ZUCIYA CHAPTER 16
Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye. Kawu ya kalleshi yace ” Asim meye hakan zaka shigo ko sallama?” Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace ” in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su.”+ Kawu ya daka mai tsawa yace “Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka dinga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?” Asim ya kafe Mumy da ido yace ” gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba.” Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace “Bangane karuwa ba?” Asim yai wata dariya yace ” Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d’anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi.” Mikewa Mumy tai tace “Nafi?bangane abinda kake nu……” Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waje, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kusa da Mumy ya jawota jikinsa yace “Karki damu munfi kowa sannin Ashraf mun kuma san bazai aikata abinda suke fadaba, Anisa kawai suke tayawa kishi ba komai ba.” Idanu Mumy ta runtse jin zage zagen da akeyi yayi yawa, nan suma suka fita, Umma ce taci damara ita da ‘ya ‘yanta maza, Anisa na tsaye sai matsar kwalla takeyi. Fada sosai ne ya kaure a waje banda zagi da cima Ashraf mutunci ba abinda sukeyi, mumy ganin bazata iya daure wa ba yasa tasa baki aikuwa kamar jira Umma take har cewa take zata daki Mumy kuma yau dole ne Ashraf ya saki ‘yarta dan bazata yarda da cin mutuncinsa ba, sai dai zancen saki burga ce kawai takeyi dan tasan bazai yiwu ba. Little wacce hayaniya yasa ta fito tai tsiru tana jin su duk jikinta yai sanyi, bata taba ganin gidansu a haka ba. Suna tsakiyar zage zage sai ga motar Ashraf ta shigo gidan, nan fa kowa yabi motar da kallo dan ganin abinda sukaji, Ashraf kam tunda ya shigo yake mamakin taruwar ta menene, itakam Nafi kanta na kasa sam bata gansu ba, yana fitowa ya zaga inda Nafi take ya bud’e mata ta fito, kallan takaici tamai. Zata wuce taji kafarta ta hard’e ta kifo zata fad’i ta gaba, da sauri ya tareta, hannunsa yasa a kugunta d’aya kuma ya rike hannunta. Sallati suka saka, Umma ta shiga tafa hannu tana sallalami, Mumy ma idanu kawai ta rufe, kawu kuwa ko ajikinsa sai ma farinciki da yake. Nan Asim ya nufoshi a zuciye, Anisa kam zama tai a kasa ta kara sa wani sabon kukan. Itakam Nafi kallan Ashraf tai sannan a hankali ta zare jikinta ta kalleshi tace “Thanks.” Bai amsa mata ba sai kallanta kawai da yakeyi, kai ta juyar gefe dan batasan kallan nan, Asim ta gani ya iso gun a zuciye ya dunkule hannu zai naushi Ashraf da sauri ta shiga gaban Ashraf ita naushin ya sameta, iya karfinsa ya sake wanda naushin sai daya sa tai baya. Ashraf ya razana da sauri ya tarota ya shiga kiranta, su Umma ne dukansu suka karaso gun suka cigaba da sallalami, Umma ta kallesu ya wani rungumota yana kiran sunanta. Tace “Lalai Ashraf bansan haka kake ba sai yau, to dama mahaifinka ya mutu kafin ka mallaki hankalin kanka, uwarka ta kasa hakura ta zauna tai tarbiyarka saboda bazata iya zama ba namiji ba ta auri kaninsa ta ma manta da danta, dama ina zakai hankali?” Ashraf ya d’ago ya kallesu dukansu, Mumy ya kalla wacce ke matsar kwalla a gefe, ransa ya kara b’aci ya kalli Nafi wacce bata farfado ba, sannan ya maida dubansa kan Umma yace ” kun taremun jikin mota ina bukatar fita dan kaita Asibiti.” STORY CONTINUES BELOW Asim ya kara zuciya zai kara kai mai naushi wani kallo da Ashraf ya bugamai yasa ya tsaya, Ashraf ya nunashi da yatsa yace “Don’t you dare think of something like this again, dan banaji zan yafema inka kuskura ka kara tunanin abu irin wannan, kasan ni kasan kuma abinda zan iya.” Umma ta kutuntumo Ashar ta maka mai tacigaba ” dan marasa tarbiya har mu zaka nunawa bariki? Daga kai har wannan tsinaniyar karuwar taka?jiki duk a kya mushe? Zaka wulakanta matarka ta suna akan wata can karuwa?” Ashraf ya kallesu, sannan yace ” In kun gama zaku iya matsawa? inada gun zuwa na dauka na sanar daku.” Kawu ya matso gunsa yace “Kai Ashraf bakada hankali ne? Akan me zaka dinga neman fita da yarinya bayan ka bar matarka ka dauketa kun tafi wani gun?” Ashraf ya kalleshi yace ” Me kuke san ji daga gareni? Kafin ku tambayeni komai na dauka kowa a nan ya amince da abinda zuciyarsa ta fadamai?” Kawu ya hade rai yace ” Ko ma menene dole ne gobe wannan yar kauyen mara asali ta koma kauyensu saboda yarinya guda d’aya bazai yiwu mu cigaba da samun sab’ani ba.” Little ce ta mikamai ruwa a jarka data d’auko ya amsa sannan ya sa mata, numfashi taja sannan ta mike zaune, sai dai gefen fuskarta har ya tashi, Ashraf ya mike tsaye yace ” who said that?” Kawu ransa ya b’aci yace “nine na fad’i haka kuma nine shugaba a gidan nan dolene ta koma kauyensu goben nan, bazan juri ganin tana neman lalata mana zumunci ba, yarinyar da ko asalinta bamu sani ba.” Nafi kam yanzu ta fahimci da ita ake, jiki a sanyaye ta mike zata wuce, hannu Ashraf yasa ya riko nata hannun, cak ta tsaya sai gabanta kawai da yake fad’uwa, Ashraf ya kalli Kawu yace “Zumunci?wanne kenan? Banaji na sanshi, sannan maganar yarinya babu wanda ya isa ya sata ta tafi dan kuwa nine na kawota nine kuma nakeda hakkin sata ta tafi.” Kallansa tai cikin takaici, tasani bazai iya cewa matarshi bace ita, yana gani yana kuma ji ana ce mata karuwa, hannunta ta fizge sannan ta kalli Kawu tace “Kawu kuyi hakuri zan tafi gobe in Allah ya kaimu.” Tana fada ta juya, hannu yasa ya kara rikota nan ta shiga kokarin kwacewa, Mumy tace “Ashraf wai ke kakeyi hakan? Bazaka saketa ba?” Murmushi ya sakar musu yace ” What should i do?” Kallansa sukai cikin alamar tambayar, yace ” ya zanyi? Tunda Nafisa matata ce wacce na aura kafin Anisa, ya zanyi in ban rike hannun matata ba?” Gaba d’ayansu cak suka tsaya kamar abu mara motsi Nafi kam kallansa kawai take sai dai tsoro ya cika mata zuciya, a da tana so taji ya fada with full confidence akan ita matarsa ce to meyasa yanzu taji gaba d’aya ba haka ba?” Ashraf ya kalleta yai murmushi yace “muje ko?” Hannunta ya ja suka fara tafiya binsa kawai takeyi, sukam kowa ya kame ya kasa motsi, suna matsawa daga gunsu Nafi ta had’iyi wani abu tace “Yaya mai ka aikata?” Murmushi ya sakar mata yace “what? Are u scared?” Kallansa tai batace komai ba, har d’aki ya kaita yazaunar da ita tare da kallan inda aka nausheta yace “Me yasa kika taremin d’azu?” Kanta na kasa tace ” nima ban sani ba.” Yai murmushi yace ” sanda naga kin taremin naushin da ya kamata ya sauka a jikina lokacin jinai komai ya daukemin a kuma wannan lokacin na gane meke damuna.” Kallansa tai kallo mai alamar tambaya, kiss ya manna mata a kuncinta yace ” Feena I think I Luv You.” Kallansa tai gabanta ya tsananta fad’uwa baki ta shiga motsawa tana san tai magana ta kasa, Ashraf ya jawota jikinsa yana daga tsaye ita kuma tana zaune akan gado, yace ” Be strong dan nasan akwai yaki babba a gabanmu, sai dai karki damu kowa zai gaji ya bari.” Kai ta jinjina mai, yai murmushi sannan ya saketa ya fita. Ko kallan inda suke baiyi ba yai b’angarensa. Anisa da gudu ta mike tai b’angaren Umma ta shige d’aki ta kulle, maganin Umma ta gani kawai ta debi guda 10, ta hau had’iya, kankace me jiri ya debeta ta fadi kasa ta suma, nan su Umma suka tadda ita a kwance, da gudu Asim ya d’auketa ya sata a mota sukai Asibiti. Nafi kam tana nan a zaune Little ta shigo da sauri bata mata magana ba kawai ta zari mayafi tai gaba, Nafi ta mike da sauri tace “Little ina zaki a daren nan?” Little bata tanka mata ba tai waje, jikin Nafi yai sanyi ta zauna a kasa ji take kamar tasa kuka, sallama taji ta mike ta leka, mai gadi ne ya miko mata leda yace ” gashi inji yalabai.” Yana bata ya juya ya tafi, bud’ewa tai taga magunguna, dana shafawa dana had’iya. Ta mike tai sallar isha’i sannan tasha, akan sallayar ta zauna kawai tana addu’oi Allah yasa komai yazo mata da sauki…… Nima nace Amin….. Su Anisa kam dukansu har Mumy aka nufi asibiti, emergency akai da ita, likitoci suka dukufa akanta, sun dade kafin su gama aikinsu, suka kallesu suka ce ” Kuna ina duk yawanku yarinya na neman kashe kanta? Umma ta harari Mumy tace “Likita masifa ce ta taso mana, bamu fargaba ta shiga d’aki.” Yai dan hucci sannan yace “She is no longer in danger amma sai kun jira zuwa anjima kafin ta farfado.” Yana kaiwa nan yai waje, Umma ta kalli Mumy tace ” Lalai danki dan masifa ne, bala’i ne kuma annoba ne.” Mumy cikin takaicin kalaman Umma tace ” Malama kisan abinda zaki dinga gada nasan yayi laifi amma ko kadan bai cancanci kalamai irin wannan ba daga bakinki ba, dama kowa na gidan.” Sun dawo gida aka bar Umma kadai acan, Mumy ta kalli agoggon jikin mota karfe 12, lalai dole ta hakura sai zuwa gobe ta samu yin magana da Ashraf in ma wasa yake to lalai kar ya sake mata irin wannan wasan. Shikam Ashraf hankalinsa a kwance yai baccinsa, itakam Nafi akan sallaya tai bacci tana jiran Little. Little ta shigo taga Nafi na bacci, shiru tai ta tsaya tana kallanta har ta kai hannu zata tasheta ta koma kan gado ko me ta tuna? Sai naga ta fasa, kayanta ta cire tai kwanciyarta. Mumy tana shiga b’angarensu taga Kawu a tsaye sai zirga zirga yake, yanzu in har da gaske Nafi matar Ashraf ce kenan ko sun kawar da Ashraf itama tanada gadonsa? Gadan me? Bayan ba wanda yasan da auren iya kaci su karyata hakan. Ya zarfafa a tunani sam baiji sallamar Mumy ba sai jiyai ta dafashi, kallanra yai sannan ya zare hannunta ya koma kan kujera ya zauna tare da daure fuska, Mumy ta karasa gunsa tace ” Me ya faru?” Ya kalleta yace ” Abinda yaran nan yai yana matukar damuna, nasan Ashraf bai daukeni a matsayin uba ba sai dai ban taba tunanin zai wulakantani haka ba.” Mumy tai ajiyar zuciya tace ” nikaina abin nan ya tabani, sai dai ina gani ya fadane kawai, gobe zanje in mai magana ai aure ba hauka bane.” Washegari da sasafe su Nafi na bacci sukaji buga kofa kamar za’a b’ala kofar, a razane suka tashi, Little ta bud’e kofar da sauri. Anisa ce a gefenta kuma Umma ce fuskarnan kamar me? Banko kofar sukai tare da shigowa ciki suka gifta Little tare da wucewa gurin Nafi wacce ta mike zaune sai dai kana ganinta kasan a tsorace take, Anisa ta karaso a zuciye ta d’aga hannu zata kifa ma Nafi mari, da sauri Nafi ta rike hannunta duk da tana tsananin tsoron yanda taga fuskokinsu sai dai bazata yarda da duka ba kuma. Anisa ta kalleta cikin tsananin kishi tace ” ke har kin…….” Umma ce tai saurin kifa ma Nafi wani wawan mari ba tare da ta zata ba, Nafi ta sake hannun Anisa tare da rike kuncinta ta kafe Umma da ido, Umma cikin mamaki tace ” ni kike ma wannan kallan?” Nafi ta dauke idanta jitai Anisa ta rufe ta da duka gaba daya hannayenta, Little ta karaso zata tare, Umma ce ta riketa tace “meye naki a ciki? Ke bakya kishin cin mutuncin da akama ‘yar uwarki?” Little ta tsaya jiki a sanyaye, Anisa kam ta dage sai sauken takaicin ta take akan Nafi, can Nafi ta mike ta rike hannun Anisa, tace “Yaya Nisa inaji yanzu kin huce ai ko?” Anisa tai sototo tana kallanta, Umma tace ” mene?” Nafi wacce taji zafin dukan iya zafi ta daure tace ” gani nai dukan ya isa haka inkuma ba kasheni takesan yi ba.” STORY CONTINUES BELOW Umma a zuciye ta fizgo wayar charger dake jikin socket tai kan Nafi zata daketa, Nafi ganin ba sarki aikam ta sake hannun Anisa tai hanyar waje da gudu, jitai ta bugi mutum, ta tsaya tare da d’agowa ta kalleshi, Umma kuma wacce suka taho itada Anisa rike da bulala zata daketa itama ta tsaya cak. Ashraf ya kallesu, yace ” me kuke tunani kuke aikatawa?” Umma ta fara hucci, Anisa kuma kallan yanda Nafi ke tsaye a jikinsa take, Ashraf ya kallesu yace “Umma me kukeyi?” Umma tace ” Kai dan marasa tarbiya,kayi kadan ka wulakantamin ‘yata akan wata banza yar daji, kuma wlh kaji na fada maka ko ba yau ba sai na mata dukan da sai an kwantar da ita a asibiti kamar yanda aka kwantar da tawa ‘yar.” Murmushi ya sakar mata wanda ya bata tsoro, yace “Umma kenan banaji ranar da zakiyi hakan ‘yarki ma zata kwana a gida.” Anisa ta matso cikin takaici tace “Yaya mai kake nufi? In umma ta daketa kana nufin nima dukana zakai ko me?” Hannu yasa ya shafi gefen fuskar Anisa yace ” No no no, kinfi kowa sanin banasan harkar duka sai dai ina nufin a ranar zamana dake ya kare.” Baya baya ta fara ja, tana girgiza kai, wannan ba Ashraf dinta bane, Ashraf ya kalli Umma wacce ta saki baki tana mai kallan mamaki yace ” i tried really hard inga na boye abinda ke raina, sai dai naga alamar bakusan wannan ba, dan haka daga yanzu i won’t tolerate anyone ko da kuwa Little ce.” Yana kai nan ya kalli Nafi yace ” koma ciki ki kwanta zanga wanda zai kara gigin tabaki.” Nafi kam yau ta zama kurma, a hankali ta koma ciki, Umma ta kalleta cikin takaici, Ashraf ya kalli Little yace “kin bani kunya.” ya juya zai fita jiyai Anisa tace “Yaya karka fita.” Juyowa yai ya mata wani kallo yace ” a matsayinki na wa?” Tace “ni ai matarka ce.” Murmushi yai sannan ya tako a hankali har inda take ya rungumota jikinsa sannan yakai bakinsa kunnenta yace ” mata wace take shan maganin hana daukan ciki? Wacce take binciken dukiyar mijinta? Wacce take jiran mijinta ya rasu ta samu gadon sa?” Kallan tsoro tamai, ya matso da fuskarta wajen kuncinta yace ” why? Kin dauka duk ban sani ba?” Ya kara mata murmushi sannan ya juya yai gaba, zubewa tai a kasa tama kasa kukan sam, Umma ta matso tace “ke ya ce miki?” Kai kawai take girgizawa, ganin haka yasa umma ta cicibeta sukai waje. Little kam da sauri tabi yayanta. Nafi kam ita kanta a d’aki zaka tai dabas tana mamakin abinda Ashraf yakeyi tun jiya, ita kanta shakkarsa take taya za’ai ya dinga fadar bakar magana hankalinsa a kwance? Bata taba ganinsa a haka ba lalai kenan akwai wani hali nashi da ya boyema ‘yan gidan. Ashraf na fita bangarensa ya nufa, yau kam gidan kamar ba safiya ba kowa ya tashi, a bakin kofarsa yaga Mumy hakan yasa ya gaidata kai tsaye ya bud’e kofarsa ya shiga. Shigowa tai itama, guri ya samu ya zauna itama ta zauna a kujerar da ke kallansa, Little ce ta shigo ganinsu tare yasa ta koma gun dinning ta zauna. Sunyi shiru kafin Mumy tace ” Ashraf!” Kallanta yai batare da ya amsa ba. Tacigaba “me kake nufi da kalamanka na jiya?” Cikin rashin kulawa yace “me nake nufi kuwa?abinda kikaji shine gaskiya.” Ido ta kuramai can tace ” kasan me kake fada kuwa? Kasan me ake nufi da aure?” Dariya yai ya kalleta yace “Mumy kenan, na dauka ko dan shekara 18 yasan me ake nufi da aure, sannan banyi tunanin zaki damu ba in nayi aure ba tare da saninki be tunda kika sake aure ba tare da sanina ba sannan kika fita daga harkata tun ina karami.” Idanunta ne ya ciciko tace ” Nasani i am a bad mother to you, sai dai Ashraf kai kanka kasan ba inda uwa zataki danta.” Idanu ya rufe yace “gashi kuwa na gani? Tunda nake dake kin taba tambayata yaya nake?meke damuna?menene matsalata? Banaji tun mutuwar mahaifina kin kara zama dani zama na uwa da danta.” Mumy tai shiru, sai idannunta da suka ciciko, Ashraf ya dan rufe bakinsa sannan ya dan sa hannu ya shafi kansa yace ” inaji a jikina ba san mahaifina dani kike ba.” Yana kai nan ya mike zai shiga ciki, sunansa ta kira “Muhammad!” Tsayawa yai cak jikinsa yai sanyi, tacigaba ” bazaka fahimci dalilina na yin hakan ba, sai dai na sani banida wani uzuri da zan kare kaina tunda komai da nai is due to ky selfishness and greed.” Bai amsa ba ya shige d’akinsa, Mumy tabi bayan dakin da kallo tare da share kwalla. Shima yana shiga ya zauna a bakin gado tare da rufe fuskarsa da hannayensa biyu. Mikewa yai tare da yin wanka yasa kaya ya dau jakarsa yai waje ganin lokacin aiki yayi. Little ya gani a zaune bai kulata ba yai waje, itama kasa binsa tai dan jikinta duk ya mutu. Ashraf a gun ajiye motoci yaga kawu shima zai fita, da saurinsa ya karasa gun kawun wanda har abin yaba kawu mamaki, Ashraf ya karasa tare da cewa “dama gunka zan fara isa in naje Company.” Kawu ya kalleshi yace “me? Ka bada hakurin laifin daka aikata?” Ashraf yadan yi dariya yace ” laifi? Basan na aikata laifi ba, sannan magana ce ta inasan kai appointing dina a matsayin chief director a company.” Kallan mamaki kawu yamai yace ” Ashraf meke damunka?” Baki yadan motsa yace ” meke damuna kuwa? So nake inyi sauri in amshi abinda yake a matsayin nawa, me? Laifi ne yin haka?” Kawu ya saki baki yana kallan Ashraf, Ashraf yace “sai naga takarda.” yana kai nan ya shiga mota yai gaba. Nafi kam yau wunin daki tai da azahar Mumy ta aiko akan taje, bayan sun gaisa Mumy fuska a hade tace ” Nafisa so nake ki fadamin gaskiyar meke faruwa.” Shiru Nafi tai, Mumy tace “ki fadamin ko?” Nafi ta kalleta tace “mumy kiyi hakuri.” Mumy ta runtse ido tace “kina nufin da gaske ya aureki kenan? Tun kafin kuzo garin nan?” Kasa Nafi tai dakai, Mumy ranta ya b’aci ta mike tai ciki, Nafi jiki a sanyaye tai waje. ******** Ashraf ya taso daga aiki yana cikin mota a gun traffic light, an tsayar dasu, shikuma yana kan mashin ta saitin gun da Ashraf yake. Ashraf ya leko kansa ganin mai saida ruwan faro ya amsa tare da mikamai dari biyar, yaron yace bari na nemo cangi, kai Ashraf ya girgiza mai yamai alama da hannu akan yaje kawai. Yaran ya juya yana murna, shikuma dake kan mashin ya leko dan ganin me wannan abin arzikin. Kallan mamaki yamai da sauri ya sauka daga kan mashin din ya matso inda Ashraf yake yace ” Wazob main ba kai bane Ashaf?” Ashraf yamai kallan mamaki yace ” Kamar nasan……” Dariya yasa yace ” bari nama inkiya ta, Do you went?🤔” Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace “Dan Littin Gayu?”+ Keya d’an Litti ya sosa yace ” Ashaf nine dai kam.” yai maganar yana washe baki. Dariya sukama juna ganin za’a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje. Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa. Gefen titi suka gangara Ashraf yai parking tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace “Dan Littin Gayu.” Dan Litti yai dariya yace “inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison.” Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace ” Ah haba? Ni ai bantaba tsammanin ganinka a nan ba.” Nan D’an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai. Ashraf yai murmushi yace ” Gaskiya kasha wahala gun nemana, ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza.” Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba ” Shi kuma wannan mahaifin Nafin…..” Sai kuma yai shiru. Dan litti yace ” Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba.” Shiru Ashraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi. Ya juyo ya kalli Dan Litti yace ” yanzu ina zaka?” Dan Litti yace “mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina.” Ashraf yai murmushi yace ” Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turanci.” Kansa ya kara sosa wa yace ” inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin.” Sukai dariya a tare, Ashraf yace “ba matsala mu tafi gidan mu.” Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf. Nafi kam yau gidan duk ya isheta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita. Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d’ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidansu Ferry. Tai sa’a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu. Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda zasuyi. ********* Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa. Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai firgigitbya kalleshi. Fito mu shiga ko?” A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle. Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud’e ya kalli Dan Litti yace ‘shiga muje ko?” Kai dan litti ya girgiza yace “a’a kadai fara shiga.” STORY CONTINUES BELOW Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace ” Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu.” Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace ” Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci.” Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma yai ciki. Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace ” ya akai?” Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace “lalai Datti zai ci Kw*******” Ya karasa yana dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace “KAI! Kai jama’a.” da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace ” ya akai?” Dan litti yace ” Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?.” Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa ” lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan.” ya kara kwashewa da dariya. Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace ” ki sa Nafisa ta kawo min abinci.” Little wacce tun dazu take neman Nafi tace “yaya wlh nima nemanta nakeyi.” Cikin rashin fahimta yace “kamar ya kenan?” Tace “wlh na dawo daga makaranta naga batannan.” Cikin fada yace “to ija taje?” A tsorace Little tace “wlh bansani ba yaya ” Tsaki yaja sannan ya kashe wayar, ya zauna a bakin gado, haushinsa da takaicinsa d’aya da ko waya bai sai mata ba, ya rufe ido cikin takaicin kansa yace ” why?” Yanzu tayaya zai soma nemanta?to inama ta sani da zata? Kansa ya dafe cikin takaici. Yana fitowa sai ga Little ta shigo da tire ta kalli dan litti mamaki ya kamata bayan Habib ba wanda yaya yake kawowa bangarensa,ina kuma ya samo wannan?” Ashraf ne ya katseta da cewa ” ko wa ya dawo?” Kai ta daga alamar eh, fuskan nan tasa a daure yace ” ki buga taro.” Ta amsa da to sannan ta fita, kallan Dan Litti yai yace ” zo ka ci abinci Gayu.” Nan ya kaishi dinning ya turamai tiren gabansa sannan shi ya fita. Tunda ake taro agidan yauce rana ta farko da Ashraf ya fara zuwa gun taron da wuri, zuwa yai ya zauna fuskarsa a murtuke. A hankali kowa ya fara shigowa duk wanda ya shigo sai yayi mamakin zuwan Ashraf da wuri. Bayan kowa ya hallara ne Ashraf ya mike yace ” bayan fitata waye ya kira matata Nafisa?” Cikin mamaki kowa ya kalleshi, Kawu yace ” dalilin taramun da kai kenan?” Ashraf yadan motsa baki sannan yai murmushi yace ” matata bayan fitatavna tabbata wani ya kirata, in kuwa ba’a kirata ba anje har inda take anci zarafinta, dan a yanzu haka bata gidan nan, ban kuma san inda ta shiga ba.” Umma tace ” to menene namu a ciki? Banaji wannan damuwar mu ce, kila ta tafi yawon karuwancinta ne.” Ashraf yq shafa goshinsa yace ” menene naku a ciki? Ina tunatarwa ne da in ban ganta ba ni kaina bansan me zan aikata ba.” Asim ya mike rai a bace yace ” kai! Kayi kadan ka taramu akan wata banzar yarinyar da mu bamu san matsayinta ma a gunka ba, wanda babu shaidar ita matarka ce.” Ashraf yadan yi murmuhsin da har hakoransa suka fito yace ” Little kiramin bakon nan.” Nan ta mike tai waje, Ashraf ya cigaba ” wlh in har wani abu ya samu Nafisa bani da guarantee din abinda zan iya aikatawa.” Mumy ta kalleshi zatai magana kawu yai saurin cewa “nina kiranta bayan ni kuma banaji akwai wanda ya kirata, inka tashi hukuncin sai kamin, tunda yanzu idanka ya rufe akan karamar yarinya sam baka tunanin kowa.” Ashraf ya kalleshi sai dai baiyi magana ba, ya gane Mumy ce ta kirata kenan, tunda yasan ai kawu suna tare gun aiki. Kallan Mumy ya shigayi, ta had’e fuska tace “eh nice na kirata, Ashraf wai meke damunka ne kwana biyi?” Idanunsa ne suka fara canza kala, a hankali ya ke fitar da wani hucci dan kar a gane ransa yakai kololuwa gun tashi. Shigowar Dan Litti ne ya taimakeshi da yayi barna dan tibiren dake gabansa mai dauke da cups na tangaran kawai yake kallo. Dan litti ya tsaya daga nesa cikin tsoro ganin duk an zubomai ido, kuma kallan tsana ake mai. Ashraf ya kalleshi yace ” karka damu mutumina gani nan anan.” Kallan Ashraf yai sannan hankalinsa yadan kwanta, Ashraf ya kalli Kawu yace “to ga shaida na nan na sanda aka daura auren, banaji daga wannan shaidar kuma kuna bukatar wata.” Kawu ya Mike ya kalli Dan Litti yace ” daga ina kake?” Dan litti yace ” kauyen gwaram.” Kawu yace ” menene hadinka da Nafisa?” Kauyensu na kusa da tamu.” Menene ita kuma tsakaninta da Ashraf? Matarsa ce. Wannan kalma ta rikita kowa, Ashraf yama Dan litti alama akan ya koma. Yana fita Ashraf yace ” zan nemo matata da kaina, sai dai bazan yafema wanda ya kuskura ya kara shiga harkarta ba.” Yana kai nan yai waje…… _Ina mika ta’aziyata ga Aisha Y. Kura na rashin mahaifinta datai, Allah ubangiji ya jikansa, yasa aljanna ce makomarsa ya kuma kai haske kabarinsa (Ameen)_6