ZUCIYA CHAPTER 17
Ashraf ya fita daga gun taron rai a b’ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace ” muje inkaika b’angaren baki ka huta ina da gun zuwa.”+ Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu. Ta ina zai soma nemanta??? Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa? Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d’auka yace “ta dawo ne?” yai maganar cikin zumud’i. A hankali tace “a’a yaya.” Yai tsaki sannan yace ” to meye?” Cikin sanyin jiki tace ” yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi.” Da sauri yace “kawa?dama tanada wata kawa ne?” Little tace “Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke.” Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil. Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu ganin Nafi shine a gabansa yace “ina ne gidan?” Tace “wlh bansani ba amma bari na turo maka number ferryn.” Yace “turon to.” Ya kashe wayar tare da dafa sityarin mota yace ” lalai Nafisa zan gamu dake.” Little ce ta turo number da sauri yai dialing sai data kusa katsewa Ferry ta d’auka cikin salon iyayi tace ” HELLO!” Ashraf yace “Farida ce?” Tace “nice, wanene?” “yayan Nafisa ne, tana nan kuwa?” Ta kalli Nafi da suke hira da Ummansu tace “tananan amma….” Da sauri ya katseta yace ” a wacce unguwa kuke?” “kabuga ta fada.” Nan tamai kwatance ya katse layin, tabi wayar da kallo tare da cewa ” kai wannan guy din Feenan sai a slow.” Mikewa tai ta koma gunsu Nafi, Nafi kam Umma ta kalla tace ” Umma ashe Baba acan yai aiki?” Umma tace ” Nabil ne ya fada miki ko?” Daya dawo ai yacemin a gidan Marigayi Abbas kike. Nafi tai murmushi tace ” ba yar gidan bace ba fa.” Umma ta kalleta a nutse tace “kiyi a hankali da wannan gidan.” Kallan mamaki Nafi ta mata tace “Umma meya sa?” Umma ta girgiza kai sannan tace ” nidai abinda zance miki kenan, har yau in na tuno da mutumin nan sai naji zuciyata ta karye.” Nafi ta kalleta cikin damuwa tace “Umma wai wani abun ne ya faru da Marigayin?” Shiru Umma tai sannan ta mike tace “bari in je kitchen Babanku ya kusa dawowa.” Nafi ta bita da kallo cikin kulawa. Tana fita Ferry ta kalleta tace “tashi kiyi wanka.” Nafi tace “ke nifa yanzu zan tafi, duk kece kikasa nai dare haka.” Ferry ta jata ta turata toilet, Nafi tai dariya dama batasan komawa, da saninta tai dare dan Umma ta hanata tafiya, wanka tai sannan tai alwalar magrib ta fito, wata had’adiyar doguwar riga taga Ferry ta fito dashi, ta mata kallan tambaya sannan tace “zance zaki ko?” STORY CONTINUES BELOW Ferry ta matso tace “Feenah gwada rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan.” Nafi ta ture hannunta tace “naki na gwada din.” Ferry tace “shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada.” jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada. Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne. Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya. Nafi tace “wai ina zamu?” Ferry tai dariya tace “sirri ne.” Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d’au wayar tai waje. Nafi ta tabe baki tace “ferry kenan uwar soyayya.” Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi. Nafi tai dariya tace “lalai to ke yaushe zaki shirya?” Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma. Nafi tace “Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?” Ferry tai dariya tace “sauko.” Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad’aba ta mike a hankali suka sauko. Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya. Nafi tai godiya suka sauko. Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa. Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace “Me kakeyi anan?” Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace ” Ba Ashraf bane?” Kallan mamaki Ashraf yamai yace “nine…Amma???” Baba yace ” me kake anan?” Ashraf ya kalleshi yace “a ina kasan ni amma?” Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace “na ganka a magazine ne.” Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida. Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai. Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya itama, ferry tace “muje mana sanyin ranki ne.” Nafi ta kalleta tace “ya akai yasan gidan nan?” Ferry ta nuna kanta da hannu, tace “kina wasa dani ko?” Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d’auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?” Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d’ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad’an shagwab’e fuska. Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace “yaya ni zan koma.” Ashraf ya kalleta yace “Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici.” STORY CONTINUES BELOW Dariya tai tace ” ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya.” Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d’auko wallet dinsa ba?” Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace “karki damu zan kawo tukuicin daga baya.” Tace “ba komai yaya.” Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, “ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan.” Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace “muje ko?” Tad’an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace ” bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba.” Ta kalleshi fuska a shagwab’e tace ” me nai da za’amin fada?” Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata ” Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina.” Itama a hankali tace “Name fa?” Yace “nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba.” Idanu ta lumshe sannan tace ” nifa ba yau naso komawa ba.” D’agota yai yace ” kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?” Kallansa tai tace ” ni kam ban saba da zancen miji ba.” Ya matso da bakinsa kuncinta yace ” ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d’in nan?” Idanu ta zaro da sauri tace ” a’a bance ba.” Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d’ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace “Allah ka d’auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin.” Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace ” b’angarena zamuje.” Idanu ta zaro tace “muyi me?” Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace “uwar tsoro abu kawai zan baki.” Tai murmushi batace komai ba. Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b’angarensa yace “ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d’aki.” Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya. Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita. Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace “kwanta.” Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d’an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin. Ashraf fuskarta yake kallo yace ” gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?” Kai ta d’agamai fuskarta d’auke da murmushi. Idanu ta bud’e a hankali tace ” na d’agama hankali da baka gan ni ba?” “Hmm, ban taba zatan zanji haka ba.” Tai murmushi tace ” I can’t help dole ne in sake guduwa wani gun.” Harararta yai ya had’e rai yace ” in kika sake gwadawa zakiga b’acin raina da baki taba gani ba kuwa.” Ta turo baki tace ” sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba.” Hararata yai yace ” ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina.” Tace “mekenan?” Yai furzar da iska yace “bazan iya fada ba.” Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah. A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud’e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d’an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare. Da sauri tace ” Yaya.” A hankali yace “Uhmm.” Tace “Abba hatsarin mota yai ko?” Kallanta yai yace “eh.” Tace “kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?” Yace eh. Tace ” Motar Abba alokacin an duba meya jawo hatsarin?” Kallan ta yai gaba d’aya hankalinsa na kanta, idanunsa taga ya kada sosai, ta mike zaune, tace” yahkuri in na ba…..” Jawota yai ya rungumeta tsam a jikinsa, yace ” me kike tunani?” Kai ta girgiza alamar ba komai. Ya dago ya kalleta hannayensa na kan kafadarta, yace ” Nasani Nafisa sai dai banasan ki cigaba da binciken abinda bai shafeki ba.” Hawaye ne ya zubo mata na tsananin tausayin Ashraf, idanunta na kansa tace ” Na dauka duk abinda ya shafeka ya shafeni?” Hannu yakai a hankali ya share mata hawayenta yace ” ba haka nake nufi ba…..” Tacigaba da zubar da hawaye tace ” Y are u enduring everything by ur self? Can’t u share it with me?” Kallanta kawai yakeyi, tacigaba da cewa ” kwanaki kasheka ya Asim yaso yi, amma ba wanda ka fadama, abubuwa nawa ka sani wanda baka fadama kowa ba? Kana tunanin in kabar mutanen da sukeyin evil deeds saboda ‘yan uwane kana tunanin zasu daina?” Yauce rana ta farko dayakeji har cikin jinin jikinsa lalai yarinyar nan ta damu dashi lalai tana sanshi saboda Allah, lalai zata iya komai domin shi. Jawota yai a hankali yakai bakinsa cikin nata… Wata duniyar suka shiga kiss suke deeply wanda gaba d’ayansu wani feelings sukeji wanda su kadai ne sukasan abinda sukeji tundaga kansu har kafafuwansu……… Ni dai nace to fa ayi a hankali kar a gangara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣. Sun yi nisa sosai, Ashraf ya saketa a hankali, da sauri ya shiga d’akinsa, itakam kafafunta ta had’e dan jitai har su rawa suke, tun da take bata taba jin abinda taji yau ba, wani irin feeling ne wannan???” + Ashraf kam kwanciya yai rufda ciki akan gado, wata muguwar sha’awa ce take tasomai sai dai bazai taba kusantarta ba har sai ta aminta dashi a matsayin miji, juyi ya shiga yi. Nafi kam ta dade itama a zaune kafin tabi kofar d’akinsa da kallo, ya kamata ta tafi kafin dari yayi sosai, a hankali ta mike tai d’akin. Sallama tai jin shiru yasa ta murd’a kofar d’akin, Ashraf najin haka yai saurin rufe idanunsa, kallansa tai a hankali ta tako tazo inda yake. Zama tai a gefensa takai hannu kan sumar kansa, ta kurama fuskarsa ido, a hankali tace “bacci?” Jin shiru yasa tad’an turo baki tace “shine ka barni a zaune kai ka taho ka kwanta?” Shiru tai tare da cigaba da kallansa a hankali takwantar da kanta saitin fuskarsa suka zama fuskokinsu na fuskantar juna, ta sa hannu a kan kuncinsa sannan tace ” please let me be the first person whom you can trust.” Murmushi tai sannan ta kai bakinta a hankali kan leb’ensa ta sumbata, sannan tace “Goodnight.” Ta mike tare da jamai bargo tai waje, b’angarensu ta nufa a zaune taga little a falo ta matso da sauri zata mata magana taga Little ta mike tayi ciki, Nafi tabi bayanta. Toilet ta wuce direct dan da alama tanajin jikinta ba yanda yake ba, a gun tsarki ta gano lalai abinda ya zubo na sha’awa ne, nan ta wanke wandon ta ta gyara jikinta tasa wani sannan ta fito. A kwance taga Little ta kalleta tace “Little yanzu haka zamuyi ta zama bakya kulani?” Little bata tanka taba, Nafi tace ” ban taba tunanin zaki iya kin kulani ba saboda kinji ance ni yar kauye matar yayanki bace, ni kaina nasan ban kai wannan matsayin ba, sai dai……..” Little ce ta katseta da cewa ” kin dauka saboda matsayinki a gun yaya nake miki haka?” Nafi ta kalleta tace “to menene in ba shiba?” Little ta mike zaune tace ” shekararmu nawa tare?nikenan da miki zancen saurayi akan ki kula wane ki kula wane, bansani ba ashe mahaukaciya kika mai dani.” Nafi cikin mamaki tace “mahaukaciya kuma?” Cikin zafi Little tace “mahaukaciya mana, inba haka ba da igiyar auran yayana a gunki amma nake neman had’aki da wani?” Nafi ta matso tare da rike hannun Little tace “Little kiyi hakuri wlh ni kaina mantawa nake akwai abu a tsakanin mu.” Nan dai Nafi tai ta bata baki har ta hakura, sun dan yi hira kadan kafin Nafi ta kalli Little tace ” nikam Little wani abu na damuna.” Kallan mamaki Little ta mata tace name kenan?” Nafi tai shiru can tace ” Abban Ashraf na ga shine ya fara zancen had’in auren Yaya da Ya Nisa, to menene dalilinsa na ajiye wasiya yace a ba matar Ashraf ta farko bayan yasan ko ince Yaya Nisa yakesan ya fara aura?” Shiru Little tai can ta girgiza kai tace “ban sani ba, ni banma taba kawo abin a raina ba, amma kina ganin da wani abun ne?” Kai Nafi ta girgiza tace “ba komai, bari nai sallah.” STORY CONTINUES BELOW Ta mike tana tunani tabbas da wani abun, sai dai menene????? ************* A b’angaren Ashraf kuwa tana fita yabi bayanta da kallo yanaji kamar ya jawota ya rungumeta sai dai ina bazai iya hakan ba, bayan yayi sallah ya d’aga katifarsa ya d’auko wani karamin makulli sannan ya zugi wardrobe dinsa ya ture kayan, nan wata yar karamar kofa ta bayana, nan yasa makuli ya bud’e ya zaro wasu takardu a ciki sannan ya koma ya kulle kofar d’akinsa da makulli ya zauna tare da baje takardun nan, bayan ya gama bincikensa da ‘yan rubuce rubucensa ya maida ya rufe sannan ya juye fuskarnan a murtuke kamar mai tafiya yaki yace ” Mu zuba mu gani.” 1 Kan gado ya kwanta ya sa diary d’in mahaifinsa, wani shafi ya bud’e an rubuta _Someone! Somewhere is made for u my dearest son_” Murmushi yai da ya tuna abinda nafi tace da kiss din data mai, hannu yakai kan leb’ensa yace ” yarinyar nan kamar ba ruwanta ashe itama killer?” A haka har bacci yai gaba dashi. Da safe ya tashi tare da sawa a kiramai dan litti, sunyi breakfast kafin Ashraf ya kalli Dan litti yace “yanzu me kakeyi?” ” Achaba.” Ashraf ya jinjina kai yace “mota fa ka iya?” Dan litti ya d’aga mai gira yace “ka sanni ai akwai karambani ai zamana a kachako sai da na koya.” Ashraf yace “gaskiya nafa sanka.” Dariya sukai kafin Ashraf yace ” zaka koma kauyene?” Da sauri yace “a ina?ai ni yanzu i am big for them.” Ashraf ya sa dariya yace “u are big?wato baka daina bako?” Ashraf ya mai alamun zip a bakinsa yace “na daina kai kawai nake san ma.” Ashraf yace “to in ba matsala nafisan ka zama driver d’ina, saboda nafisan wanda zan yarda da shi.” Zaro ido dan litti yai yace ” Ashaf kana kasheni in nazama driver dinka ai na zama dan gomna.” Dariya sosai Ashraf yai yace ” whoa! Dan litti kai kadai ke sani dariya akai akai.” Dam litti ya mike tare da yima Ashraf salute yace “yes sir!” Ashraf yai murmushi yace ” kaii ban taba ganin mutum irinka ba.” Dan litti ya zauna yace “Ashaf karka damu zan zama mutum mai rike ma amana, dama tunda muka hadu nake sanka bazan taba bari wani abu ya cuceka ba.” Ashraf yai murmushi sannan ya dafashi yace “thanks, amma kanaso kacemin wai baka iya fadar Ashraf bane ko ya?” Dan litti yai dariya yace “in na cema Ashraf ai mantawa zakai nine d’an littin gayu.” Dariya suka sakeyi kafin su mike su fita. Makullin motarsa yaba Dan litti shikuma ya wuce b’angaren kawu. A tsaye ya ganshi shima zai fito, mumy na kusa dashi, wani takaici ya kara kamashi ya matso kusa da kawu ya gaisheshi fuska dauke da murmushi sannan ya gaida mumy. Bayan sun amsa ne kawu yace “Ashraf ya akai?” Kallan mumy yai yace “magana nakeso muyi.” Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tai waje, ya matso kusa da kawu fuskarnan a sake yace “naji shiru ne, jiya banga takardar appointment ba.” Kawu ya kalleshi yace “wai da gaske kake?kasan fa matsayin Asim ne ya kakeso inyi.” Wani murmushin rainin hankali yai tare da jinjina kai yace “ahhhh! Na manta ko da yake ba matsala ka barshi a matsayinsa kai sai ka bani naka, dama ai can nawa ne ko ba haka ba???” Ya fada yana kallan kawu. Kawu ya shiga hucci, Ashraf yai murmushi sannan ya dan girgiza d’an yatsansa yace “No no no, kawu how can u get angry? Bayan a sama kaga komai?wanda ya sha wahalar yana karkashin kasa?” Kawu ya kalleshi sannan yai yake yace “ce maka akai raina ya b’aci?” Ashraf ya d’an kanne idanuwansa yace ” why?kunya kake na gano hakan? Hmm ko da yake ba matsala yi zamanka a kujerarka nizansa ka sauka da kanka in har baka ajiye da hannunka ba.” Yana kai nan yai waje,yana fita kawu ya shiga hucci, jakarsa ya cillar can gefe sannan ya zauna a kujera yana maida numfashi kamar wanda yai gudu…… Ashraf ya fitowa ya harari d’akin sannan ya juya, jiyai ance “Ya Ashraf.” Juyowa yai ya kalli Anisa wace duk ta dan fada a kwana biyu, ya matso yace” ya akai?” Kallansa tai tace ” yaushe zaka zo ka maidani b’angare na?” Kafada ya d’aga yace “da nina kawoki nan?” Kallansa tai tace “yaya ni bazan koma bane harsai ka saki wannan yar kauyen dan pride dina bazai bari in iya kallanta ba, kace ta koma kauyensu.” Hannu yasa ya dafata yace ” a maysayinki na wa kenan?” Tace “yaya!” Yai murmushi yace ” karki damu kiyi ta zamanki a gun mahaifiyarki gani nake zatafijin dadin hakan, nima kuma zan samu saukin bincike min d’aki da akemin.”1 Yana kainan yai gaba, kallo ta bishi dashi yasan komai meyasa bai taba magana ba???? Mota ya wuce, dan litti ya bud’e mai baya nan ya shiga ya rufe shikuma ya shiga mazaunin driver. * Ashraf yacema dan litti akan su tsaya a wani babban shago na wayoyi, nan suka fita tare.+ Waya ya d’auka kirar Samsung S7+ karamar ta hannunsa, sannan ya kalli Dan litti yace”kaifa wanne kakeso?” Kai Dan litti ya sosa, Ashraf yace “shikenan in ba ka so.” Da sauri yace ” ni kowacce ma ina so.” Ashraf yai murmushi yace “a d’auko mai Iphone 5.” Wani ihu da dan litti ya sake sai dayasa mai wayar ya kwashe da dariya, nan suka sai sim sannan ya kara siyan wani extra sim sannan suka fito. Suna shiga mota ya d’auko wata yar karamar waya daga cikin jakarsa, yasa wannan d’ayan sim d’in a ciki sannan ya maidata jakar. Sun isa gun aiki Ashraf ya fito d’an litti yabi bayansa, Asim ne wanda yake tsaye yake jiran isowar Ashraf ya taso da sauri, ya taho gun Ashraf fuskarnan a had’e. Dan karamin tsaki Ashraf yaja a ransa yace “The fool is here.” Asim na karasowa ya kalli Ashraf yace ” Kai bakaji kashedena ba ko? Akan kaba yarinyar nan takardarta ta bar gidan nan ba ko?” Dan litti ya matso yace ” Malam meye hakan?” Murmushi Ashraf yai yace ” barshi magana zamuyi.” Nan Dan litti ya matsa tare da had’e fuska kamar irin shi akama abun nan. Kallo Ashraf ya maida kan Asim yace ” Mahaifinka yace zai bani matsayinka, mai kake tunani?” Idanu Asim ya zaro tare da kumburo baki yace “matsayina? What do u mean?” Ashraf ya dafashi yace ” what do i mean? Da alama sai ka tambayi mahaifinka da ya dage akan bani matsayinka, mayb kuma ya kula ne u are useless.” Yana kaiwa nan yai gaba, Dan litti yabi bayansa rike da jakarsa yana hararar Asim. Ashraf ya kalleshi yace ” Dan litti kasan kanin mahaifina?” Kai ya girgiza alamar a’a yace “jiya dai na ganshi sai dai banaji zan iya gane shi.” Ashraf yace “zan nuna maka shi inaso ka dinga kulamin dashi akan abubuwan da yakeyi da kuma wadanda yake gani, sai dai karka bari kowa ya ganka kar kuma asan abinda kakeyi.” Dan litti ya mai salute da hannunsa yace “yes sir.” Hannunsa Ashraf ya ture yace ” sorry ba a military muke ba.” Nan sukai dariya sannan suka shiga. Jakarsa Ashraf ya kaimai sannan ya juyo ya fita. Asim kam yana gama magana da Ashraf yai office dinsa kamar zai fadi saboda sauri, yana zuwa ya ture takardun kan desk dinsa da hannayensa biyu, ciki hucci yace ” ni zakama haka Abba?” Kawu kam yana zuwa office yasa aka rubuta takardar ragema Asim matsayi aka aika mai. Asim yai shiru yana kallan takardar, can cikin takaici ya yaga takardar sannan ya mike cikin fishi yai office d’in kawu. A zaune ya ganshi shi da manager suna magana, nan ya tsaya suka gama, manager din ya fita sannan ya shiga. Tsayawa yai a kan mahaifinsa yace “ban yarda da ragemin matsayin nan ba.” Kawu yace ” kasan complain din da ake kawomin naka kuwa?in ban rage ma matsayi ba mai kake tunani mutane zasu daukeni?” Mamaki ya kama Asim yace ” wa zaka ba matsayina? Ashraf?” STORY CONTINUES BELOW Kawu ya juya kai yace ” haka shareholders da director’s suka yanke.” Dariya Asim yasa yace ” ko kuma ka tsara ba?” Kawu ya had’e rai yace “kai ni kake fadama haka?” Asim cikin hucci yace ” ni dai na fada kar a kuskura a ragemin matsayina in ba haka ba zan iya tona abubuwan da na sani.” Mikewa kawu yai tare da dukan desk dinsa da hannu yace ” me zaka tona?” Yai dariya yace “abubuwan da kai, kana tunanin in Ashraf yaji zai barka?wato yanzu tunda kaga Anisa batada matsayi a gunsa shine kake neman juya mana baya ka koma gunsa ko?” Kawu a zuciye ya d’aga hannu ya kai mai mari, Kallansa Asim yai sannan yai waje rai a b’ace.” Kawu ya bi bayansa da kallo sannan ya zauna tare da rike kansa. Asim sama yahau cikin takaici yahau hucci tare da kara, ko aure bai taba kawowa ba saboda yanasan ya gaji Company din nan, shine yanzu mahaifinsa zai fara juyamai baya??” ************ Nafi kam bayan ta gama aikin gyara musu d’aki ta zauna tare da daukan qur’ani tana karatu. Mumy ce ta aiko a kirata, nan ta mike gabanta na faduwa tai waje. B’angaren Mumy ta nufa ta zauna tare da zama a kasa. Mumy ta kalleta tace ” jiya ina kika je?” Nafi kanta na kasa tace ” Gidan wata kawata da mukai makaranta.” Mumy ta kalleta tace ” ina sanki a natsayinki na yarinyar da aka taimaka amma ba wai a matsayinki na matar Ashraf ba.” Nafi ta d’ago a hankali ta kalli Mumy. Mumy ta cigaba “Ashraf bai samu kulawa daga gareni ba sai bakin ciki dana dinga kunsa mai, mahaifinsa ya rasu hankali bai gama shigarsa ba.” Idanun Nafi suka ciciko, Mumy tace ” sai dai hakan ba yana nufin zan yarda ya auri mara ilimi ba alhalin aiki babba yana gabansa, yana bukatar matar datasan gari sannam takeda ilimi at least degree, shine wanda zai gaji mahaifinsa.”4 Nafi tai kasa da kai hawaye suka zubo mata, Mumy tace ” kije kiyi tunani in har kina san Ashraf to kiyi tunanin menene abinda zaifi amfanarsa a rayuwar nan.” Nafi ta mike a hankali tana share hawayenta, b’angarensu ta nufa, da gudu mai gadi ya karaso yace ” yallabai yace wai ki mai abincin rana zai dawo da anyi la’asar.” Kai ta d’aga sannan ta koma ciki. Ana azahar ta fito tai kitchen ta fara mai girke girken Asabe na tayata. ********* Umma da Anisa kam suna zaune abin duniya ya damesu, Anisa can ta nisa tace ” duk laifinku ne Umma, meyasa kuka hanani haihuwa dashi?” Umma tace “mene?” Anisa ta cigaba” da yanzu akwai zuri’a a tsakaninmu ko baya sona ai nasan halin Ashraf bazai wulakantani ba.” Umma ta mike tsaye tace ” Anisa meke damunki?” Anisa cikin dan fada tace ” wlh ni duk ku kuka cuceni, da ace na haihu dashi ai da d’ana shine zai zama yanada gadon dukiyar Ashraf amma dayake ba ni kukeso na gaji dukiyar ba shi yasa ba wanda yai wannan tunanin.” Tana gama fadar haka ta mike tai cikin d’aki tare da bugo kofa da karfi, Umma ta bita da kallan mamaki. ******* Karfe hud’u da rabi Ashraf ya dawo, b’angarensa ya nufa, shima dan littibya wuce nasa. Zama yai tare da d’aukan waya ya kira Little, yace “kin dawo?” Tace eh yaya. Yace “ki turomin Nafi.” Ta amsa sannan ya kashe. Nafi ta kalla wacce tai wanka tai kwalliya cikin atamfa riga da siket, bata d’aura d’an kwalli ba kanta ba kisto sai dai ta tifkeshi da ribon. Kan nan yayi gwanin sha’awa. Little ta kalleta tace ” Yaya na kiranki, da alama dama shi kike jira.” Nafi ta harareta tace ” ni wai ina mutumin ki? Naji shi shiru kwana biyu. Little tace “tafiya yai wlh amma gobe zai dawo.” Nafi ta zari d’an kwalinta tai waje. Kitchen ta nufa ta d’auko tiren data jera mai abincinsa sannan tai b’angarensa fuskarnan fal take da farin ciki, dukda dai kalaman Mumy suna kara yimata yawo a zuciyarta. A bud’e taga kofar hakan yasa tasa kai tare da sallama, Ashraf wanda ke zaune akan kujera ya kalleta fuskarnan d’auke da murmushi, dinning ta wuce ta ajiye sannan ta tsaya daga gun tace “ka taso.” Hannu ya mata alamar tazo nan tad’an yi kasa dakai sannan ta make kafada tace ” naki ni dai ka taso.” Murmushi yai ga mamakinta sai taga ya taso ya nufota, jingina tai da jikin dinning din tana kallansa fuskar nan d’auke da murmushi. Ya karaso kusa da ita batai zata ba sai jitai ya rungumeta. Murmushi tai sannan tace ” Yaya ka dawo lafiya?” ” Hmm lafiya lau, jiya yaushe kika tafi?” D’agowa tai ta kalleshi tad’an mai hararar wasa tace ” ba bacci kai ka shareni ba.” Idanu ya zaro yace garin yaya?” Ta turo baki tace “Allah yaya indai ina zuwa gunka kana min bacci ko?” Bakin data turo ya d’an sumbata hakan yasa ta maida shi da sauri, yace ” me za amin?” Kallansa tai tace ” kazo kaci abinci.” Murmushi yai sannan ya saketa ya ja kujera ya zauna tare da nuna mata kujerar kusa dashi. Nan ta zauna ta zuba mai, kallanta yai yace ” muci.” Tace ” am full.” Idanu ya kafeta dashi hakan yasa ta mike ta d’auko wani spoon din ta zauna. A hankali suke ci sai dai ya kamo hannunta na hagu ya rike. Bayan sun gama ne ta zubamai juice ya sha sannan suka mike. Hannu yasa a kugunta ta kalleshi tai murmushi a haka suka karasa ya zauna akan kujara tare da jawota kan cinyarsa. Kallansa tai tace ” yaya inada nauyi fa.” Dariya yai yace ” indai kinada nauyi to lalai Afra ma tanada nauyi.” Cikin shagwab’a tace ” Afran?”” Ya d’aga mata kai sannan ya d’auko ledar dake gefensa yace ” Gift.” Kallansa tai ta amsa zata bud’e yace ” ba anan ba sai kin tafi kya bud’e, yanzu dai tukuicina zaki bani.” Yai maganar yana mata wani kallo, itakam in Yaya na mata irin wannan abun mamaki takeyi dan a iya saninta da gani take mutum ne wanda bashida sakin fuska, sai dai ferry dama ta fada mata maza duk daya suke indai a harkar so ne, kenan shi yana santa da gaske.” D’an kwalin kanta ne ya zame, kanta ya kurama ido, a hankali yakai hannu ya shafa yace ” i like this.” Murmushi tamai sannan tai kasa da kanta tace ” tukuicin me kake so?” Nesa dashi ya nuna mata yace zauna, nan ta tashi ta zauna a gun, zatai magana taji ya kwantar da kansa kan cinyarta yace ” a gajiye nake, so nake inji ya bacci yake a kan cinyar matata.” Kallansa tai tare da sa hannunta kan fuskarsa tace ” amma ai kana kwanciya akan cinyar yaya Nisa.” Yai murmushi bai ce komai ba sai idanunsa daya rufe. Murmushi tai sannan tasa hannu ta fara shafar kansa. Ta ina zata iya rabuwa da Ashraf? Bataji zata iya, in kuwa tai to gaskiya rayuwarta ta gama karewa.