ZUCIYA CHAPTER 11
Sun isa gida Habib ya gangara yai parking, sannan suka fito, Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d’in ta. Habib ne ya matso kusa da ita yace ” Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. ” Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace ” da me fa? ” Nuna mata jakar bayanta yai, tai murmushi sannan tace ” ni ai ba kaya na d’auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. ” tana fad’a tai gaba. Habib ya bita da kallo, gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi. Little ce ta karaso tace ” yaya mun gode.” Ya rufe ido tare da yin mika yace ” Princess na gaji. ” Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace ” yaya kaje b’angaren su Asim ka kwanta. ” Kai ya girgiza mata yace ” a’a gida zan wuce, ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. ” Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad’i ya matso tare da sa yatsar sa ya d’ago kanta yace ” sai munyi waya.” Kai ta d’agamai, ya mika mata key yace ” Ungo kiba Ashraf zan d’auki motata nai gaba nima.” Ta d’agamai kai, tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba. Nafi kam tana shiga d’akinsu tai wani ajiyar zuciya tace ” Kai nayi Missing d’akin nan. ” Kaya ta shiga cirewa ta d’aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta. Little ce ta shigo, ta kalleta cikin shagwab’a tace ” kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? ” Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace ” Little wani irin so kikema Ya Habib? ” Little tace ” so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina.” Nafi ta tab’e karamin bakinta tace ” Shifa? ” Little ta fad’a kan gado, ta d’an mirgina tace ” Shifa haryanzu a kanwa ya d’auken.” Nafi ta girgiza kai a ranta tace ” Little nima matsalar dake damuna kenan, gwara kema banaji kinajin rad’ad’in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne sai dai yamin nisa. ” Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka. Ta dad’e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita. Sannan ta fito, bataga Little a d’akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser. Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai, ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci, Nafi ta kalleta tace ” Little ina kayana? ” Little ta bud’e mata inda ta jera mata nata kayan, Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta, nan ta zab’o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar, Little tai dariya tace ” ai dole kigafa dad’ewar da kikai bakizo ba, ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. ” Nafi ta harareta tace ” lokacin girman ne yazo, da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud’amin nawa anjima. ” Little tace ” ki d’auka mana, sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad’i ne saboda nad’an fiki kiba. ” Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci. Nafi ta kalleta tace ” Little ya gunsu Amarya?” STORY CONTINUES BELOW Little ta tab’e baki tace ” hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad’a kaca kaca. ” Cikin mamaki Nafi tace ” fad’a kuma? ” Little taja wani tsaki tace ” Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. ” Nafi ta tab’e baki tace ” ya suka kare to? ” “Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne, ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. ” Nafi ta d’an juya kai tace ” Na d’auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba? Indai har tana gudun b’acin ransa? ” Little tace ” Zigata akai ya Asim da Umma.” Nafi ta d’anyi karamin tsaki tace ” san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za’a zigata akan dukiyarsa.” Little tai ajiyan zuciya, Nafi tace ” yanzu fa? An bata ai nasan hankali ya kwanta. ” Little tace “Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d’aya ko ince wai ya ajiye kud’in a banki, to Yaya yabata kud’in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud’i kawai akace ba.” Nafi ta had’e rai tace ” shi kuma yayan me yace? ” “Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. ” Nafi ta kara tab’e baki tace ” Allah ya sauwake. ” Little ta amsa da Amin sannan ta d’aura da cewa ” kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b’angaren Amarya. ” “wa? Bada ni ba, inje in musu me? ” sukasa dariya a tare. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A b’anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane sai dai yanajin dad’in yanda yake fahimtar matsalolin ma’aikatansa tundaga kasa, yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d’in. Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa, sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa. Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki, yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe, da alama ma musu sukeyi, kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd’a kofar. Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci, Ashraf ya d’an zareta kad’an sannan yace ” Bari in shiga ciki..” Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya, shidai takaici ma hanashi magana yai. Yana shiga d’akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d’akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace ” Anie mekenan? Ba nace ki gyaramin d’aki na ba? ” Ta shagwab’e tare da kwantowa jikinsa tace ” kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. ” Ya kalleta cikin takaici yace “yau kwanan d’akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa, wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? ” Aneesa ta kara shagwab’ewa tace ” Hubby kayi hakuri zan gyara. ” Wani mugun kallo ya mata yace ” banaso fitarmin daga d’aki. ” Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had’e rai sosai, jiki a sanyaye ta fito, sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska. Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d’akin da kallo, ko sanda yana shi kad’ai baya barin d’akinsa haka amma yanzu ji d’akisa? Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai, bai dade ba bacci ya d’aukeshi. Bacci yai sosai harya makara sallar la’asar sai karfe 5 ya tashi, da saurinsa yai alwala ya fito masallaci. Sukam su Nafi ganin anyi sallar la’asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki, saboda kawar Little ce sosai, sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki. Anko suka saka, light purple d’in wani yadi ne, shiba lace bane sannan ba material bane, riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d’aurama Nafi sannan ta d’aurana kanta, Nafi tace ” amma ankon yayi kyau. ” Little tai murmushi tace ” kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. ” Nafi ta jinjina kai sannan tace ” Farin mayafi zamusa? ” Little ta girgiza kai tace ” a haka zamu. ” Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace ” taya zamu fita a haka? ” Little tace ” haka ake yi ai in ma mun d’au mayafin sai dai mu rike a hannu. ” Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace “ni dai da wannan zani. ” Little tace ” to. ” Sun fito abin sha’awa dan hatta takalminsu iri d’aya ne, sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi, kamar yanda nace Nafi ba fara bace can sai dai tana da kyau gashi batada jiki. Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud’in liki inji Little. A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta, yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya bud’e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba. Ganin d’an wake yasa ya gane dalilin kiran, zubawa yai yafara ci kenan, Little tai sallama, amsawa yai saidai bai d’ago ba, lokacin Mumy ta tashi daga falon, wata sallama ya sakeji bayan ta little sai dai wannan muryar cikin sanyi take. Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d’auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba. Little ta karaso cikin murna tace ” Yaya kaine anan? ” Nafi ta kalleshi ta baya gabanta yai wani fad’uwa yaushe rabon data ganshi, Ashraf ya kalli Little yace ” ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had’u a wani gun. ” Ta rike hab’a tace ina na isa yaya? Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai muna takura muku nikuwa ina zaka ganni? ” Baiyi magana ba, tace”Mumy fa? ” Ya ce tana ciki, da sauri Little tai ciki. Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace ” Yaya ina wuni? ” Juyowa yai dan ganin mai magana, kallan mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa…. She can’t be. Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata, tai hanyar waje, dasauri yace ” Ke! ” Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace ” ke! ” Nafi dai tana tsaye bata juyo ba, a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad’a yace ” ba dake nake ba? ” Nafi ta juyo fuska a had’e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace ” ganinai ba sunana kenan ba.” “mene? ” Nafi tad’an burtso baki, kallan mamaki ya mata yace ” Ba Nafisa bace? ” Ta kara had’e rai ta kalleshi tace ” au kama mantani? Ka d’aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? ” Ta juya cikin takaici zata wuce, da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tamai, tace ” Yaya mai kake yi? ” Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad’a a ransa, a fili yace ” ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. ” Ta d’ago ta kalleshi sai dai batai magana ba, yace ” wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? ” Tace ” menai kuma? “yanda tai maganar yasa yace “Lalai yarinyar nan. ” Kokarin kwace jikinta tai tace ” ni ba yarinya bace. ” Ya saketa tare da cewa ” ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. ” Ta juya kanta gefe tace ” nemana akeyi?” Ya koma ya zauna yace ” ina zaku haka? ” Biki zamuje. Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan. Mama ne ya kamashi yace ” lalai yarinyar nan, yaushe ta girma haka? Gaba d’aya tama canza kamar ba Nafin riga ba.” Itakam tana fita tai d’akinsu, a falo ta zauna ta matse hannayenta, jikinta sai rawa yakeyi, meyasa suka had’u? A can Little ta ganta falo zaune ta kifa kanta, ajiyar zuciya Little tai tace ” Feena meye hakan? Mun taho tare shine zaki taho nan ki barni. ” Nafi ta d’ago ta kalleta sannan tace ” Sry My Little wlh jinai kaina na d’an sarawa. ” Cikin damuwa Little tace ” ayya! Sannu, ko zaki hakura da zuwa? ” Kai Nafi ta girgiza tace ” Muje nima ina san zuwa ai, kuma kan yama daina. ” Nan suka mike Nafi ta kara gyara fuskarta sannan suka fito, sunzo shiga mota shikuma ya fito daga b’angaren Mumy, yana kallansu har suka shiga ya d’an yi wani smiling yace ” lalai yara sun girma.” abinda ya fada kawai kenan yai gaba. Su kuma suka shiga motar Little ‘yar karama wanda Kawu ya sai mata wai murnar gama secondary. ¤¤¤¤¤¤¤ Umma na zaune kusa da Asim acan kuryar d’aki, Asim ya nisa yace ” Umma tanashan maganin nan kuwa?” Umma tai murmushi tace ” Ai tunda muka bata magani tai b’arin nan na tsoratar da ita akan in har ta haihu yanzu da Ashraf to fa lalai wulakantata xaiyi dan kuwa maza basasan mace mai saurin haihuwa.” Asim yace ” to kidai tabbatar tanasha dan kuwa in har ta haihu da Ashraf to fa komai bazai yiwu ba, bazata taba bamu hadin kai ba, sannan muma in muka halaka Ashraf bayan mun amshe company d’insa da sauran dukiyarsa in har abinda aka haifa ya girma ya gano nan ma kinga akwai matsala. ” Umma ta jinjina kai tace “karka damu da wannan amma nikam har yanzu fa hankalina bai kwanta da wannan wasiyar da ya bata ba. ” Asim ya kurawa kasa ido, sannan can yace ” karya yakeyi ai ni da farko na yarda sai da naga wani murmushi da Kawu yai bayan ta kawomai haka kawai jikina yaban ba haka bane, sai daga baya nai tunani ta ina mutumin da zai mutu zai bar wasiyar kud’i kawai???? ” Umma ta jinjina kai tace ” nima yanda naga babanka nayi ne yasa nasan ba haka bane sannan nasan halin Yaya sarai bazai bada kudi kawai haka ba. ” Nan suka cigaba da kule kulensu….Nikam nace Allah ya kyauta dama ita zuciya kowa da irin tasa. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su Little kam an d’auko Amarya suka wuce inda za’ai event d’in, suna tafe ana hira saboda duk kawayene, Nafi ma yanzu bata kunyar shiga hira, har suka isa. Guri yayi kyau bayan Amarya tazo ne aka fara gudanar da shagalin biki, Nafi tana zaune daga gefe ganin yanda ‘yan mata keta rawa su Little ma an zake sosai, Nafi dai tana gefe rike da wayar Little tana dadanawa, tunanin kiran Ferry ne yazo mata, nan ta mike ta d’an matsa kadan daga inda ake shagalin. Daga can ferry ta d’auka nan suka shiga hira, tana nan a tsaye suna waya sai dai suk sanda ta kalli gun idanunsa na kanta, hakan yasa ta fara tsarguwa, daga gani shima gun bikin yazo yana zaune akan motarsa. Ganin kallan ya fara isarta yasa ta matsa daga gun, bayan sun gama waya Nafi ta juya da shirin komawa. Ganin mutum tai kawai a bayanta tana juyawa suka hada ido, Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace ” Malam lafiya? ” Wani lalausan Murmushi ya sakar mata sannan yace ” Aminci Allah su tabbata a gareki. ” Ta kalleshi cikin mamaki sannan ta d’an motsa baki a hankali tace “tare da naka, amma….. ” ” Shiiii dan Allah karki koreni kar kuma ki nuna bakya sona daga gani na yau d’aya.” Nafi cikin mamaki ta kalleshi, sai dai har kasan ranta yaso sata dariya yanda yai, ya cigaba da cewa ” Sunana Al-Amin masoyin wannan yarinyar. ” STORY CONTINUES BELOW Juyawa tai bayanta dan ganin wace yarinyar, ya sakar mata murmushi yace ” ina kike dubawa bayan gatanan a tsaye. ” Nafi ta harareshi yanzu kam ta gane da ita yake, ya d’an rike kunnuwansa yace ” Tuba nake ranki ya dade da alama na b’ata miki rai. ” Nafi batasan sanda tai murmushi ba tace ” ba wani b’ata rai sai dai kayi hakuri ni matar aurece. ” Gani tai ya hau dariya, ya kalleta yace ” matar aure? Wow na gode da alama da wuri zamuyi aure in killeceki a d’aki.” Nafi ta makamai harara, da sauri ya kara rike kunne, yace ” Taya zakice min ke matar aurece? Ina mijin? ” Shiru Nafi tai a ranta ta ce ” inafa yake? Yana can gun matarsa. ” Al-Amin yai murmushi yace ” please ki amince dani, zan kula dake yanda bakya tunani, ni d’an Katsina ne, sannan kanwar maman yarinyar da ake aurenta ne. ” Nafi ta kalleshi sannan tace ” lalai yayi kyau.” Hannunsa ya had’e guri d’aya yace ” Dan Allah sunanki?????? ” *FEENAH* abinda ta fada kenan, yace “wow nice name, a ina kike? ” Ta juya kai tace ” zan koma ciki. ” Bata jira amsarsa ba ta fara tafiya, Biyota ya fara yi sai data juyo tace ” dan Allah Al-Amin ka kyaleni. ” Kansa ya shafa yace ” kai!!! Naji dadi dan sake ki kiran sunana.” ta kara harararsa sannan ta juya. Taji dad’i sosai dataga bai biyota ba, haka kawai taji ta saki murmushi. Sai da aka gama, wajen isha’i sannan suka fito zasu tafi, suna fitowa ya taso ya karaso gunsu tare da musu sallama, Little ta amsa tana mai kallan sani sai dai ta rasa a inane, yace ” Little manya, can na ganki ai kinata rawa ana bikin Aminiya. ” Little ta nunashi da yatsa tace ” Ya Al-Amin.” “Bingo!” ya fad’a yana murmushi, itama murmushin tai tace ” Ya Al-Amin ace kaine, nifa ince na rasaka sam ashe ka zama babba ko a hanya na ganka zanyi wahalar ganeka. ” Ya harareta yace ” Haba Little a gaban Swt Feenah kike fadar hakan? ” Ta kalleshi sannan ta kalli Nafi data juya kanta, tace ” yaushe ka ganta?” Yace ” gatannan sai wulakantani take ashe kawarki ce.” Little ta kalli Naf tace ” Feena d’an uwan namu kike wulakantawa? ” Nafi ta kalli Little kamar zatai kuka, yace ” wlh ina zuwa na ajiye su Hajiya na dawo dan in kaita gida ” Nafi ta harareshi tace “cewa nai zan bika? ” Ya kara had’e hannayensa yace ” Little please.” Little ta juya da sauri ta shige motarta taja tai gaba tana dariyar mugunta. Nafi ta saki baki tana kallan Little cikin mamaki, Al-Amin ya kalleta yace ” Cwt Feena da alama dai nid’in nan nine zan kaiki. ” Ta juya kai cikin takaici tace ” da wayace kazo nan ma. ” Yace ” Matata tana guri ba dole inzo ba?” Nafi ta kalli agoggon hannunta karfe 8 ga gun duk ba mutane, katseta yai da cewa. ” Please Cwt Feenah ki taimaka, ai indai gidansu Little ne na sani. ” Nafi ba dan ranta yaso ba ta karasa gun motar ta shiga rai a b’ace, tana shiga ya zuge glass tare da kunna mata AC, itakam kanta ta maida gefe tana kallan waje. Sun fara tafiya shi kad’ai yake mata magana, ganin batada niyyar kulashi yasa yai shiru. A daidai kofar gidan yai parking, a wannan lokacin kuma, Ashraf ya fito kenan zai fita, kallan motar yai cikin mamaki, har zai wuce sai yaga alamar mace ce a ciki, badai Little bace? Abinda yazo mai kenan, hakan yasa ya ja motar yai parking a gefe. STORY CONTINUES BELOW Itakam Nafi tazo fita yasa lock cikin mamaki ta kalleshi ya kashe mata ido sannan yace ” Cwt Feenah shikenan bako sallama?? ” Nafi ta d’an turo baki tace” in na fita ai zan ma. ” Kai ya girgiza alamar a’a sannan ya mika mata wayarsa yace “a’a na yafe numberki kawai nakeso. ” Ta d’anyi murmushi tace ” sry Al-Amin sai dai banida waya. ” Kallan mamaki ya mata yace ” mene? Shikenan wato dan bakyasan ki bani mumber ki shine zaki fad’i haka? ” Kai ta girgiza alamar a’a tace “wlh ba haka bane, banida itane. ” Kallan mamaki ya mata, shikam Ashraf ya cika fam, me Little take a cikin mota har yanzu? A zuciye ya fito yazo kofar da take shikuma daidai lokacin Al-Amin ya cire sim d’insa na Mtn ya bar glo ya mika mata wayar yace ” ga tawa akwai sim a ciki ba wanda yasanni da sim d’in ni in na fita nasai wani….. ” Kallan mamaki takemai, zatai magana sukaji an kwankwasa glass d’in motar, inda take, Al-Amin ya zuge cikin mamaki. Cikin tsananin mama ki Ashraf ke kallan Nafi, ransa yakai kololuwa gun b’aci, itakam tunda ta ganshi gabanta ya shiga fad’uwa. Al-Amin ne ya katse mugun kallon da yake mata yace ” Yaya Ina wuni? ” Wani kallo ya bugamai batare da ya amsamai ba, ya kalli Nafi cikin tsananin takaici yace ” kin fito ko sai na karya ki? ” Motar ta bud’e zata fita Al-Amin ya sake cewa ” Cwt Feenah gashi. ” Juyowa tai ta kalleshi haka kawai taji tanasan ansar wayar yanzu a gaban Ashraf, hannu tasa ta amsa sannan tace ” Nagode kawai tai waje. ” Ta gabansa ta rab’a ta wuce haryanzu gabanta fad’uwa yake, Ashraf ya bita rai a b’ace, hannu yasa ya riko ta da karfi yace ” abinda aka koya miki kenan a makarantar??? ” Idanunta ne suka dan ciciko ta daure tace ” me nayi yaya? ” Yai wani murmushin takaici yace ” me kikai? Ke harkin kai ki zauna a motar namiji ku zuge glass? Ku kuma dade a ciki? ” Nafi wacce hannunta ke mata rad’ad’in rikon da ya mata tace ” kawoni yai daga gun biki.” Xaiyi magana yaga hawaye sun zubo mata cikin rawar murya tace ” Yaya hanuna. ” Kallan hannunyai sai a lokacin ya kula da yadda ya matse mata hannu sosai ga agogo agun, nan ya sake mata hannu, agoggon kuwa har ya ji mata ciwo, mamakin kansa ya shiga yi. Ya juya da sauri ya shiga motarsa ba tare da ya kalli inda take ba, Nafi kam agoggon ta cire tabi ciwon da kallo lalai ta yarda Ashraf baya ko digon santa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ta juya a hankali tai ciki. Tana shiga ta cilar da wayar akan gado tana kallan Little tana mata dariya, ta wuce toilet. A gaban madubi ta tsaya bayan tayi alwala ta kalli kanta a cikin ranta tace “dama kema kinyi laifi tun farko, kinfi kowa sanin Ashraf yafi karfinki meya kaiki???? ” Hawayenta ta share sannan ta fita jiki a sanyaye….. Bayan tayi sallah little ta dameta da zancen Al-Amin itakam shiru kawai tai, dama bata kunna wayar ba balle ma ya kirata. Ganin taki kulata yasa itama Little d’in tai shiru, itakam Nafi kwanciya tai kamar mai bacci sai dai ranta fal yake da tunani kala kala. Shikam Ashraf yana shiga mota yai wani huccin takaici, meye nashi na zakewa haka? Wata zuciyar tace to yarinyace karama ko karatu bata gamaba ko kunya ace tana xama da saurayi a mota? Ai amanace ita agunsa shi ya d’aukota daga wani garin dolene ya kulada ita kafin mazan zamani su hure mata kunne. Ya d’an bigi sityari kadan yace ” me yasa nai haka agaban wannan yaron? Salan ya rainani? Ya kara jan tsakin takaici, haka ya gangara gun abokinsa nagun aiki dazai amshi takardu ransa duk a jagule……. Washe gari Nafi bayan ta tashi daga bacci ta fita zuwa kitchen nan suka gaisa cikin farinciki da kewar juna, ta zake ta shiga tayasu aiyukan girki. Sun gama ta fito kenan sukai kicibis da Umma, had’e rai Umma tai tace “ke wacece a kuma wani dalili kiika shigo mana kitchen? ” Nafi tad’an rusuna kad’an ta gaisheta sannan ta mike tsaye tace “Umma baki ganeni ba? ” Umma ta kar had’e rai, Nafi tace ” nice fa Nafi. ” Umma ta kara kallanta ba shakka itace, ta d’an harareta tace ” uban me kike anan ba dama kina makaranta ba?? ” Nafi tace ” ai dama ana hutu nice dai kawai ban dawo ba. ” Umma ta kara had’e rai tace ” to yanzu gulma ce ta dawo dake ko me? ” Nafi kam murmushi ta saki dan itakam bataji haushin kalaman Umma ba ta kalleta tace ” Umma na shiga ciki. ” Ran umma ya b’aci ganin yanda yanda yarinyar ma ba a kula ba, gashi tasan yarinya da take ‘yar riga yanzu ta girma? Gashi dai ba wanka tai ba amma gata tsaf, ba kamar wannan kucakar tada ba. { (Anan ne zan dakatar da wannan littafin nawa mai taken Zuciya kowa da irin tasa, ina fatan zaku jirani zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.) (Yanda zamu fara azumi lafiya Allah ubangiji yasa ku gama lafiya, ya kuma bamu ikon yin ibada batare da gajiyawaba, ya karemu daga duk wani abu dazai d’aukemana hankali agun ibadaunmu, ya yafemana kura kuranmu, ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.) Ameen suma Ameen….. Umma ta juya cikin takaici da niyyar lalai sai ta sa a kori yarinyar nan kafin ta zamar musu masifa.+ Nafi kam har tayi gaba ta tsaya tare da juyowa tabi Umma da kallo, kai ta girgiza ta juya zata wuce ta hango Asim ya nufo Umma da sauri kamar zai fad’i da kasa, kallan yanda yake baza sauri take da alama akwai magana da yake san isarwa cikin gaggawa shi yasa yake wannan saurin. Umma tana hangoshi da ganin yanayinsa yasa tai hanyar b’angarenta da sauri itama, Nafi har ta juya zata koma d’aki taji sam hankalinta ya kasa kwanciya, a hankali ta tako tazo wajen b’angaren Umma sai dai ta rasa tayayya zatai karyar da zata shiga? Shiru tai ganin ba halin shigan yasa ta juya da niyyar komawa, Asabe mai aiki a kitchen ta hango ta nufo gun rike da tire babba da kuloli akai, Nafi ta karasa gunta da sauri tace ” Asabe ina zuwa?” Asabe tace ” Umma zan kaima kumallon ta.” Nafi ta amshi tiren tace ” Barshi ni bari na kaimata dama ciki zan shiga.” Cikin rashin damuwa Asabe ta bata tare da kad’a kanta ta koma inda ta fito, Nafi kam da sauri ta nufi kofar Umma, gabanta kam sai dukan uku uku yake saboda tsoro sai dai ta rasa dalilin dayasa zuciyarta keta tunzurata akan lalai ta shiga. Murd’a kofar tai a hankali ta shiga da sallaha itama ciki ciki tayi ta. Batai mamaki ba dan dama batasa a ranta za ta gansu a falo ba, nan ta wuce cikin tsoro ta ajiye tiren akan dinning sannan ta kalli d’akunan dake falon guda biyu, a ina suke???abinda ta fad’a kenan a ranta. Lalab’awa tai ta karasa d’akin farko,tare da sa kanta a jikin kofar kamar munafuka, jin alamun rashin mutum yasa ta karasa d’ayan, zuciyarta sai kara tsananta take da fad’uwa wannan karan bata sa kanta a kofa ba tana zuwa jikin kofar d’akin taji cikin fad’a wanda yasa ta tsorata taji Muryar Asim yace ” Umma nikam bakin ciki kasheni zai yi dan nikam indai har na cigaba da ganin Ashraf to fa lalai inaji ni zan bar gidan nan.” Gaban Nafi ne ya yanke ya fad’i me kenan? Ta fad’a a ranta. Kafin ta nemo amsar tambayarta taji Umma tace ” ni d’in ce maka akai farin ciki nake in na ganshi? To amma ya zakayi….???” Cikin fad’a Asim ya katse Umma da cewa ” Yanzu sam ‘yan gun aikinmu basa karramani magana ma ba yimin suke ba, sannan yanzun nan abokina na gun aiki ya sanar dani cewa shareholders na company d’in sun yi meeting akan a dawo da Ashraf matsayina inyaso ni sai a ragemin matsayi, nifa wlh in bakuyi wasa ba zanyi aika aika.” Umma ta gyara zama tace “Asim kayi hakuri abi maaganar nan a hankali.” Cikin zafin rai yace. ” a hankalin me? Ni wlh har yan daba na kira kafin nazo nan na sanar dasu inya fito aiki anjima su tareshi su kawar mun da numfashinsa.” Jikin Nafi kam rawa kawai yakeyi, har tsuma takeyi saboda tsananin tsoro da fargabar abinda yau kunenta yake jiye mata. A tsorace ta juya cikin tsananin tsoro da firgici tai waje har kafarta na hard’ewa ta fad’i kasa. A d’aki kam Umma ta kalli Asim tace ” Asim yau lahadi naga ba aiki?” Asim yai wani murmushi yace ” ai shi zai je saboda akwai wani project da sukeyi shi da ‘yan team d’insa.” Umma tai ajiyar zuciya sannan tace ” baka ganin anyi gaggawa in aka mai illa tun yanzu? Asim yai tsaki yace ” Illar me? Shima Abban ai yafi kowa san Ashraf ya mutu.” STORY CONTINUES BELOW Umma ta jinjina kai sannan tace ” Aneesa fa?” Asim ya kara jan tsaki yace ” kyale wannan in ya mutu taji ta cafki dukiyaa a hannu kina ganin zata damu?” Umma tai murmushi sannan tace ” duk da Neesa na tsananin san Ashraf banaji tana sansa kamar yanda takesan kudinsa dan na tabbata da bashida komai duk sanda takemai bazata tab’a aurensa ba.” Asim yai kwafa yace ” Ni wlh na tsani ma na gansu tare, nifa inaji duk duniyarnan ba wanda na tsana kamar yaran nan.” Umma ma tai tsaki tace ” ai nima dashi da uwarsa sune mutanen dana tsana kaf duniyar nan.” Nan suka zauna suka cigaba da sake sakensu. Nafi kam dakyar takai kanta falon b’angarensu, ta zauna akan kujera har yanzu jikinta rawa yake, sam kwakwalwarta ta kasa d’aukan abinda ta jiyoma kanta. Dif taji kwakwalwarta ta d’auke sam bata tunanin komai sai da wasu dakiku suka shud’e sannan taja wani dogon numfashi sannan ta mike a zabure tace ” Ya Ashraf????” Jitai idanunta sun kawo kwalla ace d’an uwanka na jini???wannan wace irin rayuwace???? Sanar dashi zatai?? Zai yarda da abinda zata fad’a??ko Little zata fad’ama??kai ta girgiza tace”kar itama in tada mata hankali…” Wata zuciyar tace Mumy fa???kai ta girgiza da sauri tace ” Mumy kuma da wani idan zata zauna dasu??” Kanta ta dafa dataji ya sara, can tace ” Kawu fa???” Hucci ta saki cikin damuwa tace ” shikuma matarsa ce da d’ansa.” Kan kujera ta fad’a wasu hawayen suka sake zubo mata, Ya Ashraf me kai ake neman halakamin kai???ta fad’a cikin wata irin murya mai ban tausayi. Agoggon bango ta kalla karfe tara, karfa Ya Ashraf ya fita??? Da sauri ta mike kawai ta nufi b’angarensa, hankalinta bai tsaya ba sai da ta isa kofar b’angarensa, me zata cemai??? Shiru tai ta tsaya agun kamar abu mara motsi, dan batada amsar tambayar nan. Tana tsaye ba mafita har dakika goma suka shud’e, motsin bud’e kofa ne yasa ta dawo hayyacinta, idanunta ne suka firfito cikin tsoro, ta kalli kofar. Ashraf ne ya fito, jitai gabanta ya fad’i cikin mamaki ya kalleta, sai dai kafin yai magana sai ga Aneesa ta fito rike da jakarsa, fuskarnan tata a had’e da alama ranta a b’ace yake. Cikin mamaki itama ta kalli Nafi, “Malama wacce ce ke? Me kuma kike anan?” Nafi ta had’iye yawo cikin tsoro ta kalli Ashraf, shima kallan mamaki yake mata, Aneesa ta kara kallantaa yanzu kam kallan rashin mutunci ta mata. Tace ” Ke malama wacece ke? A wani dalilin kikazo min kofar miji??” Nafi kam jira take Ashraf yai magana sai dai abin haushi gani tai ya d’auke kansa, tare da amsar Jakarsa zaiyi gaba, jitai idanunta sun fara cikowa ita gani take ai ya kamara Ashraf ya sanar da Aneesa, ganin ya fara tafiya ga tana so ta tsaidashi daga fita waje, sannan ga Aneesa ta tsareta da ido yasa duk ta rikice. Shikam Ashraf haushin abinda tai jiya da daddare ne yasa yaki kulata, Aneesa ta bud’e baki zatai magana kawai Nafi tai baya luuu jikake ta zube a kasa, wannan ita kadai ce mafita a gareta abinda ta fad’a kenan a ranta tare da runtse ido. Aneesa ta d’anyi kara tare dayin baya cikin tsoro, hakan yasa Ashraf ya juyo da sauri, cikin rud’ewa yasa ya karaso inda take, sannan ya d’agota tare da cewa ” Nafeesa!!Nafeessa!!.” Sai a lokacin Aneesa ta gane waccece, kallan Ashraf tai duk ya wani rud’e haushi da kishi suka kamata a zuciye ta matso tace ” Aljanu ne da ita??” Ran Ashraf ya b’aci ganin yanda tai maganar cikin rashin kulawa, yace ” bishiyar kuka ce a kanta…” Ya mike a zuciye ya d’agata ya nufi mota da ita, Nafi kam haryanzu gabanta bai bar fad’uwa ba tanaji ya bud’e bayan mota ya sata a ciki.3 Tanaji ya bud’e gaban mota ya shiga, ya tadata tad’anyi zafi sannan yaja motar suka fita, suna fita daga gate d’in gidan sai taji yace ” Will u get up now?” Idanunta ta kara runtsewa a ranta tace ” badai dani yake ba?” Ashraf ya kalleta ta madubi sannan yace ” abinda kika koyo a makarantar kenan? Pretending??” Nafi kunya da takaici duk suka kamata ta kara danna kanta kujera, gefen titi ya gangara yai parking sannan ya juyo ya kalleta yace ” Kin tashi ko sai na fitar dake waje da kaina?” Nafi ta mike zaune tare da zunburo baki gaba kanta na kasa, ya kura mata ido yace ” me kike san fad’amin?” Kallan mamaki tamai, tace ” ya akai kasan abu nake san fad’a?” Kallanta yai sannan ya kalli window yace ” inba abu kikesan fad’amin ba me zai sa kizo b’angarena kinsan inada mata kizo ki tsaya a waje?” Baki ta tab’e a ranta tace ” da cewa nai bakada mata?” Ya kalleta sannan taji yace ” da alama kin manta inada mata inba haka ba mezai sa kije b’angaren? Ai sai ki kirani a wayar Little ko ta saurayinki.” Nafi ta saki baki tana kallan sa tace ” to ni menace?” Ya juya kai sannan yace ” Ki tambayi abinda kika ce a zuciyarki.” Nafi tai shiru rai b’ace. Ashraf yace ” to fad’amin? Menene?” Nafi tai shiru tare da maida kanta kasa. Ashraf ya kara had’e rai yace “zan saukeki fa inja motata inyi gaba ko ce miki akai banda abinyi??” Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, cikin wani irin murya tace “banifa da lafiya, xaka saukeni.” Wani murmushi ya saki na rainin hankali yace ” harda karya kika koyo a makarantar? ” Ta kalleshi sannan ta d’an shagwab’e murya tace ” nifa Yaya ba karyar dana koyo.” Har cikin ransa sai dayaji wani abu, sai dai ya sake dakewa yace ” ke jiranki nakeyi ko?” Nafi ta kalleshi tace ” Yaya dan Allah kar kaje gun aiki yau.” Kallan mamaki ya mata yace ” bangane ba? Ke harkinkai matsayin da zaki hanani abu?to ko Aneesa bata samu wannan matsayin ba.” Nafi ta kalleshi cikin wani yanayi tace ” Na sani Yaya banida wannan matsayin kuma ban kai kaina wannan gun ba, sai dai ba dan nibaaa ba kuma dan halina ba sai dai ka duba darajar Allah ka hakura da zuwa aikin nan yau.” Ta karasa magana tare da kawar da kanta alamar idanunta nasan kawo kwalla, kallan mamaki yake mata, sai dai yanzu yasan tabbas da wani abun…….