ZEHRA CHAPTER 11

ZEHRA CHAPTER 11

It’s never nice to lose someone close to you; unfortunately, life goes on, and we have to make peace with it and move on” + ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Allahu Akbar!!! A wannan safiyar hankula sun tashi, Zuciyoyi sunyi sanyi yayinda suke ta juyayin rashin Muhammad. Tabbas duniya wuri ne na wucewa ba na wanzuwa ba, gidan wucewa ne zuwa gidan tabbatuwa sannan babu wani wanda ya isa ya qi tafiya. Babu shakka mutuwa riga ce wadda ba ta fita, ta ma fi qarfin a kira ta da riga domin kuwa fatar jiki ce da ba a iya yage ta a jefar. Kowane mutum yana da qarshe mai zaqi ko mai daci. Mutuwa ta tafi da Muhammad ta bar mu da juyayi. Gaba dayan su tun suna kuka da hawaye har hawayen ya qafe. Wuraren qarfe bakwai na safe aka shirya Muhammad aka yi mishi sallah. Mustapha kuwa har a wannan lokacin bai yi kuka ba, da alama he is still in shock. An kira Mummy, Anty da Fadeela sun je sunyi mishi addu’a wanda kuwa sai riqe su aka yi aka fitar da su domin kuwa Fadeela ma suma tayi yayinda qafafuwan Mummy suka kasa daukar ta. Daddy, Papa, Zain da abokanen shi suma sunyi mishi nasu addu’o’in. A lokacin da Mustapha ya fara yi mishi addu’o’i kuwa sossai jikin mutane yayi sanyi, daga jin yadda yake karanto addu’o’in kuwa ka san akwai shaquwa mai tsanani a tsakanin su. Yawanci mutane sai da suka zubar da hawaye domin kuwa sun tausaya matuqa. Har su Papa sai da suka zubar da hawaye because it was really an emotional scene. Haka aka dauki Muhammad aka kai shi gidan shi na gaskiya. Mustapha dai ganin kowa ya juya yayinda aka bar Muhammad a cikin rami sai kan shi yayi mishi wani mugun nauyi yayinda ya kasa daga qafar shi. Basu ankara ba suka gan shi ya zame ya fadi sumamme a nan maqabartar. Aikuwa nan da nan aka dauko shi aka yi aisbiti da shi. Mutuwar Muhammad ta girgiza su. Duk wanda ka gani qarfin hali kawai yake yi amma sossai tafiyar shi tayi affecting rayuwar su. Fadeela ma hatta dan jaririn ta sai da ya san akwai matsala domin kuwa sai an sa ta a gaba take shayar da shi. gaba daya hankalinta baya tare da ita.2 Mummy kuwa addu’o’in da ta dinga yi su suka dinga sanyaya mata zuciya amma dukda haka tana zaune zaka ga hawaye suna bin fuskar ta. Mustapha dai sai da aka yi mishi qarin ruwa. Ko da ya dawo hayyacin shi kuwa kuka ya dinga yi, da alama sai a wannan lokacin ne ya tabbatar lallai Muhammad ya tafi. Zehra kuwa duk ta bi ta jigata, jaririyar cikin ta ma ta sha wahala. A lokacin da ta farfado ne Dr. Haleema ta bada shawarar ayi mata C-section a ciro jaririyar don kar a samu matsala. Aikuwa a ranar da Muhammad ya cika kwana biyu da rasuwa aka yi ma Zehra C-section aka ciro ‘yar jaririyar ta kyakyawa fara sol. Anyi mata huduba da sunan mahaifiyar Zehra da Muhammad wato Aesha (Aisha) amma aka rufe sunan da Yasmeen. Wannan yarinya dai ta ga soyayya domin kuwa gabadaya son da ake yi ma Muhammad ne ya dawo kanta. Sai da Zehra tayi sati biyu a asibiti sannan aka sallame su. Zehra dai a kullum tana cikin kuka, lallashinta ake yi amma a banza. A duk lokacin da ta kalli Yasmeen kuwa Muhammad ne yake dawo mata. Sossai take wishing yana nan, she was willing to change… to reciprocate his love amma inaaa… hakan ba zai yiwu ba domin kuwa ya riga yayi nisa. STORY CONTINUES BELOW Wani lokacin haka zasu ji tana ta hira da Yasmeen din inda take bata labarin Babanta. Wani lokaci kuwa ta sa ta a gaba tayi ta rusa kuka tana fadin how sorry she is that she wasn’t able to reciprocate his love. Hankulan su Papa ya tashi ganin yadda duk ta bi ta lalace. Sossai aka duqufa wurin addu’o’i akanta tare da sanya ta a gaba ana yi mata nasiha. Cikin ikon Allah kuwa suka yi tasiri akanta wanda kuwa cikin dan lokaci ta fara samun natsuwa amma dukda hakan a kullum zaka ganta tayi shiru tana tunani. Mustapha ma akan dole ya rungumi qaddara. A koda yaushe yana dakin shi yana tuno rayuwar su tare da abubuwan da yayi mishi wanda he will forever be grateful. Addu’a kuwa Muhammad ya sha ta.. Muna yi mishi kyakyawar zato domin kuwa mutum ne na qwarai. Fatan mu Allah ya kyautata tamu qarshen idan ta zo… Ameen!!2 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE A yau wata daya kenan da rasuwar Muhammad. Zaune yake a falon Papa riqe da Yasmeen yayinda ya qura mata idanuwa yana ta kallonta. Mustapha dai ya qara ramewa akan ramar da yayi. Idan ka kalle shi zaka rantse yayi wata da watanni a kwance yana jinya. Sossai yake son Yasmeen, da alama itama tana son shi domin kuwa ko kuka take yi idan dai aka kawo mishi ita zaka ga tayi shiru tana ta kallon shi. Tunda aka haife ta a kullum sai ya zo gidan ya ganta. Wani ikon Allah kuwa rabon shi da mahaifiyarta tun ranar da Muhammad ya rasu a lokacin da ta suma a jikin shi. Anty wadda take kallon shi ce tace “Mustapha yanzu goben zaka koma Italy din?” Yace “Eh Anty, I have missed a lot kuma ana ta yi mun waya” Papa yace “ai gwara ka koma kar suyi delaying dinka, yanzu saura shekara uku kenan” Yace “Insha Allah papa” Anty ce tace “shekara uku da tsawo Mustapha” Papa yace “ai kamar yau da gobe ne zaki ga ya gama ya dawo” Mustapha wanda yake wasa da hannun Yasmeen ne yace “Uhm Papa dama ina so in tuna maka maganar da muka yi last week…” Murmushi Papa yayi yace “kar ka samu damuwa Mustapha, Alqawarin da nayi maka yana nan. Allah ya dawo da kai lafiya” hmmmm🤔🤔 Anty tace “ameen” yayinda yace “nagode sossai Papa” Haka ya cigaba da wasa da Yasmeen yayinda suka dinga kallon shi cike da tausayawa. Sun sani sarai soyayyar da yake yi ma iyayen ta shine ya dawo kanta. Gani suka yi ya kalli agogo sannan yace “Okay Princess, I have to go now. I will miss you a lot” Yayi mata kiss a goshi da kumatu sannan ya miqe ya nufi wurin Anty ya miqa mata ita. Papa yana murmushi yace “ai itama zata yi missing dinka, da alama tana son ka Mustapha” Murmushi yayi yayinda Anty tace “kayi sallama da Zehra ne ko in….” Da sauri yace “a’a Anty ki barta kawai… Na san maybe she is sleeping, My regards to her” Haka suka yi mishi fatan alkhairi sannan ya tafi. ************* Tsaye take a jikin window din dakinta yayinda ta hango shi zai shiga motar shi. Gani nayi ta qura mishi idanuwa har ya shiga motar ya tada. STORY CONTINUES BELOW Ko da ya kai bakin gate gani tayi ya sauke glass ya miqa ma gateman wani abu, da alama dai kudi ne domin kuwa gani tayi gateman din ya duqa har qasa yana godiya. Bayan ya bar gidan ne na ga ta runtse idanuwa yayinda hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan ta. Anty ce ta shigo dakin riqe da Yasmeen yayinda tace “Zee lafiya na gan ki tsaye kina zubar da hawaye?? har yanzu baki daina kukan nan ba??” Da sauri ta goge fuskar ta yayinda ta nufi wurin Anty tace “babu komai Anty” ta karbi Yasmeen daga hannunta. Ajiyar zuciya ta saki a dalilin qamshin turaren Mustapha da ya bugi hancinta. A koda yaushe idan aka dawo da Yasmeen daga wurin shi zaka ji tana qamshin shi. Qamshin da take bala’in so a rayuwarta. Gani nayi ta rungume Yasmeen yayinda ta ji Anty tace “Mustapha yace a gaishe ki, Gobe zai koma Italy idan Allah ya kaimu” Zuciyar ta ce ta buga yayinda wasu hawayen suka fara gangarowa daga idanuwan ta, wannan karon dai bata goge ba sannan bata fasa zubar da su ba. Anty ce ta janyota ta zaunar da ita kan gado ta karbi Yasmeen a hannunta ta kwantar da ita sannan ta janyo ta jikinta ta rungume ta tace “everything will be okay Zee, have faith and Insha Allah komai zai daidaita” Cikin kuka ne Zehra tace “ni yanzu shikenan Anty duk wadanda suke close to me sun tafi sun bar ni kenan?? First it was Momma, then My Baby yanzu Yaaya ma ya tafi…” Anty tace “Ssshhhh, kiyi haquri Zee Allah ya jiqan Momma da Muhammad kuma ya raya abinda suka bari, Mustapha kuma is still alive, he is going away for just three years.. Insha Allah everything will fall into place kin ji??” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Zehra ta fita takaba tun lokacin da ta haihu kamar yadda addinin mu ya tsara. ●●●●●●●●●●● …….To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu, a wannan lokacin karshen Takabarta shine ta sauke abinda take dauke da shi, koda ko ranar da ya rasu ne, Misali ya rasu 7:00 na safe ita kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shikenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani yace yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru(ana karbar gaisuwa ana daurin aure) dalili kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-Talak aya ta 4 ” Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda suke dauke dashi” Hadisin Subai’a Al-aslamiyyah, ” Ita ta kasance tana auran Sa’ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir dan Lu’ayy, yana daga cikin wadanda suka halarci gwabzawar Badar, sai ya rasu ya barta tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi sai ta haihu, a lokacin suna kuwa harda kwalliya tayi, sai Abu-Sanabil Dan Ba’akk yazo wurinta, shi kuma ya fito ne daga gidan Abduddar, sai yace da ita ” Lafiya naga kin cancara ado, ko kina son kiyi aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, har sai kin yi wata hudu da kwana goma. Sai Subai’a tace “Yayinda ya fadi min haka, maraice na yi sai na tattara kayana na je wurin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya bani amsa da cewa ai na kamala Takabata tun lokacin da na haihu, ya bani dama da inyi aure a duk lokacin da na ga dama”. Wannan hadisin Bukhari ya ruwaito shi, hadisi na 4909 da kuma na 5318, haka nan ma Muslim da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa’I, da Ibnu Majaah…. ●●●●●●●●●●●●●● Dukda hakan kuwa bata fita ko ina. A kullum tana nan cikin gida tare da Yasmeen. Gaba daya qadarorin da Muhammad ya mallaka anyi converting dinsu zuwa kudade, wadannan kudade kuwa masu yawan gaske an hada da savings din shi gaba daya an zuba ma Yasmeen da Zehra a banki domin kuwa sune magadan shi. STORY CONTINUES BELOW Haka lokaci ya dinga tafiya wanda kuwa akan dole kowa ya rungumi qaddara ya cigaba da al’amuran shi. A kullum sai Mustapha ya kira Anty a waya ya ji lafiyar Yasmeen. Har sa Anty yake yi ta dauko ta yayi ta kallonta a Video call, hakan kuwa yakan sa Anty dariya. Wani ikon Allah kuwa haka take yin shiru tana sauraron muryar shi kamar wadda take gane abinda yake fadi. Dukda Mustapha baya kusa da Yasmeen sun shaqu sa juna sossai. Daidai da rana daya kuwa bai taba kiran Zehra a waya ba sannan bai taba ce ma Anty ta bata su gaisa ba amma kuma kullum sai yayi tambayar wellbeing dinta sannan yace a gaishe ta. Haka idan yayi waya da Fadeela ma yana tambayar Zehra wanda kuwa a koda yaushe Fadeela takan tambaye shi dalilin da ya sa bazai kira ta direct ba amma sai ya dinga kawo mata wasu silly excuses. Ita dai Fadeela addu’a take yi Allah yasa they end up together domin kuwa ta sani sarai basu daina son juna ba. Shin haka din ne???🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ 2 YEARS LATER….. YEAR 2017 A kwana a tashi babu wuya tuni Zehra ta yaye Yasmeen har an sa ta makaranta. A yanzu haka makarantar su daya da cousin dinta Yazeed wanda suke kira da Ameer. Sossai Yasmeen tayi wayau domin kuwa har Magana idan tana yi ana ganewa. A yanzu kuwa idan Mustapha yana hira da ita a waya sossai yake gane maganar ta. Yasmeen tana bala’in son Mustapha, Abbu take kiran shi wanda kuwa hakan ba qaramin farin ciki yake sanya shi ba. Har yanzu kuwa bai taba neman yin Magana da Zehra ba. A duk lokacin da yake hira da Yasmeen din Zehra tana yawan sauraron hirar tasu wadda yawanci duk shirme ne. Ita kam har mamaki take yi yadda Mustapha yake biye ma Yasmeen din suyi ta buga shirme, bata taba tunanin he is so much into kids har haka ba. A yanzu haka Zehra ta canza gaba daya. Ta qara kyau sossai, ta qara haske, ta yi ‘yar qiba sannan ta qara zama babbar yarinya. Bayan ta yaye Yasmeen musamman Anty ta gayyato shaharriyar mai gyaran jikin nan ta qasar Egypt mai suna Layla Hayat. Musamman aka yi Mata masauki a gidan yayinda ta gyara ta har kusan tsawon wata biyu. Zehra dai ta sha wuya amma fa an ga result. Gaba daya jikinta ya canza sai qyalli take yi. Jikinta tamkar auduga saboda laushi. Boobs dinta sun cika sun koma tamkar ba na wadda ta gama shayarwa ba. Idan ka ganta zaka rantse bata taba yin aure ba ma balle kace ta haihu. Duk inda ta zauna kuwa babu abinda kake ji sai qamshi. Wasu kalolin turaruka da mayuka Layla ta hada ta da su wanda kuwa tayi alqawarin zata dinga turo mata su daga Egypt akai-akai. Layla Hayat dai ta kwashi kudade masu yawan gaske. Babu qarya aikin ta yayi kyau. Ta buqaci a sanar da ita duk lokacin da Zehra zata yi aure domin kuwa akwai shiri na musamman da zata yi mata. hmmmm… Zehra dai a halin da ake ciki yanzu maza dayawa suke bibiyar ta suna neman ta da aure. Ba samarin ba sannan ba masu auren ba. Ko lokacin da take budurwa bata samu masu bibiyar ta kamar yanzu ba. STORY CONTINUES BELOW Ni kuwa nace a lokacin Musty ya kasa ya tsare🤣 Manyan masu kudin cikin garin Abuja sun matsa mata. Sossai Fadeela da Hidaya suke yi mata tsiya. Lokutta da dama sukan tsokane ta da matar Alhaji mai qaton ciki ko kuma Alhaji dattijo ko kuma Alhaji bagidaje…. Sunaye dai kala-kala. Shin na gaya muku Hidaya tayi aure?? Yeah… tayi aure shekara daya da ya wuce. Ta auri saurayinta wanda suka dade tare mai suna Al-ameen. Al-ameen dai yana aiki ne a NCC na nan cikin garin Abuja. Har yanzu kuwa tana nan a matsayin Manager din catering service din Zehra wanda kuwa suke running dinshi smoothly. ♤♤♤♤♤♤♤ ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE Fadeela ce kwance a kan gadon dakinta riqe da Tab yayinda Yasmeen da Ameer suke hira da shi via Video call kamar kullum. Zehra tana zaune a kan kujerar dakin yayinda take sauraron hirar tasu. Yasmeen ce tace “Abbu ka zo” A dayan bangaren Mustapha wanda yake dariya yace “Zan zo princess, saura kadan in dawo” Fadeela wadda itama take dariya tace “Gaskiya gwara ka dawo mu huta da rigima, ka kuwa san wani lokaci idan ta ga dama sai ta qi cin abinci wai sai kaine zaka zo ka bata sannan fa duk abinda aka yi mata sai tace wai zata fadi ma Abbu…” Yana dariya yace “Allah sarki my Princess, I can’t believe tayi wayau sossai haka” Fadeela wadda ta dan kalli Zehra ce tace “ai Amminta ta biyo, wayau na bala’i” Zehra wadda fuskarta take a murtuke ta danna ma Fadeela harara yayinda suka ji yayi dariya yace “How is she??” Tace “She is fine, ko in bata ku gaisa ne??” Da sauri yace “No, I gotta go” Ya kalli Ameer da Yasmeen yace “okay my dearies bye bye” Gaba dayan su suka dago mishi hannu suka ce “bye bye Abbu” Bayan sunyi sallama ne ta kira mai aikinta ta zo ta kwashe su suka fita daga dakin. Fadeela ta kalli Zehra wadda take ta latsa wayarta tace “Babes wai meyasa baku magana da Ya Musty ne?? kullum fa idan nayi mishi maganar in baki waya ku gaisa sai ya dinga kawo excuses why??” Zehra dai ko kallonta bata yi ba balle ta amsa ta. Fadeela tayi murmushi tace “Zee I am talking to you” Zehra ta ajiye wayarta ta kalle ta sannan tace “what Dee?? Me kike so in ce??” Fadeela tace “just anything, why are you both avoiding eachother??” Tace “I really don’t know and I don’t care” Fadeela tace “hmmmm, toh wai in tambaye ki, do you still love him??” Zuciyar Zehra ce ta buga yayinda tayi saurin daukar wayarta tana latsawa. Fadeela tana murmushi tace “I know you still do kuma I am sure he does too, let’s assume yanzu ya dawo yace kuyi aure will you marry him??” Ranta a bace tace “what the hell Dee, bazan taba auren Baby ba… I have already lost him and I can’t go back to him… Infact I DON’T LOVE HIM ANYMORE”3 Cike da mamaki Fadeela tace “…… and you still call him BABY??” Zehra wadda ta rude kuwa gani nayi ta fashe da kuka yayinda tace “Dee please stop it.. wallahi idan kika matsa mun zan bar miki gidan ki kuma bazan qara zuwa ba… nace miki bana son shi kuma bazan aure shi ba. ki qyale ni mana” Fadeela ta sauka daga kan gadon da sauri ta koma wurinta tayi hugging dinta tare da fadin “Please forgive me… I am sorry” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ YEAR 2018 ABU-YAZEED RESIDENCE A guje ta rugo cikin Falon Papa da gashin kanta buzu buzu yayinda take ta ihu tana fadin “Abbu ka zo, Ammi zata kama ni…” Papa da Anty wadanda suka saba da wannan abu kuwa sai dariya suke yi. Zehra wadda ta biyo Yasmeen a guje sai qoqarin kamo ta take yi amma yarinyar ta qi. Da ta kula Zehra ta kusa cafko ta ne ta fada jikin Papa tana fadin “Papa please hide me” Papa ya rungume jikar tashi yace “Haba Yasmeen, me zai sa kullum sai kin ba Ammin ki wahala idan zata yi miki kitso? Kina so idan Abbu ya dawo ya zane ki da bulala??” Da sauri tace “No Papa” Yayi murmushi yace “toh be a good girl ki je Ammi tayi miki kitso, kin ga gobe Monday akwai school” Juyawa tayi ta kalli Zehra wadda take tsaye tana kallon su tace “Ammi bana son mai zafi” Zehra tace “ba mai zafi zan yi miki ba, I promise” da qyar dai ta amince suka koma daki don tayi mata kitson. Bayan sun fita daga falon ne Papa yace “Allah sarki, kamar jiya jiya aka haifi Yasmeen. Allah ya jiqan mahaifin ta” Anty tace “ameen” Suna cikin hira ne Fadeela ta shigo gidan. A guje Ameer ya ruga wurin Papa yana fadin “Papaaaa” Fadeela kuwa ta qarasa wurin su ta duqa har qasa ta gaishe su sannan ta wuce sashen Zehra. Zaune take bisa kan gado yayinda Yasmeen take kwance a bisa cinyarta tana yi mata kitso. Fadeela ce ta shigo dakin yayinda Yasmeen tace “Mamy oyoyo, Ina Ameer??” Tana murmushi ta qarasa wurin su tace “yana wurin Papa, yanzu zaki gan shi, how are you??” tace “fine” Ta kalli Zehra tace “su Gadara manya… ace wai sai an hau gado sannan za’a yi kitso. Yasmeen hoo” Zehra wadda take murmushi tace “ai tunda ma ta amince ayi mata ta kyauta, kin ga guje gujen da muka yi kuwa??” Fadeela tana ta dariya. Ai kuwa da qyar aka gama kitson domin kuwa ita Yasmeen din wai akan dole sai ana yi tana wasa da Ameer.. Fadeela ce ta riqe Ameer din har aka gama mata sannan suka kora su. Suna cikin hira ne wayar Fadeela tayi ringing. Ko da ta amsa ji nayi tace “is it ready?? Okay so we meet in thirty minutes at the house?? Alright then bye” Zehra wadda take kallon ta ne tace “ke da waye Dee?” Fadeela tayi murmushi tace “hmmm, gadon master bedroom din Ya Musty ne aka kawo, wanda aka kawo da farko fa sai bayan anyi fixing… yana ganin hoton yace su je su kwashe wai bai yi ba. Kin san Ya Musty komai nashi daban, kuma fa I swear Zee gadon ya masifar haduwa amma wai yace bai yi ba toh yanzu shine suka kawo wani” Zehra dai shiru tayi bata ce komai ba. Ji tayi Fadeela tace “yauwa Zee, ki shirya mu je ki ga gidan don nasan baki taba zuwa ba. Mehn, kin ga gidan kuwa?? yadda kika san an dauko shi daga turai. Na tabbatar ba qaramin fortune ya kashe ya gina wannan gidan ba, the interior décor is to die for I tell you…” Kai tsaye Zehra tace “bazan je ba Dee, Ina so in huta for the rest of today.. kin ga gobe Monday” Fadeela ta Harare ta tace “waye baya so ya huta, ki tuna fa ke CEO ce. Idan kin ga dama you can even choose not to go. Mu kuma ma’aikatan gwamnati mu ce me?? Ai baki isa ba sai kin raka ni. Dama kin tashi kin shirya hajiya” STORY CONTINUES BELOW Aikuwa duk nacin Fadeela sam Zehra ta qi. Anty da Khadeeja wadanda suka shigo dakin suka ji Fadeela tana ta masifa suma sunyi da ita amma ta qi. Khadeeja ce tace “ni kam zan bi ki in gani” Fadeela tace “yauwa Deeja je ki shirya mu je” Anty kuwa cewa tayi “mu dai sai zamu je kai amarya sannan…” Jin hakan kuwa sai da gaban Zehra yayi mummunar faduwa wanda gaba dayan su sun kula.2 Fadeela ce tace “aikuwa wannan amaryar ba qaramin morewa zata yi ba, gida kamar aljannar duniya, abin ba’a cewa komai” Gani suka yi Zehra ta miqe ta shige bathroom yayinda suka kalli juna sukayi murmushi. ************* Haka suka je suka dawo yayinda Khadeeja ta dinga basu labarin tsarin gidan da yadda yayi bala’in kyau. Ta kalli Zehra tace “Anty Zee, kin tuna gidan nan da yake birge mu wanda kullum idan zamu wuce sai munyi Magana akan shi?? wallahi shine. Gidan ma babu nisa da nan gidan” Zehra kuwa tayi mamaki matuqa domin kuwa a yadda tsarin wannan gidan yake sun sa ran na wani babban dan siyasa ne domin kuwa ba qaramar dukiya aka narka a ginin ba. Ji tayi Khadeeja tana fadin “hmmm, Idan kuka ga bangon gidan zakuyi tunanin glass ne…. kai amma dai matar Ya Musty fa zata huta” Haka suka dinga kwasar dariya yayinda Fadeela tace “toh ko zaki taya amaryar zaman daki idan anyi auren??” Da sauri Khadeeja tace “Dagaske idan dai Ya Musty ya amince zan taya ta…aikuwa idan na shiga gidan bazan sake fitowa ba” Aikuwa sossai suke dariya yayinda Zehra ta tashi ta bar falon. Bayan ta fita ne Anty ta kalli Fadeela tace “wai ban tambaye ki ba, me yake faruwa da qawar taki naga tana ta kumbure kumbure ne??” Fadeela tace “hmmm, ai Anty ni na kasa gane kan Zee. Kamar maganar Ya Musty ne fa bata so” Khadeeja ce tace “Anty Dee I thought she still loves him…” Fadeela tayi saurin fadin “ssssshhhh, kar ki sa ta jiyo ki ta fito tayi exploding mana a nan. tace bata son shi kuma bazata taba auran shi ba when I asked her” Anty ce tace “sai wadannan dattijan masu zuwa wurinta ne take so kenan??” Fadeela da Khadeeja suka fashe da dariya yayinda Fadeela tace “wallahi Anty don ma fa baki gan su ba, a cikin su fa akwai wanda a shekaru ya girmi Daddy da Papa” Haka dai suka dinga kwasar dariya. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ One week later… A cikin wannan satin ne wani babban abin farin ciki ya faru inda shugaban qasa yayi appointing Daddy a matsayin Chief Justice na qasa. Hakan ya faru ne a sanadiyar bincike da ake yi akan wanda yake riqe da muqamin, a dalilin trial din da ake yi akanshi ne aka sauke shi. Asali dai National Judicial court sune suka yi nominating Daddy wanda kuwa Shugaban qasa ya bashi appointment din. A yanzu haka Daddy zai cigaba da zama a wannan kujerar har sai ya kai shekaru saba’in ko kuma idan mutuwa ta dauke shi. Sossai mutane sunyi murna da wannan zabin domin kuwa Daddy mutum ne mai riqe gaskiya da amana a aikin nashi. Ana matuqar alfahari da shi. STORY CONTINUES BELOW Sossai gidan Daddy yake ta cika da mutane kala-kala ana ta taya shi murna. A dalilin wannan ne aka shirya Dinner gagaruma wadda za’a yi ranar sati don taya shi murna formally. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ BLUEVELVET MARQUEE EVENT CENTRE ABUJA Wurin ya cika da manyan baqi, a ciki kuwa harda ‘yan siyasa da dama. Kowa ka gani yayi shiga ta alfarma. Wurin da su Daddy suke zaune kuwa cike yake da mutane wadanda suke ta kai gaisuwa tare da taya shi murna. Fadeela dai tana zaune tare da qawayen ta su Yusra yayinda suke ta hira harda Hidaya. Har aka fara kuwa Zehra bata iso ba domin kuwa bata bar Catering service dinta ba sai da ta tabbatar komai is in order. Bayan ta baro kuwa straight gida ta wuce don ta shirya. An bude taron da addu’a wanda kuwa Papa shine ya gabatar sannan ya gabatar da tarihin aminin nashi tun suna yara da dukkanin fadi tashin da suka yi har zuwa yau. Daga nan ne aka dinga Kiran abokanen aikin shi wadanda suka yi aiki tare don su fadi albarkacin bakin su. A wannan lokacin ne Zehra ta shigo hall din. Tana shigowa kuwa kallo ya dawo kanta. Zehra dai saboda bata so ta janyo attention shiyasa tayi shiga very simple domin kuwa atamfa ta sanya simple style sannan ta yafa gyalen ta. Ko make up bata yi ba saboda a yanzu kuwa tsoron yin shi take yi, ko meyasa oho… Da alama dai bata tsira ba domin kuwa almost all eyes were on her, musamman mazan da suke wurin. Matan yawancin su kuwa sai tsine mata suke yi akan ta dauke ma mazajen su hankali. Tana qarasawa table din su Fadeela ne Yusra tace “big madam, kina hada Go-slow fa… anya yau bazaki ja rikici a gidajen aure ba kuwa??” Fadeela da sauran qawayen ta sai kwasar dariya suke yi yayinda Hauwa tace “Ga wani can ma kamar matar tayi fushi ta tafi abinta” Zehra ta bata rai yayinda tayi watsi da su. Haka aka cigaba da shagali yayinda ma’aikatan Zehra suka dinga serving mutane cikin qwarewa… abin gwanin ban sha’awa. Yanzu dai kusan babu wanda bai san Catering service din Zehra ba a cikin garin Abuja, its like one of the best. Sossai mutane suke yaba abincin, sossai aka dinga kwasar girki mai tsari da dadin gaske. Wayar Zehra ce tayi ringing yayinda ta duba. Gani nayi ta dan bata rai sannan ta tashi. Fadeela ce tace “Alhaji 1 ne ko 2 ko 3??” Zehra ta harare ta yayinda ta dan matsa wani gefen da babu kowa don ta samu privacy. Da ganin yadda take Magana a wayar kuwa ka san lallai ta qosa suyi sallama. Alhaji Mas’ud Galadanci shine ya kira ta a wayar. Wani shaharraren dan kasuwa ne a cikin garin Abuja wanda ya nace ma Zehra akan lallai shi son ta yake. STORY CONTINUES BELOW A yau tun safe yake ta kiran ta amma ta qi amsawa a dalilin she was very busy. Yanzu ma kawai ta amsa ne saboda kiran ya ishe ta sannan ba abun ta kashe wayar ba saboda shi. Tana cikin Magana da shi ne Zuciyarta ta buga a dalilin maganar da ta ji MC yana yi. “I have just been informed that the son of the Celebrant just arrived, in person of Colonel. Mustapha Omar tafida…. The most eligible bachelor at the moment…” Shin na fadi muku cewar Mustapha ya samu promotion zuwa Colonel??? yeah… wata shidda da suka wuce aka yi mishi qarin girma from lieutenant Colonel to Colonel. Zehra wadda jikin ta ya fara rawa gani nayi ta juya tana kallon entrance. Mustapha ne ya shigo hall din sanye cikin wani tsadaden farin yadi Wanda aka yi ma dinkin zamani, Hular da ke kanshi kuwa Zannah Bukar ce mai kyan gaske. sai baza qamshi yake as usual…. Sossai yayi kyau. Abin mamaki tare yake da wata kyakyawar mace mai kyan tsari, fara sol kamar balarabiya wadda suke ta magana suna dariya.6 Wani simple yadi ta sanyo dinkin doguwar riga wanda kuwa dukda simplicity din yadin ka san ya ja kudi. Tana ta qoqarin gyara gyalen da ta yafa yayinda Mustapha yake riqe da hand bag dinta. Zehra wadda jikinta yake ta rawa kuwa gani nayi ta saki wayar da take hannun ta yayinda na ji muryar Alhaji Mas’ud ta cikin wayar yana ta fadin “Hello… Helllo…..” Dafe qirjinta tayi saitin da zuciyar ta take yayinda hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan ta. Ko qyaftawa ta kasa yi yayinda take ta bin su da kallo. Gaba daya hall din kuwa su ake kallo domin kuwa sunyi masifar kyau. Sun dace sossai domin kuwa kyau ne ya hadu da kyau. Amma fa duk kyan da tayi bata kai shi yin kyau ba. Yusra wadda take dafe da qirjinta ji nayi tace “oh Allah, Dee wai ni kam why is your brother so handsome ne?? Kin ga yadda ya qara kyau?? Toh yanzu wannan kuma wacece yake tare da ita?? An shiga uku…” Fadeela wadda ta ga yayan nata da wata wadda bata sani ba tayi mamaki sossai. A ranta ne tace “but he never told me he was seeing somebody… Ya salaam, muna nan muna tunanin he will get back with Zee ashe ya manta da ita?? Oh Ya Musty why??” Sossai jikinta yayi sanyi wanda ma har ta kasa tashi ta je wurin shi. Hidaya ce ta kai bakinta saitin kunnen Fadeela tace “wai dama ashe yana dating wata shine muke tunanin zai dawo ma Zee??” Fadeela tace “wallahi I dont understand this… I am just so confused Hidaya, I can’t believe my eyes” Su Mustapha dai straight wurin su Daddy suka nufa wadanda suka ji dadin ganin shi sossai. Ko da suka qarasa wurin su Miqewa Mummy tayi sannan ta rungume shi cike da murna sannan Daddy ma ya rungume shi. Zehra wadda take ta kallon su gani tayi Mummy ta rungume wadda suka zo tare yayinda ta dan russuna ta gaida Daddy wanda ya amsa cike da fara’a. Mustapha ya koma wurin su Papa suma suka gaisa sannan suka cigaba da gaisawa da sauran abokanen Daddy. Hankalin Zehra bai qarasa tashi ba sai da ta ga Sun nufi wurin Zain wanda bayan sun rungume juna da Mustapha ta ga ya kalli wadda suka zo tare yana yi mata Magana da expression din sanayya a tsakanin su. STORY CONTINUES BELOW Gani tayi sun fashe da dariya yayinda ta koma gefen Zain ta zauna suka fara Magana. Mustapha ya dan duqo yayi mata Magana sannan ya juya ya bar su suna ta hira da Zain. Wato Zain ma ya san ta kenan?? Toh wacece ita??5 Zehra wadda hawaye ke ta gangarowa daga idanuwan ta tana ta gogewa da qyar tayi forcing din kanta ta daina kuka amma fa hankalinta a matuqar tashe yake. Mustapha wanda ya hango Fadeela ne ya nufi table din da take. Tun kafin ya qaraso ta miqe jiki a sanyaye ta qarasa wurin shi tayi hugging dinshi. Ji nayi yace “Oh Baby Dee, how I missed you guys” ta dan yi murmushi tace “we missed you too Ya Musty” Suka saki juna yayinda tace “shine bayan munyi waya da kai jiya baka fadi mun zaka zo ba?” Yayi murmushi sannan yace “I wanted to surprise you ne” Tana kallon table din da Zain yake zaune tare da friends dinshi ne tace “wai wacece waccan da kuka zo tare?? Don’t tell me itace in-law din tamu?? Plus na ga suna ta hira da Sweetheart, ya san ta ne???” Mustapha wanda na ga yana ta kalle-kalle ne yace “Dee tambayoyin sunyi yawa.., guess you will have to go find out yourself, just go ahead” Daga nan kuwa na ga ya cigaba da kalle-kalle kamar wanda yake neman wani abu. Duk inda ya gifta kuwa idanuwan ‘yan mata na kan shi. Haka ya dinga bin table by table yayinda wasu ma har gaishe shi suka dinga yi ko Allah zai sa ya kalle su. Ni kuwa nace kun ga mutum ya shigo da tsaleliya amma kuma kuna farauta… huh🤨 *********** Tsaye yake nesa da inda take zaune yayinda ya ga tayi tagumi, da ka ganta kasan akwai damuwa a tare da ita. 8 Mustapha dai gani yayi Zehra ta canza mishi gaba daya, ta qara haske sannan ta qara masifar kyau. Direction din inda take kallo ya kalla yayinda ya ga table din su Zain ta sa ma ido, da alama wadda suka zo tare take kallo wanda kuwa a yanzu Fadeela ma tana zaune tare da su yayinda ta ga sun cigaba da hirar tare har tana dariya itama. toh fa… Kusan minti biyar yana nan yana ta kallonta wanda kuwa ko shekara zai yi a haka he wouldn’t mind domin kuwa staring at her beautiful face alone gives him plenty of joy. Mustapha dai ya sani sarai ko za’a shekara dubu dari, matsayin Zehra a cikin zuciyar shi bazai taba canzawa ba. Ajiyar zuciya ya saki sannan ya qarasa wurinta ya tsaya. Zuciyarta ce ta buga a dalilin jin qamshin turaren nan wanda take bala’in so a rayuwar ta. Dago kai tayi da sauri ta kalle shi yayinda tayi freezing gaba daya. Tunda Mustapha ya shigo hall din ta kula ya qara haske yayi kyau amma kuma yanzu da ya matso kusa da ita gani tayi ba kyau kawai yayi ba, yayi masifar kyau ne sannan abin mamaki after like 3 years rabon ta da ganin shi he looks younger.. is it even possible?? Gani nayi ta miqe da sauri yayinda ta ruga a guje wanda kuwa ya bi bayan ta da sauri yana fadin “hey wait..” Zehra dai a guje ta shige ‘Ladies’ ta rufe qofa ta dinga sauke numfashi. Gani nayi ta fashe da kuka yayinda ta ji shi yana fadin “hey I am sorry..” Can kuma ta ji yace “zaki iya fitowa, ni na tafi. ga wayar ki zan ba Dee ta ajiye miki” Daga nan kuwa ta ji alamun tafiya wanda ya tabbatar mata da lallai ya tafi ne. Ji nayi ta qara fashewa da sabon kuka. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE Zaune yake a falon Anty yayinda take tsaye a gefen shi tana ta birkita gashin kanshi da sunan tana yi mishi kitso. Mustapha dai kusan awan shi biyu da zuwa gidan wanda kuwa tunda ya hadu da Yasmeen ta gane shi. Tuni ta maqale mishi yayinda take ta murnar ganin shi. Surutu kuwa ya sha shi wanda kuwa tun yana ganewa har yayi losing track. A yanzu haka nace mishi tayi wai sai tayi mishi kitso kamar yadda Amminta take yi mata. Anty da Khadeeja kuwa sai kwasar dariya suke yi yayinda take ta cukwikuye mishi gashi. Anty ce tace “wai yanzu dagaske sai ka koma ka qarasa watanni biyun da suka rage?” Yana murmushi yace “eh wallahi Anty, akwai examz din da zamu yi wanda daga nan shikenan.. ai na gaji da qasar wallahi” Tace “toh yanzu kwana nawa zaka yi a nan?” yace “maybe zanyi wata daya or more” Khadeeja ce tace “ni kuwa Ya Musty yaushe zaka yi aure ne??” Cike da mamaki ya kalle ta yayinda Anty ta fashe da dariya tace “don’t mind her, gidan ka ta je duk ta bi ta rude wai shine tace zata je ta taya amaryar ka zaman daki” Fashewa da dariya yayi yayinda yace “what?? Ai wallahi Deeja baki isa ba. ranar da amarya ta zata tare ko awa daya bazaku qara a gidan ba zan kore ku gaba daya” Turo baki tayi tace “haba Ya Musty duk girman gidan nan?? wallahi yayi muku girma, ni kam ko sashen guests dinnan a bani ina so” Girgiza kai yayi yana dariya yayinda Anty tace “Allah ya kaimu ranar bikin nan dai, I really can’t wait” Murmushi yayi yace “I can’t wait too Anty”2 Suna nan zaune suna hira ne ta shigo falon sanye cikin wata doguwar rigar atamfa dinkin fitted gown wanda ya fitar da curves dinta gaba daya. Sossai dinkin yayi kyau sannan ya dace da jikinta. Kanta babu dankawali yayinda kitson kalban da tayi ya kwanta a kan kafadunta da bayan ta. Fuskar ta kuwa cikin tsananin damuwa, she even looked as if she cried all night long. Tunda ta shigo Mustapha ya sa mata idanuwa kamar yau ya fara ganin ta. Shi kam sossai Zehra ta canza mishi, dukda damuwar da take tattare da ita sossai tayi mishi kyau. Har ta kawo tsakiyar falon kuwa bata kula da shi a zaune ba sai qamshin turaren shi ne da ta ji na ga tayi freezing a tsaye. Dago kai tayi ta gan shi zaune yayinda Yasmeen duk ta bi ta birkita mishi gashin kanshi. Gaba dayan su ita suke kallo a yanzu. Bata ankara ba ta ji muryar Yasmeen tana fadin “Ammi, kin ga kitson Abbu??” Gani suka yi ta juya da sauri ta koma yayinda Mustapha ya saki ajiyar zuciya ya kalli Anty yace “wai me ke damun ta ne?? jiya ma fa tana gani na ta gudu kamar ta ga ghost??” Khadeeja ta fashe da dariya yayinda Anty tace “Oh ashe dama kai ka koro ta gida kenan muka dinga neman ta bamu gan ta ba? Yunusa Driver ne yake fadi mana ta kira shi tace ya dawo da ita gida”……… Zehra dai tunda ta koma daki ta kasa zama. Gaba daya ta zama confused yayinda ta rasa abin yi. Tun dawowar shi ta zama so restless, gaba daya a rude take musamman idan ta tuno wadda suka zo tare. STORY CONTINUES BELOW Who is she??2 Gani nayi ta dauki wayarta sannan ta kira Yunusa driver tace mishi ya zama on standby zata fita anjima. ina zata je??🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤ ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE Zaune suke a falonta suna ta hira kamar wadanda suka dade da sanin Juna. Abubuwan motsa baki ne birjik a gaban ta. Zehra ce tayi sallama ta shigo gidan.. Ko da ta shigo ta gan ta zaune a falon Fadeela gani nayi hankalinta yayi masifar tsahi yayinda ta juya zata koma. Da sauri Fadeela tace “hey Zee meye haka daga zuwa zaki gudu?? Ga Adda Ummie kuma baku gaisa ba” Ni kuwa nace Zee ki dawo kiyi facing reality.. ah toh🤨 A razane Zehra ta juyo ta kalli Fadeela yayinda Adda Ummie ta taso tana murmushi ta qaraso wurin ta tare da riqo hannunta tace “I am finally honoured to meet you our Angel”2 whoa… Zehra wadda zuciyarta take ta bugawa ta zama so confused yayinda take kallon ta. Jikin ta har rawa yake yi domin kuwa a yanzu da ta qara kallon Adda Ummie gani tayi ta masifar haduwa, gata fara, kyakyawa sannan big garl wadda ta riga ta gama dacewa da Mustapha ta kowanne fanni. Adda Ummie ta janyo ta suka koma kan kujera suka zauna. Har a wannan lokacin kuwa a rude take. Tana kallon Zehra tace “masha Allah you are very pretty….. I can see why he is madly in love with you… na so mu hadu jiya Amma Musty yace mun you ran away from him” Tana riqe da hannun Zehra har yanzu ta cigaba da fadin “please I beg you stop running away from him, the guy has suffered enough”7 Zehra dai tuni ta qarasa zama confused. Dama ba budurwar shi bace?? Ji tayi Adda Ummie tana fadin “ni sunana Ummu Aimana, ni mutumiyar Adamawa ce amma kuma iyayen na suna zaune a nan cikin garin Abuja. Nayi karatu na a qasar Switzerland tare da yayan ki Zain, we were actually in the same class” Zehra wadda ta cika da mamaki a ranta tace “Ya Zain’s class mate?? Shine take looking this young??” Ummie ta cigaba da fadin “I am a Counsellor and Psychotherapist in Italy, Ina zaune ne tare da Maigida na wanda shima qwararren likita ne sai yaran mu guda biyu Farid da Faeeza… Actually four years ago I received a call from your brother Zain wanda yake bani labarin abinda ya faru da Mustapha, a lokacin ya sanar da ni cewar he was coming to Italy for a course amma ya sani sarai he is going to need help and ya tabbatar I am the only one that he knows who can help him. Well, the thing is a lokacin da Mustapha ya zo Italy he was in a really bad shape. He kept telling me he was okay amma I knew he was not. Sossai yake qoqarin yaqi da zuciyar shi akan ta manta da ke amma ya kasa. A lokacin da na fara having sessions da shi na fahimci cewar soyayyar ki a cikin jinin shi take. Na tabbatar ko mutuwa yayi kina nan a cikin zuciyar shi. At a point in time ban ma san ya zanyi da shi ba domin kuwa my Job was to help him forget you amma kuma it seemed impossible ganin yadda kika zama stuck inside him. Tunda nake handling cases ban taba handling emotional one kamar na Mustapha ba. He kept telling me cewar he was proud he finally did something for his brother- Sacrificing his love for him, and at the same time it was killing him”3 Zehra wadda take kwance a jikin Fadeela tana sauraron wannan labarin kuwa babu abinda take yi banda kuka. Adda Ummie ta cigaba da fadin “When I realised cewar talking about you was the only thing that could keep him going, you then became the subject of our every day’s discussion. Sessions din da muke having da shi suka zama babu amfani. Nayi realizing zaman shi a Suite din shi all alone made things worse, he was holding on to some memories of you- wasu sketches na idanuwan ki, your pictures, hundreds of text messages da kika aiko mishi and even your perfumes. Da qyar nayi nasarar tilasta mishi akan ya dinga zuwa gidana muna zama muyi hira da maigida na. it was a very good decision saboda sossai na ga canji a tare da shi. A haka har ya fara course din shi and I was glad it also took away his time, dukda bai daina tunanin ki ba but na tabbatar ya rage” STORY CONTINUES BELOW Tana kallon Zehra wadda take ta sheshekar kuka ta cigaba da fadin “three years ago bayan rasuwar Muhammad, your late husband komai ya koma mishi sabo, he lost a very important person in his life… the person he saw as a father figure- his role model…. his everything. A kullum maganar shi daya, halin da kike ciki, he wanted to call you ya ji yadda kike amma ya kasa, wai bai san abinda zai ce miki ba, he didn’t know how to console you. He felt so guilty for putting you through all that trauma at a young age…” Ta kamo hannun Zehra ta riqe sannan tace “Zehra bazan boye miki ba, Mustapha went through hell a dalilin ki, I beg you don’t leave his side. Not now not ever”3 Wayar Adda Ummie ce tayi ringing, ko da ta duba gani nayi tayi murmushi sannan ta amsa tace “Sareenah yaya dai?” Ta dan yi shiru sannan tace “toh shikenan, Allah ya kiyaye hanya. Da zarar kunyi landing please let me know. Bye” Ko da ta kashe wayar kuwa tace “that was Sareenah my younger sister, the poor girl that unconditionally fell in love with Mustapha…”3 Zuciyar Zehra ce ta buga da jin wannan maganar yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa. Wannan karon kuwa har Fadeela tayi mamaki domin kuwa basu yi labarin Sareenah ba. Adda Ummie tace “Sareenah tana karatun ta a nan Italy yayinda take zaune tare da mu, ta hadu da Mustapha a lokacin da yake zuwa gidana wanda kuwa ta zama so concerned about halin da yake ciki. Nayi mamakin yadda lokaci guda na fara ganin su suna hira wanda kuwa har dariya tana sa shi wani lokacin. Well, na san zai yi wuya dama mutum ya zauna da Sareenah bai saki jiki da ita ba because there is this Charisma da take da shi wanda yake sa ta shiga ran mutum farat daya, I never expected Mustapha to blend with her knowing the horror he was going through a lokacin. Hatta abinci ita take dafa mishi sannan tayi persuading din shi ya ci. Abu daya da muka fahimta da shi kamar baya son zama ya ci abinci, a tunanin mu saboda halin da yake ciki ne but we got to realize cewar nature din shi ne. Sareenah handled that perfectly because mun ga improvement” Girgiza kai tayi tace “The next thing da na ji a bakin Sareenah was she has fallen in love with him wanda kuwa na dade da na kula da hakan, tun tana boyewa har ta kasa ta fito fili ta fadi mun. A zahirin gaskiya na so ace yayi reciprocating soyayyarta but unfortunately he never did” Murmushi tayi tace “Ya sani sarai Sareenah tana bala’in son shi amma kun san me yayi?? He pretended kamar bai sani ba. I personally told her to back off amma ta qi, a cewar ta soyayyar da take yi mishi tana yi mata dadi a zuciya don haka bata damu ba idan baya sonta. Abinda ta sani shine as long as Mustapha zai yi aure a duniyan nan toh fa itace matar tunda dai ba zai taba iya auren matar yayan shi ba. Well, she had hope until when your husband died, daga wannan lokacin ne ta zama so insecured as if she even had him initially” Ta saki ajiyar zuciya sannan ta cigaba da fadin “Har yau dinnan bata fadi mun cewar ta haqura da shi ba but I am hoping so saboda maganar gaskiya with you, she stands no chance. In as much as ina son qanwa ta kuma zan so Mustapha a matsayin siriki na I prefer seeing you two together saboda na tabbatar hadin ku daga Allah ne..” Zehra wadda ta ci kuka har ta gaji gani suka yi ta miqe ta bar falon a guje yayinda ta bar su sake da baki. Fadeela ce ta kalli Adda Ummie tace “Adda a tunanin ki tana son shi har yanzu?” Murmushi tayi tace “sossai ma kuwa, ai baza su taba daina son juna ba” Fadeela ta girgiza kai tace “but she told me she doesn’t…” Kai tsaye Adda tace “qarya take yi” Fadeela ta saki ajiyar zuciya tace “Allah sarki Ya Musty, I used to think he is a strong person ashe ba haka bane…” STORY CONTINUES BELOW Adda Ummie wadda take dariya tace “ai Yayan ki is as fragile as a day’s old baby” Fadeela ta fashe da dariya yayinda tace “toh ko in je in lallashe ta ne??” Adda ummie tace “just let her be, she surely needs to process everything…” A haka dai suka cigaba da hira har Zain ya dawo suka dora. Har a wannan lokacin kuwa Zehra tana daki bata fito ba sannan basu bi ta kanta ba. Abincin da Fadeela ta aika a kai mata ma ko kallon shi bata yi ba. Bayan sallan magrib ne Mustapha ya shigo gidan. A lokacin kuwa Adda Ummie tana shirin tafiya. Zuwan shi kuwa ya sa suka dauko wata hirar har aka kira sallar Isha’i. Adda Ummie ce tace “ikon Allah, ace tun da rana da na zo gidan nan har ana kiran sallan Isha’I ban tafi ba..” Fadeela wadda take dariya tace “ni dama ki kwana a nan kawai” Tace “na qi wayon, yanzu da zarar nayi sallah zan tafi” Mustapha wanda ya miqe tare Zain zasu je masallaci ne yace “da mota kika zo?” Tace “nope, driver ya kawo ni” yace “toh jira ni idan na dawo sai in sauke ki a gida” Tayi murmushi tace “okay”. ************** Bayan sun fito daga masallaci sun shigo gidan ne suka ga direban gidan Papa, Yunusa. Cike da mamaki Zain yace “me ya kawo Yunusa da daren nan kuma? Hope all is well?” Ko da ya gansu cike da girmamawa ya qaraso wurin su ya gaishe su. Zain yace “Yunusa lafiya kuwa??” ya dan yi murmushi yace “Hajiya qarama ce tace in zo in kai ta gida” Cike da mamaki ya kalli Mustapha yace “Zee??” Jin haka kuwa na ga Mustapha ya dan shafa kan shi sannan ya kalli Yunusa yace “koma gida abinka, zan dawo da ita” 🤨🤨🤨🤨 Haka yunusa yayi musu sallama yayi tafiyar shi. Ko da suka shigo falon sun tarar da Adda Ummie ta shirya tsab tana jiran shi. Ganin ya samu kujera ya zauna ne tace “malam na shirya fa” Yace “bari My Angel ta fito, tare zamu tafi” Fadeela tace “ya akayi ka san tana nan?? kunyi waya ne?” Zain ne yace “yanzu muka ga Yunusa ya zo yana jiranta wai ita ta kira shi, I was even surprised ace duk drivers din gidan nan babu wanda zai mayar da ita gida har sai ta kira Yunusa?? What is going on?? Yaushe ma ta zo gidan nan??” Fadeela ta dan yi murmushi tace “she has been around fa tun da rana, ka san halin ta ai, mood swing gareta kamar wata mai tsohon ciki” Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Mustapha yake ta sauraron fitowar ta. Aikuwa bai ankara ba ya hango ta tana saukowa riqe da wayar ta. Da ganin fuskar ta kasan tana cikin damuwa. A ran shi ne yace “why is she looking all tensed up??..” Ko da ta qaraso falon tsayawa tayi cak yayinda take kallon shi. Zuciyarta sai harbawa take yi.. Sossai yayi mata kyau wanda har ta kasa daina kallon shi. Muryar Zain ta ji yace “kallon ya isa haka malama, dama ke ake ta jira” Ko da ta juya ta kalle su gani tayi Fadeela da Adda Ummie sun fashe da dariya yayinda suka ga ta juya zata koma. STORY CONTINUES BELOW Tana gab da hawa steps ne ta ji muryar Zain yana fadin “wallahi kika hau steps dinnan sai na bata miki rai, common dawo ki wuce ku tafi gida” da kyau Yayan mu🤣🤣 Ko da ta juyo ji suka yi tace “ni anan zan kwana” Fadeela da Adda Ummie kuwa sai dariya suke yi yayinda hankalin Mustapha yake a tashe. Ya kula ma gaba daya Zehra gudun shi take yi. Toh ya zai yi??🤔 Zain ne yace “kin san Allah?? Wallahi nayi rantsuwa bazaki kwana mun a gida ba” whoa… Mustapha ne ya miqe tare da fadin “Don Allah kayi haquri, idan nan din zata kwana please allow her..” Zain wanda bai tsaya sauraron Mustapha ba yace “Zee I said leave my house now..” toh fa.. Jiki a sanyaye ta wuce ta fita yayinda suka yi sallama suka bi bayan ta. Shi dai Mustapha bai ji dadin hakan ba domin kuwa duk wani abinda bata so har ga Allah shima baya so. ni kuwa nace even if it means HIM???7 Ko da suka fito sun tarar da ita a tsaye tana jiran su. Ganin sun nufi direction din motar shi ne ta bi bayan su. Ita dai Adda Ummie qofar baya ta bude ta shige yayinda Mustapha ya bude ma Zehra gaba. Bayan ta shiga ne ya rufe yayinda ta saki wata muguwar ajiyar zuciya. Wani asirtaccen qamshi ne ya bugi hancinta sannan ga wani irin extra comfortability da motar take da shi. Ita dai dukda bata san motoci ba ta tabbatar wannan din daban ce a cikin saura. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Ko da suka kama hanya Adda Ummie da Mustapha sai hira suke yi. Zehra kuwa hankalin ta gaba daya baya kan su, addu’a kawai take yi Allah yasa ita zasu fara saukewa domin kuwa har fargabar a bar su daga ita sai shi take yi amma kuma kash… Adda Ummie ya fara saukewa. hahahaha… can’t stop laughing🤣🤣 Ko da suka isa gidan su Adda Ummie har cikin gidan suka shiga sannan ta sauka. Ta kalli Zehra tace “toh Angel good night” da qyar ta saita murya tace “good night” Zehra dai bata ankara ba ta ji Mustapha yace “Sareenah tana hanya ko?? Tace “yes, na san any moment ma zasu yi landing” Yace “okay, let me know idan ta iso” Tana murmushi tace “ai na tabbatar zata kira ka idan ta iso” Bayan sunyi sallama ne ya ja motar shi. Aikuwa ko gate din gidan basu fita ba ya ga ta rushe da kuka. Cike da tsananin mamaki a ranshi yace “like seriously?? Why is she crying??” ni kuwa nace are you even asking???🤔 Da farko qyale ta yayi saboda a tunanin shi he will only add fuel to the fire ne idan yayi mata magana amma da ya kasa jure sauraron kukan nata ne yayi parking motar a gefen titi. Bata ankara ba ta ji muryar shi yana fadin “My Angel, ni ne nake sa ki kuka??” Zuciyar ta ce take ta bugawa yayinda ta ji yace “Me yasa kike gudu na?? kin daina sona ne??” A razane ta dago kai ta kalle shi yayinda ta ji yace “Look I am very sorry for everything that happened…” Daga nan kuma ya dan yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ta ji ya cigaba da fadin “I swear I never stopped loving you my Angel, not for a single second…” Shiru ya qara yi yayinda sautin kukan ta ya qaru. Tambayar da yayi mata next ita ta razana ta. “do you still love me??” Runtse idanuwan ta tayi tana ta kuka. “ba kuka nace kiyi mun ba my Angel, a simple Yes or No will do” Gani nayi ta sa hannu zata bude qofa ta fita amma ta kasa, da alama ta fara zama suffocated domin kuwa numfashin kirki ma ya fara gagarar ta. Bata ankara ba ta ji ya kamo hannun ta yayinda gaba daya jikinta ya fara rawa. A yanzu haka suma ne kawai bata yi ba domin kuwa hannun nata da ya riqe ji tayi yayi mugun sanyi. Ga sanyin AC da yake ratsata ta ko ina making things more difficult for her. A bangaren Mustapha kuwa jin hannun nata yayi kamar hannun jarirai saboda laushi, sossai yake jin wasu abubuwa suna yawo a cikin jikin shi. Bai ankara ba ya ga tana qoqarin qwacewa wanda kuwa ta kasa. Ji tayi yace “kin dai san bazaki iya qwacewa ba ko? Don’t stress it” Tabbas ba tun yau ba ta sani sarai bazata taba iya qwacewa ba don haka ne na ga ta natsu yayinda ta kwantar da kanta a kujera tana ta kuka. Jikin ta sai rawa yake yi yayinda bugun zuciyar ta yayi trippling. Kusan minti biyar yana riqe da hannun ta bai ce komai ba. Shi kan shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa saki. Gani nayi ya shafa zoben da yake hannun ta yayinda ya saki ajiyar zuciya. Atleast the ring is still intact…. Ba tare da ya saki hannun nata ba ya tada motar ya hau titi. Zehra dai hawaye ne kawai suke ta gangarowa daga idanuwan ta yayinda take ta ji yana wasa da yatsun hannun ta. Gaba daya ta rude. Har suka iso gidan kuwa bai qara ce mata komai ba. Gab da Porch yayi parking sannan yace “good night My Angel.. I love you” ya saki hannun ta yayinda ya bude mata lock. Aikuwa jiki a sanyaye ta fita ba tare da ta kalle shi ba balle tayi mishi magana. Wani nauyayen numfashi ta saki wanda da alama ta dade tana riqe da shi. Da qyar ta lallaba ta shige cikin gida yayinda ya bi ta da kallo. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Answer: She is Adda Ummie and she poses no threat to us!! Yeeey💃💃3 Toh amma SAREENAH fa??? Is she significant or not??🤔🤔3 Finally mun ji kadan daga cikin rayuwar da Musty yayi a Italy… so sad☹☹+ Da alama dai soyayyar da yake yi ma Zehra is still intact… is she happy about it or not??🤔🤔3 what is going on in her mind??🤔🤔3 Me kuke tunani zai biyo baya???🤨3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *