ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 10
Zeenat shuru tayi, Ahmad Kuwa se driving yakeyi har ya shugo cikin unguwarsu, ganin mutane yasa ya daga Glass din Dan Karmutane su gansu Yana zuwa bakin Gate Me gadi Akai Sa’a bayanan yaje masallaci, Alhamdulillah yace a mind dinshi nan ya fito ya bude gate din sannan ya kulle, Yazo Wajen parking space yayi yace” My Xee ki fito, Sakko da kafarta tai ahankali sannan ya kulle kofar motar yana tafe tana binshi a baya har suka Isa wani Kofa ya bude sannan yace ki Shugo
Suna shiga taga Falon kamar ba na namiji ba sekace na amarya komai yayi kyau a ma’ajinsa Parlourn ya hadu matuka, Nan ya nuna mata wani daki yace” ga lnda zaki zauna nan komai kike bukata yana ciki, a kitchen Nan da komai da komai a ciki
Bata CE komai ba se binshi da kallo takeyi, Allah dai yasa bata fada wrong hand ba, me yake nufi da tai zamanta nan? Wani hawaye suka zobo mata, Zata fadi kenan yai sauri ze rikota tace” don’t touch Me!!! Dakyarta samu ta zauna wani zufa na keto mata Tace” 0h Ni zeenatu yaushe zan dena shan wahalal! Bangaren Su Mudansir Kuwa sun shiga kauyen ba lnda basu tambaya ba saidai ace masu basuga wata Yarinya ba gaskiya
Sun gaji sun wahala ga yunwa wani a cikinsu yace” Oga mudansir Mu kyale Yarinyar nan kawai nasan yanzu ta tsorota tasan takai ka gaba zaka Iya kasheta, Mudansir kallonshi yayi cikin bacin Rai yace” karka Sake shigamun harka Sau nawa zan fada maka INA son na aureta? Bama kai kadai ba duk Wanda ya karamun maganar akan na rabu Da My Baby Sena Koreshi A cikinku, Dukansu Suka sausautar da murya sukace Kayi hakuri ranka ya Dade Yai tsaki yace” sai Ku tashi Mu koma dajin Mu tunda bamuyi Nasara ba, Nan dukansu suka mik’e suka Nufa motar, Mudansir ranshi a bace! ‘
Bayan Zeenat taci kuka ta godema Allah, Ahmad yazo yana bata hakuri shifa taimakon ta zaiyi, in ba haka ba ba abun Da zaisa ya kawota cikin gidan nan
Nan ya mata wasu yan maganganu hankalinta ya kara kwanciya dashi,Yace” to Yanzu zaki Iya ban camera din nagani na kara tabbatar da abun da kika fadamun?
Tace” why not tashi tai yabi bayanta da kallo, Nan yaji Zuciyarshi na rayamai wani Abu, A mind dinshi yace” A‘uzubillah gaskiya bazan lya zama da Zeenat a gidan nan for long ba dole nasan abun da muke ciki Dan Zama mace da namiji waje daya akwai matsala, Shaidan zaita kawo musu Abu a zukatansune Yana Zaune yana tinani Sega Zeenat ta Fito tace” gashi! Firgigit ya waigo ya kalleta murmushi tamai, Yasa hannu ya amsa, Fara kallon pics din yayi ranshi yai matukar baci, yace” se an kwatar ma Yarinyar nan yanci, wasu mazan Wallahi se ahankali, kalletafa
Yarinya karama! Zeenat tace“ wlhi Kuwa Nan yace” zamusan abun da zamuyi gaskiya
Bayan kwana 4….._ Zeenat ta saba da gidan Sosai k0 hira me tsaho basayi da Ahmad yana dawowa tamai sannu Da zuwa ta kawo mai abinci yaci Seya shige Daki, Cos shi yasan kanshi, bawai ya
taba zama da mace bane a’a seda zeenat tazo gidan yasan abun da Maza keji idan sun kebance da Mace, Shi yasa yake baya baya da ita Dan anything can happen…
Washe gari dama ya mata alkawarin zekaita gidan Mamanta, Dan haka da wuri ta tashi ta shirya shiko bacci ma yakeyi, Around 8 taje tamai knocking, Ya tashi a gajiye shi yama manta gajeron wando ne da vest ajikinshi, Yazo ya bude kofar Zeenat na ganinshi ta rufe ido tace” ahhhm am sorry please, ta juya ta shiga daki da gudu, tana maida nunfashi Dan bata taba ganin namiji haka ba Lol
Ahmad Kuwa kallon kanshi yayi yace” oops Toilet yai maza ya shiga yazo ya shirya ya fito yaga tea da bread da kwai a parlour dama yunwa yakeji, Nan ya tsaya yaci Sannan yace” Zeenat ta amsa na na’am ki fito Mu tafi A kunyace ta fito,
Ya tada motar taje zata shiga sit din baya yace” dawo nan gaba, duk kunya yabi ya isheta tunda ta shiga motar ba Wanda yace ma wani uffan, Ahmad Kuwa se kallonta ta ta mirror yakeyi, sonta na kara shigarshi,
ooooooooooooooo
Bangaren mahaifiyarta kuwa tana Sharan cikin gidan taji gabanta yai mugun fadi, waje ta samu ta zauna taji dukjikinta yai sanyi ta koma kamar Mara lafiya, Addua take tayi, kome zai sameta Allah yasa yazo mata cikin sauk’i ‘
Daki ta shige tana jiran taji me zai biyo baya Sallamar namiji taji da mace” gabantane taji yace Gham! Kamar zata nitse a cikin katifa, Kodai mutuwar zeenat aka zo Sanar da ita, bata gama tinani ba Sega Zeenat ta shugo dakin da gudu ta rungumeta tana mamma mamma mamma
Maman ta tace” Zeenat Zeenat Ashe kina Raye kai Alhamdulillah, Naji dadi sosai nan zeenat ta gaisheta tace” bani kadai bace nan ta Ieko tace ma Ahmad ya shigo, yana shuguwa shima ya sama waje ya zauna Ya gaisheta kowa yai shuru Jim, Maman ta aranta
tana cewa Zeenat aure tayi kome? Mudai mukace ki tsaya kiji amsar daga bakinta
Nan Zeenat tace” mammah, tun daga randa aka saceta, ta ba mahaifiyana labari bata boye mata komai ba har izuwa yanzu da sukazo,
Mamantaa tai kuka sosai Tace” kai Dannan Amma Allah yasaka maka da alheri,
Ahmad yace” Amiin Yanda yaga mahaifiyarta na kuka se Ahmad ya kara tausayinsu gaba daya yace” Allah Sarki, Suna cikin magana ne sega Call ya shugo wayan Ahmad yana dubawa yaga Frnd Kabir, Rejecting yayi, Kabir na ganin haka yai kwafa yace” Wai meke faruwa da Ahmad? Tsaki Kabir yayi ya maida wayarshi cikin aljihu Su Zeenat kuwa da mamma da Ahmad Sun taba hira sosai, Ahmad yace” mama tunda an zama Daya, Inason Zeenat da aure, Mama tadanji nauyin maganartace” uhm, Seka turo manyan ka A zuciyarta kuma tana cewa ai tabbas halaccin da kai mun ka temaka yarinyata ai dole kai zan ba!
Sun gama hirar kenan Ahmad yace zasu tafi, Mama tace” to ba komai gadai Zeenat nan amana, Dan nasan Indai aka barta anan tsab zasu lya zuwa su kasheta, Dan har shuguwa gidan sukeyi su gama bincikensu basa ganinta, Ahmad yai mamaki sosai yace” lalla wadennan muguntarsu hartakai haka kenan
Sun mik’e zasu tafl, Ahmad yai gaba maman ta ta kirata tace” Ki kama kanki, ki tsare mutuncina da naki, Na miji namijine, Karki yarda dan zai temakeki Ya wulakantaki, ki tsaida Allah a zuciyarki, Allah ya tsare! zeenat Tace Amiin mamma nagode sai kin sakejina, Ta Ciro wayarta ta bata tace” gashinan zan dinga kira naji muryanki ta wayan Ahmad tace” to ba komai Sun flto har sun kama hanya, sukaga wasu sun kura musu ido, da sauri Ahmad ya daga glass din motarshi gaban Zeenat se faduwa yakeyi, yace” karki damu!! Aiko suna Barin unguwar Wanda su Mudansir sukai assigning akan su dinga dubuwa ko Zeenat na zuwa, nan take suke Kira Mudansir aiko sunga Zeenat Yace” What? Nan ya kira yaranshi yasa handsfree yace” MORA me kace?
Mora yace” munga Zeenatu da wani a cikin Mota Mudansir ne yace” are you serious? Mora ya amsa da cewa” oga ai bazan maka karya ba, Mudansir yace” A Ina ka gansu? Yace” right now suka fita daga gidan mahaiflyarta, OK OK
Mudansir yace” zamuyi wani Abu akai
Then ya kashe wayar Yana kashewa ya kalla yaranshi da dukansu suke gabanshi, Yana wani lashe baki yace” yanzu ya kuke ganin za’ai?
daya daga cikinsu yace” Oga a kasheta saboda this girl ta bamu wahala sosai, Mudansir yace” dama nima last decision Dana yanke kenan, amma before na kasheta sena bata mata rayuwa sosai, dolene na dandana zumarta, Se tasan tayi wasa da hankalin Mudansir ya
kare maganar dauke da wani shu’imin murmushi a fuskarsa Ya kara da cewa” Ku shirya zuwa gobe da motoci Kuyi shigan Sodoji kuje Ku tsaya a hanya Ku dinga duba motoci da Zaran kun ganta Ku rike motar, amma fa Ku kasance cirin shiri
saboda idan Akaji labari real soldiers zasuzo su kamaku kunga akwai Matsala
Wani daga cikinsu yace karka damu zamuyi taka tsantsan, Wunin ranar Mudansir cikin Murna yake
Su Zeenat Kuwa tun da zuka bar gidan mahaifiyarta, Wata hanya taga Ahmad yabi, Tace” INA zaka kaimu tana maganar ne cike da tsoro Dan yanzu Dan Adam ba abun yarda bane
Smiling yayi yace” zeenat har yanzu you don’t know da wa kike tare amma soon zaki Sani Do you think zan kaiki lnda zan cutar da rayuwarkine? Kunya taji yakamata sosai tace” uhm nifa bance komai ba ranka ya Dade, Taflya sukeyi basu tsaya ba har kusan 2hours tace” yunwa fa nakeji, nan ya tsaya wani ostrich yai mata siyayyan snacks da fresh milk, ya miko mata taci Sosai shi kam se Kallonta ta mirrow yake yanda take cin abincin hankalinta kwance, Wani Sonta yaji se shigarshi yakeyi, A mind dinshi yace” _Matatah Sun danyi tafiya mai tsaho taga ya shiga wani Babban Court dake Garin abuja, Dagani an sansanshi cos tunda suka shigo taga se gaisheshi akeyi abun ya bata mamaki Sosai, Wajen parking ya nufa yayi sannan ya kashe motar, tace” mezamuyi anan kuma? Yace” kedai ki fito Mu tafi Yana tafe tana binshi a baya har suka iso wani Dan madaidaicin Office ya shiga tabishi a baya Samun waje sukai suka zauna
Nan Ahmad ya gaisar da Barrister Lawal, _Barrister lawal mutun ne me kwato yancin duk Wanda aka zalunta, ya tsayar da gaskiya_
Ahmad yace” Barr please wani case na kawo maka so nake kasa hannu Dan Allah a ciki,
Barrister lawal yace” ai ko kai ma zaka Iya tunda hanyar Mu daya Nan Zeenat tace a Zuciyarta k0 kaima zaka Iya
(ta shiga tinani) Nan Ahmad dai ya fayyace mai komai game da Zeenat irin gwagwarayar da tasha a rayuwa musanman da Mudansirya sata a gaba
Barrister ya kalleta yace” itace zeenat din? Dan daga kai Ahmad yayi yace itace ranka ya Dade! Barr Lawal yace” zuwa Monday ai kai kananan duk abun da ake ciki zakaji, hope dai akwai shaidu ko? Ahmad yace” eh Barr lawal yace” OK Nan ya CE ke kinsan gidan yaron? Zeenat gabanta na fadi tace” eh nasani
Nan ya rubuta takardan sammaci yace” bari a kira masu aikin sukai gidan seki musu jagora, Ahmad yace” mutane Biyu ma sun isheni ka bani su Mu tafi dasu Barr yace” OK
Tafiyan Kusan awa 3 sukai from Abuja to Kano Zeenat ta nuna musu gidan, Ahmad yace” Kar ta fito nan ya kulleta cikin motar,
Kwankwasa kofar gate din sukai me gadi Yazo ya bude, ya gaishesu a tsorace Dan yanda yaga fuskar Ahmad ya murtuke ya kara tsorata Ahmad yace” INA matar gidan, gate man yace” bari naje na kirata, nan Ya kirata ta fito cikin iko da Isa
Tai warrr da ido me kuke bukata? Wani banzan kallon Ahmad ya wurga mata yace” gashi sammacin dankine aka kawo daga kotu, gabantane ya fadi Sosai,
Amsa tayi idonta cike da kwalla, Ahmad yace” Ku lika sauran ajikin gidan ta ko INA nan suka fara aikin su,
Zeenat Kuwa na cikin mota tana kallo tana dariya Nan suka barta a tsaya kamar Mara Lfy Sukam suka shiga mota suka wuce abunsu Daki ta shiga ta rasa meka mata dadi nan take ta kira wayar Mudansir taji a kashe, Me gadi kuma Yadanji abun amma besan me Mudansir din yayi ba, kunna redio yayi nan yaji wai an kara shigar da case din Mudansir Wanda yai ma Yarinya fyade
Kan kace meye Wanda sukaji a radio da Wanda sukazo wucewa suka tsaya sukaga me aka manna a gidan, nan danan labarin ya karwada unguwa Mudansir Kam ya shiga uku daga musu cewa Allah ya kara se masu cewa karshen Mugu yazo!!
oooo
Tai kiran duniyar nan Number Mudansir is not going Wani tsaki tayi tace” Dan banzan yaro kawai se up an down takeyi a cikin dakin ta rasa me zatai
Su Ahmad Kuwa bayan ya sallama Wanda suka rakosu ya basu Kudi me yawa suka mai godiya sosai Suna hanyane zeenat tace” dazu naji Barr lawal yace” ko kai zaka lya what did he mean?
Smiling Ahmad yayi yace” I’m a lawyer too, am sorry na boye maki tun farko, Dan zare ido tayi then letter on Tace” WOW WOW Allah ya Baku ikon rike gaskiya
Yace” Ameen suna tafe suna hira har suka Isa gida, sun Dan taba hira Kadan ta tashi ta shiga kitchen shi kuma Ahmad ya bude fridge ya dakko lemon Dan feelings din da yakeji ya Dan ragu, Bayan yasha yazo ya zauna se addu’ar Neman tsari yake Kar shaidan yayi tasiri akanshi Kabir Kuwa Friend din Ahmad, rabonshi dashi harya manta Key din bike dinshi ya dakko ya taho gidan Ahmad, yana zuwa ya shiga dakin, Kabir yace”
Wallahi kwata kwata baka da mutunci, baka son ziyara yanzu bansan me yasa ba. Ahmad yace” kayi hakuri ba haka bane, Ina Dan busy ne, Busyn da Ahmad yace” Kabir ya dago kai idonshi akan gyale, Ashe zeenat ta manta dashi a pallow
Kabir yace” Ahmad meye wannan ba gyalen mace bane” kodai abun da nake zargi ya tabbata ne? Shi yasa idan nai maka maganar aure se kace ba yanzu ba ko Ahmad Ahmd!!!! Kaban kunya
Hmm