ZEHRA CHAPTEF 8

ZEHRA CHAPTER 8

VILLAGE XXX, MAIDUGURI Kwana hudu kenan da suka shiga qauyen. Sossai ake ta fafatawa dare da rana. A daren yau ne Su Mustapha suka shiga ainihin wurin da Terrorists din suka riqe mutanen qauyen wandanda aka rufe su a cikin wani masallaci babu ci babu sha tsawon kwanaki.+ Tunda suka shiga wurin kuwa babu abinda kake ji banda harbin bindiga. Suna cikin wannan halin ne company din da suke biye da Mustapha suka neme shi suka rasa. Hakan kuwa ya tada musu hankali amma a dalilin ana tsakar yaqi ne yasa suka cigaba da bude wuta yayinda second in command dinshi yayi taking over. A wannan lokacin kuwa wata dama Mustapha ya samu wadda kuwa idan har ya sake ya shiga ba lallai bane ya fito da rai. On normal basis yakamata yayi commanding wasu su shiga ne amma kuma Our Mustapha being the fearless One ya wuce ya shiga da kanshi. Wannan ne yasa Company dinshi suke bala’in son shi, baya taba sa su at risk, he’d rather risk his life for them. Mustapha dai mamayar terrorists din yayi, domin kuwa basu ankara ba suka ji an buda musu wuta wanda kuwa kafin suyi wani motsin kirki tuni ya fara share su. Hakan ya sa battalion din gaba daya suka samu shiga wurin da confidence yayinda suka dafa mishi suka qarasa da sauran. Sossai jarumtar Mustapha da rashin tsoro yana ba colleagues dinshi mamaki sannan yana birge su. A wannan lokacin kuwa banda ihun ‘yan qauyen babu abinda kake ji. Tuni sojojin suka balle qofar Masallacin suka fitar da su. Yawancin su kuwa duk sun jigata. Tsofafin cikin su da yara duk sun tagayyara. Abin ban tausayi ma wasu sun mutu sannan an harbe masu taurin kai wadanda da alama sunyi gardama ne. *********** Tsaye suke suna bincika Maps da sauran tarkacen da Terrorists din suka bari ne wata dattijiya ta riqo hannun Mustapha tace “Yaro Allah yayi maka albarka da kai da yaran ka, Ubangiji Allah ya sada ka da alkhairin da yake cikin duniyar nan. A yadda ka ceci rayuwar mu Allah ya dafa maka a dukkanin al’amuran ka. Matar ka ta gode ma Allah da ya bata jarumi a matsayin miji. Ka fadi mata Inna Binto tace kar ta sake ta bata maka domin kuwa Allah bazai barta ba” Gani nayi Mustapha yayi murmushi yayinda yake ta sauraron ta. Ji nayi ta cigaba da fadin “Yaran ka dole ne suyi alfahari da kai…” Daya daga cikin sojojin da suke ta zuba ‘yan qauyen a cikin motoci ne ya qaraso wurin su yace “Mama mu je ki shiga mota..” Mustapha ne yace “don’t worry, she will be right behind you…” Dattijiyar wadda har yanzu ta qi sakin hannun shi ce tace “yaran ka nawa??” Yana murmushi yace “Inna ko mata bani da..” STORY CONTINUES BELOW Da sauri tace “toh kazo zan baka mata, akwai ‘ya ta Shamsiyya sai in baka ita ka aura..” Wannan karon dai Mustapha fashewa yayi da dariya wanda har yawanci colleaques dinshi sai da suka juyo suna kallon shi domin kuwa sun sani sarai shi din ba mai fara’a bane. Yana dariya yace “Ai Inna ina da wadda zan aura kuma bala’in sonta nake yi, duk jarumtar nan tawa da kike gani idan na rasa ta wallahi kaya zan zama” hahahaha… Itama dariya tayi tace “Allah sarki, Allah ya baku ikon cika burin ku sannan Allah ya raba ku da sharrin mai hassada”2 Haka dai ta cigaba da yi mishi addu’o’I kala kala wadanda ya ji dadin su. Dukda Mustapha ba mai associating da mutane bane ya ji dadin interacting da wannan dattijiyar. Sai da asuba ne suka isa Barrack yayinda ake ta murnar nassarar da aka yi. Chief of Army Staff na qasa ya iso Maiduguri wanda kuwa a dalilin jarumtar da Mustapha yayi ne aka yi mishi instant Promotion zuwa Lieutenant Colonel. yessss💪 Tuni kuwa kafafen yada labaru suka dinga yadawa a gidajen talabijin da Radio. Kafin a ce kwabo kuwa labari ya zagaya Nigeria har qasashen qetare. ♤♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL ABUJA Daddy ne zaune a ofis din Dr. Hamisu yayinda suke tattaunawa a game da case din Muhammad. Sossai hankalin shi yake a tashe. Daddy yace “Doctor, yanzu da ya kai wannan stage din please tell me the truth do you think he will get out alive?” Likitan ya gyara glasses din da ke idanuwan shi yace “Gaskiya I really can’t say Alhaji. It’s like he is trying to deal with whatever problem it is da yake damun shi amma kuma his heart is failing him. I am afraid nan da 24 hrs idan bai farfado ba zamu yi connecting dinshi da life support machine but I assure you muna iya qoqarin mu akan shi” Haka dai suka cigaba da tattauna case din Muhammad wanda ban gama tantance abinda yake faruwa ba.2 🤔🤔🤔🤔 ************ Mummy wadda hankalin ta yake a tashe tana zaune a waiting room din ne Daddy ya shigo. Miqewa tayi ta qarasa wurin shi tace “yaya? Me likitan yace??” Daddy wanda ya riqe ta ne yace “he is going to be fine Insha Allah, mu cigaba da yi mishi addu’a” Daddy dai ya qi sanar da ita abinda yake faruwa domin kuwa ya sani sarai ba qaramar damuwa zata shiga ba. Mummy is such an emotional being… *********** Da safe suna zaune a waiting room suna ta jira a basu izinin shiga ganin shi. Tuni Papa da Anty sun iso, Zehra dai tana gida bata ma san abinda yake faruwa ba saboda dai ta riga tayi pulling kanta away from kowa. STORY CONTINUES BELOW Ganin halin da take ciki na damuwa ne yasa su Papa basu bi ta kanta ba. Mummy dai sai zubar da hawaye take yi yayinda Anty take ta bata haquri. Abinda ya fi tada mata hankali ma shine yadda aka hana su shiga ganin shi har yanzu. Tana bala’in shiga damuwa idan Yaran ta sun shiga matsala domin kuwa bala’in son su take yi musamman Muhammad. why is that???🤔🤔 Wayar Daddy ce tayi ringing yayinda ya miqe ya fita sannan ya amsa. Alhaji Tukur Abdallah ne yace “Alhaji Omar ashe yaron ka yayi aikin jarumta a qasar nan??” Cike da mamaki yace “wane yaron?” Yace “Mustapha mana, Yanzu nake gani a news sunyi nasarar qwato qauyen nan da mutanen banzan nan suka yi hijacking wanda aka kashe sojojin mu wancan satin. Gashinan anyi mishi promotion yanzu da safen nan. Hala dai baka kalli news ba?” Cike da mamaki Daddy yace “Yanzu ashe dama yaron nan Yaqi ya tafi shine yayi mana qarya??” Alhaji Tukur yana dariya yace “baya so ku tada hankali ne. Amma tsakani da Allah samun yara irin su Mustapha masu kishin qasar su abu ne mai wahala. Ubangiji Allah yayi mishi albarka, Allah ya cigaba da kare mana su” Daddy ya dan yi murmushi yace “Ameen Alhaji Tukur, ai nima rabo na da gida tun jiya wallahi. Ga mu a asibiti Muhammad babu lafiya” Yace “subhanalillah, aikuwa bari in shigo in duba shi. wane asibiti ne?”………. A haka dai suka gama Magana a waya wanda kuwa bayan ya gama ne ya shigo waiting room din yayinda yake fadin “Na rasa gane wannan irin hali na Mustapha, Yaro tun kana qarami baka jin magana” Da sauri Mummy ta dago kanta tace “Me ya faru da shi kuma??” Daddy ya basu labarin abinda yake faruwa. Mummy tana salati tace “Na shiga uku da wannan yaro da baya jin Magana, yanzu dama tafiya yayi ya saida ranshi shine bai fadi mana ba? Ni wallahi bana son wannan aikin nashi, da mun sani da bamu amince yayi aikin sojan nan ba. Mu shikenan kullum muna cikin zullumi da tashin hankali” Papa ne yace “haba dai Mummy, ai kuwa yakamata ace kina cikin farin cikin abinda yayi, gaba daya fa duniya maganar shi ake yi. ai wannan abin alfahari ne. Mu cigaba da yi musu addu’a akan Allah ya cigaba da kare mana su, Allah kuma ya ba Muhammad lafiya” ♤♤♤♤♤♤♤♤ 7 DIVISION ARMY BARRACK MAIDUGURI Tsaye yake a falon gidan yayinda yake riqe da wayar shi wadda yake qoqarin kunnawa. Aikuwa yana kunna wayar ne messages suka dinga shigowa. Gani nayi ya ajiye wayar a kan centre table yayinda ya wuce daki ya fara hada kayan shi. Mustapha dai a yau dinnan yake shirin dawowa gida domin kuwa dukda abubuwan da suka faru daidai da second daya Zehra bata fita daga tunanin shi ba. Sossai yake missing dinta. Ya sani lallai idan ya rasa Zehra ba zai ganu ba. Bayan ya gama hada kayan shi ne ya koma falon don kiran driver din da zai kai shi Airport. STORY CONTINUES BELOW Normally yakamata ya tafi tare da colleagues dinshi ne a jirgin su na sojoji wanda kuwa sai bayan kwana uku zasu tafi amma sam ya qi. Shi kam a yadda yake ji idan bai ga fuskar ta ba har qaramin hauka ma zai iya yi don haka ne first thing da yayi was to book a flight. Yana daga wayar kuwa ya ga text messages din da suka shigo har guda 187.6 Ji nayi yace “whoa..” yayinda ya bude inbox din ya duba. Gani nayi yayi murmushi sannan yace “My crazy Angel” A cikin text messages din kuwa guda 156 duk daga Zehra ne sai sauran from different random people. Bai bude messages din ba ya koma kan kujera ya zauna yayi dialing lambar ta. Ai kuwa ringing din farko ta amsa wayar. Kasa magana tayi kusan tsawon minti biyu. Murmushi na ga yayi sannan yace “hey My angel talk to me mana… I missed you very much” Wata ajiyar zuciya ya ji ta saki yayinda ta fashe da kuka. Sossai ta bashi tausayi. Mustapha dai ya sani sarai Zehra tana bala’in son shi, ya sani cewar her whole world revolves around him sannan shine yake riqe da zuciyar ta a hannun shi kamar yadda tashi take hannun ta. Ko da ganin yawan messages din da ta aiko mishi ma ya san tayi missing din shi ba kadan ba. Ji nayi yace “My Angel I am sorry please ki daina kuka, yanzu haka gani nan zan je Airport, Babu abinda nake son gani banda kyakyawar fuskar ki, I really missed you alot” Tana share hawayen ta tace “Baby Wallahi rayuwa without you is hell” Murmushi yayi yace “same here my Angel, Na sani cewa I can’t survive without you, as soon as I reach Abuja zan zo in gan ki” Ji yayi tace “Allah na gode maka, bari in tashi in shirya maka abinci kala-kala masu dadin gaske” Da sauri yace “hey don’t stress yourself, kala daya ma ya isa..” Cikin shagwaba tace “I swear Baby kana da eating disorder, ni kam yau sai na dura maka abinci kuma sai ka cinye duka wanda zan dafa maka” Dariya yayi sannan yace “duk yadda kika ce haka za’a yi My Angel. Just know that ganin ki ya fi komai dadi. Now let me pack up and reach the airport kar inyi missing flight din” Bayan sun yi sallama ne kiran Daddy ya shigo wayar shi. Cike da girmamawa ya amsa yayinda yace “hello Daddy ina kwana” A dayan bangaren ne Daddy yace “yanzu fisabillilah abinda kayi ka kyauta kenan?? A ce ka tafi mission irin wannan bazaka fadi mana ba? Yanzu da wani abin ya same ka shikenan sai dai mu ji labari?” Cike da girmamawa Mustapha yace “don Allah Daddy kar kayi fushi, wallahi ban san yadda zan fadi muku bane. Ko kadan bana so ku shiga damuwa. Insha Allah bazan qara ba, please forgive me daddy” Daddy yace “toh ya zan yi da kai, tunda dai kafaffe ne kai tun kana yaro na san ka. I am proud of you Son, You are truly a hero and congratulations to you on your promotion” STORY CONTINUES BELOW Mustapha yana murmushi yace “thanks Daddy” Daddy yace “Kayi qoqari dai ka gama abinda kake yi ka dawo don yayan ka baya da lafiya gamu a asibiti tun jiya da daddare” Cike da tsananin tashin hankali yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, me ya same shi Daddy??” Daddy yace “ya samu attack ne…” Kafin ya qarasa magana Mustapha ya dinga salati yayinda idanuwan shi suka kada suka yi ja. Muryar shi tana rawa yace “Daddy me aka yi mishi??” Yace “I have no idea Mustapha, har yanzu ma bamu samu ganin shi ba. It’s very serious amma Mummyn ku bata san hakan ba so be careful not to get her all tensed up idan ka iso” Muryar Mustapha tana rawa yace “I will be in Abuja the soonest insha Allah Daddy” Sossai hankalin shi ya tashi yayinda ya bi ya rude. Addu’a kawai yake yi kar wani abu ya samu dan uwan shi domin kuwa life without Muhammad will be a disaster for him. hmmm hmmm hmmm… ♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL ABUJA Zaune take a kan gadon yayinda yake kwance akan cinyar ta. Idanuwan shi a rufe yayinda take ta shafa kanshi tana yi mishi sannu. Kusan awa daya kenan da Muhammad ya farfado wanda bayan likitoci sun dudduba shi ne suka ba su Mummy izinin ganin shi. Dr Hamisu yayi warning Daddy akan kar a fara yi mishi tambayoyi har sai ya huta. Mummy wadda take ta shafa kan shi ce tace “Yanzu ina yake yi maka ciwo??” Muryar shi qasa qasa yace “babu ko ina mummy, kawai I am weak ne” A zahiri kuwa qarya yayi mata domin kuwa zuciyar shi ce take yi mishi tsananin zafi amma saboda baya so ta shiga damuwa ne yayi mata qarya. Anty ce tace “amma dai yakamata ka ci abinci” Idanuwan shi a rufe har yanzu yace “sai anjima Anty” Mummy tace “toh me kake so?” Ya gyara kwanciyar shi akan cinyar ta tare da riqe hannunta gam yace “ina so in cigaba da kwanciya akan cinyar ki ne kawai Mummy” Murmushi tayi tace “for as long as you want my Son” A haka kuwa Muhammad ya dinga jero addu’o’I kamar kullum a cikin ranshi har bacci ya kwashe shi. ************* Mustapha ne ya qwanqwaso qofar dakin ya shigo. Gaba dayan shi a hargitse yake. Dama ga rashin isashen bacci tsawon kwanaki biyar, ga gajiya sannan kuma ga shocking news da yayi receiving na rashin lafiyar dan uwa shi. Da ka kalle shi kasan ba daidai yake ba. Anty ce tace “soja mazan fama, saukar yaushe??” STORY CONTINUES BELOW Mustapha wanda yake kallon Muhammad ya qarasa wurin shi da sauri yayinda yace “wallahi yanzun nan Anty” Ya shafa kan Muhammad tare da kallon Mummy yace “Ya jikin nashi Mummy?” tace “da sauqi” yace “Allah ya bashi lafiya” Anty tace “amma ai da ka qarasa gida ka huta sannan, you look exhausted” Girgiza kai yayi yace “I can’t Anty” Mummy tace “ai yaran nan yadda kika san tare suka fado duniya” Anty tayi murmushi tace “Allah ya barku tare” Haka dai suka cigaba da hirar rashin lafiyar Muhammad wanda kuma daga baya Mummy ta dinga yi mishi fadan rashin fadi musu abinda ya kai shi Maiduguri. Haka nan yayi ta bata haquri yayinda Anty ta sa baki. Daga baya kuwa suka dinga yi mishi congrats na qarin girma da ya samu tare da yi mishi addu’ar tsari daga sharrin maqiya. ************* Bayan sallan Isha’I Mustapha yana zaune a gefen gadon shi yayinda su Mummy suke zaune a waiting room. Gani nayi Muhammad ya dan motsa yayinda ya bude idanuwan shi. Da sauri Mustapha ya matsa daf da shi ya dafa shi tare da fadin “bro how are you feeling??” Muryar shi qasa-qasa yace “fine, yaushe ka dawo?? How was it??” Mustapha yace “dazu na dawo and it was a success, I even got promoted today” Fuskar Muhammad tayi displaying tsananin farin ciki yayinda yace “Masha Allah, I am so proud of you Musty. Allah ya cigaba da tsare mana kai” Yace “ameen bros, thank you” Ganin yadda Mustapha yake ta kallon shi cike da tausayawa ne yace “common, give me a hug mana tunda dai I can’t reach out to you” Yayi hugging dinshi wanda kuwa sun kusa mintuna biyar a haka sannan sukayi breaking hug din. Gani nayi Ya riqo hannun Muhammad din sannan yace “hey, what happened to you? Why are you here on this bed?” kai… anya zaka so ka ji kuwa??🤔2 Bata rai yayi yayinda ya rufe idanuwan shi. Babu abinda yake gani illa kamarnin ta. Sossai telephone conversation dinta da masoyin ta yake yawo a qwalwar shi. Ji nayi yace “nothing Musty, Allah ne ya saukar mun..” Kafin ya qarasa maganar shi kuwa Mustapha yace “We both know there is something, Everyone is worried about you especially Mummy. Is it something we can help you with?” Muhammad yace “nace ka manta da zancen Musty” Mustapha yace “ka dai san bazan qyale ka ba sai ka fadi mun ko??” Idanuwan shi a rufe yace “Okay fine, zan fadi maka amma it should remain a secret between us” yace “deal” Kai tsaye yace “I have fallen in love…”2 Cike da murna Mustapha yace “whoa, dagaske??..” Bai qarasa magana bane ya ji Muhammad yace “with the wrong person” Da sauri yace “ban gane with the wrong person ba, tell me who is she?? me ya faru??” Ran shi a bace ya cigaba da fadin “Kar kace mun ita ta jefa ka cikin wannan halin?? Wane irin rashin Imani ne hakan..” Muhammad wanda har yanzu idanuwan shi a rufe ne yace “Ba laifin ta bane Musty. She doesn’t even know, infact bata taba gani na ba ma” Ya dan gyara kwanciyar shi sannan ya cigaba da fadin “Sau daya na ji muryar ta tun kusan wata biyar da suka wuce and it kept echoing in my brain, it became a melody that I enjoy reminiscing on. I didn’t realise I have fallen in love with the owner of the voice until I saw her at the wedding. lokacin da nayi niyyar gabatar da kaina zuwa gareta ne na gano cewar she has someone wanda kuwa daga hirar da na ji tana yi da shi a waya I knew that I stand no chance, not in this lifetime or the next” Mustapha wanda yake ta sauraron shi ne ya cika da mamakin abinda Yayan nashi yake fadi. What a mystery he thought.. Muhammad ya dafa qirjin shi daidai saitin da zuciyar shi take sannan yace “I swear I tried taking ZEHRA out, but my heart failed me…”2 Mustapha wanda zuciyar shi ta buga yayinda yake qoqarin processing last statement din yayan shi ne na ga yayi saurin sakin hannun shi. Muryar shi tana rawa yace “Z..E..H..R…A??… kace…??” Muhammad wanda ya runtse idanuwan shi yace “yes bro, Dee’s best friend..”7 Gani nayi Mustapha ya miqe tsaye yayinda idanuwan shi suka kada suka yi jajawur. Gaba daya jikin shi kyarma yake yi yayinda kan shi ya fara azabar ciwo. Zuciyar shi kuwa kamar zata fito waje saboda azabar zafi yayinda maganganun Muhammad suke ta kai da komowa a cikin qwalwar shi. Runtse idanuwan shi yayi yayinda yake addu’a Allah yasa mafarki yake yi ba gaske ba amma inaa, Yana bude idanuwan shi ya tabbatar it’s not a dream… THIS IS REALITY. Ji nayi yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”3 ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance yake a kan Chinese rug din falon shi wuraren qarfe biyu na dare yayinda yake fama da azabar radadi a cikin zuciyar shi. Tun da ya shigo gidan kusan awa biyar da suka wuce yake kwance a same position ba tare da yayi ko motsi ba. Banda don numfashi da yake yi da zaka yi tunani babu rai a tare da shi. Gani nayi ya tashi zaune yayinda ya riqe kanshi. Gaba daya qwalwar shi a toshe take. Ban ankara ba na ga hawaye na gangarowa daga idanuwan shi wanda kuwa bai ma san yana yi ba. Ji nayi yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un….” Yayinda ya tuno maganar da suka yi bayan ya sanar da shi zancen Zehra. Composing kanshi yayi ya koma ya zauna kan gadon tare da riqe hannuwan shi yace “bro,, I need you to be strong and leave this bed ASAP, I will make sure you marry the girl..I promise you” Da sauri Muhammad yace “No bro, ko kadan bana so inyi sanadiyyar raba ta da masoyin ta. Na gwammace in mutu da in hana ma wasu farin cikin su. Trust me, rabuwa da masoyi is not a good experience” ya dan yi shiru sannan ya cigaba da fadin “if you were in love you’d understand better”3 Ji nayi Mustapha yace “if only you know cewar ni ne masoyin nata.. if only you know cewar I know exactly how it feels… If only you know cewar a dalilin bala’in son Zehra da nake yi I can’t sacrifice her for anything or anyone but then, I can’t let you die” Gani nayi yayi Kneel down yayinda ya kwantar da kan shi a kan kujera. Da alama ya rasa inda zai sa kan shi ya ji sanyi. Daga nan kuma ya fara tuno conversation din su da Dr Hamisu bayan ya baro dakin Muhammad. “a gaskiya bazan boye maka ba he has reached the final stage, right now he is trying to deal with his problems amma his heart is failing…”6 Runtse idanuwan shi yayi yayinda yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” Ahankali na ji sautin muryar shi tana fita yayinda yake fadin “wannan wace irin qaddarar rayuwa ce? Gaba daya zuciya ta tana hannun ta, My heart beats for her alone. My whole world revolves around her. Rayuwa ta bazata taba yin amfani ba idan babu ita a tare da ni…” Ya ja numfashi sannan ya cigaba da fadin “ya kasance the only person that watched my back tun ina qarami, Yayi sacrificing so many things just to make me happy. Yana yin fada da kowa a dalilina ko da kuwa bani da gaskiya. The one that helped me achieve my biggest dream in life, I wouldn’t have been who I am today if not for him.. And now he is dying because of her” Wasu zafafan hawaye ne suka qara gangarowa daga idanuwan shi yayinda yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” Ni kuwa nace “Allah ya dafa maka Musty”5 STORY CONTINUES BELOW ♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari da safe wuraren qarfe bakwai ne wayar shi ta fara ringing. Gaba daya har gari ya waye bai runtsa ba. Saqe-saqe kawai yake yi yayinda yake cikin tsananin tashin hankali. Sossai kan shi yayi nauyi domin kuwa banda azabar ciwo babu abinda yake yi mishi. Nikuwa gani nayi har ya rame yayinda ya zama so disorganized. Wayar tana gab da tsinkewa ne ya amsa. Muryar ta ce ta daki qwalwar shi wanda har sai da zuciyar shi ta buga. Ji yayi tace “Baby how are you feeling? Jiya nayi ta kiran ka baka amsa ba. I am so sorry about Ya Moha, Anty take fadi mun an kwantar da shi asibiti babu lafiya. Ya jikin nashi??” Mustapha wanda yake ta sauraron muryar ta ma kasa Magana yayi, Banda tafasa babu abinda zuciyar shi take yi. Jin yayi shiru ne tace “Baby are you on the line??” Muryar shi qasa qasa yace “yes My Angel..” Zehra tace “subhanalillahi, me ya same ka?? Ciwon nashi yayi tsanani ne haka?? Kana asibiti ne? dama na ji su Anty suna fadin zasu je su dubo shi anjima, I will come with them” Da sauri yace “No” Cike da mamaki tace “Yau na shiga uku, Baby No?? what?? Are you okay??” Tuni muryarta ta canza yayinda ta shiga tsananin damuwa. Gani nayi ya tashi zaune yayinda ya dafe kai yace “kar ki bi su, zan zo anjima kadan I want to talk to you” Zehra wadda hankalinta yake a tashe ce tace “don Allah Baby ka fadi mun me ke faruwa. You don’t sound okay…” Kai tsaye yace “just wait for me My Angel and promise me duk abinda nace kiyi zaki yi” ghen ghen ghen… Ba tare da tayi tunanin komai ba tace “Baby I promise duk abinda kace inyi zan yi. Meanwhile congrats to you on your promotion. I am soo happy for you, so proud of you and I love you soooo very very much amma kuma idan ka zo You will surely get a spank from me for lying to us..”2 Gani nayi Yayi murmushi wanda bai ma san yayi ba. Sossai Zehra take affecting rayuwar shi. Shi kam bai san wane irin mugun so yake yi mata ba. Bai ankara ba ya ji tace “Ina nan ina jiran ka Baby na” Yace “okay My angel, sai na zo” ♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE Wuraren qarfe tara da rabi na safe ya iso gidan, A lokacin kuwa su Anty sun tafi asibiti. Zaune yake a falon qasa yayinda ya dafe kan shi. Sossai Mustapha yake cikin tsananin damuwa. Da ganin yanayin shi ka san lallai akwai matsala. Duk da yayi looking so disorganized, Yayi kyau sossai. STORY CONTINUES BELOW Bai ankara ba ya ji ta riqe hannuwan shi da soft hands dinta. Da sauri ya dago kai ya ganta tsugunne a gaban shi. Yanayin yadda ta gan shi ne ta zaro idanuwa tare da fadin “Baby, what happened to you??” Da sauri na ga ta dafa goshin shi wanda hakan kuwa ya saukar mishi da wani irin sanyi a jikin shi. Ji yayi tace “baka da lafiya ne??” Shi kam kallonta kawai yake yi yayinda ya ga ta miqe tana fadin “let me get you something to eat sai ka sha magani..” Da sauri ya riqo hannun ta yace “hey come here” Ta dawo ta tsugunna a gaban shi tace “Baby don Allah ka fadi mun abinda yake damun ka, You are a mess right now, look at your hair looking rough which is so unusual, its like ma baka yi bacci ba all through the night. Rashin lafiyar Ya Moha ne??” Gani nayi ya saki ajiyar zuciya tare da riqo hannun ta ya miqar da ita sannan ya zaunar da ita a gefen shi. Juyowa yayi ya fuskance ta sannan yace “Muhammad is seriously ill My Angel” Zehra wadda ta tausaya mishi ce tace “wai wane irin ciwo ne yake damun shi? na ji Anty tace wai kamar its related to his heart ko? Dama yana da heart problem ne?” Kai tsaye yace “Yes My angel, he has a Congenital Heart disease. He was born with it, an gano hakan ne when he was only seven years old” Hannuwan ta ya matse a cikin nashi yayinda ya cigaba da fadin “A lokacin da aka gano yana da ciwon kuwa it was almost too late because ya riga yana gab da shiga final stage that could cause him to give up amma somehow da taimakon Allah yayi surviving. Tun daga wannan lokacin ne aka dora shi akan treatment yayinda likitoci suka bada strict warning akan a kiyaye duk wani abu da zaiyi triggering ciwon nashi…” Zehra wadda ta cika da tausayin Muhammad ce tace “toh yanzu meye yayi triggering ciwon nashi? I thought he was doing fine ai..” Mustapha wanda ya qura mata idanuwa ne yace “My Angel its you..” Cikin rashin fahimta tace “ni kuma Baby? Me nayi? Ban gane ba” Kai tsaye yace “Moha yana kwance a asibiti saboda ke…” Da sauri ta miqe tare da fadin “what are you saying Baby? Ni fa ko ganin shi ban taba yi ba..I was supposed to meet him during Dee’s wedding amma wallahi I never saw him. Toh ya za’a yi ace yana asibiti saboda ni? Me nayi mishi toh??” Mustapha dai kallon ta kawai yake yi yayinda yake tunanin abinda zai ce mata. Gani nayi ya riqo hannun ta yace “My angel zauna ki ji abinda zan fadi miki” Ko da ta zauna fuskar ta a murtuke take yayinda tayi shiru tana sauraron abinda zai ce. Mustapha wanda yake ta kallon ta kuwa gani yayi ta canza fuska. Duk zaman shi da ita bai taba ganin bacin ran ta ba kamar na yau. Sossai zuciyar shi take qoqwanton fadi mata abinda ya zo da shi. Ni kuwa nace “toh me kazo da shi???” STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ya Kwantar da kanshi a kujera yayinda ya rufe idanuwan shi. Har yanzu hannuwan su riqe da juna. Kusan minti goma suna a hakan. Daga bisani ne ta ji muryar shi yana fadin “Muhammad is one of the best people a duniyan nan. Ya kasance mutum mai haquri, mai son mutane, baya so ya ga kowa a cikin damuwa. Duk wani abu da ya mallaka na kowa ne. Abun hannun shi bai taba rufe mishi ido ba” Ya saki ajiyar zuciya sannan ya cigaba da fadin “I was trouble when I was a kid. Muhammad shi kadai yayi tolerating dina wanda kuwa hatta iyayen mu da suka haife mu I am sure they felt like giving me away. Duk barnar da nake yi Muhammad always took the blame and the punishment for me. Akwai lokacin da su Daddy suka gane cewar he was protecting me all the while wanda kuwa suka yi grounding dina for 2 weeks. Damuwar da ya shiga a lokacin ko rabi ban shiga ba, a koda yaushe yana jingine da qofar daki na yana bani haquri tare da jaddada mun cewar he is doing everything possible to make them forgive me. Lokutta da dama har kuka yake yi wanda ni ne nake bashi haquri. There was a time da Mummy tayi punishing dina inda ta hana ni abinci for good three days saboda na fasa mata glass din motar ta. Muhammad shine yake bani abincin shi a boye sannan ya zauna da yunwa…. So many things he did for me” Shiru ya dan yi sannan ya cigaba da fadin “duk abubuwan nan da yayi mun kuma ni ne na janyo mishi attack din ya kusa kai shi lahira…” Zehra wadda take sauraron shi kuwa gani nayi ta zaro idanuwa yayinda ta cika da tsananin mamaki. Ya cigaba da fadin “I have always seen fireworks on TV and I have always wanted to experience how it works shine wata rana na sa driver ya kai ni store na siyo, the money I got from Muhammad as always… Honestly it was not my intention to scare him, infact ni kaina ban san abun zai yi irin qarar da yayi ba. A lokacin da na kunna shi a tsakar gidan mu dadaddare he had no idea what I was doing. Abinda na tuna a lokacin da na buga abun shine both of us went down cike da tsananin tsoro. Ba su Daddy ba hatta neighbours sun tsorata domin kuwa abu ne da ya zo ma kowa unexpected. A lokacin da hankali na ya dawo gareni Muhammad was still down unconscious. He was rushed to the hospital wanda kuwa likitoci suka sha wuya akan shi. He was even placed on life support for a whole month. Ban taba ganin Mummy da Daddy suna kuka ba sai ranar. Sai da Muhammad yayi wata daya kwance a asibiti sannan Allah ya taimaka ya farfado. Guess what he said immediately he woke up da su Mummy suka tambaye shi abinda ya faru?? ‘Mummy, Daddy please kuyi haquri, I never thought it will cause problems for everyone. Insha Allah bazan qara ba’ A lokacin na so in fadi gaskiyar abinda ya faru amma ya hana ni. It was a secret they never got to know har yau. Sai da hukuma ta sa Daddy ya biya fine a lokacin saboda an shiga haqqin maqwabta” Dago kan shi yayi ya kalli Zehra wadda take zubar da hawaye yace “it all came down to lokacin da na kammala secondary school and I wanted to join the army. Su Daddy suka qi, sossai na shiga damuwa a lokacin because nothing interests me aside wanting to join the army. My greatest problem a lokacin shine na kasa convincing dinsu because bana interacting da su atall, Iyaye na ne amma bana iya zama muyi hira tare da su. Muhammad shine kadai ya san duk wani abinda yake faruwa a rayuwa ta. A bakin shi suke jin halin da nake ciki a koda yaushe. Sossai yayi qoqarin convincing dinsu akan su amince mun amma sam suka qi. Dare da rana babu abinda yake yi banda roqon su amma suka qi. Muhammad gradually pulled away from them, ya daina cin abinci sannan ya daina zuwa school all because of me. Su Daddy sunyi noticing amma suka yi watsi da shi, the thing is they never liked the profession because of the danger involved sannan Mummy is a very emotional person, abu kadan yake tada mata hankali ta shiga tsananin damuwa” STORY CONTINUES BELOW Ya saki ajiyar zuciya tare da fadin “could you believe Muhammad fell seriously ill because of this??… For me??… Da su Mummy suka tsorata da al’amarin ne akan dole suka amince mun” Ya riqo hannuwan Zehra duka biyu yace “My Angel Muhammad has done so many things for me in life, In return I have done nothing for him” Muryar zehra tana rawa tace “Baby abinda ban gane ba shine what has all these got to do with me??” Good question my dear… Ba tare da ya kalli idanuwan ta ba yace “Muhammad has fallen deeply in love with you, somehow he heard our phone conversation ranar dinner din su Dee wanda hakan yayi discouraging dinshi from approaching you…” Zehra dai tunda ya fara wannan maganar ta fashe da kuka tana sauraron shi. Ta riga ta fahimci inda maganar tashi ta dosa wanda kuwa bazata taba amincewa ba. Ji tayi yana fadin “trust me Muhammad yana sa interest din kowa kafin nashi, yana qoqarin haqura da ke amma his heart is failing him. Yanzu haka ya qi fadi ma kowa sai ni wanda kuwa da ya sani cewar ni ne masoyin ki bazai taba fadi mun ba, he’d rather die than separate us” Gani nayi ya saki hannuwan ta sannan ya sa hannuwan shi biyu ya shafa kanshi yace “My Angel I want us to sacrifice our love for him… Ina so ki aure shi” Da sauri ta miqe tace “whaaat??” Fashewa tayi da sabon kuka tace “dagaske kake yi ko wasa?? Wallahi bazan iya ba, babu wanda nake so a duk fadin duniyan nan sama da kai Baby” Da sauri tayi kneel down a gaban shi tana kuka tace “Baby ban san ya SO yake ba sai akan ka, zuciyata gaba daya tana hannun ka. Rayuwa ta bazata taba yin amfani ba idan babu kai. Kana cikin qwalwa ta round the clock 24/7, Please Baby don’t do this to me now. Wallahi zan iya mutuwa idan ban aure ka ba. I am sure idan ka fadi mishi kai nake so he will understand, kamar yadda yayi maka sacrifices a baya he will deal with this..” Mustapha wanda yake qoqarin kar yayi breaking down a gaban ta ne ya kauda kanshi tare da fadin “hey I can’t, he is my brother whom have done so much for me and I don’t want to lose him. Infact I LOVE HIM MORE THAN I LOVE YOU right now…” Zuciyar Zehra ce ta buga yayinda ta kalle shi cike da tsananin mamaki. Gani nayi ta sa hannuwan ta ta tallabo fuskar shi ya fuskance ta tace “Wallahi qarya kake yi, ka kalle ni cikin ido ka maimaita abinda kace” Mustapha wanda zuciyar shi take zafi kallonta yake yi ba tare da yayi Magana ba. Shi kam ya san bazai taba iya kallonta cikin ido yace baya sonta ba domin kuwa it’s a big fat lie.. Babu wadda Mustapha yake so fiye da ran shi a duniyan nan irin Zehra.. Hawaye suna ta ambaliya a fuskarta tace “na sani cewar bazaka iya ba, Baby I know you love me more than anything and anyone in this world please tell me you are lying and don’t give me away on a silver platter I beg you..” Gani nayi Mustapha ya zare hannuwan ta daga fuskar shi ya miqe tare da fadin “Just forget about me and marry my brother. He is better than me in every aspect, I promise you bazaki yi regretting auren shi ba” Yana tsakiyar falon yayinda zuciyar shi take ta tafasa ga kan shi yayi nauyi. Gani nayi Hawaye na gangarowa daga idanuwan shi wanda yayi saurin gogewa. Bai ankara ba ya ji ta rungume shi ta baya so tight tana kuka tace “Its you I love Baby, Halinka nake so ba nashi ba. I find all your flaws to be perfect My Baby, You are better than kowa a duk fadin duniyan nan a wurina. Don Allah kar kayi mun haka, ko ka daina sona ne ni wallahi ina sonka. Na amince zan aure ka ko baka sona. Duk azabar duniyar nan ka gana mun na yafe maka kuma a hakan zan zauna da kai. Ko Yanka ni zaka yi a gidan ka wallahi na amince zan zauna da kai. I can’t live without you Baby” Da sauri ta sake shi ta zagayo ta gaban shi ta qara rungume shi tana wani irin kuka wanda kuwa bata taba yin irin shi ba ta cigaba da fadin “don Allah baby ka fadi mun mafarki ne wannan ba gaske ba, tell me you love me more than anything in this world, tell me you can’t sacrifice our love for anything or anyone a duniyar nan..” Mustapha wanda ya daskare a tsaye kasa motsi yayi domin kuwa tunda Zehra ta rungume shi ya ji duk duniya babu inda yayi belonging idan ba tare da ita ba. Sossai kalaman ta suke dukan qwalwar shi. Gani nayi yayi wrapping hannuwan shi around her yayinda yayi hugging dinta very tight like his life depend on that particular hug. A yanzu kuwa su biyun duk kuka suke yi wanda kuwa na Zehra ke fita da sauti yayinda shi kuma yake na zuci. Kusan minti Biyar suna maqale da juna. Mustapha ne ya ankara. Da sauri ya banbare ta daga jikin shi ya dan tura ta baya yayinda yake ta roqon gafara a wurin Allah. Ba tare da ya kalle ta ba yace “Unfortunately everything is true Zehra.. Good bye”2 Daga nan kuwa ya fita da sauri yayinda ya barta tana ta ihun kiran sunan shi. Gaba daya ma ta kasa motsi domin kuwa jikin ta kyarma yake yi yayinda qafafuwan ta suka yi mugun nauyi. Gani nayi ta zame qasa tana ta kuka mai ban tausayi Yayinda na ji tana fadin “ba da gaske bane, mafarki nake yi… Baby bazai taba yi mun haka ba. He loves me alot and I can’t live without him….” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ ONE MONTH LATER VILLA DEL PARCO, SARDINIA ITALY “When I miss you I am not okay. Baby I swear I am far from okay, my heart aches because you are not here with me” “I will never forget the amazing memories I had with you, but we can always create more of them. Come back baby” “I love you soooooooooooooooooooooooooo very much” “I miss you” “Do you know what the worst part of missing is? Everytime I try to tell myself to stop missing you, I only miss you more.” “Dagaske Baby idan na rasa ka na tabbatar mutuwa zanyi” Kwance yake a kan gadon lafiyayyen dakin Suite din shi tun da safe yayinda yake karanta cikin saqonnin da Zehra ta aiko mishi lokacin da yayi tafiya zuwa Maiduguri wata daya da ya wuce. A yanzu kuwa messages dinnan sun zama mishi kamar karatu wanda idan har ya karanta yakan ji dan sanyi a cikin zuciyar shi. Ji nayi yace “I just pray you are okay My Angel, I am so sorry for what I did to you” Bai ankara ba ya ji wayar shi tana ringing. Ko da ya duba gani nayi ya runtse idanuwan shi sannan yace “Oh my God, na manta” Bayan ya amsa ne na ji yace “kiyi haquri gani nan zuwa amma fa yau baza mu dade ba because I am not feeling okay” Can yayi shiru sai kuma yace “wallahi I am trying to forget her but I just can’t, she is just like an in-built Memory in my brain that can never be erased but please bear with me, I will close the chapter insha Allah” Shiru yayi yana sauraron ta sannan kuma yace “Yes dear, I’ve had my breakfast” Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude sannan yace “okay I lied… ban ci ba. Zan ci kafin in fito Insha Allah” Girgiza kai yayi sannan yace “toh shikenan zan zo in ci a wurin ki, Happy?? Ya dan yi shiru yana sauraronta sannan yace “bari inyi wanka in fito” Ni kuwa nace who is SHE???🤔2 ♤♤♤♤♤♤♤ ♤♤♤♤♤♤♤ FLASHBACK… NATIONAL HOSPITAL ABUJA A lokacin da Mustapha ya bar gidan su Zehra asibiti ya tafi straight. Ko da ya isa kuwa ya tarar da su tsatsaye a waiting room din yayinda hankulan su suke a matuqar tashe. Ya tarar da su Fadeela har sun iso. They had to cut their honeymoon trip short a dalilin jin labarin rashin lafiyar Muhammad. Fadeela da Mummy kuwa kuka kawai suke yi yayinda ake ta basu haquri. Daddy dai had no choice but to tell them cewar ciwon nashi is worse than yadda suke tunani tunda dai sauqi ya qi samuwa gareshi. Hankalin shi a tashe yace “me ke faruwa ne??” Papa ne yace “He had another attack not long ago amma likitocin sun ce they are doing their best” Gani nayi Mustapha ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu a ranshi yace “yanzu yakamata in sanar da su halin da ake ciki, forgive me bro but I have to do this” STORY CONTINUES BELOW Bai ankara ba ya ga likitoci sun fito daga dakin, a cikin su kuwa harda Zain wanda shima hankalin shi yake a tashe. Dr. Hamisu ne yace “gaskiya yakamata a san abinda yake damun shi before it becomes too late….right now we had no choice but to place him on life support…” Muryar Mustapha suka ji yace “nasan abinda yake damun shi” Gaba daya suka juyo suna kallon shi cike da tsananin mamaki. Dr Hamisu ne ya kalli daddy yace “I will be in my office Alhaji” Daga nan likitocin suka basu wuri yayinda su Daddy suka juyo suna sauraron abinda Mustapha zai ce. “ba wani abu yake damun Moha ba banda soyayyar Zehra…” Gaba dayan su suka ce “what????” Yayinda suke ta zabga salati. Mummy wadda take cike da tsananin confusion tace “toh ya akayi haka?? Wannan wane irin abu ne?? bai san cewar budurwar ka bace??” Fadeela wadda take kuka tace “Ya Musty dama baka fadi mishi maganar Zehra ba all this while?? Why??” Girgiza kai yayi yace “I really don’t know why Dee, guess its because this is how its meant to be ne shiyasa” Da sauri tace “ban gane how it’s meant to be ba… what are you talking about Ya Musty??” Mustapha wanda hawaye ke gangarowa daga idanuwan shi ya goge sannan ya kalli Papa ya matsa kusa da shi tare da hada hannuwan shi yace “don Allah Papa ina neman alfarma daya a wurin ka, Please ka amince ayi auren Zehra da Muhammad, I really don’t want to lose my brother” Gaba dayan su kallon Mustpaha suke yi cike da mamaki da tausayawa yayinda Papa ya janyo shi ya rungume yace “da kai da Muhammad daya kuke a wurina Mustapha, a bangare na ni kam bani da matsala. As long as hakan zai sa Muhammad ya samu sauqin ciwon zuciyar shi” Da sauri Daddy yace “haba Papa, akan wane dalili zaka ce haka?? Insha Allah Muhammad zai samu sauqi ba sai ya auri Zehra ba. Idan aka yi ma Zehra haka ba’a yi mata adalci ba. babu wanda bai san irin soyayyar da take tsakanin ta da Mustapha ba..” Mustapha ya katse shi tare da fadin “mun riga mun yi maganar da ita Daddy..” Cike da mamaki Fadeela tace “kuma ta amince Ya Musty??” Girgiza kai yayi yace “bata amince ba, but I am hoping she will come around. The most important thing right now is saving his life. Don Allah ku taimaka ku bashi abinda zuciyar shi take so” Anty wadda ta jinjina zancen ce tace “A gaskiya ban ji dadin wannan al’amarin ba amma kuma Mustapha is right, lets think about what Muhammad is going through right now. Zehra kuma insha Allah da lallashi zamu samu kan ta” Mummy wadda take kallon yaron nata cike da tsananin damuwa tace “what about you? Can you deal with this??” Yace “I will be fine Insha Allah Mummy. Alfarma daya nake nema a wurinku, Don Allah kar ku sanar da Muhammad cewar ni ne. Idan ya ji labarin cewar nayi giving dinta up for him zai yi fushi da ni sossai because a yanzu haka dukda bai san ni bane yace ya gwammace ya mutu da ya raba Zehra da masoyin ta and ofcourse I can’t let that happen” Sossai wannan al’amarin ya taba zuciyoyin su amma kuma it is the best decision to make a halin da ake ciki. Zain wanda tunda aka fara Magana bai ce komai ba ne ya qarasa wurin Mustapha ya rungume shi tare da fadin “hey are you sure you will be okay?” Yace “I am hoping so, I think I am going to need your help” Zain yace “anything” Fadeela kuwa cike da tsananin damuwa tana kuka ta kalli Anty tace “Anty mu je gida mu dubo Zee, wallahi nasan ba daidai take ba after receiving this news” STORY CONTINUES BELOW ♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE Khadeeja ce ta sauko qasa sanye cikin kayan baccin ta. Da alama bata dade da tashi daga bacci ba. Ganin Zehra tayi kwance a qasan falon. Kusan awa biyu kenan da Mustapha ya bar gidan. Da sauri ta qarasa wurinta ta dan taba ta. Zaraf ta miqe kamar wadda aka yi ma shocking yayinda tace “Deejah ina waya ta?? Khadeeja dai ta cika da tsananin mamaki ganin yadda ta ga Zehra a birkice kamar sabuwar mahaukaciya. Ko kafin khadeeja tayi Magana kuwa tuni Zehra ta ruga sama a guje ta nufi dakinta yayinda ta bi bayan ta. Wayarta take ta nema bata gani ba. Gani nayi tana ta janye abubuwa a dakin yayinda take ta neman wayar. Ban ankara ba na ga ta fara wurgi da abubuwa. Gaban Vanity table ta nufa ta sa hannu ta ture duka kayan da suke bisa yayinda duk suka waste a qasa… Gaba daya turaruka duk suka fashe a kan tiles. A daidai lokacin ne khadeeja ta shigo ta tarar da barnar da tayi yayinda ta ji tana fadin “wallahi baka isa ba, I swear ka fi sona a kan shi kuma bazan auri kowa ba banda kai..” Khadeeja wadda ta qaraso wurinta ce na ga tayi saurin kaucewa a dalilin ganin Zehra ta daga remote na Tv din dakin ta jefa. Ita dai Khadeeja fashewar Vanity Mirror kawai ta ji yayinda ta ga Zehra ta ruga a guje ta fita tana ta surutai. Khadeeja wadda ta fara kuka ce ta bi bayan ta tana fadin “don Allah Anty Zee ki tsaya, me ke faruwa ne??” Zehra dai ta sauko daga steps kenan tayi karo da Fadeela wadanda shigowar su kenan suna shirin hawa saman. Fadeela ce ta rungume ta yayinda take neman qwacewa tana kuka tace “Dee wallahi Baby yana sona, I need to go talk to him, he cant just runaway and leave me like this. Ni yanzu ya yake so inyi da sonshi da yake yawo a jinin jikina??” Fadeela wadda take kuka itama tace “Zee please listen to me, calm down..” Zehra tayi ma Fadeela wani irin kallo tace “calm down?? Ta ya zanyi calming down when I am about to lose the only precious thing I have a duk fadin duniyan nan” Gani nayi tana share hawayen ta yayinda ta riqo hannuwan Fadeela tace “Dee please talk to him, he is your brother. kin sani sarai idan ban auri Baby ba rayuwa ta tana cikin matsala” Ta koma wurin Anty wadda take kallonta cike da tausayawa tace “Anty please help me, Nephew dinki ne shi kuma I am sure he will listen to you” Zain ne da Papa suka shigo gidan suka tarar da su tsaye cirko-cirko suna sauraron ta yayinda Fadeela da Khadeeja suke ta kuka. Ganin Papa ne ta ruga a guje wurin shi ta rungume shi. Cikin kuka tace “Papa don Allah ku roqe shi ya aure ni ko baya sona, wallahi ko yanka ni zai dinga yi a gidan shi na amince, bazan taba iya rayuwa babu shi ba” Papa wanda yake rungume da ita ne yace “sssshhhhh my Baby ya isa haka, daina kuka. Mustapha ya sadaukar da soyayyar shi ga dan uwan shi ba don baya sonki ba sai don ceton rayuwar shi. Rayuwar Muhammad tana cikin garari. A matsayin ki ta musulma yakamata ki yi Imani da qaddara Alkhairi ko sharri. Idan Allah ya qaddara Mustapha ba mijin ki bane babu yadda muka iya. So nake yi kiyi tawakkali ki rungumi dukkan qaddarar da ta zo miki a rayuwa. A kullum ki kasance mai addu’ar Allah ya zaba miki mafi alkhairi a rayuwa…” STORY CONTINUES BELOW A yadda Zehra tayi shiru tana sauraron Papa kuwa zaka rantse ta haqura domin kuwa a yanzu ma hatta kukan ta daina.3 Ya cigaba da fadin “a matsayina na mahaifin ki na zaba miki Muhammad a matsayin miji kuma ina roqon ki kiyi haquri ki zauna da shi.. Insha Allah..” Gani nayi ta janye daga jikin Papa yayinda ta dafe kanta wanda yake juyawa. Wani jiri ne ya debeta ta zube qasa wanda kuwa daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba. Gaba dayan su suka yi kanta da sauri yayinda Zain yayi saurin daukar ta ya nufi dakin ta da ita. ♤♤♤♤♤♤♤ Tuni Zain yayi setting din Zehra up yayinda aka sa mata drip. Ya so ya kai ta asibiti amma Papa ya hana, a cewar shi idan an kai ta asibiti zata iya langwabe musu. Tuni qawarta Hidaya ta zo. Ko da Fadeela ta bata labarin abinda yake faruwa tayi mamaki sossai. Labarin yayi mata kamar tatsuniya yayinda ta tausaya ma qawar ta sossai. Zehra kuwa bata farfado ba sai da yamma. A lokacin kuwa Fadeela, Hidaya, Khadeeja da Anty ne zaune a dakin suna ta hirar yadda rayuwa ta canza ma masoyan lokaci guda. Gani suka yi ta zabura tare da tashi zaune tace “Ina Baby yake??” ta kalli Fadeela tace “where is my phone Dee?” Daga nan sai gani suka yi ta sa hannu zata zare drip din hannun ta wanda kuwa Fadeela tayi saurin riqe hannun ta tace “hey Zee stop it, wayar ki kike so zan baki but you need to relax” Khadeeja ta miqo ma Fadeela wayar yayinda ta cigaba da fadin “Baby kike so ki kira ko? Fine, you can call him but idan har bai amsa ba kiyi haquri zuwa anjima sai ki qara kira” Zehra wadda ta karbi wayar kuwa jikinta yana rawa tayi dialling Number din Mustapha. Har ta gama ringing bai amsa ba. Gani nayi hawaye sun fara gangarowa a fuskar ta yayinda ta sake dialling. Wannan karon kuwa kashewa yayi. Dago kai tayi tana kallon Fadeela tana kuka tace “Dee na shiga uku a duniyan nan, Yau Baby ne yake kashe mun waya??” Gani suka yi ta jefar da wayar yayinda ta daga hannuwan ta sama tana kuka tace “Ya Allah please take my life already, I don’t want to live anymore..” Anty ce tayi saurin rungume ta tare da rufe mata baki tace “me kike fadi ne haka Zee, common stop this nonsense, Yanzu yau idan Mustapha faduwa yayi ya mutu shikenan bazaki cigaba da rayuwa ba?? please stop it” ************ Haka dai Zehra ta birkice musu gaba daya. Musamman Zain ya dauko Nurse don ta dinga duba ta domin kuwa idan har tana a farke fincike drip din hannun ta take yi. Duk ta bi ta ji ma kanta ciwo. Sossai ake zuba mata magungunan bacci a cikin drip din amma kuma wani ikon Allah bata wani yin baccin. Da alama damuwar da take ciki ta fi qarfin magungunan baccin. Cikin ‘yan kwanaki duk ta bi ta rame ta lalace. Abinci ma bata ci, Kullum sai anyi drama da ita sannan take ci. Sossai hankalin su Anty kullum a tashe yake. Su Papa kuwa tuni sun sa ranar bikin Muhammad da Zehra wanda kuwa duka duka juma’ar da zata zagayo ne za’a yi.4 *********** Aikuwa ranar juma’a aka daura auren Muhammad Omar Tafida da Zehra Abu-Yazeed akan sadaki naira dubu dari.4 Idan ka ga Mustapha a ranar bikin kuwa zaka rantse bayada wata damuwa domin kuwa abu daya da ya iya shine masking damuwar shi. Illa iyaka dai ya rame sossai. STORY CONTINUES BELOW A ranar da aka daura auren kuwa gidan shi na Barrack ya wuce domin kuwa sossai yake cikin tashin hankali. A wannan ranar ya tabbatar cewar yayi losing dinta for good, ya tabbatar cewar shi da Zehra kuma sai dai a lahira domin kuwa ta riga ta zama matar yayan shi.+ A wannan ranar Mustapha broke down completely. Wani mugun Zazzabi ya saukar mishi. Dukda baya son anything Hospital most especially allura haka ya kira Zain akan ya zo ya duba shi because he needs to get better and leave the country the soonest. A tunaninshi kuwa zaman shi a Nigera will only suffocate him so yayi deciding ya tafi Italy din dukda kuwa ba lokacin yakamata yayi tafiyar ba. Wasa wasa dai sai da Zain yayi mishi qarin ruwa har Leda biyar. Ganin dai baya son Allura ne ya bashi magunguna yayinda yayi mishi wasu alluran a cikin drip din. Cikin kwana biyu kuwa ya dan warware. Sossai Zain ya tausaya ma masoyan uku. All three of them are in pain. He just couldn’t believe cewar his sister is stuck in this kind of situation. Abinda dai ya sani shine everything happens as per Allah’s wish kuma Allah yasa hakan da ya faru shine abinda ya fi zama alkhairi a garesu baki daya. Nikuwa nace Ameen… ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Mustapha dai ko da ya dan ji sauqi gida ya nufa ya fara tattara kayan shi. Yana cikin kwashe kayan nashi kuwa ya nufi drawer din Vanity table dinshi ya bude. Gani nayi ya kwaso wasu turaruka masu yawa ya zuba a jaka. Har ya sa hannu zai rufe jakar ne na ga ya dan tsaya tare da dago wani turare. Mamaki yayi sossai na yadda akayi turaren ya shigo dakin shi domin kuwa turaren ma na mata ne. Budewa yayi yayinda ya dan fesa, aikuwa yana shaqar qamshin turaren ya lumshe idanuwa. Qamshin turaren Zehra ne. Da sauri na ga ya bude sauran yayinda ya dinga fesa su yana shaqar qamshin. Wadannan turarukan kuwa wadanda Zehra ta siyo ne ta ajiye mishi tun lokacin da zai dawo daga Russia. a wannan lokacin da bata taba sanin zai zama masoyin ta ba… Hada su yayi wuri daya ya zuba cikin akwatin shi yayinda yace “its definitely something I can hold on to” Ko da ya koma wurin drawer din ya bude dayar sai ya ga sketch din zanen idanuwan da ya dade yana nema wanda ya samu amma kuma ya rasa. Da sauri ya ninke sketch din ya sa a akwatin shi. Bayan ya gama hada kayan shi ne ya wuce asibiti don yin bankwana da Muhammad wanda yake fatan ya farka kafin ya tafi. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL, ABUJA Zaune yake a gefen shi yayinda yake ta kallon shi cike da tausayawa. Muhammad dai har yanzu yana numfashi ne da taimakon life support machine din da aka yi connecting dinshi da shi. Mummy da Fadeela dai sunyi kuka har sun gaji. Fadeela kuwa kamar mahaukaciya, ta ma rasa inda zata tsaya. minti kadan sai ta nufi asibiti duba Jikin Muhammad, minti kadan kuma ta dawo wurin qawarta. Minti kadan kuma ta kira Mustapha don jin halin da yake ciki. Dayake Mustaphan ya gargadi Zain akan kar ya fadi musu rashin lafiyar da yayi babu wanda ya san cewar ya kwanta ciwo har ya sha ruwa leda biyar. Abinda ya fi damun Mummy shine Muhammad ya qi ya tashi balle a sanar da shi an magance mishi matsalar shi. Yanzu haka Mustapha ya lallabata ta wuce gida don ta huta. Shi kuwa Daddy a dalilin aikin shi sai ya zama free yake zuwa. Mustapha wanda duk ya bi ya rame cikin ‘yan kwanakin kuwa gani nayi ya shafa kanshi tare da riqe hannun shi yace “I will be forever grateful for everything you have done for me brother” Ya matse hannun shi a cikin nashi yace “please wake up I have good news for you” Tashi yayi ya zauna kan gadon sannan ya duqo tare da kai bakin shi saitin kunne shi yace “guess what?? You are officially a married man. An daura maka aure da Zehra..” Ji yayi Muhammad din ya matse hannun shi yayinda Mustapha yayi saurin kallon fuskar shi. Gani yayi ya bude idanuwan shi a gajiye yayinda yake nema yayi Magana. Ganin ya farfado ne Mustapha ya danna wata na’ura yayinda Likitoci suka shigo da sauri. Mustapha ne ya tashi daga kan gadon amma kuma Muhammad wanda yake riqe da hannun shi ya qi saki. Dr Hamisu yayi disconnecting Machine din yayinda suka cigaba da dudduba shi. Mustapha wanda yake tsaye yana kallon yadda yayan shi ya lalace kuwa ya tausaya mishi sossai sannan ya tabbatar decision din da yayi taking was the right one. is it??🤔35 Dr. Hamisu ne yace “Yakamata a bar shi ya dan huta..” A gajiye Muhammad yace “please I want to speak with my brother..” Dr Hamisu ya girgiza kai tare da fadin “its okay, but don’t stress yourself” Bayan likitocin sun fita ne Muhammad wanda yake kallon Mustapha muryar shi qasa qasa yace “hey.. me na ji kana fadi?? Why did you break the promise you made to me?? Me zai sa ku raba ta da masoyin ta? wannan ai rashin adalci ne. You should have let me deal with this, I am sure I will overcome this illness somehow…” Mustapha ne ya katse shi tare da fadin “I am sorry brother… Please forgive me” Ya riqo hannun shi ya cigaba da fadin “kar ka damu, munyi magana da saurayin nata kuma ya fahimci komai, infact he was even here yesterday to check on you” Muhammad wanda yake girgiza kai yace “yanzu kana nufin itama ta amince??” Mustapha ya dan yi murmushi wadda ta fi kama da a kira ta yaqe yace “She will get use to the idea bro, lafiyar ka is more important right now. Ka san mata suna da saurin yin sanyi, she will come around” Shi kam Muhammad tunda Mustapha ya fara yi mishi wannan maganar gaba daya sauraron shi kawai yake yi amma sam bai amince ba. A ran shi ne yace “Something is not right… Even if this will cost me my life I am going to make sure she gets what she wants… Idan har bata son zama da ni dole ne in sake ta. I will surely set her free…” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *