, sai da ta idar ta sallolinta tsab tare da dadewa akan sallaya dan mik’a kukanta ga ubangiji, ta dad’e a zaune a wurin ba irin addu’ar da bata yi ba da Allah ya bata ikon cinye wannan jarabawa, tana zaune taji an turo k’ofa, haka ta juya ta maida hankalinta wurin,

“In kin gama kizo parlor sisi na neman ki”

Tana gama fad’i da k’ara yin waje abunta, haka ta tashi ta ninke abun salla sannan ta fita itama, tana isa parlor taga dukan su a zaune yanzu harda k’arin wasu mata biyu way’anda ba ta gani ba d’azu, ita kuwa duk y’ayanta mata ne, gashi kuma basa kama da ko wacce a cikin su, haka t shiga yima kanta tambayoyi har ta sami wuri ta zauna a kusa daga wata daga cikin su, sai da matar ta tabbata ta zauna ta nustu sannan ta fara bayani,

STORY CONTINUES BELOW

“Nasan kina tayi wa kanki tambayoyin ina ne nan, yanzu zanyi miki bayanin komi, duk wacce kika gani anan”

Ta fad’i tare da nuna y’an matan,

“Zaman kanta take”

Bata gane ba, zaman kai kuma? mai haka yake nufi, kan ta bud’e baki tayi magana matar ta riga ta,

“Wacce y’ar farar sunanta, saratu amma anfi kiran ta da sarah, wacce mai billan sunan ta zainab amma ana ce mata zeezee, ta kusa da ita sunan ta jamila ana ce mata jamy, wacce mai wushirya sunnan ta, ummeeta, sai kuma hadiza, hadi”

Sakeena shiga tunani tayi na me yasa ta ake mata bayanin sunan su, mene dalilin yima sunayen su k’ak’ale,

“Dukkan sun da kike gani su suke fita su kawo mun abunda zanci, kuma ba alak’a ta jini da ta had’a mu”

Zaro idanunta waje tayi, dan yanzu ta fara gane inda matar ta dosa, zan kad’a zan k’adan matan na zaman kansu? Sai sun fita sun kawo mata abunda zata ci, shin kasuwanci sukeyi ko aiki sukeyi ita bata gane ba,

“Ban gane ba alak’a ta jinin tsakanin ku ba?”

Ta tambaya a sanyaye,

“Me ya saka kike mata wata kwana kwana,” umeeta ta kalli sisi tayi mata maganar, sannan ta maida hankalin ta kan sakeena,

“Ke kinga, dukkanin mu nan karuwai ne, kema abunda ya kawo ki nan kenan”

Wani irin muguwar fad’uwa gabanta yayi, zuciyarta ta fara harbawa, me kuwa take nufi,

“Daga ya kawo ni nan ya ajiye ni sai kice karuwan ci nazo”

Sakeena ta fad’i murya na rawa, hankali a tashe, jin dariyar sun da yayi ya k’ara saka ta a matsanancin tashin hankali,

“Ke yanzu me da kika zata kinzo yi nan?”

Sisi ta tambaye ta, sannan ta k’ara da

“Ai kallo na kikayi kinsan ban had’a jini da mutumin nan ba balle har kice dan uwa na ne, mutum da yaka kama da larabawa, mutumin dake wanka da naira ga kasaita da jan aji, ki fa dube ni tsaf ki kagani”

Da wani mugun sauri ta mik’e, tare da fara ja baya, ga hawaye na kwarara daga idanunta, girgiza kanta ta fara, bayan addu’ar da ta fara yi a ranta, meke shirin faruwa da ita ne?, kamal gidan karuwai ya kawo ta? tayi mene? wani fad’uwar gaba ne ya k’ara kamata, binsu tayi ta kallo taga ko wacce da alamun murmushi a fuskarta, wani mahaukacin tsoro ne ya baibayeta ga sabbabin hawayen da suka sake zuba da gudu tayi hanyar waje, baza ta tab’a tsayawa a cuci rayuwarta ba, bud’e k’ofar tayi taga ta k’i bud’uwa, k’ara jan handle din tayi amma ina, da taga k’ofar tak’i bud’ewa ga tane nema ta b’ata mata lokaci ta saka k’arfinta ta k’ara buga ta da jikinta, ko ciwon abun bata ji ita kawai ta samu ta gudu daga wurin mugayen mutanen nan,

“In da zaki daina wahalar da kanki da yafiye miki, kinga dai k’ofar k’arfe ce duk abunda zakiyi mata baza ta bud’u ba sai dai kiji ma kanki ciwo”

Sarah ce ta fad’i wannan karan, tana tauna chewing gum yana k’aras k’aras, ga hannunta da yake wasa ta kistsan attach d’in kanta, sakeena bata bi ta kanta ba, yima tayi kama
r bata jita ba ta cigaba da buga k’ofar ga kukan da take yanzu mai sauti, ta dad’e tana abu d’aya har ta gaji da zube a k’asa a parlor d’in ta ci gaba da rairai kukanta mai abun tausayi, can kuma ta mik’e tayi wajan sisi, wacce tayi banza dasu tana ta faman danna waya, tsugunnawa tayi a gabanta tare da kamo cinyoyinta

“Dan Allah ki kyalle ne na tafi, wallahi ban tab’a sanin d’a namiji ba a rayuwa ta, ban tab’a aikata zina ba, dan k’wanar da kika ma manzon Allah ki bari na fita daga cikin gidannan”

K’ara yin banza da ita sisi tayi, a gefan ta tana ji ummeeta da sarah na dariya harda shewa da tafawa, sakeena yanzu ba takan su take ba, so kawai take wannan matar ta saurare ta,

“Kudi kike so?” Tayi mata tambayar a rikice, “in kud’i kike so ko nawa ne zan baki, duk abinda kike so zan baki amma dan Allah kada ki jefa ni cikin mugun halin nan, dan Allah ki taimaka min ki kyale ni nabar garin nan” wani kukan ya k’ara sub’oce mata, sai a wannan lokacin sisi ta d’ago ta kalle ta,

“Nace miki kud’i nake so?, kuma duk arzik’in ki banji kina da irin kud’in da wanda ya kawo ki yake bani”

Tana gama maganar ta uwarci zeezee da jamy su kama sakeena su kaita d’aki dan kukanta ya fara damun ta, haka suka mik’e suka kamata, duk shure shuren da take basu sake taba daman su biyu sun d’anfi girma da k’arfi a cikin su,

Suna shiga d’akin suka jefa ta akan katifa, jamy ta juya ta bar d’akin, ita kuwa zeezee na tsaye ta kifa ma sakeena kallo wacce take kuka kamar ranta zai fita,

“Bari na baki shawara, wannan kukan da kike bazai tab’a saka kowa a cikin gidannan yaji tausayin ki ba barin ma sisi, kuma tunda kin shigo hannunta na miki alkwarin baza ki tab’a fita daga hannunta ba, kin shigo kenan, dan duk garin nan kowa yasanta ya san da zaman ta a harkar dabanci ta tashan ci dan haka gwanda ki kwantar da hankalin ki ki san ki zo zaman dindin din a gidan nan sai kuwa wani ikon Allah”

Tana gama maganar ta juya ta bar dak’in tare da rufi mata k’ofar.

Sababin hawayen ne suka k’ara zuba a fuskar ta, inallillahi wa inaillahi rajiun kawai take ambata, yau tashiga uku, mijinta na sunna da kanshi da hannunshi ya kawota inda za’a ci mata mutunci, inda za’a zubar mata da k’imarta ta y’a mace, wani irin zafi taji k’irjinta ya fara mata, da rad’adi da ciwo, wana irin mutum daddy ya aura mata, wani irin mugun dan adam Allah ya had’ata dashi, ko a mafarki bata tab’a zatan haka zata faru da ita ba, shiga tunanin tayi a lokacin, me ta tab’a yima kamal a duniya yake san cutar da ita, mutumin da bata tab’a sani ba a rayuwarta, kanta ne ya fara wani sara mata, sa hannun tayi ta ruk’e kan ko zai daina yi mata ciwo, in har mugun abu ya faru da ita ta sanadiyar kamal wallahi baza ta tab’a yafe mishi, ko bayan ranshi ko bayan ranta, ko a ranar lahira.A hankali yake tuk’a motar har ya isa hotoro GRA, bayan yazo saitin makeken gidan ya fara yin horn, bai jima ba aka zo aka bud’e mishi haka ya saka hancin motar shi ya shiga cikin har yayi parking a harabar gidan, ya jima kafin ya fito, a sanyaye ya taka har ya isa parlor d’inshi, yana shiga ya wani zube a kan doguwar kujera tare da k’urawa pop d’in d’akin ido, wani irin nishad’i yake ji, bazai taba iya misilta irin farin cikin da yake ciki ba, ranshi yayi mishi wani irin fari, baima fara azabtar da ita ba, wannan kawai somun tab’i ne, sai ya tabbata an gama da ita a gidan karuwanan an tsorata ta tare da raba ta da kwanciyar hankali da farin cikin ta sannan ya dawo da ita gidan nan ya k’arasa gamawa da ita, yayi alkwarin sai ya maida ita zararriya kuma tab’arb’iya sai ya musguna mata irin muguntar da ta fita daga tsamanin ko wane irin mutum.

+

Yana gama tunanin shi ya mik’e yayi kitchen, fridge ya bud’e ya d’auko bottle water ya fara zubawa cikin sai da ya sha ya k’oshi sannan ya fita yayi hanyar bedroom d’inshi, yana shiga ya fara neman switch dan ya kunna fitila saboda duhun d’akin, d’akin na kawo haske yayi idu biyu da frame d’in dake fashe akan tiles, wata irin ajiyar zuciya yayi, sannan a hankali ya fara takawa har ya isa wurin, kamar wanda bashi da laka haka ya tsugunna ya d’auke frame d’in a hankali, da fuskar kamil ya fara cin k’aro, jin wani abu yayi ya soki zuciyar shi, ya nemi duk farin cikin da yake ji d’azu ya rasa, haka ya dunk’a kura ma fuskar shi kallo kamar kamil ne yake kallo a zahiri, idanunshi sunyi jajawur dasu a d’ank’ank’ani lokaci, k’walla ta cika idanun taf,

“zan rama maka abunda tayi maka, yarda ta hana ka farin cikin, ta saka ka a cikin rayuwar kwunci nayi alk’warin sai na ninninka mata abunda kaji, sai na saka ta dana sanin zuwa duniya kamil, yacce ta zama sanidiyar mutuwar ka nima sai na zama sanidiyar tata ko bata mutu ba sai na tabbata na raba ta da hankalin ta”

A hankali yake maganar ga wasu kwalla masu zafi da suke zuba a idanunshi, har yau ba wanda yasan mene ya hardasa cutar kamil, ko mami da abba, shi kad’ai ne ya sani, shi kad’ai ne yasan irin tashin hankalin da kamil ya shiga a sanadiyar sakeena, shine kad’ai yasan yarda so ya azabtar da d’an uwanshi, shine k’adai yasan wahalar da kamil yasha a hannunta, dan haka duk abunda yayi mata daidai ne, duk rashin imanin da zai nuna akanta daidai ne dan ita muguwar mace ce, mayaudariya maici amana, dama zai iya maida hannun agogo baya da sai ya hana kamil zuwa turkey, dan ya sani da bai je k’asar ba da ba abunda zai tab’a had’a shi da ita, wani irin tsananar ta yaji ya k’ara bi mishi jini, ba abinda bai gaya ma kamil ba lokacin da yazo wurin shi yayi mishi maganar ta, ba abunda bai gaya mishi ba akan san da yake ma yarinya yayi yawa amma sam sam bai ji maganar shi ba, shi kuwa da yaga d’an uwanashi cikin tsan tsan farin ciki shine abun da ya hana shi k’ara mishi wata maganar, kuma yayi mutuk’ar danasani, hawaye sun gama jik’a fuskar kamal, ji yake zuciyar shi na tafasa kamar zata fashe tsabar bacin rai, ya tsane ta ba y’ar k’aramar tsana ba, yak’i jininta.

Zumbur yayi ya mik’e kamar wanda aka tsikara wa alura, bayan ya ajiye frama d’in a k’asa, hannunshi ya saka a back pocket din wandon shi ya d’auko wayar shi sannan yayi dialing kan number d’in haj maimuna, ba’a dad’e ba ta d’auka, shi ya fara magana ko amsa sallamar ta bai tsaya yi ba,

“Ina so ki had’a ta da wani a daran yau, wanda zai lallata mata rayuwar ta wanda zai mata tabon da baza ta tab’a mantawa dashi ba, ina son ki had’a ta da wanada zai saka ta cikin fargaba da tsoro da dana sanin zuwa duniya”

Yana gama fad’a ya kashe wayar shima bai jira amsar ta ba, wasu hawayen ne suka sake zubowa a fuskar shi, a hankali ya sami wuri ya zauna akan gado tare da saka tafin hannunshi ta kulle fuskar shi ko dan hawayen zasu daina zuba, amma kamar ya k’ara kunna su, ba abunda yake tunawa irin muguwar wahalar da kamil yasha, cutar da yayi wacce tak’i ci tak’i cinyewa, mintinan da yake jera wa yana aman jini, kwanakin da yake a kwance ba ya iya ko motsi, duk sabida wata banza mace, macen da ma yafi k’arfinta, yayi ma kanshi alkwarin bazai tab’a yin kuskuren da d’an uwanshi ya tafka ba, bazai tab’a kula mace ba balle har yayi irin wannan mahaukaciyar soyyayar, haka ya zauna shi kad’ai a d’aki ba abunda yake sai zubar da kwalla dan yayi mutuk’ar kewan kamil, sai da ya gama kukan shi mai isar shi sannan ya mik’e yayi bathroom dan yin wanka da alwala ko ya d’anji sanyi a ranshi.

(To yanzu dai munsan mai ne ya faru da kamil, ciwon mutuwar sa da har yanzu baibar kamal ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *