ZAFIN RABO CHAPTER 9 BY SAKIEYY
Bayan sun idar da jam’in sallar azahar, kamal ya gama add’oin shi a niste, ya mik’e ya fito daga masallacin a hankali yake tafiyar shi, cikin nutsuwa da kasaita, yaso ya tsaya har ayi sallar la’asar yadda ya saba a kullum amma yaga yau bazai iya tsayawa ba, shima kanshi baisan mai ya saka ba kawai dai yana so ya koma gida, haka ya tsallaka titi ya nufi hanyar makeken gidan shi da yake tsallaken masallacin, yana knocking gate d’in bai dad’e a tsaye ba mai gadi ya taho da sauri ya bud’e mishi, yana mik’a gaisuwa, kamal d’aga mishi hannu yayi, tare da yin cikin gidan, bai tsaya danna doorbell ba ko knocking kawai ya saka muk’ullin shi ya bud’e k’ofar, bai yarda da ita ba soboda haka ko da wasa bai bar k’ofar a bud’e ba,
Baiyi mamaki ba da yaga parlor din wayam dan yasan bazata tab’a fitowa ta zauna a ckin shi, amma abunda ya bashi mamki da yaga ba kowa a dak’in ta, ko a bathroom d’inta da ya lek’a, haka ya k’ara fitowa ya lek’a duk d’akunan gidan bata nan, bai tada hankalin shi ba saboda yasan tana cikin gidan bata je ko ina ba, k’ofa a kulle ina ma zata, yayi hanyar kitchen saboda shi kad’ai ni bai duba ba, ai kan yayi rabin hanyar yaga an bud’e k’ofar a hankali ta fito cak ya tsaya, idanunta a k’asa, haka ta kulle k’ofar, manyan idanun kamal akanta,
dariya taso ta bashi yarda yaga ta kinkimo robobin ruwa, hannayen sa ya nanad’e akan k’irjin shi, ya had’e fuska ya bi sakeena da kallo wacce har lokacin idanunta na k’asa, bama tasan yana wurin ba, bai matsa ba har ta buge k’irjinshi, yana jinta a jikinshi yaji wani abu ya taho mishi tun daga tafin k’afarshi har tsakiyar kanshi, baisan lokacin da yayi baya ba a tsorace, itama sakeena tayi baya tare da sakin abun hannuta da zaro manyan idanunta waje, tsoro ya fara bayyana a fuskar ta, jikinta nasan fara rawa,
Zuciyar shi ce ta fara bugawa bai san dalili ba, lumshe idanunshi yayi da sauri dan ya rasa meke damun shi, sai da nustuwa tazo mishi sannan ya bud’e su, sunyi jajaye dasu, yana maida idanunshi wurin da yabar sakeena ya neme ta ya rasa, yana waiwayawa yaga har ta kusa d’akinta, tana tafiya a hankali dan bata so yaji takun ta, wato wayo zatayi mishi kenan,
“Ina kike shirin zuwa ma”
A hankali yayi maganar, yana gani ta tsaya cak da tafiyar ta, yana shirin yaga ta juyo ta maida hankalinta wurin shi, ai haba sai ganin yayi ta saka gudu, a guje ta shiga d’akin tare da banko k’ofar, yana jin k’arar muk’ulli alamun ta kulle d’akin, duk yarda baya san yayi dariya bai san lokacin da ya sake ta ba dan ta bala’in bashi dariya, haka kamal yabi k’ofar ta da kallo yana murmushi, can ya juya ya koma hanyar kitchen, yana shiga baiga alamun komi ba, shiga tambayr kanshi yayi komai tazo yi a kitchen, a haka har ya lek’a store, shima ya shiga ya fara dube dube, yaga kwalin indomie a bud’e da kwalin sardines, murmushi ya saki,
“Wato yunwa ce ta koro ta”
Ya fad’i a zuciya, girgiza kanshi yayi tare da bud’e kwalin talia da makaroni, da kuskus, duk ya d’auko guda biyu ya ajiye a gefe, sannan kuma yayi waje ta kofar baya ta kitchen d’in tare da kwalla wa mallam isyaku kira wato mai gadi, malam isyaku da sauri ya k’araso, kamal umarta shi yayi ya kwashe duk kayan abinci ya saka mishi a mota, malam isyaku mai zaiyi ba in ba binshi da kallon tambaya, kamal kuwa ya had’e girar sama da k’asa sai kace wanda bai tab’a dariya ba,
“Zaka fara kwasar kayan ne ko kuma zaka ci gaba da kallo na”
Yana gama maganar mallam isyaku da sauri ya fara kwasar kaya, dan yasan halin mai gidan nasa, baya san raini da wasa, kamal na ganin ya fara d’ibar kayan, shima ya juya ya kwashi way’annan abinci da ya d’ebo ya fito daga kitchen d’in, bedroom d’inshi ya fara zuwa dan d’aukar spare key, bayan ya dauko ya fito yayi hanyar bedroom dinta, ya saka key d’in ya bud’e kofar, yana bud’e kofar ya ganta zaune akan gado, ta kankame jikinta, tana jin shigowar shi d’akin zumbur ta mik’e, kamal na ganin yarda tsoro ya baiyana akan fuskarta bayan zaro manyan idanunta waje, d’auke idanunshi yayi daga kanta sannan ya cilla mata abincin kan gado, fuskar shi a d’aure tamau ba wasa a ciki,
“Ga abincin da zai ishe ki na wata d’aya, bana san kina shiga kitchen d’ina kina mun sata kamar wata b’era”
Wani irin kallo ta bishi dashi, wanda yake d’auke da tsoro da harara,
“Sata??, dan ina jin yunwa na shiga na dafa ma kaina abincin da aka siya da kud’in ubana shine nayi sata?,
Mamaki ta k’ara bawa kamal, yarda duk abunda zai mata bakinta baya tab’a mutuwa, a hankali ya fara matsowa kusa da ita, ita kuma tana ja baya har bayan ta ya bugi bango, a haka kamal ya k’ara matsowa kusa da ita baifi inchi d’aya bane tsakanin su, sunyi kusa sosai sobada har numfashin su ya zama d’aya, yana gani yarda ta kwada kanta tare da lumshe idanunta, tsoro ya k’ara kamata, kamal wani murmushi ya saki a ranshi, tsoro fal cikinta amma bai hana ta maida mishi da magana ba,
“Kika k’ara wata maganar zan kwashe abincin dana kawo miki ki zama baki da abunda zaki saka a bikin ki har na tsawan kwanaki”
Yana ganin jikinta ya fara rawa, ta k’ara shigewa jikin bango, har lokacin idanunta na kulle, matsawa yayi, saboda kamshin jikinta da turarenta sun fara tada mishi hankali, sai da ya tabbata bata da abinda zata k’ara cewa sannan ya juya zaibar d’akin, baiyi taku uku ba yaji wani abu ya daki bayan shi, da sauri ya juyo tare da maida idanunshi k’asa yaga ledar makaroni, sannan ya d’ago su ya maida kan sakeena wace take ruk’e ta ledar kuskus tana shirin k’ara jefo mishi, sai da ta kalle shi cikin idanunshi sannan ta jefo mishi ledar, yana gani ta jefo yayi saurin kwacewa sai ga ledar a k’asa, k’ara maida idanunshi yayi kanta, wanda sun k’ad’a sun koma jaa, farar fuskar shi itama ta koma jajawur saboda b’accin rai, sakar mata fuska yake da har zata dube shi ta cilla mishi wani abu,
“Ka kwashe abincin ka bana so, da nakai wani abu naka bakina na gwammace yunwa ta kashe ni”
Kamal kawai binta yake da kallo ya rasa mai zaiyi a wurin, tunda yake a rayuwar shi bai tab’a ganin mace ba irinta, saboda ko yarda take da yarda tayi maganar yanzu a tsorace take, amma bai hanata yi mishi abunda taga dama ba, ya zaiyi da ita ne, yaga bata da shirin canza halinta, da sauri ya tako har isa wurinta tare da ruk’e kafad’unta ta buga bayan ta da bango, ya kafa mata wannan jajayen manyan idanun nashi, muryarshi a d’an sama, sai huci yake, in ka ganshi a wurin dole ya baka tsoro,
“Baza ki daina maida mun da magana ba, ni mijinki ne, kiyi respecting d’ina”
3
Ga mamakin shi sai gani yayi ta saki murmushi, sannan ta k’ara kafa mishi manayan idanunta wanda suke cike da tsoro,
“Respect fa kace?, ai ni yarda na sani respect is earned not given kamal, da kana so nayi respecting d’inka ka a matsayin mijina da ka…”
Ai kan ta k’arasa zancen ta, ya d’auke ta cak, ya saka ta akan kafad’arshi, yana ji tana dukan shi dan ya sauk’e ta, amma kamal a zuciye yake, ya gaji da gasa mishi maganganun da take, ko dan tasan bazai tab’a saka hannun ya dake ta ba, a haka tana ta dukan shi da jan laulausan gashin kanshi, da ihon ya sauke ta shi kuwa yayi banza da ita har suka fita daga cikin gidan.
wata irin tafasa zuciyar ta take, kan tayi tunanin kulle bakinta ta maida mashi da murtani, ko yanzu da ya d’aga ta cak akan kafad’arshi bakin ta yak’i ya daina shiru, duk maganganun da take yayi banza da ita sai tafiyar shi yake abunshi, sakeena k’ara saka hannun tayi ta ja mishi gashi da kai mishi duka wai duk dan ya sauke ta, amma ina yak’i ajiye ta har sai da suka shiga wani d’aki da yake a wajen gidan sannan ya dire ta, d’akin kamar store ne, dan taga kwalayen tv, washing machine, microwave, dishwasher, da dai sauran su, tana gama k’arewa d’akin kallo ta juyo ta sauke idanunta akan shi, da suka had’a ido sai da gabanta ya fad’i, fuskar shi ba annuri ko na d’igo d’aya, gaba d’aya kamaninshi sun canza, tsoro ne ya kama, tayi saurin ja baya dan fargabar kada yayi mata wani abu, kamal jajayen idanunshi ya saka akanta ta baya ko k’ifta su, duk da sakeena a tsorace take, haka ta dake ta kawar ta tsoranta gefe ta kalle shi cikin idanunshi, ta fara cewa,+
shirin cire hijab d’inta, ai da sauri tayi baya, har ta fara juyi zata fad’i saboda wani jiri da ya kamata, amma kan ta fad’i kamal yayi saurin ruk’ota tare da dawo da ita jikinshi, tana jin jikinta ya tab’a kirjinshi ta k’ara yin baya, sai dai yanzu bata kwace daga hannunshi ba saboda ya ruk’eta sosai, kunya ce ta rufe ta, wai me ya same shi yau d’innan, anya kamal ne wannan, mai da manyan idanunta tayi kanshi taga shima nashi manyan idanun nakan ta, zuciyar tace ta fara mahaukacin bugawa a k’irjinta, fuskar shi d’auke da murmushi, kamar yana jin d’ad’in abunda yake faruwa da ita, ita tasan duk duk sabon salan muguntar sa ce,
in hanyar d’akinta zuciyar shi ta dawo bugawa a k’irjinshi, kamal share wa yayi, yana zuwa k’ofarta yayi knocking, sai da ta barshi a tsaye yafi na minti biyar, spare key d’in d’akinta yana cikin aljihun wandon shi amma ya kasa d’auka ya bud’e shi kanshi baisan me ya saka dalili ba, amma kuma haushin ta yake ji, daba dan yana so su d’an daidaita kan su kausar su zo ai da bazai ma zo wurin ta ba tana mishi wulaqanci, yana cikin tunani yaji k’arar muk’ulli a hankali k’ofar ta bud’e, sakeena na tsaye, a cikin wani k’aton hijab ba abunda take mishi in ba binshi da wani mugun kallo ba mai d’auke da harara ta kuma tsana, kamal kuwa murmushi ya sakar mata, yasan zai k’ara k’ullar da ita ne, sannan yabi ta gefan ta ya shiga cikin d’akin, ajiye mata abincin yayi akan bedside drawer sannan ya juyo, tana tsaye a wurin da ya barta, idanunta kaf akanshi, yaga tsoro a cikin su,