ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 7 KARSHE BY AISHA-SHAFIEE

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Gidan a share yake tas, dama ya gaya mata tun a hanya, yace ya saka yaron da yake masa shara kafin zuwanta ya gyara, don haka sai taga kamar jiya suka tafi yau suka dawo. Komai yana nan inda yake ba’a taɓa ba, hatta ƴar ragowar dubu ɗayanta da ta bari a cikin wardrobe tana nan, don haka tana ajiye kayanta banɗaki kawai ta shige tayi wanka, ta janyo daya daga cikin dogwayen rigunanta mai sauƙin nauyi wata ƴar fale-fale kalar sea green ta saka, ta feshe jikinta da ɗaya daga cikin turarukanta da bata taba sawa ba sannan kai tsaye ta nufi wajen sahibul qalbinta… Kitchen.3

Madaki bai ƙaraso ba har a lokacin don bayan sun iso gari, direbobi biyu suka tadda a parking lot na airport ɗin, ɗaya ya kawo motar Mubarak ɗaya kuma Baba Saminu ne da motar Madaki, kuma sai bayan sun rabu da Mubarak ne sun shigo motar yake gaya mata cewar yayi booking appointment zai tsaya a asibiti ganin likitansa don haka bayan sun sauke shi, ita kadai Baba Saminun ya ƙaraso da ita gida sannan ya koma ɗauko shi.

Ta nufi kitchen ɗin zuciyarta na yawo a gajimare kan tuna yadda gabadaya tafiyar ta shafe hannunta na cikin nasa yana zana wani abu kamar adadin yadda zuciyarsa ke ƙaunarta, kuma saboda Mubarak a tare dasu basu yi wata magana mai tsawo ba amma lokaci-lokaci ya kan tambaye ta wani abu game da kwanakin da suka shafe basu haɗu ba, kwanakin da har yanzu bata ga laifinsa ba don bai nemeta ba, mahaifinsa ya rasa cikin mutuwa irin wadda tafi taɓa zuciya da shiga ciki, mutuwar bazata, to kuwa don shi yafi kowa ɗokin aure sai ya manta komai ya neme ta a cikin dubunnan jama’ar masarautar nan? Mutanen da ko a yau da suka taho an share makoki ma amma ba kowa ne ya gama tafiya ba.4

Dukkan tunaninta sai yabi iska a lokacin da ta buɗe ƙofar kitchen ɗin nan tayi arba dashi, haɗadden kitchen ɗin da a yanzu babu wani kokwanto ta san zata rayu dashi tsawon lokaci, shima a share yake tas, ƴan dim fitilolin nan na ƙasan drawers ɗinsa na haskawa yayin da lubalensa na jikin window yake a rufe… Ya Allah! Ashe tayi kewarsa kamar me…!4

Labulen windon ta fara budewa sannan ta nufi fridge ta buɗe don taga lafiyar kayan cikinsa, ilai kuwa duk da sanyin da yake yi su karas da kabeji dake ƙasa sun fara ruwa ta gefensu wasu ma sun narke gaba ɗaya. Don haka ta fito dasu ta ware ƴan ragowar da suka rage masu kyau sannan ta wanke su ta canja musu waje, kafin ƙwaƙwalwarta ta shiga lisasafin abinda zata dafa mai sauki, don yamma ta fara yi kuma ta san ba lallai Madaki ya kai magriba ba.

Ta nufi store ta buɗe tana kallon kayan abincin sai idonta ya kai kan kwalin wata taliya mai irin siffar shinkafa, don haka a lokaci guda ta yanke shawarar yin jollof dinta, sai ta danyi farfesun ragowar kifin da ya rage mata guda ɗaya a fridge.

Wuyar girki shine in baka sami kayan aiki akan lokaci ba, da yake tana da komai har markade a fridge cikin lokaci kankani sai ta hada ruwan jollof ɗin har m ya tafasa ta zuba taliyar, tana yi kuma tana grating din atturuhu da albasa na farfesun bayan ta fito da kifin daga fridge, cikin ɗan lokaci sai gashi shima ta gama hada shi kitchen din ya baɗe da ƙamshin curry kala-kala. Sai kuma tayi tunanin ta ɗanyi coslow tunda bata saka nama a jollof ɗin ba don haka ta nufi fridge ta fito da kabeji da karas kawai ta fara yankawa tana ganin ai yanzu ma zata gama komai, abinda bata sani ba shine lokaci ya tafi da yawa itace kawai dake jin dadin aikin bata gani ba.

Kuma hakan ne yasa kwata-kwata bata ji ƙarar buɗewar ƙofar kitchen ɗin ba sai gani tayi alamun mutum na tahowa gabanta, tana tsaye ne a tsakiyar kitchen din daga gefen island ɗin nan, ta dora plate ɗin da take yanka kabejin akan island ɗin yayin da ita take tsaye, jin motsi yasa idonta ya kai hanyar ƙofar ya dawo kafin ta sake maida shi da sauri ta kalli Madakin dake shigowa, hannayensa duka biyu sanye cikin aljihun wandonsa yayin da lumsassun idanunsa ke kallonta.

Ta kalli ƙofar bayansa sannan ta sake dawowa ta kalle shi a lokacin da ya tsaya a ɗaya ɓarin teburin.

“Wa’alaikum salam.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta amsa sallamar da bata ji ta ba har a lokacin da mamaki akan fuskarta, sai ya motsa gefen bakinsa cikin wani abu da bata tabbatar murmushi bane sannan yace.

“Nayi sallamar, baki ji ni bane.”

Kamar ta bashi amsa da cewar don bai yi maganar da ƙarfi bane sai kuma ta fasa, ta gyada kanta kawai sannan tace.

“Sannu da zuwa.”

“Yauwa.” Ya amsa a gajarce yayin da idaunsa suka zamo kan hannayen ta da kuma farantin kabejin da take yankawa.

“Baki gaji da hanya ba kike aiki?”

Muryarsa ta fito a hakali yana kallon yadda yatsunta ke rike da wukar ba tare da ta cigaba abinda take yi ba, wani abu ne ke bi takan zuciyarsa a lokacin, wani abu da bai san menene ba, yana ƙoƙarin fasa ginin daya lullube ta, bai san menene shi ba, nutsuwa ko kuma dadi na cewar aƙalla yana da wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa, bai rasa komai gabaɗaya ba.

Allah ya sani shi ya manta ma da wani lissafin abinci balle ya hango cewar in har shi bai damu ba ita zata nemada sun tsaya tun a hanya sun siya ya hutar da ita, amma kuma shima yanzu da yaji ƙanshin sai yaji cewa cikinsa ya faɗa don ko breakfast ɗin safe da aka kawo musu kaɗan kawai yaci ya tashi ya shiga neman Sunusi akan yaje banki ya ciro masa kuɗi don na hannunsa sun ƙare.

Kamar tace ‘Ta gaji, amma saboda shi take yi…” Sai kuma ta fasa don watakila basu ƙaraso gabar wannan kai tsayen ba, saboda haka ta cigaba da yankanta a hankali sannan tace.

“Baka da lafiya dama?”

Ga mamakinta sai yayi wani abu da ya tabbatar mata cewa sun bar irin rayuwar da suka fara a gidan ta farko kafin ya bata amsa, kujerar jikin island ɗin yaja ya zauna daidai saitin inda take tsaye sannan ya ajiye wayoyinsa biyu akai.

“I’m fine, kawai naje check-up ne saboda heartburn ɗin daya dameni tun jiya.”

“Menene heartburn?”

Kai tsaye ta tambaye shi ba tare da ta ɗago ba, don ita kalaman turancinsa ba kowanne take ganewa ba, watakila nan gaba zata gaya masa cewa karatunta iyakarsa secondary kuma secondary ma ta cikin gidan Sarki. Sai ya ɗanyi shiru shima kamar ya manta sunan abin da hausa kafin yace.

“Wannan abin da yake tasowa daga ƙirjin mutum mai zafi…”

“Oh kwannafi?’

“Right, shi.”

Sai ta gyada kanta kafin tace.

“Allah ya sawwake Allah ya baka lpya.”

“Ameen Jay.”5

Muryarsa ta fito alamun yaji daɗin addu’ar, amma ba wannan ne yasa ta ɗago ta kalle shi ba, sunan da ya faɗa ne, J? Ita yake nufi? Sai dai kallon da yake mata yasa ta kasa wani tunani mai kyau ta haɗiye yawu ba shiri ta sake hadiyewa, don duk dauriyarta wannan lumsassun idanun nasa sai da suka sa zuciyarta ta buga sau biyu a lokaci guda.

“Me zaki hada da cabbage ɗin?”

“Coslow.” Ta amsa a take kamar yin maganar ne zai kore idanunsa da take ji kamar suna bi ta kan fatar ta ko kuma tunanin da zuciyarta ke son fadawa, amma kuma sai yayi shiru bai ƙara cewa komai ba, gwara suyi maganar gwara yace wani abu tun kafin ta rasa ƙarfin cigaba da yanka kabejin.

“Ai kana ci ko?” Ta tambaya muryarta na ƙoƙarin sarkewa.

“Ina ci, indai zaki bani.”

Me? Tuna mata zai yi da tana girki babu shi? Sai ta cije leɓɓenta na ƙasa a hankali sannan tace.

“Zan baka, indai likitanka bai hana ka ci ba.”

Ta san har yanzu kallonta yake, abinda bata sani ba shine har yanzu alhini ne ko kuma ciwon ne yasa waɗannan lumsassun idanun nasa ke ka kallonta kasa-ƙasa haka?

STORY CONTINUES BELOW

“Doctors ɗina suna da kirki, basa hana ni cin dadi, gishiri ne kawai basa so in cika ci da yawa.”

“Coslow shine daɗi?”

“Bashi da daɗi?” Ya dawo mata da tambayarta.

Sai ta girgiza kanta.

“Yana da dadi a wajen ƴan gayu, amma ni bai dame ni ba.”

“Meye ya dame ki?” Yana harde hannayensa akan taburin sanda ya tambayi hakan, wadannan dogwayen hannun nasa.

Jidda bata taɓa wani iya kewaye-kewaye ko ƙarya ko iyayi ba, saboda haka kai tsaye cikin ƴar sakewar hirar tace.

“Manja, yaji, ko kuma duk wani abu da za’a saka masa atturuhu da albasa yaji kuma maggi sosai.”

A yanzu ta tabbata abinda yayi a ɗazu murmushi ne, don ba kallonsa take yi ba amma har sautinsa yanzu taji.

“Shi yasa baki da ƙiba ashe.”

Sai ta ɗago ta kalle shi mamaki na haskawa a fuskarta.

“Bani da ƙiba? Baddo kuwa kullum cewa take yi ina da jiki, tace nafi Jamila ma.”

Ya gyada kansa.

“Eh kina da jiki, amma baki da ƙiba, ina ganin kamar zan iya karya ƙugunki da hannuna kawai.”

“A ina…”

Maganar Jidda ta katse saboda wani ɓangare na ƙwaƙwalwarta da ya kwalla ihu a cikin kanta, tambayarsa zaki yi a ina ya taba gani?? Sai kawai ta sunkuyar da kanta sannan ta canja zancen da cewar.

“Babu grater a kitchen ɗin nan ko?”

Bai bata amsa kai tsaye ba, taji alamun ya cigaba da kallonta, idanunsa na shigarta don tana jin tasirinsu har a cikin yatsun ƙafarta.

“Zaki fini sani don yanzu kitchen ɗin naki ne ai Jay, duk sanda kike bukatar wani abu idan kiyi list kawai zan bawa Baba Saminu ya kawo miki.”

Abubuwa da yawa sun hadu a cikin wannan maganar, Kitchen ɗin nata ne sannan sunan ɗazu ya sake faɗa, J… Sunan da zai dinga kiranta dashi kenan? farkon sunanta… J. Ya Salam! Ashe zata taba samun suna mai dadi haka? Amma tsaya, bayan haka me yace ne? Tayi list ɗin abinda take so a kitchen ɗin? Da yawa fa, ko dai tace ya bata kudin ne kawai taje kasuwar da kanta? Zai ga zaƙewarta kuma ai, don a ka’ida ma bashi yake da alhakin siya mata kayan girki ba iyayenta ne, kuma saboda kawai auren ya faru a banbarakwai ne da ta sani Baddo zata yi iya kokarinta itama ta siya mata duk abinda zata bukata. Don haka tunda dai shi ya tambaya yanzu ba roƙa tayi ba, zai ga list kuwa.2

Saboda haka ta gyaɗa kanta sannan tace.

“Insha Allah, Madallah. Allah ya saka da alkhairi.”1

Watakila ya amsa amma dai bata ji ba, wayarsa ɗaya da ta shiga vibrating akan island ɗin ya dauka ya shiga waya da wani Habibu har ma aka hada shi da wani Samuel ta cikin wayar, don haka ta karasa yanka karas ɗinta ƙanana sannan ta mike taje wajen girkinta, ta kashe wutar kifin amma taliyar bata gama ba har a lokacin don tana da ɗan tauri fiye da asalin taliya, sai ta tsaya a jikin sink don ta sake wanke karas da kabejin kafin ta dawo ta hada coslow ɗin.

Madaki ya dago daga wayar da gama a lokacin ya kalle ta, watakila don ya kwana biyu bai ganta bane, amma yana ji kamar fuskarta ta canja masa, kamar ta shafa wani abu daya kara fito da komai na zanen fuskar tata. Ya san haka ya santa dama tun farko, kullum fuskarta babu kwalliya amma a yanzu sai yake ganin kamar ta saka wani abu ne daban, musamman yadda kalar fatarta take, wani abu tsakanin baki da fari, kamar ruwan ƙasa ko na taɓo a lokacin da akayi ruwa, koma ace shayin da yasha madara da bournvita.1

Tunda suka taho a hanya yake jin wani abu ne ke yawo a cikin kansa yana gaya masa cewa da gaske yayi kewarta don yana jin kamar wuta ce zata tashi duk sanda ta ɗago ta kalle shi idanunsu suka haɗu, idan tayi masa magana kuwa, muryata na ratsawa ne har cikin ruhinsa, yana gaya masa cewa yaci ace sun wuce wannan matakin a yanzu, saboda haka sai kawai ya ajiye wayarsa ya isa gare ta a hankali kuma ba tare da yace komai ba ya tsaya a bayanta sannan yasa duka hannayensa biyu ya riƙo ƙugunta ya manna ta da jikinsa sannan ya sanya fuskarsa cikin wuyanta yana shakar ƙamshin turaren da ta fesa.8

STORY CONTINUES BELOW

Gayawa zuciyarsa yake cewa daga yau babu sauran wani abu da zai sake masa katanga da ita, ya san har yanzu bata bashi amsar daya nema ba amma he doesn’t care anymore, tunda har ta yarda ta biyo shi suka dawo ya san ta karbe shi kenan cikin rayuwarta don haka ko bata fada masa komai ba, ya samu amsarsa don haka ba zai iya dinga hana zuciyarsa abinda take so ba.

“Thank you for coming back, thank you Jay.”

(Nagode da kika dawo, nagode Jay.)

Ya faɗa a hankali yayin da fatar bakinsa ke gogawa a gefen wuyanta.4

Duk wata jijiya ta jikin Jidda ta shiga juyawa a take, tunaninta ya ɗauke sannan wani abu ya shiga hurawa a jikinta, yadda numfashinta ke busawa akan fatar wuyanta kaɗai yasa tunaninta hargitsewa, zuciyarta ta shiga bugawa a cikin kunnenta sannan ƙafafunta suka shiga rawa ta yadda duk da yana riƙe da ita, ta dinga jin kamar zata faɗi don haka babu shiri ta juyo da sauri a cikin hannayen nasa ta riƙo gaban rigarsa kamar hakan ne zai hana shi, sai dai kuma ba abinda ya kara ma illa sake riƙe ta da Madaki yayi sannan ya sunkuyo da fuskarsa ya lalubo gefen kunnenta a hankali yace.

“Can I kiss you?”6

Tambayar ta ƙwala wata ƙatuwar tsawa a cikin kan Jidda, ba shiri ta ɗago da fuskarta ta kalle shi idanunta na haskawa wani abu da bai gama tantance shi ba, sai kuma tayi saurin sakin rigar tasa zata matsa baya amma hannayensa dake riƙe da ita suka tuna mata cewa ƙarshen takunta kenan.

Sai kawai ya matso da fuskarsa ya kara goshinsa da nata sannan idanunsa suka sauka a lips ɗin nata.1

“Just one kiss…”

Hade da numfashi ya furta maganar cikin wani irin sauti da yasa ta rufe idanunta a lokaci guda tana jin kafafunta na ƙara lugwuiguicewa kamar dafaffiyar taliyar hausa. Ganin haka yasa ya matso da fuskarsa yayi brushing saman leɓɓensa akan nata sannan muryarsa ta sake fitowa cikin raɗa.1

“… Kinji?”

Jidda bata san sanda ta shiga ɗaga masa kai ba saboda wani irin abu da take ji yana ƙoƙarin hargitsa mata ƙwaƙwalwa, kuma ba tare da bata lokaci ba ya karkatar da kansa kaɗan sannan ya haɗe ƴar TAZARAR DAKE TSAKANINSU.2

Sai dai a daidai wannan lokacin ne limamin dake masallacin unguwar ya zaɓi yin kiran sallar magriba sannan wayar Madakin dake kan island ta shiga vibrating tana motsi akan glass ɗin alamun shigowar wani kiran. Jidda taji sanda yayi wani sauti kamar na ƙorafi kafin ya matsa da fuskarsa a hankali, idanunta a rufe suke amma ta tabbata taji sautin murmushinsa kafin ya zame hannayensa duka biyu daga jikinta.

“Ki jira ni Jay, zamu cigaba daga inda muka tsaya.”11

Abinda taji yace kenan kafin su juya dukkaninsu a tare, ita ta juya ta dafe jikin sink, yayin da shi kuma ya nufi wayarsa ya ɗauka sannan ya fita daga kitchen ɗin yana amsawa.

Ana idar da sallar kuwa bayan ƴan mintuna kaɗan sai gashi ya dawo, a lokacin Jidda ta gama girkin har ta zuba a plate kasancewar babu wani flask mai girma a gidan, ta ajiye musu akan dining har da irin lemukan da yake sha a fridge da ruwa sannan ta tafi ɗaki yin tata sallar, don haka sanda ta fito yana zaune a dining ɗin yana jiranta, ya ciro cokalin dake daya plate din ya hada a nasa, kuma tun tana ɗan jan jikinta har ta saki jiki suka ci abincin, yana gaya mata cewa yayi daɗi sannan a hankali yana bata labaruka da suka danganci abin kala-kala, santi yake a fili amma bai sani ba, itama kuma bata faɗa masa saboda ƙwaƙwalwarta nata lissafin  abinda ya faru ɗazu sannan a gefe guda kuma ta san aƙalla yana hirar ne don ya kore alhinin da yake ciki, don har yanzu tana iya jin hakan a muryarsa ma, magana kawai yake amma da damuwa a sautinsa.2

Saboda haka tayi ta binsa da gyada kai har suka gama cin abincin ta kwashe kayan, kuma da yake da sauran kayan data ɓata a kitchen sai wanke kwanukan ya dauke ta lokaci, har ya fita masallaci bata gama ba, don haka tana ƙarasawa da ta fito taga baya nan sai itama tayi sallarta anan falon sannan ta nufi ɗaki da niyyar yin brush da wanke fuskarta.

STORY CONTINUES BELOW

Sanda ta shiga dakin taji alamun babu iska don haka ta tuna ashe tun da suka dawo bata bude windows din ba don haka taje ta buɗe su sannan ta ɗage labulen daya ma ta soke shi a jikin ƙarafan windon, bata kunna fitilar ɗakin ba kawai ta kunna ta toilet ɗin ta shiga, kuma har ta gama brush ɗin tana mitar taurinsa a ranta saboda shima wannan matar mai saida maganin gargajiya ce ta siyo mata, ta wanke fuskarta tata sannan ta fito, tana murɗa ƙofar kuma abinda idonta ya fara gane mata shine Madaki tsaye a cikin ɗakin, a gaban wardrobe ɗinta ya buɗe kofofin gabaɗaya yana ƙarewa kayan ciki kallo.

Ta sako kafarta waje sannan ta rufe ƙofar a hankali amma duk da haka ƙarar ta shiga kunnensa tasa shi juyowa ya kalleta, hasken fitilar waje ta windon nan data bude ne kawai a ɗakin amma duk da haka tana iya ganin fuskarsa da kuma idanunsa wanda suka tuna mata da zuwansa na farko ɗakin sanda yazo da tambayoyin kalubalantar ta, kuma kamar wancan lokacin idanun nasa sun zurma ciki suna ƙara fitar da sheƙin maiƙonsu, sai dai a yanzu ta sani cewa damuwa ce kawai da alhini.

“Su kenan kayanki?”

Muryarsa ta tambaya a sake yana kallonta bayan ya rufe wardrobe ɗin. Abinda take tunani daban ne a wannan lokacin, babu dankwali akanta don wannan bandakin na cikin ɗaki ita ganinsa take kamar dakin shima don haka bata wani damuwa da sai ta saka ɗankawali, kuma shuku ne ƙanana akanta sai jelar bata fi kamu biyu ba an tufke ta a can baya don haka ta tabbata fala-falan kunnayenta sune a fili… Su yake kallo ma yanzu.6

Sai tayi ƙarfin halin girgiza kanta daga inda take tsaye sannan tace.

“A’a, akwai wasu a gida.”

“Ina nufin anan, wannan sune kaɗai kayanki?”

Sai ta ɗaga kai lokacin da ta ƙaraso bakin gadon ta dauki ɗankwalin da tayi wulli dashi akai.

“Eh, amma na taho da wasu suna cikin ledar da take booth din motarka.”

Shima ya karaso gabanta sanda take fadin hakan don haka babu wani ɓata lokaci yasa hannayensa duka biyu ya tallafo gefen fuskarta sannan yace.

“Ba motata ba, motarmu zaki ce, from now on duk abinda na mallaka kema naki ne Jay, don in har zan iya saki a zuciyata to zan iya baki duk wani abu dana mallaka, kin gane?”1

Kamar malami da dalibarsa sai ta gyaɗa kanta a cikin tafin hannun nasa alamun ta gane ɗin, kuma duk da haka sai bai janye hannun ba.1

“Hakan ya tuna min, baki bani amsata ba na ran nan…”

Yaji sanda fuskarta ta motsa a cikin hannun nasa alamun ta hadiye wani abu amma duk da haka bata dago ta kalle shi ba, sai ya matso da tasa kamar zai ƙara goshinsa a saman nata sannan a hankali muryarsa ta sake fitowa.

“Ko kawai mu tsallake wannan part din?”

Ga mamakinsa kawai ta miƙo hannayenta itama ta riƙo nasa sannan ta girgiza kanta kafin muryarta ta fito a hankali.

“Kar mu tsallake, nima ina son in gaya maka cewa zuciyata tana sonka, ina son in zauna da kai tsawon rayuwata sannan ina son in taimake ka ta duk hanyar da zan iya, na yarda cewa Allah ya riga ya haɗa ƙaddararmu waje ɗaya saboda tun kafin in sanka zuciyata ta riƙe sunanka kuma ban taba mantawa ba.”3

Madaki ya rufe idanunsa ya buɗe su a lokaci guda yana godiya ga Allah a cikin zuciyarsa kafin ya shiga motsa babban ɗan yatsansa a gefen fuskarta a hankali sannan yace.

“Waye ya gaya miki sunana?”

Yaji ta ƙara motsa fuskarta kamar mai shirya furta wani abu babba sannan muryarta ta sake fitowa akan hannunsa.

“Karantawa nayi a jikin takardar asirin dana taɓa tonewa.”

Tana fadin hakan ta ɗago ta kalle shi, don haka idanunta suka nuna mata yadda yanayin fuskarsa ya shiga canjawa zuwa mamaki cikakke, sannan ya matsa da fuskarsa baya yana kallonta kamar a lokacin ya fara ganinta.

“Asiri? Wane irin asiri?”

Ta girgiza kanta, hakan ya motsa hannayensa.

“Ban sani ba, na san dai Fulani ce tasa akayi kuma wadanda suka binne sunce wai zai sa baza ka dawo Lagos ba a lokacin sannan ɗayan kuma zai sa kayi duk abinda Fulanin tace ba zaka yi mata musu ba, amma duka na tone su, na farko laya ce da takarda na biyu kuma wani abu ne mai jini sai muka ƙona shi dani da Sadiya.”

“Tun yaushe wannan ya faru kuma me yasa baki taɓa gaya min ba?” Muryarsa ta fito fayau! Don saboda tsananin mamaki ba zaka iya tsinto komai a ciki ba.”

“Tun kafin in sanka ne, kuma ban san yaushe ya dace in faɗa maka ba, kuma ma naga al’amarin ya riga ya wuce ne.”

Wani abu ya ratsa tun daga kan Madaki har tafin ƙafarsa, ba wai zancen asirin ba don wannan kwanannen zance ne ya san cewa tun daga lokacin da Mai martaba ya danƙa masa dukiyarsa a tsaye take akansa, kuma addu’oin da yake dagewa dasu su suke sawa Allah ya ke kare shi daga sharrinta, don haka abin mamakin shine yadda Jidda ta kasance ɗaya daga cikin kariyar tasa, wace irin zuciya ce da ita ne wai? Tun bata sanshi ba take sa kanta a cikin hatsari don kare shi? Allah ya riga ya haɗa rayuwarsa da tata amma har ya bari da farko zuciyarsa ke zarginta kan wani abu daban, kan wani abu da baya son tunawa ma.

Sai kawai yasa hannu ya sake ɗago da fuskarta a hankali sannan ya dawo da fuskarsa ya kara goshinsa a saman nata.

“I love you so much Jay, ina so ki sani cewa kece abu mafi muhimmanci bayan mahaifina daya taba shigowa rayuwata kuma kece fatan dana daɗe ina rokon Allah ya bani, ba zan taba cutar dake ba Maijidda, zan riƙe ki amana kuma ina fatan Allah ya bani damar ninka miki fiye da farin cikin da kika kawo min a rayuwata…”

Kuma bai jira komai ba ya haɗe leɓɓensa da nata a hankali cikin wani irin salo nasa shi kaɗai, wani irin salo da yasa Jidda ta sake damƙe hannayenta akan nasa sannan tafin ƙafarta ya ɗaga sama don tana ji ne kamar wani abu ne ke janta zuwa can sama, kamar zai yi fiffike ne ya tashi da ita zuwa wata duniya tasu su biyu kawai.

A hankali ya ɗan ja daga jikinta amma ba tare da ya raba fuskarsa da tata ba sannan muryarsa ta fitowa a hankali yana kallon idanunta dake rufe.

“Kin yarda dani Jay? Kin yarda da duk abinda na faɗa?.”

Idanunta a rufe suke, gashinsu a sauke ba mai tsawo ko laushi ba amma a cike yake taf cikin layi mai kyau, sai ta ɗaga kanta a haka ba tare data bude idon ba, kuma bata daina ɗaga kan ba har bayan ta san ya fahimce ta ɗin, so take ya ƙara sani shima cewa a shirye take ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwar tasa, ya san cewa zata zauna tare dashi a kowanne yanayi na farin ciki ko baƙin ciki, zata shiga har cikin zuciyarsa ta fahimci kowanne faɗuwa da tashin dake jikinta, ta san duk wani ciwonsa ta yadda zata zama haske a duk wani waje da yake da duhu a cikinta.

Madaki ya ƙara kissing ɗinta a hankali kuma wannan karon yafi kowanne tasiri don har sai da jikinta yayi rawa a cikin hannunsa sannan numfashinta ya shiga kakkatsewa, sai ya zame hannunsa ɗaya daga fuskarta ya riƙo ta sosai a cikin jikinsa yana ƙara gaya mata wani saƙo da bai taɓa gayawa kowacce mace a duniya bayan ita ba, wani saƙo da yayi kaca-kaca da duk wani ragowar lissafi da tunani Jidda, don haka bata san sanda ta maida hannayenta biyu ta riƙo wuyansa ba itama, manyan yatsunta biyu sirara suka sauka a gefen Adam’s apple ɗinsa daga kowanne gefe tana jin motsawarsu yayin da bakinsa ke motsawa, kuma hannunta a wajen shine wani abu da ya ƙara susuta dukkan wani sanity na Ibrahim Ahmad Madaki!2

Iska ta tuge labulen da Jidda ta ɗage daga can jikin windo a lokacin, don haka hasken da yake shigowa ta waje ya disashe, duhun ɗakin ya baiyana, wani irin duhu mai lumshi.2

Kuma a cikin wannan duhun ne, tushen wata sabuwar rayuwa ya wanzu.”Nadiya…”

Muryar Abdallah ta kira ta cikin wayar dake kare a kunnen Nadiyan, a lokacin tana zaune ne akan bedside drawer ɗakin Safina bayan ta baro ɗakin mahaifiyarta, Fulani.+

“…Yaushe zan zo in ɗauke ku?” Ya tambaya.

Wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarta ba shiri.

“Au ka fasa turo securityn su tafi damu? Ko ka manta ne kira na ƙarshe da kayi abinda kace kenan?”

“Lokacin raina a hasale yake, for god’s sake ta yaya zaki tsallake kasar nan har ki tafi U.S ban sani ba? Munzo kusan mu bakwai da freinds ɗina yi muku gaisuwa amma akace min wai ba kya nan, and I tried your line God knows how many times ban same ki ba, so yaya kike so reaction ɗina ya zama a lokacin dana same ki?”

Nadiya ta cije leɓɓenta, gaya mata yake yi yazo gaisuwar mahaifinta da iya abokansa su bakwai kawai, babu ƴanuwansa ko ɗaya balle kuma uwa-uba iyayensa, kuma har dan bai same ta ba zai iya buɗe baki yayi ƙorafi bayan sai da akayi arba’in ɗin mutuwar sannan suka bar ƙasar, kuma bayan ɗan guntun text ɗin sa da ta gani a cikin wayarta bai ƙara waiwayar tata sai bayan arba’in ɗin, a idonta ta hango ƴanuwan mijin Aisha yadda suka dinga sauka mota-mota har sai da aka share makoki, shi kansa mijin nata kwanansa biyu a garin.

Ta sani cewa yin ƙorafinta a wannan lokacin bashi da wani amfani, don ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba yayi abubuwa makamancin waɗannan ɗin kuma maganarta bata canja komai ba, balle a yanzu da take jin zuciyarta na tsoron sake jangwalo wani abun da zai sa abubuwa suka ƙara ɓaci a tsakaninsu.3

A yanzu ta fara gajiya da wannan zaman da take yi, wata biyu an share makoki kowa ya tafi ya barta, Aisha ta koma gidanta tuni sannan Safina kuma ta koma makaranta, an gama dukkan wata hatsaniyar sarauta kuma duk yadda aka kai ruwa rana, duk wata fafutuka da Saifudeen ƙannen Mai martaba suka yi, sarauta ta kuɓuce daga gidansu.

Saifudeen bai samu sarautar ba, cin hanci da siyasa sunyi kaka-gida sunyi baƙe-bake ta kowanne ɓangaren masu zaɓen Sarkin, anyi amfani da karfin naira da kuma na siyasa an danƙa sarautar garin Kiyari ga zuri’ar gidan Auwalu Rumfa, babban jikan gidan mai suna Yakubu shi ya maye wajen zaman mai martaba, wani mutum mai ƙarancin addini da kuma son zuciya, don haka alhini ya ƙaru a zuciyoyin mutane ta yadda har bayan an share makokin arba’in jama’a basu bar jimami ba.

Kuma bayan an share makokin ne Saifudeen ya haɗa ta da wani cousin ɗinsu da yake waba wajenta mai suna Ashraf suka je har U.S kai Fulani asibiti, kuma har sun dawo anyi mata aikin gashi ta fara jin sauki ma don tun kafin su taho tana fahimtar dukkan wani abu da ake gaya mata har ma ta kanyi tambaya kan wasu abubuwa da suka faru a baya duk da maganarta bata fita sosai.

Satinsu uku acan yanzu kuma satinsu ɗaya da dawowa, amma har ta fara gajiya don duk da akwai mahidimta a ɓangaren ammad ba abinda take yi tunda suka dawo ɗin sai kula da Fulanin, don har yanzu ko hannunta bata iya ɗagawa, matsalar da aka magance a U.S ta ƙwaƙwalwarta ce kadai amma shanyewar jikinta na nan ba abinda ya canja duk kuwa da gashin ƙashin da ake mata safe da yamma.

Don haka a hankalinta san cewa wannan zaman ba shine mafi alkhairi a wajenta ba, sannan kuma ta lissafa taga cewa in har ta dage kan rabuwa da Abdallah a yanzu to ba ƙaramin kuskure zata yi ba don da kyar ne idan zata sake samun wani kamarsa saboda dame zata yi taƙama a yanzu? Uban da ya mutu? Sarautar da ba tasu ba? Ko Uwar da baza ta taba iya tsaya mata a komai na harkar rayuwa ba? Dama bayan muƙamin mahaifinsu, da Fulani suke takama wajen cewa itace ƙafarsu a ga duk wasu duk manya-manyan mutane na ƙasar nan, amma a yanzu da ita da babu banbanci kadan ne fon haka dame zata bugi ƙirji tace zata samu miji wanda yafi Abdallah? Yaro, kuma mai kuɗi da tashe irinsa? idan tayi sa’a wataƙila sai dai irin manyan alhazawan nan da suka tara ɗan kuɗinsu ta shiga a ta uku koma ta huɗu.

STORY CONTINUES BELOW

Wata rayuwa da bata jin zata taba iyawa, don ta sani cewa duk ɓacin ran da take fuskanta daga gurin Abdallah ko mahaifiyarsa, idan ta tuno kammaninsa da kuma dukiyarsa zuciyarta kan ɗan sarara da wani abun, aƙalla ko ba komai ta san zata ci mai kyau tasha ta kwanta a waje mai kyau. Shi yasa take ta lallashin zuciyarta da wata ƙarya mai ma’ana, ƙaryar xmr cewata da cewar ko ba komai yana sonta ko don ƴar data haifa masa.

Kuma ta yarda cewa wannan itace irin tata ƙaddarar rayuwar, tata jarabawar… dama ance sunan ƙaddadar guda ɗaya ne, sai dai siffofinta mabanbanta wanda ya danganta da rayuwar kowanne bawa.

Ita ga irin tata nan, don tun daga tasowarta a duniya, ta samu dukkan wani farin ciki da jin daɗi, bata taba neman komai ta rasa ba, sai a yanzu da ƙaddarar tata ta faɗa kan wani abu da yafi ƙarfin ikonta, rashin kulawar miji da kuma rashin soyayyar ƴanuwansa.

“Baka gaya min ba, Mama ta yarda mu dawo ɗin ne?”

Taji alamun ya gyara kwanciyarsa daga cikin wayar sannan yace.

“Dama ranta ya ɓaci ne a ranar but komai ya wuce, har tace in miki gaisuwa ma.”

Sai ta haɗiye yawu a hankali tana jin wani ɓangare na zuciyarta na matsewa, ba zai taɓa ganin laifin mahaifiyarsa ba ta sani, amma ko mai rangwamen hankalin zai san wannan abinda ya faɗa bai dace ba, ta yaya za’ayi mata gaisuwar mahaifi ta wannan sigar? Sigar da sai itace ta tambaya ma.

“So, inzo ɗin ne ko in turo a ɗauke ku?”

A yanzu wannan abinda ya matse a zuciyarta ya wargaje don bata san me ya dace tace ba kuma, tunda al’amarin nan ya faru bai ko taba tambayar ya halin mahaifiyarta yake ba, sannan lokacin da yazo gaisuwar sun tafi kaita asibiti ko ita bai gani ba balle Fulanin, amma har yake tambayarta wai yazo? ita tata uwar ba komai bace a wajensa kenan tasa ce kawai mutum… Babu yadda zata yi sai kawai ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsunta dake motsi akan rantsatstsen material ɗin dake jikinta, ƙwalla ta taru a idonta kafin tace.

“Duk wanda kaga yafi dacewa Abdallah.”

“Shikenan idan na sami dama cikin satin nan zan shigo, in kuma abubuwa sun riƙe ni zan turo driver kawai ya taho daku.”

Ance wai mai hankali ake gayawa magana har ya fahimci saƙon cikinta, don haka bata yi wani mamaki ba dashi bai fahimci shaguɓen cikin maganarta ba.

“Kince tayi bacci ko?”

Ta san wa yake nufi, ƴarsa. Don ita kaɗaice halittar da take jin zai nema a rayuwarsa bayan mahaifiyarsa, itama kanta ta san albarkacinta take ci, don haka sai ta gyada kanta kamar yana ganinta kafin ta amsa.

“Eh taci abinci ne sai tayi bacci.”

Bakinta ya furta ƙaryar da bata yi wani hasashe a cikinta ba don bata ga dalilin da zai sa ta farantawa mutumin da bai damu da nata farin cikin ba.

“You’re sure kuma ba wani abu da ya same ta?”

“Lafiyarta ƙalau.”

“Okay, to sai kin ji ni kenan.”

“Insha Allah.”

Tana faɗin hakan ya kashe wayarsa ɗib, kuma ta san ita da ta sake jinsa wataƙila sai ranar da zai turo a ɗauke sun… Don ko zata kira shi ma in ya ɗauka yau ba lallai ya ƙara ɗauka gobe ba, don kamar sauran maza irinsa ya riga yasa a zuciyarsa cewa duk abinda zata yi masa don dukiyarsa ne kawai ba wai don wata kyautatawa ta daban ba.

Wayarta ta sake ƙara kafin ta tashi daga wajen, A’isha ce, ta ɗauka sannan ta kara a kunnenta.

“Yaya jikin Mama?”

A’ishan ta tambaya bayan sun gaisa.

“Da sauki, don har ta tambaye ki ma shekaranjiya.”

“Maganar tata ta fara fitowa sosai?”

STORY CONTINUES BELOW

“A’a, kamar da dai, amma ana ganewa.”

“Allah ya ƙara sauki, dama kira nayi inji har yanzu Abdallahn bai kira ki ba?”

Nadiya ta cije leɓɓenta daga gefe tana danne wani abu dake shirin tasowa a cikin ranta kafin ta faɗa mata wayar da suka gama yi yanzu dashi, sai dai ta canja kusan rabi na zancen ta kuma ɓoye abubuwa da yawa, amma duk da haka dai labarin ba mai gamsarwa bane.

“Allah ya sawwake Adda, nima ina ganin gwara ki koma ɗin, ko ba komai watarana zaki ci ribar haƙurinki.”

Nadiya ta gyada kanta.

“Insha Allah Ishsh, Allah zai dube mu, insha Allah. Kinyi magana da Muhammad ɗin?”

Kamar tana ganinta, Aisha ta girgiza kanta daga can ɓangaren.

“Har yanzu bai neme ni ba Addah, na gaya miki tunda na dawo baya ko bi ta kaina, yau kwana biyu kenan ma ban ganshi ba, kafin ya dawo nayi bacci, in dai zai fita kuwa yawanci har na gama shiryawa na shiga Cikin Gida, don haka bama haduwa kuma wallahi ni yafi min ma, don ko daga nesa na hango shi gabana sai ya faɗi.”

“Kar ki damu komai mai wucewa ne, atleast ƴanuwansa na sonki don haka ki karɓi wannan ni’imar ma ki godewa Allah, wannan itace ƙaddarar rayuwarmu Ishsh, amma nayi imani watarana ni dake ɗin duk zamu ci ribar ko haƙurinmu insha Allah.”

“Insha Allah.” Aishan ta amsa kuma da haka suka yi sallama kowanne zuciyarsa a ƙulle.

Nadiya ta miƙe ta fita zuwa falo na farko daga nan cikin ɗakin, wani haɗaɗɗen falon Fulanin mai ɗauke da komai kalar maroon da gold, anan kan kujerar ta tadda Hidaya tayi barci da ƴar ledar chocolte ɗinta a hannu, ashe dai ba karya ta yiwa Abdallah ba, sai ta ƙarasa ta kashe makeken screen din plasma dake nuna tashar cartoon sannan ta dawo da ɗauke ta, ta kaita ɗakin Safina inda suke kwana yanzu ta canja mata kaya zuwa na barci sannan ta dauko wiper ta goge mata gefen bakinta da ya ɓaci da alawar, ta lulluɓe ta ta kashe fitilar ɗakin sannan ta fito.

Ta wuce duka sauran falukan da a yanzu suka zama tamkar kango saboda rashin mai zama a cikinsu har zuwa wani d’an karamin falo dake manne da turakar mahaifiyarta.

Hafsat Muhammad Gani (Fulani).

Dattijuwar mace ce da kallo ɗaya zaka yi mata daga nesa zuciyarka ta motsa saboda tausayin halin da take ciki, musamman in zaka ganta a lokacin da likitoci suka taru akanta ana aikin yi mata gashin ƙashi ta koina, sai zuciyarka ta matse har ka tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa.

Tana kwance ne amma idanunta a tsaye suke ta kafe su tana kallon ɗanta Saifudeen wanda ke zaune a gabanta da labarin cewa zasu bar masarautar nan da sati guda su koma gidan mai Martaba na cikin GRA wanda yake sa rai cewa idan anzo raba gado zai faɗo wajensu.

A halin da ake ciki dukkan wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a ƙirjinta, tana jin ƙirjin nata ne fayau kamar Allah bai taɓa halittar komai a wajen ba don abubuwan da suka same ta da wanda ta gani da idanunta sunyi ƙarfin da zuciyarta ba zata iya ɗauka ba balle har ta iya fassara su a ranta, tun daga lokacin da hankalinta ya dawo har ta fahimci rasuwar mai martaba bayan ta Farouk ɗin da hankalinta ya gushe a cikinta, shikenan komai na cikin zuciyar tata ya mutu, ta zama bata da wani emotion ko na misƙala-zarratin, hatta shi kansa ɓakin cikin sai ta fahimci cewa wata rahama ce ta ubangiji ga bawa ya fuskance shi.

Tun bayan lokacin data fara fahimtar abubuwa a wannan asibitin na U.S da aka kaita, ta matsu da tambayar dukkan abinda ya faru don wanda zata iya tunawa kaɗan ne kafin gushewar hankalinta.

Ta san dama ance mata ta rasa aminiyarta jakadiya Babbba, ance mata ta mutu, ta tafi da duk wani buri da ta shafe rayuwarta tana gina shi, sannan akace mata ta rasa ɗanta kuma, ɗan da rabi na cikar burinta ya ta’allaƙa akansa… Bayan farkawarta kuma sai aka tabbatar mata da cewar ta rasa Mai martaba shima, ta rasa miji kuma uban ƴaƴanta, ta rasa wani ginshiƙi na rayuwarta, akace mata yau duniyar da take ciki babu Ahmad, babu wannan Ahmadun data so fiye da komai a rayuwarta kafin ruɗin shaidan yaci galaba akanta.13

STORY CONTINUES BELOW

Don haka halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abun awo a duniyar nan da za’a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi. Taci burika da yawa a rayuwarta, tun daga zamanin ƙuruciyarta, lokacin da Allah ya ƙaddara aurenta da mai martaba, tun daga wannan lokacin shaiɗan ya fara rinjayar zuciyarta na cewar tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta tarawa ƴaƴan da zata haifa tarin dukiya da kuma damar mulki ta yadda har bayan ɗaruruwan shekaru sunanta da nasu ba zai goge a tarihi ba, a ganinta wannan shine ribar zuwa duniyar ba ka tafi a manta da kai ba.

Kuma mahaifiyarta ita ta fara ɗora ta kan turbar bin malamai tun tana sane da cewa hakan ba daidai bane har tazo ta manta dukkan wani fatanta ya ta’allaƙa a gare su, musamman da Madaki ya zama ƙalubale a cikin rayuwarta. Hakan yasa ta ture komai gefe hatta tarbiyyar ƴaƴanta da kuma soyayyar da take wa mijinta, ya zama fufutukar bin bokaye shine abu mafi muhimmanci a wajenta.

Wata fafutuka da ko ta sami nasara akan wani abun sai wata matsalar da ta fi shi kuma ta ɓullo don haka sai ta zama kamar mai hakan rijiya….. Tana girma tana ƙara mu’amalantar mutanen dake yin abinda yafi nata wanda hakan yasa zuciyarta ta ƙara ƙeƙashewa kuma bata taɓa hango rashin dacewar abinda take yi ba balle har ta fahimci talalar da rayuwa ke mata. Sai da komai yazo ƙarshe tukunna sannan a yanzu ta afka cikin ramin nadama wanda ta kira da mara amfani.

Kuma mafi ciwon abun shine rashin lafiyarta a yanzu, ta kan kasa yarda a duk lokacin da ta kalla taga cewar wai yau mace kamar ita, FULANI! itace kwance jiki a shanye maganarta bata ko fita kuma babu wani abu da zai tayar da ita sai Allah, ubangijin dai data juyawa baya tun farko. Duk waɗannan tarin kuɗin data ƙallafa rai akansu da bokayen da ta shafe rayuwarta tana bautawa basu da ƙarfin ikon yi mata komai a yanzu, hatta tarin ƙawayenta manyan mata irinta da take taƙama dasu, Nadiya ta shaida mata ba kowa ne ma yazo dubata ba balle har ayi mata ta’aziyyar ɗa da kuma mijin data rasa.

Sannan mafi rincabewar al’amarin a yanzu gidan sarautar ma yafi ƙarfinsu, duk tsawon shekarun data ɗauka tana zuba mulki a cikinsa a yau ya koma tamkar ba’ayi ba, lokaci ya wuce da damar da ta shagaltar a banza kuma babu mai ikon canja komai, dole ne su fita su bawa masu zamani waje suma su taka tasu rawar.

Madakin dai da ta shafe rayuwarta tana ƙoƙarin ganin bayansa a yanzu shi kaɗai ne ya sami dukkan wani alkhairi don ko ba’a gaya mata ba ta san cewa wannan auren nasa da ta zama sanadiyyarsa ya gyara rayuwarsa ta ɓangare da za’a iya cewa bayan rasuwar Mai martaba a yanzu, shi bashi da wani aibu a tasa rayuwar, don ta ganshi kafin ya tafi, yazo ya dubata duk da a lokacin bata cikin haiyacinta sosai.

Kuma Saifudeen ya shaida mata cewar shi ya samo asibitin da aka kaita a U.S har ta sami rangwamen sauƙi a yanzu, sai dai duk da haka zuciyarta bata ganin farinsa har yanzu, zuciyarta ta riga ta gama mannewa da tsanarsa tun asali don haka ba abinda zai taɓa canjawa duk da irin nadamar da take ciki a yanzu. Don a tunaninta ma ba don shi ba, ba lallai ta dore wajen bin bokaye ba har ta sami wannan nakasar, sannan dukiyar da yake amfani da ita a yanzu wajen kula da ita ai ba tasa bace ta mijinta ce kuma uban ƴaƴanta, don haka babu wani abin birgewa da yayi a wajenta.

Tana jin ma da Allah zai iya ƙaddarawa ta miƙe, zata iya cigaba da neman kassara Madaki ta wata hanya daban bata bin bokayen da a yanzu taga cewa bata ɓullewa ba…3

(Allah ya kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba don shi ɗin zanen dutse ne.)7

***

08:19AM

Lagos.

Gidan Mubarak.

“Mubarak? King?… Sarki?”

Muryar Khadija ta kira duka sunaye ukun a lokacin sa ta durƙusa a gaban Mubarak tana kallon fuskarsa, idanunsa ba ita suke kallo ba, hange yake ta saman kafaɗarta cikin zurfin tunanin da a kwana biyu yake yini yana tashi dashi.

STORY CONTINUES BELOW

“Ya akayi wai?”

Muryarsa ta tambaya ba tare da ya kalle ta ba.

Sai ta miƙo hannunta ta tallafo fuskarsa ko ta wane ɓangare.

“Ka kalle ni mana…”

Ba musu ya dawo da idon nasa ya kalle ta.

“Bani da lafiya naje asibiti.” Ta faɗa kai tsaye don ta san in ta tsaya jan zancen tsaf zai iya tashi ya tafi wani abun.

“Really?… Ya akayi ban sani ba?”

“Ɗazu da safe da naje kai su Aliyu makaranta na tsaya asibitin nan na gefen makarantarsu.”

Sai ya gyaɗa kansa alamun yana saurarenta.

“So, anyi min test ance wai…”

“Wai me?”

A lokaci guda yanayin fuskarta ya canja zuwa tsantsar farin ciki, ta sake sirranta muryarta sannan cikin ɗan ihu tace.

“We’re going to have a baby!”3

(Zamu samu ƙarin baby!)

“Da gaske kike Yaarym? Da gaske?”

Shima ya tambaya murmushi na haskawa har a idanunsa.

“Wallahi, sunce wai 5 weeks.”

Sai ya riko hannayenta duka biyun ya ratsa yatsunsa a tsakani.

“Ya Allah! I’m so happy, wallahi nayi farin ciki sosai, shekara nawa kenan? Shekarar Hanan nawa?”

“Shida.” Ta faɗa da dukkan farin cikinta itama.

Sai ya rufe idanunsa ya buɗe sannan a hankali ya furta kalmar.

“Alhamdlilah.”

Daidai lokacin kuwa da wayarsa dake gefen gadon ta shiga ƙara, ba shiri ya saki hannayenta ya ɗauki wayar kuma sunan da ya gani a jiki yasa wani bari na zuciyarsa lafawa. Sai dai kafin ya ɗaga ya juyo ya kalli Khadijan yace.

“Ina Salwa?”

Mamaki ya ɗan kama Khadijan, me yasa zai tambaye ta? Bayan ya san cewa fiye da wata guda tun bayan da ya dawo da ita daga gidan kangararrun da yasa aka tsare ta zamanta baya wuce cikin ɗakinta sai kuma ɗan ƙaramin falon su Hanan da Tvn ciki ba abinda take nunawa illa tashoshin Cartoon. Amma sanin yadda halinsa yake a cikin ƴan kwanakin nan yasa ta ture mamakin tace.

“Tana ɗaki.”

“Kice ta saka hijabinta ta fito main falo yanzu zata yi baƙo.”

Ba shiri mamakin kan fuskar tata ya dawo har ma yafi na da kafin tace.

“Bako? Salwan? Daga ina?”

“Zan miki bayani anjima, for now just let her know.”

(Zan miki bayani anjima, a yanzu ki sanar da ita tukunna.)

Kuma da haka ya nemi hanyar ƙofa ya fice, takunsa akan tiles ɗin mai ƙarfi kamar yadda zuciyarsa take da ƙarfi da kuma yaƙini akan abinda yake shirin aiwatarwa. Ya wuce main falon nasu ya bude ƙofar waje ya fita,a compound ɗin wata mota ce ke haska kyallinta cikin hasken fitilun wajen.

Kuma ya ƙarasa sai ƙodar mazaunin direba ta buɗe kuma tar idanunsa suka hasko masa wanda ya fito daga ciki.

Habibu.

“Ranka ya dade Barka da fitowa, ai nazo tun ɗazu ina ta gwada wayarka network yaƙi signaling, sai yanzu na samu.”

“Ba komai, ka ƙarasa duba takardun LAT?”

“Eh, and I came across some errors, amma na kusa ƙarasa su ma Insha Allah.”

Sai Mubarak ɗin ya gyada kansa.

STORY CONTINUES BELOW

“Dont rush, ai muna da isashshen lokaci.”

“Insha Allah.” Cewar Habibun yana ɗan sunkuyar da kansa kamar mara gaskiya.

“Mu ƙarasa ciki, yanzu zata fito.”

Saura kaɗan Habibu ya sake buɗe bakinsa ya tambaya cewa wai da gaske Mubarak ɗin yake har yanzu babu wasu sharaɗai da zai gindaya masa a wannan al’amarin? Don tunda ya same shi sati biyu da suka wuce da zancen daya faranta ransa kuma ya bashi mamaki har yanzu bai bar tunanin cewa zai kafa masa wasu sharaɗai akan al’amarin ba.

Cewa yayi wai yana neman alfarmar daya auri ƙanwarsa, zai bashi gida sannan zai sa hannu Madaki ya kara masa muƙami a kamfaninsu. Kuma bayan hakan babu wani sharaɗin abinda zai yi kawai abinda yake so shine ya auri kanwar tasa, sai dai ya gaya masa komai game da ita, rashin jinta har ma da irin mutanen data mu’amalanta kafin ta dawo wajensa, kuma shi wannan ba matsalarsa bace don duk ƴanmatansa ma irin halayyarsu kenan, kuma in dai yana tare dasu to cikin sassauƙan mataki yake raba su da kowa ya zama in bashi ɗin ba babu maganar wanda suka isa su saurara.

Don haka kamar an kawo kuka gidan mutuwa ne, komai taurin kan wannan Salwar ya san cewa ya buga da wanda suka fita kuma ba zai canja tsarinsa ba akanta, in ma mutuwa zata yi shi ba ruwansa indai har ya riga ya sami gida da ƙarin muƙaminsa, ba dai neman kai ake da ita ba? To tabbas kuwa an kawo ta daidai wajen daya dace. Yasa hannu ya danne button ɗin wayarsa dake vibrating alamun shigowar kiran Lulu, ya kaɗa kansa sannan yayi murmushi a fili kafin yabi bayan Mubarak da yayi gaba, ya riga ya gama da wata Lulu kuma a yanzu filin na Salwa ne kafin yaci moriyar ganga…2

Salwa ta kalli cikin idanun Khadija a lokacin da take faɗa mata saƙon Mubarak, kuma bata yi mamaki ko kaɗan ba balle har ya kai na Khadijan da take gani a fuskarta, dama ai ta riga ta sani ta san cewa dole akwai abinda Mubarak ke shirya mata shi yasa itama ta biye masa suka yi wannan wasan tare, don ta riga ta tsara cewa zata nuna masa cewa da gaske tayi nadama irin nadamar da yake son gani a tattare da ita, Allah barshi duk ranar da zuciyarsa ta bashi tabbaci ko yaya ne game da ita, sai ta samu ƴancin da zata ɓalle zuwa inda zata kafa sabuwar duniyarta.7

Don a yanzu zuciyarta ta riga ta gama haƙura da Madaki, ba don ta daina sonsa ba sai don ta san in har ta dage sai shi ɗin, to zata yi biyu babu ne, babu shi ɗin kuma rayuwarta ba zata taɓa tafiya a yadda take so ba.

Wataƙila kuma ta taka rawar tata da kyau, tunda gashi har ya yanke shawarar yi mata aure a tunaninsa cewa ta shiryu, don haka suje zuwa, ai auren ma shine hanya mafi sauƙi ga ƙudirinta da take son cimmawa, ta hanyarsa zata samarwa kanta ƴancin da in ta tafi baza su sake ganinta ba kuma har abada, don haka ko waye ya kawo zata yarda ta aure shin kafin taci moriyar ganga… ta yar da kaurenta!4

***

#Majid

Washegari, Lahadi.

08:10Am.3

“Kana nufin shima Habibun ya yarda zai aure ta?”

Madaki ya tambaya ta cikin wayar da yake yi a safiyar ranar lahadi, yayin da yake kishingiɗe kan kujerar tsakiya ta falonsa, falon da har yanzu ke bada sassanyan ƙamshin turaren da Jidda ta baɗe gidan dashi a jiya, don babu wanda ya sakta taje ta ƙona busashshen ɓawon lemon da ta dade tana tarawa wai maganin sauro ne, da koina a gidan ya baɗe da ƙauri kuwa ba shiri ta kunna turaren wuta ya bi ta kansa.

“Yes, nasa yazo gidan jiya sun gaisa kuma daga shi har ita kowa ya tabbatar min cewa ya zai zauna da ɗaya.”

Muryar Mubarak ta amsa ta cikin wayar.

“Habibu is like family to us, amma kai kanka Mubarak ka san halinsa da gyara, so I wish wani daban ka samo mata bashi ba ko don ƴaƴan da zata iya haifa dashi.”

“Mdee ka yarda dani, na riga na auna komai na san me nake yi, Habibu shine daidai da Salwa, idan har na samo mata akasinsa kamar na bata ƙofa ne da zata cigaba da halayenta don wallahi har yanzu bata yi nadama ba, ina ganin hakan ƙarara a idanunta, so kamar yadda hausawa suka ce ne ɗan birni shine maganin ƴan birni, na san idan har zan riƙe Habibu da wasu alƙawuran to ba zai taɓa bata wata ƙofar da zata yi wani abu ba. Beleive me.”

STORY CONTINUES BELOW

Madaki ya gyada kansa kafin a hankali yace.

“Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma please kar ka cigaba da takurawa yarinyar nan Mubarak, atleast ka san mata da biki, ka barta tayi abinda take so in har zancen auren ya tabbata.”

Mubarak bai amsa ba don ba zai amsa abinda ba zai iya ba, ya riga ya tsara komai a cikin kansa cewar daya sanyo magabata a cikin maganar, a rana ɗaya za’a ɗaura auren ba wani taro, ko mutum shida ne sun isa wakilci, kuma duk tarin ƴanuwansu wasu gwaggoninsu guda biyu kawai zai sa su kaita gidanta a ranar, babu wani taro balle ma a saka ran dafa ko ƙwayar shinkafa da sunan murna.

Saboda haka sai kawai ya juya akalar zancen nasu ga fafutukar da suke ciki a yanzu na ƙoƙarin ware dukkan wata riba da kamfanin Royal K ya samu daga lokacin da aka fara tara ribar zuwa yanzu saboda harkar rabon gadon Mai martaba da za’a fara wani watan.

Babu yadda Mubarak baiyi ba da farko akan cewa su haɗa kudi su biyu koda kuwa sai sun hada da wani ne su siya kamfanin ya koma nasu gabaɗaya amma fafur Madakin yaƙi, sai da ya matsa ne sannan ya fit masa wata tsohuwar takardar wani agreement da Mai martaban ya taɓa rubutuwa cewa ko bayan ransa bai yarda a haɗa kamfanin cikin gadonsa ba ko kuma a saida shi ga wani saboda kudi, ya rubuta cewa ko naira biyar kaɗai ake samu daga cikinsa yana son wannan kuɗin ya zama abu guda ɗaya da zai cigaba da haɗa kan ƴaƴansa ya zama akwai dai wani abu da ya haɗa su ba kowa an bashi gadonsa ba ya kama gabansa.

Don haka wannan takardar da sa hannun Sarkin da komai ita zai gabatar ga masu rabon gadon in an tashi sai kuma zunzurutun kudin ribar kamfanin da aka tara don a fara raba musu kafin zagayowar kowacce shekara kuma ya dinga kawowa akai-akai. Kuma yayi alkawarin cigaba da aiki a kamfanin iya tsawon ransa in har ba Saifudeen da yake babba a yanzu ne yayi niyyar canja shi ba. Don ya yarda cewa babu wani aiki da zaiyi a duniya wanda yafi ya cigaba da raya kamfanin mahaifinsa kamar yadda ya ɗora shi akai tun farko, kuma ya yarda cewa babu wani kuɗi da zai samu wanda zasu fi albashinsa daga wannan kamfanin albarka, don iya albashin da yake samu ya san zai ishe shi tsawon rayuwar da zai shafe tare da Jidda har ma da ƴaƴan da zasu haifa nan gaba.

Kuma a haka wayar tasu da Mubarak ta ƙare, dama ya kira shi ne kan wani code da yake son ya karɓa na kayansu da suka iso daga tashar shige da ficen jirgin ruwa ta ikkon.

Madaki ya bar wayarsa anan falo sannan ya koma daki, ƙafafunsa na taka tiles ɗin ɗakin a hankali don kar ya tashi Jidda dake bacci duƙunƙune cikin bargon gadonsa, dama kiran wayar Mubarak ɗin ne ya fito dashi falo don kar ya tashe ta. Sai dai yana shiga cikin bargon kuwa ta buɗe idanunta.

“Ƙarfe nawa?” Muryarta ta tambaya a lokaci guda

Ya san tunani take cikin sati ne, kar lokaci ya ƙure mata bata tashi ta haɗa masa breakfast ba don haka maimakon ya amsa mata sai kawai yasa duka hannayensa ya janyo ta jikinsa a hankali sannan yace.

“Bamu tashi ba, go back to your sleep.” (Ki koma baccinki).

“Ka gaya min time ɗin tukunna.” Muryarta ta sake fitowa a hankali daga jikinsa, sai ya sunkuyo da fuskarsa daidai saman kanta yadda zata fi jinsa yace.

“Ƙarfe Lahadi, daidai lokacin da ya kamata ace kina jikina, so dan Allah kar ki tashi kin san gobe i-yanzu ba zan sami wannan damar ba.”

Jidda bata gama wartsakewa ba amma duk da haka ta shiga jin sak irin abinda taji a lokacin da ya fara gaya mata cewa yana sonta a masaukinsa na Kiyari, kuma irin abinda take ji a duk lokacin da ya furta mata wata maganar da tayi wa zuciyarta daɗi, wai yaushe zata saba ne?

Sai ta ɗago da kanta ta kalle shi, muryarta a hankali can ƙasa ta sake cewa.

“Na san weekend ne, amma duk da haka zamu ci abinci ai ko?”

STORY CONTINUES BELOW

Ya girgiza kai yana kallonta kafin yasa hannunsa ya maida kanta ta kwanta.

“Ki koma baccinki Jay, idan mun fara jin yunwar zan tashe ki.”

Ta san abinda yasa ya damu da kar ta tashin, tunanin gajiyar da tayi yake na aikin data sha jiya wajen haɗawa Jamila wasu ƴan ƙananan jakunkunan data gano a kasuwa wanda zata rabawa ƙawayenta da biki, suna da kyau sosai amma basu da zip a jiki saboda haka da tayi tunanin zasu fi kyau da zip ɗin sai tasa ya bawa Baba Saminu ya siyo mata zips ɗin a kasuwa tare da gum ɗin da zata manna, kuma da yake suna da yawa sai ta ɗauki lokaci tana yi har sai da hannun nata ya ƙage.

Don haka bata sake cewa komai ba sai ta ƙara gyara kwanciyarta akan ƙirjin nasa yayin da yatsanta ɗaya ya shiga bi a hankali kan adon zaren jallabiyarsa, zuwa wani ɗan lokaci kuwa baccin ya sake ɗaukarta yayin da shi kuma ya jawo tab ɗinsa ya shiga dube-duben ayyukansa da ya saba.

Kuma ba ita ta sake farkawa sai wajen ƙarfe sha ɗaya saura na safen, a lokacin ita kaɗai ce a gadon sai sharar baccinta take ɗin haka ba shiri ta tashi ta fito falo inda daga nan ta tagar falon ta hango shi daga can compound yana ta faman fito da wasu takardu daga bayan motarsa yana ɗorasu a saman motar yayin da yake waya. Kayan jikin sa wannan sealed ɗinkin ne na maza, ta fahimci kusan duka kayansa haka suke kuma cikin kalolin da basu fi guda biyar ba, amma he looks perfect, style ɗin ya karɓe shi tare da yanayin jikinsa, baya buƙatar wani abu daban kuma don ya ƙara haiba da kwajininsa. A cikin ranta ta godewa Allah ta sake gode masa da baiwar da yayi mata, don a yanzu Madaki ya cike kowanne gurbi na zuciyarta ta yadda take ganin kome zaiyi mata ba zata taɓa tsanarsa ba.

A cikin wata biyu kawai ya haskaka rayuwarta da wata irin kyautatawa da kuma ƙaunar da bata taba hangowa kanta ba, tana jin kamar ko zai zo daga baya ya ƙwace komai nasa, zuciyarta baza ta taba manta wannan farin cikin ba da kuma irin feelings ɗin daya haddasa a ranta.

Kuma kamar yadda ya sake cika mata kitchen da kayan abinci haka kayan sawa ma a yanzu har ta kan manta ranar data sa wasu, kowanne cikin ra’ayinta don yawanci stores suke zuwa tare ta zaɓo wanda take so, me Baddo tace mata ne wai?… In ta karɓi ƙaddararta hannu biyu ita zata fi kowa amfana da hakan…

Har ta gama tsaiwarta a falon nan tana kallonsa bai juyo ba, waya kawai yake yi yana faman bankaɗa takardu, kuma ta san ba zai wuce harkar kamfani da kuma rabon gadon Mai martaba da yace mata ana shirin yi ba. Don haka ta juya ƙafafunta ta shiga harkokinta, tayi wanka sannan ta tafi Kitchen koƙarin hada musu breakfast tunda gidan babu shara.

Kuma sanda ta gama soya doya da sauce ɗin kwan da tayi shima a lokacin ya gama gama wayar ya shigo ciki, har yana ƙoƙarin kunna Tvn falon da ita bata taɓa damunta ba ko sanda take shan zamanta ita kaɗai balle a yanzu da tayi waya ma, don ita yanzu hankalinta gabaɗaya ya ta’allaƙa ne akan haɗaɗɗiyar wayar daya bata ba Tv ba.

Kuma wannan itace sabuwar rayuwar da suke shimfiɗawa a gidansu tsawon watanni biyu, akwai shaƙuwa da fahimtar juna sosai a tsakaninsu, a yanzu ya san duk wani tarihinta kuma itama ta san nasa don Jidda wata irin mutum ce open-minded, duk abinda ke ranta zata faɗe shi kai tsaye ne sai dai in har yayi nauyi sai ta san yadda zata sakaya shi cikin magana, yayin da Madakin yake mai tsananin kulawa da appreciation kan dukkan kulawarta gare shi, tunda wani abu ne da bai taɓa samu ba, bai ma san yaya yake ba don haka zuciyarsa cikin ɗokin hakan take da kuma ƙoƙarin gujewa duk wani abinda zai dame ta balle har a iya samun akasi.

Idan ranakun weekend ne ba inda yake fita sai masallaci ko kuma in har zasu fitan ma to zai ɗauke ta ne suje zagaya gari tare, saboda ko gidan Mubarak sau ɗaya ya taba kaita bayan ita da Khadijan sun dame shi da ƙorafi tunda ita dasu Hanan suna yawan zuwa wani lokacin daga makaranta ma zasu tsaya, kuma shima baya son zuwan nata ne saboda Salwa duk da cewar bama su haɗu ba sanda taje ɗin don bata fito daga ɗakinta bar ya dawo ya ɗauke ta, kuma ko shi da ya nemi ganinta ƙiri-ƙiri Mubarak ɗin kallonsa yayi yace ‘A’a’.

STORY CONTINUES BELOW

Idan ranakun aiki ne kuma ya kan shafe rabin aikinsa yana duba lokaci don jiran la’asar tayi ya koma gida, a yanzu ya yarda cewa cikar farin cikin kowanne namiji a duniyar nan shine bayan fafutukar neman halalinsa ya koma gida ya tarar da matarsa cikin kyakkyawan hali tayi kwalliya tana jiransa, a gefe daddaɗan abincin da hannunta ya tanada masa sannan a cikin idonta labarin kewarsa kala-kala. Watarana ma sai ya kasance har da ɗansu rike a hannunta, watakila ma biyu ko uku…

In yayi wannan tunanin sai yayi tsaki a ransa, yaga wautarsa a fili sanda Mubarak ke roƙonsa da cewar yayi aure tuna lokacin amma yaƙi… Sai dai da yayin fa? Zai samu Jidda ne?

***

November, 19.

“Sati ɗaya ko?”

Jidda ta tambaya a lokacin da ta tsugunna a gaban Madaki ta miƙo masa kunun farar shinkafar data yi tun safe ta ajiye a flask, yanayin garin irin na sanyi ne daya fara shigowa amma baiyi yawa can sosai ba, don haka sun saki labulayen gidan gabaɗaya harda na kuma koina an kunna fitulu, Tv na nuna tashar films ɗin holywood yayin da ake wani film mai taken ‘Little Women’, kuma in banda sassanyan ƙamshin Air freshner dana turaren wuta ba abinda ke tashi a iska sai ko na ƙamshin sababbin kujerun da suka sake a falon.

Madaki ya ɗago ya kalle ta daga kan screen ɗin MacBook ɗin dake gabansa inda a gefenta ya baza tarin takardunsa.

“Sati ɗaya a me?” Ya tambaya a hankali da ɗan guntun murmushi a gefen leɓɓensa yayin da idanunsa ke kallon kayan jikinta da taje ta sake bayan doguwar rigar atamfar da ta saka tun safe, wani wando ne fari da bai kai har karshen ƙafarta ba, sannan ƙasansa yayi beza ne gabadaya kamar an saka almakashi an yayyanka shi, rigar jikinta kuma lemon green ce mai hannun vest, tana da tsawo ta baya amma ta gaba bata ƙarasa ma cinyarta ba. Kanta babu ɗankwali don a yanzu ya riga saba mata da rashinsa, in dai yana gida da ta saka ma ƴan mintuna ne zai cire shi, sannan bata yin kitso ma, yafi son a koyaushe ya zura hannunsa ciki ya tsefe tsawonsa.

Ta gyara zamanta a gabansa sannan ta kai kofin nata kunun baki kafin tace.

“In munje Kiyari nake nufi zamu yi sati ɗaya? Kaga kaima zaka yi naka fafutukar rabon gadon nan.”

“Who told you? Ni ba abinda zanyi, zan basu takarda ne kawai su gani, kuma da sun yarda shikenan na gana komai, idan naje na gaishe da Hajja, kinga kenan ko washegari in kin gama sai mu ta taho.”

Ba shiri ta haɗiye ragowar kunun dake bakinta.

“Washegari? Haba mana, bikin Jamila ne fa, duk shirin dana daɗe ina yi?… Ko Baddo ai baza taji dadi ba kawai in kwana ɗaya in tafi, bayan ba’ayi komai da bikina ba.”

Tsakaninta da Allah ta fadi maganar ba tare da sanin tasirin da tayi a zuciyar Madaki ba, don kallonta yayi na ɗan wucewar sakanni biyu kafin ya ture labtop ɗin dake gabansa a hankali zuwa gefe sannan ya kamo hannunta ya jawo ta jikinsa sannan kamar koyaushe ya haɗa fuskokinsu waje ɗaya.

“Idan taro kike so Jay, ki bari duk ranar da Allah ya bamu baby, zan haɗa miki shi har sai kin ce min ya ishe ki…”

Yayi shiru yana kallon gashin idanunta dake kallon ƙasa kafin muryarsa ta sake fitowa. Yana son wannan ƴar kunyar tata ko kuma yadda take nuna masa cewa yana da effect akanta, don har yanzu ko taɓa ta yayi zai ji sanda zata ɗan zuki numfaahi ko kuma jikinta yayi rawa kaɗan.

“… Ko kuma mu haɗa kawai ma yanzu, sai mu samo reason ɗin da zamu gaya mutane in mun gaiyace su?”

Sai ta ɗago idonta ta kalle shi.

“Muce me?”

Ya ɗaga kafaɗunsa har tata fuskar ta motsa.

“Ko muce musu bamu yi komai da aurenmu ba, ko shaddar ɗaurin aure ban saka ba sannan kema ko ɗan gwaggwaron nan ba’a ɗaura miki ba.”1

STORY CONTINUES BELOW

Ba shiri murmushi ya suɓuce a leɓɓenta, murmushi kamar dariya ma kafin tace.

“Cewa zasu yi bamu da hankali…”4

Madaki bai san sanda yayi murmushin ba shima kafin yace.

“I dont care Jay, in dai zai sa ki daina tunanin wani abu game da aurenmu wallahi zan iya yi.”

Sai ta girgiza kanta.

“Bana tunanin komai, ban taba tunani komai ba Allah, na faɗa ne kawai don ka barni in kwana da yawa.”

Sai ya sake yin murmushi yana riƙo hannunta dake zagaye da kofin kunun sannan yace.

“Kar ki damu zaki kwana iya son ranki, saboda dama ni da Saifudeen zamu kai Fulani Kaduna wajen wani mai magani, so asha biki lafiya.”

A take Jidda ta dawo da murmushin kan fuskarta harma yafi na da sannan tace.

“Inshallah. Allah ya kaiku lafiya, Allah ya dawo daku lafiya, nagode sosai.”

“Ameen.”

Ya furta a hankali sannan ya riƙo fuskarta da hannunsa ɗaya.

“Sai dai nafi son ɗayan Jay, wannan addu’ar ina samunta daga dubunnan mutane, shi kuma ɗayan naki ne ke kadai.”

Ta san me yake nufi, don haka ta rufe idanunta da sauri yayin da wannan abin data saba dashi ya shiga ratsawa cikin jijiyoyinta kafin muryarta ta fito tar daga maƙogwaronta.

“I love you.”

“Say it again..” (Ki sake faɗa.)

“I love you.”

“Again…” (Ki ƙara.)

“I love you…”

“Again…”

“I love you so much Em. I love you, wallahi ina sonka da gaske!”

Madaki yayi wani irin murmushi mai zurfi daya taɓo har wani ɓangare na can cikin zuciyarsa kafin a hankali ya haɗe tazarar dake tsakaninsu.

Wani ɓari na zuciyarsa ya furta addu’ar…

Nagode da sabon fatan saka bani a rayuwata ya Allah…!

*

#FashinBaƙi.

Ansha sha’anin bikin Jamila da angonta Sulaiman a daidai lokacin da ubangiji ya riga ya kaddara faruwarsa…

Anyi auren Salwa da Habibu, kuma ƙuddirin kowannensu ya rushe a lokacin da zaman aure yasa su duka suka fahimci cewa ba kowacce ganga ce ake gama cin moriyarta a rayuwa ba balle har ayi tunanin yar da kaurenta, rahama da alkhairin aure yasa kowannensu ya sauka daga sharrin zuciyarsa sun zamewa junansu sanadin gyaruwar ƙaddarar rayuwarsu…

Saifudeen ya ajiye sarautar Turaki, ya buɗe katafaren kamfanin tsarin gine-gine (Architecture) abinda ya karanta a makaranta, alaƙarsa da Madaki ta inganta ta sanadin sanin abubuwan dake gudana a kamfanin Royal K, sannan ya auri wata cousin ɗin kishiyar mahaifiyarsa (Nene Hadiza) wata ƙaddara da inda Fulani na kan ganinyarta, faruwarta zai zama tamkar a mafarki…

Nadiya da Aisha sun cigaba da zaman haƙuri a gidan mazajensu, ga dai kuɗi fal amma babu isashshen farin ciki, yayin da autarsu Safina ta gama makaranta kuma samuwar miji yayi wuya a wajenta, ƙaddararsu rayuwarsu ta faru ne da taimakon halin mahaifiyarsu…

Jidda ta cika burinta akan Suraj (saurayinta na farko) lokacin bikin Jamila ta haɗu da yarinyar da yake so har cikin zuciyarsa, watakila kwatankwacin yadda taso shi itama kafin ya nemi ɓata rayuwarta, kuma tunda tasa yarinyar nan a kwana ta shiga fallasa mata duk munanan halayensa da ita yake ɓoye mata, bata ƙyale ta ba sai da ta tabbatar cewar ko yarinyar nan ba zata zage shi ba in ya sake zuwa wajenta to tsaf zata iya yi masa korar kare….

Fulani ta rasu da shekaru biyu bayan faruwar duk wadannan abubuwan, bayan Saifudeen da Madaki sun sha mutuƙar ɗawainiya da ita gurin yawon nema mata sauki a cikin shekarun, wasu shekaru data shafe cikin jinya da kuma tarin nadamar da bata da amfani, irin nadamar da ubangiji baya karɓa, tata ƙaddarar kenan…

Kuma kamar yadda rayuwar kowanne bawa bata taɓa cika goma cif-cif ba, haka ciwon zuciyar Madaki bai taɓa warkewa ba sai dai samun sauƙi, sannan bai taɓa samun iyaye ko danginsa ba, amma ya samu mafi alkhairin arziƙin da kowanne namiji ke bukata a rayuwarsa, ya samu mace ta gari da bata da burin komai illa ganin ta faranta masa, macen da ta CIKE DUKKAN WANI GURBI da ya taɓa kasancewa mai zurfi a rayuwarsa sannan macen da ƙaddara ta mallaka masa ita…4

Don me akace ne?

Ƙaddara tana da tarin ma’anoni a duniyar nan, kuma bayan fuskar da aka santa da ita, tana iya ɗaukar siffar alkhairi ma….

Sauran rayuwar MAJID kuma, na barwa tunaninku….!3

Tamat bihamdillah!

Alhamdlilah Alhamdlilah.

Ina fatan Allah ya hada mu a ladan alkhairin dake cikin littafin nan sannan yayi min gafara a kuskuren dake cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *