ZAFIN SO COMPLETE HAUSA NOVEL
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tafiya muke nida Hanee ko waige bama yi, da abn yayI nisa ma har gudu muka koma yi duk dan muga mun tarar da wannan hamshaqiyar yarinyar, bamu muka tsaya ba sai bakun wani qayataccen gida wanda da ka ganshi gasan na wani mai muqami ne, a daidai vakin gate yarinyar ta tsaya da motarta qirar range rover ash colour, horn tayi amma shiru ba’a bud’e gate ba, sai bayan kamar minti biyu ta qara wani horn d’in amma shiru gate man bai bud’e gate d’in ba. A fusace ta fito daga mota ko jakarta bata d’auka ba ta bar motar bud’e ta shiga gidan. Koda shigarta ta samu gate man d’in kwance yana rawar sanyi alamar baida lafiya, bata ko duba yanayinshi ba ta d’aga hannunta ta wanke shi da mari, dafe kumatunshi yayi wani zazzafan hawaye na saukar mishi, kafin ya ankara ta qara d’auke shi da wani marin, sai a lokacin tace “kai uban waye da zanyi maka horn har sau biyu amma ka kasa bud’e min gate? Bayan kuma kasan bisa ga d’abi’ata horn daya kawai nakeyi ko sallah kake dole kabarta kazo ka bud’en gate in shigo gida, mtswww wawan banza!”.
Fita tayi bata koma takan motar ta dake waje ba, tayi tafiya mai nisa kafin ta isa inda farfajiyar gidansu take, shiga tayi kai tsaye babu ko sallamah. Ta samu momy kishingide ana mata matsar qafa, fad’awa tayi jikinta tana mayar da numfashi, a firgice momy ta miqe zaune tana fad’in “na shiga uku, auta me ya faru dake na ganki kamar ba’a hayyacinki ba?”. Kyakkyawar budurwar tace “momy wai waye ta kawo mana wancan wawan a gidan nan?”, momy tace “wa kenan?”, a shagwa’be tace “gate man d’in can mana”. Momy tace “ai! Wai baba faruku? Dady da kanshi ya kawo shi wai yana tausayinshi ne, me ya miki ne auta ta?”, “momy wai har sau uku ina horn amma yaqi bud’en gate, motar ma tana can na bari a waje har da key d’in yana jiki ban cire ba tsabar takaici”, miqewa tsaye momy tayi tace “auta! Baki da hankali ne? Baki gudun a sace ta ne? Kin san fa jiya aka kawo ta, waccan d’ayar ma ajiyeta kikayi fa aka sace miki a gidan biki”. Kamar tana jira momy ta gama maganar aikuwa ta fashe da kuka tana fad’in “momy! Yau nice kike yiwa fad’a har da nuna min yatsa? Momy tunda nake baki ta’ba yi min haka ba, a dalilin wancan wawan tsohon gate man d’in? Tou barin je inda yake, wlh sai yabar gidan nan, ko uban wa ya tsaya mashi”.
Fita tayi ko dan kwali babu a kanta, bata ko nemi takalmi ba ta kama hanyar d’akin me gadi, ta same shi still yana rawar sanyi wadda tafi yanda tabarshi d’azu. Bara jira komai ba ta fad’a d’akinshi, finciko shi tayi ta jefar waje, ta duba bakin katifar shi taga wata qaramar Ghana most go, dauko ta tayi ta jefa mashi a daidai isowar momy wurin, fitowa tayi daga dakin tace “a dalilinka momy na tayi man fad’a harda nuna ni da yatsa tayi, wlh yau sai kabar gidan nan, tsohon banza zaka nemi takurawa rayuwata, sai ka koma qauye aci gaba da cin tuwon dawa ai, mtsww” taja tsaki tare da barin wurin.
Abn haushi wai momy ta kasa ce mata komai, har tayi nisa da qyar tsohon nan me gadi yace “SAFNA!!! Ni kika wulaqanta haka? Ni kike kira da tsohon banza? Ko da yake banga laifinki ba, laifina ne da na qasqantar da kaina nake bauta a gidanku, hmmm!! Neman halak kenan, insha Allahu yanda na nema gareku kina wulaqanta ni bayan kuma nayi jika dake, ina roqon Allah ya kawo ranar da kema zaki nema a wuri na….” ya qarasa maganar cikin kuka da ban tausayi.
Da sauri ta dawo wurinshi ta sake wanke shi da mari tace “ba amin ba tsohon NAJADU!! Allah ya fika, kuma ni bazan ta’ba nema a wurinka ba, babana yana da kud’in da ko bayan ranshi zanci har in kyautar wa mabarata irinka” ta tofar da yawu qasa tace “tir! Da MUMMUNAN FURUCINKA”.
Barin wurin tayi da gudu saboda qunar da zuciyarta ke mata. Momy bata ce komai ba sai bin bayan ‘yarta da tayi tabar me gadi nata goge hawaye. Bayan kamar minti biyu yaja Ghana most go d’inshi ya fita. A hankali yake tafiya dan yana tsananin jin zazza’bi.
Da qyar ya samu yaje tasha ya hau motar qauyensu BAGARUWA, d’an chanjinshi ya biya kud’in mota ya isa. Ya samu Nawwaf na zaune qofar gida ya buga tagumi, koda yaga babanshi tuni ya tashi ya nufI wurinshi ya kar’bi jakar suka qarasa ciki yana mashi sannu da zuwa.
Da shigar shi gida bai jira komai ba ya kwanta kan wata tabarma dake shimfide a bakin qofar d’aki, NAWWAF dai sai bin babanshi yake da kallo ganinshi da yayi sukuku, “Abba sannu da zuwa”, ya ansa da “yauwa NAWWAF, ina umman taka?”,,,,,” tana daga ciki ina jin, Ummah!”, “ga ni nan, zuwa fa, aahhh lale marhaba da mutan birni, sannu da hanya” ummah ta fada tare da fitowa daga daki.
Wasu irin zafafan hawaye suka fara ambaliya a fuskar Abbah, duk hankalunsu ya tashi ganin abbah na kuka, a rude NAWWAF yace “abba wai me ya faru ne? Tunda kazo naga kana da damuwa a zuciyarka, ka fada mn matsalarka wlh na dauki alqawari indai ina da maganinta”.
Ummah tace “malan meke faruwa da kai, kuka fa kakeyi, tunda nake dakai ban taba ji ko ganin kayi kuka ba, amma da mamaki sai gashi yau kana yi har idonka yayi jaa”.
Sun d’auki tsawon lokaci shiru basu samu ansa daga Abbah ba, jin bashi da niyar basu ansa ne yasa Ummah tayi qarfin halin cewa “ka watsa ruwa malan ka kwaso rana sai kaci abinci”. Baice mata komai ba ya miqe jikinshi na rawa ya nufi toilet. Da gamawarshi ya fito, abinci kawai yaci ya kwanta bacci yayi gaba dashi.
NAWWAF duk abn duniya yabi ya dame shi, sai zaman tagumi yake har abba ya farka yaga Ummah zaune kusa dashi tana hawaye, ga NAWWAF ma zaune a gefen Ummah, ganin su cikin wannan halin yasa shi cewa “kuyi haquri, bana son na fada maku abnda zai saku bacin rai ne shi yasa naqi fada maku, amma tunda kuna son ji yanzu zan fada”,,,,,,,,,,nan ya hau basu labarin duk abnda ya faru tun farko har qarshe.
Zumbur NAWWAF ya miqe tsaye yace “Abbah ka bar naje Katsina na samu jakar yarinyar nan, wlh sai naci mutuncin ta kamar yanda taci naka mutuncin, kawai qaramar yarinya ta kiraka da tsohon banza, munafuki, Subhanallah! Abbah yau yau din nan zan tafi”. Bai jira komai ba ya tafi dakinshi da nufin canza dressing.
Tsawa daya abbah ya mashi dole ya tsaya, abba yace “na saka ne? Wau kai NAWWAF yaushe zaka rage wannan ZAFIN zuciyar taka ne? Ya kamata fa kasan ka girma, kuma nace kabarta da duniya, duniya zata bida ta, ai laifi na ne da naje gidansu da aiki, kaga inda ace banje ba ai da bazata ci min mutunci ba, amma yanxu da nabar gidan ba shikenan ba? Sai kuma tayiwa wani ai”.
Ummah tace “hakane malan, tou amma yanxu idan ka dawo gida ka zauna ya zamuyi da abincin da zamuci? Shi NAWWAF bai iya ko wace sana’a ba, shidai karatun boko kawai ya tasa a gaba, ni fa yanxu kusan shekarar shi biyu kenan da gama degree dinshi, har service ya gama amma babu wani aikinyi kullun sai zaman qofar gida yake, sai matacciyar zuciya kawai”.
NAWWAF da hawaye ya wankeea fuska yace “Ummah indai hakane zan nemi kudi insha Allahu, neman kudi kuma ta tsaftatacciyar hanya, zan nemi halal insha Allahu ko ta hanya mafi wahala ne”.
Koda sukaje kuwa sun samu Mal. Shazali anyi layi a gidanshi kowa da abnda ya kawo shi, Hamza yace “sai kabi bayan wannan na qarshen”,
Nawwaf yace “yanzu wannan uban layin duk sai na bishi?”,
Hamza yace “qwarai kuwa sai ka bishi, da haka kowa ya fara har aka kaiga na farko, yanxu za’azo kanka ai tunda naga duk masu bada balance ne”,
Nawwaf yace “tou”.
Layin yaita bi har akazo kanshi, mal. Shazalin da kanshi ya bashi kurar amma fa yasha gargadi kafin a bashi, da alqawarin zai ringa kai balance kullun yabar wurin cikin farin ciki da zumud’I, harda jarkokin aka bashi yaja suka kama hanyar gidan hayar da hamza yakeda daki a ciki.
TUSHEN LABARI.
Alhaji Marwan d’ane ga malan Sani mai gilashi, ya taso cikin tsananin talaucin iyaye, tun yana dan shekara biyar aka sakashi makarantar primary, daqyar da wahala suke samun kudin breakfast ma dan su kansu wanda zasuci wahala yake basu, mal. Sani kuwa baida wata sana’a kullun yana zaune a gida, baki daya xuciyarshi ta mutu, baya da wani burin tashi ya nemi na kanshi, Rabi itace matarshi, mata mai kokarin neman na kanta, kullun naseeharta daya ce wadda bata wuce mal. Sani ya nemi halak ba, amma sam baya daukar maganarta, wani lokaci ma sai yace wai gori take mashi dan taga itace ke ciyar dasu, har kuka takeyi idan ya fada mata haka.
Bayan shekara biyu a lokacin Marwan yana da shekaru bakwai a duniya kwatsam Rabi ta samu juna biyu, tayi godiya ga Allah amma sam abn bayyi mata dadi ba, saboda abincin da zasuci ma wahala yake masu, tun suna su uku kenan ina ga sun qara yawa, mal. Sani yaji dadi sosai data sanar dashi tana dauke da juna biyu,
Bayan kamar kwana uku da sanar dashi da tayi tace “mal. Kaga dai yanxu ina da ciki wata uku ya kamata ka fara qoqarin neman na kanka tun kafin lokacin yayi kuma aita daddafe daddafe a rasa yanda za’ayi”,
Mal. Sani yace “sata kike so nayi ko yaya? Ko kuma ke zaki bani jarin?”,
A zuciye Rabi tace “nifa malan ba haka nake nufi ba, me zaisa nace kayi sata? Amma kuma ai akwai hanyoyin neman kudi da dama wanda akeyi, kai kenan kullun kwanxe a gida, ni kwance kaima kwance babu mai tada wani”,
Yace “kyayi kya gama Rabi, ni banda Inda zanje idan kin matsu ki fita kiyi dako”, yaja tsaki ya shiga dakinshi.
Haka Rabi taita jan cikinta cikin rashin kulawa har yakai wata bakwai, alokacin ne ta yanke shawarar tsaida duk wani aiki da takeyi kamar; dakau, wanki da guga na kudi da sauransu. Bayan cikinta ya cika wata tara Ta samu da qyar da wahala ta tattar dubu sha daya harda tsohuwar ajiya, taba mal. Sani tace “mal. Ga wannan, a siyo ko qaramar tunkiyace wadda za’ayi yanka, idan kudin sun samu chanji sai a yo mana cefane. Ni kuma akwai dubu biyu hannu na sai in siyo kayan jinjiri dasu”,
Mal. Sani da murmushi yace “yauwa uwar gida, wlh kina burgeni, zuciyar maza ne dake”, bata bashi amsar komai ba da qyar ta shiga makotansu gurin A’I me kayan koli, irin kayan nan masu hangan roba ta siya wasu na mata wasu na maza ta hada kala takwas dasu sannan ta koma gida.
Ta samu mal. Sani bayanan a tunanin ta ya tafi siyo tunkiya dan ta fada mashi ta fara jin naquda. Bayan kamar minti arba’in mal. Sani yazo yana kuka,
“Me ya faru ne malan?”
Yana goge hawayen yace “dama na siyo tunkiyar ne na hadu da wasu mugaye a hanya suka qwace suka min duka a hanya”, ido bude Rabi tace “tunkiyar? INNA LILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI’UUN” ji kake tiiiiii ta fadi qasa, hankalinshi bai ko wurin yaci gaba da “kuma fa uwar gida da sauqi aka samu tunkiyar, naira dubu tara aka bar min ita, baki ga girmanta ba qatuwa da ita”,
Jin shiru ba amsa ne yasa shi cire hannunshi daga Ido da yake murzar qwallan qarya, ganin jini nata malala daga jikin Rabi yasa shi fasa ihu a daidai shigowar Marwan,
“Abba me ya samu mamana? Jifa jini na fita, mama ki tashi dan Allah”, kuka yake sosai abn tausayi yace “abba kaine ka duki mama ko?”,
Mal. Sani yace “wlh ban duketa ba Marwan”,
“Ka duke ta mana Abbah! Ga jini na fita, ai idan ba’a duki mutun ba jini baya fita”,
Bai kuma bashi ansa ba ya samu ya ciccibi Rabi ya saka a baro ya kama hannun marwan da hannu daya, dayan kuma yana tura baron.
Basu zarce ko ina ba sai qaramar asibitin dake cikin qaramar hukumar Kaita, da hanzari aka kar6eta domin ceto rayuwarta, sun dauki kimanin awa biyar akanta,
Wata nurs ce ta fito tace “wa keda Rabi’atu Sani?”,
Da sauri mal. Sani yace “ni nazo da Ita, ina fatan ta sauka lafiya”,
Saida ta jinjina kai sannan tace “ina son ka sani da rayuwa da mutuwa duka a hannun Allah suke, ka dauka dama rai arone aka bamu kuma a ko wane lokaci wanda ya ara mana zai iya zuwa karvar abnshi, Allah baya barin wani dan…..” bata gama fadi ba sakamakon tsawa da mal. Sani ya daka mata yace “me kike nufi? Kina nufin matata ta mutu ko kuwa danda ta haifa? Karki mayar dani sha3 mana”,
Qaramin likitan ya fito duk yayi xufa yace “malan daga fadan gaskiya sai ka mata wannan tsawar? Matarka ta samu zubar jinu sosai tare da mummnar faduwar gaba kafin ta fara naquda, babu wanda ya isa ya qetare lokacin da allah ya tsara mashi. Matarka ta rasu munyi iya qoqarin mu dan ganin mun ceto rayuwarta amma da yake iyakar rayuwar kenan bamu iyaba, kayi haquri amma an ceto jinjirin namiji ne kuma lafiyayye”,
Wata irin nadama tazowa mal. Sani, kuka yake sosai ya shiga dakin ya rungume gawar matarshi yana fadin “ki yafe mn Rabi’atu, na soki sobda bazan taba iya yiwa wata mata shiba, nine na kashe ki Rabi’atu kuma a shirye nake da kai kaina ga hukuma tun kafin naje ga bbar hukuma”, ya miqe tsaye yace “yalla6ai ku kira ‘yan sanda su tafi danI a yanke min hukuncin kisa, wlh nune na kashe ta, likita bani da wata sauran rayuwa data rage min a doron qasa, don allah ka kaini a yanke minhukuncin kisa”.
Babu musu kuwa likita ya kira ‘yan sanda tare da shaida masu duk abnda mal. Sani ya fada da bakinshi, su kuma basuyi wani bincike ba kawai suka tura kotu, jin gamsasshiyar hujja daga bakin mal. Sani yasa aka yanke mashi hukuncin daurin rai da rai babu wani bincike, basu tambayeshi ta wace hanya yabi ya kashe matarshi ba kawai aka tafi dashi prison.
Marwan kuwa yana zaune ya hada kai da guiwa yana tunanin hakun daya tarar da mamanshi ciki har zuwa asibiti da sukayi tare, duk baisan an tafi da babanshi ba, gajiya da yayi ga kuma yunwa yasa ya miqe tsaye yana ta kuka yana kiran “Abbah! Abbah” amma shiru, sosai yaqara fashewa da wani kukan.
Dr. Nasir na bakin gawar Rabi ya rasa ya da zayyi da Ita, a hankali yake jiyo kukan Marwan, da sauri ya fita dan ganin wanda yake kuka, ganin Marwan yayi har ya galabaita, likita yace “yaro me ya faru kake kuka?”,
Marwan yace “babana nake nema, kima gashi mamana bata da lafia, can naga an shiga da ita har yanxu bata fito ba”, jin hakan ya tabbatar wa Dr. Nasir cewa marwan dan mutumin nan ne, jan hannunshi yayi cikin tausayi ya kaishi gaban gawar mamanshin.
Cikin natsuwa Dr. Nasir ke magana yace “ya sunanka?”,
“Sunana marwan”,
“Gud, Marwan an saka a islamiyya kuwa?”,
“Ehh an saka ni harda tahfiz ma inayi”,
“Yauwa Marwan, an taba baku labari akan mutuwa?”,
“Ehh ana fada mana, kuma har malamin mu yace duk kan mai rai sai ya dandani mutuwa, kuma komai sonka da mutun Allah bazai barshi dankai ba, komai girma komai qarantar mutun idan lokacinshi yayi sai ya mutu”,
Sosai maganar marwan ta ratsa dr. Nasir. Cikin mamaki yace “marwan shekarunka nawa?”,
“Am 8years old”,
Da dabara yace “tou marwan indai ka tabbatar da cewa Allah shine yake bayarwa kuma yake qwacewa ka fada mn”,
“Ehh na yarda”,
“Yanxu idan ka arawa wani pencil dinka na makaranta zaka koma ka karbi abnka?”
“Ehh zan koma”
“Tou Marwan, Allahn daya raya mamanka ya bata aron rai tou yau ya karbi abarsa, ina so kayi mata addu’ah ka fawwalawa Allah komai dan daman shine ya ara mata”,
Marwan yace “tou unle na yarda kuma Allah yani kan mamana”,
“Ameen” dr. Yace. Tare da miqawa marwan jinjirin data haifa.
Ya karba yana ta kallonshi yaro mai kyau mai irin fuskar mamansu, saI daya kalli jinjirin yaji wani irin kuka mara control yaxo mashi tausayin qaninshi na matuqar addabarshi, bayan ya gama kukan ne yace “uncle ina babana?”,
Bai boye masa komai ba ya fada mashi, wani irin haushi yaji gashi bai san kowa a danginsu ba.
A babbar masallaci dr. Nasir ya sanar da mutuwar Rabi, anan aka dauko gawarta aka kawo, ta samu masallata sosaI tare da yan rakiya, aka kaita kushewarta.
Dr. Nasir kuma yayi alqawarin daukar su marwan tare da riqesu tsakaninshi da Allah. Yayiwa jinjirin huduba da sunan babanshi “SANI”.
Haka sukaci gaba da rayuwa gidan Dr. Nasir, baya nuna masu komai face tsantsar soyayya, matarshI Saude kuwa ta tsane su, kullun sai tsana da tsangwama, Sani da ake bawa madara bata kula dashi sai dai me aikinta Zulai ce ke bashi madara aduk lokacin daya dace, Marwan kuwa kullun da kalar azabar da take gana mashi, danta Shahid ma har dukan marwan yakeyi idan babanshi baya nan.
Kwatsam wata rana Dr. Nasir baya nan Saude ta aiki Marwan da kudi yaje shago, a hanyarshi ta zuwa ne ya yarda kudin, ya neme su ya rasa, yaita kuka dan yana tsabar tsoron masifar Saude.
Kawai ya yanke shawarar yaqi komawa gidan, haka yaita tafiya bai san inda zaije ba. Tun daga nan nima na tafi na barshi dan karmu 6ata tare, har iwa yanxu ban san inda Marwan yake ba.
A 6angaren gidan su kuwa jin Marwan shuru bai dawo ba yasa Saude tace danta Shahid ya tafi ya nemoshi, yaita nema amma bai ganshi ba ya dawo gida. Tuni Saude ta tsure dan bata san abnda zatace wa mijinta ba. Har bayan isha Babu Marwan babu alamanshi, Zulai tafi kowa rudewa saboda tana son marwan amma gashi uwar gijiyanta ta kasa daukar wani mataki akan 6atan yaron.
Dr. Nasir ne ya dawo shahid ya fara bashi labari, yace “dady mamy ce ta aiki Marwan shine har yanxu bai dawo ba”,
Cikin kidima Dr. Nasir yace “Marwan din? INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN”, da sauri ya qarasa cikin gidan yana kwalawa Saude kira.
“Ina kika aiki Marwan da har yanxu bai dawo ba? Saude tun yaushe na hanaki aiken Marwan? Idan gaskiya ne me yasa bakya aiken Shahid tunda yama girmi Marwan?”,
Da in ina Saude ta kasa bashi ansa, “d d…dm..ma..naa ras…”
“Yi mn shiru Saude! Tunda abn naki hakane zan nemo wanda zata ci gaba da kula mn da Sani, Zulai ta ringa taimaka mata, na kula ke kam bazaki iyaba, ina nufin zan qaro aure dan Sani kawai”,
Da sauri ta zabura tace “aure alhj.?! Aure fa kace? Saboda wannan shegen yaron da baida asali zaka qara aure?”
” Ke kikaga shegun yara Saude, nikam ban hada kowa dasu ba, na daukarwa kaina alqawari a idanuwan mutane a cikin babban masallaci tun kafin a dauki gawar mamansu, kina so inci alqawarin ne? Tou ni ban iya wannan ba, da hankalI na da komai bazaki sani jin kunya a idanuwan mutane ba, kuma yanxu zan fita neman Marwan, matuqar ban ganshi ba tou kema sai kin kwana a seil”,
Sosai Saude ke kuka tana fadin “wato alhj. Ni kake so ka tozarta ko?” Taci gaba da kuka ko kulata Dr. Nasir bayyi ba ya nufi bakin motarshi.
Tunda ya fita yake neman Marwan lungu da saqo amma babu ko alamunshi, har saida ya jigatu sannan ya nufi police station, harda hotonshi ya gwada masu (wanda ya dauke shi a waya yana riqe da Sani), ya basu wadatattin kudi sannan ya tafi gida daka ganshi zaka gane yana cikin damuwa mara adadi.
Ya shiga gida kanshi a dafe bai kula kowa ba sai zulai daya gani yace “ina Sanin yake? Ko shima an barshi ya tafi?”,
Cikin tsoro tace “yana daki yallabai, na gama bashi madara ne yayi bacci”,
Bai gama jinta ba ya isa dakinta, ya samu shi cikin net dinshi kwance yana bacci, a hankali ya bude gidan sauron ya sumbaci Sani a goshi tare da fadin “insha Allahu zan riqeka fiye da yanda iyayenka zasu riqeka, zanyi bakin kokari na ganin ka samu farin ciki har qarshen rayuwarka, dan uwanka daya 6ata ma insha Allahu zan bada kudi ko nawa ne indai za’a ganoshi”,
Rifewa yayi yana share ‘yar kwallar data fito mashi yabar dakin.
‘Dakin shi ya shiga baiko bi ta dakin Saude ba, wai shi a nufin shi yana gwadata ne yaga ko zata shiga dakinshi ta tambayeshi labarin Marwan saboda taga sanda ya shigo amma ta koma dakinta wai ita a dole mai kishi, shiru shiru bata fitoba har bacci ya daukeshi. Qarfe ukun dare ya farka da tunanin rashin ganin Marwan, tashi yayi ya dauro alwala, ya hau sallar da koshi bai san adadin wadda yayi ba, ya hau adduah “yaa Allah ka bayyana mana wannan yaron, idan kuma 6atanshi alkhairi ne Allah ka kaishi wuri mafi alkhairi, Allah ka kareshi da kariyarka ya Allah” kuka yaci qarfinshi ya tsaya da addu’an.
Washe gari da sassafe baiko nufi aikiba saida ya fara zuwa gidan momma (mamanshi) ya gaishe ta tace “Nasiru ya kwanan yaran dasu saude?”,
“Lafiya ba lafiya ba momma”,
“Me ya faru?” Cikin kidima ta fadi haka tana mai son jin abnda ya faru,
“Momma marwan ne Saude ta barshi ya fita tin jiya bai dawo ba, har police station naje amma sam babu wani labari, sai daga baya Shahid yake bani labarin kalar azabtar dashi da sukeyi shida Saude”,
Miqewa momma tayi tace “na shiga uku! Marwan din?! Amma kuwa Saude bata kyauta ba, dama kalar riqon da takewa marayun Allah kenan? Tou shi kuma Sani ya maganarshi? Tana dai feeding dinshi yanda ya kamata ko?”,
Jin tambayoyin momma bazasu qare ba yasa a taqaice yace “Sani ma zulai me aiki ta barma shi wai ita ke kula dashi, tou ni a gani na kawai in qara aure ko zan samu mai kula dashi tunda ita bazata iya ba”,
“Shawara me kyau kenan Nasiru, dama akwai Maryam ‘yar qanwa ta, kamilalliyar yarinya ce mahaddaciyar Qur’ani, wannan shekarar ta gama makaranta, insha Allahu yau zan tinkari mahaifiyarta da maganar, kome kenan zan kiraka”,
“Tou momma nah, shiyasa bana gudun kI da duk shawarar dana ke nema, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”.
Cikin sati bayu aka gama maganar auren Dr. Nasir da Maryam. Ba’ayi wani abu ba sai walima.
Saude tasha kuka ita a dole mai kishi, ganin bata da yanda zatayi yasa ta dangana. Gida daban aka kai Maryam, saboda Dr. Nasir yasan baza su ta’ba zaman lafiya ba matu’kar ya had’e Saude masifaffiya da Maryam nitsatstsiyar yarinya.
Kwananta uku a gidan shi ya kar’bo Sani, sai da ya sai mashi komai sabo kafin ya kaishi, har da madarar da ake bashi mai kyau da tsada.
Sosai Maryam taji dad’in Sani, saboda ita dama can maI son yara ce, musamman Sani da Dr. Ya aure ta musamman saboda shi.
Kula sosai yake samu wurin Maryam, ko kukan shi bata son ji. Tsakanin ta da Saude kuwa ko ta kai mata ziyara bata ko kallon inda take, magana ma bata ansawa idan tayi mata. Sai harare harare. Da zarar Sani yayi rarrafe ya nufi inda take kamar taga kura take mashi. Ta kai da tsoron ta ma yake ji, ko gidan sukaje baya nufanta.
Marwan kam babu ko labarin shi, anyi nema har an gaji, Dr. Nasir yace ma Maryam “ni har ma na fawwakawa Allah komai, fata na dai Allah yasa yana lafiya a duk inda yake”,
Maryam tace “Ameen ya Allah”.
Kwance tashi babu wita wurin Allah har Sani ya shekara hud’u ya shiga makaranta, yana da haza’ka sosai dan duk class d’in su babu mai ‘ko’karin shi. Har Dr. Yana yawan mamakin Sani, bai ta’ba ganin yaro kamar shi mai sharp brain ba.
A haka har ya gama Secondary School, a lokacin Maryam nada yara uku duka mata, babbar itace Zarah, mai bi mata kuma Futha, sai autar ta Khairat. Duk a cikin yaran Sani yafi sha’kuwa da Futha, suna shiri sosai har idan bata ganshi ba bata jin dad’I. Kwatsam da gamawar shi gwamnati ta d’auki nauyin fitar dashi UK karatu. Futha tasha kuka kafin su rabu, sai da yaita bata baki kafin ta amince.
Sani bai dawi Nigeria ba sai da yayi Ph. D ya zama professional Doctor. Ranar da zai dawi Futha ta had’a mashi abubuwan jin dad’I, tayi gayu sosai na dawowar d’an uwanta.
A Airport suka d’auko shi ya ‘kara kyau sosai dan dama indai wurin kyau ne to baza’a barshi ba.
Wata d’aya da dawowar shi ya samu aiki a FEDERAL INLAND REVENUE branch d’in Katsina, Dr. Nasir yace “to Sani kaga dai ka samu aiki mai kyau, yanzu abunda ya rage maka kawai aure, bana so ka fara zuwa Office ba tare da aure ba, me kace?”.
Susar ‘keya ya fara sannan yace “Dady dama…..” sai kuma yayi shiru.
“Dama what? Talk Sani”,
“Dady ina son ka nema mun wadda zan aura, saboda banda budurwa” ya du’kar da kanshi cikin kunya.
Dad yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace “dama haka nake son yi, na dad’e dayi maka mata, kuma matar ma wadda kuka sha’ku sosai da ita”,
Kanshi ya d’ago yace “to Dad godiya nake, Allah yasa ta zama abokiyar zaman alkhairi”.
Dad yace “Ameen”.
Sani bai ko tsaya jin wacece za’a aura mashi ba, da mamaki ya tafi dan yasan a iya sanin shi babu wata mace wadda ya sha’ku da Ita, a iya sanin shi Futha ce kawai, to ai kuma Futha blood sister na ce. Ni kuma Amrah nace “ba wani blood sis, kaine dai kake tunanin haka amma ba haka bane” mudai je zuwa zaka san ko wacece zaka aura.
A ranar da Dad ya shaidawa Sani da Futha cewa zai had’a su aure ba ‘karamin mamaki sukayi ba, babu wanda ya iya tankawa a cikinsu, sun d’auki misalin awanni biyu a haka bayan Dad ya basu wuri ganun basu da niyyar magana yace “su same shi a d’akin shi idan sun tashi jin labari”. Tashi sukayi Sani na gaba Futha biye dashi kowa da kalar tunanin da yake.
Sun samu Dad yana karatun jarida, jin alamun su yasa ya ajiye yace “kun shirya kenan?”, kai kawai suka d’aga yace “kuje ku kira Khairat da momy’n ku, na riga da na kira Zarah tana kan hanya ma”.
Cikin ‘kan’kanin lokaci duka suka hallara har da Zarah dake da tsohon ciki. Cikin dattako ya fara da “naaan duk kan ku zakuyi mamaki abunda zai fito daga baki na, to ba abun mamaki bane kuma ya zama fole na fad’e shi, bana so wani ya bani wata fassara haka kuma bana so inji wata magana daga baya”, nan ya hau basu labari tun farko har ‘karshe, duk abunda ya faru sai daya fad’a har da labarin Malan Sani da akaiwa d’aurin rai da rai a gidan yari, da kuma Marwan daya ‘bata tun shekaru 29 da suka wuce. Sunsha koke koke, Sani ma yayi kuka tare da yin godiya ga Dr. Nasir saboda irin ri’kin da yayi mashi, bai ta’ba nuna bashi ya haife shi ba, baya nuna banbanci tsakanin shi da Shahid yaron daya haifa, har ma yafi nuna kulawa a gareshi saboda Shahid shaye shaye yake babu abunda baya sha, shi yasa ma baI wani damu dashi ba. Saude tayi masifar har ta gaji.
Cikin mako uku aka gama hidimar biki, Futha ta tare a katafaren gidan da Dad ya mallakawa Sani.
Rayuwar aure suke mai cike da soyayya da ‘kauna, da farko Futha ta kasa sakewa dashi, sai daga baya ta saki jikinta, sosai yake bata kulawa itama tana bashi duk wani ha’k’kin shi.
Wata uku da auren su ta fara laulayin ciki, tasha wahala sosai dan ko ‘kanshin gidan ta bata so, a dole Sani ya mayar da ita gida. Satin ta biyu ta warware ta koma gida. Zo kuga kula wurin Sani, ko tsinke baya so dmta d’auke, hutu ma ya d’auko a wurin aiki musamman dan ya baiwa matar shi kula. Ga arzi’kinshi kullun ‘kara ha’baka yake, business yake sosai duk fad’in Nigeria babu wanda bai san SS ba, idan ma baka san shi ha to zaka san sunan shi, babu inda baya da branch a Nigeria, tun daga saida motoci, plaza, gidajen mai da sauransu. Gashi da taimakon al’ummah, babu wanda baya alfahari da SS sai dai wanda bai san shi ba.
Bayan wata bakwai cif Futha ta haifi kyakkyawar yarinya son kowa ‘kin wanda ya rasa. Dad da Mom kuwa ba ‘karamin dad’I suka ji ba, saboda Zarah bata haihuwa, shekarar ta uku kenan da aure amma shiru ko ‘batan wata bata yi ba. Tun a asibiti Dad yace “idan zaka bani dama zanyi wa yarinyar hud’uba”, Sani yace “na baka dama Dad”.
Dad yayi mata hud’uba da RABI’ATU, bayan ya gama ya fito yace “na mata hud’uba da sunan mahaifiyarka marigayi ya, sai a ringa kiranta da BABY”. Sosai Sani yaji dad’I. A ranar aka sallame su daga asibiti.
Shekarar Baby uku aka ‘kara yi mata ‘kanwa, anan Dad ya bash izinin yayi mata hud’uba da duk sunan da yake so, shine yayi mata da SAFNA.
Some years later.
Baby ce ta tafi Bangladesh karatu, Safna kuma wannan shekarar ce ta kammala Secondary School. Akwai banbancin hali sosai tsakanin Baby da Safna, domin kuwa Safna bata ragama kowa, komai tsufan mutun sai ta zage shi, tana amfani da damar data samu ta dukiya take wula’kanta duk na ‘kasa da ita, Baby kuma tsakanin ta da mutane sai giramamawa, Safna ta samu goyon baya ne daga mamanta, dan kuwa bata son laifinta ko kad’an.
CI GABAN LABARI…
Haka Nawwaf ya kasance kullun yana sayar da ruwan shi kuma yana samun nasarah. Sai dai baya rabuwa da takardun shi Na degree. Sosai malan Shazali yana jin dad’in huld’a da Nawwaf saboda yana bakin ‘ko’karin shi Na ganin ya cika al’kawarin kawo balance d’in shi na kullun. Tuni ya kama nashi d’akin a gidan da Hamza yake haya, babu Wanda baya jin dad’in shi a gidan.
A ‘bangaren Safna kuwa tun ranar data kori baba tsoho take faman mafarkin Wanda bata bata San shi ba, da zarar ta kwanta bacci ya d’auke ta sai tayi mafarkin saurayin. Koda kuwa baccin rana ne. Abun ba ‘karamin damun ta yake ba amma ta kasa fad’awa kowa damuwarta. Sai dai kuma duk ta rasa kuzarin ta, ko makaranta take bata da aiki sai tunanin mutumin da data san asalin shi ba.
Mom CE kwance tana tuna irin wula’kancin da Safna tayi wa baba tsoho, saboda tun da abun ya faru hankalin ta bai kwanta ba. Idan tana tuna irin furucin da yayi wa Safna har hawaye take yi.
Kwatsam Mom tazo gittawa ta gaban d’akin Safna taji ta sama sama tana kuka, a hankali ta matsa bakin ‘kofar taci gaba da sauraren ta, bata dai shiga ciki ba sai jin ta tayi tana fad’in “I love youh ! Me yasa ka kasa bayyana min kanka? Me yasa kullun kake zo min a mafarki? Bayan kasan Na kamu da ‘kaunar ka, I can’t live without you, pls ka bayyana min kanka”.
Sosai hankalin Mom ya tashi da jin furucin da Safna keyi. Kasa shiga d’akin tayi sai ta nufi nata tana taya ‘yar ba’kin cikin soyayya da d’an mafarki.
Alhaji Sani ne tafe cikin motar shi yana driving cikin natsuwa, a hankali motar ke shirin tsayawa har ta tsaya da kanta, sosai ya firgita Dan bai San yanda zayyi ba kuma gashi babu masu gyara a wurin. Fitowa yayi daga motar ya bud’e gabanta yana tunanin yanda zayyi.
Nawwaf ya taho yana turin baron shi data ciko da ruwa. Ganin mutun tsaye alamar yana Neman taimaki ne yasa shi matsawa inda mutumin yake yana fad’in “Alhaji lafiya kuwa?”
“Wallahi kuwa kaga ina cikin tafiya he ja fara jin tana tsayawa ban san dalili ba har said da ta tsaya”,
Cikin tausayi yace ” Allah sarki! Barin duba duk da ba wai na iya gyaran bane”
“To Bismillah” Alhaji Sani ya fad’a fuskar shi d’auke da murmushi.
‘Dago kanshi yayi yace “Alhaji ai babu ma ruwa a cikin motar nan, kaga” yayi mashi nuni da ya duba ya gani.
“Kana da gaskiya kuwa, Ashe babu ruwa a ciki, kuma fa wallahi har sai da na cewa Sanusi ya zuba mun ruwa wata ‘kila ya manta ne, shi yasa ma banyi tunanin rashin ruwa bane”.
Nawwaf ya d’auko jarka d’aya a baron shi yayi amfani da marfin jarkar har ya cika wurin ruwan.
Sosai Alhaji Sani yaji dad’I, ya kalli Nawwaf cikin jin dad’I yace “ya ma kace min sunanka?”,
“Sunana Nawwaf” ya bashi ansa,
“Malan Nawwaf ha’ki’ka naji dad’in yanda ka taimake ni, kuma bani da abun biyanka sai dai inyi maka addu’ah, Allah ya saka maka da alkhairi, ga wannan card d’ina ne” ya mi’ka mashi card d’in shi wanda yake d’auke da address d’in gidan shi dana office, sai kuma phone number da occupation d’in shi.
Nawwaf ya kar’ba yace “Alhaji wannan fa?”,
“Ka neme ni dan Allah, saboda yanzu zan bar garin ne zuwa Kano yasa bazan tafi da kai ba, amma wannan katin nawa sai ka neme ni insha Allah zan samar maka aiki ko da messenger ne na office d’ina, amma sam wannan aikin bai kamace ka ba”,
Nawwaf yayi saurin katse shi da “Alhaji ni fa dan Allah nayi maka ba wai dan ka biya ba, kayi ha’kuri ka kar’bi katin ka”,
Alhaji Sani yace “kayi ha’kuri ka kar’ba malan Nawwaf, nima ba wai ina son biyanka bane, kawai dai kayi min hallaci ne shine nima nake son saka maka da shi”.
Da ‘kyar ya shawo kan Nawwaf ya yarda zai same shi a office ba gida ba. Nan suka rabu cikin farin ciki kamar dama sun san junan su. (Nima marubuciyar sai da suka bani mamaki, ta yanda naga suna yi ma junan su, ko da akwai wata dangantakar oho).
Da komawar Nawwaf gida kuwa ya bama Hamza labarin duk yanda sukayi da Alhaji Sani,
Hamza yace “amma kai banza ne Nawwaf, ai inda ka mayar da katin nan da kayi wa kanka, wai ma ban in ‘kara gani”. Kar’ba yayi ya ‘kara ganin occupation d’in shi sannan yace “kaga fa VICE CHANCELLOR ne na UMYUK, Nawwaf kai da ke neman aiki ka sani ma ko ya nema maka? Degree ne fa gare ka, kuma yanzu naji ance har masu degree d’in ana d’aukan su lecturing sai daga baya su ‘karo karatu, ai yanzu yanda za’ayi kawai ka shirya gobe mu tafi dan ban sani ba ko nima in samu ko da labourer ne”,
Nawwaf cikin murna yace “ka ga kuwa hakane, inda na biye ma wannan mugun halin nawa shike nan da nayi wa kaina santacciya, kuma nifa ban ma karanta komai na katin ba sai yanzu, ai shikenan kawai sai mu tafi, amma gaskiya gobe ina son zuwa ‘Kauyen mu kuma kwana biyu zuwa uku nake son yi, insha Allahu idan na dawo sai muje”,
“Tou Allah ya kaimu, kai wannan halin naka na zurfin ciki bai da wani amfani, wai ace ina tare da kai har zakayi tafiya amma bazaka fad’a mun ba sai da labari ya kawo labari, kuma kasan dole akwai sa’kon da zan bayar akai ma su Baba”,
Cikin halin ko in kula Nawwaf yace “tou naji ni dai tashi ka raka ni in kaima oga balance, har da baron ma zan kai dan kar in aje a sace ta ko kuma yayi tunanin zan kai mashi balance gobe”,
Hamza ya mi’ke yace “nikam a shirye nake, kaine uban tsafta da zakace dole sai kayi wani wankan”,
“Haba Hamza yanda ake yin ranar nan mai ZAFI ai dole sai da wanka sau uku a rana”,
Hamza yace “nikam wallahi bazan iya ba, wannan sai kai Allah ya d’aura mawa”.
Da wannan suka tashi suka nufi hanyar gidan malan Shazali, a hanya suke fira Hamza yace “nikam Nawwaf ina mamakin yanda mutumin nan yake sakar maka fuska, kaga fa yanda yake da kowa babu mutunci ba fara’a, amma kai har yafe maka kud’I yake yi, gaskiya nikam ina mamaki”,
Nawwaf yace “ba kai kad’ai kake mamaki ba, dan wallahi har ni idan na zauna da kaina na mamakin hakan, a dalili na fa kaima har yafe maka kud’I yake yi, kuma gashi kaine ya fara sani kafin ni, hasali ma kai ka kawo ni wurin shi”,
Hamza yace “kai share kawai, had’uwar jini ne”,
“Hakane kuma” Nawwaf ya fad’a tare da yin sallamah a ‘kofar gidan malan Shazali.
Fitowa yayi fuskar nan murtuk, dama haka yake yiwa mutane idan aka zo nemanshi, koda ya had’a Ido da Nawwaf yaga shine nan da nan ya saki fuska yace “Ahh malan Nawwaf ne? Marhaban da kai”,
Har ‘kasa Nawwaf ya du’ka ya gaishe da shi, Hamza ma ya gaishe shi ya ansa masu da sakin fuska.
“Yalla’bai dama na kawo balance d’ina ne”,
Malan Shazali yace “a’a ka barshi na yafe maka Nawwaf”
Nawwaf yace “yalla’bai ai baza’ayi haka ba, ko jiya fa baka kar’ba ba”,
Babu yanda bayyi ba amma sam ya’ki kar’ba, daga ‘karshe dai ya ha’kura ya mayar da kud’in aljihun shi sannan yace “nagode yalla’bai, dama kuma ina so zanyi tafiya ne gobe zanje garin mu, tou shine naga ya kamata in mayar da baron dan kar in ajiye a d’uke ta”,
Malan Shazali yace “tou babu komai Nawwaf, ga wannan ka ‘kara kayi ku’in mota, wannan kuma kayi tsaraba dashi”.
Sam yace bazai kar’ba ba, amma malan Shazali ya tilasta mashi dole ya kar’ba yayi godiya suka bar wurin.
Washe gari sassafe ya shirya, yayi bankwana ya kama hanyar ‘kauyen su Bagaruwa.
Anyi murna sosai da ganin shi, mahaifin shi yashi Mata albarka da ganin guzurin da yayo masa, ya kuma tabbatar mashi da halaliyarsa yake nema. Babu wanda baiji dad’in ganin shi ba, kwanan shi uku ya koma Katsina cike da kewar barin gida da yayi.
Kwana biyu da komawar shi Katsina suka fara tunanin neman address d’in Office d’in Alhaji Sani, basu wani wahala ba suka gane address d’in, kasantuwar sananne ne babu wanda bai san UMARU MUSA YAR ADUWA UNIVERSITY ba, uwa uba kuma idan yace office d’in VC, kowa yasan shi, duk wanda ya fad’a ma yana neman Office d’in VC raina shi suke yi, wasu ma har dariya suke mashi, wasu kuma sai ya wuce suke fad’in “wai ji wancan wawan dashi, ‘kazami wai yake neman office d’in VC, barshi yaje a nasan securities ma baza su barshi ya wuce ba”. Kowa dai da kalar tsegumin shi har ya samu suka isa.
Note: Ayi ha’kuri da rashin jina kwana biyu, wallahi munyi fama da rashin wita ne, ga kuma Skul. Insha Allahu zakuci gaba da jina a koda yaushe.
A bakin office d’in suka had’u da securities mutun uku, nan suka hana su shiga yayi yayi amma suka ‘ki.
Da ‘kyar su ka bari ya shiga amma suka hana Hamza shiga. Sallamah yayi a ciki ma ya samu wani security, ya ansa sallamar tare da cewa “Bismillah malan”,
Shiga yayi ya samu Alhaji Sani na ‘yan rubuce rubuce bai d’ago kai ba, sai daya gama sannan ya mayar da kallon shi ga Nawwaf. Cikin jin dad’i yace “Ahh ashe Nawwaf ne, ina ta tunanin ka kuwa ashe kana kusa”,
“Wallahi kuwa yalla’bai, ya aiki?”,
“Lafiya ‘kalau, ya gida ya aiki?”,
“Alhamdulillah yalla’bai, dama nazo ne akan maganar da mukayi”,
Da murmushi yace “tou ba damuwa, messenger kake so ko labourer?”,
Nawwaf yayi ‘kasa da murya yace “yalla’bai ina da takardu anan, sai dai ban san ko za’a d’auke ni dasu ba”,
“Kawo su in gani”.
Kar’ba yayi ya fara dibawa a hankali tun daga na primary, origine, secondary certificate da sauransu har ya kai ga na degree. ‘Dago kanshi yayi ya kalli Nawwaf daya ‘kura mashi ido yana kallo yace “kaine NAWWAF SANI?”,
“Ehh nine” ya bashi ansa.
“Kana nufin dama harda degree gareka?” Ya washe baki yace “aikam zaka samu aiki mai kyau insha Allahu, ai ban san ma kana da karatu ba”.
Nawwaf yace “kusan shekara buyu kenan dana gama amma aiki ya gagara, shine kawai na yanke shawarar zuwa nan birni in kama sana’a saboda mahaifina baya aikin komai”.
Da sauri ya d’ago kai yace “baya aikin komai? Kana nufin zaune yake haka kawai?”,
“Ehh baya aikin komai, da yana aiki a nan garin sai aka wula’kanta shi, shine ya yanke shawarar ya bar aikin kawai ya koma gida”.
Cikin tausayi yace “Allah sarki! Ai mutanen ne na yanzu basu da wani kirki sai wula’kanci, da zarar suka ga sun samu d’aukaka sai su kama wula’kanta mutane, idan ka samu lokaci ko ba yanzu ba sai ka kawo shi idan yana so sai a bashi aiki ko ‘karami ne”.
“Tou insha Allahu zan kawo shi yalla’bai, mun gode ‘kwarai”.
Alhaji Sani yace “babu komai Nawwaf, haka kawai nakeji ka kwanta mn a rai, jinka nake tamkar jinin jiki nah, ka dawo nan da kwana uku kafin nan komai ya kankama”,
“Tou Allah ya kaimu yalla’bai”.
Har waje ya raka shi ya samu Hamza zaune yana kiran fitowar shi.
Alhaji yace “au ashe tare kake da wani?”,
“Ehh yalla’bai sun hana shi shiga ne”.
Sosai yayi ma securities d’in fad’a saboda shi ba halinshi bane wula’kanci. Yace ma Hamza “kaima kana da karatun ne?”,
“A’a ni daga primary na tsaya”,
“Tou kana son messenger ko labourer?”,
Da sauri ya sosa ‘keya yace “ehh ina so indai zan samu”.
Ya tambaye shi sunanshi ya fad’a mashi, ya kuma ce dashi su dawo tare da Nawwaf.
Haka suka tafi cikin jin dad’in samun nasarar da sukayi. Ta gidan Malan Shazali suka bi, suka gaishe shi cikun sakun fuska ya ansa, Nawwaf ya shaida mashi duk yanda sukayi da Alhaji Sani, ya taya shi murna sosai ya kuma ce idan zasu koma zaije dan yayi mashi godiya.
Bari mu koma ‘bangaren Safna mai Dream guy. Baki d’aya ta rasa sukunin ta, har Skul d’in ma ta daina zuwa sai fama take da ciwo duk tabi ta rame, tun abun baya damun Mom har ya fara damunta, ta samu Dad da maganar, har sabbatun da tajita tanayi sai data fad’a mashi, tare suka nufi tinkarar ta a d’akinta tana kwance.
“Yauwa Mom ‘kwara da kika shigo, Mom gashi nan kullun yana zo mun a mafarki, wallahi Mom ina ‘kaunarshi, bazan iya airen kowa ba sai shi, Dad ka taimaka ka nemo mun shi duk inda yake, indai da gaske kuna sona tou dole ku nemo mun shi saboda shine farin cikin rayuwata”.
Cikin tausayi Dad yace “Safna me kike fad’a ne wai? Waye shi a ina yake?”,
“Dad ban sanshi ba ban san inda yake ba, dan Allah ku nemo mun shi”,
“Ki kwantar da hankalinki Safna, kiyi min bayanin komai cikin natsuwa mana”,
Share hawaye tayi tace “Dad so d’aya kawai na ganshi a bakin wani layi, tunda na ganshi naji na kamu da sonshi, kullun idan na dawo Skul sai nabi ta hanyar amma bana ganinshi, shine kullun yake zo mun a mafarki, yana nufo inda nake, da zarar ya na nufo shi sai ya ‘bace, Dad kullun haka nake”.
Sosai suka tausaya ma ‘yar tasu, Mom ta matsa Inda take tace “kiyi ha’kuri kinji auta ta? Yau saura kwana biyar ‘yar uwarki ta dawo, ki kwantar da hankalinki insha Allahu idan ta dawo za’a san yanda za’ayi”.
Cikin shagwa’ba tace “tou Dad zaku nemo mun shi idan ta dawo?”,
“Insha Allahu kuwa” ya bata ansa tare da goge guntun hawayen daua rage a fuskarta.
Bayan kwana uku.
Shirye shiryen taryar Baby kawai sukeyi, hankalin Safna ya d’am kwanta saboda al’kawarin da Dad yayi mata. Sukam ma’aikatan gidan mu rna kawai sukeyi saboda sunji dad’in dawowar da Baby zatayi, dama kuma tunda Safna ta kamu da son Dream guy ta raga masu, sam babu ruwanta da kowa, hakan ba ‘karamin dad’I yayi masu ba.
Nawwaf da Hamza ne suka shirya suka nufi gidan Malan Shazali kamar yanda sukayi al’kawari. Sallamah sukayi ya fito dama ya shirya su kawai yake jira. Tafiya sukayi suka hau keke Napep har UMYU ta sauke su.
Office d’inshi suka direct amma suka samu baya nan, har sun jiya zasu tafi wani Labourer yace “kaine Nawwaf Sani?”,
“Ehh nine” Nawwaf ya bashi ansa.
Labourer’n yace “tou yalla’bai yace wai ince maku ku same shi a gida, wai kuyi amfani da wannan katin zaku gane address d’in” ya mi’ka mashi wani d’an card ‘karami.
Kar’ba sukayi suka samu wata napep d’in, kallo d’aya yayi wa card d’in yace “ai nama san gidan wannan, koba shi bane wannan mai kud’in? Wanda da yake aiki a Inland revenue daga baya ya samu d’aukaka?”,
Nawwaf yace “indai ka gane shi tou shine, bana son yawan magana”.
A daidai ‘kofar gidan mai napep d’in yayi parking. Alhaji Shazali da kanshi ya biya kud’in sannan suka nufi ‘kofar shiga gidan.
Direct suka shiga kasantuwar babu gate man tun tafiyar baba tsoho. Wani mai bama flowers ruwa suka gani Nawwaf yace “Dan Allah malan muna da tambaya”,
“Allah yasa na sani” ya fad’a yana ‘ko’karin matsowa inda suke.
“Nan ne gidan Alhaji Sani kuwa? Mun so tambaya tun a waje sai bamuga kowa ba har bakin ‘kofar”,
“Ehh ai nan ne, Alhaji mai son mutane kenan, mara wula’kanci, sai dai kuma baya nan wallahi yanzu suka fita su duka gidan wai zasu taro babbar ‘yar shi data dawo daga ‘kasar waje”,
Yana cikin maganar sai ga Mati driver yace “ko kune wanda yace zakuzo? NAWWAF ko?”,
Saurin d’aga kai Nawwaf yayi yace “ehh mune”,
Mati yace “tou yace in kaiku d’akin ba’ki idan kunzo wai bazasu dad’e ba”.
Bayan shi sukabi har cikin wani katafaren d’aki mai d’auke da kayan jin dad’I da more rayuwa.
Umurni yayi masu da su zauna kan wasu luntsumammun kujeru, zama sukayi suna ta f aman kalle kalle.
Bayan Mati ya bar d’akin ne Hamza yace “ohh! Masu kud’I suna jin dad’in su, kuga fa yanda d’akin nan yake dan’kare da abubuwan duniya, ga sanyi ta ko ina yana ratsa fata, ‘kanshi kuwa sai ratsa hanci na yake, wannan fa itace aljannar duniya”.
Nawwaf yace “kai fa Hamza matsalata da kai magana gareka wallahi, yanzu miye amfanin hakan? Idan fa maeu gidan suka shigo ko kana so su raina mu ne? Dan nifa bana son raini kuma kafi kowa sani”,
Malan Shazali yace “ayi ha’kuri dai”.
Wata budurwa ce tayi sallamah hannun ta d’auke da serving tray tana turawa, har ‘kasa ta du’ka ta gaishe su cikin ladabi sannan tace “ga wannan kuci kafin masu gidan su dawo”.
Godiya suka mata sannan ta tafi ta barsu. Food flasks d’in da aka zuba abincin kanshi abun kallo ne, cikin fasaha Nawwaf ya bud’e ya fara zuba yellow rice, d’ayan ya bud’e yaga vegetable soup da taji hanta da ‘koda, zuzzuba masu yayi sannan yace wa maoan Shazali “ga naka”, ya mi’kawa Hamza ma nashi sannan suka fara kwasar girki suna santi.
Bayan sun gama tass ya zuba masu exotic drink a glass cups ya basu, shi kuma ruwan faro ya zuba saboda baya son za’ki sosai.
Murna sosai tayi lokacin data hango ‘yar uwarta tna sauka daga jirgi. Da sauri tayi hugging d’in ta daidai isowarta wurin su. Cikin tausayi tace “Safna me ya same ki kika koma haka? Kinga yanda kikayi rama kuwa?”,
Kamar tana jiranta ta fashe da kuka ta rungume ta. Rarrashinta ta fara yi amma sam ta’ki yin shiru. Da ‘kyar ta tsagaita da kukan suka nufi inda Dad da Mum suke.
Sunji dad’in yanda suka ga ‘yar su ta ‘kara kyau abunta, dama kuma gata jar fata. Shiga motar sukayi suka kama hanyar gida.
Dad da kanshi ya sauka ya bud’e gate sannan ya dawo motar yace “wallahi ina haushin rashin gate man d’in nan, gashi kuma mutanen yanzu wuyar yarda gare su, tunda Safna ta korar mana da gate man shiknan. Na yarda da mutumin nan sosai ban ta’ba zama da wanda naji lokaci d’aya ya kwanta min ba kamar shi, kawai sai dai na dawo na tarar babu shi, dama kuma ban san garin su ba a masallaci kawai muka had’u dashi”.
Baby tace “Dad wai ashe har yanzu Safna bata daina wannan halin ba? Ai ni nasha ta girma ta daina”,
Dad yace “ina kuwa zata daina? Ai banga ranar ba”.
Safna ta fashe da kuka tace “Dad ai fa tunda Aunty Baby ta dawo nasan bazaka sake sona ba, indai tana gida haka muke da kai”. Kuka sosai t akeyi cikin si’kewar murya.
Mum tace “gaskiya ku ‘kyale mun ‘yata ta huta, bana son ana mata haka fa”.
Da wannan maganar suka ‘karasa cikin gidan fuskar Sagma duk hawaye ya bushe mata.
Duka ma’aikatan gidan suka fara du’kawa har ‘kasa suna gaishe da Baby, saboda sunfi sonta Miy da kowa dake gidan. Fuskarta d’auke da murmushi take ansa gaisuwar. Mati driver yace “yalla’bai bakin ka fa sunzo tun d’azu kai suke jira”,
Dad yace “ok ka shiga kace masu ina zuwa”.
Abinciccika kala kala suka tayar kan dinning Zarah ta jera. Sallah kawai sukayi sannan suka fara kwasar girkin Zarah. Dady yace “gaskiya ina alfahari da yarinyar nan Zarah indai wurin girki ne, duk irin ba’kin da zanyi bana haufin ta”.
Mum tayi saurin ‘bata fuska tace “tou ashe shi yasa nake barinka da ita tana dafa maka, tun da kai baka son girki na kullun sai dai na Zarah”.
Caraf Safna ta kar’ba tace “kema dai Mum tun yaushe nake ce maki ki bari in kori yarinyar amma kin ‘ki bari, indai baki barni na koreta ba har hawan jini sai ta saka miki”.
Baby tace “haba Safna! Wai ke yaushe zakiyi hankali ki daina wula’kanta mutane? Safna kiji tsoron Allah! Duk wanda zaki gani a duniya tou yana da tashi darajar, kuma mutun da kike gani ba abun wula’kantawa bane, idan kuma baki daina ba tou wallahi dole akwai ranar dana sani”.
Mum tace “Allah ya rabata da dana sani, insha Allahu bazata ta’ba yin dana sani ba a rayiwarta.
Murmushi Dad yayi yace “duk laifi na ne dana tado maganar ai, yanzu dai ba wannan ba, ina da ba’ki suna can suna jirana”.
Mum tace “su waye?”,
“Wannan mai saida ruwan dana baki labari mana, Nawwaf”,
“Au! Wanda kace ya taimake ka ko?”,
“Ehh shi fa, nayi masu al’kawarin zamu had’u a office ne yau, so kuma sai ga batun dawowar Rabi’atu, shine na bada sa’ko idan sunje ace su same ni a gida”.
Mum tace “ok”.
Tashi Dad yayi yace “idan na shiga sai kuzo ku gashe su kuma”. Bai tsaya jin amasar su ba ya tafi.
Sallamah yayi suka amsa yace “afwan fa ma barku”,
“Babu komai” Nawwaf ya fad’a. Sai a lokacin Dad ya kula da malan Shazali, wata irin fad’uwar gaba yaji, kawai ya samu kanshi da son mutumin da bai ta’ba gani ba sai yau.
Bayan sun gaisa su Mum suka shigo, itace gaba sai Baby da Safna bayanta. Wurin zama suka samu Baby ta gaishe su cikin girmamawa. Safna kuwa ko kallon arzi’ki baeu ishe taba. Sun d’auki kimanin minti biyar zuwa shida ta mi’ke tace “Mun na tafi sai kun shigo” fuskarta yatsine kamar mai tsohon ciki.
Har ta tafi kuma ta waigo, had’a idon da zatayi kawai taga dream man d’inta. Idonta ta murza sosai sannan cikin tsoro tace “bawan Allah kayi ha’kuri ka tafi, kullun gizon da kake mun kenan, ka hanani duk wani jin dad’in rayuwa ta” ta juya ta kalli Dad tace “Dad kayi min al’kawarin duk inda yake zaka gano min shi amma ka’ki, Dad wallahi bazan iya rayuwa ba tare dashi ba”.
Duka wurin kowa kallon ta yake yanda ta koma oamar mahaukaciya lokaci d’aya. Musamman ma Nawwaf da yaga tana nuni dashi alamar duk maganganun da take fad’I dashi take.
Mum tace “wai Safna meke damun ki ne? Waye dream man d’in naki?”,
“Mum gashi nan a zaune, wallahi mum shine kullun yake zo min a mafarki, son shi ya zame min ciwo wanda bazan iya maganin shiba matu’kar ban aure shi ba” ta fad’a cikin kuka da ‘karfi.
“Safna wannan shine kike mafarkin?” Mum ta fad’a.
“Ehh shine Mum, shikenan nasan ciwo na ya warke tun da gani gashi, ai zaka aure ni ko?” Safna ta fad’a tare da matsawa inda Nawwaf yake tana murmushi.
Kyakkyawan mari Mum ta wanka mata, cikin fushi tace “Safna kina da hankali kuwa? Yanzu ke wannan matsiyacin kike so? ‘Kas’ kantacce mai tallar ruwa a baro? Baro fa yake turawa da jarkoki manya a ciki, Safna ki kalle ki ki kalle shi, ai wallahi The different is clear, tou tun wuri ma gwamma ki fidda son shi a ranki, saboda kinfi ‘karfin wahalalle”.
Cikin tsawa Dad yace “ya isa haka, Hajiya bafa na son wula’kanci, dan me zaki ringa cima bawan Allah fuska a gaban shi?”,
“Ai kuwa cin fuska yanzu na fara matu’kar bai bar gidan nan ba, rufin asirin shi d’aya ne kawai ya tafi kar ya sake dawo wa, wama yasan ko asirce min ‘ya yayi? Idan ba haka ba mai zai sa yarinya ta haukace lokaci d’aya akan shi alhali bata san shi ba?”
Nawwaf yayi sairin katse ta da “ke Hajiya ki kama kanki, wallahi kawai ina d’aga miki ne saboda ina ganin kimar mijin ki, amma daba haka ba wallahi ba’ayi wanda zai yi min wannan furucin in ‘kyale shi ba, kuma da kike maganar ni wahalalle mai tallar ruwa a baro ai nan halaliyata nake, ni banga wahala anan ba, ki tambayi mijin ki kiji ai har sai da na’ki yarda da yace zai sama min aiki shi ya matsa lallai sai nazo, ki kama kanki wallahi nafi ‘karfin ki, Hamza ku tashi mu tafi”.
Baby tayi saurin tashi cikin kuka tace “dan Allah kayi ha’kuri bawan Allah, ni kaina banji dad’in yanda take gaya maka magana ba, amma banda magani ne yasa nayi shiru, and zan ro’ke ka wata alfarma ka taimaka kayi min ita”,
Nawwaf yace “mecece alfarmar?”,
Magana tayi mashi da koni maribuciyar banji me tace ba, kawai dai naga ya koma ya zauna yana ajiyar zuciya.
Safna tayi d’an guntun murmushi tace “zaka aure ni ko?”,
‘Kara murtuke fuska yayi bai bata ansa ba.
Dad yace “ya isa haka dan Allah, yanzu dai abunda nake so dakai Nawwaf ka saurare ni kaji me zan fad’a maka”,
Da ‘karfi Mum taja Safna a dole sai sun bar d’akin amma sam Safna ta’ki binta, dole ta tafi ta barta anan.
Dad yayi gyaran murya yace “Nawwaf da farko dai ina mai baka ha’kuri da cin fuskarka da Hajiya tayi, nasan nine naja maka da nace maka ku same ni a gida, inda a office muka had’u da duk haka bata faru ba, sannan kuma ina so ka d’auka abunda tayi maka can tsakanin ku ne bata shafe ni ba, ka d’auka komai bata faru ba kuma zan baka aiki kamar tanda nayi al’kawari”,
Murmushin ‘karfin hali yayi yace “babu komai yalla’bai komai ya wuce”.
‘Kara matsawa Safna tayi inda yake tace “tou zaka aure ni?”,
Da sauri Dad ya daka mata tsawa yace “ku tashi ku tafi ku bamu wuri”.
Baby taja ta suka nufi ‘kofar fita, juyowa safna tayi tace “dan Allah Dad kace kar ya tafi ya barni, wallahi ina cikin tsananin damuwa, nasan dan ya tafi bazai sake dawo wa ba saboda kar Mum ta ‘kara yi mashi wani wula’kancin”.
Sosai safna ta bama Dad tausayi, gyad’a kai yayi cikin ranshi yace “insha Allahu zanyi bakin ‘ko’karin samo maki soyayyar Nawwaf” a zahiri kuma yace “tou naji jeki”.
Haka ta fita tana waigen Nawwaf har suka bar arean d’akin.
Dad ya juyo yace “barin d’auko maku upper’n”,
“Tou” kawai Nawwaf yace yaci gaba da bin Dad da kallo.
Da fitar shi malan Shazali yace “Nawwaf a ringa ha’kuri dan Allah, kasan Allah yana tare da mai ha’kuri, kuma indai kana shiga mutane dole ka rage wannan ZAFIN ran naka”,
Hamza yace “gaskiya ne kam, nima dai abunda na gani kenan, dan wallahi furucin da yayi wa matar nan shi yayi amma ni naji kunya, dan ji nayi kamar in fita in bar d’akin”.
Nawwaf dai baice komai ba sai kallo. Suna cikin haka sai ga Dad ya dawo hannun shi d’auke da takardu.
Zama yayi ya mi’kawa Nawwaf wata takarda guda d’aya, Nawwaf ya kar’ba ya duba sosai yaga Upper ce.
Dad yace “Nawwaf ka samu junior lecturer kasantuwar karatunka bayyi nisa ba, amma a ko wane lokaci zaka iya ‘karo karatu don ka samu ‘karin girma”,
Ya kuma mi’kawa Hamza wata yace “kaima ga wannan, zaka ringa share share da goge goge, kuma insha Allahu zaka ringa samun albashi mai ‘kwarie”.
Godiya sosai suka yi mashi, ya fad’a masu cewa su fara zuwa aiki daga ranar Monday. Haka suka bar gidan cikin jin dad’I da farin ciki, malan Shazali ma ba ‘karamun farin ciki yayi ba.
A ranar Nawwaf ya shirya ya kama hanyar Bagaruwa dan ya shaida wa mahaifan shi.
Da shigar shi gida ya samu Abbah da Ummah zaune suna hira, yayi sallamah ya zauna inda suke. Ba ‘karamin farin ciki sukayi ba da suka ganshi, Abbah yace “Nawwaf lafiya dai kazo yanzu ko?”,
“Lafiya lau Abbah, nazo na baku albishir ne”,
Ummah tayi murmushi tace “wane irin albishir Nawwaf?”,
“Yau dai na samu aiki, na zama malamin jami’ah”.
Sosai sukayi murna da jin haka. Abbah yace “aikuwa tare zamu tafi zanyiwa mutumin godiya, eaboda a wannan lokacin ba lallai bane a samu mutane irin shi”,
Ummah tace “lallai kam, nima dai sai inbi ku ayi dani”,
Nawwaf yace “ehh sai mu bari sai zuwa gobe mu tafi”.
Haka suka shirya washe gari suka kama hanyar Katsina, sai da suka biya ta gidan Malan Shazali dan dama haka yace dashi. Sun samu baya nan, Nawwaf ya bar sa’ko yace “idan ya dawo a fad’a mashi sunzo tare da babanshi, kuma zasu wuce gidan Alhaji Sani sai ya same su acan”,
Sun isa gidan daidai sallar azahar, sun samu Alhaji Sani ja shirin tafiya masallaci, yayi farin ciki sosai daya gansu, ya dai ga Nawwaf tare da wani tsoho da wata dattijuwar mata, yayi masu umurni da su shiga d’akin ba’ki. Ya koma cikin gida yasa Zarah ta kawo masu abinci.
Suna cikin cin abinci ne malan shazali yazo, daidai shigar shi ne Alhaji Sani shima ya shigo, kawai gaban Safna ya fad’I, jikinta ya bata Nawwaf yana cikin gidan. Da gudi ta nufo d’akin ba’ki, ganin tana gudu ne yasa a rud’e Mum da baby suka biyo bayanta.
Tir ‘kashi! Kome wannan had’uwar zata zama? Sai kuci gaba da kasnacewa dani don jin ‘karshen labarin.
Da hanzari baban Nawwaf ya mi’ke tsaye cikin sar’kewar murya ya fara ‘kokarin magana amma sam ya kasa, komawa yayi ya zauna ya ri’ke kai yama rasa abunda zayyi, ganin haka ne yasa maman Nawwaf cewa “malan me ya faru ne?”,
Bai bata amsa ba naji muryar Safna cikin kuka tace “Nawwaf ka taimaka ka rufa mun asiri ka aure ni, wallahi I cant live without youh, kai ne jinin jiki na, wallahi tunda nake ban ta’ba jin son wani namiji bayanka ba”,
Sai a lokacin ta kula da baba tsoho,
Cikin mamaki ta zaro ido tace “baba mai gadi!”
Shi kuwa Abbah tunda ya du’kar da kanshi babu abunda yake sai tariyo wasu abubuwa da suka faru a baya, so d’aya kawai ya d’ago kai ya ‘kara kallon malan shazali da shima shi yake kallo, ‘kara sunkuyar da kanshi yayi wasu zafafan hawaye na binshi.
A gaban baba Tsoho ta koma ta risinah tace “ban san da wane irin baki Zan maka magana ba, nasan naci mutuncin ka naci zarafin ka, na maka abunda duk wacce ta aikata shi tou bata cancanci a yafe mata ba, na kira ka da munanan kalamai, kuma tunda na maka haka ban ‘kara samun natsuwa ba, tun tafiyar ka nake faman dakon son wanda bai san dani ba, bai san da halitta ta a doron ‘kasa ba, na shiga tsantsar tashin hankali mara misaltuwa a dalilin sonshi, sai gashi kuma ashe d’anka ne na cikinka, yau gani a gabanka ina ro’kon alfarma a gareka akan ka taimaka kasa Nawwaf yaso ni, ka sani Baba tabbas Allah ya kar’bi addu’arka, a gabana ka d’aga hannu kace “Allah ya kawo ranar da nima zan ro’ki wata alfarma a gareka”,
Na kiraka da tsohon najadu, yau gani a gabanka na risinah ina mai baka ha’kuri, nayi nadamar munanan halaye na, nayi nadamar hud’ubar da Mum ke bani, nayi nadamar d’aukar kaina da nayi wata high class, nayi nadamar jiji da kai da girman kaina, sai gashi yau basu amfanar min da komai ba sai dana sani, da na sani kuma wanda bashi da wani amfani”
Sosai Safna ke kuka ta ri’ke ‘kafar wandon Baba tsoho da ko saurarenta baya yi.
Kowa idon sa akan Safna da Baba tsoho, sun dad’e a haka kafin Baba tsoho yace:” Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad’aukakin sarki! Abunda na dad’e ina fata yau ya tabbata”,
Kowa ya maida kunnuwan shi ga baba tsoho dake bayani kafin yaci gaba da: “kunga wancan da kuke gani” ya nuna malan Shazali,
“Ehh”suka fad’a su duka.
Yace “d’ana ne Marwan”,
Bai gama maganar ba naji sallamar Dr. Nasir da matan shi.
Sai a lokacin Baba tsoho ya ‘kara rikicewa, Dr. Nasir da sauri yaxo ya rungumi baba tsoho yana kuka.
Sun d’auki tsawon lokaci a haka kafin Dr. Nasir yace ” Sani! Yau dai abunda muka dad’e muna ro’kon Allah ya tabbata, dama ance addu’ah bata fad’uwa ‘kasa banza, yau dai gaka ga mahaifinka wanda ya haifeka”,
Ido bud’e Alhaji Sani yace “what? Dad! Kana nufin baba mai gadi ne mahaifina?”,
“Tabbas kuwa, ashe ma ka sanshi” dr. Nasir ya fad’a,
“Ehh Dad, dan ma dai baka zuwa gidan nan ne ai da ka sanshi, ya dad’e yana aiki a gida na tun kafin mu dawo sabon nan”,
Dr. Nasir yace “tou shine mahaifinka, wannan wani dogon labari ne wanda bazai yiwu yanzu ba”,
Baba tsoho yayi sujada yace “Nawwaf yau kam Allah ya had’a ka da ‘yan uwanka da na dad’e ina baka labarin rabuwata dasu, wancan shine na sani dan yana da shekara takwas muka rabu, shi kuma Sani ban ma sanshi ba, saboda a wurin haihuwar shi ne maman shi ta rasu”.
Dr. Nasir ya sunkuya gaban malan Shazali yace “Marwan ina ka shiga tun shekarun baya? Munyi nemanka har mun gaji amma bamu same ka ba”,
Malan Shazali ya goge hawaye yace “nima dai abunda zan iya tunawa kad’an ne bada yawa ba, na dai san Mum ta aike ni da kud’I suka ‘bata, ni kuma sai nayi tunanin zata duke ni idan na koma babu su shine nayita tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, a hanya na had’u da wani mutumi ina ta kuka shi ya taimaka ya tafi dani gidan shi, ya saka min suna shazali ne saboda yaron shi mai irin sunan ya rasu, tun daga nan sunan ya bini, a hannun shi na koyi sana’o’in hannu har Allah yayi mashi cikawa lokacin ni kuma ina da ‘karfin neman na kaina, nayi aure yanzu yaka ina da yara hud’u, dama tun ranar da Nawwaf ya fara zuwa wuri na nake jin shi a jikina, sai gashi kuwa ashe d’an uwana ne na jini uban mu d’aya dashi”.
AlhajI Sani yace “nima abunda naji knan a jiki na lokacin da Nawwaf ya taimake ni, ashe ‘kani na n…”,
Bai gama maganar ba Safna ta mi’ke tsaye tace “kar ku raina min hankali mana, kuna nufin Nawwaf ‘kanin babana ne kome? Kenan babu aure a tsakanin mu? Aikuwa bazan ta’ba iya rayuwar aure da wani ba”,
Tsawar da Dad ya daka mata ne yasa tayi shiru tana ajiyar zuciya had’e da kuka.
Baba tsoho yaita bata baki har tayi shiru, sun dad’e suna mayar da labari akan abubuwan daya faru ga kowa, baba tsoho ma ya bada labarin tun tafiyar shi prison har sako shi da akayi kasantuwar an gane ba laifin shi bane.
Safna tayi nadama sosai dan kuwa har yanzu ji take ina ma ace mafarki ne take, ina ma ace zata auri Nawwaf, sai dai kuma kash! Hakan bazata ta’ba yi wuwa ba.
Wannan labarin ishara ce ga duka kan masu hali irin na Safna, domin kuwa a kwaisu da dama wanda basa ganin kimar babban mutun. Allah ya shiryi masu irin wannan halin amin.
Bayan wata uku.
Shirye shiryen biki ake sosai a familyn, duba nakai domin ganewa Ido na wanda akewa biki, can na hango Zarah mai aikin su Safna taci ado cikin alkyabba fara, daga gefenta kuma Nawwaf ne yanata fara’ah.
A d’ayan gefen kuma Baby ce na hango itama cikin wata jar alkyabba tasha ado, hannunta ri’ke da wani kyakkyawan matashi dogo fari mai tsarin halitta sai fara’ah suke.
‘Kara murza ido na nayi naga Safna daga gaban su ri’ke da selfie stick tana masu selfie. Ita kam Safna anyi cim’bu babu mijin aure, domin kuwa ko wane namiji tsoron tinkarar ta yake.
A filin da ake kamu ne na hango members na Amrah and Rerbee’art novels suna ta rububin pop corn, kusa dasu kuma na hangi Nafee and Amrah Novellas suma suna ta ‘ko’karin su samu souvenirs, members d’in Zarah bb na gani har da dambe suke wai basu samu ba, Extreme Hausa writers kuwa bakin ‘karfin su suke don ganin sun shiga filin rawa, sai dai kuma basu samu wuri ba saboda wisdom Hausa writers sun cika wurin.
Excellent writers kuwa Nafee Ankah ce na gani ta wakilce su tana ta shoki. Mufarka mata kuwa su suka gyara amare domin indai wurin gyaran amare ne tou ba daga baya ba, su kuwa na Amrah’s kitchen girke girke suka koyawa amaren biyu.
Bayan Shekara uku.
Dad ne na hanga cikin masallaci bayan an gama sallah ya bayar da hoton Safna yace inda wanda yake sonta ya aura, kowa tsoronta yake saboda duk ansan halinta na wula’kanci, ganin basu da niyyar tanka mashi yasa yace “na bama liman sadakar ‘yata safna indai yana sonta, na d’auke mashi komai nata tun daga gida, lefe, kayan d’aki da komai, zai kuma biya sadaki mafi ‘karanci wanda shima nine zan bayar, idan liman ya amince gobe za’a d’aura aure insha Allah.
Take kuwa liman ya fara fara’ah, yaji ance za’ayi mashi komai. “Na amince ko yanzu ma a d’aura” ya fad’a cikin jin dad’I,
Dad yace “a bari goben dai tukuna”.
Batayi wa Dad musu ba saboda itama mijin take nema, Mum ma taji dad’in hakan. Washe gari aka d’aura auren Safna da limamin masallacin ‘kofar gidan su.
TAMMAT BI HAMDULILLAH
Anan ne zan d’igawa labarin aya, labari ne wanda banyi zaton zayyi tsayin haka ba, sai gashi har ya d’auki wannan lokacin, ina fatan masu karatun sunji dad’in shi kuma sun fad’akartu a cikin shi. Kurakuren dake ciki Allah ya yafe min, inda nayi daidai kuma Allah ya ‘karo baseerah mai amfani.
Kunfi kowa a gareni
Iyayena abin alfahari na, ina ‘kaunarku kuma ina yaba maku.
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafin ga ‘yar uwata kuma ‘kawata RABIATU SK MASHI, naki ne Zafin so, kina da damar wallafa shi.
Bazan manta daku ba ‘kawaye na; Zarah BB, Ummeeter Gidado, sadiya Afka, Kirratul-Ayn, Munayshat, rash Kardam, maman khairat, maman Abideen, mum hairullah, kdeey, nafee anka, ummu abrar, maman usman, kausar luv, mimi B, mrs. Umar, hajar, stylish, teemah luff, zee hrt, meesha lurv, autar hajiya, maryam mukhtar, Nuccee luv, Nana Diso, Futha, Zahra, khadeejah candy, Aunty M. Jabo and Xeenur.
Bazan manta daku ba Abdul jega, Muhammad abba gana, Raheem jega and Mr. Smiles.
Naso ace duk sunayen ku su fito amma babu hali, duk wadda ban ambaci sunanta ba tayi ha’kuri tana raina kawai dai babu fili ne saboda mai karatu zai iya gajiya dani.
Tabbas hausawa sunce MAHAKURCHI mawadaci ne, domin kuwa BABU MARAYA sai raggo, ku duba irin YAUDARA data faru tsakanin FADEELAH DA NABEELAH, da kuma RAMUWAR GAYYA da YARIMA SAIFULLAH yayi, wannan wane irin SO DA SHAKUWA ne tsakanin Rabiatu da Imran? Tabbas DAUKAKA DAGA ALLAH take, akwai TSANTSAR ZALINCHI a cikin labarin RADIYAH, sai dai kuma DR. RAFIQ ya magance masu komai, oh! INA ZANGA KDEEY abar alfahari na?, mujiya ce ME BAQIN JINI inji hausawa, soyayyar da KHAULAT tayiwa Tahir ba ta wasa bace har iyayen su na fad’in “wannan wane Irin ZAFIN SO ne suke wa junan su? Ni kuma nace ku rakani wurin HAYDAR DA HAYBAR don ganin wace Irin rayiwa suke ciki.
Alhamdulillah! Littattafan Marubuciyar kenan, HAYDAR DA HAYBAR na naj zuwa bayan sallah insha Allah, karku bari a baku labari.
Inawa kowa fatan shiga wata mai albarka lafiya, Allah ya sada mu da duk alkhairan sake cikin shi.
Amrah ke gaishe da duk wani masoyinta na nesa dana kusa.
Luv youh all