ZUCIYA CHAPTER 12
Yanda yake kallanta yasa ta had’e rai tare da maida kallanta wajen window, itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma ‘yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata tsauri.+ Ga mamakinta jitai yace ” tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida.” Nafi ta kalleshi a tsorace tace ” Sauka zanyi a haka??” Kai ya d’aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace ” taya zan iya fita ahaka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud’in da zan tafi da kaina.” Ya d’aga mata kafad’a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b’aci a zuciye ta matsa da niyyar bud’e kofa, har ta zura kafa d’aya zata fita sai taji yace ” shigo in ajiyeki ba dan halinki ba inada abinyi.” Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud’e kofa zata fita sai kuma ta juyo tace ” Yaya ina zaka?” Kallanta yai yace ” banaji wannan yana d’aya daga cikin damuwarki tunda dai baki fad’amin me kike nufi da kar inje aiki ba, kin kuma san halina ba a sani abu.” Nafi ta kalleshi cikin kulawa tace ” Yaya tunda kaga na furta hakan ai kasan da dalili, in ba haka ba meye nawa da zance karkaje aikinka?ni ba matarka ba?” Juyowa yai ya kalleta kalamanta na karshe sun tsayamai a wuya, sai dai ya share yace ” ke nake jira zan fita ko?” Nafi batasan sanda wani takaici ya kamata ba ta kafeshi da ido na takaici, kallanta yai sannan ya juya ya d’au wayarsa, bakin ciki ya hanata d’auke idanunsa daga kansa jitai ya tada mota, alamar zan tafi, takaici yasata ta fito daga motar a zuciye tana kallo yaja motarsa ya tafi, tabi motar da kallan takaici. Wannan wani irin mutum ne, duk yanda na damu da rayuwarsa amma shi ko a jikinsa?? Sai ma rashin mutunci ne zai biyo baya?. Sam ta kasa d’auke idanunta daga hanyar daya wuce, jitai an dafa ta a firgice ta juyo, Mumy ta gani tsaye itada Little. Nafi tai saurin share kwallarta sannan ta kakaro murmushi tace ” Mumy ina kwana???” tafad’a tare da risinawa, mumy ta amsa sannan tace ” Nafi me kike yi anan? Little duk ta damu tanata nemanki?” Nafi ta kalli Little sannan tai murmushi tace ” Ayya My Sisto tuba nake.” Little ta harareta sannan ta juya tai b’angarensu, Mumy ta kalli Nafi databi bayan Little da kallo tace ” Nafisa ina kika je???” Nafi tai kasa dakai, Mumy tai murmushi sannan tace ” shikenan, kije gun ‘yar uwar taki dan hankalinta ya tashi.” Nafi ta d’aga kai sannan tai bayan Little da sauri. A tsaye ta ga Little ta cire kaya daga ita sai towel da alama wanka zata shiga, Nafi ta karasa gunta ta zauna akan gado tana kallan Little wacce ta had’e rai. Nafi tai murmushi tace ” Little bazaki kulani ba?” Little ta juya tai hanyar toilet, tanaji Nafi ta kara cewa ” My Sisto tuba nake kinji kiyi hakuri.” Little ta wuce toilet ba tare da ta amsa mata ba, nan Nafi ta mik’e ta gyara d’akinsu ta gama shara kenan Little ta fito, Nafi ta kalleta zatai magana taji Little tace ” ki je kiyi wanka Yusra tun d’azu take kira wai dan Allah muje yanzu.” Nafi ta mike ta karaso gun Little ta rungumeta tare da cewa ” Little wlh wani abu ne ya taso min dayai gaba da duk tunanina.” Little tace ” Shikenan Feena ni kin barni anan cikin tsoro tunda na tashi naga banganki ba na kuma fita kaf na zaga ban ganki ba.” STORY CONTINUES BELOW Nafi tace ” Sry nayi laifi.” Murmushi sukama junansu, nan Nafi ta saketa sannan itama tasa nata towel d’in ta nufi toilet, har taje zata bud’e kofar ta juyo tace ” Little nikam a iya sanina ba wata matsala dake tsakanin Mumy da Umma ko?” Little ta kalli Nafi tace ” Feena kenan, a haka dai kamar babu, sai dai inaji a jikina kamar da wani abu.” Nafi ta kalleta tace ” kamar me??” Little ta d’an tab’e baki tace ” kinsan a duniya in har akace kud’i to fa an gama komai, kud’i da kike ganinsu sune matsalolin komai na rayuwar duniyar nan, duk wata matsala inka dubashi daga kasa to fa lalai zakiga kud’i shine silar komai.” Nafi ta shiru tana mamaki, can tace ” Amma dai nan banaji za’ai fad’a akan kud’i ko? tunda dai naga kowa yanada shi.” Little ta furzar da iska sannan tace ” Feena kenan ai a gidan da ake da kud’in anfi samun matsala akan kud’in tun balle in dukiyar da mai ita.” Nafi ta mata kallan mamaki, Little tai murmushi sannan tace ” share kawai.” Jiki a sanyaye Nafi ta shiga wanka, sam wanka take amma tanata nanata kalaman Little dukiyar da mai ita? Kawu kenan? To in shine meye na neman kashe Ya Ashraf?” Ta dad’e kafin ta fito, tana fitowa taga Little ta ciro musu dinkin Less anko ne shima, Nafi ta zauna itama ta fara shafe shafe. A b’angaren Ashraf kuwa yana fita daga gidan ya nufi gidan abokin babansa ko ince lawyer d’in babansa, bayan sun gaisa yace ” dama so yake ya d’auki mota d’aya daga cikin motocinsa dake gidan. Nan ya d’auko masa keys d’in Ashraf ya d’au d’aya sannan sukai sallama ya fita. Hanyar Company d’insu ya nufa, yasha kwanar karshe ya hango wasu mutane kusan su goma a cikin wata katuwar mota baka kirin sai dai sun sauke glass d’in motar sannan wasu sun zuro kansu suna duba hanya, bakaken kaya garesu haka kuma baza’a ganesu ba saboda tabarau baki dake fuskarsu. Ashraf ya rage gudu dayazo kusa dasu, sam sukam sun d’auke kai daga kallan motarsa ganin ba irin ta bace wanda aka basu umarni. Hakan ya bashi damar ganin yawan mutanen dake ciki, sannan ya wuce, lalai ya tabbatar shi suke nema saboda yazo giftawa yaji wani yace “wai ya haryanxu banga mota kirar Marcedes_Benz C300, wai ya tabbatar nan zai biyo??” Ashraf ya giftasu zuciyarsa fal da mamaki, meke faruwa? Me Nafeesa ta sani? Me taji???? Ya karasa gun aikinsu nan ya tadda ‘yan team d’insa sun dad’e da zuwa, nan ya zauns suka fara abinda ya kawo su. Su Nafi ansha kwalliya, suna fitowa Habib na yin parking, tundaga nesa Little ta hangoshi ta saki wani lalausan murmushi na farinciki, Nafi ta kalleta sannn ta kalli inda take kallo ganin Ya Habib yasa tai murmushi itama tace ” Little a dinga kokarin dannewa irin wannan nuna soyayya kirikiri haka??” Little ta harareta sannan tace ” haka nace miki?” Nafi ta d’an rangwad’a kai tace ” Little kenan.” Juyowa yai shima ya hangosu, nan ya tsaya tare da kurawa Nafi ido, gaskiya yarinyar nan type d’insa ce ba karya, har suka iso gun yana kallanta, Nafi ta d’an had’e fuska tare da kawar dakai ge. Little ta matsa gunsa tace ” Ya Habib daga ina haka?” Idanunsa nakan Nafi yace ” wlh wucewa nazo yi shine na shigo.” Little ta kalli Nafi dan taga yanda yake kallanta, sai dai bata kawo wani abu ba tace” Nafi tayi kyau ko yaya?” Habib yai murmushi yace ” Sosai ma kuwa.” Nafi ta matsa daga saitinsa sannan tace ” inafa wani kyau dan kowa yaganki yasan kece kikai kyau.” Ta fad’a tare da cewa ” Ya Habib ko ba haka ba?” Ya kalli Little kunya tad’an kamashi yai wani murmushin burin kunya yace ” dama ai Princess daban ce.” Little ta saki murmushin farin ciki. Little ta kaleshi cikin kauna tace ” Ya Habib yaushe zaka tafi?” yace ” zuwa la’assar dan inasan ganin Ashraf.” Kai little ta d’aga tace “Allah yasa mu dawo mu sameka.” Yace Ameen tare da satar kallan Nafi. Nan sukamai sallama suka shiga motar Little sukai gaba. Su Umma kam da Asim suna zaune a falo suna jiran good news tunda sunga fitarsa daga gidan da motar mercedes wanda hakan yasa Asim ya sanar dasu sunan motar da number ta, sai dai jin shiru har shad’aya ba labari yasa Asim ya kira, sun sanar dashi har yanzu motar bata wuce ba, nan suka kara jinkirtawa zuwa azahar, nan ma akace motar bata wuce ba, cikin takaici Asim ya kira wani ma’aikacinsu na company ya tambayeshi Ashraf yazo? Ga mamakinsa jiyai ance tun d’azu yana nan. Haushi da takaici suka turnukeshi ya kirasu ya hau su da fad’a sannan yace ” su tafi daga gun kafin ma a zargi wani abun.?” Little ta kai bakin gate wayarta ta fara kuka, Nafi ta zaro wayar daga cikin jakarta ganin Sunan Big Bro yasa Nafi tai saurin mika mata, Little ta amsa tare da gaidashi.+ Nafi duk ta tattara hankalinta kan Little tanasan taji me yake cewa sai dai batajin komai sai amsar da Little ta bashi “Yaya har mun fito fa?” tai maganar tare da had’e fuska, Nafi sai ji tai tace ” Yaya dan Allah ka…..” da alama katseta akai wanda ta karasa maganar da cewa ” To Yaya.” Tana kashewa ta kashe motar tare da kallan Nafi ranta duk a b’ace, Nafi ta kalleta tace ” ya akai?” Little tace ” wai Yaya ne yace kije ki gyaramai b’angarensa.” Nafi ta kalli Little da mamaki tace ” Ni kuma?” Little ta d’aga kai alamar eh, Nafi ta canza fuska sannan tace ” Matarsa fa? Ita bata iya gyaran bane ko me yake nufi?” Little tai karamin tsaki tace ” wannan uwar san jikin me zatayi? Banda chatting.” Nafi ta d’aure fuskarta tamau sannan tace ” Mu tafi kinji?” Little ta kalleta cikin mamaki tace ” Me kike nufi?” ” Mu tafi inda zamu.” Little kam tayi mamakin Nafi dan bata taba tunanin zata iya ture maganar Ya Ashraf ba ganin yanda take girmama shi. Little ta kalleta tace ” Feena….!” Nafi tai murmushi tace ” Mu tafi kinji, wato matarsa bazata gyara musu muhallinsu ba shine ni zanje in gyara musu, sannan ba kunya su shiga suna farin ciki, sannan gobe ma aa kara kirana in gyara, to ba da ni ba.” Little ta jinjina kai alamar ta gamsu da zancen Nafi sai dai tana jiye mata b’acin ran Ashraf, iya kuluwa Nafi ta kulu wato ita da bai damu da ita ba shine yake neman sata gyara musu b’angaren su a lokacin da suke shirin fita, ta d’anyi kwafa kadan a ranta tace ” ni d’azu kamar zan zauce jin wani abu zai sameshi ni kuma wato wannan ne sakayyar da zaimin. Bata sake magana ba har suka ita gidan su Yusra sai dai kana kallanta kasan ranta a b’ace yake. A bakin gate Al_Amin wanda ke zaune yana ganinsu ya saki wata fara’a tare da mikewa ya nufo su, sam Nafi bata kula ma da shi ba, har ya iso inda suke Little ta mai murmushi sannan suka kalli Nafi wanda sam hankalinta baya gunsu sai ma ci gaba da tafiya da takeyi. Hannu Little tasa ta rikota wanda hakan ne yasa Nafi ta juyo ta kalleta, ganin Alamin a tsaye yasa ta mai kallan mamaki. Rausayar da kai yai cikin salon soyayyarsa yace ” I am disappionted Feena.” Nafi ta kakaro murmushi sannan tace ” Sry wlh ban kula ba, sam hankalina na wani gurin.” Ya d’an shagwab’e kadan yace ” in har damuwarki ba akan wani namiji bane na hakura in kuma har akan namiji ne ba ni ba banaji zan hakura.” Little ta saketa tai gaba ta barsu ganin Alamin ba kunya agabanta yake wannan sakalcin. Nafi ta juya kai gefe sannan tace ” just 4get, ya kaje gida jiya?” Alamin ya kura mata idanunsa wanda ya kashesu kai kace a haka idanunsa suke, Jitai bazata iya kallansa ba hakan yasa tai kasa da kanta, ya kara matsowa sannan yace ” Feena jiya na baki waya amma sam ko kunnata ma bakiyi ba, sannan yanzu kin wuceni ko kallona bakiyi ba, Feena please kar ki wahalar da zuciyar dake tsananin kaunarki.” Nafi ta d’ago jiki a sanyaye, ganin yanda har yanzu kallan nan yake mata yasa tad’an kalli gefe sannan tace ” Ba haka bane, jiya bayan na shiga gida bacci nai da wuri, yau kuma sam ban ganka ba.” Alamin yai kasa dakai sannan yace ” Ko dai…..” Katseshi tai da cewa ” Alamin me yasa kake da yawan complain ne? Na fada ma uzuri na why not kai believe da abinda nacema meyas kake neman tursasani akan fadar abinda na shine ba?” Tana kai nan ta juya ta nufi hanyar da zata sada ta da ciki, da sauri Alamin yasha gabanta tare da rike kunnuwansa biyu yace ” Sry Feenah please!!” Nafi ta kalleshi bata cemai komai ba sai kokarin canza hanya tai gaba da takeyi, bai san sanda ya riko hannunta ba, Nafi ta watsa mai wani mugun kallo sannan ta fizge hannunta tai gaba. Kai ya dafe cikin tsananin tsoron abinda ya aikata, me zata d’aukeshi? Nafi tana shiga ciki aka nuna mata d’akin da su Little suke nan ta shiga ta taddasu ana ta hira, duk yanda sukaso su jata da hira taki aminta a karshe ma kwanciya tai batasan sanda bacci yai gaba da ita ba. Can cikin bacci taji Little na tashin ta, ta bud’e ido a hankali, Little ta kalleta tace ” Feena ya zamuyi?” Nafi ta mata kallan da me fa? Little tace ” Ran Yaya ya b’aci yana waje yana jiranki.” Idanu ta zaro gabanta ya yanke ya fad’i ta mike zaune da sauri tace ” Da gaske?” Little tace ” wlh, yace ki fita yanzun nan, in kuwa kika bari ya shigo sai ranki ya b’aci.” Nafi ta mike tare da d’aukan mayafinta tai waje. Little tace ” inzo muje?” Kai Nafi ta girgiza mata alamar a’a sannan tai gaba. Nafi tana fita ta shiga neman motarsa dan itakam bata ganta ba, horn taji an mata wanda yasa ta juya ta kalli inda taji horn d’in, nan ta karasa gun jikinta duk ya mutu ga bacci ga tsoron me zai biyo baya, tana zuwa jikin motar ya zuge glass d’in motar sannan ya mata alama da hannu akan ta shiga. Nafi ta bud’e motar ta shiga tare da rufe kofar. Bai mata magana ba sai jan motar da yai, sai da sukai nisa ya juyo ya kalleta rai a b’ace yace ” wato ni ban isa dake ba ko? Maganar saurayin ki ta fi tawa ko?” Cikin mamaki ta kalleshi ta daure tace ” ban gane ba.” Wani irin burki dayaja sai da numfashinta yai gaba na wucin gadi. Nafi a tsorace ta kalleshi, ransa a b’ace yace ” ban bada sallahu ki gyaramin part d’ina ba?” Nafi ta kalleshi tace ” ka fada amma gani nai ni meye nawa na shiga part din mai mata?” Ashraf mamaki ya kamashi yaushe ‘yar nan tai baki haka? Yace ” to ita kinsan ba ‘yar wahala bace dan nace ki taimaka mata shine zaki tafi gidan saurayinki?” Wani mugun kishi ne ya taso ma Nafi, ita ba ‘yar wahala bace?” Kallan mamaki take mai, yacigaba da cewa ” sannan ke harkin isa in saki abu ki kama hanya kiyi tafiyar ki??” Nafi batasan sanda ta saki wani murmushin takaici ba, ta goge kwaIlar data taho mata, tace ” Yaya ba sai ka fadamin magana akan matarka ba, nafi kowa sanin ita ba ‘yar wahaka bace, ni da ka d’aukoni daga riga mai shan madara da nono kullum, mai kiwon dabobbi nice ‘yar wahala.” Jikinsa ne yai sanyi, a zahiri shi gidan saurayin ne bayasan taje ya kuma rasa dalilinsa na rashin san hakan, shi yasa yasata aiki bawai wulakantata yakesanyi ba. Nafi ta share kwallarta sannan ta cigaba da cewa ” Yaya ka maidani garinmu inda nake, na fi kowa sanin banda matsayi a gunka dama sauran mutanen gidan, Little ce kadai mai sona dama can ni haka Allah ya halliceni da bakin jini, ubana ma ba sona yake ba, uwata ta d’auki kanina ta tafi dashi ni da bataso ta barni a riga, ban taba samun wani wanda yake sona tsakani da Allah ba in har ka cire little, gwara ka………. Jitai an jawota an rungume ta, kalamanta ne suka tsaya cak, bama su kadai ba duk wata gaba ta jikinta jitai ta daina aiki, shi kanshi sai daya rungumeta hankalinshi ya dawo jikinsa, me ya aikata? Sai dai ya kasa zare jikinsa………. Sun dade a haka kafin Ashraf ya d’agota daga jikinsa, kansa ya maida yana kallan gefen titi, a zahiri kunyar kallanta ma yakeyi, Nafi kam anyi dif kamar kazar data fad’a ruwa, kallansa kawai takeyi, Ashraf ya juyo ya kalleta ganin har yanzu bata dawo daidai ba yasa yai saurin cewa ” Ke wai yarinyar nan yaushe kika yi baki haka? Sai magana kike ba tsayawa?” Nafi ta bud’e baki zatai magana sai shakuwa, jikake heee’i, kanta tai saurin sawa a cinyoyinta tana kokarin maida shakuwar, Ashraf yai saurin tada mota suka fara tafiya, shiru ne ya biyo baya Nafi ta d’ago a hankali ta kalleshi, ganin sun wuce hanyar gida yasa tace ” Yaya ina zamu?” Kallanta yai sannan ya maida kansa titi tare da cewa ” Hotel.” A tsorace ta kalleshi sannan tasa hannu a kafafunta ta matse jikinta, ya juyo ya kalleta dariya ta kusa zuwa mai, yace ” lalai yarinyar nan me kike tunani?” Kallansa tai sannan a hankali tace ” bakomai.” A ransa yace ” lalai makarantar nan ta b’ata yarinyarnan, bayaji sanda tazo garin nan tama san me ake nufi da aure amma yanzu aga zancen hotek har tana wani matse cinyoyi? Shi me zaiyi da yarinya karama ma kamar wannan? In ma iskanci zaiyi?” Nafi kam aranta abubuwa da dama take ayanawa, ne zai mata a hotel d’in? Tunowa tai da sanda ya rungumeta da sauri ta girgiza kai alamar a’a, Ashraf kam kallanta kawai yake saura kad’a ya bigi wata mota, da sauri yaja burki sannan ya kalleta yace ” badai tunani kikeyi ni? Kamar ni Ashraf zanyi miki wani abu ba? Banaji kinkai wannan matsayin ko da kuwa iskancin na keyi.” Nafi wanda kalamansa suka b’ata mata rai tace ” nima ai bance wani abu zakamin ba, sannan ko wani abun ne ai banaji nakai wannan matsayin.” Kallan mamaki ya mata, sannan ya had’e fuska tamau yace ” Da alama raini yafara tasiri a tsakanin mu.” Juya kai tai batace komai ba sai d’an kunkuni datai, a zuciye ya fizgi motar, lalai yarinyar nan shi take ma kunkuni? Sun isa Hotel din ya karasa gun parking, kallanta yai sannan yasa hannu ya fizgota sam baisan da karfi ya jawota ba wanda hakan yasa ta fad’a kirjinsa, a hankali ta d’ago cikin tsoro, ya kalleta yace ” me kika ce d’azu?” D’an karamin bakinta ta turo gaba tace ” ni me nace?” Yai wani murmushi yace ” bakima san me kika ceba ko rainin hankali? Da alama ma zagina kikai.” Idanu ta zaro cikin mamaki ta d’aga jikinta daga nashi tace ” ni? Yaushe? Taya za’ai in zageka koda kuwa naman jikina kake yanka?” Ya kura mata ido sannan yace ” inkinaso in yadda baki zagen ba to ki fad’amin a ina kikaji zancen za’a tareni a hanyar zuwa office.” Kallan sa tai cikin tsoro, ya matso da fuskarsa kusa da nata yace ” what? Bazaki iya fad’a ba?” Idanu ta kifta sannan ta had’iyi yawu, ya sa idanunsa cikin nata sannan yace ” bazaki iya ba?” Idanunta tai saurin maidawa kasa saboda wani abu dataji ya taho mata, komawa yai yazauna tare da d’aukan wayarsa yace ” kijirani ina zuwa.” Yana kainan yai hanyar fita, batasan sanda tasa hannu ta riko rigarsa ba, yazo fita yaji an rikeshi, ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigarsa inda ta rike. Nafi cikin tsoro tace ” tsoro nakeyi Yaya.” Idanunsa ya kankance yana kallanta, ta cigaba ” Tsoro nake kar na zama silar jawo gaba ko fad’a a tsakanin ku.” Ashraf yai karamai ajiyar zuciya sannan yace ” Nafisa me kika sani? Me kika sani game dani da ‘yan uwana? Mutane sun d’auka ganin fara’a a fuskar mutane shi yake nuna suna cikin farinciki sai dai abin sam ba haka yake ba, kowa da kike gani shi kadai yasan wace rayuwa yakeyi a cikin zuciyarsa.” Nafi tai shiru kanta na kasa bata kuma sakeshi ba, Ashraf ya sa hannu akan hab’arta ya d’agota yace ” Asim ne?” Kai ta d’aga mai tare da maida kanta kasa, Ashraf yace ” sakini inje in dawo lokaci na tafiya.” A hankali ta saki rigarsa, ya fita.Kallo ta bishi dashi jikinta duk ya gama sanyi. Shikam Ashraf sam baiyi mamaki ba dan dama jikinsa ya bashi hakan, ya sani mutane dayawa ba sanshi suke ba a gidan amma kowa na kokarin b’oyewa banda Asim. Yana shiga ya bada takardun dayazo badawa sannan ya fito.Nafi kam abin duniya ya dameta, Ashraf ya bud’e ya shiga, ganin yanda take kallansa yasa ya d’aga mata gira yace ” ya akai kuma?” Nafi ta girgiza kai alamar ba komai sannan ya tada mota sukai gidan lawyer d’in babansa, nan ya ajiye wannan motar ya d’au tasa ta da sannan sukai gida. B’angarensa suka nufa, yana gaba tana binsa a baya, sunje wuce wa ta b’angaren su Asim sai gashi. Ashraf ya saki wani murmushin rainin hankali sannan ya cigaba da tafiya, ba wanda yama juna magana har Asim ya gifta Ashraf kad’an. Yaji Ashraf yace ” ASIM” Ba Asim ba hatta Nafi wanda Asim d’in ke saitin ta ta tsorata da yanda Ashraf ya kirashi, Asim kam tsoro ne karara a fuskarsa, Ashraf ya tako a hankali yazo kusa dashi sannan ya sa hannu ya dafashi yace ” ka tab’aji inda kura ta nemi kama zaki?” Asim yamai kallan mamaki sai dai bai amsa ba, Ashraf yai murmushi sannan yace ” Ita kanta kurar da take tsoron zaki kaga kuwa ta ina ta isa ta kama sarkin dabobbi?” Ya kara matsowa kusa dashi sosai yasa bakinsa a saitin kunnensa yace ” In har kurar tana neman halaka sarkinta to lalai sai tayi amfani da kwakwakwarta.” Ya fad’a tare da nuna tasa kwakwalwar. Sannan ya cigaba ” in har batai amfani da nan ba to lalai ita zata fad’a cikin trap d’in datai na kama sarkinta.” Yana kai nan yasa hannu ya bubugamai kafad’a sannan yai gaba. Nafi kam a tsorace tabi bayan Ashraf. Shikam Asim anan suka barshi sai dayai kusan minti biyar a tsaye kamar abu kara motsi kafin ya juyo da niyyar kallan Ashraf sai dai sam baya gun. Sun isa b’angaren sa, Ashraf ya kalli Nafi yace ” D’akina nakeso ki gyaramin.” Ta kalli falon wanda duk yayi kaca kaca ko sanda yake shi kadai baya taba yanda falonsa yai haka bare yanzu. Ta kalleshi tace ” nifa d’akinka kawai zan gyara.” Yace “Falon fa?” Tace ” Wannan kuma matarka sai tayi ai aikinta ne ba nawa ba.” Matsowa ya farayi ita kuma tana matsawa baya, tsoro takeyi sai dai itakam bazata taba yadda ta gyara musu falo ba wato ta gyara suzo su zauna suyi soyayyarsu a ciki? Jin tazo jikin bango yasa ta tsaya tare da kallansa a tsorace, Ashraf ya kalleta sannan yace ” Maimaita kalamanki.” Kasa tai da kanta ba tare data maida ba, ya saki wani murmushi yace ” in aka tambayi iyayenki matsayina a gunki me zasuce? Ahh i am really curious.” Zaro ido tai cikin mamaki tace ” ban gane ba.” Yace ” Menene matsayina a gunki?” Gabanta ne ya fad’i da sauri tace ” Yayana mana.” Yace ” Good.” Menene matsayinmu a gun iyayena da ‘yan uwana? Tace ” Wanda ya taimakeni.” Yace ” Bravo!, to menene kuma matsayina a gun ‘yan kauyenku da mahaifinki?” Baki ta shiga motsawa tana san magana sai dai bazata iya fad’a ba. Ya juya ya fara tafiya sannan yace ” in kina san ‘yancinki kimin biyayya sai in baki takardarki cikin sa lama ki auri wanda ranki yakeso.” Cikin takaici tace ” in naki fa?” Yace ” Well! Wannan kuma ya rage naki kinsan dai ba’a aure kan aure ko? Haka nan zakiyi ta zama har ila masha Allah.” Yana kainan yai hanyar dinning. Tabishi da kallan takaici, ba ma zaka zauna dani ba sai dai haka zan ta zama har ila masha Allahu, lalai ma Ya Ashraf….. Cikin takaici ta shiga gyaran gida ranta inyayi dubu to fa ya b’aci, takaici duk ya turnuketa, ko inama wannan matar tasa taje? tai maganar ranta a b’ace. Hotunsu ta kalla dake manne a falo sunyi masifar kyau kamar me, taja tsaki sannan tace ” Aikin kawai ko kyau ma.” Lol nikam ai dariya ce ta kamani na kara kallan hoton wanda yaune rana ta farko danaji an kushe wannan hoton…..Su Nafi ko me yasa akaga munin hoton da ni kaina na bash A1????? Shikam gogan yana zaune kan dinning yasa laptop a gaba yana aiki, da d’akinshi ta fara tasha kura mamaki ya kamata, lalai ma mutumin nan da alama sakalta matarshi ma yakeyi,ta gama d’aki kenan ta dawo falo sai ga Aneesa. Kallan Nafi tai wacce ranta ya kara b’aci ganin Anisa ta kamata tana aiki a cikiciki ta gaidata, Anisa ce tai murmushin farin ciki sannan ta kalli Ashraf tace “Hubby nagode sosai.” Har zai fad’a mata bakar magana sai dai ganin Nafi yasa yai shiru, ta karasa kusa dashi tare da sakala hannayenta kan wuyansa ta rankwafo tare da mannamai kiss a kumatu, wata irin harara Ashraf ya buga mata. Ita kam Nafi jitai numfashinta na rawa da sauri ta juya musu baya, a hankali taji hawaye yana zubo mata, ta sani Anisa matarsa ce sai dai me yasa takeji wani abu na taso mata? Ji take kamar taje ta zanesu dan bakin ciki. Haka ta cigaba da aiki idanunta sunyi jaa, Aneesa kam ta dade a gun Ashraf daga nesa zaka d’auka soyayya suke sai dai Ashraf banda bakar magana ba abinda yake fad’a mata a karshe yace “da alama zai maidata gun Umma in ta koyo yanda ake kula da miji da gda sai ta dawo. Mikewa tai cikin takaici sannan ta zo gun Nafi tace ” ke inkin gama da nan ki shiga d’akina ki gyara min.” Mamaki ne ya kama Nafi ta d’ago cikin tsananin mamaki ta kalleta tace “Ban gane ba?” Aneesa ta had’e fuska tace “nace inkin gama da falo nima inasan ki gyaramin d’akina.” Nafi batasan sanda tai wani dariya ba dama a kule take da ita taje tana wani rungume Ashraf yanzu kuma me?? Cikin mamaki Anisa ta kalleta tace “wa kikewa dariya?” Nafi ta ajiye taintsiyar sannan tace “akan me ma zan gyara miki b’angaren mijinki?” “Me kikace?”Ashraf yana zaune yana kallansu haka kawai sai ya sami kansa da murmushi, Nafi yake kallo cikin burgewa.Nafi ta ja mayafinta ta nufi hanyar waje, a zuciye Anisa ta fizgota, ta d’aga hannu da niyyar marinta. Da sauri Ashraf ya mike ya fara takowa, sai dai kafin ya karaso gani yai Nafi ta rike hannun dake shirin sauka a kuncinta.To fa!!!!! Nikam kujera na samu na baje rike da birona inasan ganin yanda zata kare.