ZUCIYA CHAPTER 15 S
Ranta yakai koluluwa gun b’aci Ashraf bai tsamani ba kawai yaga ta bud’e motar ta fita, ga ruwa ake sosai, da sauri shima ya bud’e kofa ya fita, tafiya kawai take tsabar ruwa batama san ina take sa kafarta ba, Ashraf ya hanzarta ya riko hannunta. Kallansa tai sannan ta fizge hannunta da karfe ta nemi ci gaba da tafiya, hannayensa biyu yasa ya rike kafad’arta ya juyo da ita saitinsa yace ” Nafisa!!” ya fad’a tare da jijiga mata kafad’a, Nafi ta shiga neman kwace jikinta ganin yanda ruwa ke dukansu gashi da alama taurin kai take nemanyi yasa kawai ya d’agata cak yai mota da ita ahakan ma saj wutsul wutsul take, ya bud’e mota ya sata sannan ya zaga da sauri ya shiga tare da sama motar lock. Nafi ta juya kanta gefe, hannunta ya kamo yace ” menene wai?kanki d’aya kuwa?” Ta kalleshi da idanunta da suka ciciko cikin wani irin murya ta kalleshi tare da cewa ” yaya ni nace ka aureni?” Kallan mamaki ya mata, ta share hawayenta duk da tasan abanza dan kuwa hawayen sai ma kara zubowa takeyi, ta kalleshi sannan ta cigaba ” Yaya ni bw mutum bace?dutse ce ni ko kuwa?” Kallanta kawai yake sam ya kasa magana, hawayen da takeyi da kalamanta sune kawai ke ratsa shi, ta kara share wasu kwallan sannan ta cigaba ” ka tab’a ganin inda mace a ranar da aka daura mata aure miji yake mata zancen saki? Ka taba tunanin yanda wannan matar zataji duk da yarintar dake damunta a lokacin??” Ashraf jikinsa ya mutu sosai, Nafi ta sake goge kwallar sannan tace ” ka bani takarda ta yanzu inaji shine kawai abinda ya kamata, a gun iyaye da mutanen garinmu ne kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad’a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?” Ashraf ya kara rike hannunta yace ” Nafisa!” Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace ” na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawara ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata.” Idanu Ashraf ya runtse sannan ya bud’esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa kwacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya jike shakaf. Kuka take sosai wanda ke taba duk wani lungu da sako na jikinsa, kanta ta kwantar a wuyansa a lokacin da ta fara tsagaitawa da kukan, jin jikinta yai ya fara d’aukan zafi ya daure ya d’agata sannan ya riko hannunta ya shiga hura hannunta da bakinsa yana murzasu, kallansa kawai takeyi tanajin wani irin sabon kaunarsa na ratsata, Why?? Meyasa ita da takesan ta daina sanshi amma takejin haka. Ya kalleta yace ” zazzabi ke neman kamaki, me yasa bazaki min magana ba kika shiga ruwa?” Ta kifta ido sannan tace ” yaya ka tab’a tunanin ya nakeji inkamin zancen saki bayan ban tabbatar da matsayin aurena ba ma? ” Ashraf ya kalli yanda jikinta yai sharaf sannan ya kalli idanunta cikin dan fada fada yace ” ina miki zancen jikinki kinamin zancen abinda ba shiba?” Idanu ta kafeshi dashi, ya kalleta shima, kallan juna suka shigayi dukansu wani abu na ratsasu, Nafi ta daure ta d’auke idanta ta juyar da kanta jikin window, Ashraf ya sa hannu ya rikota tare da jawota kusa dashi. Idanun Nafi ne suka fifito ya kalleta yace ” kalleni.! A hankali ta d’ago tana kallanshi ta maida kanta kasa, jikinta ne ya mutu ganin ya sa kanta akan kafadarsa yace ” ki zauna a haka na yan mintina.” Why? Tafad’a a hankali yai gyaran murya yace ” zai taimakawa jikinki dake neman kamuwa da zazzabi.” Tai murmushi batace komai ba, ya sake gyaran murya yace ” ba kuma cewa nai kiyi hakan ba da wani.” Tace ” me yasa? Naga taimako ne.” Ya harareta yace ” ni ai haryanzu akwai aurena akanki.” Tad’an tab’e baki tace ” auren da ni kaina ban tabatar ba.” Me kikeso ki tabbatar? Idanu ta rufe kamar mai bacci dan batada amsa. Ya kalleta sannan yai murmushi. Ganin ruwa ya fara d’aukewa yasa ya gyara mata kwanciya zuwa kujerarta duk da yasan ba Bacci take ba, sannan ya tada mota ya jata a hankali. Nafi kam juyawa tai tana murmushi lalai wannan rana ta shiga cikin tarihin rayuwarta ba wai cewa yai yana santa ba sai dai ta rasa dalilin farincikin nata. Sun isa gida sannan yai parking yasa hannu a wuyanta yaji dumin kadan ne sannan ya kalleta yace ” mai baccin karya ki tashi ki shiga ciki ki dan zuba ruwan zafi a jikinki kisa kaya mai dan nauyi.” Kai ta d’aga ba tare da ya juyo ba, sannan tai sumsum tai waje ya bita da murmushi. Yasa ankai mata kayanta sannan ya wuce b’angarensa yai wanka shima da ruwan zafi sannan yasa kaya ya kwanta akan gado tare da dora hannunsa akan goshinsa, meke damunshi? Me yasa yake abu kamar ba shi ba, me yasa yake yawan murmushi tare da yin abubuwan da bai saba ba in yana tare da yarinyar nan? Wata zuciyar tace badai kamuwa kafarayi da santa ba? Kai ya girgiza da sauri yace ” No way, how can i….” Shiru yai yana tuno sanda ta kwanta ajikinsa tana kuka, murmushi ya saki tare da lumshe ido…… Nafi kam haka taitayin komai cikin farin ciki har Little ta ke tambayarta yau meya same ta haka?Nafi kawai sai dai tai dariya.. Washegari litinin da safe Ashraf ya shirya ya tafi gun aiki sabosa sunada Meeting yau ranace babba agunsa don project din da yai kusan wata 6 yana planning yau zaiyi presenting dinsa a gaban directors na company din. Karfe goma ne presentation din dan haka ya isa gun karfe 9 da kansa ya Shiga gyara gun har 10 tai, mamaki ne ya kashi ganin har 10 da rabi ba kowa a gun sai shi kad’ai nan ya fito ya fara dan zazagawa, wani member na team dinsa ya kira yace ” ya dubamai ko ancanza lokaci ne.” Yana nan a tsaye sai ga Mansir ya taho, ya karaso inda Ashraf yake yace ” har an fara?” Ashraf yai kasa dakai cikin rashin jin dadi yace ” ba wanda yazo shiyasa nake tunanin ko ancanza time ne.” Kawubya d’an nuna rashin jin dadinsa a fili sannan ya d’aga waya ya kira Secretary dinsa, ko me ya cemai ya kashe tare da kallan Ashraf yace ” Ashraf ance project dinka plagiarism ne.” Cikin tsananin mamaki Ashraf yace ” Ban gane ba?” Kawu yace haka aka sanar da directors din ciki kuwa harda members na team dinka sannan project din har anyi lunching dinsa ma a comapny din da muke rivals.” yana kai nan yad’an bubuga kafadar Ashraf sannan ya juya ya tafi. Da kallo Ashraf ya bishi ya saki wani murmushin takaici a ransa yace ” ko kuma ka d’auka ka basu ba? Kana tsoron hakan zai sa mutane suyi acknowledging dina.” Ya runtse ido saboda wani takaici da ya kamashi, yai kwafa tare da zubar da takardun yai waje. Mota ya shiga ransa yakai kululuwar b’aci ya dage ya daki sityarin mota da hannunsa tare da kwantar da kanaa jikin kujera ya saki wani huccin takaici. Little ce ta kirashi sai data kusa katsewa ya d’aga sai dai muryar Nafi yaji tace ” Yaya ina kwana?” Ya amsa a hankali, tace ” driver din yazo zamu tafi gashi bakanan bare muyi sallama.” Yace ” da inzaki tafi makarantar sai kinyi sallama dani?” Mamaki ya kamata tace “Yaya gani nai….” Katse wayar yai sannan ya kasheta gaba d’aya ya runtse idansa da karfi zuciyarsa na kara tafasa. Nafi kam mamaki ne ya kamata, cikin takaici ta shirya da taso in sukai waya yace ta bari ba yau ba sai dai yanda ya amsa mata yasa taji batasan zaman gidan ma sam a wannan lokacin, ta kalli Little ta mika mata wayar Alamin sannan tace ” ki bashi wayarsa kicemai na koma skul inda rabon mu sake had’uwa to inkuma babu Allah ya hada fuskokinmu a aljanna.” Little ta kalleta fuska a hade tace ” wai dan Allah bazaki hakura da tafiyar nan ba?” Nafi ta girgiza kai cikin takaici tace ” karki damu little kwana nawa ne?” Little ta harareta sannan tace ” wani irin sako ne wannan haka kikeso in fad’ama al’amin din?” Tace “eh, bari naje nama Mumy sallama.” Sunyi sallama da Mumy, sannam ta shiga mota ranta duk ba dadi suka tafi….. Ashraf ya gyara zamansa a cikin mota sannan ya kira lawyer kuma abokin babansa, bayan sun gaisa ne yace ” Uncle taimako nake san kamin.” Yace “me kakeso Ashraf kasan saboda kai nake ta d’aga time din retire dina.”+ Ashraf yai murmushi sannan yace ” Nasani Uncle please so nake kaje Slc company kace ina tuhumarsu da satarmin project ka basu takardar shaidar sammaci a kotu.” n Lawyer yai murmushi yace ” da alama yanzu ka shirya fito na fito da su.” Ashraf yai dan kwafa yace ” Uncle a duk sanda sukamin abu kalaman Abba daya rubutamin shi ke fad’omin sai dai inaji ajikina yanzu shima Abban bazaiso in barsu su kara b’ata ba.” Lawyer yai dariya sannan yace ” Hakane, dama ance Eye for eye, tooth for tooth.” Sunyi sallama Ashraf ya bud’e mota ya fito, Asim ya gani ya nufoshi yana wata tafiyar kasaita. Ashraf yaja tsaki yace ” The biggest fool is here.” Asim ya karaso cikin isa sannan ya shiga tafama Ashraf, kallansa Ashraf yai yace ” kai kuma me ke damunka?” Asim ya saki dariya sannan yace ” Ashraf shi yasa nace maka ka kiyayeni ni ba sa’an yin ka bane.” Kallan sa Ashraf yai yace ” kana tunanin kaika aikata hakan?” Asim ya jinjina kai yace ” sosai ma tunda ninasa aka sace project din.” Kai Ashraf ya jijiga alamar tausayawa sannan ya matso yad’an bigi kafadar Asim da hannu yace ” u are such a big fool, ka daiyi tunani dakyau amma ninasan kanka bashida wannan basirar, kaidai basirarka d’aya ka turo a kasheni.” Yana kai nan ya juya yai gaba. Asim yabishi da kallo cikin kuluwa yace ” me? Yasan Abbanane yasani ko me?”kai ya jijiga alamar a’a sannan yace ” ai ba yanda zaiyi ya zargi mijin mahaifiyarsa. Ashraf kam office ya koma ya cigaba da aikinsa, wanda akasa ya saci takardun a cikin members dinsa sai b’uya yake yi, sam Ashraf bai kulashi ba sai ma wani abu dake mai yawo a zuciya, wato kawu abin tsoro ne na gaske, ya tura d’ansa yayi abu yanzu in asiri ya tuno fa? Lalai mutumin nan wato akan abinda yakeso he can use anyone.” Yaja tsakin takaici inya tuna uwarsa ma amfani yake da ita. Sai yamma ya tashi nan lawyer ya sanar dashi yace Slc ya sanar musu sai dai sunce a jira director ya shigo gobe dan shine yai proposing din project din. Gida Ashraf ya wuce, yana shiga yai parking sannan ya kira Little a waya, bayan ta d’aga ne yace ” turomin kawarki.” Little tace ” wa kenan?” Ashraf ya had’e fuska yace ” wace kawa zance ki turon bayan Nafisa.” Da mamaki tace ” naga kunyi sallama d’azu ta tafi ai.” Da sauri taji yace ” bangane ba? Ina ta tafi?” Little tace “Skul ba ta kiraka ba?” Katse wayar yai sannan yai wirgi da ita gefen kujera sai a lokacin ya tuno mai sukai, yai hucci sannan yace ” waya bata permission?” Kansa ya shafa sannan ya fito ransa duk a jagule, b’angarensa ya nufa ya bud’e kofa ya shiga, kamshin turaren daya jine yasa ya d’ago dan ganin meke faruwa? Anisa ya gani sanye da wasu ‘yan iskan kaya riga ce iya cibiya sai wani mini siket a jikinta tayi kyau sosai sannan kwalliyace ta tada hankalin duk wani namiji indai yanada lafiya, duk da shigar ta daki Ashraf matuka gashi dama ya dade rabonsa da ita dan dama ko da tana gidan haushin abinda takemai yasa yake kin kusantarta. Idanu ya kankance yace ” ke kuma me kikeyi anan?” Cikin takun jan hankali ta taso ta fara tahowa tana tuno shawarar Umma ki maidashi naki, zuciya da gangan jiki bayan mun gama amfani dashi sai mu munamai yayi kuskuren fifita kucakar yarinyarcan akanki.” Ta karaso tare da zura hannayenta ta wuyansa ta kwanto a jikinsa sannan ta saki ajiyar zuciya tace ” Hubby do u know how much i miss u?” Ashraf ya d’agota sannan yace ” me kikeyi anan…….” Bakinta ta saka a nashi nan fa kaji tsit malam….Duk yanda yaso ya daure ya ture Anisa ya kasa dan kuwa in zuciyarsa bataso to fa jikinsa naso. Nan ya sungumeta sukai d’aki……..Ni kuma da jawo musu kofa nai gaba. Bayan sun gama ne sunyi wanka sannan Ashraf ya had’e fuska tamau, ta matso kusa dashi tare da daura kanta akan kirjinsa Tace ” Hubby bazaka yafemin ba?” Kallanta yai sannan yace ” Anisa sam ni na rasa mai ke damunki.” Ta cusa kanta a kirjinsa tare da sakala hannunta ta bayansa tace ” tuba nake dear, kaji? Bazan sake ba.” Yai shiru hakan yasa ta cigaba ” Bakasan yanda nakeji ba in ina zaune a gun Umma.” D’agota yai zaiyi magana Nafi ta fad’o mai a rai, jiya ya tuno sanda ya rungumeta a jikinsa me yasa bayajin irin wannan yanayin inyana tare da Anisa? Mikewa yai tsaye ya wuce toilet tabi bayanshi da kallo sannan ta tuno sanda tagansu sun shiga mota da Nafi. Ashraf kam a toilet ruwa kawai ya sakar ma kansa a ya sa hannunsa ya rike bango ruwa na dukansa a bayansa, idanu ya runtse sai dai abin takaici Nafi ya hango sanda ta shiga cikin ruwa, ya bud’e idanunsa tare da kallan madubin dake toilet din mamakin kansa yakeyi ace kamar shi yazauna yana tunanin wata ‘yar karamar yarinya?” ********** Nafi kam tun bayan isarta makaranta sam ta rage ko magana dan daba ba kawar da zatai hira da ita, karatunta kawai takeyi sai dai a ‘yan kwanakin nan har rama tai saboda ko abinci takeci tunanin Ashraf takeyi wannan abun duk ya isheta ta kosa su Ferry su dawo ko dan ta samu damuwar dake damunta ta ragu. ****** Scl hankalinsu ya tashi jin gaskiyar al’amari agun director cewarsa abokinsa ne ya bashi, wannan dalili yasa suka rubuta takardar hakuri suka aika company din su Ashraf wanda hakan ya sa ma’aikatan company d’in suka tausaya ma Ashraf sannan sukai dana sanin abinda suka aikata a gareshi, matsayinsa ya d’aukaka dan su cewa sukai a bashi matsayi babba wanda ya dace dashi. Kawu kam duk yanda kaso kasan bakin cikin dake ransa bazaka taba sani ba a fili yafi kowa farin ciki dan har murna aka dinga tayashi ganin yanda yake ta farin ciki kamar me. Sai dai Ashraf kam kallansa kawai yakeyi dan yasan sarai yafi kowa bakin ciki. ********* Sati biyu da komawar Nafi makaranta ‘yan skul suka dawo, farin ciki agunta kuwa ba’a magana, nan suka had’u da Ferry da Ferry da Jibiya, sai dai Ferry na ganinta tasan akwai abinda ke damunta. Da daddare bayan jibiya tayi bacci Ferry ta kalli Nafi tace ” Feenah meke damunki?” Nafi tai yake tace ” ba komai.” Ferry tasa hannu ta dafata tace ” Nafi akan yayanki ne?” Hawayen da ta dade tana had’iyewa ne suka zubo, Ferry hankalinta ya tashi tace ” Feenah menene?” Nafi ta goge hawayenta sannan cikin muryar tausayi da radad’in zuci tace ” Ferry inaji san Yaya Ashraf shine zai zama ajalina.” Ferry ta kalleta tace ” Feena me kike fad’a haka?” Nafi ta kara share hawayenta tace ” Ferry ko bacci nake da tunanin mutum nan nake kwana kullum sai nayi mafarkinsa, rashin ganinsa na hanani komai a rayuwan nan na rasa ina zansa kaina.” Ita kanta jikin Ferry sai dayai sanyi tace ” Feenah.” Yanda ta kira sunan Nafi ne yasa Nafi ta tattara hankalinta kanta. Ferry ta cigaba ” Na fahimceki sai dai Feenah inaso ki koyama kanki danne so, kada ki kuskura ki bari shi wanda kikema wannan san ya fahimceki in kuwa kika bari har hakan ta faro? Maganar gaskiya ko shima yana sanki zai dinga wulakanta ki.” Nafi ta kalleta tace ta ya ya? Ferry tai dariya tace karki damu zan koya miki yanda zakiyi ki mamaye zuciyar wannan yayan naki, ba tare da kin wulakanta ba. Nafi tai murmushi tare da rungume Ferry tace ” Ferry shiyasa nake ma Allah godiya dayasa kike a matsayin Aminiyata.” Ferry ta harareta tace ” ba wani nan bayan nayi nayi kizo muje gidan mu kinki?” Nafi tai murmushi tace ” nafisan zaman skul.” Ferry tace ” Shikenan in kinasan kisan komai na kama saurayi sai kin yadda zaki bimu wannan hutun, Ammi nasan ta ganki kuma kinga daga wannan hutun sai extension.” Nafi tace ” I will think about it.” Sukasa dariya dukansu….. ******** A riga kuwa yayyan Datti suka matsamai sai da sukasa shi ya sake aure, ya auri wata bazawara bafulatana, tanada ‘ya’ya uku sai dai yace shi bazai rike ba, ita kadai ya d’auko sannan yamata kashedi sosai akan dabobinsa, ko garken ma ya hanata zuwa saboda bayasan ma tasan yawan dabobinsa, in zai fita kwad’o yake sawa a kofar karken sannan ya kakara itace. Itama sam ta nunamai ba ruwanta da shirginsa hakan yasa yakejin dadin zama da ita…… Su Nafi manya anyi hutun first term da kyar ta yarda tabi su Ferry gida tai hutu, sunyi waec sunyi neco. Yau sun tashi suna ta shirye shiryen graduation ceremony da za’a musu. Zuwan Little biyu d’aya da Mumy d’aya kuma itada driver tana zuwa kawoma Nafi provision. Sun tashi a gida ita kadai zataso dan Mumy tanada biki, hakan yasa ta kira Habib ta fad’amai da sauri ya amsa akan zaizo dan kuwa shima yana san ganin Nafi. Bayan Habib yazo ne ya karasa gun abokinsa wato Ashraf nan ya sanar dashi inda zasu, shiru Ashraf yai yana tunani tabbas yanajin rashin yarinyar nan har cikin jikinsa, amma zuwansa bazai kawo masa raini ba kuwa??” Habib ya dafashi yace ” mutumin mu mun wuce.” Da sauri yaji Ashraf yace ” Nima zani dan ina ganin bai kamata har ta gama skul banje ba.” Habib yai dariya yace ” ashe kasan abinda ya dace, na tabbata da Little ce acan da kaje yafi a irga.” Ashraf bai amsa mai ba ya tashi ya shiga d’aki, bayan ya shirya ya fito, kallan d’aki Anisa yai wanda ya tabbata bacci take har lokacin aya zari key yai waje. Sun tsaya gun ajiye motoci Ashraf yace “ku tafi da motar ku dan ni tawa tafiyar daban sannan banaji zanyi hour d’aya ma acan. Sun fito suka fara tafiya, Habib na gaba shi yana baya, a hankali yake tuki yana tunanin me zai ce mata in sun had’u? Wata zuciyar tace ” Sannu? Congrat? Hi? ‘yan Mata? ‘yan makaranta?” Kansa ya shafa yace ” ke zai sa in fara mata magana? Ita zata gaida ni ai nasan ni kuma sai na amsa.” Yai murmushi ganin komai yazo da sauki. Har suka isa yana ta ‘yan tunane tunanensa. A makaranta kuwa lokacin har an fara programs, su Nafi anshirya cikin kayan ‘yan mata atamfa da siket ansha d’auri zasuyi drama ne itace lead, alokacin dasu Ashraf da habib suka iso, daidai nan an fara gabatar da drama din kenan. Nafi sam bata kula sun iso ba ta zake sosai tana gudanar da scene dinta na star din cikin dramar, kowa ya nutsu yana kallo Nafi sai burge mutane takeyi da turanci ga iya acting, bawai dan tafi kowa bane aka sata a’a sai dan yanayin yarinyar yanayin Nafine. Su Little sai fara’a akeyi, Habib kam kallan Nafi kawai yake yana tsananin mamakin yarinyar da batai primary ba itace take turanci haka?? Shi kuwa gogan ya kafe kaf, shi bawai turancin bane yafi tada mai hankali ba, yanda ta girma ne yafi bashi mamaki, bawai wani kiba tai ba sai dai cikar mace kam Nafi tayishi a wannan lokacin, ta kara gogewa. Sam ya sha’afa cikin tunanin yarinyar jiyai Little na tab’ashi, ya kalleta fuskan nan a d’aure. Little tace ” Yaya kaga Feena? Dan Allah bata burgeba?” Ya harareta sannan yace ” ina wani abun birgewa ta fito kandar kandar ko mayafi?” Ya fad’a tare da juya kai, Little ta d’an turo baki sannan ta kalli inda Nafi take. An gama drama Nafi tun anayi ta hangosu, aikam ana gamawa ta taho gunsu, little ta rike hannunta cikin tsananin farin cikin ganin junansu, Nafi tace ” Little!” Little ta saki murmushi tare da kara rike hannun Nafi tace ” Yar Uwa Congrats.” Nafi tai murmushi sannan ta kalli Habib tace “Ya Habib.” Habib yai murmushi cikin kulawa yace ” Princess Congrats tun dazu naketa kallanki sai birgeni kike sake yi.” Nafi ta maida kallanta kan Ashraf wanda shima kallanta yake tun da tazo gun, kallan sa kawai tai tace ” yaya sannu.” tana fada ta maida kallanta kan Little. Kallan mamaki ya bita dashi, is that all? Abinda ya fad’a kenan a ransa Cikin mamaki, yaya sannu? Ya kara kallanta gani yai sam ma hankalinta baya kansa ransa yakai kololuwar baci. Nafi kam hannun Little taja tace ” ya Habib muna zuwa.” Sukai gaba, kallo Ashraf ya bita dashi. Sukam gun su Ferry suka nufa nan suka cigaba da hira ita kuma Nafi taje ta canza kaya zuwa kayan makaranta tare da sa graduation gown dinta. An gama taro suka fito tare da su Habib jikin wata bishiya suka zauna babbar sallaya irin manyan nan suka shimfida suka zauna, Ashraf da Habib kuma suka zauna a kan wani benci dake gun. Ashraf ya d’au waya yana dannawa sai dai jefi jefi yana kallan Nafi, haushi duk ya isheshi ganin yanda sam ta d’auke kai daga kansa ko gaidashi batai ba balle ma yasa ran zasu danyi magana. Had’e ransa yai tamau ya rike wayarsa kawai yana dannawa, Su Ferry ne suka iso suka. Nafi ta kallesu tace ” wannan Yayana ne Ya Habib.” ta fada tare da nuna Habib, yai murmushi. Su Ferry suka gaisheshi, ta kalli Ashraf tace ” wannan ma yayanane sunanshi Ya Ashraf.” tafad’a tare da nuna Ashraf, Ashraf ya sake hade fuska wato shi da Habib duk matsayinsu d’aya take nufi ko me? Yayana? Ya Habib? Ya Ashraf?” Wani mugun kallo ya bita dashi, Nafi kam d’auke kai tai tare da kallan Ferry. Yana kallo suka zauna suna hira sam ma ko kallan inda yake batayi. Ashraf kam ya cika fam ko hira da Habib yake neman jansa dashi ya kasa biyemai. Suna nan a zaune suna hira sai ga wani saurayi nan ya iso kana ganinsa kasan yayan Ferry ne dan suna kama sosai, yana isowa ya kalli Nafi sannan yasa hannu a saitin inda zuciyarsa take yace ” Feenah zuciyata za za za……” Yai kamar irin numfashin na neman yankewa, Ferry da Nafi sukai dariya, Nafi tace ” Ya Nabil zaka fara ko?” Little ta kallesu tace au wasa yake?” Nabil yai murmushi sannan ya kalli Little yace ” Yar uwar mu.” Little ta zaro ido dan mamaki, yacigaba ” ke yar uwar Feena ce kinga kuwa yar uwa tace.” Habib yai dariya yace ” Lalai guy din nan kana da abin dariya.” Nabil ya cigana da magana yana kallan Little yace ” Little in baki taimaken ba kinsa kanwarki ta soni ba inaji zakuzo jana’iza ta.” Nafi da Ferry suka sake dariya, Ashraf ransa ya kara b’aci a zuciye ya mike ya karasa gun motarsa ya shiga, kansa ya kwantar akan kujera zuciyarsa duk ta gama kuluwa haka take ma maza dariya?” Kallan gun yai ya d’auka zai ga tana ko kallan inda yake sai dai abin haushi hira suke cikin annashuwa da Nabil. Motarsa ya tada, Nafi ta kalli gun da sauri zuciyarta duk ta fara sanyi anya kuwa wannan hanyar itace? Ferry ce ta mintsineta a cinya wanda hakan yasa ta daina kallan motar sai dai zuciyarta duk ta karaya. Little ce ta kalli Habib tace ” Ya Habib ina yaya zaije?” Habib ya girgiza kai sannan yace “wlh bansani ba nima.” Ashraf har ya fara tafiya yaga bazai iya jurewa ba a zuciye ya fito inda suke hannu yasa ya fizgo Nafi dake zaune suna barkwanci da Nabil. Nafi ta kalleshi, fuskar sa a had’e yace ” mike.” A hankali ta mike, yai gaba ta bi bayansa, jikin mota ta tsaya, ya kalleta yace ” shiga.” Fuska itama ta had’e tace ” ina?” Yace ” za ki shiga ko na shigar dake da kaina? Kallan mutanen gun tai ta had’e rai sannan ta shiga fuska a hade. Shima ya shiga, glass din motar ya zuge, ya maida kallansa kanta yace ” i am a joke?” Ta kalleshi itama tace ” me nai kuma?” Me kikai?tambaya ta ma kike? Ta turo baki tace ” to ni menai? Ka fad’amin” Ashraf ya kura mata ido cikin takaici yace ” kinasan kice min bakisan me kika min ba? Sannan ko kunya ma ki fito gaban maza kadar kadar ko mayafi wai ke a dole kina drama ko?” Nafi bata amsa ba sai baki data turo ya kara cewa ” shi kuma wancan waye? Meye hadinki dashi zaki zauna kina washe mai baki?” Nafi ta kalleshi sannan tace ” Mun saba dashi ne fa.” What?kun saba? Meye shi a gunki?” Nafi ta juya kai tare da yin dan yin kunkuni, yace “me kike cewa?” Kallansa tai tace “jirana akeyi nabar mutane.” Zai sake magana yaga ta bud’e kofa kallan mamaki ya bita dashi…… A zuciye yaja motarsa da gudu yai waje, Nafi tabi bayan motar da kallo jikinta duk yai sanyi, idanunta suka ciciko, Ferry ce ta matso ta dafata suka kalli juna sukai murmushi.