ZAGON KASA HAUSA NOVEL

Ƙarfe biyar da minti arba’in da takwas na yamma, ta faka Motarta a parking space, ajiyar zuciya ta sauke ya fi sau uku, sannan ta kalli takardun da ke gefenta kamar mai tunani, daga bisani ta kai hannu ta ɗauka, ta buɗe motar ta fito.
Jiki a sanyaye ta nufi harabar gidan, gurin da Mahaifinta yake zaune yana shan iska, daman a al’adarsa ya kan zauna a habarar gidan da yamma, wani sa’in ya kan duba jaridu wani lokacin kuma ya leƙa yanar gizo, dan sanin me duniya take ciki.
Da kamar fargaba Namra ta doshi gurin da yake, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama.

talkamin ƙafarta ta fara cirewa tun kamin ta ƙasara kusa da carpet ɗin da aka saba shimfaɗa masa, sallama ce ta fito bakinta kanta na ƙasa kamar mai jin nauyin kallonsa.

“Assalamu Alaikum”

Bai amsa sallamar ba, sai dai ko kaɗan hakan bai bata mamaki ba, daman bata tsammaci zai amsa mata ba, sai kawai ta ɗora da gaisuwa.

“Abban sannu da hutawa ya aikin?”

Ya yi jinkirin amsa mata na daƙiƙon da zai kai ashiri zuwa ashirin da biyar, sannan ya amsa mata can ƙasan maƙoshinsa

“Al-hamdulillah”

Bata yarda wata kalmar ta ƙara fito daga bakinta ba, sai kawai ta tashi jiki ba ƙwari ta saka takalminta, ta nufi hanyar da zata sadata da part ɗin Mahaifiyarta.
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata kamin ta kai hannu ta murɗa ƙofar falon ta shiga. Babu kowa a parlor sai air conditioner dake ta aikinsa, Kai tsaye ɗakinta ta wuce zuciyarta cike da rauni.
Saman gadonta ta zauna ta lumshe ido tana sauraren bugun zuciyarta, kalaman da Mahaifinta ya yi mata ɗazu da safe suƙa riƙa dawo mata, irin yadda ya riƙa aibanta ta, yasa ta ta yi saurin dafe kanta, sai kuma ta fashe da kuka tana murza zoben dake hannunta.

Haka ta zauna a ɗakin bata fito ba har sai da aka yi sallah Magariba, bayan ta yi sallar ta fito ta nufo parlor fuskarta babu yabo babu fallasa.
Duk ƙannenta suna zaune parlor suna kallon Dadin kowa, babu wanda ya lura da fitowarta sai Mahaifiyarta. can nesa da Mahaifiyarta ta zauna tana gaisheta.

“Anty barka da dare”

Bata amsa mata ba, sai kallonta take tana karantar irin halin da ƴarta take ciki.

“Tunda kika dawo daga makaranta Namra kina cikin ɗakin, so kike yi damuwa ta yi miki yawa ko? Yau ranar girkina ce amman saboda ke Abbanku bai leƙo nan ba, na shiga sashensa na rasa gane kansa, so kike ki kashe min aure ko Namra? kin fi son ki rayu da son zuciyarki fiye da farincikin iyayenki? bana ƙin zaɓin ki Namra, amman tun da mahaifinki ba ya so barin shi ya fi alheri”

Matsewa ta yi cikin kujerar tana wani irin kuka da ba zata iya fitarwa ba.
Sai yaushe Abbah ta zai fahimci halin da take ciki ne, sai yaushe zai tausayawa rayuwarta? ji take idan har ta yarda ta rabu da Asim zata iya mutuwa, bata jin zata iya rayuwa da wani Namji da ba Asim ba, kuma idan har bata aureshi ba, ta san Allah ba zai yafe mata ba, mutane zasu masa dariya, daman an daɗe ana masa kirarin ita ɗin ba sa’arsa bace, ta san irin son da Asim yake mata, ta ya zata iya sanar da shi ba zata aurensa ba? Yayyu ta Mata da Maza Tara Mahaifinta ya aurar, duk kuma a cikinsu babu wanda ya yi ma zaɓin miji ko matar aure sai ita.

Sallamar Barrister Yasmin da Mijinta ne, ya ankarar da ita ta yi saurin share hawayenta, tana gyara fuskarta dan kar su gane ta yi kuka.
Anty Amarya ce ta amsa musu fuska a sake kamar yadda ta saba tarbonsu.

“Maraba maraba da Lauyoyi, cikin daren nan ake tafe”

Yasmin ta zauna a kujerar da Anty Amarya take zaune, yayin da Uzair ya zauna a kujerar da ke kusa da ƙofa, idonsa na kan Namra wace ta banye ɗaurin ɗankwalinta tana ƙoƙarin magana da matarsa.

“Anty Barrister ina Afnan?”

“Yanzu na biyo uban daren nan na miƙe hanya ki rasa wanda zaki tambaya sai Afnan? amman yarinyar nan akwai ki da rainin hamkali”

Kusa da ita Namra ta dawo ta zauna tana faɗin

“Kaji Anty da wata magana, toh ai ita ce Ƴata dan haka ni ita zan tambaya”

“Idan kina son ganinta kawai ki je gidan Gwaggo ki ganta, amman indai tambaya zaki yi, ki riƙa cewa ya na ke ni da Mijina”

“O’oh masu miji manya, toh ni ban ga mijin na ki ba ai”

“Ni ai na ganki”

Uzair ya amsa daga inda yake zaune yana kallon ƙugunta zuwa saman ƙirjinta.

“Jar uban nan, ka ji min wata magana! saboda ke fa muka biyo ta nan amman zaki wani ce baki ganshi ba”

Duk suka sa dariya Maryam ta ce

“Toh mijin na ki ai tsoron mutane yake shiyasa ya maƙure gurin kamar wani ɗan fashi”

Anty Amarya ta kai mata dudu

“Wai dan kun ga baya magana shiyasa kuka raina shi ko?”

Dariyar suka sake yi, sannan Anty Amarya ta shiga tambayar Barrister ya aiki. Namra kuma ta nufi hanyar kitchen dan ta ɗauko musu ruwa, tun da ta tashi Uzair ya bi bayanta da kallo har ta shige kitchen ɗin.

Bayan sun sha ruwan ne Barrister ta ce

“Anty Mun zo aron Namra ne, Uzair zai yi ɓaƙi daga Abunja,kuma yana son ayi musu wainar kaza kinsan Namra ce ta iya shiyasa muka zo mu faɗa miki”

“Aa ni ba ruwana ga ku ga Namra”

Cewar Anty Amarya tana kallon Namra da ta ɗan ɓata fuska kaɗan, dan sam yanzu bata son zuwa gidan Yasmin, Hakan kuma ya samo asali ne tun lokacin da Uzair ya soma nuna mata maitarsa a fili.

“Kai gaskiya na so nayi tilawar haddata, dan Saturday nan ne walimar mu fa”

Yasmin ta ɗan zungureta

“Ke uwar kuiya, just for one day ne fa zaki mana, ai yau Wednesday, zaki iya yi Friday”

“Haba kije mana idan kin gama musu da wuri ma ai zaki iya dawowa”

Anty Amarya tasa baki. Yasmin ta ce

“Kuma ni kin ga fita zan yi ba gida zan wuni ba, ina da cases har huɗu ƙila sai yamma zan dawo balle ki ce zan dame ki da surutu, Uzair kuma sai biyar yake dawowa, ke kaɗai ma za’a bari a gidan”

Ta amince ba dan ta so ba, sai dan babu yadda zata yi, indan har ta ce ba zata je ba, Yasmin zata zargeta, Anty Amarya kuma zata mata faɗa, sa’arta ɗaya gobe ba su da lacca.
ba su wani daɗe sosai ba, suka yi ma Anty Amarya sallama suka fice. Har gurin Mota Namra ta rakasu, Yasmin na laƙame da kafaɗarta tana mata tambihi game da haƙuri, dan ta fi ƙowa sanin halin da Namra take ciki, kasancewar shaƙuwarsu, Namra bata ɓoye mata ƙomai.

Bayan sun wuce ne ta dawo jiki a sanyaye ta shigo parlor.

“Ni wallahi bana son zuwa gidan Anty Yasmin”

Ta faɗa tana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Maryam ta kalleta ta ce

“Saboda me?”

Kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru ta kalli tv.

“Tashi kije ki ci abinci”

“Bana jin yunwa”

“Ai gaki nan, duk kin bi ki koɗe sai fama kike da rama kamar wata marar lafiya”

“Wallahi Allah bana jin yunwa Anty”

“Ta ya zaki ji yunwa kin ɗauki damuwa kin sawa ranki, Allah ya sauwaƙe miki wannan rayuwa”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, dan ta dan duk yadda zata yi ma mahaifiyarta bayani, ba ganewa zata yi ba.
Annur ne ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa hannunsa riƙe da lemu ya ce

“AntyAmarya wai Abbah ya ce ki zo tare da Anty Namra”

Gabamsu ya faɗi dukansu, bama kamar Namra data ja wani dogon numfashi ta sauke, kamin ta kalli Mahaifiyarta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tashi suka nufi part ɗinsa, kishingiɗe suka tararda shi, kofin tea na gefensa yana sanye da madubi fuskarsa babu annuri yana duba wasu documents.
Namra ta zauna ƙasa cikin ladabi, Anty Amarya kuma ta zauna saman kujera tana faɗin

“Annur ya ce kana kiran mu!”

Bai ce uffan ba, har sai da ya ƙare duba takardun da yake sannan ya cire gilashin idonsa, ya kalli Namra babu alamun wasa a tare da shi ya ce

“Kin san Alhaji Madu Sanusi?”

“Eh”

Ta amsa ƙasa-ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa, aikan ta san Alhaji Madu akan farin sani, mutumen da kwana biyu, uku yana gidansu, aminin mahaifinta.

“Shekaran jiya ya yi min magana akan ki, saboda yana son ƙara aure dan ki zame masa first lady tunda sauran matansa basa jin turanci, kuma a takarar da yake akwai buƙatar ya auri mace ƴar boko, mun gama magana da shi gobe da dare zai zo ku gaisa”

Tun da ya soma maganar hawaye ke zuba a idonta har ya ƙare, daker ta iya amsawa da

“Allah ya kai mu”

Anty Amarya ta amsa da “Amin” Tana sauke ajiyar zuciya, sam bata jindaɗin yadda Abbah yake yi ma ƴarta sai dai babu yadda zata yi, ko magana ta yi cewa yake ita ke ɗaure mata gindi tana yadda take so.

Cikin sauri Namra ta taso, ta baro falon zuciyarta cike da zulumi, tana tsaron abunda zai je ya dawo, ta rasa ƙwaƙwaran dalilin da ya saka Mahaifinta ba ya son tarayyarta da Asim.
Har ta shigo ɗakinta kalmar Alhaji Madu ce take mata yawo a kunne, saman gado ta kwanta hawaye na bin fuskarta, sai ta kai hannu ta janyo wayarta, gallery ta shiga ta kamo hoton Asim tana kallo.

“Miyasa Ƙaddarata zata min haka? kin san ba zaki barni na yi soyayyah da shi cikin kwanciyar hankali ba kuma kika haɗa mu? kinsan ba zan auresa kuma kika sa na sansa, Allah kayi min mafita karka ka bar ni da kaina”

Rumgume wayarta ta yi sosai tana kuka da tuna kalaman daya faɗa mata yau a makaranta.

‘Ina son ki sosai Namra duk da jikina yana bani lallai ba zaki aure ni, saboda ni da ke ba ɗaya ba Namra, ga shi mahaifinki baya son na, Mahaifiyata tana yawan faɗa min wai zaki ɓata min lokaci ne kawai ba zaki aure ni ba, Namra ina gudun ranar da zan wayi gari kin zama matar wani magauta suyi min dariya…’

Kuka take sosai har da karkarwa, tana matsar idonta da buga ƙafafunta.


Manjo Usman Zamau tsohon soja ne, mai mata biyu Hajiya Barau wanda ake kira da Mama da kuma Hajiya Larai wanda ake kira da Anty Amarya. Gidan Alhaji Usman babban gida ne mai ɗauke da part uku, part ɗin uwargidan sa da kuma na Amaryarsa sai nasa.
Uwargidansa na da ƴaƴa tara hudu mata biyar maza kuma dukansu sun yi aure, wasu suna tare da ita wasu kuma aure ya kai su nesa, a yanzu bata da ɗa ko ɗaya a gidan sai jikoki da ƴaƴan ƴan’uwa.

Anty Amarya ce aka auro daga baya, ita ce mai yara huɗu dukansu mata, Namra ce babba sai Maryam dake binta da kuma Hindatu da Aisha. cikakkancen sunan Namra shine Khadija mahaifiyarta ta kan mata Alkunya da Namra ne kasancewarta ita ta fari gareta. Namra na 100l a jami’ah ta haɗu da Asin, suka ƙula soyayyar da babu wanda ya sani har suka kai 300l, sai a yanzu ne abun ya zame musu matsala kasancewar Asim ba ɗan kowa bane face talaka mai neman abunda zai sa a bakinsa.

Ita kuma ƴar masu arziki ce musamman yanzu da Mahaifinta yake takarar Senator, daman can mutun ne mai abun hannunsa dan yana da kamfanoni da dama ciki da wajen ƙasar nan.
A duk familynsu da shi suke tinƙaho dan Allah ya yi masa rufin asiri ta ko ina.
Gashi shi ƙaɗai mahaifiyarsa ta haifa a duniya, a duk familynsu ya fi shaƙuwa da Mahaifiyar Yasmin da Kuma Mahaifiyar Uzair kasancewar kakanninsu guda, kuma yana ganinsu mata, yana tausayinsu sosai.

WANNAN KENAN


SECOND FAMILY…

Tun da ta dawo daga aiki take cikin damuwa, abun duniya ya fara isarta komai ya taru ya yi mata katutu a rai, kullum ta fita ta dawo sai anyi da ita a unguwa, ƙawayenta su zolayeta familynsu ayi ta tambaya, kamar ita ta ɗorawa kanta rashin aure.

Kallon kanta take ta madubi tana hawaye, ta ko’ina Allah ya yi mata sura, mace ce abunda ake cewa mace, amman babu mai neman aurenta sai mutanen banza, duk acikin manemanta babu na ƙwarai da zata ware da sunan wanda zata aura, duk wanda ta yi ma maganar aure ba zai sake dawowa ba, sai dai su nuna suna son jikinta.
Sa’aninta duk sun yi aure, sun barta sai kace wanda ta zagi maza, tun tana sa ran idan ta gama karatu ta samu wanda zata aura yanzu ga shi har ta gama ta samu aiki amman ba shiru, ada abun ba ya damun iyayenta amman yanzu ya zame tunaninsu, suna addu’ah amman kamar basa yi, sun aurar da ƙannenta biyu mata ita shiru, babu mashinsshini balle malashi.
Faɗi tashi na neman magani babu irin wanda bata yi ba ita da iyayenta, amman ba wani labari. Yanzu kan har ta fara fidda rai daga samun mijin aure.

Kallon kanta take sosai da sosai a gaban madubi tana mamakin yadda take ƙokarin kare kanta daga zina da alfasha, tana ƙokarin sallah dare da sadaka, amman ta kasa samun mijin da zai aureta.
Hawaye ne suka zubo mata tana tuna irin yawan ƙawayenta, amman babu ko ɗaya duk sun yi aure sun barta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sai ta kalli Screen ɗin wayar Salma ce rubuce a fuskar wayar, cikin sauri ta share hawayenta ta ɗauki wayar ta kara a kunne.

“Hello Salma”

“Na’am Kalsoom ya kike?”

“Lafiya ƙalau, ya Ahmad?”

“Lafiyarsa ƙalau, idan kina da time gobe ki shigo da wuri zamuje wani guri”

Da toh kawai ta amsa mata ta aje wayar, ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ko bata faɗa ba ta san ba zai wuce ta kai ta gurin wani Malamin ba, dan duk cikin ƙawayenta ita ce ta fi kowa damuwa da rashin aurenta, ita ce take ta faɗi tashi akan taga ta yi aure.

Kiran da ta ji ana mata downstairs ne yasa ta motsa ta tashi ta nufi ƙofar fita. Karo suka yi da Momy sai ta ja baya da sauri tana faɗin

“Kirana kike yi?”

“Eh yanzu mijin Zainab ya kira wai bata da lafiya tun shekaranjiya”

“Subhannallah miye same ta?”

“Wai maleria ce, amman dai na san ba zai wuce ciki ba, shine nace ki shirya gobe kije can ki yi mata ko da kwana uku ne idan ta ɗan sarara sai ki dawo”

“Haba Momy ni kuma? miyasa Saleena ba zata je ba ni fa yayarta ce kuma ace na koma can na zauna”

“Toh miye a ciki? ai ansan lalura ce ta kai ki, Saleena Exam za su fara gobe kinga ba zai yiyu ta je can ba, amman ke tunda aiki ne ai idan kin dawo sai ki ɗan taya ta aikin gidan da dafa musu abinci”

“Amman Momy ai yana da ƙanne mata kuma za a iya ɗauka mata ƴar aiki”

“Ya san da ƙannensa amman ya zo nan ya faɗa mana, idan mutum yana mutunta ya kamata kai ma ka mutun tasa, kwana uku kawai zaki yi ki dawo kin ji?”

Ta ɗaga mata kai alamar toh, zuciyarta cike da damuwa.

“Allah ya yi miki albarka”

“Amin”

Daga haka Momy ta juya ta sauka ta barta a gurin tsaye. Jinginawa Kalsoom ta yi jikin ƙofar tana addu’ah

“Ya Allah idan mijina yana nesa da ni Allah ka kusan to dashi a gare ni, idan yana kusa da ni Allah ka haɗa mu”

Juyawa tayi ta shiga ɗakinta tana cika ma bakinta iska.

DOWNLOAD BELOW ⬇️