ZEHRA CHAPTER 6
EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICES Mustapha ne yayi parking motar shi a Parking lot.+ Tun Kafin ya qarasa fitowa ne Ma’aikatan wurin suke ta kawo mishi gaisuwa cike da girmamawa yayinda yake ta amsawa amma fa fuskar shi a daure domin kuwa shi kam asalin shi ba mai yawan fara’a bane. Idan ka gan shi yana murmushi harda dariya toh fa Lallai Zehra ce take kusa da shi. Wurin yana functioning sossai musamman bangaren small Chops. A yau ma kamar kullum mutane birjik ana ta siyan abubuwa yayinda wasu suke tafiya da shi wasu kuma suna zama a nan su ci. Mustapha a ranshi yace “Kowa da abinda yake so, ita kuma My Angel ta rasa abinda take so sai irin wannan” Girgiza kai yayi ya haura sama. Ko da ya qarasa lounge din office din ya samu Salima Secretary dinta zaune akan table dinta yayinda take ta aiki a computer. Tana dago kai kuwa ta gan shi ne tayi saurin miqewa tace “Ina wuni Sir” tare da russunawa. Yace “lafiya, is your madam in?” Tace “yes sir, suna Meeting ne amma let me inform her..” Dakatar da ita yayi yace “don’t worry, I can wait” Mustapha dai zama yayi yayinda Salima ta ajiye mishi drink a gaban shi ta koma ta zauna. Yana nan zaune yana ta latsa wayar shi, ko kallon drink din da ta ajiye mishi bai yi ba. ni kuwa nace dama ai ba sha zaiyi ba… ************ Zehra dai basu gama meeting din ba har sai kusan bayan mintuna arba’in da zuwan shi. Yana nan zaune ya ga mutane suna ta fitowa daga office dinta, maza da mata yayinda suka dinga gaishe shi tunda dai babu wanda bai san shi ba. A cikin su kuwa harda Hidaya. Shin na fadi muku cewar Hidaya itace Manager din Zehra?? Yes, Zehra tayi ma Hidaya tayin position din wanda tayi accepting gladly domin kuwa Hidaya tana bala’in son Zehra.3 Bayan duk sun gama fitowa ne Salima ta kalli Mustapha tace “Sir, sun gama..” Kafin yayi Magana ne Zehra ta fito daga office dinta a gajiye. Sanye take cikin wata doguwar rigar kimono Burgundy color yayinda ta nada baqin gyale a kanta. Sossai tayi kyau dukda kuwa she is looking tired. Tsayawa tayi cak tana kallon shi cike da mamaki yayinda tace “Baby? Yaushe ka zo?” Da sauri ta kalli Salima cikin masifa tace “shine kika bar shi zaune a nan??” STORY CONTINUES BELOW Muryar Salima tana rawa tace “kiyi haquri Ma’am, he asked me not..” Mustapha wanda ya taso ya qaraso wurinta ne ya dakatar da Salima tare da fadin “I asked her to not interrupt your meeting, ya kike?? You look tired” Murmushi tayi tace “wallahi na gaji Baby, ashe haka running irin wannan wurin yake?? Ka ga fa I have so many contracts a qasa sannan ga bikin Dee. Anya zan iya kuwa??” Fashewa yayi da dariya yace “Ke fa raguwa ce ashe. Zaki iya mana.. Come on you are doing good honestly. Keep it up” Tare suka shiga office din nata yayinda Salima take ta mamakin yadda Mustapha baya yi ma kowa dariya idan ba Zehra ba. Tunda ya zauna fuskar shi a murtuke amma yana ganin ta kuwa ya sauya. Ji nayi tace “Allah ya cika musu burin su”3 nace “Ameen”1 ************** 5 Zaune take a kan hannun daya daga cikin kujerun office din yayinda yake ta snapping dinta hotuna. Gani nayi ta miqe ta nufi kujerar da yake zaune ta zauna a gefen shi tace “let me see the pictures, idan basu yi kyau ba zaka yi deleting” Murmushi yayi ya sa wayar a aljihun shi yace “Ai My angel ko kuka kike kyau kike yi so relax… I got this one” Murmushi tayi tace “Thanks Baby” Tana kallon shi tace “kayi kyau sossai” Dariya yayi yace “ke wai babu ranar da bazan yi miki kyau bane??” Tana dariya tace “ai kai kyakyawa ne, wallahi har bana so kana fita sossai don kar ‘yan mata su qwace mun kai” Fashewa yayi da dariya yayinda ta cigaba da fadin “ka ga Saliman nan ma haka ta ajiye ka a wurin ta tana ta kalle mun kai, sai na bata query” Yana dariya yace “yi haquri Angel, tunda na zauna she was on her computer” Ta Harare shi tace “ka rantse bata kalle ka ba?” Yace “tana dan dagowa ta kalle ni amma ai..” Turo baki tayi cikin shagwaba tace “toh meyasa baka ce mata ta daina kallon ka ba??” Dariya yake ta yi yayinda yace “Relax My Angel, We belong to each other, Insha Allah babu wanda zai yi separating dinmu sai dai mutuwa wadda nake fata ta dauke ni before you” STORY CONTINUES BELOW Ta girgiza kai tare da fadin “na fi so ta dauke ni kafin kai My Baby, I can’t live without you” Yana murmushi yace “lest I forget, tunda Daddy ya dawo yau zan same shi inyi mishi maganar auren mu” Cike da murna tace “Alhamdulillah, I can’t wait to become Mrs. M. Tafida” Yace “and I can’t wait to have the beautiful Zehra Abu-Yazeed as my wife” A haka dai suka cigaba da hirar soyayyar su yayinda tayi cancelling dukkan appointments dinta. Dukkanin mutanen da suka zo kuwa wurin Manager dinta suke zuwa. ♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Da daddare Daddy da Mummy suna zaune a falon Daddy suna kallon news ne yayi sallama. Cike da girmamawa ya qarasa suka yi musabaha da Daddy yayinda ya koma kusa da Mummy ya zauna tare da gaishe ta. Cike da farin ciki iyayen nashi suka amsa gaisuwar shi. Mummy ce tace “ya akayi ne? don nasan dole akwai abinda ya kawo ka” Daddy ne yace “ai kam babu laifi a ‘yan kwanakin nan yana shigowa muna hira sossai. Allah yayi ma Zehra albarka” Mustapha dai dafe kai yayi cike da kunya yayinda Mummy wadda take yi mishi dariya tace “Ameen” Daddy ne yace “toh muna sauraron ka” Mustapha ya dan shafa kan shi tare da fadin “uhm Daddy dama maganar tafiyar da zanyi ne bayan bikin Dee” Daddy yace “tafiyar ka zuwa Italy?” Yace “Yes Daddy, I will be there for almost four years..” Mummy tace “what?? Shekaru hudu?? Gaskiya wannan aikin naku bana son shi. yanzu har tsawon shekara hudu baka tare da mu?? Mun samu yayan ka zai dawo kai kuma zaka tafi?? ni shikenan yara na haka zasu cigaba da zagaye duniya tsawon shekaru??” Daddy wanda shima bai ji dadi ba yace “gaskiya shekaru hudu sunyi yawa Mustapha, is there anything I can do to stop this??” Mustapha wanda yayi murmushi yace “Daddy please don’t, ka san bana son neman alfarma akan komai. I was one among many that was chosen to reperesent my country so I think it’s a good thing” Ya dan saki ajiyar zuciya yace “dama Daddy ina so ne kafin in tafi a daura mun aure da Zehra, sai mu tafi tare”4 Aikuwa cike da murna Mummy tace “kai amma kuwa na ji dadin wannan shawarar” Ta kalli Daddy tace “ya ka gani?” Yana murmushi yace “ai wannan ba wani abu bane, hakan yayi daidai. Zamu samu lokaci muyi maganar da Papa insha Allah” Mustapha yana murmushi yace “nagode Daddy” Daga nan kuwa suka dan taba hira sannan yayi musu sallama. Aikuwa ko da su Daddy suka yi maganar tuni sun shirya akan bayan bikin su Zain za’a fara shirye shiryen na su Zehra tunda dai abu ne na gida wanda ba wani buqatar shiri mai yawa zai yi ba. STORY CONTINUES BELOW Sossai Zehra ta ji dadin wannan zancen. Dukda kuwa ba wai an sa rana bane amma ta sani cewar lallai they are getting closer to their dream. hmmmmm🤔🤔11 ♤♤♤♤♤♤♤ BAYAN LOKACI.. A lokacin da aka shigo satin bikin Fadeela da Zain kuwa gaba daya gidajen biyu hidima ake ta yi.3 Tuni Fadeela ta dauki hutun Annual leave dinta. OMAR TAFIDA RESIDENCE Ranar Laraba da safe ne Amaryadotcom tare da team dinta suka zirara ma amarya da qawayen ta lalle. Sossai lallen yayi kyau. Henna Party lafiyayye suka hada. Millie Mamza CEO na Dazeita ita tayi ma amarya kwalliya yayinda Fati Mamza CEO na Mamza beauty tayi ma Zehra da sauran qawayen amarya, sossai sunyi kyau. Kayan da amarya ta sanya kuwa shaharariyar fashion designer dinnan Hudayya ita ta dinka mata. Sossai aka yi shagali a nan gidan. Ahmed Zol kuwa ya dinga kashe hotuna. 6 Fadeela👆 ♤♤♤♤♤♤♤ Da daddare bayan sallan isha’I ne suna zaune a dakin Fadeela ana ta hirar shagalin Henna party din da aka yi ne wayar Zehra ta fara ringing. Fadeela wadda take kwance a kan gado ce ta kalle ta tace “toh Angel, Baby ya shiga matsala bai gan ki ba yau” Zehra wadda take dariya ta amsa wayar tare da fadin “Baby how far” A dayan bangaren kuwa muryar shi qasa qasa yace “haba Angel, yau fa throughout baki neme ni ba, haka ake yi fisabilillah??” Fashewa tayi da dariya tace “Yi haquri Babyn Angel na san kuna da meeting yau ai kuma ka ga mu ma we were busy with our henna party” Yace “well yeah, but you didn’t send me a picture ai” Tace “kana ina yanzu? Bari ma in zo in nuna maka” Mustapha wanda yake shirin shiga motar shi ne yace “gani nan zan fita” Miqewa tayi da sauri tace “fita?? zuwa ina?? Wait for me I am coming” STORY CONTINUES BELOW Veil ta janyo ta yafa ta fita a guje. Fadeela da sauran qawayenta ne suke ta yi mata dariya yayinda daya daga cikin su mai suna Hauwa tace “hmm, soyayyar Zehra da yayanki tana birge ni. I can’t wait for their wedding” ahhh… me too🤨 ************ Zaune yake cikin motar shi yayinda yake latsa wayar shi. Bude qofar motar tayi ta shiga ta zauna. Wutan motar ya kunna yayinda ya sa mata idanuwa yace “hey, na ga kin qara kyau ne, what’s the secret??” Tana dariya tace “I will not tell you” Hannunta ya janyo yana kallon qunshin da aka yi mata yace “wow, this is beautiful” Tana murmushi tace “thank you, yakamata ka biya” Yana shafa hannunta yace “nawa zan biya?” Cikin wasa tace “500k” Girgiza kai yayi yace “kawai??” Cike da mamaki tace “oh yayi kadan?? Toh na mayar 1m” Ji tayi yayi shiru yayinda yake latsa wayar shi har tana fadin “ya na ji kayi shiru?? ko in rage ne bazaka iya biya ba??” Kafin ta rufe bakin ta kuwa ta ji qarar shigowar message. Tana dubawa ta ga credit alert na 1m daga Mustapha Omar Tafida. A razane ta kalle shi tace “na shiga uku, Baby meyer haka?? I wasn’t being serious fa..” Yana murmushi yace “okay…” Bata rai tayi tace “I was only kidding.. kai baka san wasa bane?? Gaskiya bana so yadda kake kashe mun kudi haka, its too much. Ni fa kai kadai nake so not your money or anything” Yana kallonta yadda take magana cike da masifa yayinda yake ta murmushi yace “ina so idan kina masifa, you look cute while at it” Hararar shi tayi tace “Oh, wato ma baka dauki maganar da nayi serious ba ko?” Ta juya zata bude motar ta fita ne yayi saurin riqo hannun ta yace “yi haquri My Angel, bazan qara ba I promise” Turo baki tayi tace “toh yanzu dai bani account number dinka in mayar maka da wannan..” Yana murmushi yace “toh ina kika taba ganin an mayar da hannun kyauta?? Wannan ma ya riga ya shiga hannun ki fa. Please I am sorry, accept this one ni kuma zan kiyaye gaba” Wayar shi ce tayi ringing yayinda ya duba. Murmushi yayi ya kalle ta yace “your brother, the Groom” Ko da ya amsa wayar kuwa ji yayi Zain yace “haba Bros Inlaw ina ka shiga ne ina ta jiran ka?” Mustapha wanda yake kallon Zehra wadda itama shi take kallo ne yace “yi haquri ango, Qanwar ka ce ta riqe ni kuma ka san idan bata sallame ni ba I cant go. Gani nan zuwa amma” Bayan ya kashe ne tace “meyasa yake kiran ka??” Yace “Zamu je Barbing salon ne” Ya dan taba gashin kanshi yace “kwana biyu na dan tara gashi, I need to reduce it kar yayan amarya ya fito buzu buzu ranar daurin aure” Zehra wadda ta tabe fuska tace “uhm, ni kam ban ga wani gashin da ka tara ba, kawai kayi zamanka mu cigaba da hira” Girgiza kai yayi yace “yi haquri My Angel, nayi mishi alqawarin zan dauko shi mu je, besides he is the groom and he needs to look his best” Tace “well its true” Nuna shi tayi da yatsa tace “toh, idan kuka gama dai ku dawo gida. Kar ka sake ka je ko ina” Yace “Yes Ma, I love you. Sai na dawo??” Tayi squeezing fuska tare da fadin “kora ta kake yi??” Fashewa yayi da dariya yace “ni ban qi ma in tafi da ke ba, I swear I love you my Pepper queen” Dariya ya bata tace “I love you too” Ta bude qofar ta fita yayinda yace “I will call you later” tace “okay” Bai bar wurin ba har sai da ta shige cikin gida. Ajiyar zuciya ya saki yace “Allah ya kai mu lokacin da zan mallake ki a matsayin matar aure, Insha Allah we are getting closer to our dream My beautiful Zehra, can’t wait” I cant wait too oooo🤔🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau ne za’ayi bikin kamun Fadeela wanda kuwa tun da safe kowa yake ta shiri a gidan.+ Gidan kuwa ya cika da ‘yan uwa da abokanen arziki. Zehra wadda take tsaye a tsakar dakin su tana waya da Mustapha ne na ji tace “Baby wai dagaske fara ka qara siya?? Meaning all your three cars are white??” A dayan bangaren ne yace “yes dear, come and see it before Iro ya fita da ita filling station” Fadeela wadda take zaune a kan gado tare da qawayen ta ce tace “Zee ba dai farar mota ya qara siya ba?” Zehra ta janyo Hijabi dogo ta dora a saman gajerar nighty dinta tace “hmm, ke dai bari Dee. The guy is obsessed with white color” Fadeela tana dariya tace “toh Allah dai yasa ba Mercedes ya qara siya ba” Tace “toh Ameen, let me go and see” ************** Tsaye yake a gaban motar sanye cikin wandon Camo na sojoji da black T-shirt yayinda yake Magana da Iro driver. Tana qarasowa wurin su ne Iro Driver ya dan russuna yace “Ina kwana Anty” Zehra tana murmushi tace “lafiya qalau, ya aiki??” Kafin ya amsa ne Mustapha Wanda fuskar shi take a murtuke ya daga mishi hannu tare da fadin “dan bani minti biyar” Bayan Iro ya tafi ne ya Harare ta yace “meye na yi mishi murmushi?? Harda wani extra tambaya?” Dariya tayi tace “yi haquri Baby. It’s good to always smile, Sunnah ce. Na ga alama idan ba ni ba baka yi ma kowa fara’a especially the house help.. not fair” Daga hannu tayi sama yayinda tace “Ya Allah, Allah ka sa in haifo yaro mai fara’a ba kamar baban shi ba” Gani nayi ya zaro idanuwa tare da fadin “what the…” Gwalo tayi mishi tana dariya sannan ta juya tana bin motar da kallo tace “wow, Baby this is beautiful” Girgiza kai yayi yana murmushi a ranshi yace “she is crazy I swear” Gani yayi ta zagaya motar tana qare Mata kallo sannan ta bude ta shiga. Leqowa tayi tace “what’s with you and Benz ne wai?? Yanzu fisabilillah you have three cars, duka farare sannan Mercedes benz. How do you expect people to differentiate between them??” Murmushi yayi ya zagaya shima ya shiga motar tare da fadin “ai saboda baki san mota ba shiyasa bazaki iya differentiating ba, but there is a huge difference even in the looks. Again, white is my favourite color, it signifies peace and yes Benz is Bae, idan ba Mercedes ba toh ba mota bace” Murmushi tayi tace “hmmm, okay oo. Ni kam kar ka manta kai zaka kai ni Kamun Dee don bazan bi motan kowa ba. Na Baby na zan dana” Yana dariya yace “ban manta ba My Angel, I still can’t believe you don’t know how to drive. Yakamata ki manta da abinda ya faru a baya kiyi qoqari ki koya. You need to be able to drive yourself wherever you want to saboda there are times you wont get someone to..” STORY CONTINUES BELOW Kai tsaye tace “wallahi Baby bazan iya ba, ni kam na gwammace in shiga motar haya ma” Yana dariya yace “matsoraciya kawai” Itama dariya tayi. Wayar shi ce tayi ringing ya duba. Gani nayi yayi murmushi sannan ya amsa. Ji nayi ya fashe da dariya sannan yace “Oh Bro, finally dai ka gama da England” Shiru yayi sannan yace “okay, I will come pick you up Insha Allah, I am glad zaka samu halartar daurin auren Dee don kuwa na ji ta fara qorafi” Dariya yayi yace “safe trip bro, alright bye” Zehra wadda take ta kallon shi har ya gama wayar ne ta ji yace “Moha is coming back today, Oh Allah I am so happy..” ghen ghen ghen.. Bata rai tayi tace “hmm, kishiya na ko?” Fashewa yayi da dariya yace “meyasa kika ce haka??” Cikin shagwaba tace “toh ai na ga kamar ka fi son shi fiye da ni…” Da sauri yace “what?? Hell no. I love you both in different ways My Angel” Tana murmushi tace “Allah ya dawo da shi lafiya, finally I will get to see our best brother” Yace “Ameen, kin san cewar ban fadi mishi about us ba??” 🤔🤔🤔🤔 Tace “haba? Why?” Yace “ina so inyi suprising dinshi ne because a kullum yana cikin tsokana na wai a yadda hali na yake I can never date a girl, wai auren dole ma kawai za’a yi mun” Fashewa tayi da dariya tace “Dee ma fa tace wai qila sai dai a kai hoton ka masallaci..” Ya zaro idanuwa yace “what?? I swear Dee bata jin Magana” Zehra wadda take dariya tace “don’t mind them, you are the best lover boy on earth. I swear sometimes har tsoron irin soyayyar mu nake, I find it to be so perfect that I feel something might go wrong..” Da sauri ya dakatar da ita tare da fadin “nothing will go wrong My Angel, Insha Allah ke ce uwar ‘ya’ya na” Wayar ta ce tayi ringing yayinda ta duba. Ganin sunan Salima ne yasa tace “oh my God, I swear na manta” Daga nan ta amsa wayar yayinda tace “I will just be on my way Salima” Bayan ta kashe ne tace “baby duk laifin ka ne I swear, a kullum idan ina tare da kai manta komai nake yi. Yanzu haka I am supposed to be in the KITCHEN, ka san nace musu ina so in ga komai da za’a shirya na bikin Dee..” Murmushi yayi yace “yi haquri Hajiyata, je ki shirya ki zo in kai ki. Nima dama zan je Barrack” Bayan sun fito daga motar kuwa ta wuce cikin gida wanda bai daina kallon ta ba har sai da ta bace mishi sannan ya juyo. Iro wanda yake tsaye kusa da shi sai mamaki yake yi domin kuwa minti biyar kawai Mustapha yace mishi amma kuwa sai da suka kwashi kusan minti talatin. Ya tabbatar cewar ba qaramar soyayya ke tsakanin su ba. Bayan Mustapha ya gama yi mishi wasu bayani ne ya miqa mishi makullin motar sannan ya nufi sashen shi. ************ Zehra dai tana shiga dakin su ne Fadeela da qawayen ta suka dinga yi mata tsiya. Fadeela tace “daga zuwa ganin mota sai aka koma zance, wai ace har da safe ma sai kunyi zance. I swear this una love dey sweet me” STORY CONTINUES BELOW Zehra dai dariya ta dinga yi. Ba tare da tace komai ba ta shiga dressing room ta fara shirin shiga wanka domin kuwa ta san idan ta biye ma su Fadeela bazata samu ta shirya ta fita ba. Daga cikin dressing room din ne tace “Dee yau Ya Moha zai dawo” Cike da murna tace “haba?? Ai wallahi har nayi fushi da shi” Zehra tace “anjima Baby zai je dauko shi a Airport so relax, he will attend your wedding Insha Allah” Fadeela tace “I am so happy kuwa. finally the family will be complete once again” Ta cigaba da fadin “Toh wai ban tambaye ki ba, wace irin mota kuka siyo?” Zehra ta fito daga dressing room din daure da towel tace “hmm… its Mercedes again” Fadeela ta fashe da dariya tace “an shiga uku da naci wurin Ya Musty” sauran qawayen ta suka dinga dariya. *********** Kamar yadda suka shirya tare suka fita inda ya sauke ta a ofis dinta yayinda ya wuce Barrack. Bayan Zehra ta tabbatar da dukkannin kalolin abincin da za’a yi na bikin Kamun Dee ne ta kira Iro driver ya zo ya dauke ta ya dawo da ita gida. ************ Tuni Millie Mamza ta iso inda ta fara tsantsara ma amarya kwalliya yayinda Fati Mamza da team dinta suke yi ma qawayen ta. Zehra wadda ta shigo dakin ta tarar suna ta shiri. Gani nayi ta fada kan gado ta kwanta yayinda tace “wasshhh” Fadeela ce ta kalle ta tace “ban gane ba, meye na wani kwanciya?? Don Allah tashi ki fara shiri” Zehra tana dariya tace “don Allah kiyi haquri in dan huta, ni fa dama ba tare da ku zan je ba. Baby zai kai ni” Fadeela ta girgiza kai tace “toh Angel din Baby, amma I swear idan kika bata lokaci I will disown you, na daga miki qafa ne saboda na san what you have done for me” Zehra tana murmushi tace “Godiya nake yi Gimbiyar mu” Yayinda ake ta yi musu dariya. Bayan Millie ta gama yi ma Amarya kwalliya ne na ji gaba daya dakin ana ta yaba Kyan da tayi. Sossai Fadeela tayi kyau. Mummy kanta da ta shigo qarasawa tayi ta rungume ta yayinda take fadin “masha Allah autar Mummy, kin yi kyau sossai. Allah ya albarkaci rayuwar auren ki kuma ya sa a yi a sa’a” Gaba daya dakin aka amsa da “ameen” Ganin dai kowa ya gama shiri ne Zehra ta shige bathroom don yin wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin atamfar ankon su ne ta zauna gaban Fati Mamza ta fara yi mata kwalliya. Motocin da zasu kwashi amarya da qawayen ta ne suka iso yayinda suka fara fita. Fadeela ta kalli Zehra tace “Zee kin dai san kina da presentation ko? Please kiyi sauri” Zehra tace “I will my love, sai mun hadu” Aikuwa amarya tana fitowa na ji an fara rangada guda. Gaba daya gidan ya kaure da gudan Mata yayinda ake ta yaba kyan da tayi ana bin ta da addu’ar fatan alkhairi a sabuwar rayuwar zaman aure da zata shiga. ************** Minti kusan ashirin da tafiyar Amarya da qawayen ta. Sossai gidan yayi shiru domin kuwa yawanci daga ‘yan aiki sai tsofaffi cikin dangi wadanda basu je ba. Mustapha wanda yake zaune a cikin motar shi ne yana Magana da ita a waya na ji yana fadin “Angel please ki fito haka nan, kar ki manta zan je Airport fa” STORY CONTINUES BELOW Zehra wadda take tsaye a staircase ce tace “I swear na gama shiri, kawai fa Furera tana dauka na hoto ne amma gani nan zuwa” Mustapha yace “Toh My Angel, ki zo ki tura mun hoton” tace “dama can naka ne My Baby” Yana zaune ya hangota ta fito sanye cikin wata atamfa mai kyan gaske (atamfar ankon bikin) yayinda tayi masifar kyau. She looked so simple yet so elegant. Ajiyar zuciya yayi yace “I pray I don’t ever lose you My Angel” Ni kuwa nace “why this negative thought all of a sudden Musty??”🤔🤔🤔 Ko da ta qaraso ta bude ta shiga kafa mata idanuwa yayi babu ko qyaftawa. Tana murmushi tace “thank you very much” Cike da mamaki yace “for what?? I didn’t even say anything and..” Ji yayi tace “I can read people’s minds, remember” Dariya yayi tare da girgiza kai yace “mu ga hoton” Ta miqa mishi wayarta ya karba yayinda ya sa ma hoton idanuwa. 1 Ajiyar zuciya ya saki tare da fadin “Masha Allah, My angel you are beautiful” Ya kalli fuskar ta tare da fadin “wallahi bala’in sonki nake, soyayyar ki ta mamaye rayuwa ta kaf I swear” Dariya take tayi cike da jin dadin kalaman shi tace “nima bala’in sonka nake yi My Baby” Miqa mata wayoyin su yayi yace “send me the pictures please, I really want to have something to hold on to whenever we are not together” Haka ta karba ta tura mishi yayinda ya ja mota suka fita. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Bayan ya sauke ta a event hall din ne kuwa ya wuce Airport. Yayi mata alqawarin dawowa ya dauke ta don haka kawai ta kira shi a waya idan sun gama. ************ BLUE VELVET MARQUEE Zehra dai tana shiga MC ya fara yi Mata kirari a matsayin ta na babbar qawar amarya sannan qanwar ango. Sossai wurin taron ya cika da mutane. kowa ka gani yayi shiga ta alfarma. Ahmed Zol kuwa yana ta sana’ar shi ta daukar hotuna yayinda MC shima yake ta nashi aikin. Amarya Fadeela sanye take cikin wani tsadaden leshinta Wanda Hudayya ta dinka Mata. sossai tayi kyau.  STORY CONTINUES BELOW Dangin su Zehra ne suka fito suka kama amaryar yayinda suka ba qawayen amaryar envelope na Cheque har na naira miliyan daya. Sossai kamun yayi kyau. Haka dai aka cigaba da shagali yayinda aka sha rawa sannan aka ci aka sha. An yaba qwarai da abincin da aka yi serving din mutane. Presentation na staff din Zehra ya birge mutane. Komai nasu gwanin ban sha’awa sannan gaba daya staff din sanye suke cikin Uniform dinsu. Tuni Kitchen din Zehra ya fara bagging contracts, dayake Hidaya is present a wurin ita tayi ta karbar contracts din. ♤♤♤♤♤♤♤ NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA Tsaye yake a harabar arrivals yayinda hannuwan shi suke cikin aljihun wandon shi yana ta kallon matafiyan da suke fitowa. Tuni jirgin su Muhammad ya sauka yayinda ake checking kayan su. Mustapha wanda yake tsaye ne ya hango shi janye da akwatin trolley dinshi yayinda ya rataya wata jaka a bayan shi, da alama kuwa jakar laptop ce. Sanye yake cikin qananan kaya na sweatpant baqi da shirt. Ni da nake tsaye a gefe saida nace ‘wooow’ domin kuwa wani kyakyawa na hango.5 Dogo ne amma ba fari ba domin kuwa Mustapha da Fadeela sun fi shi haske. Daga ganin yanayin fatar jikin shi kasan ya huta, sossai yayi kyau. Gani nayi Mustapha ya saki murmushi tare da qarasawa wurin shi da sauri wanda shima sai gani nayi ya saki trolley din nashi tare da bude hannuwan shi suka rungume juna. Gaba dayan su sun kasa Magana, banda murmushi babu abinda suke yi. Tsawon mintuna uku sannan Muhammad yace “Musty talk to me mana” Qara matse shi yayi tare da fadin “I really missed you Bro, I am glad you are back, welcome home” Muhammad wanda yayi murmushi yace “thank you my favourite bro” Suka saki juna yayinda Mustapha ya janyo akwatin suka nufi parking lot suna hira. Muhammad yana kallon motar yace “wow, this car is dope mutumina. I am sure yau ka fara hawan ta right?” Mustapha wanda ya saka akwatin a boot ne yace “yes bro, thanks very much” Muhammad ya girgiza kai yace “amma kuma white again?? I swear obsession dinka da white color is getting outta hand” Yana dariya yayinda suka shiga mota na ji yana fadin “trust me bro, white is the best color amongst others” Uhmm..🤨 ********** Bayan sun baro Airport din ne Mustapha wanda yake tuqi yace “ya hanya? Hope dai ka dawo kenan?” Muhammad wanda yake latsa wayar shi yace “wallahi fine, I am back for good Insha Allah. Ni da England kuma sai dai hutu. Yanzu I will focus on my firm kawai” Mustapha yace “masha Allah, but dai ba gidan ka zaka je ba sai bayan bikin Dee ko?” Yace “uhm, yeah. I will go to my house after the wedding Insha Allah” Suna gab da isowa gida yayinda suke ta hira. Muhammad ne ya dago kan shi ya ga zoben hannun Mustapha yace “hey, ina ka samo wannan zoben mai kyau?? Don’t tell me you are engaged because it looks like an engagement ring” Mustapha wanda ya fashe da dariya kafin yayi Magana ne wayar shi ta fara ringing. Ko da ya duba ya ga sunan Col. Y M Bamanga, da sauri ya amsa yayinda yace ma Muhammad “just a minute bro” Muhammad yace “go ahead” Ni dai ji nayi Mustapha yace “what?? Yaushe? Inna lillahi wa’inna ilahir raji’un, gani nan zuwa Sir, I will be there in fifteen minutes” Bayan ya kashe wayar ne Muhammad yace “me ya faru Musty, you look worried” Yace “anyi attacking wasu colleaques din mu a Maiduguri this morning, gaba daya sun mutu” Muhammad yayi salati yace “Allah ya jiqan musulmi. But hey, hope you are not planning on going?” Mustapha wanda yake cikin tsananin damuwa yace “ai ni I have a course da zanyi a Italy, I am not a part of this kawai zan je mu hada kai ayi strategizing ne” Ji nayi Muhammad yace “Toh Allah ya taimaka kuma ya cigaba da tsare mana ku, honestly things are becoming bad in this country” Haka dai suka cigaba da hiran abubuwan da ke faruwa a qasar mu har suka iso gida. Ko da ya sauke Muhammad, Juyawa yayi ya nufi Barrack. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ LUNGI MAITAMA BARRACKS ABUJA Zaune suke a conference room yayinda yake tsaye yana Magana. Mustapha wanda ran shi yake a bace yana riqe da Marker yayinda yake bayani akan abinda ya faru da sojojin su yau da safe. Ji nayi yace “from all indication they didn’t strategize well, if they had grouped themselves into companies all these wouldn’t have happened. According to our informants the terrorists have taken over the village and as we speak, the villagers are being held hostages. If we dont act fast, I am afraid they might spread all over Maiduguri and before you know it the entire country will be unsafe” Col. Y. M Bamanga ne yace “what do you think we should do Major?” Mustapha wanda ya nufi map din qauyen ne yace “I think we will attack at night but we won’t strike at once, we need to form companies and surround them if at all we want to succeed” (Two or more companies makes up a battalion) Wani colleaque dinsu Major B. Isah yace “you keep saying ‘we’, you are not coming with us… are you??” Ji suka yi yace “I am coming with you my friends, we need to fight this together”3 Nace ‘whaaaaat???’🙄🙄 Sossai Col Y.M Bamanga ya ji dadi domin kuwa dama yana so ya roqi Mustapha akan ya bi su mission din domin kuwa yana da qwalwa sossai musamman when it comes to strategy na yadda za’a yi attack amma kuma yana tunanin yadda zai yi mishi Maganan domin kuwa he is not on the list. Wayar shi ce tayi ringing inda yayi saurin dubawa. Sunan ta ya gani yayinda ya dan kalli Col. Yace “Sir, can I?” yace “go ahead” Mustapha ya matsa gefe sannan ya amsa wayar. “Baby an gama fa, kai nake jira kuma ma office zan wuce because I need to prepare for tomorrow’s events” abinda tace kenan. Shafa kanshi yayi sannan yace “My Angel don Allah kiyi haquri zan turo official driver dina ya zo ya kai ki” Da sauri tace “why?? Kai fa??” Yace “I am in an important meeting right now kuma ba yanzu zamu gama ba” Murmushi tayi tace “its okay My Baby” Yace “I swear you are my priority amma this is very important ne, hope baki yi fushi ba??” Dariya tayi tace “Na isa inyi fushi da kai Baby? ai duk abinda kayi daidai ne, na sani cewa its important. Just send the driver I will be waiting” Bayan sun yi sallama ne ya kira official driver din shi na nan Barrack din ya sanar da shi ya je ya dauko Zehra ya kai ta office dinta. Bayan ya dawo wurin su ne yace “sorry please” daga nan kuwa suka cigaba da strategizing. ♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Gab da Magrib bayan an dawo daga Bikin Kamun Fadeela gaba daya kowa a gajiye don haka ne aka yi haramar Sallah. Dayake gidan a cike yake da baqi babu inda bazaka ga dan adam ba. Hirar bikin ake ta yi da yadda amarya tayi kyau sossai. Haka aka dinga yaba abincin da aka ci na bikin. STORY CONTINUES BELOW Fadeela tana zaune da qawayen ta a daki suna ta hira ne wayar ta tayi ringing. Ganin sunan Muhammad ne yasa tayi ihu tare da amsawa tace “yeeeey, tunda na ga Nigerian line dinka na san ka dawo, where are you??” Yana dariya yace “Yanzu na shigo dakin Mummy amma kuma yanzu zan fita because mata sunyi yawa…” Kafin ya qarasa ta miqe tare da fadin “don Allah wait for me..” Ta jefar da wayar sannan ta ruga a guje ta fita har qawayen ta suna yi mata dariya. Muhammad wanda yake zaune a kan Kujerar dakin Mummy sai ji yayi kawai ta fado jikin shi yayinda ta rungume shi cike da murna tana fadin “oyoyo Ya Moha, I swear I missed you a lot” Girgiza kai yayi yace “Ke kam you will never change. Wai baki san kin girma bane?? For crying out loud its your wedding fa” Turo baki tayi cikin shagwaba tace “toh ai it doesn’t matter tunda dai ni ce auta kuma I will always remain your Baby Dee, ko ba haka ba??” Yana dariya ya ja kumatun ta yace “haka ne my chubby bubbly… I am so happy gobe daurin auren ki, can’t wait to see your kids” Da sauri ta rufe fuskar ta cike da kunya tace “haba Ya Moha, daga aure kuma sai kids??” Mummy ta fashe da dariya tace “Au, toh me kike tunani??” Anty Maimuna da Anty Saratu ‘yan uwan Mummy suka shigo dakin. Ko da suka gaisa da Muhammad kuwa sai ya miqe ya lallaba ya fita domin kuwa Mata sai shigowa suke yi kamar an koro su. Haka ya fita suna ta yi mishi dariya. ************* Zehra dai bata dawo gida ba sai wuraren qarfe tara da rabi na dare wanda kuwa washe gari tun da sassafe zata koma saboda events din da za’a yi. Banda yinin biki da daurin aure akwai dinner wanda kuwa she has to make sure everything is in order. A gajiye ta shigo dakin yayinda ta fada kan gado. Fadeela ce tace “Allah sarki Zee, ina ta baki wahala ko?” Murmushi tayi tace “haba dai Dee, idan ban yi miki hidima ba wa zan yi wa?? Afterall you are not just my best friend you are my sister inlaw” Munnira ce tace “aikuwa mun shaida, the inseparables” Hauwa tace “ni dai bikin ki da Ya Musty kawai nake jira, please don’t forget to invite us” Zehra tana murmushi tace “insha Allah I wont” Haka dai suka cigaba da hira yayinda Zehra take ta kiran wayar Mustapha amma har ta gama ringing bai dagawa. Tunanin lallai basu gama meeting din bane ta tura mishi text message sannan ta wuce dressing room tayi shirin wanka. LUNGI MAITAMA BARRACKS ABUJA Ba su suka gama meeting din ba har sai wuraren qarfe goma sha daya na dare yayinda suka yi concluding akan gobe zasu tafi wanda kuwa Mustapha ne zai zama Frontline Commander na Battalion din. Ainihin mission din is supposed to be commanded by a Lieutenant Colonel because sune suke leading Battalions amma a dalilin error din da aka samu wanda yayi sanadiyar mutuwar sojojin wanda kuwa harda Lieutenant Colonel din da yayi leading dinsu ne yasa suka yi finalizing cewar Mustapha will lead the battalion this time dukda kuwa he is a Major.4 mazaaaa💪… Sanin cewar daurin auren qanwar Mustapha washegari ne yasa Col Y M Bamanga yace sai bayan daurin auren zasu tafi yayinda Mustapha yayi mishi godiya. STORY CONTINUES BELOW ♤♤♤♤♤♤ Yana tafe zai shiga motar shi ne na ga ya duba wayar shi. Missed calls dinta ya gani har guda goma sha uku sai text message dinta wanda tayi rubutu kamar haka: “Hey Baby, please idan ka dawo kar ka manta ka ci abinci, again don’t forget to call me no matter how late, I love you” Murmushi yayi sannan ya shiga motar shi. Gani nayi ya maqala Bluetooth a kunne yayinda yayi dialing lambar ta sannan ya tada mota ya fita daga Barrack din. A lokacin da ya kira ta kuwa har ta fara bacci. Cikin baccin ne ta amsa wayar tace “hey Baby” Yace “My Angel kinyi bacci ne??” tace “na dai fara, kun gama meeting din?? ka ci abinci??” Murmushi yayi yace “yeah, yanzu muka gama, gani akan hanya ina dawowa gida, And I promise idan na isa gida I will eat something” Ji yayi tace “but its like the meeting was kinda important ko? Na ga fa baka taba kai this late ba” Ajiyar zuciya ya saki tare da fadin “yes My angel, kar ki damu we will talk about it tomorrow Insha Allah, yanzu dai have some sleep and make sure you dream of me” Murmushi tayi tace “insha Allah My Baby, I love you very much and Good night” ♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Ko da Mustapha ya iso gida bayan yayi parking motar shi straight sashen shi ya nufa. Ya tarar da Muhammad kwance a kan kujerar falon shi yana kallon tashar BBC. Ganin Mustapha ne ya tashi zaune tare da fadin “Musty sai yanzu?” Ya zauna a gefen shi yace “wallahi sai yanzu Bros, abun is very serious” Muhammad yace “yanzu nake ganin news din on TV fa, abun ban tausayi wallahi. Toh yanzu ya ake ciki??” Mustapha ya shafa kanshi tare da fadin “Bros I have to go” Cike da tsananin tashin hankali Muhammad yace “what?? You are joking right?” Yace “No I am not” Daga nan ne yayi mishi bayanin dukkanin halin da ake ciki da yadda Col. Y M Bamanga yake da confidence akan shi da kuma yadda shi baya iya declining saboda mutuncin da ke tsakanin su sannan kuma deep down within him he really wants to go domin kuwa its what he likes doing with passion. our guy na gallant soldier ooo🔥3 Gani nayi Muhammad ya dafe kai tare da fadin “Oh Brother, I still cant believe you chose this as a profession, ina regretting yadda ka sa ni a corner nayi convincing su Daddy akan su barka ka yi aikin soja. I swear the danger in it is so unimaginable..” Mustapha yayi murmushi yace “Hey bros please don’t say that, wannan yana daga cikin abinda kayi mun wanda bazan taba mantawa ba a rayuwa na, I wouldn’t have achieved my dream if not for you” Muhammad ya girgiza kai yace “toh yanzu me zaka ce ma su Mummy?” Yace “Bazan fadi musu exactly what I am going there to do ba, lets just leave it as zanyi tafiya zuwa Maiduguri and that’s all” Haka dai suka cigaba da hira wanda kuwa Muhammad is not comfortable da facts din da shi Musty din yake kawowa na cancantar shi zuwa mission din. ♤♤♤♤♤♤ STORY CONTINUES BELOW EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Zehra dai tun qarfe bakwai ta iso office din. Suna tsaye a Kitchen din yayinda suke ta supervising komai ita da Hidaya. Hidaya ce tace “you shouldn’t have bothered ai Oga madam, everything will be in order” Zehra tace “I know Hidaya but I just have to support you guys, there is much that needs to be done” ********** Wuraren qarfe Tara ne wayar ta tayi ringing inda ta duba. Sunan shi ta gani yayinda tayi murmushi ta amsa. Ji tayi yace “My Angel ina ofis dinki” tace “toh gani nan” Mustapha dai sunyi da ita akan zai zo suyi Magana wanda kuwa Zehra bata san wacce Magana bace amma kuma haka kawai tunda ya fadi mata take jin hankalinta yana tashi.3 oh oh oh..🤔 Ta tarar da shi zaune a kan sofa na ofis dinta yayinda ya kwantar da kanshi a bayan sofa din. Idanuwan shi a rufe, da alama yayi nisa cikin tunani. Har ta zauna bai sani ba. Sai da ta dan taba hannun shi tace “Baby..” Da sauri ya dago kanshi yace “hey, yaushe kika shigo?” Tace “me ya faru ne na ga hankalin ka yayi nisa?” Murmushi yayi yace “nothing” Tace “Baby just tell me, I know something is wrong and its work related” Juyowa yayi ya fuskance ta tare da riqe hannun ta yace “My Angel please promise me you will never leave me” Cike da mamaki tace “Baby why are you saying this?? Ka sani cewar I will never leave you. You are my life fa, without you there is no Zehra” Lumshe idanuwa yayi yace “thank you” Yana riqe da hannun ta yace “I am travelling today, zan je Maiduguri” Gani yayi ta bata rai tare da zare hannun ta daga nashi ta dan juya. Cikin shagwaba tace “you told me cewar bazaka sake yin tafiya ba har sai tafiyar ka zuwa Italy which I believe tare zamu tafi Insha Allah, why now??” Ajiyar zuciya ya saki a ran shi yace “I can’t tell her I am going on a dangerous mission, can I??” Ayyah…hell no Gani nayi ya sauka daga kan kujerar ya koma gaban ta ya tsugunna. Zaro idanuwa yayi tare da fadin “subhanalillah, are you crying??” Zehra dai kamar dama jira take yi yayi Magana sai kawai ta qara fashewa da kuka. A cikin kukan ne tace “why do I feel like you are not just travelling but leaving me? Why do I feel like I am about to lose you?” Shi kanshi Mustapha abinda ke ranshi kenan. Haka kawai yake ji kamar zaiyi losing dinta. uhm uhm… the negative feeling though☹ Gani nayi ya zaro handkerchief daga aljihun shi sannan ya kai fuskar ta ya fara goge mata hawayen tare da fadin “hey relax, you are not gonna lose me” Ya dan yi murmushi yace “besides idan na je can aure zanyi da zakiyi tunanin losing dina??” Hararar shi tayi tace “aikuwa da na mutu idan na ji labari” Fashewa yayi da dariya tare da miqewa ya koma gefen ta ya zauna. Gani nayi ta karbi handkerchief din ta riqe yayinda yace “baki gama kukan ba kenan?” Girgiza kai tayi tace “I just feel like holding on to it, ka bani?” Murmushi yayi yace “duk wani abu da na mallaka naki ne my Angel, ni kaina naki ne sai yadda kika yi da ni” Bata san lokacin da tayi murmushi ba tace “toh yanzu yaushe zaka dawo?” Shafa kan shi yayi yace “honestly I don’t know, kuma the worst part of it is babu network a qauyen da zamu je” Zaro idanuwa tayi tace “qauye?? How can you survive staying in the village? Babu abinci mai kyau, babu ruwa mai kyau sannan ga sauro, maybe har electricity babu…” Shi kam kallonta kawai yake yi yayinda yake ji sonta yana ta zagaye jikin shi. A rayuwar shi he enjoys watching her, he derives pleasure in just watching her talk musamman idan tana masifa. A ran shi ne yace “its like she doesn’t even know the nature of my job for her to be saying this” gaskiya ga dukkan alamu bata sani ba.. Ji yayi tace “ka fadi musu kai bazaka iya zama a qauye ba, baka saba ba” Fashewa yayi da dariya yace “who told you that? I have gone to so many Villages My angel, it’s a great experience trust me. Yanzu dai so nake ki dinga yi mun addu’a har in dawo” A razane tace “mission zaku je??” Da sauri yace “no, kawai wani bincike ne” Tace “Alhamdulillah, har na ji sanyi. Toh yanzu how do we speak on phone??” Yace “kar ki damu idan na samu network I will always call you” Haka fa suka cigaba da hiran soyayya har kusan lokacin daurin auren Fadeela da Zain. Kiran Muhammad ne da ya shigo wayar shi ya sa shi saurin dubawa. Da sauri ya amsa yayinda ya ji Muhammad din yana fadin “guy kana ina ne? lokacin daurin aure ya kusa fa” Shafa kan shi yayi yace “yi haquri bros, Gani nan” Bayan ya kashe ne Zehra tace “na shiga uku, ka san na manta cewar Ya Moha ya dawo?? With everything that is going on I swear I just forgot” Murmushi yayi yace “hey we both know how busy you are plus nima fa bamu wani samu time munyi hira ba. Could you believe har yanzu ma ban fadi mishi about us ba??” Tace “haba?? Guess I have to introduce myself to him right??” Yana murmushi ya miqe tare da fadin “yes My Angel, I will let you do that before I return sai in bashi details”5 Yana riqe da hannun ta yace “God knows I will miss this beautiful lady” Tana shirin fashewa da kuka ne yayi saurin matse hannun ta tare da fadin “please don’t My Angel, trust me before you know it I will be back. I love you so much and please take care of yourself for me” yayinda ya dan ja kumatun ta. Ajiyar zuciya ta saki tace “I love you too My Baby, please take care too and don’t stress yourself a qauyen nan” Nikuwa nace mutumin da zai tafi yaqi..🤨 Yace “Insha Allah my beautiful angel” Har wurin motar shi ta raka shi wanda a nan ma sai da suka bata lokaci. Da qyar dai ta bar shi ya tafi wanda kuwa har ya fita gate tana nan tsaye. Aikuwa yana fita na ga ta ruga a guje ta koma ciki yayinda ta kulle kanta a ofis dinta ta koma kan kujera ta kwanta tana ta rusa kuka. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Hmmmm…