ZANEN DUTSE CHAPTER 2 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 2 BY AISHA-SHAFIEE

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

LARABA, TA BAWA RANAR SA’A.+

Kamar yadda burin kowacce uwa a duniyar nan shine ta aurar da d’iyarta da zarar ta kai munzalin aure, haka ma Baddo ke da wannan burin akan ki da kuma Jamila, kamar yadda jinkirin aure ga ‘yar ke sanya k’unci da damuwa a zuciyar kowacce uwa haka ma Baddo ta shiga wannan halin kafin Jamila ta samu tsayayyen da a yanzu har aka sanya musu rana.

Kin sani Jidda, kin san hakan kuma kin san wannan yana daga cikin dalilin da yasa Baddo bata hana ki ganin Suraj tun farko ba saboda kar ta maimaita irin kuskuren da tayi akan Jamila ba wai don ta yarda dashi itama ba.

Jamilar kad’ai kuma ta ishe ki misalin ganin irin ciwon dake cikin ‘Jinkirin aure’ ko kin manta lokutan da kike kamata a d’aki tana kukan da ma’anarsa bata wuce na yadda bayan danginku hatta mutanen dake kewaye daku ke mata kallon ‘K’ask’anci’ don kawai ubangiji bai k’addara aurenta a lokacin sa’anninta ba.

Don haka kar kiyi saken jefa kanki cikin irin wannan halin kizo kina nadamar damar da kika samu a yanzu Jidda…

Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga b’arin zuciyar Jidda wanda zata iya kira da ‘mai hankalin’ kafin d’aya barin da yake madugu uban tafiya a kusan duka al’amuranta ya rushe shi.

Komai ai Mukk’addari ne daga Allah Jidda, don kin rama abinda Suraj yayi miki hakan baya nufin zai tafi kuma kin rasa mai sonki kenan har abada.

Kina son Suraj amma abinda yayi miki rainin hankali ne, kawai ki san yadda zaki yi ki rama kema tunda ai yana sonki, don yayi fushi haka baya nufin zai rabu dake… D’an sab’ani ne kawai irin na yau da gobe zai shiga tsakaninku kafin lokaci ya wuce dashi, kuma kinga kin koya masa hankalin da a gaba ba zai sake yi miki irin wannan rainin hankali ba.

Kamar gaske wannan shawarar ta tafi har k’arshe, sai kuma ta girgiza kanta don bata jin zata iya d’in, zuciyarta tana son Suraj kuma bata jin zata iya saki na dafen wasa da lamarinsa, don a yadda mu’amarlarsu take yanzu tsoro take komai kankantar abu zai iya sake nesanta ta dashi ne. Gashi yace mata zai zo a yau, wanda rabon da ta ganshi sau biyu a d’an k’ank’anin lokaci an dad’e, to don me kuwa zata yi wasa da damarta? Watakila ma ya huce ne.

Sai ta cije lebb’enta na k’asa a hankali tana cigaba da tsige Salad d’in da take gyarawa, ta rasa wace irin yarda zuciyarta ke bawa Suraj, tunda gashi yau har ta bashi darajar wanda ya isa ya raina mata hankali kuma ya tafi da nasarar hakan.

“Wai ace har na dafa kwai, fiye da minti goma amma kina zaune baki gama gyaran Salad d’in ba..”

Muryar Jamila ta fad’a daga kanta.

“Idan Baddo ta fito daga wanka kin san dai ba jiranki zata yi ba.”

Ta k’ara fad’a tana yin gaba, sai dai kuma jin bata yi rashin kunyar data saba yi mata ba yasa ta d’an tsaya sannan ta juyo ta kalle ta, wani d’an gajeran tunani ya gifta cikin ranta saboda haka ta dawo ta tsaya akanta, sai kuma ta zauna a kusa da ita sannan ta kira sunanta.

“Jidda… Me ya same ki?” Muryarta ta fito da irin wannan kulawar dake nuna matsayin yaya ga k’anwarta.

Jidda ta had’iye wani abu a bakinta cikin jin nauyin tambayar don bata san me zata ce mata ba, Suraj d’in da bata so ya fara raina mata hankali ko me? Sai ta girgiza kanta kawai sannan tace.

“Ba wani abu da ba zan iya dashi bane.”

“Na sani, amma kin san abubuwa sun fi sauki idan ka tattauna su tare da wani musamman wanda ka yarda dashi, ko ni baki yarda dani bane?”

Ta d’an yi shiru kafin ta fad’i gaskiyar zuciyarta.

“Ba wai ban yarda dake bane, ke matsalarki ne yanzu na san idan na gaya miki wannan abin har abada baza ki daina kafa misali dani ba.”

STORY CONTINUES BELOW

Kafin Jamilan kuma tace wani abu, Sadiya ta bud’e k’ofar net d’in d’akin ta shigo, saboda haka ta canja zancenta da cewar.

“To ga aminiyarki nan sai ki gaya mata ita.”

“Dan Allah Aunty Jamila kice min shinkafa da wake kuke yi?”

Cewar Sadiyan tana kallon salad d’in dake zube a gaban Jidda, Jamila ta mik’e tsaye tana fad’in.

“Har da Salad da kwai.”

Sai ta washe baki cikin farin ciki kafin ta tambayeta.

“Har kin dawo daga cikin gida ne? Naga lokaci bai yi ba.”

“A’a Jakadiya ce ta bani hutu saboda ciwon k’afar Baddo.”

‘Au haka ne fa.. Allah ya bata lafiya.”

Ta k’araso gaban Jiddan ta zauna yayin da Jamila ta shige kwallin d’akin dake manne da madaidaicin falon nasu, inda a falon suke gudanar da kusan komai na rayuwarsu hatta kwanciya, don cikin d’akin yayi k’ank’antar da kaya kawai suke iya ajiyewa.

“Wai Jidda jinin da ya shafi d’ankwalin Baddon ya fita kuwa?”

Sadiya ta tambayeta bayan ta zauna.

D’ankwalin Baddo. Kalmar ta dira a kan Jidda kamar dukan guduma, sai ta d’ago ta kalle ta a lokacin da ragowar zancen Suraj ya ruguje a ranta.

“Wallahi bai fita ba Sadiya, ni tunda na tashi ma na manta, yana cikin kayana na ajiye shi dana ga zai b’ata min rai.”

“Dole ne fa a wanke shi, don ko yau sai da Hajiya tace min wai in karb’o d’ankwalin Baddon gobe zata shiga kasuwar cikin gari.”

Jidda ta d’an ja tsaki.

“Ni ban san yaya akayi na saka abin nan a cikin jakata ba wallahi, don bayan d’ankwalin har littattafaina sun b’aci da jinin.”

“Kin san me? D’azu da safe nayi tunanin kawai mu saka bleach a wajen koda atamfar zata b’aci, don gwara a b’ata wajen da suga jinin.”

Babu musu Jidda ta yarda da wannan shawarar, don haka bayan ta taya ta sun gama aikin, suka tafi har kantin d’an bala dake can baya suka siyo bleach d’in sannan suka nufi bayan ginin d’akunansu kusa da inda suka k’ona asirin dai da suka tone.

Sadiya ta ware d’ankwalin sannan Jidda ta shiga yaryad’a bleach d’in akan duk inda ya b’aci, a lokaci guda kuwa wata farar kumfa ta dinga fitowa tana fitar da k’ara alamun k’onewar koma meye a wajen sannan ta dinga k’aruwa tana tashi kafin a hankali kuma ta fara yin k’asa- k’asa.

Sadiya mik’owa Jidda ruwan da suka deb’o a buta ta kwara akan d’ankwalin sannan ta matse shi tsaf! Kafin ta ware shi zuciyarta ta shiga tunanin dalilin da zata gayawa Baddo na yadda d’ankwalinta ya kod’e, Sai dai me?

Tana warewar idanunsu suka ci karo da abinda yafi k’arfin tunaninsu… Zuciyar Sadiya ta buga sannan tata ta d’an yi rawa kad’an.

Duk wani zane dake jikin atamfar ya kod’e a inda bleach din ya sauka, tayi fari ba’a ma iya ganin wani alamar zanen balle kala, amma jinin da suke zaton shima ya tafi, yana nan tar dashi kamar a lokacin ne ma aka gama shafa shi!3

Watakila na shiga uku!8

Jidda ta ayyana a ranta.

***

Laraba, Ta bawa ranar sa’a!

08:00 PM.

D’an madaidaicin falon na d’auke da duk wasu irin kaya na alatu da suka amsa sunansu, sannan bayan haka zaka iya cewa babu kowa a ciki idan ba ka hango wanda ke zaune daga can gefe na d’akin ba saboda shirun da ko’ina ya d’auka.

STORY CONTINUES BELOW

Madaki ya d’ora biron da yake rike dashi a hannunsa yana kallon takardun dake baje akan d’an teburin dake gaban kujerarsa.

“Gaskiya suna da Proof Mdee…”

Muryar Mubarak ta fito daga tablet d’in dake jingine akan teburin tana kallon fuskarsa, kusan minti talatin kenan yake zantawa tare dashi ta videocall na waya akan meeting d’in da yayi tare da masu aikin kamfanin a jiya. Mubarak ya cigaba da cewa.

“Babu cost report d’in komai na site labour sai total d’in da aka tattauna kawai.”

Madaki ya d’ago da idonsa ya kalle shi, fuskarsa ta nuna alamar zuzzurfan nazari kafin yace.

“Idan haka ne da Minutes d’in ranar suka yi amfani, waye ya rubuta shi lokacin da akayi meeting d’in?”

“Sa’id ne, ai shine mai rubuta Minutes koyaushe…”

“Ba Sa’id bane..” Ya katse shi yana kallon fuskarsa ta cikin wayar.

“… Don na tuna bai zo office ranar ba, kuma kamar George ne ya karb’e shi a ranar ba Bologun ba ko?”

“Tabbas kuwa George ne don na tuna na karanta Minutes d’in bayan kun fito daga meeting a ranar, kuma handwriting d’insa ne.”

Shiru ya sake ratsa d’akin kafin Madaki ya ajiye biron hannunsa sannan ya koma da baya.

“Ka san me? Inaga wannan abin ma ya fito fili kawai, don tun daga meeting d’inmu na farko ake tattauna zancen farashin komai, ba zai yiwu ace a minutes kuma ba za’a rubuta komai dalla-dalla kamar yadda aka tattauna ba sai dai a had’e total d’in kawai lokaci guda ba.”

“Me kake tunani?”

Mubarak ya tambaya yana kallonsa ta cikin wayar, Madaki ya dunk’ule hannu d’aya kan bakinsa alamun tunanin kafin yace.

“Ina tunanin George yana da alak’a da mutanen nan ne shi yasa ya karb’i rubuta minutes d’in, kuma watakila ma su suka yi sanadiyar hana Sa’id zuwa office a ranar, zai iya yiwuwa akwai abinda suke shiryawa tare… Ka san me? kana da address d’insa?”

Ya k’arasa yana kokarin lalubo wayarsa akan kujerar dake gefe.

“Ina dashi Mdee, amma me za’a yi?”

“Ali zan kira suje su tafi dashi division d’insu a yau, a fara tsorata shi tukunna kafin in sa a taho dashi nan.”

Mubarak ya girgiza kansa.

“Bana jin hakan shine daidai, saboda idan kuma aka same shi babu laifi me kenan?”

“Sai a biya shi diyyar kama shi da akayi ba laifi, na san dai ai shine k’arshen zancen, just send me the address.”

Kamar Mubarak d’in ya sake cewa wani abu amma sanin cewa ba zai canja hukuncinsa ba sai ya fasa, ya jawo d’aya wayarsa ya shiga lalube a ciki.

“Kunyi magana da mai martaban?” Ya tambaya hankalinsa na kan wayar da yake dannawa.

Madaki ya girgiza kansa.

“Na dai je gaishe shi jiya amma bai ce komai ba, nima d’in ne dai kusan kullum sai dare nake dawowa, in na shigo da yamma kuma ina wajen Hajja, amma may be tunda abubuwa sun fara warwarewa zan je in same shi…”

Kafin ya k’arasa k’arar shigowar sak’o a daya wayarsa dake gefe ya katse shi, sanin cewa personal number ce da ‘yan kalilan mutane a duniya ne kawai ke da layin, yasa yasa ya mik’a hannu ya dauko ta.

Saifuddeen, shine sunan daya nuna b’aro-b’aro a b’angaren mamallakin number, sannan daga k’asa sak’on daya zama mataki na biyu wajen canja akalar rayuwarsa ya fito tar!

Zan iya ganinka yanzu? Please… Ina tsaye a lambun dake bayan turakar Mai martaba.

“Ya akayi?” Mubarak ya tambaya daga cikin wayar yana kallon yadda yanayin fuskarsa ke canjawa.

STORY CONTINUES BELOW

“Turakin ka ne yake son ganina.”

Kafin Mubarak yace wani abu ya d’ago ya sake fad’in.

“A tunanina na gama magana dashi tunda har naje na same shi ya nuna baya sha’awar harkar aikin nan kuma nayi convicing mutanen nan mun cire sunansa daga cikin ‘Project Managers’ d’in, what else is there to say kuma? (Me kuma ya rage zai ce min?)

Mubarak ya ajiye wayar hannunsa sannan yace.

“Ka gane Mdee, ba lallai zancen aikin nan ne yasa ya nemeka ba, zai iya yiwuwa wani personal issue ne daya shafi rayuwarku, and saboda ya nuna bashi da interest a harkar nan hakan baya nufin cewa kun yanke alak’a kenan…”

“Bani da wata rayuwa bayan abinda ya shafi aikin nan Mubarak, don haka ban san me zan tattauna dashi ba.”

Sai yayi ajiyar zuciya a hankali yana kallonsa kafin yace.

“Kana nufin inda nima zan neme ka akan wani abu da bai shafi aikin nan ba kenan you will just turn me down? (ba zaka saurare ni ba?)”

“Ba haka nake nufi ba…”

“To me kake nufi Mdee? For god’s sake Turaki yana amsa sunan d’anuwanka ne, ko wane irin abu ne ya shiga tsakaninku a baya da kuma yanzu ya kamata ka duba rinjayen alkhairinsa ba sharri ba, yau idan ka d’auki hanya ka bar Kiyari sai ka shekara hud’u- biyar baka sake ganinsa ba… To don me baza ka ara masa minti goma ba kawai a cikin rayuwarka?”

Madaki yayi shiru kawai yana jinsa, kowanne b’angare na tunaninsa na tsinto ma’anar dake cikin kalamansa yana ware su gefe, zuwa can sai kawai ya mik’a hannunsa zuwa madannin kashe kiran ya danna shi tare da fad’in.

“Sai da safe.”

Kafin Mubarak d’in kuwa ya sake cewa wani abu, dib! Kiran ya katse.

Ya koma da baya ya rufe fuskarsa da tafin hannayensa, sannan ya fitar da ajiyar zuciya a hankali tare da ambaton istigfari a zuciyarsa.

Wucewar minti biyu kafin ya mik’e ya nufi can kan gadon d’akin, ya d’auko wata ‘yar k’aramar jaka a akwatinsa wadda ke d’auke da wasu ‘yan tarkacen da yake son ya kai mota, sannan ya d’auki muk’ullin motar, ya kashe fitilar d’akin ya nufi waje.

Daga nan cikin k’atuwar farfajiyar da fuskar d’akin take, mintuna biyar ne suka kaishi wajen harabar lambun.

“Barka da isowa ranka ya dad’e, Turakin yana ciki yana jiranka.”

Cewar wani bafade dake tsaye a k’ofar, ba tare da ya bashi jakar hannunsa da yake kokarin karb’a ba yayi masa godiya kawai sannan ya shige ciki.

Saifudden d’in na zaune kan wata kujerar dutse dake fuskantar hanyar shigowa, yana ganinsa ya mik’e tsaye a hankali sannan ya nad’e hannayensa a k’irji.

“Barka da isowa.”  Muryarsa ta fito da zurfi yana kallonsa.

Madaki ya gyad’a kansa sannan ya amsa.

“Barkan mu dai.”

“Zaka k’araso ne?”

Ya k’ara tambaya yana nuna masa kujerar, sai ya girgiza kansa kafin shima yayi tasa tambayar.

“Maganar tana da tsawo ne?”

“Ko kad’an, ina so in fara baka hakuri ne akan rashin sanya hannuna cikin aikin Kamfanin…”

“Kar ka damu na fahimci uzurinka.” Ya katse shi.

Saifuddeen ya d’anyi shiru yana kallonsa, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace.

“Abinda kake tunani ba haka bane Madaki, nak’i sanya hannu ne kawai saboda Mai martaba, don ko kad’an baya son mu’amalata da wani abu bayan sha’anin sarauta.

Shi yasa nake son ka gyara fahimtata akanka, ka goge wannan hoton da kake ganina dashi a kullum don rayuwata ta dad’e da canjawa, na zama shugaba a yanzu na bar matsayin wannan yaron da FULANI ke juyawa.”

Madakin yayi shiru kawai yana kallonsa daga inda yake tsaye ba tare da yace komai ba, sai ya girgiza kansa shima sannan ya juya ya kalli wata bishiya dake can gefe… Ya riga ya sani daman, kamar yadda lokaci baya dawowa baya haka ma zuciyar Madaki ba zata tab’a dawowa baya wajen yarda dashi ba.

Ya sake juyowa ya kalle shi sanda zuciyarsa ta yanke shawarar fad’ar abinda ke ransa koda babu tasirin hakan.

“Dama na nemi ganinka ne don in gargad’e ka game da ita.”

Ba sai ya fasa kalamar ‘Itan’ ba, Madaki ya riga ya san wa yake nufi.

“Ban san me take shiryawa wannan karon ba, amma ta tabbatar min cewa ba zata fasa k’udirinta akanka ba don haka kayi a hankali, kuma ina baka shawara akan ka takaita zamanka.”

Maganar tabi a hankali tun daga cikin jijiyar kunnen Madaki har zuwa lungun da kwakwalwa ke fahimtar bayanai, a lokaci guda yaji zuciyarsa tayi yunk’urin d’aukar zafi amma sai ya cije lebb’ensa na k’asa da k’arfi kamar hakan ne zai tsaida ta.

“Na barka lafiya.”

Saifudeen d’in ya sake fad’a da muryar dake nuna sallamawa kafin ya taho gaba da niyyar tafiya, sai dai yana zuwa dab da kafad’arsa zai wuce ya tsinci abinda bai tab’a tunanin jinsa daga bakin Madakin ba.

“Na fahimce ka…”

Sai yaja ya tsaya sannan ba tare da ya bari zuciyarsa ta tace gaskiyar kalman ba ya karb’e su hannu bibbiyu har cikin ransa.

“… Kuma nagode da kulawarka, sai da safe.”

Madakin ya sake fad’a kafin ya juya ya riga shi fita daga wajen.

Saifudeen yabi bayansa da kallo sannan a lokacin d’aya tunaninsa ya ajiye duk wata hassada a gefe ya lak’aba masa tauraron ‘Namiji mai aji’ don ba tun yau ba ya sani cewa Allah ya mallakawa Madaki wani irin cikar zati da kwarjinin da ko su da suka shafi jinin sarauta basu samu ba… Kuma a baiyane yake cewa mahaifiyarsa bata tab’

a tsayawa ta kalle shi ba balle har ta san da wa take wasa.

Madaki tafiya kawai yake ba tare da yasan tak’amaiman abinda ya dace ya rik’e a matsayin tunani ba don idanunsa kusan a rufe suke sanda ya nufi hanyar da zata fitar dashi harabar ajiye motoci…

A baya abubuwa guda biyu ne kad’ai ke yin hijabi da irin nasa ikon, su kad’ai ke hana shi daidaita rayuwarsa kuma Fulani tana cin albarkacinsu ne duk tsawon wannan lokacin…  Albarkacin ‘ya’ya da kuma miji irin wanda ta samu.

Amma a yanzu yana ganin tura ta kai bango, dole ne ya nuna mata cewa shirunsa baya nufin gazawarsa, watak’ila anzo gejin da zai shata mata iya matsayinta a rayuwarsa don ta fahimci cewa bai kyaleta tsawon shekarun baya saboda ba zai iya ba.

Watakila anzo gejin da zai tarwatsa Fulani da dukkan iyawarsa don ance mai laya ya kiyayi mai zama….2

Tunaninsa ya katse sanadiyyar numfashin da ya zarce cikin k’irjinsa a lokacin da wani abu ya taho da gudun gaske ya dake shi, jakar hannunsa ta fad’i k’asa sannan saboda rashin zip d’in jikinta abubuwan dake ciki suka tarwatse gabad’aya kan interlocks d’in dake wajen.

Sai yaja da baya a hankali sannan ya kalli fuskar yarinyar data buge shi, a lokacin itama ta d’ago da idanunta da suka yi jawur alamun tashin hankali ta kalle shi.8

Wannan yarinyar ce… Wannan yarinyar daya gani tare da wani saurayi a safiyar da zai je neman Saifuddeen. Me take yi a waje a daren nan? Me ya same ta?1

Tambayoyin suka d’arsu a ransa daidai lokacin da abinda ke dunk’ule a hannunta ya fad’i…

Sannan daidai lokacin da mataki na uku wajen canja k’addarar rayuwarsa ya wanzu!1

Wata irin k’addara!Da misalin k’arfe takwas da rabi na ranar laraba, Jidda ta nufo hanyar zuwa shamaki don isa ga Suraj dake jiranta acan.+

Zuciyarta fes take da tunanin cewa ta gama da zancen jinin daya b’ata d’ankwalin Baddo balle kuma littattafanta, don bata saurari maganganun Sadiya ba a d’azu ta had’a daga d’ankwalin har littattafan ta k’one su tsaf! A yadda tunaninta ya nuna mata gwara tace dasu Baddo jakarta ce ta fad’i gabad’aya aka rasa komai na ciki har kuwa d’ankwalin.

Idan yaso ta daurewa mitar Baddo ta kwana biyu kafin ta hak’ura ta gama, sannan kuma ta jurewa wulakancin Jamila ma kafin ta bata kud’in sake siyan wasu littatttafan tunda itama bata san me ke faruwa ba, don a ranar da suka tono asirin nan bayan sun dawo gida ba yadda Jamilan bata yi da ita akan ta nuna mata abinda ta gani a hannunta ba amma ta kafe cewar babu komai, haka ta hak’ura ta rabu da ita.

Ta yanke bin wannan shawarar ne ba wai don ta tsorata da abinda tayi ba, sai don gudun kar barin jinin ya haifar da wani tasirin da zai shafe su, taje garin taimakon wanda bata sani ba ta jawowa kanta matsala. Saboda haka a yanzu matsalar Suraj ce kawai a gabanta, kuma shima ta yanke shawarar janye k’udirinta akansa, zata tsaya taga iya gudun ruwansa tukunna kar tazo tana dana sani daga baya.

Yana tsaye a jikin wannan doguwar katangar da kullum suke had’uwa k’asanta, don tun farko ya zab’i wajen ne saboda ba hanya bace babu wulgawar mutane sosai.

Yana sanye da farar riga mai tambarin ‘Reebok’ da aka rubuta cikin kalar bak’i, hasken wayar da yake dannawa ya haske fuskarsa dake murmushi yana kallon wayar, wani b’angare na zuciyarta ya shiga narkewa a take, wa yace ne da zata iya gangancin rabuwa da Suraj?

“Barka da zuwa.” Ta fad’a tana girgiza tafin hannunta akan fuskar wayar tasa, saboda har ta tsaya bai nuna alamun ya san da isowarta ba.

Sai ya d’ago ya kalle ta sannan a lokaci guda murmushin dake fuskarsa ya baje, ya kashe hasken wayar sannan ya mayar da ita cikin aljihu.

“Ke zan yiwa sannu da zuwa da kika k’araso yanzu.”

Bata damu da rashin fara’ar tasa ba tayi murmushi tana fad’in.

“Haka ne kuma fa…  To ka iso lafiya? Ya mutanen gida?”

“Lafiya.” Ya amsa a tak’aice sannan kuma yayi shiru.

Sai ta cije lebb’enta tana cigaba da kallonsa, don wannan bak’on yanayin nasa ya tabbatar mata cewar akwai abinda ke shirin faruwa, Allah yaso ma bata b’ata lokacinta wajen yin kwalliya ba tunda a shak’e yake.

“Nace miki zamu yi magana idan nazo ko?”

Ta gyad’a kai tana cigaba da kallonsa, ya gyara tsayuwarsa kad’an lokacin da iska ta buso mata k’amshin turarensa.

“Dama akan maganar da muka yi ranar nan ne, gaskiya Jidda na duba naga cewa abubuwa ba lallai su cigaba da tafiya tsakanina dake ba, saboda kin san kowanne irin zama a duniyar nan hatta na aure kuwa ana yinsa ne kan turbar ‘Yarda’.

Don haka ina ganin idan har baki yarda dani tsawon shekarun da muke tare ba, to bana tunanin nan gaba ma zaman mu zai iya d’ore…”2

“Na fa baka baka hakuri.”

Muryarta ta katse shi kai tsaye don a baiyane yake cewa bata shirya musayar baki dashi a yau ba.

Sai ya girgiza kansa.

“Ai babu zancen hakuri anan Jidda, kin riga kin fad’i ra’ayinki akaina ne kuma na yarda…”

Ya d’anyi shiru kafin ya cigaba.

“… Shi yasa nake ganin lokaci yayi da zan yiwa iyayena biyayya, don tun farko dama akwai wata ‘yar uwarmu da suke son had’ani da ita amma na bijere na maida hankalina kan ki, so idan ke baki yarda dani ba ina ganin watakila ita zata fahimce ni…”4

STORY CONTINUES BELOW

“Kana nufin zaka rabu dani kenan?”

Ta sake katse shi ba tare da jiran k’arshe ba, kalaman suka fito da tsananin mamaki daga idanunta yayin da a lokaci guda jikinta yayi shafal kamar fallen takarda, sannan zuciyarta ta shiga bugawa da kowanne irin ambato na kar amsar sa ta zama gaskiya…

Amma sai ya gyad’a kansa yana kallonta.

“Haka nake nufi, saboda ace unguwa kad’ai ba zaki iya raka ni ba Jidda meye amfanin irin wannan zaman? Gwara rabuwarmu kawai ita zata fi, kuma wannan zuwan ma dana yi na gaya miki ba k’aramin mutunci bane da zaki tabbatar cewa ni na baki dukkan yardata, da nayi niyya sai dai kawai ki daina ganina ko kum…”1

Ai bai ka ga rufe bakinsa ba wani irin mari mai sauti ya sauka a fuskarsa, idanunsa suka rufe tare da marin kuma ya kasa maido su ya bud’e, ba wai don zafinsa ba sai don yadda abin ya daki zuciyarsa, ta yaya hankali zai tab’a tunanin cewa yarinya kamar Jidda zata iya samun k’arfin gwiwar marinsa?3

Mamaki ya tsarga tun daga kwakwalwarsa har cikin zuciyarsa, don ko kad’an bai tab’a kawo hakan a matsayin martaninta ba, yayi zaton zai yi nasarar tsorata ta don ta yarda ta bishi wajen da zai cimma manufarsa akanta ne kawai, saboda ya dad’e da fahimtar cewa tana mutuk’ar tsoron rabuwa dashi shi yasa yayi amfani da wannan hanyar.5

“Dama Jamila ta fad’a min…” Muryarta ta fito a tar tana kallonsa.

“Ta dad’e tana gaya min cewa wasa kawai kake yi da hankalina in rabu da kai amma na k’i yarda da ita, nak’i bari zuciyata ta tab’a ganin laifinka, kullum tunani na mai kyau ne a kanka, kullum zuciyata na baka uzuri… Sai gashi yau da bakinka ka rushe komai, ka nuna min cewa abinda take fad’a gaskiya ne.”

Sai a lokacin ya bud’e idonsa sannnan ya juyo ya kalle ta, idanunsa a k’ank’ance cike da fushin da har ya sanya mak’ogwaronsa rawa yace.

“Ni kika mara Jidda? Mari? Ni?”

Bata ko fahimci me yace ba ta cigaba da kallonsa kawai, a cikin ranta, tana jin kanar wani ne ke sa guduma yana rushe dukkan wannan yardar da zuciyarta ta bashi, sai kuma ta girgiza kanta sannan tace.

“Allah zai saka min tsakanina da kai…”

“Babu abinda ubangiji zai saka miki akaina Jidda kuma wallahi kinyi kad’an inyi asara biyu akanki…”

A lokaci guda abinda bata tab’a tunani ba ya faru, Suraj ya cafki hannunta na dama, sannan na hagun kafin ta kai ga iya kare kanta, a ranar ta d’aura ‘Fullo’ ne a hannunta maimakon wuya, saboda haka sanda ya rik’o hannun nata da k’arfi yaji wani abu na kokarin ji masa ciwo sai kawai ya fizge shi.2

Fullo ya fad’o kan dandaryar wajen daidai lokacin da ya sa d’aya hannunsa ya rufe bakinta dake shirin kwala ihun neman agaji, sannan ya shiga magana yana kallon kwayar idanunta dake fallasa irin girmansu.

“Idan ban same ki a yadda nake so ba Jidda, baki isa kuma ki mare ni in tafi da asara biyu ba wallahi…”

Ko’ina a jikinta ya shiga rawa yayin da wani irin azababben tsoron da bata tab’a sanin da wanzuwarsa a duniya ba ke dokawa a cikin k’irjinta, amma sai tayi k’arfin halin fara k’ok’arin kwace kanta, k’ok’arin dake k’ara sanyawa ta ji ta a jikinsa…

“.. Kin zata duk wata d’awainiyar da nake akanki banza na ke tarawa ko kuma kin zata kamar ni zan iya aurenki ne?..”

A lokaci guda idanunta suka cika da kyallin kwalla, don maganar ta daki zuciyarta da dukkannin irin illar da zata iya yiwa zuciyar ‘ya mace.

Sai dai kafin Suraj ya kai ga sake magana ko kuma cimma wani abin, ubangiji ya jefo wasu tsofaffi biyu dake gadi a wajen suka karyo kwana

“Su waye anan wajen?”

STORY CONTINUES BELOW

Muryar d’aya daga cikin mutanen ta fad’a kafin hasken sabuwar torchlight d’insa ta haska tar! akansu.

“La’ilaha ilallahu mahammadur rasulullahi…”

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…”

Wad’annan maganganun suka sanya shi sakinta a take sannan ya shiga kokarin kare hasken daga fuskarsa.

Jidda na jin hannayenta a iska idanunta suka kai kan Fullo dake yashe a k’asa, sai kawai ta sunkuya cikin tsananin rikicewa da rud’ewa ta d’auke shi sannan ba tare da ta jira k’arasowar mutanen ko wani abu ba ta juya da matsanancin gudu ta bar wajen.

Ko’ina a jikinta rawa yake sannan zuciyarta na bugawa kamar zata faso daga k’irjinta, Allah ya sani ko lokacin rasuwar mahaifiyarta bata taba tsorata irin wannan ba don haka gudu kawai take tana share hawaye da fatan ta ganta a k’ofar d’akinsu ta shige ta rufo sakatar net d’in, sannan ta k’udundune cikin zanin rufarta ko hankalinta zai dawo daidai.

A wannan lokacin ne kuma ta bugu da wani mutumi dake tahowa ba tare da ma ta ganshi a gabanta ba, watakila shima kuma idanunsa a rufe suke don yaci ace ya kaucewa gudun nata. Jakar hannunsa ta fad’i sannan kayan ciki suka tarwatse a k’asa, yaja da baya sannan ta d’ago ta kalle shi daidai lokacin da tsoron yadda jikinta ya sake had’uwa dana wani yasa ta saki Fullon dake hannunta ba tare da ta sani ba.

Kuma anan ma bata tsaya jiran faruwar wani abu ba ta sake fyallawa da gudu tayi hanyar isa ga makwancinsu.

Madaki ya juya ya bita da kallo cike da mamakin abinda ta gani ya tsorata ta da kuma mamakin b’arnar da tayi masa ba tare da ma ta lura ba, sai kawai yayi tsaki a hankali sannan ya juyo ya tsugunna ya shiga kwashe kayansa, a cikin tsilli-tsilli mutanen dake zirga-zirga babu wanda ya lura da waye shi saboda sha’anin dare.

Kwakwalwarsa ta koma kan tunanin da yake yi kafin yarinyar ta katse shi, tunanin yadda zai k’ask’anta Fulani ta san cewa ita d’in kamar kwaya ce guda d’aya akan teburinsa da zai iya saka yatsa d’aya kawai yayi bal da ita!

Ya tattara komai ya mayar cikin jakarsa, komai na nufin har da Fullon Jidda data yar a wajen ba tare da ya lura dashi cikin kayansa ba..!1

***

A Wannan Daren.

K’asaitaccen falon na Fulani ya d’auki wani irin shiru mai d’auke da tambarin shakka da kuma tsoro, don in banda k’arar kukan Ac baka isa ka tsinci ko sautin fitar numfashin mutanen dake d’akin ba wanda ke tsugunne su uku kan tattausan carpet d’in d’akin, sannan kusan tazarar mita biyar tsakaninsu da wajen wasu saitin kujeru da aka jera kamar shima wani falon ne daban.

Fulani na zaune kan d’aya daga cikin kujerun ta juya musu baya tana amsa wayar amintacciyar aminiyarta Hajiya Bilki, matar wani d’an majalisa dake cin karensa ba babbaka a fadar gwamnatin tarayya.

“Me na gaya miki ne wai Hafsatu? Ta yaya zaki had’a aikin mak’udan kud’ad’e ne dana k’ananan kwabbai? Kin sani a miliyan biyu kad’an ne bai k’arasa ba wajen had’o wannan aikin, na nuna cewa zan iya hak’ura da bawa wacce tayi oda in baki duk don ki sami kan yaron nan, amma me kika ce? Wai kina ganin kin samu garantin malami daga k’asar Gabon zaki fara gwada nasa tukunna. Yanzu ai ga tasirin aikin nasa nan ace har kwanaki hud’u da zuwan Madaki garin, amma bai tako k’afa inda kike ba.”

Fulani ta cije lebb’enta na k’asa kawai tana saurarenta, kafarta ta hagu banda girgizawa babu abinda take faman yi, don tun wayewar garin yau, ranta ya kai k’ololuwa wajen b’aci ganin abubuwa na canja salo daga samun nasararta, a baya ko Madaki bai shigo b’angarenta ba, ta kan had’u dashi a wajen Mai martaba har su gaisa, amma wannan karon in banda d’uriyar labarin zuwan nasa bata ga ko bayan takalminsa ba.

Bayan tabbaci ne cewa layar farin zakarar da aka binne zata juyo da tunaninsa kanta, don har cikin zuciyarta bata da haufi akan zancen malamin nan tunda gashi asirin kiranye daya fara bata akansa yaci, to me zai hana sauran kuwa?

STORY CONTINUES BELOW

Haufinta d’aya a duniya shine ‘Turaki’ ta san halinsa sarai, ta san zai iya bin kowacce hanya don dak’ushe ta, amma wannan sirrinta ne, sirrin da ko Hajiya Bilkin bata isa ta ji shi ba. Tana yin komai a duniya ne saboda ‘ya’yanta don haka babu wani dalili kuma a duniyar da zai sa ta iya b’ata su a gaban kowanne mahaluki.

“A bar duk waccan zancen Bilki, na yanke shawarar karb’a kawai kuma wallahi da zan iya ma da kaina zanyi aikin nan, don a yanzu ina tsoron akasi.”

“Babu akasi a wannan aikin Fulani, abinda kake kokwanto akansa shi ake samun akasi amma banda wannan. Ki kwantar da hankalinki kawai, a nemo miki matar da bata tab’a haihuwa ba, ita zata je ta kafa aikin a k’ark’ashin gadon da aka tabbatar Madakin ya kwanta.

Bayan haka, sharad’in mai sauki ne, akwai ruwa mara yankewa a jikinsa kuma zai dinga zuba ne da d’igo guda duk bayan wani lokaci, daga sanda d’igo guda kuwa ya zuba a k’asan gadon nan Fulani, Madaki ya zama naki don ba zai k’ara yarda da wata magana a duniya ba in ba wadda ta fito daga bakinki ba.”1

“Kin tabbata Bilki?”

Daga cikin wayar Hajiya Bilki ta kyalkyale da dariya kafin tace.

“Bari in fasa miki wani sirri, zaki iya tuna sanda muka je gidan k’anwata dake nan cikin Abuja?”

Ta yaya zata manta wannan ziyarar? Don taga abinda ba zai tab’a goguwa a ranta ba, yadda k’anwar Hajiya Bilkin ke juya mijinta kamar d’an da ta haifa, don suna gidan ta kira shi a waya ya baro meeting d’in da yake mai muhimmanci ya taho gida bata kud’in wasu kaya da Hajiya Bilkin zata siyo mata daga Dubai, suna zaune amma kamar bai san da su ba, ‘To’ kawai yake amsawa matarsa da duk abinda tace.

Abin yayi mutuk’ar burge ta, har ta nemi da a samo mata irin sirrin itama bayan sun fito, amma sai Hajiya Bilkin tayi dariya da cewar _’Wannan ba irin naku bane Fulani, ku da zaku karb’i sarauta kusa-kusa? Ai sai a sauke ku ko kuma mulkin ya dawo kanki, ya hana ki sha’anin gabanki..’_

“In har kin tuna, to wannan shine irin aikin dana sa aka yi mata.”

Fulani ta dad’e tana k’arb’ar tarin alk’awura akan Madaki kuma tana fad’awa cikin mafarkinsu, amma a hak’ik’anin gaskiya bata tab’a jin zuciyarta ta doka tsallen yarda kan d’aya daga cikinsu kamar yadda tayi a yanzu ba.

Saboda haka ta yanke duk sauran maganar bakinta da cewar.

“Shikenan, ki sako Idrisu (d’an aikensu) dashi a jirgi gobe, zan ninka miki kud’insa.”

Hajiya Bilki ta sake kyalkyalewa da dariyarta kafin ta katse kiran.

Isowarki lafiya uwa bada mama,

Lafiya baya goya marayu,

Lafiya dai tufaniyar gabas!

Cewar Jakadiya sanda ta zagayo ta zauna a kujerun dake gabansu.

“Jakadiya.” Muryarta tar! ta kira sunanta ba kamar d’azu da bak’in ciki ke sata sark’ewa ba.

“Alheri ya isar miki!” Jakadiyar ta amsa.

“A tsayar da komai, a samo min muk’ullin masaukin Madaki zuwa gobe, shi kad’ai nake buk’ata!”

***

WASHEGARI.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un… Yanzu dan Allah Jidda abinda ya faru kenan?”

Jidda ta juyar da kanta gefe sannan ta ja majina cikin hancinta, idanunta a kumbure suke suntum na irin kukan data sha a daren jiya, kukan da rabon data yi irinsa tun lokacin rasuwar mahaifiyarta.

Ta girgiza kai tana kallon sauran cincirindon mutanen dake gabansu, don suma d’in suna zaune ne kan bokitinsu a gaban dogon layin d’iban ruwan dake gabansu. Tayi kwafa sannan tasa hannu ta d’auke wata kwallar dake shirin taruwa a idonta.

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi Sadiya, na rantse da Allah Suraj ba zai ci zarafi na a banza kuma in kyale shi ba, dama ina d’aga masa k’afa ne saboda tsoron kar in rasa shi kawai amma tunda wannan abin ya faru, wallahi babu abinda zai hana ni k’untata masa nima.”

“A’a Jidda, kina gani fa yanzu marinsa kawai kika yi ga abinda ya biyo baya, sannan kuma baki da tabbacin cewa shima ya kyale ki ne to ina ga kuma kije ki k’ara wani abin?”

Ta sake girgiza kai sannan ta juyo ta kalle ta.

“Ta hanyar da zan fito masa ba zai tab’a gane nice ba Sadiya, don ba zai k’ara ganina ba a rayuwarsa sai dai ko tsautsayi, amma wallahi abinda zan masa sai yaji ciwo fiye da wanda ya sanya ni a ciki.”

“Me zaki yi masa?” Ta tambaya tana kallonta, sai dai bata amsa ba ta sake juyar da kanta tana kallon wata tsageruwar yarinya dake zuba rashin kunya a can gaban fanfon, tana zage-zage akan an matsar mata da bokiti baya.

Sadiya tabi fuskarta da kallo tana k’ara jinjina girman al’amarin, don bata tab’a ganin abinda ya raunana zuciyar Jidda har ta zubar da hawaye irin haka ba, kamar  zata ce wani abin sai kuma ta fasa.

Kusan awar su guda a wajen kafin su samu su d’ebi ruwan su tafi, inda kuma yinin ranar haka Jidda ta shafe shi cikin rashin walwala, tun Baddo na fad’an wani irin ciwon kai ne da zai hana ta sukuni haka har ta gaji tayi shiru.

Jamila kuwa kawai kallonta take, don Allah ya sani ita bata yarda da zancen wani ciwon kai ba, tun da ta dawo musu jiya a firgice daga d’akinsu Sadiyan da ta tafi tace wai kanta ne ke ciwo zuciyarta bata karb’i zancen ba… Don ta riga ta san halin Jidda tsaf! Babu wani ciwo a duniyar nan da zai saka tayi irin kukan da har zai hana ta bacci sosai jiya.

Wajen bayan sallar isha’i ne tana taya Sadiya shanyar kayan Hajiyarta data wanke, idanun Sadiyan ya kai kan hannunta daya fito ta cikin hijabi mai hannun data saka, shatar ciwo ce a wajen don har fatar ta taso.

“Me ya same ki a hannu?”

Babu alamun Jiddan taji ta, don tun safe in banda tarawa da d’ebewa babu abinda kwakwalwarta ke yi, neman hanya kawai take ko wace iri da zata d’auki fansa akan Suraj.

“Jidda ciwo kika ji a hannu?”

Sadiyan ta sake tambaya, sai a lokacin taji ta, ta juyo ta kalle ta kafin ta sunkuya ta kalli hannun nata.

A lokacin ne kuma gabanta ya fad’i kamar irin fad’owar jirgi daga sararin samaniya sannan kuma zuciyarta ta buga.

Fullo… Ina Fullonta yake? Shi ta d’aura a wajen… Suraj ya fizge shi jiya, amma kuma ai ta d’auke shi bayan nan… Kuma har lokacin da ta taho ta buge wannan mutumin yana hannunta, tsaya!… Kar dai a wajen ta yarda dashi, don bata iya tuna sanda ta ganshi baya nan.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… Sadiya na yar da Fullo, wallahi ina jin na yar dashi.”

“Kin yar dashi? A ina?” Sadiyan ta tambaya da tsananin mamaki itama.

Sai ta saki d’ankwalin data d’auko daga cikin bokitin da sauri tana kallonta idanu a zare. Ya akayi bata lura cewa tun safe baya tare da ita ba? Zuciyarta ta sake tsinewa Suraj don duk tunaninsa ne ya d’auke hankali daga kwakwalwarta.

“Watak’ila sanda na taho na buge wani mutumi ne a daidai wajen filin Uwar Soro… Ya salam! Anan ne ma wallahi, Dan Allah zo ki raka ni muje in duba.”

Dubawa? Ta yaya zasu ga abinda ya fad’i tun jiya a hanyar da mutane ke wucewa? Zuciyar Sadiya ta ayyana hakan amma sanin irin muhimmancin da abin yake a wajenta da kuma yanayin da ta tashi dashi a yau d’in yasa ta ajiye kayan hannunta cikin bokitin itama sannan tabi bayanta.

Sai dai ba irin neman duniyar da basu yi ba a harabar filin Uwar soron amma babu Fullo ba dalilinsa, har cikin hanyar wucewar ruwa dake can gefe Maijidda ta dinga lek’awa amma babu ko dutse mai irin kyallinsa, zuciyarta ta shiga rawa a k’irjinta, don Allah ya sani bata iya hango rayuwarta a gaba ba tare da abin nan ba.

STORY CONTINUES BELOW

Tun Sadiya na binta har dai ta gaji ta samu k’asan wata rumfa a can k’arshen filin ta zauna, zuwa can Jiddan itama ta k’araso ta same ta anan, fuskarta sai gumi take kamar ba iska ake yi a wajen ba.

“Anya Sadiya mutumin nan bai had’a da Fullo cikin kayansa ba, don sanda na buge shi jakar hannunsa ta fad’i k’asa har kayan ciki suka zube.”

“Ba lallai ba fa, kin manta nan hanya ce? Mutane fa suna wucewa, sannan abu tun jiya zai iya yiwuwa wani ya gani ya d’auka.”

Tabbas hakan mai yiwuwa ne amma zuciyarta bata son ta karb’i shawarar, bata son ta yarda cewa Fullo yana wajen da baza ta iya hasashe ba, saboda haka ta bud’a baki da niyyar fad’in wani abu amma muryar wani tsoho dake gefe cikin tarin kayan sak’ar igiyarsa ta katse ta.

“Ashsha! Yarinya ashe kece kika buge mutumi nan jiya? Baki kyauta ba kuwa don baki ko bashi hak’uri ba kika gudu, haka ya tsugunna ya kwashe kayansa anan kafin ya tafi.”

Ya tafi. K’arshen zancen tsohon ne kawai ya tsaya a kwakwalwar Jidda, kuma kamar iya abinda ya fad’a kenan, sai ta matso da sauri ta kama icen makarin rumfarsa tace.

“Ina ya tafi? dan Allah Baba kaga inda yayi? So nake in bashi hak’uri dama.”

Bakinta ya fad’o hakan don kawai ta sami abinda take so. Sadiya ta kalli tsohon cike da mamakin yadda Jidda ke sauraronsa don a baiyane yake k’arara cewa mai rangwamen hankali ne, kowa a masarautar ya riga ya san shi, nan gurin ne makwancinsa cikin tarin kabar da yake sak’ar igiya dasu.

“Da kuwa kin kyauta..” Cewar tsohon.

“… Nan wajen ofishin buga hatimi naga ya nufa, watakila zaki same shi acan tunda hanyar ba mai b’ullewa bace.”

Ba tare da wani dogon tunani ba kuwa, zuciyar Jidda ta amince da shawarar neman inda mutumin yake don ta sami Fullonta, saboda tunaninta yafi k’arfi kan cewa zai iya had’a shi cikin kayansa ba tare da ya lura ba.

Sai dai da ace bata karb’i wannan shawarar ba, da k’addarar dake shirin faruwa a wannan daren bata zama mai b’ullewa ba.3

***

A daidai wannan lokacin, Madaki ya baro sashen ajiyar motoci zuwa masaukinsa, shigowarsa kenan daga wajen aikin da ya kawo shi, don a yau meeting d’in da suka gudanar ya d’auki zafi sosai, tun jiya Habibu da kuma wasu mutum biyar daga can ma’aikatar tasu ta Lagos suka iso tare da ‘George’ wanda ake zargi da duk wata k’ulleliya da kuma ‘yan sandan da yake hannunsu.

Don haka ba k’aramin rikicewa mutanen suka shiga ba ganin yadda abubuwa ke fitowa ana neman tona musu asiri, kuma yaso kwarai ace sun kammala meeting d’in a yau koda kwana zasu yi, amma azababben ciwon k’irjin da ya rik’e shi tun yamma ya tsaida komai, don ya riga ya sani cewa ciwonsa ne ke shirin tashi kuma ba zai yi gangancin nuna rauni ko kuma fallasa sirrinsa a gaban ma’aikatansa ba.

Yaso bin su Habibu guest inn da suka sauka wanda yake kusa da ma’aikatar, ya samu d’aki inda zai k’ulle kansa yayi jinya ba tare da takurawar kowa ba, amma ba zai iya ba… Ba zai tab’a iya tsallake umarnin Mai martaba ba, ya riga yasa an tanadar masa masauki don haka ba zai tab’a jin dad’i ba in har ya neme shi bai ganshi ba.

Shi yasa dole ya k’ok’arta ya dawo masarautar, kuma a lokacin daya k’araso k’ofar masaukin nasa dake harabar ofishin buga hatimi, jikinsa ya riga d’auki zafi sosai sannan kansa na juyawa da jiri, da kyar ya iya zaro muk’ullin sashen daga cikin jakar takardun hannunsa ya zura shi a k’ofar, murd’awa d’aya kawai ya bud’e ya shiga sannan ya zare muk’ullin ya maida shi ta ciki ya k’ulle k’ofar.

A falon ya ajiye jakarsa sannan ya nufi cikin d’aki inda zai sha magungunan dake cikin akwatinsa kafin ya kwanta.

A lokacin ne kuma ‘yar aiken jakadiyar Fulani, wadda akayi dabarar shigo da ita ta tagar band’akin falon kafin dawowarsa, ta fito daga bayan labulen da take lab’e a cikinsa.

Ba tare b’ata lokaci ba kuwa ta bud’e k’ofar d’akin sannan ta zare muk’ullin ta fito.

Zuciyarta na dukan tara-tara ta damk’e muk’ullin a hannunta sanda ta biyo harabar wajen dake da duhu saboda k’arancin fitilu, fatan ta a lokacin d’aya ne… ta isa ga Jakadiya ba tare da wata matsala ba don ta sami kud’inta.

Sai dai bata ko yi rabin tafiya a harabar ba, zuciyarta ta doka sakamakon wata murya da taji a bayanta na rangad’a sallama.

Ta juya daidai sanda idanunta suka gane mata siffar wata yarinya tsaye a bakin k’ofar shiga sashen na Madaki. Mamaki ya kama kowacce gab’a ta jikinta, Mace a d’akin Madaki? A daren nan? Me hakan ke nufi?

A take kwakwalwarta ta shaida mata cewa wannan ba k’aramin labari bane da zai jawo mata k’arin kasafi a kud’inta, don haka ta lalubo ‘yar k’aramar wayarta ta shiga kiran lambar da zata sada ta da Jakadiya Babba.

A wannan lokacin ne kuma Jidda ta kai hannu kan k’ofar don ta kwankwasa jin ba’a amsa sallamar da take jerawa ba, sai dai ga mamakinta tana tab’a k’ofar ta koma tayi ciki a hankali.

Ta d’an tsaya tana kallonta da mamaki kafi tunaninta ya yanke shawarar kawai ta shiga ciki, don watak’ila idan babu kowa zata iya ganin wannan jakar ma ta d’auki abinta ta fito kawai, amma d’aya b’arin zuciyarta mai hankali ya shiga gargad’inta da hakan, don har maganganun Sadiya kafin su rabu sai da ya tuna mata.

_”Wallahi ba zan biki ba Jidda, kina da tabbacin cewa da kin je kin tambaye shi ne zai d’auko jakar ki duba? ko kuma ba kya tsoron ma zuwa wajen mutumin da baki sani ba wannan daren?” _

Sai dai kamar koyaushe da zuciyarta da bata d’aukan shawarar data dace, ta ture wannan tunanin sannan ta kutsa kanta ciki, daidai lokacin da ‘yar aiken Jakadiya Babba ta gama yi mata bayanin me ke faruwa ta wayar dake kare a kunnenta.

Daga can b’angarenta, Jakadiyar tayi wani murmushin dake baiyana tsantsar jin dad’in labarin sannan ta kada baki tace.

“Bita ki rufo k’ofar!”Ki gayawa Fulani da k’annenta (sauran matan Sarki) cewa Mai martaba zaiyi tafiya gobe, zai je check-up k’asar India, kuma da misalin k’arfe takwas na safe jirgin da zai hau zai tashi, don haka yana buk’atar ganinsu suyi sallama yau da dare saboda ba lallai su iya ganinsa a goben ba.

Don yace min bayan sallar asuba zai je ya gana da Madaki, kuma da alama maganar da zasu yi mai muhimmanci ce, saboda yace shi zai je masaukin nasa da kansa ba sai an kira shi ba.

Ranki ya dade, wannan itace sak maganar da Jarmai ya shaida min a jiya da safe kafin in zo in sanar dake nima.”

Cewar Jakadiya Babba a lokacin da take durk’ushe gaban Fulani, a wannan daren da muk’ullin sashen Madaki ya iso garesu, kuma bayan dawowar Fulanin daga yiwa Mai martaba sallama.

Fulani ta k’ank’ance ido cikin nazari tana kallon muk’ullin dake ajiye akan teburin gabanta, tunani da yawa na giftawa a cikin kanta amma ta kasa tattare su waje guda, don abinda ke faruwa wani abu ne da bata tab’a mafarkinsa ba balle har ta sa ran Allah zai nuna mata faruwarsa.

“Rakiya…”

Karo na farko a tarihin rayuwar Jakadiya Babba, taji harafan sunanta ya fito daga bakin Fulanin, sai ta k’ara sunkuyar da kanta cikin tsananin girmamawa sannan ta amsa.

“Allah ya dafa miki.”

“Kika ce yarinya ce?”

“Haka Saratu ta tabbatar mun ranki ya dad’e, kuma tace kanta tsaye ta shige d’akin babu alamun wani tsoro.”

Fulani ta gagara had’iye abinda ke bakinta, don kwakwalwarta ta kasa yarda da wannan al’amarin, ta gagara yarda cewa Madakin data sani zai iya neman mace a k’ark’ashin rufin masarautar ubansa ko da kuwa hakan halinsa ne. Dole ne dai akwai wani abu daban da ya kai yarinyar wajensa, sai dai ta san hakan bashi ya kamata ya dame ta ba, abu mai muhimmanci shine suyi amfani da wannan damar da lokaci ya basu kawai.

“Mace a masaukin Madaki, k’ofa a k’ulle, ga mu’k’ullin a hannun mu, sannan Mai martaba zai ziyarce shi da sassafe, me hakan ke nufi Jakadiya?”

Jakadiya Babba tayi gyaran murya cike da zumud’i kafin tace.

“Nasarar da bamu tab’a shirya mata ba ranki ya dad’e… Don a tarihin masarautar nan tun asali, ba k’aramin laifi da kuma cin fuska bane a kama wani da neman mace a cikin masarauta, kuma Mai martaba ya fimu sanin hakan don ance a zamanin baya ma har hukuncin kisa ake yankewa mai wannan laifin.

Kuma haka in har muka yi nasara to tabbas zamu sami wani abu da bamu tab’a tsammani ba, don darajar Madaki zata zabge a idanun Mai martaba sannan ko bai yanke wani hukuncin mai tsanani akansa ba, hakan zai zame mana kamar sharar fage yadda nan gaba duk abinda zai yi bayan an kafa asirin nan, Mai martaba ko wani ba zai tab’a zargin da sa hannunki ba.

Sai dai kuma ba lallai ne wannan dalilin da muke hange shi ya kai yarinyar wajensa ba, amma ranki ya dad’e mu zamu iya siffanta hakan a idon Mai martaba, zamu iya bashi yak’inin da ko shi kansa Madakin bai isa ya fidda kansa ba.”

Fulani ta juyo ta kalle, idanunta na haskawa da tsantsar nazari sannan bakinta ya furta tambayar.

“Ta yaya?”

Sai Jakadiya Babba tayi murmushi mai zurfi sannan ta sake gyara tsugunnonta, zuciyarta na gaya mata cewa zata bada shawarar da ko bayan ranta Fulani zata yi alfahari da sadaukarwarta a gare ta.

***

“Assalamu Alaikum.”

Muryar Jidda ta sake rangad’a sallama daga jikin wata kujera dake farkon falon, sai dai kamar yadda sauran sallamomin nata suka baje a banza ba tare da an amsa mata ba, haka wannan ma ta tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Ta d’an ja tsaki a k’asan numfashinta lokacin da sanyin Acn d’akin ya buso mata da wani k’amshi da ta kasa tantance inda ta sanshi, don har yanzu zuciyarta ba’a nutse take ba balle ta shiga lalube a kwakwalwarta ko zata iya tunawa.

Watak’ila gaskiya Sadiya take fad’a, tsohon nan bashi da hankali bai san inda mutumin nan yayi ba, babu alamun akwai wani anan.

Zuciyarta ta ayyana mata hakan sannan ta juya da niyyar fita, dare ma ya fara yi ta san yanzu Baddo zata fara nemanta. Ta isa ga k’ofar ta sa hannu ta murd’a marik’inta, sai dai me? Bam! take ba alamun bud’uwa.

Sai kuma ta tuna ai ciki ta turo sanda zata shigo, don haka ta sake murd’awa sannan ta jawo ta… Babu abinda ya canja.

Mamaki ya kamata, ko dai bata nan ta shigo bane, ta juya kowanne b’angare na d’akin bata ga wata k’ofar ba sai manya- manyan tagogi dake rufe ruf da dogwayen labulaye. Gabanta ya d’an fad’i don babu wata k’ofar kuwa in ba ita ba, amma me ya faru? Ko dai cijewa take yi ne?

Sai ta tattaro dukkan k’arfinta ta shiga jijjiga ta amma ko kad’an babu wata alama ta cewar zata bud’e ko tana shirin bud’ewar, sai ta juya da sauri wajen tagar dake dama, hannunta ya shiga d’age labulen jiki don ta bud’e ta fita ta nan, sai dai hannayen nata suka tsaya cak jin k’arafa a jiki kafin a tadda gilasan (burglers), ta koma wajen d’aya tagar, itama dai haka take… Gumi ya fara tsatstsafo mata. Sai ta juya ta sake kallon girman d’akin, k’ofofi uku ne a jikinsa, d’aya ta shiga wani d’an corridor da ko ba’a gaya mata ba ta san d’aki ne wannan.

Saboda haka da saurinta ta nufi d’aya k’ofar dake b’arin dama, hannunta na rawa ta bud’e ta, sai dai itama me? Wani d’an madaidaicin kitchen ne da yasha saitin drawers masu kyau, ta rufo shi da sauri sannan ta nufi d’aya k’ofar, ko’ina a kwakwalwarta fata yake ita ta kasance wata hanyar fita ce.

Amma fatanta ya ruguje har garinsa sanda da tayi arba da b’andaki, hasken fitilar ciki ya dallare tar akan fararen tiles d’insa, sai ta mayar da ita ta rufe yayin da gabanta ya shiga bugawa da gaske.

Ya zata yi da rayuwarta in har da gaske k’ofar nan tak’i bud’ewa? Anan zata kwana kenan? Tunda wa zai zo ya bud’e ta a daren nan? Ta riga ta gargad’i Sadiya cewar kar ta sake ta gayawa su Baddo inda ta tafi, kuma ta san in har ba safiya ce tayi ba, ba fad’ar zata yi ba.

K’afafunta na gurd’ewa a cikin carpet d’in ta sake komawa wajen k’ofar, ta murd’a ta jijjiga amma babu abinda ya canja, hannanyenta suka shiga rawa akan marik’in k’ofar, komai fa zai iya faruwa idan bata bud’e ba… Ta ayyana a ranta, don waje irin wannan da ba mutane to tabbas ne baza ‘a rasa aljanu ba… Kuma ta san in har ta cigaba da kasancewa ita kad’ai, ko ita kanta baza taga laifin duk aljanin da ya shiga jikinta ba don ita ta kawo kanta.1

Idonta ya hasko mata yadda mata ke tada aljanu suna hauka a makarantar bokonsu, sai ta shiga girgiza kai sannan ta zube a k’asan k’ofar, hannayenta dai na rik’e da handle d’in, idonta ya fara ja sannan kwalla ta cika taf a cikinsu, dama kukan data sha jiya na abinda Suraj yayi mata ba gama tafiya yayi ba.

Ta cigaba da zama a wajen hannayenta a d’age tana rarraba idanunta waje-waje cikin falon. A lokacin ne idonta ya kai kan wata jaka dake yashe akan kujera, tunanin cewa zata iya ganin Fullonta a ciki ya d’arsu a ranta, sai ta saki k’ofar ta mik’e da sauri zuwa wajenta, in har ta ganshi to kamar rabin matsalarta ta gushe ne, zata iya jure koma meye tunda ta san baza’a barta ta mutu a ciki ba.

Ta zuge zif d’in farko amma babu komai sai takardu fal, ta firfirto dasu ta bincike har kasan aljihun amma babu ko dutse balle ta san ran shine, idonta ya kai kan rubutun dake jikin takarda d’aya, wani tsararren turanci ne data tabbatar baza ta tab’a fahimta ba, sai dai a saman mafi yawancin takardun akwai wani tambari mai d’ankaren kyau da aka yi da kalar ruwan gwal, a k’asansa an rubuta.

STORY CONTINUES BELOW

Royal K Group of Companies.

Ta tattara su ta mayar sannan ta bud’e d’aya zif din, anan tarin wayoyi ne kawai da tablet sannan da cajojinsu, sai kuma wasu irin had’add’un biruka kala-kala da taji inama ace an bata d’aya ta dinga zana fulawoyi a litattafanta.

Babu Fullo ba alamarsa don haka ta mayar da zip d’in ta zuge, dadai lokacin da b’arin zuciyarta mai hankali ya shiga aiki…

In har an sami wannan jakar to kenan da mutum a d’akin, zuciyarta ta shiga dukan tara-tara sanda ta d’ago ta kalli hanyar corridon inda d’aki yake. Dole ne ta san hanyar da zata yi ta fita daga wajen nan tunda dare ya fara yanzu, ko waye ya fito daga d’akin ya kamata bata da wani dalilin da zata gaya masa na shigowa cikin d’akin.

A lokaci guda kwakwalwarta ta tuna da tagar band’akin nan da ta gani wadda ita ba k’arfe a jiki, sai ta saki jakar sannan ta nufi k’ofar band’akin, ta bud’e ta shiga sannan ta mayar a hankali ta rufe. Cikin sa’a tagar na daga saman toilet seat ne don ha haka ta taka shi ta hau, sai dai kuma wata matsalar shine b’angare d’aya ne na tagar kawai zai bud’u, ta jijjiga sauran taji kamar ma an tab’a cire su an mayar don suna rawa kad’an, amma duk iya nata kokarin ta kasa sanin yadda zata fitar dasu saboda k’arar da suke yi.

Sai ta auna fad’in cinyoyinta da hannununta sannan ta auna fad’in b’ari gudan daya bud’u, wata zuciyar ta gaya mata cewar zata iya fita a karkace don haka ta lek’a taga tsawon tagar bashi da nisa da k’asa, don ko anji k’arar dirar ta ma zata iya fyallawa ta bar wajen kafin na ciki ya fito, don haka ta fara jefa takalmanta sannan ta yunk’ura ta fara zura kanta waje.

A hankali tana jan jikinta yana wucewa cikin dabara har zuwa kug’unta, inda anan hanyar ta cije, taja-taja amma ta kasa fitowa, gashi rabin jikinta na lilo a waje kuma bayanta ya fara k’agewa, sai kawai tatattaro duka k’arfinta ta sake yunk’urawa cikin rashin sanin abinda zai biyo baya.

Don cikin abinda bai wuce k’iftawar ido ba wani k’arfe dake cikin mahad’ar tagar ya yanki jikinta da wani irin kaifi, zafin ya tafi ya tsarga har cikin kwakwalwarta, hakan yasa ba shiri ta janyo jikinta ta dawo sannan ta dira a k’asan band’akin, ta tattaro k’arshen doguwar rigarta ta d’age daidai lokacin da jini ya fara zirara daga yankan yana d’iga akan farin tiles d’in dake k’asa.1

***

“Yanzu Allah Jamila, baza kiyi da jiki ki fita ki nemo min ‘yar nan ba?”

Cewar Baddo dake kwance tana kallo k’ofar kitchen d’in da Jamila ke girki a ciki.

“Na kashe wutar fa, had’a kayan da suka b’aci kawai zanyi in fito.”

“A’a barsu, zo ki saka hijabinki kije ki nemo min ita, hankalina ya kasa kwanciya tun d’azu.. Kuma wallahi ni da ita ne, ganin ina kwance ai shi yasa ta tsiri sh*gen yawon na dare amma daga yau ba zata k’ara ba, duk uzirinta tayi shi ido na ganin ido don na gaji.”

Jamila ta ajiye wasu farantai data d’auko a hannunta sannan ta fito daga kitchen d’in, a hak’ik’anin gaskiya itama tata zuciyar ta fara damuwa da dad’ewar Jiddan, don ba kasafai take fita ta dad’e haka ba sai in har da wani abu mai muhimmanci wanda in ma hakan ne, to da wuya ne in ba tare suke ba.

Ta d’auki hijabinta dake ninke a saman sallaya ta zura sannan ta fita, ta fita ta bar Baddo nan zaune tana faman kwafa tare da maimaita Jiddan zata zo ta gamu da ita.

Kuma kanta tsaye hanyar d’akin su Sadiya ta nufa, don zuciyarta na da yak’inin abu guda biyu, ko dai tana can ko kuma duk inda Sadiyan take to tabbata suna tare.

Ko da ta isa d’akin tayi sallama ta shiga, Hajiya laraba (kakar Sadiyan) ta fara gani zaune tana cin tuwonta, sannan daga cikin d’aki akwai hayaniyar mutane kad’an-kadan, a gefenta kuma shimfad’a ce da mutum kwance cikin abin rufa, ta riga ta san cewa jikokin Hajiya laraban da yawa kan ziyarce ta wani lokacin har ma su kwana, amma sai taji gabanta ya fad’i, sai taji zuciyarta tayi rawa da tunanin in Sadiya ce a kwance to ina Jidda kenan?

STORY CONTINUES BELOW

“Mun yini lafiya Jamila? Ya k’afar Baddon?”

Hajiya laraba ta amsa sanda ta durk’usa tana gaishe ta.

“Da sauk’i Hajiya, dama Jidda nazo nema, mun ga bata koma ba har yanzu.”

“To! Ya akayi haka kuwa? Ga Sadiya ta shigo ita tun d’azu har ta kwanta?”

Gaban Jamila ya fad’i, taji tana son yarda da tunanin dake gaya mata wani abu ne ke shirin faruwa, amma sai zuciyarta ta ture hakan, ta karb’i cewa watakila rashin mutuncin Jiddan ne kawai ya tashi, ta tafi jajibo rigima a wani waje.

“Ke Sadiya? Sadiya? La! kinga ‘yar nan.. bata dad’e fa da kwanciyar ba.”

Cewar Hajiyan tana k’okarin tashin Sadiya da hannunta da bata saka cikin abincin ba.

“Hajiya kyale ta kawai, bari na koma watakila ma ta dawo yanzu.”

“To shikenan, Allah yasa ta koma d’in… Kinga ban miki bismillah ba muna ta magana.”

“Haba dai, Nagode wallahi sai da safe.”

Da haka Jamila ta nufi k’ofar d’akin ta fita, kuma a daidai lokacin Sadiya ta bud’e idanunta a cikin zanin data rufa sannan ta had’iye yawu a bakinta, kwakwalwarta na tuna mata kalaman Jidda tar akanta.

‘Billahillazi kar ki gayawa wani ga inda na tafi, musamman ma Jamila don na san ita zata fara tambaya… Ke kinga kafin ma su neme ni na dawo, don haka ki tafi kiyi kwanciyarki kawai.’

Wani abu ya faru kenan, tunda har bata dawo ba an fara nemanta, anya kuwa ta kyauta da tak’i binta suje tare? Ko kuma tayi daidai yanzu da taki fad’in abinda ta sani?

Allah yasa dai ba wani abu ne ke shirin faruwa ba. Ta ayyana a ranta.

Kamar a mafarki, Jamila ta koma d’akinsu amma babu Jidda ba alamarta, kuma ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba illa idanun da Baddo ta zubo mata yayin da take rik’e da hannun k’ofar net d’in d’akin, idanun da suka d’ashe cike da taraddadi da kuma fata, sai taji gwiwoyinta sun yi sanyi a take, ta kasa shigowa ta kasa komawa… Sannan fatanta ya dunk’ule waje guda cikin addu’ar ubangiji yasa ba wani abu ne ke shirin faruwa ba…

Sai dai abinda bata sani ba shine, fatanta ya banbanta da k’addarar da ubangiji ya halatta a wannan daren.

***

Karfe biyar da rabi na safiyar Juma’a!

Bayan sanyin iskar asubar daya fara kad’awa, wata k’ara ce ta daban kuma ta tashe ta, k’ara daga can nesa kamar sautin kid’an alarm d’in waya. Jidda ta bud’e idanunta a hankali sanda zafin dake cinyarta ya tuna mata da ciwon da taji, don har a cikin baccinta ko yaya tayi motsi tana jinsa.

A hankali idanunta suka sauka akan kalar labulayen da take b’oye a bayansu, so take ace mafarki ne, so take ace dukkan abinda ya faru a jiya hasashe ne kawai, so take ace tana d’akinsu kuma yanzu zata fara jin mitar Jamila akan ta tashe ta fiye da sau goma don sallar Asuba amma tak’i tashi.

Sai ta maida idanun ta rufe yayin kwalla ta cika taf a cikinsu, rayuwarta ba daidai take tafiya ba, abubuwa sun rikice mata kuma duk Suraj ne sila, da bai cire Fullo a hannunta ba, baza ta tab’a tsintar kanta anan ba… Zuciyarta ta rantse, ta kuma rantsewa sai ta tarwatsa tasa rayuwar da dukkan iyawarta.

A yanzu gari ya waye kuma asuba tayi, ta san ko waye a cikin d’akin zai fito ya bud’e k’ofar ya tafi masallaci ita kuma ta kama gabanta. Ta riga ta rufe tagar band’akin nan jiya kamar yadda ta ganta, sannan ta wanke jinin daya d’iga a k’asa ma, kuma bata jin ta bar duk wata alama da za’a gane shigowarta.

Don haka matsalar dake gabanta a yanzu shine bayanin da zata yiwa su Baddo na inda taje ta kwana da zarar ta fita daga nan da kuma yadda zata ga Fullonta a gaba.

STORY CONTINUES BELOW

.

Kiraye-kirayen sallar Asuba shi ya farkar da Madaki daga baccinsa, nauyayyan baccin da yayi awon gaba dashi tun bayan da ya shigo a jiya yasha magungunansa ya kwanta, Allah ne ma ya taimake shi yabi jam’in sallar isha’i a wani masallaci dake hanyar dawowarsa, da bai san wace irin sallah zaiyi a lokacin nan ba.

Ciwon k’irjin nasa ya ragu sai dai bugun zuciyarsa har yanzu bai dawo daidai ba, don tana da bugawa ne da wani irin saurin da yafi na wanda yayi tseran gudu, ya riga ya sani cewa dole ne ya tak’aita ayyukansa ya koma Lagos da wuri don ganin likitansa, in ba haka ba rayuwarsa na kan gejin da a koyaushe zuciyar zata daina bugawa baki d’aya.

Ya ture bargon jikinsa sannan ya mik’e a hankali lokacin da limamin masallacin ke rangad’a sallama.

Ya rasa jam’i, kuma duk rashin wayoyinsa a kusa ne, suna cikin jakar da ya bari a falo a can alarm d’in yayi ya gama, kuma bayan haka Allah kad’ai ya san yawan sak’onnin dake jiransa ma. Ya zura wani takalmi dake gefen gadon sannan ya fito don shiga band’aki ya d’auro alwala.

A daidai lokacin da ya shiga ya rufo k’ofar band’akin, a lokacin ‘yar aiken Jakadiya Babba ta k’araso k’ofar sashen daga waje, muk’ullin data cire a jiya rik’e a hannunta, ta d’anyi dube-duben cikin duhun asubar ta tabbatar babu mai ganinta sannan ta fito da garin wani abu ta barbad’a a k’ofar d’akin, cikin k’ok’arin kiyayewa kar ta taka shi ta d’auko muk’ullin ta zura a jikin k’ofar, sai dai tana jin alamar kwad’on ya fita ta juya ta bar wajen cikin matsanancin sauri ba tare da ta bud’e ba.

K’arar bud’ewar k’ofar ta shiga kunnen Jidda wadda ke mak’ale a bayan labulen tana saurare, sai dai bata mik’e ta fito a lokacin ba, don tunaninta ya bata cewar ta jira sai wanda ya bud’e k’ofar yayi nisa tukunna yadda zata fita ba tare da ya ganta ba, watak’ila zuwa nan da sakwanni ashirin.

Madaki ya fito daga band’akin rik’e da d’an k’aramin tawul a hannunsa yana goge ruwan dake fuskarsa saboda bai fiye son fuskarsa a jik’e ba, k’afafunsa suka karyo cikin falon don gabatar da sallarsa anan.

Ya cire takalmansa daga farkon carpet d’in sannan ya jefa tawul d’in kan kujerar dake gefa, sai dai me? Kafin ya juya zuwa b’angaren alqiblah, idanunsa suka kai kan wani d’igon jini akan tiles daga d’aya bangaren d’akin, kuma abin mamakin shine a gaban d’igon akwai wani ma, sai ya matso gaba a hankali inda wani mamakin ya sark’e shi, don kujerar wajen ce ta kare ganinsa da sauran abinda ke gaba.

Ba d’aya bane balle biyu, jinin na tafiya ne cikin layi bi da bi har zuwa jikin tagar dake can gaba, idanunsa suka bi labulen tagar da kallo cikin nazari, tabbas akwai mutum a bayansu don ga alamu nan yana gani, amma waye zai shigo masa waje alhalin ya rufe k’ofa? Sannan jiinin na meye?

Ya juya ya kalli k’ofar, da gaske ne kuwa wani ya shigo don babu muk’ulli a jiki kamar yadda ya barshi jiya, kuma ba tare da shakkar komai ba ya shiga tafiya zuwa saitin labulen, zuciyarsa na ayyana masa cewa ko waye a wajen zaiyi nadamar abinda ya kawo shi.

… Sha takwas, sha tara, ashirin!

K’irgen sakwannin da Jidda keyi ya k’are daidai lokacin da zuciyarta ta kintaci cewa zata iya fitowa ta nemi hanyar tsira, kuma ko kad’an kunnenta baiji sassanyan takun dake isowa gare ta ba don ta yaya zata yi tunanin wani mutum na ciki bayan ta tabbatar da k’arar bud’ewar k’ofa a d’azu…

Ta mik’e a hankali sannan ba tare da tunanin komai ba ta janye labulen daidai lokacin da Madaki ya ja k’afafunsa ya tsaya a gabanta!

Wani irin shiru ne ya gifta a cikin d’akin, sakwan d’aya, biyu, uku, hud’u, biyar, shida… kafin al’amarin ya gama dira a kwakwalwar kowannensu.

Sai tayi saurin komawa da baya ta mannu da jikin tagar saboda yadda yake tsaye daf da ita, lissafinta ya rikice a lokaci guda sannan zuciyarta ta shiga dokawa a k’irjinta yayin da idanunta ke kallonsa a gigice, tunaninta kuma ya shiga sark’ewa wajen jerawa kanta tambayoyi… Dama bai fita ba? Shine mai d’akin? Ya akai bata ji motsinsa ba?

STORY CONTINUES BELOW

Idanunta suka wulk’ita kan k’ofar da taji an bud’e d’azu, an rufe take babu alamun an bud’e tan… Shikenan ta shiga uku!

Madaki ya k’ank’ance idanunsa yana kallonta cike da mamaki shima, tsaf ya gane ta, wannan yarinyar ce data buge shi shekaranjiya, wadda ya tab’a gani tsaye tare da wani saurayi kwanakin baya, me ya kawo ta cikin d’akinsa kuma yanzu? Ta yaya ta shigo? Bibiyarsa ta ke yi ko me?

“Ke me kike yi anan? Wa ya shigo dake?”

Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, wani b’ari na tunaninsa na gaya masa cewa da wuya idan ita d’in mutum ce.

Jidda ta sake rikicewa, don amon muryarsa kad’ai wani irin sauti ne da bata tab’a ji ba, mai zurfi da kauri sannan a nad’e da wani irin zak’in da ya kara haska kwarjininsa, sai ta had’iye yawun da bata san dashi a bakinta ba sannan ta shiga girgiza kai.

“Da kaina na shigo…”

‘Yar k’aramar muryarta ta shaida tsoro k’arara, don haka a take Madaki ya watsar da zancen cewa ba mutum bace.

“Ta ina kenan? kuma me ya kawo ki?””

Hannayenta duka biyu suka damk’e k’asan hijabin dake jikinta, hakan yasa yabi jikin nata da kallo, anan ya sami amsar jinin da ya gani a k’asa, don daga wajen cikinta, gefen hijabinta a b’ace yake sosai da wani busashshen jini, ya dawo da kallonsa kan fuskarta yayin da ransa ya fara b’aci shirun nata…

“Nace me kika zo yi anan?”

Ya k’ara tambaya cikin tsawar data kad’a hatta ‘ya’yan hanjin cikinta ba hantar ta kad’ai ba.

Sai dai a wannan lokacin tazarar k’addarar dake tunkarar kowannensu ta k’aranta, don haka kafin Jidda ta samu damar sake magana, k’ofar d’akin ta bud’e kuma ba tare da b’ata lokaci ba, Jarmai (Babban bafaden Mai martaba) ya kutso kansa ciki had’e da rangad’a sallama.

Dukkansu suka juya a tare, Jidda taja numfashi cikin k’irjinta kamar mai shirin shid’ewa yayin da mamakin ganin Jarmai a wannan lokacin ya daki tunanin Madaki.

Idanun Jarman shima suka zare da tsantsar mamaki sannan sallamar bakinsa ta gutsire, sai kawai yayi saurin durk’usawa har k’asa sannan ya shiga fad’in.

“Barkanmu da Asubahi ranka ya dad’e, Mai martaba ne ya iso don ganawa da kai…”

Mai martaba?A masaukinsa? Yanzu? Ta yaya ma k’ofar take a bud’e?

Madaki ya furta wad’annan tambayoyin a zuciyarsa, tambayoyin da amsarsu ta tabbata a take, don kafin d’aya daga cikinsu yayi wani yunk’uri, cikakkiyar muryar Mai Martabar tayi sallama a sanyaye cikin falon, kuma ya shigo sanye da fararen kaya na babbar riga da kuma wani sassauk’an nad’i daya k’ara fito da ilhamar mulki da kwarjininsa.2

Babu shiri Madaki ya durk’ushe har k’asa sannan tsoro ya shige shi kad’an na tunanin yadda zai yiwa mahaifin nasa bayanin yadda yarinyar ta shigo masaukinsa, don ya riga ya sani cewa Sarkin bai iya fushi ba.

A b’angaren Jidda kuwa, ji tayi bata tab’a tsintar kanta a wani irin gigitaccen hali irin lokacin ba, don tun bayan zuwanta cikin masarautar sau d’aya ta tab’a ganin Mai martaban, ranar hawan idin sallar bara… Sai gata yau a gabansa, ‘yar tazara kad’an tsakaninsu sannan a cikin halin da babu wani mahaluki a duniya da zata so ya ganta a haka, sai kawai ta zame k’asa ta durk’ushe gwiwoyinta itama, cikin kwakwayon irin tsugunnon da Madaki yayi.

Sarki Ahmad Uba Kamsusi ya kalli hoton da idanunsa ke d’auka a gabansa… Hoton da kwakwalwarsa ta fassara masa shi da wata irin ma’ana, ma’anar da bai tab’a hasko ta akan kowanne mutum na duniya ba balle kuma Madakinsa.

A idanunsa Ibrahim na rungume da yarinyar ne kuma shigowarsu ce tasa ya sake ta, sannan zai iya rantsewa daga bakin k’ofa kunnensa ya jiyo masa muryarta cikin magiya saboda haka ne ma yayi saurin shigowa kai tsaye… Yaji kansa ya sara a lokaci guda sannan hawan jininsa na shirin tashi.

Maganar data kawo shi wajen Madaki a yanzu wadda ya lak’abawa kalmar ‘Muhimmanci’ ba kowwacce bace illa maganar aure, don tun kafin zuwansa ya riga ya yanke cewa ba zai barshi ya koma ba tare da wata kwakwarar magana data shafi hakan ba, saboda wannan dalilin ne ma yasa aka tanadar masa masuki a cikin masarautar ba wai don bai san cewa a duk zuwansa garin yafi son kwanan guest inn da cikin masarautar ba.

Sai gashi yayi kicib’is da mummunan abin da ya zarta girman tasa maganar, tunaninsa ya nemi rikicewa sanda wani b’arin na zuciyarsa ke hasko masa wasu tarin al’amura da suka shud’e, amma sai yayi k’ok’arin ture su da irin wannan k’arfin hali da jajircewar da ubangiji ke mallakawa Shuwagabanni.

“Barka da Asuba ranka ya dad’e…”

Muryar Madaki tasa ya maido da hankalinsa kansa, ya san cewa shi mutum ne mai karfin hali, amma bai san cewa k’arfin halin nasa zai iya bashi damar magana a yanzu ba… Watak’ila don bai san irin girman abinda ya aikata bane, bai san irin cin fuska da muzantar da zai jawowa mulkinsa ba in har wannan labarin ya fita.

Jin shiru yasa Madaki ya d’ago da idanunsa a hankali ya kalle shi sannan bakinsa ya shiga fad’in…

“Ranka ya dad’e ni kaina ban san wacece ita ba balle kuma ta yadda ta shigo, na fito ne kawai na ganta…”

Maganar tasa ta yanke ba don wani ya tsaida shi ba ko kuma don wani abun ya katse shi, sai don yanayin fuskar Sarkin dake tsaye a gabansa, wani yanayi da tunda yake a rayuwarsa sau d’aya ya tab’a ganin irinsa… shekaru ashirin da suka gabata, ranar da Sarkin ya saki Fulani ta dalilinsa!

Saboda haka sai ya mayar da kansa k’asa ya sunkuyar, cikin salon dake nuna sallamawa…

Mai martaba ya kai idonsa karo na biyu kan Jidda data rakub’e a gefe cikin hijabinta dake b’ace da jini, ransa ya k’ara dunk’ulewa ya b’aci, sai ya juyar da fuskarsa a hankali sannan cikin muyar dake shaida tsantsar fushi da iko ya kira sunan Jarmai.

Jarmai ya rarrafo da sauri daga bakin k’ofar da yake tsugunne, hannunsa dunk’ule a iska yana fad’in.

“Lafiya waliyyin Allah,

Lafiya jinjirin wata sha kallo.”

Muryar Mai martaba ta sake fitowa a kausashe, sannan ya fad’i abinda ubangiji ya riga ya k’addara faruwarsa tun kafin wanzuwar duniya.

“A soke tafiyar da zanyi yau, a nemo iyayen wannan yarinyar, zan d’aura aurenta da Ibrahim anjima idan mun idar daga sallar Juma’a!”

Ya rufe bakinsa daidai lokacin da kwakwalwar Madaki ta dawo masa da maganganun Saifuddeen..

Ban san me take shiryawa wannan karon ba, amma ta tabbatar min cewa ba zata fasa k’udirinta akanka ba don haka kayi a hankali, kuma ina baka shawara akan ka takaita zamanka.

Mai martaba ya juya ya fita, Jarmai ya bishi a baya cikin sassarfa…

Nan suka bar halittu biyun dake durk’ushe kan gwiwoyinsu cikin wani irin gigitaccen hali.1

Halittun da labarin rayuwarsu ke shirin kafa tarihin da zai manne a zukatan al’umma!

Pheeew!

Waye ya kula cewa har yanzu Jidda bata san waye Madakin da take tone asiri akansa ba?😄2

Kuna ganin auren nan zai yiwu?3

Madaki zai bari ayi?2

Me zai biyo bayan hakan?Karfe shida da mintuna na safiyar Juma’a!+

“Assalamu Alaikum…”

Muryar k’anwar mahaifiyar Sadiya ta fad’a a wayar dake kare a kunnenta, tana daga cikin matan dake zazzaune a d’akin Baddo cikin jimami.

“… Aminu Zainab ce, mun tashi lafiya? Dama nace k’arfe nawa zaka shiga aiki yau? Sai tara? Kaga wallahi jikar Baddo ce ta b’ata tun jiya ba’a ganta ba shine wai ake son a kawo case d’in wajen hukuma…”

Ta d’anyi shiru tana sauraren bayanin da na cikin wayar ke yi kafin ta cigaba da fad’in.

“Wallahi Aminu an duba kusan ko’ina a cikin masarautar nan babu ita, to yanzu tunani ake watakila fita tayi shi yasa aka ce gwara hukuma ta shigo cikin lamarin.”

Jamila dake zaune a can gefe ta d’auke kwallar data sake taruwa a cikin idonta… ta share irinta ba adadi daga daren jiya har zuwa wayewar garin yanzu… Don abin kamar wasa tun suna neman Jidda a d’an tsakanin tsukin wajensu har zancen ya girmama aka nemi taimakon wasu maza wad’anda suka shiga dubawa hanyar cikin gida da harabarsa amma babu ko alamarta.

Kuma haka mazan suka dinga k’aruwa wasu na tashin wasu don al’amari ne da ba kasafai aka saba jinsa a masarautar ba, mutane suka rabu kusufa-kusufa aka dinga neman Jidda duk inda aka san zata je dama inda ba’a tunani cikin unguwannin masarautar amma har misalin k’arfe d’aya na dare babu ita ba alamarta.

Baddo ta tsure, hankalinta ya tashi in banda salati ba abinda take yi, sauk’inta d’aya ne, shigowar wasu daga cikin matan dake mak’otaka dasu har su biyar don taya su jaje, daga baya kuma Hajiya laraba ta turo Sadiya da Aunty Zainab, haka suka kwana zaune tare dasu cikin jimami.

A yanzu kuma tunani ake ma Jidda bata masarautar bakid’aya kamar yadda wasu daga cikin mazan suka yi hasashe, shi yasa akace dole a shigo da hukuma cikin al’amarin.

Idanunta suka shiga hasko mata girma da fad’in garin Kiyari, ina Jidda zata je a cikin garin da bata san kowa ba? Ta ina ma za’a fara nemanta yanzu? Sai ta juya ta kalli Sadiya dake rakub’e a can gefen itama tayi tsuru-tsuru.

Allah ya sani har yanzu zarginta na kan ta ne, don duk irin rantse-rantsen da tayi na bata san inda Jiddan take ba bayan al’amarin ya tsawaita sun taho ita da Aunty Zainab (K’anwar mahaifiyarta), bata yarda ba ko kad’an saboda ta riga ta san irin mu’amalar dake tsakaninta da Jiddan.

K’awaye ne su amma Jidda na juya ta ne kamar uwa da ‘yarta, ita kuma tana kiyaye dukkan maganganunta kamar bawa da ubangidansa, don haka tsaf zata iya sanin inda ta tafi amma ta kasa fad’a.

Shi yasa bata so aka d’auki shawarar kai lamarin gurin ‘yan sanda ba, don zasu iya tsare Sadiyan da tambayoyi ta hanyar azabtarwa, a tunaninta idan aka bar komai anjima ne kad’an itama zata tsure da al’amarin ta fito ta fad’i inda taje…

Sai dai kafin Jamila ta gama wannan tunanin nata, ko Aunty Zainab ta k’arasa wayar da take yi, ko Baddo ta kai ga zagayowa farkon carbin da take ja a hannunta, ko kuma wasu mata su kai ga mik’ewa don tafiya wajen iyalansu ganin safiya tayi…. Wani abu kamar almara ya faru a idanun kowannensu.

K’ofar d’akin ta bud’e da wani irin sauri sannan Jidda ta fad’o ciki a guje… Kuma bata zame ko’ina ba sai can cikin d’aki, ta tsallake dukkaninsu babu alamun ta lura.

Jamila dake zaune a can gefe bata tabbatar da abinda ta gani gaskiya bane sai lokacin da taji na ambatar salati wasu kuma na kiran sunan Jiddan, sannan taga matan suna mik’ewa don nufar cikin d’akin da giftawar tayi, sai kawai ta saki wayar dake rik’e a hannunta sannan ta mik’e ta riga su isa k’ofar d’akin yayin da Baddo dake k’ok’arin tashi ke faman fad’in..

“Jiddan ce kuwa? Ku gane min mana in itace, Zainabu, Rahma…magana fa nake? Maijiddan ce ko kuma k’ak’a?”

Idanun Jamila suka gane mata Jidda tsaye a cikin d’akin, sanye cikin wani hijabi daya b’aci da jini sannnan tana k’okarin janyo kayanta daga cikin durowa suna fad’uwa a k’asa, kuma babu alamun cewa hankalinta ya nuna mata da mutane a bayanta balle har taji hayaniyar salatinsu, ba shiri ta k’arasa sannan ta kamo ta.

STORY CONTINUES BELOW

“Jidda me kike yi haka? Me ya same ki? Daga ina kike?”

Kamar wadda aka tasa daga bacci, sai a lokacin Jiddan ta lura da Jamila da kuma mutane da suka shigo d’akin, sai dai hankalinta baya tare da ita sosai balle ta fahimci irin tashin hankalin dake fuskarsu suma, ta kalle su kawai sannan ta sake juyowa ta kalli Jamilan muryarta na karyewa ta shiga fad’in.

“Ringim zan tafi dan Allah ki kira yaya Abdullahi yazo ya tafi dani yanzu, ko kuma ki bani kud’in mota, wallahi ba zan zauna ba Jamila… Kuje ku gaya musu suyi hak’uri dan Allah…”

“Su waye Jidda? Wasu ne suka biyo ki?”

Sai ta juya ta kalli Aunty Zainab d’in da tayi maganar, idanunta a rikice sannan muryarta na karkarwar kuka tace.

“Aunty Zainab wallahi ba wani abu ne ya kaini d’akin ba, Fullo kawai naje nema kuma ban ganshi ba ma… Shi ma kuma ya sani, Mai martaba ne kawai bai fahimta ba…”

A baiyane yake cewa ba’a haiyacinta sosai take ba don basu fahimci komai a maganarta ba kuma kafin wani ya sake magana, ta sake juyawa wajen Jamilan.

“Dan Allah kuje ku gayawa Mai martaba yayi hak’uri… Dan girman Allah Jamila, kice masa wallahi ba zan k’ara zuwa ba. “

“Jidda wane Mai martaba? A ina kika ganshi? Ina kika je wai? A ina kika kwana?”

Jamilar ta k’ara tambaya a lokacin da sauran matan suka matsawa Baddo ta shigo d’akin da d’ingishinta, Jidda na ganinta tayi saurin tahowa ta tsaya a gabanta.

“Baddo dan girman Allah kema kiyi hak’uri ba zan k’ara ba, wallahi ba zan k’ara fita da daddare ba, kuje ku fad’a musu suma suyi hak’uri.”

Baddon na jin haka, zuciyarta ta bata tabbacin cewa ba sai an tsaya tone-tone ba,  Jidda ta shuka abinda ta dad’e tana tsoron faruwarsa tun lokacin dawowarta k’ark’ashinta, watakila ta aikata abinda zai kawo k’arshen zamansu a masarautar don ba k’aramin abu ne zai tsorata ta haka ba, don a baiyane yake cewa yanayinta ba na shafar aljanu bane.

Sai ta kamo hannayenta duka biyun cikin nata sannan tayi k’okarin sassauta b’acin ran muryarta.

“Me ya faru Hauwa’u? Gaya min daga ina kike?”

Zuciyar Jidda ta sake tsinkewa, wani d’aci ya cika mak’ogwaronta, ta rasa ta ina zata fara bayanin da zasu fahimta, sai kawai hannayenta suka shiga rawa cikin na Baddon yayin da hawaye mai d’umi ke gangarowa kan fuskarta.

Ganin hakan yasa Aunty Zainab ta juya ta shiga rok’on sauran matan dake tsaye ko zasu d’an bada wuri a samu ta nutsu kafin a san me ya same ta, amma Jamila da ranta ya kai kololuwa wajen b’aci tayi saurin matsowa gaba ta sake kamo ta.

“Wai ba magana ake miki bane? Jidda me ya same ki? Jinin meye a hijabinki? Ina kika je kika kwana?”

A lokacin kukan da take k’ok’arin dannewa yaci galaba akanta, komai ya sake hargitse mata, tunaninta ya k’ara juyewa sanda idanunta ke k’ara hasko mata abinda ya faru, sai kawai ta fashe da kukan dake fitowa kamar zai tafi da numfashinta…

“Ban sani ba Jamila, nima ban san inda naje ba kuma ban san WAYE SHI ba, kawai Mai martaba yace zai d’aura masa aure dani ne bayan sallar Juma’a!”

Ita kanta sai da taji kalaman sun bada k’arin gudunmawa a cikin kukanta yayin da kuma kai tsaye suka yi dirar mikiya a kunnen kowanne mahaluki dake wajen, kamar k’arar tsawar data taho tare da walk’iya mai haske, sannan k’arara fuskokinsu suka haska da tsantsar mamaki da kuma rashin fahimtar kan zancen…

A lokacin ne gwiwoyin Jidda suka kasa d’aukarta, k’afafunta suka shiga rawa sannan zuciyarta ta sake matsewa da taraddadi, sai kawai ta zube har k’asa a wajen kafin muryarta ta sake fitowa cikin karyewar kukan…

STORY CONTINUES BELOW

“Dan Allah Baddo kuje ku bashi hak’uri…”

***

“Mdee kaje ka bashi hak’uri..”

Muryar Mubarak ta fito ta cikin wayar dake rik’e a hannun Madaki, ba videocall bane, amma saboda hargitsatstsen halin da kwakwalwarsa ke ciki, ya kasa kai wayar gefen kunnensa.

“For what Mubarak? Akan laifin da ban aikata ba? Ko kuma akan hukuncin daya riga ya yanke?”

Amon muryarsa ya fito a dunk’ule, cikin tsananin b’acin rai. Mubarak yayi ajiyar zuciya daga cikin wayar sannan ya kira sunansa, ainihin sunansa…

“Ibrahim…”

“… wannan lamarin fa ba wasa bane, ba wai contract ne na aiki da yake da wa’adin lokacin da zai k’are ba, aure Mai martaba yake shirin d’aura maka da yarinyar da baka sani ba.

Aure wanda ko a wane irin hali aka yishi mutane basa fatan rabuwarsa Mdee, ko kuwa kana tunanin cewa idan an d’aura nan kusa zaka iya sakin yarinyar ne babu wani dalili? Kana tunanin hakan zai tab’a yiwuwa ba tare da mutane sun d’auki abinda kayi a matsayin cin fuska ga mahaifinka ba, ko kuwa kana ganin idan har kayi hakan ba zaka yi nasarar sake b’ata ran Mai martaban ba?”

Shiru ya gifta na wasu ‘yan sakanni a falon yayin da tarin abubuwa ke yawo a cikin kwakwalwar Madaki, kuma a ciki ya rasa wanda zai kama ya rik’e a matsayin tunani… Ya fuskanci tashin hankali da yawa a rayuwarsa amma bai tab’a shiga irin wannan ba, don a baya kalmar ‘Aure’ na yin ma’ana a zuciyarsa ne kawai duk sanda ya samu katin gaiyata daga abokan huld’arsa ko kuma ya halarci d’aurin auren, bayan haka bai tab’a danganta ta da kansa ba balle har wata rana yayi mafarkin faruwarsa.

Ko sanda Habibu ke ta k’ok’arin tursasa masa da zancen wata k’anwarsa jinsa kawai yake don yana son ya bashi had’in kai su kammala wani aiki, daga baya ma Allah ya taimake shi yarinyar ta rufe ido akan wani tsohon d’an siyasa zancen yabi iska.

Sai gashi a yanzu ‘yan awanni ne kawai tsiransa da auren da bai tab’a shirya masa ba, kuma hakan na shirin faruwa a sigar da bai isa ya tsaida shi ba… Sai ya girgiza kansa sannan muryarsa ta fito fili.

“Wannan ba shine mafita ba Mubarak, ka riga ka san halin Mai martaba, ka san irin fushinsa, don haka ba lallai ya bani damar ganinsa ba ma kafin ya aiwatar da hukuncinsa…”

“Wace shawara ka yanke kenan?”

Mubarak d’in ya katse shi don ya fahimci watak’ila ya riga ya yanke hukuncinsa.

Madaki ya sake yin shiru yana kallon mintunan kiran dake tafiya akan screen d’in wayar.

“Daga ita har yarinyar zan tarwatsa Mubarak…”

Ya fitar da iska ta bakinsa sannan ya rantse da Allah.

“… Wallahil azeem an gama wannan lokacin da shiru na ke k’ara bata dama, a yanzu ta k’araso gab’ar da ba zan iya jurewa ba.”

“Wai Fulani Mdee? Kana tunanin da hannunta ne a ciki? Nayi zaton mai Martaba ne kawai ya yanke hukuncinsa…”

Kafin ya k’arasa, ya katse shi.

“Ranar da Saifuddeen ya nemi gani na, ya gaya min da akwai abinda take shiryawa, yace bai san mene ne ba amma ta tabbatar masa cewa ba zata fasa k’udirinta akaina ba… To kana tunanin wannan ba aikinta bane? Kana tunanin wani ne zai b’ata lokacinsa ya shirya min wannan abin? Akan me?

Shi yasa na yanke cewar zan basu damar da suke nema Mubarak, zan bari Mai martaba ya d’aura auren nan don na fahimci hanya mafi sauki da zan iya tarwatsa Fulani shine ta hanyar wannan yarinyar, kuma hakan shi zai bani damar da zan iya wanke kaina a wajen Mai martaba nan gaba…

STORY CONTINUES BELOW

Don haka zan bari tazo Mubarak, zan bari suyi nasarar shigo da ita cikin rayuwata, don ni kaina ina buk’atarta!”

Abinda Ibrahim Madaki bai sani ba a lokacin shine, kalmar ‘Bukata’ suna ta tara!

***

Karfe goma da rabi na safiyar Juma’ah!

“Me zaki ci yanzu?”

Muryar Ahmad ta tambaya daga cikin wayar, a hankali cikin amon dake nuna cewa bai dad’e daga tashi daga bacci ba, sannan cikin sigar da a wajen Safina shi kad’ai Allah ya mallakawa irin hakan.

Safina (Autar Fulani wadda bata fi shekaru ashirin ba) ta lumshe idanunta sannan ta k’ara cusa fuskarta cikin filon da take kwance alamun dad’i kafin ta d’ago tace.

“Me kake so inci?”

“Zab’i kike bani ko shawara kike nema?”

Yatsanta ya shiga kanannad’e jelar dogon kitsonta kanta.

“Zab’i na baka.”

“Idan na fad’i abinda baku dashi a Kiyari fa?”

Ta juya fararen idanunta tana murmushi kamar yana kallonta sannan tace.

“Sai insa a siyo min shi a koina yake a duniya, ko ka manta ni wacece ne?”

“Ta yaya zan manta matsayin Gimbiyar Kiyari? Kawai dai ina tunanin koda wannan matsayin ba lallai ki same shi bane.”

Mamakin ya d’an dira a fuskarta sanda ta tsaya da motsa hannunta sannan tace.

“To ina jinka, ka gaya min menene shi?”

Gabad’aya hankalinta ya ta’allak’a wajen jiran amsar sanda kiran ya katse, taja tsaki a hankali sannan ta dawo da wayar gaban fuskarta ta kalli screen d’in, bama sai ta kalla ba ta riga ta san kiran waye ya shigo, don duk duniya namba d’aya ta sanyawa wannan tsarin na kowacce irin waya take yi ta katse in dai nambar ta neme ta… Nambar babbar k’awarta Juwaira.

“Allah ya tsine miki Juwee…”

Ta fad’a ranta a b’ace, don wannan ne karo na farko da taji bata mararin kiran nata, ta yaya zata katse mata wayar Ahmad? Saurayin da zuciyarta ta gama narkewa akansa tun bayan had’uwar da suka yi kwanaki biyu da suka wuce.

“Safina, Safina kina jina?” Muryar Juwairan ta fito a hanzarce daga cikin wayar.

“Ina jinki mana, me ya faru da sassafen nan? Mutuwa aka miki?”

“Wannan yafi mutuwa don wallahi gwara ko Daddy ne ya rasu da abinda naji, wai da gaske ne za’ayi d’aurin aure a masarauta yau?”

“Inji ub*n wa? Wa za’a d’aurawa auren?”

“Yanzu nan Sulaiman yake gaya min wai Mai martaba ya aikowa babansa d’aurin aure da azahar… In kina k’aunar Allah kice min ba auren Saif bane, Safina na shiga uku idan aurensa za’ayi… Wallahi zan iya kashe kaina..”

Mamaki ya d’aure tunanin Safinan, bata ma saurari k’arshen zancenta ba don tunani take auren wa za’a d’aura a masarautar tana zaune bata sani ba? Ta yaya ake aure ma babu wanda ya sani? Wa ma zai d’aura? Tunda ai jiya suka je yiwa Mai martaba sallamar tafiyar da zai yi kuma babu wanda ya ambaci wani aure.

Kai koma auren ne dai zuciyarta na da yak’inin cewa bana Saif bane, don shi yanzu ba abinda ke gabansa kenan ba… Sai ko Umar, tunda bayan shi babu wani namiji in ba wannan jaririn na amaryar Mai martaban ba.

Amma bama zata yaudari kanta ba ta san ko mahaukaci ba zai d’aurawa Umar aure yanzu ba, tunda baya ma k’asar yana can Russia inda yake karatun Jami’a a mataki na uku.

“Kinga zan nemo miki duk abinda ke faruwa yanzu, ki kwantar da hankalinki… Ko auren ne ma ni na san bana Turaki bane, tunda kwanaki da nayi masa zancenki ai kinga har nambarki ya k’arb’a. Kawai bani minti biyu… Yanzu zaki ji ni.”

STORY CONTINUES BELOW

Tana gama fad’in haka ta kashe wayar sannan ta mik’e, zucyarta cike da inda zata samu gamsashshen bayani, don tun daga kan yayyenta Fulani kwata-kwata bata sanar dasu irin al’amuran nan sai iya abinda suka tsinta a wajen bayi kawai, a kullum tafi basu kwarin gwiwar cewa suyi sha’anin gabansu kawai su rabu da harkar masarautar, kamar akwai wani abu da take tsoron zasu iya saninsa.

Saboda haka a yanzu ma bata da tabbas cewa zata sami wani bayani in dai ba auren d’aya daga cikin yayyen nata za’ayi ba. Sai dai ko ta nemi d’aya daga cikin jakadun b’angaren kawai ta tambaye su,  ta yafa d’an k’aramin mayafi akan doguwar rigar baccinta sannan ta fita.

Ta dinga wuce manya-manya kuma k’awatattun falukan mahaifiyar tata kafin ta isa hanyar da zata kaita wajen da zata fara ganin bayi, a daidai sanda ta k’araso wajen wata harabar ‘dining’ na falon k’arshe ne taga shigowar Jakadiya Babba, inda take tsaye yana da d’an duhu don haka ita bata ganta ba har ta karya kwanar da zata kaita wani d’an karamin falo dake manne da turakar Fulanin, inda a k’aida kullum a nan take karyawa kafin ta kimtsa ta fito.

A lokaci guda zuciyarta ta gaya mata cewar ta bi bayanta taji me zasu ce don ta tabbata abinda ya shigo da ita da sassafen nan nan ba zai banbanta da abinda ya taso da ita ba itama.

Don haka kai tsaye tabi bayanta sanda da ta shige hanyar corridon, ta isa daidai lokacin da Jakadiyar tayi sallama sannan ta zube a gaban Fulani tana zabga kirari, bata bita ciki ba, ta tsaya daga corridon ne kawai inda zata iya jin amsarta ba tare da sun ganta ba.

“An samo bayanin?”

Ta tsinci muryar mahaifiyar tata da wani irin nishadin da ko lokacin bikin yayarta Aisha bata ji shi ba.

“An samo ranki ya dad’e, yanzun nan daga wajen Jarmai nake, kuma yayi min bayanin komai…”

“Wacece ita?” Wannan karon Fulanin tayi magana alamun tana cin wani abu.

“Allah yaja da zamaninki, yace binciken da suka yi yarinyar jikar d’aya daga cikin jakadun tsakar gidan nan ce mai suna ‘Baddo’ yarinyar kuma sunanta ‘Maijidda’.

A yanzu haka ma har an tura da mota garin ‘Kacalla’ inda akace ‘yanuwan mahaifinta suke don a taho dasu.”

Shiru ya ratsa wajen kafin muryar Fulani ta sake fitowa cikin wata sassanyar dariya.

“Juma’a babbar rana! Nagodewa k’ok’arinki Rakiya, nagodewa k’ok’arinki daya nuna min wannan ranar… Ranar auren shalelen Mai martaba, aure na k’ask’anci irin wannan!

Wallahi kayi kad’an ka gujewa sharri na Madaki, yanzu muka fara tafiyar… Ko baka gani bane.”

Tayi maganar cikin sigar tambaya, amma ba tambayar bace, zance ne kawai dake k’ara k’awata maganar tata.

Mamaki ya sauka akan fuskar Safina, dama Madaki yazo garin ne bata da labari? Kuma har za’a d’aura aurensa a yau? Koda yake ai dama shi kamar ba d’an gida bane, tunda tun asali basa shiri da Fulani dole ba wani biki za’a yi masa ba, abinda kawai bata fahimta ba shine me yasa mahaifiyar tata take irin wannan farin cikin da auren?

Sai ta tab’e baki kawai ganin ita ta sami amsar da zata bawa Juwaira don haka ta juya da shirin komawa, sai dai a daidai lokacin da k’afafunta suka motsa a lokacin ta tsinci wani b’angare na mahaifiyar tata da bata tab’a tsammani ba.

“Ranki ya dad’e kina ganin kuwa mu bari ayi auren nan? Ina nufin ba haka muka tsara tun farko ba, bamu yi tunanin haka hukuncin Mai martaba zai kasance ba, kar azo ayi dana sani daga baya idan…”

“Ba zamu tsayar ba Jakadiya…”

Muryar Fulanin ta fito da wani irin amo da Safina ta kasa tsinto sautin mahaifiyarta data sani a ciki.

“… Zamu bari ayi, zamu bari mai martaba ya bud’e mana wata k’ofar da zata sauk’ak’a mana hanyar cimma manufarmu, don na fahimci a yanzu hanya mafi sauk’i da zamu kawar da Madaki shine ta hanyar wannan yarinyar…

STORY CONTINUES BELOW

Ko kin manta kince ita d’iyar Jakadiya ta ce? Kinga kuwa ina da iko da kuma hanyoyin da zan juya ta cikin umarni na ko tana so ko bata so.

Don haka kamar an d’aura auren nan ne an gama Rakiya, ina buk’atar yarinyar nan a kusa da Madaki, ina bukatarta!

Abinda Fulani Hafsatu bata sani ba a lokacin shine, kalmar ‘Bukata’ suna ta tara!

***

Karfe sha d’aya da mintuna na safiyar Juma’ah!

Su bakwai ne, suna zaune a cikin wani wawakeken zaure daya sha ado irin na zanen gidan sarauta a duka bangwayensa da kuma wasu tausasan kilisai da suka nutse cikin daddad’an laushinsu. Biyar daga cikinsu in banda kalke-kalle da kuma yabawa adon wajen ba abinda suke yi sai kuma tarin farin ciki fal a zukatansu na damar da suka samu ta halartar masarautar.

“Kaga wani al’amari na manya Alhaji, ace wayewar garin Allah kawai azo da mota a d’auko ku da sunan neman aure babu wani bayani? In ba irinsu ba wa zaiyi wannan sha’anin?”

Wanda aka kira da Alhaji ya gyada kansa yana karewa wajen kallo sannan yace.

“Bari kawai Sama’ila, ni da aka kawo mu ma na zata zamu fara ganin ita Baddon tayi mana gwari-gwarin akan abinda ke faruwa amma kawai sai aka zube mu anan… Allah yaso dai munyi shigar mutunci don da alama wani babban zamu gani anan.”

Sai dai kafin Sama’ilan ya sake magana, k’arar taku daga soron dake manne da wajen ta bak’unci kunnuwansu… Taf! Taf! Taf! Sannan kuma kirarin Fadawa ya rud’a wajen.

Sai suka mik’e gabad’ayansu cikin alamun girmamawa, wani farin dattijo ne ya shigo fadawan na take masa baya cikin shiga ta alfarma, alfarmar irin ta sarauta wadda ta tabbatar musu cewa ba k’aramin mai muk’ami bane shi.

“Takawarka lafiya hana kangara,

Isowarka lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa,

Isowarka lafiya dai Galadiman Kiyari.”

Cewar fadawan sanda ya nemi waje ya zauna kan d’aya daga cikin tintin d’in dake zube a wajen… Sai da fadawan suka gama gyara masa zama sannan aka bawa su Alhaji damar zaunawa.

“Barkanku da isowa, fatan kun tashi lafiya?”

Muryar Galadima ta fito a sauk’ake cikin amon dake nuna iko irin na sarauta, dukkanninsu suka k’ara sunkuyar da kansu yayin da Alhaji ya amsa gaisuwar cikin girmamawa.

“Na san an shaida muku dalilin kiranku nan, amma Mai martaba yace yana son a sake gaya muku cewar yana nemawa d’ansa ne auren d’iyarku Maijidda, idan kun amince za’a d’aura auren a yau bayan an idar daga sallar juma’a.”

Alhaji wanda yake a matsayin wan mahaifin Jidda ya had’iye yawu a cikin mak’ogwaronsa saboda girman zancen, tun a Kacalla mutanen da suka taho dasu sun shaida musu hakan amma a yanzu da yake jin zancen daga bakin babban mutum irin Galadima sai yaji wani irin nauyi da bai san irinsa ba ya lullub’e shi ruf, sannan kuma kunya na sauka akan bargon nauyin.

Yace bai amince ba? A matsayinsa na wa? Har yaushe yake da ikon hana Mai martaba bawa d’ansa auren Jidda? Yarinyar da ba’a kansa nauyinta yake ba, bai san cinta ba bai san shanta ba? Yace A’a a dalilin me? Ta yaya ma zai tab’a tankwab’e wannan kwaryar arzik’in?

Sai ya sunkuyar da kansa kamar zai dungura har k’asa sannan ya furta abinda ya zama sanadin d’aure k’addarar Madaki da Jidda waje guda.

“Akwai motoci guda biyu a waje, (Shuttle Bus) Mai martaba yace a shaida muku zaku iya aikawa dasu a taho da wasu daga cikin  ‘yanuwa da abokan arzik’i kafin lokacin da za’a d’aura auren.”

Cewar Galadima a matsayin k’arshen maganar sa dasu.

***

KARFE DAYA DA RABI NA RANAR JUMA’AH!

Harabar masallacin gidan Sarki cike take taf da tarin al’umma wad’anda mafi yawancinsu suka tsaya bayan jin sanarwa cewa za’ayi d’aurin auren d’an Mai martaba a lokacin, mafi yawancinsu sun cika da mamakin jin zancen daga sama, amma da yake babu wanda ya san labarin dake bayan hakan sai cece kucen ya k’aranta.

AURE YA DAURU!

AN BAYAR AN KARB’A

SADAKI DUBU D’ARI

LAKADAN BA AJALAN BA

IBRAHIM YA ZAMA MIJIN MAIJIDDA

UBANGIJI YASA MASU FAHIMTAR JUNANSU NE!7

Wannan maganar ita ke karad’e ilahirin masallacin da kuma kewayensa, tana fita ta cikin lasifikokin dake manne a kowanne bango.

A daidai wannan lokacin kuma Sunusi ya shiga masaukin Madaki, biye dashi wata baiwa ce daya nemo wadda ta san duk wani tarihi da bayani akan MAIJIDDA!

Haka kuma a daidai wannan lokacin, Fulanin ta aika da tarin kuyangu b’angaren d’akunan Jakadai, a d’auko mata amarya MAIJIDDA don gabatar da kamun aure irin na al’ada!4

Yau amarya kin fito ana kallonki,

Yau amarya zaki kwana babban d’aki,

Sallama dai zaki yiwa ahali naki,

Kuyi Sallama addu’a ake yi dangi,

Daina kuka ke Amarya ba’a raki,

Daina kuka ya biya sadaki naki,

Daina kuka don idonki zai dame ki….

Wannan wak’ar ita ke fita daga bakin wasu dattijan mata dake zaune a falon b’angaren Fulani suna kid’an kwarya, yayin da b’angaren ke cika a hankali da al’ummar dake b’ulb’ulowa daga koina a masarautar jin cewa ana biki, wanda mafi yawancinsu duk jama’ar masarautar ne da unguwannin cikinta.

Falon farko na b’angaren Fulanin aka shimfid’e da tarin dardumai inda kowa ke da ikon shigowa a yau sannan kuma an tanadi abinci kala-kala yadda wani zai rantse cewa dama an dad’e ana shiryawa wannan ranar.

Daga cikin wata hanya a falon kuma akwai wani d’an madaidaicin d’aki wanda aka yi shi musamman saboda saukar bak’i irin na nesa, a cikinsa ne Amarya ke zaune tare da wasu daga cikin ‘yanuwanta.1

Jidda na k’unshe cikin wani k’aton farin mayafi da aka sa ta canja kafin a taho da ita, tana zaune daga tsakiyar makeken gadon dake d’akin ta kifa kai tsakanin cinyoyinta, tana sheshshek’ar kukan da yak’i karewa tun daga lokacin da ‘yan uwan mahaifinta suka iso d’akin Baddo da cewar an d’aura aurenta da mutumin da kowa ke kiran sunansa da Ibrahim, wanda bayan lokacin da taji Baddo na yiwa ‘yan uwan mahaifin nata cewa shima d’an Mai martaba ne bata san wani abu game dashi ba kuma.1

Kasancewar babu kujera a d’akin yasa kusan dukkanin wanda ke ciki a kan gadon suke zaune, amma Aunty Zainab da Jamila sune a kusa da ita, Jamilan na rik’e da hannunta cikin sigar lallashi yayin da Aunty Zainab ke ta tausarta da maganganun da take tunanin suna tasiri akanta.

Sadiya na tsaye daga can jikin tagar d’akin tana faman rarraba ido cikin irin nata tashin hankalin itama, don ba komai ne ya k’ara hargitsa ta ba sai ganin irin kukan da Jidda keyi tun d’azu, Jiddan da ta sani mai k’arfin zuciya da tunkarar kowanne irin abu cikin ganganci… Yau sai aka samu wani yak’in da yaci galaba akanta.1

Daga jikin tagar da take tsaye, kunnenta na jiyo mata sautin kid’an kwaryar dake tashi a can falo inda akace za’ayi kamun, har a yanzu zuciyarta ta kasa yarda, ta kasa yarda wai bikin Jidda ake yi a yau kuma a b’angaren Fulani, b’angaren da ko a jiya tsakaninsu dashi sai dai hange ko kuma in har wani dalili ya shigo dasu to tabbas gwiwoyinsu zasu durk’ushe ne a k’asa cikin jiran umarni.

Saboda haka ta kasa gano dalilin da zai sa ayi musu irin wannan girmamawar, don kowa ya riga ya san cewa Fulani bata tab’a sanyo sha’anin wani cikin nata, don haka ta yaya zata sa ayi wannan hidimar don auren d’an mijinta kawai? Tunda kowa ya san cewa wanda aka kira da Ibrahim d’in ba d’anta bane, amma ana kyautata zaton d’an Mai martaba ne tunda haka aka sanar a masallaci cewar za’a d’aura auren d’an Mai martaba.

A d’azu kafin tahowarsu Jidda ta riga ta shaida musu duk abinda ya faru kuma kowa ya gamsu da ita sanin cewar k’arya ba halinta bane, saboda haka ne ma Baddo da Hajiya Laraba suka yanke shawarar cewa dole ne a canja labarin da zai isa kunnen mutane don a rufe laifinta, sai aka gyara shi da cewar Mai martaba ya yanke hukuncin had’a auren ne ba tare da shirinsu ba suma, saboda haka duk wanda yayi wani k’orafi cewa ‘wane irin aure ne wannan?’ hakan ke rufe bakinsa.1

Sai dai mutanen masarautar wad’anda suka san da labarin b’atanta jiya sun d’an shiga rud’anin ta yadda hakan zai kasance a lokaci guda, amma da yake babu wani mai kwakkwarar hujja in banda matan da suka kwana a d’akin Baddo a ranar, sai suka ja bakinsu suka yi shiru saboda tsoron abinda zai iya biyo baya tunda ana ganin sun shiga fada a yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma kafin lokacin da Fulani ta aiko a taho da Jiddan, Baddo ta sanya an kira wasu daga cikin ‘yanuwanta dake cikin gari an shaida musu, don haka ne ma a yanzu d’akin da suke ya d’an cika, kowa sai murna yake yana fad’in ashe dawowar Jiddan hannun Baddo alkhairi ne.2

Basu ko damu da ganin yadda take kuka ba, a tunaninsu yarinta ce kawai da kuma taraddadin auren fari tunda ance itama bata san mijin ba, kawai hankalinsu na hangen matsayin da zata samu ne da kuma cewa ta shiga gidan arzik’i, don har wata a cikinsu na fad’in..

‘… kin cika wauta Jidda! Ban da abinki ko tsoho aka aura miki in dai jinin masarautar nan ne meye na kuka? Yawo zaki yi dashi ko lik’awa a goshi? Ubangiji yayi miki wannan alfarmar a zab’o ki cikin dubunnai a d’ora ki a wannan matsayin amma ki dinga kuka? Jamila ki fad’a mata wannan ba dabara bace gwara ta saki jikinta ta zama wayayyiya irin ‘yan mata a shekarunta…’

A baiyane yake cewa ba su kad’ai ba kowa na hangen cewa Jiddan ta taki sa’a ne kawai tunda babu wanda ya san mak’asudin abinda ya haddasa auren.

“Jidda… Kina jina ko? Nace ki d’ago ki kalle ni.”

Muryar Aunty Zainab ta fad’a bayan wani lokaci.

Daga yanayin muryarta kad’ai Jidda ta san cewa ranta ya soma b’aci kuma da gaske take, don haka ta d’ago da fuskarta a hankali daga cikin duhun dake tsakanin cinyoyinta, hasken d’akin ya shiga cikin kumburarrun idanunta da suka sha kuka, sai ta runtse su yayin da kanta ya sara.

“Kukan naki ya fara yawa, ya kamata ki hak’ura haka ki saduda, tunda dai kin san babu abinda zamu iya yi yanzu, sai dai kuma in so kike mutane su fara zargin wani abu.”

“Kanki yana ciwo?”

Ta girgiza kai.

“To me zaki ci? Ba abinda kika sa fa a cikin ki tun safe?”

“Ba abinda zan iya ci Aunty Zainab, bakina ba dad’i.”2

Muryarta ta fito a tsaye amma cikin sautin wanda yasha kuka, a lokaci guda Jamila taji hankalinta ya d’an kwanta, don ta tsinto ainihin Jiddan data sani a cikin sautin muryar, k’anwarta da ba komai ke tsorata ta ba balle har zuciyarta ta karye, hakan ya tabbatar mata da cewar kukan da take yi na takaicin faruwar abinda bata tab’a tsammani bane, ba wai don zuciyarta ta karaya da komai ba.1

“Zaki cuci kanki ne wallahi…” Cewar Aunty Zainab din.

“… Idan kika ce baza kici abinci ba kina ganin hakan zai canja wani abu ne?”

Jidda ta had’iye k’ullutun wani abu a mak’ogwaronta, ta riga ta cuci kanta ai tun a jiya data je wajen daya ruguza dukkan mafarkan da ta dade tana tarawa a kwakwalwarta, irin mafarkin da kowacce mace ke yi na yadda aurenta zai kasance tare da wanda zuciyarta ta zab’a a kuma a yanayi na farin ciki… Amma ai gashi ita da gudunmawarta ta janyo k’addarar da ta juya komai a sigar da babu ko d’aya daga wad’ancan burikan.

Da ganin mijin, da d’aura auren nata kwata-kwata bai fi tazarar lokacin da za’a soya gyad’a, a k’ulla ta a leda cikin farashi mabanbanci, sannan mai talla ya d’ora a kai ya zagaya ya siyar ba, to don me kuwa ita da zuciyarta ba zasu yi makokin hakan ba?

“Ai babu zancen ba zata ci abinci ba Zainab, so take ta fad’ar mana a hanya ko kuwa so take a kai ta zuru-zuru angon ya zata sikila aka aura masa?”3

Cewar wata daga cikin ‘yan uwan Baddo, sai kuma ta kalli Jamila tace.

“Wai yaushe za’a kaita ne ma?”

Ya kamata ace tambayar ta bata tsoro, amma ko kad’an zuciyarta bata girgiza ba, don ta riga ta yarda cewa baza a k’araso wannan gab’ar ba, babu ta yadda za’ayi wannan mutumin data gani ya yarda ya zauna da ita a rayuwarsa, su ne basu sani ba tunda basu ganshi ba amma shi da ita kamar hanyar mota ne da kuma akori kura… Yana da wayewar da in an d’aura masa ita ba da son ransa ba, tsaf zai iya cilli da ita da irin nasa ikon.1

STORY CONTINUES BELOW

Don ta riga ta sani kuma har ta tab’a gayawa Sadiya cewa masu kud’i da muk’ami kamar sa, ba irinsu suke aura normal mutanen gari ba sai kyawawan matan da suka amsa sunansu, shima kuma Mai martaba don dattijo ne bai san da hakan ba shi yasa rashin sani ya d’ebe shi wajen yanke wannan hukuncin.1

Ta lumshe idanunta a hankali tana hango nasa sanda yake tsaye a gabanta jiya, bata manta ba, bak’ar T-shirt ce a jikinsa mai gajeran hannu, fatarsa tayi haske sannan gashinsa da alamun jik’ewa kamar ya fito daga wanka, bayan haka tana iya tuno k’amshin turarensa wanda ya dinga busawa a hancinta ta rasa inda ta san irinsa.

A wannan lokacin, ita kuma tana tsaye ne a gabansa da kumburarriyar fuskarta data tashi daga bacci, watak’ila ma har da kwantsa a idanunta sannan ga cukurkud’adden hijabinta daya b’aci da jini… Don haka kallon da idanunsa ke mata kamar yaga wani tsumman kitchen ne jik’akk’e!2

“Ki tashi Jidda, la’asar ta kusa ga band’aki nan kiyi wanka sannan ga kayan da zaki saka in za’ayi kamun… Kuma idan mun dawo wallahi dole ne kici abinci.”

Muryar Jamila ta fad’a bayan sun gama tattauna amsar da bata maida hankali taji ba. Ta juyo ta kalli kayan da take mik’o mata, wani lace d’in sallarta ne wanda kwanaki ba irin rok’on da bata yi mata ba akan zata ara mata ta saka in za’ayi maulidin makarantar darensu amma ta rantse da Allah ta kuma rantsewa cewa ba zata bayar ba, sai gashi yanzu a b’agas.2

“… Sannan zaki yanke wannan farcen naki, kuma zan miki kitso komai dare, kanki a wanke ya ke ma?”

“Ba alama…” Cewar Aunty Zainab sanda take ture mayafi da d’ankwalin kanta.

“… Kema kin san ba son wanke kai take yi ba.”

Bata ce dasu komai ba, don zuciyarta na gaya mata zasu zo suyi nadamar wahalar da zasu sha ne, watakila ma sai Jamila ta tsine mata akan saka lace d’in lokacin da aka aiko da takardar sakinta. A cikin kumburarrun idanunta da suka sha kuka ta hango cewa watakila ya rubuto takardar da d’aya daga cikin wad’annan had’add’un birukan da ta gani a jakarsa….3

Ni Ibrahim na saki k’azamar yarinyar da aka d’aura min aure da ita a yau saki d’aya…8

Biyu, watakila ma har uku, sannan ya zana irin wannan had’add’iyar signature da ta gani a k’asan takardunsa.2

“Yauwa Sadiya, taya ta da wad’annan kayan zuwa band’aki dan Allah, bari mu koma da Yaya Fati in k’ullo d’akin, yanzu Hajiya laraba ta aiko wai Fulani ta kira Baddo yanzun nan.”

Jamila ta fad’a tana mik’awa Sadiya data matso kayan hannunta kafin ta mik’e daga kan gadon. Dama tun farko Baddo bata biyo su ba, a can suka barta saboda su Alhaji basu tafi ba, sun tsaya cin abincin da aka kawo musu musamman daga gidan Galadima, shi yasa Hajiya Laraba ma ta zauna tare da ita.

Jidda ta d’ago ta kalli Sadiya wadda ta karb’i kayan daga gefen gado, idanunta sun d’an canja itama alamun ta shiga irin nata tashin hankalin, ta riga ta san cewa laifin kanta take gani na cewar da ta bita sunje neman Fullo tare, da watakila duk wannan al’amarin bai zo a haka ba.

Itama kuma ta yarda cewa har da kamashon laifin nata a ciki, kuma in har tana son ta wanke kanta, to dole ne ta ajiye duk wani tsoronta ta taya ta d’aukar fansa akan Suraj bayan wannan bidirin ya k’are an sake ta.1

Idonta ya kai kan had’add’iyar wallpaper dake manne a bangwayen d’akin, a lokacin wani tunani ya gifta cikin kanta, tun a washegarin sanda ta dawo masarautar, lokacin da Baddo ta kawo ta wajen Fulani don ta gaishe ta bata sake tako k’afarta cikin b’angaren ba, ashe k’addara ce zata sake kawo ta cikin wani irin matsayi.

Zuciyarta ta d’anyi mamakin dalilin Fulsninna sawa a kawo ta amma muryar Aunty Zainab da ta sake yi mata magana yasa ta sauka daga kan gadon a hankali tabi bayan Sadiya zuwa k’ofar band’akin dake manne daga gefe.

STORY CONTINUES BELOW

A lokaci guda taji k’afafunta sun sage saboda zaman da tayi waje d’aya sannan kanta na sarawa, sai dai kukan nata ya riga ya tsaya dalilin wad’annan tunanin da kwakwalwarta tayi.

Gani take komai ya kusan zuwa k’arshe, watakila ba lallai satin nan ya k’are ba mijin k’addarar zai je ya sulhunta da mahaifinsa ya samu damar rabuwa da ita. Ta san cewa sunan ta ne zai b’aci, zata zama ‘yar k’aramar bazawarar da mutane zasu yi ta cece kuce akanta, amma kwana biyu ne hakan zai wuce komai ya dawo daidai.

Komai! Sai dai ban da Fullonta… kawai dai zata iya dawowa kan rayuwarta ta cigaba daga inda ta tsaya.1

Abinda Jidda bata sani ba a lokacin shine, ‘Komai’ d’in zai fara ne daga sanda ta fito daga band’akin nan!

***

Akwai wani irin shiru dake ratsa waje a lokaci guda, misali d’aki mai cike da mutane ana hayaniya, sai kaga an sami dacewar lokaci yadda cikin had’in baki kowa zai yi shiru a lokaci guda, hakan bashi da wani tushe amma mutane kan danganta shi da alamun mutuwa, ta yadda har ya sami lak’abin sunansa ‘Ta ratsa!’

Irin wannan shirun ne ya faru a falon Fulani na uku lokacin da Jakadiya ke shaidawa Baddo cewar akwati biyar d’in dake gabanta wanda kowanne shak’e yake da nau’in kaya na atamfa da laces da kuma mayafai wai nata ne ita da Jidda.

Kowannensu yayi shiru a d’akin sannan a lokaci guda hayaniyar dake tashi daga can waje ma ta mutu, hatta masu kid’an kwaryar nan sai da suka kai aya kamar suma sun tsinci girman zancen.

Baddo ta d’ago ta sake kallon akwatinan, sannan idonta ya sauka akan Fulani, wadda ke hard’e cikin luntsumemiyar kujerarta tana kallonta d’auke da murmushi a fuskarta, sai tayi saurin dawo da idanunta k’asa ta sunkuyar sannan tace.

“Ranki ya dad’e ban fahimci zancen ba ayi min gafara.”

Muryarta ta fito cikin girmamawa da kuma rud’ani.

“Abinda ta fad’a miki haka yake Jakadiya, wannan kyauta ce daga gare ni zuwa matar Madaki da kuma ke da kike kakarta… Kyauta ce kawai irin ta tsakanin sirika zuwa ga sirikanta.”

A lokaci guda Baddo ta had’iye yawu yayin da ciwon k’afarta dake durk’ushe ya harba zuwa kanta, a cikin abu guda biyu bata san wanne yafi rud’ata ba, ganin ta yau fuska da fuska a gaban Fulani abinda bai tab’a faruwa ba tunda suka karb’i sarauta ko kuma cewar Fulanin da kanta ta d’auko kyautar da bata tab’a mafarkin irinta ba tsawon rayuwarta ta dank’a mata?

Zuciyarta ta ayyana mata cewar da gaske ne hasashenta… da gaske ne hasashen da take yi tun daga lokacin da Jidda ke shaida musu Mai martaba zai d’aura mata aure da mutumin da bata san shi ba, da kuma lokacin da ‘yan aiken Jarmai suka zo neman mai raka su Kacalla suke shaida mata cewa Ibrahim Madaki shine wanda Sarki zai d’aurawa jikarta aure dashi.

Bata yi kuskure ba ko kad’an, don a shekaru hamsin da uku da tayi tana rayuwa a masarautar, kwakwalwarta ta riga ta san duk ire-iren wani makirci da kutunguilar gidan sarauta. Kuma ubangiji shine shaida ko a baya sanda ta yiwa d’aya daga cikin matan Sarki mai rasuwa ‘Jakadiyar d’aki’ bata tab’a bata shawarar da zasu muzuntawa wani don cimma wata manufa ba.

Sai gashi a yau ita ta fad’a irin wannan tarkon, Jidda ta d’auko su ta cilla cikin man dake tafasa akan wuta, don watakila har gwara hakan akan wannan k’ulalliyar tarzomar da suka shigo cikinta ta tsakanin Fulani da Madaki, k’iyayyar da babu wanda ya san asali balle tushenta, don tun kafin hawansu mulki ance itace sanadin da yasa saki ya tab’a shiga tsakanin Fulanin da Mai martaba.

Shi yasa a lokacin da suka ji zancen da safe, ita da Hajiya Laraba da wasu daga cikin abokan aikinta suka yi kokarin b’oye sunan Madaki a wajen mutane musamman ma mazan da suka zo d’aurin aure, kowa ya tafi da cewar sunan mijin Ibrahim kawai.

STORY CONTINUES BELOW

Ta san cewa hakan ba shi ke nuna cewar sun gujewa komai ba, hasali ma komai zai fara ne daga rana mai kama da ta yau.

Sai gashi nan kuwa tsibe a gabanta… Tarin dukiyar dake musu maraba lale da shigowa wani sabon sirad’i na rayuwa, wanda ta san yana cike da dukiya da kuma kyale-kyalen da tsaf zasu iya rasa imani dama rayukansu in ta kama.2

Ta sani cewa Fulanin shugabarta ce wadda bata isa ta tsallakewa umarninta ba amma babban abinda ta sani shine Jidda jikarta ce, gudan jinin da irinsa ne ke yawo a nata jikin, don haka ba zata tab’a bari ta rasa ta ba akan k’iyayyar dake tsakanin wasu mutane guda biyu.1

Ta ayyana hakan daidai lokacin da muryar Fulani ta sake sulalewa zuwa kunnuwanta, d’auke da wannan ikon da take ganin cewa duk duniya babu wanda ya isa ya tankwab’e mata shi.

“Aje a taho min da Amarya Jakadiya, da kaina zanyi kamun matar Madaki!'”1

***

A k’aidar masarautar Kiyari, akwai babbar harabar da ake ajiye motoci daga k’ofar kudu, wadda in ka wuce filin farko nan ne wajen da zaka fara gani kafin ka isa cikin kwaryar masarautar.

Wata irin k’aida ce da aka kafa tun usuli cewar mota bata tab’a wuce wannan wajen, don ko garejin ajiyar motocin Mai martaba anan yake, duk inda yaje ya dawo anan zai sauka ya k’arasa cikin gida da k’afarsa.

Da misalin k’arfe hud’u da ‘yan mintuna, daidai sanda limamin babban masallaci ya rangad’a sallamar sallar la’asar, Madaki ya karaso harabar ajiyar motocin, ya isa ga inda tasa take lokacin da muryarsa ke magana a cikin wayar dake kare a kunnensa.

“I don’t care Mabarak, na riga nayi compling komai kuma yau zan taho don haka babu wanda ya isa hana ni.”

“Mdee kabi abin nan a hankali, ba lallai yarinyar nan…”

Dib! Ya katse wayar sannan ya bud’e motar ya cillata ciki kusa da inda jakar sauran kayansa da Sunusi ya kawo masa take.

Kamar zai shiga ciki kuma sai ya dafe kansa yana kallon sitiyarin motar, babu abinda ke harbawa a kan nasa illa maganganun baiwar nan, bi da bi suke bi suna shiga kowanne lungu da sak’o na kwakwalwarsa har da inda bai san akwai ba.

Idanunsa sun riga sun rine da tsananin b’acin rai sannan zuciyarsa na bugawa da dukkan yamutsin dake gaya masa cewa yana cikin matsala in har bai gana da likita a yau ba… Amma hakan zai biyo ne idan ya kammala abinda ke gabansa kawai.

Ya shiga motar ya saka mata key ya tayar sannan yayi baya ya fito daga cikin jerin motocin dake cikin layin, sai da maimakon ya juya yayi hanyar fita, sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar cikin gida.

Ba wai gudu yake ba amma saboda tashin hankali ganin abinda bai tab’a faruwa ba yasa mutanen dake kan hanya suka dinga darewa, yara na ihu tun kafin ma ya k’araso inda suke.

Tana ina yanzu?

Muryarsa tayi amsa amo a cikin kansa.

Tana b’angaren Fulani, za’ayi mata kamun al’ada…

Muryar baiwar ta biyo bayan tasa.

Ya cije lebb’ensa da k’arfi sanda ya sha kwanar da zata sada shi da kwaryar tsakar gida inda anan b’angaren matan sarkin yake, wasu tarin yara dake wasa a gefe suka kwallara k’ara ganin mota na yo kansu… Madaki yaji k’arar na amsawa har cikin kwakwalwarsa yayin da kowannensu ya dare.

Sai dai bai tsaya ba har sai da ya isa daidai kofar shiga b’agaren Fulanin inda yawaitar mutane wajen ta tabbatar masa da cewar da gaske baiwar take, da gaske Maijidda na cikin wannan taron.

Bai ko damu da yadda mutanen ke rikicewa kafin su bashi hanya ba har sai da ya dangana da k’ofar shiga b’angaren sannan ya tsayar da motar, kuma bai cire muk’ullin jiki ba balle ya tsaya rufe k’ofar, ya sanyo k’afafunsa waje kawai ya fito.

STORY CONTINUES BELOW

***

“Masha Allah, Amarya dai kowacce iri ce bata b’uya, kinyi kyau.”

Cewar d’aya daga cikin matan dake zaune a d’akin lokacin da Jamila ta gama yiwa Maijidda d’auri sannan ta yafa mata k’aton farin mayafin da ya dace da lace d’in jikin nata.

“Sai aukin kumburarrun idanuwa..” Cewar Aunty Zainab.

“Wadannan masu wucewa ne ai…”

Wata ta fad’a, hakan yasa da yawansu yin dariya, a lokacin kuma an kawo musu abinci don haka kowa da faranti a hannunsa suna ta ci cikin santin nau’in abincin kala-kala.

“Tunda kinyi sallah kafin mu fita sai kin ci abincin nan Jidda, bari in zubo miki.”

Cewar Aunty Zainab, sanda ta juya inda aka ajiye musu kulolin abincin.

Sadiya ta matso ta mik’o mata wasu ‘yan kunnaye data d’auko daga jakar Aunty Zainab, Jiddan ta kalle ta sannan a hankali muryarta ta fito.

“Wai meye kike ta had’e rai ne? Nifa ba fushi nake da ke ba.”

Ta d’an tsaya tana kallonta kamar zata ce wani sai kuma tayi murmushi mai fad’i, a lokaci guda Jidda itama taji murmushin ya sub’uce daga bakinta, tsakanin kwanaki uku kawai tayi kewar yinsa kamar wata uku.

Abinda bata sani ba a lokacin shine, tazarar dake tsakanin sake yinta da wani murmushin mai tsayi ce.

K’ofar d’akin ta bud’e a daidai wannan lokacin, kuma a lokaci guda idanun duk wanda ke d’akin suka gane masa siffar wanda yake tsaye rik’e da hannun k’ofar, wani mutum mai cike da cikar zati da kwarjinin daya haifar da mutuwar bakin kowa a d’akin, sannan shiru ya gifta a lokaci guda, irin wannan shirun da akewa lak’abi da ‘Ta ratsa!’

Jidda dake zaune tana fuskantar k’ofar ta ware idanunta akansa kamar kowa, sai kuma ta rufe su sannan ta sake bud’ewa duk a cikin abinda bai wuce dakika guda ba… A take kuma zuciyarta tayi k’ulik’ulin kubra sannan ta fad’o daga wata sama mai nisa.

Yana sanye ne cikin wani bak’in yadi d’inkin fitted mai kyau, rigar bata kai gwiwa ba sannan babu aiki a jikinta sai irin sealed d’inkin nan da maza ke yayi, kuma babu hula akansa sai sumar kansa data sha taza wanda hakan ya k’ara fito da hasken fatarsa.

Ya saki hannun k’ofar daya rik’e daidai lokacin da idanun Jidda ya gane mata tarin bayin da suka biyo bayansa wad’anda ke ta faman durk’usawa cikin gaisuwa wasu kuma sun riga ma sun zube a k’asa, sai dai babu alamun cewa shi d’in san dasu.

“Sunana Ibrahim Ahmad Madaki.”

Amon muryarsa mai kauri da zurfi ta keto cikin d’akin kamar tsawar ruwan dare.

A lokaci guda ruwan cikin Jidda ya k’ara tsurewa, ba wai don tunanin cewa sauran mutanen d’akin basu gane shi ba, sai don taraddadin inda ta san cikakken sunan…

IBRAHIM AHMAD MADAKI!

Ai kuwa ba tare da wani kewaye-kewaye ba idanunta suka hasko mata ranar bikin Aisha, sanda ta tone ramin asirin nan na farko, a jikin layar data d’auko daga k’asan wannan rubutun da bata iya karantawa ba, wannan shine sunan da aka rubuta b’aro-baro cikin harafan boko.

Idanunta suka sake girma kamar gurjiyar da aka watsa a faranti, sannan wani ya d’auki zuciyarta yayi cilli da ita wata duniyar daban… Ibrahim d’in da Mai martaba ya d’aura mata aure dashi a yau shine Madakin da ta dad’e tana tone asiri akansa??? Dama d’an Martaba ne? Ya akayi babu wanda ya gaya mata hakan?1

Shikenan ta shiga uku! Daga ita har Sadiyan dake tsaye a gefenta kuwa.

“Barka da isowa ranka ya dad’e…” Muryar Aunty Zainab ta katse shirun d’akin lokacin da take ajiye plate d’in hannunta wanda ta fara zubawa Jidda abinci a cikinsa.

Maimakon ya amsa sai ya kalleta kawai sannan dunk’ulalliyar muryarsa ta sake cika d’akin.

“Wacece Maijidda a cikinku?”1

Inda ace a duniya ana fad’awa d’an adam ranar da zai mutu kuma hakan ya tabbata, to kwatankwacin irin wannan tashin hankalin kwakwalwar Jidda ta shiga lokacin da Aunty Zainab ta juyo ta nuna ta.

Kallo d’aya Madaki yayi wa wajen da hannunta ya nuna, ya gane wacece Jiddan don shigarta ta k’aton farin mayafi ta banbanta da sauran.

Bayan hakan bai kula da komai ba ya k’araso cikin d’akin, ya wuce wad’anda ke zaune a k’asa ya zagaya ta gefen gadon ya isa gabanta.

K’amshin turarensa shi ya k’ara tsurar da Jidda ta fita daga haiyacinta, kuma a lokaci guda ta gane inda ta san k’amshin, a jikin wannan layar ne da kuma asirin da suka hak’o na biyu… Sai dai kafin ta kai ga gama wannan tunanin abinda bata tab’a tsammani ba ya faru.

Madaki ya sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan taji d’umin hannunsa d’aya ya nad’e cikin nata… Kuma ba tare da jiran wani abu ba ya d’ago da ita sannan ya shiga janta suka nufi hanyar k’ofa.

Tsabar mamaki da rud’ewa yasa ta shiga juyowa tana kallon mutanen bayanta yayin da a cikinsu suma aka rasa me cewa wani abu. Madaki bai tsata ba ya cigaba da jan ta suna wucewa ta hanyar wajen har zuwa babban falon inda ake gudanar da kid’an kwarya.

A daidai lokacin kuma Baddo ta fito daga wata k’ofa a jikin falon, biye da ita wasu bayi ne d’auke da akwatunan kayan nan wad’anda da sun ajiye zasu fito da Jidda don don a fara gudanar da kamun bisa umarnin Fulani. Kuma anan ma Madaki bai tsaya ba yana rik’e da hannunta suka dinga wucewa ta cikin mutanen dake ta faman durk’usawa suna gaishe har suka ya dangana da waje, inda motarsa take.

Suna k’arasawa ya bud’e k’ofar wajen mai zaman banza ya sanya ta a ciki sannan ya rufe ya zagayo ya shiga mazaunin direba.

A lokacin idanun Jidda suka hango mata su Aunty Zainab da suka biyo bayansu tare da sauran mutane suna firfitowa, sai dai kafin idonta ya gama tsayawa ma akansu Madaki ya juya kan motar da wani irin gudu suka bar wajen!7

***

Fulani ta shirya,

Baddo ta shirya,

Amma da alama Madaki a shirye ya kwana…

Yaya kuke tunanin zaman nan zai kasance?

Me baiwar nan tace daya harzuk’a Madaki?+

Me Madaki ya shirya akan Jidda ta yadda zai d’auki fansa akan Fulani?

Ta wace hanya yanzu Fulani zata isa ga Jidda  har ta samu galaba akan Madaki?

Na gaya muku cewa Jidda ta shiga tsaka mai wuya!😅

***

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *