ZUCIYA CHAPTER 21
Da yamma Dan litti ya kawo mai mota, bai bari ma sun gaisa ba makullin kawai yaba mai gadi ya juya yai gaba.+ Suma wajen karfe 6 suka fito daga gidan, hannunsu rike da juna, tana dan dingisa kafa kadan kadan. Tuki yake zuciyarta nata sarka masa abubuwa kala kala, Nafi kam ganin haka yasa ta kwanta kawai batace komai ba. Sunje shiga gida ya zaro Atm daga wallet dinsa ya mika mata. Kallansa tai tace ” Name nene?” Yace ” nasan akwai abinda kike bukata sai kuje ke da Little, sannan ki barshi a gunki incase in akwai abinda zaki bukata nan gaba.” Kallan mamaki tamai tace ” nan gaba in zan nema ba sai na fadama ba?” Kansa yad’auke baice komai ba. A karamar purse dinta ta saka suka shiga gida. Sunje gun ajiye mota sukaga Anisa da su Umma a tsatsaye sai masifa akeyi, ga Asim nan ya rike kofar motar Anisa shima yana fada. Tunda suka kula da motar Ashraf sai duk suka zubama ma motar ido kowa fuskarnan a murtuke, Nafi kam yau ko a jikinta jitake yanzu bazata iya jurar wulakancin kowa ba. Ashraf na tsayar da motae ya bud’e da sauri tare da kallansu, kafin yai magana Anisa ta matso a harzuke ta cakumi wuyan rigar Ashraf kamar zata fashe saboda tsabar masifa tace ” Wlh Yaya yau sai ka zaba ko ni ko wannan yar iskar, har ni zatacima mutunci d’azu? Sannan yanzu ka dauketa kun tafi yawan iskanci, wlh da so nai in ja mota duk inda kuke in nemeku, nagaji da wannan dadirancin da kukeyi.” Umma ta matso itama tace ” Kai Ashraf a wani matsayi Anisa take a gurinka? Ka maidata kamar ba matarka ba sam ka daina ko shiga harkarta, kana tunanin mu iyayenta zamu barka ne?” Asim kam kallan Ashraf kawai yake yana hucci. Nafi ta bud’e motar ta fito tana kallan ikon Allah, Ashraf ya zare hannun Anisa daga jikinsa a hankali yace ” Nisa calm down wannan fadan fa?” Kallansa tai idanunta ya ciciko tace ” yaya bazan iya ba, na san ba sona kake ba, ni kuma wlh bazan iya zama da waccen tsinaniyar ba.” Ta fada tana nuna Nafi. Ashraf ya dan kalli Nafi kadan sannan ya maida idansa kan Anisa mayafinta da ya fadi kasa saboda masifa ya tsugunna ya d’auko mata, ba wanda ya zata sai gani sukai ya yafa mata mayafin ya kalleta cikin kulawa yace ” Nisa kalleni nan.” Jikin kowa ne yai sanyi, Umma a ranta tace ” dama ta ina za’ace yaron da suka taso tun suna kanana har yafi san wata wacce basu dade da haduwa ba.” Nafi kam jitai wani abu ya tokare mata makoshi, kallansu kawai take tama kasa ko motsi. Asim ma mamakin Ashraf ne ya kamashi. Gogar kuwa duk jikinta ya gama sanyi kallan Ashraf kawai take kamar yanda ya umarceta, Ashraf yace ” Nisa!” A hankali tace ” Naam.” Yai murmushi yace ” Yauwa ko kefa.” Kallansa ta tsaya tanayi, ya saketa tare da juyawa ba tare da ya kalli Nafi ba zai wuce. STORY CONTINUES BELOW Da sauri Anisa ta riko hannunsa tace ” yaya nidai wlh ka zaba ko ni ko waccen, banaji zan iya ganin tana zama kusa dakai zuciyata bata fashe ba.” Ba tare da ya juyo ba ya had’iyi wani abu sannan yace ” Karkisata a ranki u r so dear to me.” Yana kaiwa nan ya ja hannunsa yai gaba. Nafi kam bata san sanda taji hawaye ya zubo mata ba tana kokarin mai magana taga ko kallanta baiyi ba yai gaba. Yana tafiya Umma ta matso gunta tana dariya tace ” ah ah su Amarsu yanzu kin tabbatar da matsayinki?” Kallansu tai ba tare da ta tanka ba, mamaki take mai ya samu Yaya daga shigowa? Umma tai dariyar mugunta tace ” ah to da an fada miki barno gabas take? Shi dama namiji kan ya samu abinda yake so ne zai ta lallabaki amma da ya samu shikenan kin zama kashi.” Wani irin kallo Nafi ta kafe Umma dashi, Umma ta wanka mata mari tace ” A da in mun barki kinyi iskanci saboda mijinki ya baki matsayine bawai yanzu da kike kamar bola ba.” Anisa ta matso tace ” ke harkin isa dama kice zaki kwace min miji? Yar kauye dake? Mutumin da na taso dashi tun muna yara ke kuwa yar karo?” Nafi wacce ke rike da kuncinta ta daure tace ” wannan kuma tunaninku ne ba na yaya ba.” Tana kaiwa nan ta fara dingisa kafa tana gaba. Anisa ta matsa ta fizgota da karfi tace ” ni kika fadama magana d’azu ko?” Nafi ta kalleta tare da fincike jikinta ta cigaba da tafiya, Anisa tasa dariya tace ” yi maza ki je ki shiya yan kayan da kika samu anan kafin insa a baki takardarki.” Nafi bata juyo ba tai bangarensu. Tana shiga ta zauna akan kujera a falo, meke faruwa? Tayaya ya Ashraf zai canza mata lokaci d’aya? Da sauri ta girgiza kai alamar a’a tace ” Yanada reason dinsa ni na sani, zanje anjima in ma laifi na masa in bashi hakuri.” Da wannan shawara taji hankalinta ya kwanta. Anisa kam tana ganin tafiyar Nafi suka kwashe da dariya, Asim ya matso yace ” Anisa ina mamaki fa ya akai hakan?” Anisa ta dan yi fari da ido tace ” yaya na sona ni nasani kawai abinda ya faru ne yasa ya shareni.” Asim yace ” to yanzu kije ki lallabashi ki samu kisan yawan dukiyayonsa da kuma inda takardun suke, karki bari ya gane komai.” Kai Anisa ta jinjina alamar gamsuwa tace ” karka damu yaya ni nasan ya Ashraf a tafin hannuna yake.” Dariya sukai dukansu, Anisa ta wuce bangaren Umma da sauri tai wanka ganin magrib tayi tai sallah sannan ta saka wasu riga da siket ‘yan kanti sun bi jikinta sosai. Mayafi ta yafa sannan ta fito tace “Umma ya kika ganni?” Umma ta shiga tafa mata tace ” yauwa ‘yata sai da safe.” Nan Anisa ta fito cikin tsantar farin ciki. Bangarensu ta nufa tare da bud’e kofa. Ashraf na zaune ya baza wasu takardu yana dubawa, jin motsi yasa ya d’ago. Ganin Anisa yasa ya sakar mata sansanyan murmushi. Cikin rangwada ta karaso gunsa tace ” yaya shine bakazo biko ba ko?” Kallanta yai bayan ta zauna daf dashi yace ” sry Nisa kunya ce ta hanani zuwa.” Kankameshi tai tace ” yaya nagode da ka nunamin kana sona.” Zareta yai daga jikinsa yace ” Amma kin dawo kenan ko?” Cikin shagwaba tace ” anya kuwa?” tafada tana karema takardun kallo, tace ” wad’an nan fa?” Tataresu ya farayi yace ” ba komai.” ya fada tare da mikewa da sauri Ya nufi d’akinsa.” Kallan bayansa tai tace “da alama takardune masu amfani ganin yanda ya kwashesu da sauri, sannan da tana dubawa taga kamar takardun fili.” Mikewa tai da sauri tabi bayansa, kofar dama bai rufe taba. Yana kokarin sawa a drawer ta jikin madubi sai ga Anisa. Da sauri ya tura yasa key, ta matso gunsa tare da rungumeshi ta baya tace ” ka gama?” Makullin ya bari a jiki ya juyo ya kalleta yace ” eh muje falo.” Nan ta kara kallan gun sannan sukai falo. zama sukai ta zauna akan cinyarsa tare da rungumeshi ta fara sambatarsa, sam hankalinta ya gama tashi saboda rashinsa datai kwana biyu bataji buga kofar da ake ba. Ashraf ya d’an zareta kadan yana kokarin sauketa Nafi ta turo kofa, tunaninta jin tanata bugawa ba’a bud’e ba mayb yana masallaci sai tai tunanin ajiye masa abinci tai gaba. Cak ta tsaya daga jikin kofa tana kallansu. Anisa kam ganin Nafi ce yasa tai wani dariyar mugunta sannan ta kara kai bakinta cikin na Ashraf tana mai wani saban salo. Nafi kam jitai jikinta yana kakkarwa anan bakin kofar ta ajiye abincin tai waje da sauri. Tafiya kawai take batasan inda take sa kafarta ba sam kuma bata kallan gabanta. Saura kiris ta buge da bango taji an jawota, kallan wanda ya jawota tai, jitai yace ” Gimbiya me kike tunani haka?” Kallansa take kamar bata cikin hayyacinta ta kwace hannunta tana kokarin ci gaba da tafiya. Gabanta yasha yace “Gimbiya menene? Baki kula dani bane?” Kallansa tai sannan ta kewayeshi tai gaba. Bin bayanta ya farayi yana mata magana sai dai da alama batama san yanayi ba. Sunje shiga bamgarensu, Little kuma na shirin fitowa. Ganin Nafi yasa ta karaso da sari tace ” Ni harzan gudu gun Mumy muyi hira dan nasan ke kuma sai gobe ni da na ganki.” Nafi ta kalleta sai dai batace komai ba, muryar Habib taji yace ” Princess kece?” Da sauri ta matsa daga gun Nafi ta karasa gun Habib, itakam Nafi ciki ta shiga kawai ta zauna a bakin gado. Hoton yanayin datagansu sam ya ki barin kwayar idanunta, ta sani matarsa ce ba kuma ta da hakki akan hanashi yin abinda yaga dama da matarsa sai dai me yasa takeji kamar Ashraf yayi betraying dinta?????? Nikaina bansan me zance ba Feenah👩🏻🏭 ittle ta kalli Habin tace ” Yaya sai yau fa naganka!” cikin shagwaba tai maganar, ya kalli kofar da Nafi ta shiga yace ” Princess nazo ai bamu hadu bane ba kawai.”+ Ta dan turo baki tace “na kiraka ma baka dauka ba.” Ya hada hannayensa biyu yace ” sry mayb ban kula bane.” Ta kalleshi tace ” naga sako na gode.” Kallan mamaki ya mata yace ” sako?” Kai ta daga alamar eh tace ” eh mana wanda kaba Feenah ta bani.” Shiru yai a ransa yace ” au kayan dana bata ma Little taba?” Bai dawo daga tunaninsa ba Little tace ” yaya, bari inje inga Feenah da alama yaya ne ya b’ata mata rai, nayi mamakin ganin ta haka.” Sannan ta karasa maganar a hankali ” Naga they get along with eachother very well, da alama fadan masoya sukai.” Ya kalleta yace ” Ai Asharaf sai a slow, amma….” Little ta kalleshi jin yayi shiru, kallan mamaki ya mata yace ” me kikace daga karshe?” Cikin rashin damuwa ta maimaitamai tace ” Allah naga tunda mukasan tsakaninsu kullum suke tare da juna.” Cikin tsananin mamaki yace ” me kikace?” Yanda yai maganar yasa jikinta yadanyi sanyi tace ” oh bakasan fa ashe matar yaya bace fa ko?” Gani tai yadan yi baya tare da rike kansa, cikin wani irin yanayi yake kallan Little wanda yasa tasha jinin jikinta, yace ” matar wa?” Kasa maimaitawa tai sai kallansa kawai datakeyi, ganin tayi shiru yasa ya juya jiki a sanyaye yai gaba batare da ya kara cewa komai ba. Little tabi bayansa da kallo me kenan? Ko dai shock ne irin wanda sukaji da suma suka samu labarin?” Ciki ta shiga ta samu Nafi ta sauko daga kan gado ta zauna a kasa tare da d’aura kansa a kan jikin gadon. Little ta matsa kusa da ita tace “matar yaya da alama fada kukai ko?” Nafi ta kalli Little sai dai batace komai ba, Little tai dariya tace ” karma ki fadamin nima ba san ji nake ba, na kuma san goben nan zaku shirya.” Ta karasa maganar tare da mikewa. Nafi da kyar ta tashi ta watsa ruwa kawai tai sallah ta kwanta, sam ta kasa bacci ita ba wai ganin yanayin da suke ciki da Anisa bane yafi daga mata hankali, kiss din da sukai a gabanta shine ya tsaya mata a kwakwalwarta, ai karama wani abun ce, ta tuna sanda yake ce mata su zauna a shagari su biyu. Wani dogon tsaki taja tace ” kamar irin da gaske ya manta da matarsa din nan.” Sam kasa barci tai sai juyi kawai take, da kyar baccin ya d’auketa. A b’angaren Ashraf kuwa sun zuba love shida nisa sai dai sam yaki yadda ya kusanceta, ganin ta matso da hakan yasa ya d’an matsa kadan, haushi ya kamata tace ” Hubby meye hakan?” Kallanta yai tare da rike hannunta yace ” sry Nisa.” Ta fizge hannunta cikin fushi tace ” me? Kana tunanin matarka Nafisa ne ko me?ko kuwa so kake kace baka sha’awar yi dani bayan kayi da yarinya?” STORY CONTINUES BELOW Jawota ta yai jikinsa ya rasa me zaice, baisan sanda yace mata” ba haka bane, banajin dadi ne wanda likita ya hanani saduwa amma inani ina kin matata?” Nisa ta kalleshi cikin zargi tace ” me ya sameka? Sannan naji Umma tace ka kwana da Nafi fa!” Kara jawota yai yace ” zargin Umma ne kawai karki wani sashi a ranki.” Da wannan yasa ta saki ranta, shikuma ya kwanta yai bacci. Tana gani yayi bacci ta mike a hankali ta bud’e drawer din nan a hankali ta zaro takardun nan tai falo. Karantasu tai taga tabbas kuwa takardun filayene da wani babban gona. Tai dariya tace ” da alama zan gano komai wannan karan.” Nan ta dau hotunan a waya ta turama Asim, sadi ya kara kamashi tace ” yaya in sato su?” Yace ” a’a ki maidasu sai mungama ganin ragowar tukunna karya gane.” Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta maidasu a hankali ta koma ta kwanta. Hankalin Ashraf a kwance ya tashi yai asuba, duk yanda yaso ta tashi tai sallah taki, dama inda sabo ta saba dan bata sallah sai rana ta fito. Sai daya gama shirinsa na gun aiki sannan ta farka ta kalleshi yana fesa turare. Mikewa tai tazo ta bayansa ta rungume shi, yai murmushi yace ” kun tashi My Neesa?” Wani irin sanyi ne ya ratsata tace ” eh hubby.” Ya juyo da ita gabansa yace ” da fatan kinyi bacci mai dadi.” Kai ta daga tace ” sosau ma, na dade rabon danai bacci mai dadin haka.” Yai murmushi yace ” gud, ni zan fita.” Kiss ta mannamai a kuncinsa tace ” sai kadawo.” Kai ya d’aga mata baice komai ba. Yana fita waje yasa hannu ya goge inda tamai kiss din sannan yai waje. A waje yaga Asim da kansa ya karasa ya mikamai hannu suka gaisa wanda hakan yai bala’in ba Asim mamaki, Ashraf yai murmushi yace ” Asim dama inasan magana dakai.” Asim yace ” inaji.” Ashraf yace ” kamar ya kamata muwa Kawu magana ya karama matsayi inaganin kamar inda aka maidakai yanzu is too low for someone like u.” Cikin tsananin mamaki Asim ya kalli Ashraf yama kasa magana, Ashraf ya dan dafa kafadarsa da hannu daya yace ” barshi in baka so.” Yana kai wa nan yai gaba, da sauri Asim yasha gabansa yace ” da gaske kake?” Fuskar Ashraf a maze kamar yanda yake kullum yace ” wasa nakeyi to da?” Asim ya sa dariya yace ” mamaki nake yi ai bantaba tunanin za ka taimaken bane ba ai naga tun muna yara bama wani shiri.” Ashraf yace ” ko ba ma shiri ai kai dan uwanane.” Yai gaba abinsa daga fadar haka, Asim yai dariya yace ” wai yau me nakeji haka?” Bangaren Kawu ya nufa cikin zumud’i ko sallama baiyi ba ya tura kofar d’akin, kawu na gaban wannan akwatin, jin Asim yasa yai saurin rufewa tare da turashi karkashin gado da sauri, ya kalli Asim cikin fada yace ‘” kai wai sai yaushe zakai hankali ne?” Asim yabi akwatin da kallo sannan ya basar yace ” Abba anya kan Ashraf d’aya kuwa?” Kawu yamai kallan mamaki yace ” ban gane ba.” Asim ya matso yace ” yanzu wai yacemin ya kamata muma magana ka karamin matsayi wannan matsayin nawa na yanzu is too low for me.” Kawu yai wata dariyar rainin hankali yace ” amma ba kada hankali ko?” STORY CONTINUES BELOW Asim cikin mamaki yace ” bangane ba.” Kawu yai dan tsaki tare da mikewa yace ” Kanaso kacemin Ashraf ne yace ma haka?” Da sauri Asim ya daga kai, Kawu ya hade rai yace ” ba ka cikin hayyacinka da alama mafarki kai.” Asim zai sake magana Kawu yace ” mu fita ni.” Haushi ya turnuke Asim yai waje a zuciye, har yayi nisa ya dawo gun Kawu yace ” Abba me kake nufi dani?” Kawu ya kalleshi cikin mamaki ba tare da ya amsa ba, Asim ya cigaba ” menene baka yarda dashi ba game da ni? Ni din ne baka yarda Ashraf yayi acknowledging din aiki na ba ko kuwa baka yarda da zan iya wani abun bane?” Kawu ya kalleshi cikin kulluwa da wannan halin nashi, yace ” duka, u always disappoint me.” Yana kai nan yai gaba yabar Asim a tsaye a gun. Asim yabi Kawu da kallo cikin tsananin takaici da haushin yanda Kawu yake mai. Kawu kam mota ya shiga cikin takaici. *********** Nafi kam bayan tayi wanka tana zaune a d’aki ita kadai duk abin duniya ya isheta ta kira Ferry a waya nan sukai ta hira har Ferry ta sanar da ita jarabawarsu ta fito. Nafi tace ” haba?kin dubo?” Ferry tace ” a’a amma ya Nabil yau zai dubo min.” Naf tace ” kice ya dubo da nawa ” Ferry tace ” to, amma Nafi karfa ki yaudaren kije ki cike wata makarantar ba BUK ba.” Nafi tai dariya tace ” karki damu duk inda kike nima ina nan, sai dai in samu ne banyi ba amma ina zani?” Sun dade suna hira kafin suyi sallama bayab sun gama tsara bikin Jibiya da za’a fara nan da 2wks, Nafi tace ” Zata kawu mata kudin ankon inyaso sai a musu gaba d’aya komai iri d’aya.” Tana kashe wayar tai shiru, a ranta tace ” Ferry fa batasan ni matar aure bace fa ko? Ya kamata in sanar da ita kar taji daga baya ta d’auka ko yaudararta nai.” ********** Ashraf na zaune a office ya dukufa sosai gun aiki yaji an banko mai kofa, Secretary dinsa yana biye da wanda ya bud’e kofar yana cewa ” malan meye hakan?” Ashraf ya kalli Habib yama Secretary din alama da hannu akan yaje. Nan yai gaba, Ashraf ya kalli Habib yace ” Habib lafiya naganka haka?” Habib cikin fada yace ” Ashraf me ake nufi akan kai mijin Nafi ne?” Ashraf yamai kallan mamaki yace ” ban gane ba?” Habib yace ” baka gane ba kamar ya? Little tace kai mijin Nafisa ne, ni kuma banaj na taba jin wannan labarin.” Ashraf ya koma ya zauna fuskarnan a hade yace ” yanzu ai kaji.” Habib ya matso cikin tsananin kishi ya kamo wuyan Ashraf yace ” how can u do this to me? Kasan kuwa yada nake da burin auren yarinyar nan? Taya za’ai kac…….” Ture hannunshi Ashraf yai da karfi yace ” kai ko kunyata ma bakayi? Taya za’ayi kazo kanamin zancen wai so bayan kasan kanwata yanda take sanka?” Habib ya kalleshi, Ashraf yai wani murmushin yace ” badai cemin zakai baka sani ba? Zan iya aminta inka fadi wani abu amma ba wannan kalmar ba.” A hankali Habib yadanyi baya, Ashraf ya sake murmushi yace ” mubar wannan maganar, ina Dady?” Jiki a sanyaye Habib yace ” yana gida.” Ashraf yace ” Allah sarki Dady baka gani ya kamata a dan ko karamai girman asibitin nan ko kuma a bud’e mai wani babba?” Habib yai dariya yace ” tab lalai, dady din?” Wani irin kallo kasa kasa Ashraf yamai, Habib yacigaba ” kabar Dady kawai sani ne bayasan ayi amma yanada kudi sosai inaj fa yanada gidajen haya manya kusan guda goma.” Ashraf yai murmushi yace ” amma wannan ai mayb daga baya ya saisu.” Habib ya girgiza kai yace ” a’a wlh, ni fa rannan inajinsa da Mumy yana zancen da gidajen lokacin duniya na kwance basa kawo kudi sosai amma yanzu dayake komai ya tashi kudi suke kawowa sosai.” Ashraf yai murmushi, kafin daga baya Habib ya tafi. Ashraf ya d’au waya da sauri ya kira Uncle bayan sun gaisa yace ” Uncle nikam kasan komai ma dukiyar Abba kuwa?” yai maganar cikin bugar ciki. Uncle yai dariya yace ” a iya sanina nasan komai nashi.” Ashraf yai shiru jikinsa ya fara sanyi, can ya daure yace ” kasan komai nashi tun kafin ya rasu?” Salim ya sake dariya yace ” gaskiya nidai a iya sanina nasan komai.” Ashraf yai shiru can yace ” shikenan na gode.” Yana kashe wayar ya mike tare da zuge glass din window yana kallan titi, a ransa addu’a kawai yake Allah yasa ba haka bane……” Nafi tana zaune a d’aki taji ana kwankwasa kofa, a hankali ta mike ta bud’e.+ Ganin Mumy ce yasa tad’anyi baya da sauri tare da cewa ” Mumy sannu da zuwa.” Mumy ta shigo ciki tare da zama akan d’aya daga cikin kujeru biyun dake d’akin, Nafi ta zauna daga d’an nesa da ita a kasa tare da gaisheta, Mumy ta amsa sannan ta kalli Nafi tace ” Zaman kadaici baya damunki?” Nafi ta girgiza kai alamar a’a, Mumy ta dan yi shiru, kafin ta nisa tace ” Nafisa!” Yanda ta kira sunan yasa Nafi ta d’ago a hankali tare da shan jinin jikinta, ta sani cewa zatai tabar gidan. Mumy tacigaba ” Ashraf yaro ne wanda baisan farinciki ba, bai san soyayyar iyaye ba, bai kuma san soyayyar ‘yan uwansa ba.” Nafi tai kasa da kai idanunta suka dan ciciko, Mumy tad’an yi ajiyar zuciya kafin ta cigaba ” na sani i am not a good mother to him, ban taba tambayarsa ko da damuwarsa bane bare har inkai ga bin bayansa ko nunamai kulawa.” Nafi ta kalli Mumy cikin tsananin tausayin mijinta, Mumy ta d’anyi murmushin takaici, tace ” duk kuma da wannan abun danake mai ya nunamin ke a matsayin matar da yakesan zama da ita sai dai shima hakan ban bi bayansa ba.” Hawayen da ke kwance a idanta ne ya gangaro, tai saurin sa hannu ta goge su, Mumy ta cigaba “A nawa ganin Ashraf matar da yake bukata itace mai ilimi wacce tasan kanta wacce kuma zata kula dashi.” Nafi ta goge hawayenta sannan ta kalli Mumy jin tayi shiru, tace ” na fahimceki Mumy na kuma sani ba tun yanxu ba Yaya yafi karfina, sai dai ni na kasa fahimtar ki.” Mumy ta kalleta, Nafi ta daure duk da tsoron da takeji tace ” bakya gani Yaya na bukatar kulawarki? Ko baki nunamai ba a kalla kya sanar dashi dalilinki na kin nunamai soyayya.” Mumy ta maida kwallar ta dake neman fitowa tace ” me yasa kike tunanin akwai dalilina nayin hakan?” Nafi tai murmushi tace ” Mumy ta yaya uwa zata haifi d’anta tace ba ta sansa? Ta yaya uwa tana ganin danta a cikin wani hali tace ba ta damu ba? Ta ya ya uwa zataki d’anta wanda yake maraya ne? Duk inda nakai ga tunanin zai iya yiwuwa sam zuciyata bata yarda da hakan, ni nasan akwai dalilinki nayin haka, sai dai a gun yaya shidai rashin so ne yasa kike mai haka.” Nafi da sauri taga Mumy ta mike tayi waje, ta bita da kallon tausayi. Ta dade a zaune agun kafin ta d’au wayarta ta kira Ashraf, sai dai duk yanda wayar ke ringing bai d’auka ba. Ta ajiye wayar tare da kwantar da kanta jikin kujera. *********** A b’angaren Ashraf kuwa yana azahar ya wuce gidan Uncle bayan sun zauna a falo sun gaisa Ashraf ya kalli Salim yace ” Uncle a labarin da ka bani kwanaki banaji kacemin an anso kayan su Dady.” Salim yai shiru yana kallan Ashraf. Ashraf ya cigaba ” nasan asibiti da makarantar sa na Abba ne amma bansan gidajen hayansa nawaye ba.” Salim ya shafi fuskarsa da hannayensa yace ” Ashraf you are very smart,ban taba tunanin zakai zargin wani abu ba game da wannan, shiyasa ma ban sanar dakai komai ba.” Ashraf ya kalli Uncle yace ” me ke faruwa?” Salim yaja numfashi yace ” a lokacin da mahaifin Ruma ya rasu bayan an gama zaman makoki Hisham ya shiga gararin rayuwa, kaf kudinsa sun kare bayan rashin kudin ashe har loan yaci a banki wanda ya jinginar da gidansa. STORY CONTINUES BELOW Bayan an gama zaman makoki ‘yan bankin sukazo amsar kudinsu kamar yanda ya sanar dasu lokacin dazai biyasu. Sai dai a lokacin gidansa abincin ma dazasuci nema yake ya gagaresu. Da yake Ruma na gidan ita ta kira Abbas ta sanar dashi halin da ake ciki nan ya je bankin ya biyasu kudinsu sannan makarantar da yake masifar so ya mallakama Hisham duk dan ya farantamasa, sai dai kwanansa d’aya da bashi makarantar Allah ya d’auki ran Abbas.” Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace ” asibitin fa?” Salim yai ajiyar zuciya yace ” Ashraf wannan sai bayan rasuwar mahaifinka sukazo min da takarda akan Abbas ya mallakama Hisham asibitinsa da aka gama ginawa ko fara aiki ma ba’ai ba.” Ashraf cikin rashin fahimta yace ” ta yaya ya bashi makaranta mai girma irin wannan ya sai mai gida sannan ya kuma bashi asibiti?” Salim ya kalli Ashraf yace ” nima da naki yarda da bada takardun asibitin to amma abin mamaki rubutun mahaifinka ne.” Cikin fada Ashraf yace ” zasu iya sa expert su kwaikwaya ai.” Salim yace ” yes shiyasa naki yarda sai dai mahaifiyarka itace tace tabbas Abbas ne ya rubuta.” Shiru Ashraf yai kafin yace ” gidajensa fa?” Salim yace ” bansan wannan ba gaskiya sai dai bayan mutuwar Abbas naji jita jita akan bai daina safarar bindigogi ba zai iya yiwuwa da su ya siya ko kuma gadon Ruma ne.” Cikin mamaki Ashraf yace ” gadon Mumy?” Salim yace ” ban tabbatar ba amma tunda kace gidaje dayawa nasan tanadasu dan Abbas tun yana da rai yake siyan gida da sunanta sannan da ya rasu aka bata gadon wasu.” Ashraf yai shiru baice komai ba, Salim ya dafashi yace ” Ashraf mahaifinka burinshi kai rayuwa mai dadi ba wai ta wahala da kunci haka ba.” Murmushi Ashraf yai yace ” Uncle kana tunanin zanyi rayuwa mai dadi bayan duk ‘yan uwana makiyan Abba da ni suna zagaye da ni?” Salim baice komai ba sai kallan Ashraf dayake yi. Ashraf ya sake murmushi yace ” ka binciko min inda Auwal Max din yake?” Salim yace ” eh to wanda yake binciken yace yana zariya sai dai yace in kara mai 1day ya tabbatar da shi din ne.” Kai Ashraf ya jinjina sannan ya mike yace ” kace kafin Abba ya rubutawa matata wasiya munyi tafiya zuwa wani kauye dashi ko?” Salim ya jinjina kai yace ” kwarai kuwa saboda bazan manta lokacin ba nayi mamaki kwarai daya kawon wasiyyar da daddare.” Ashraf yace ” Malam Mahmud ko?” Salim ya daga kai alamar eh. Ashraf yai godiya kafin yai waje. Mota ya fad’a ya d’aga wayarsa sakon Nafi ne yaga ya shigo kamar haka ” _Yaya dafatan kaci abinci?_” Ya dade yana kallan sakon kafin ya ajiye wayar ba tare da ya mata reply ba. Makaranta ya wuce, yai sa’a kuwa yana zuwa Malam na kokarin fita, nan ya ajiye mota ya karasa suka gaisa, Malam yai murmushi yace ” Muhammad daga ina haka?” Ashraf yai murmushi yace ” gaisawa nazo muyi.” Malam yai dariya yace ” nagode da baka manta da wannan tsohon ba.” Nan sukai dariya, Malam yace ” Ina Matar taka?” Ashraf yace ” tana nan.” Malam yace ” yarinyar fa nake nufi.” Ashraf yadan sosa keya. Malam yai murmushi yace ” da alama tana nan.” Ashraf ya kalleshi yace ” malam tambaya nazo da ita.” Malam yace ” Allah g yasa na sani.” Ashraf ya nisa sannan yace ” kafin Abba ya rasu munyi tafiya ni da kai da shi ko?” Malam yace ” Hakkun.” Ashraf yace ” Malam zaka iya tuna abinda ya faru a lokacin?” Malam yai murmushi yace ” shekarun da yawa na dai san munje zagaye da taimakon bayin Allah dake da bukata, wannan shine tafiyarsa ta karshe.” Ashraf ya jinjina kai yace ” ba wani abu na mamaki da ya faru game da ni?” Malam yai shiru kafin yace ” tabbas akwai na tuna, abinda ya dade yana bani mamaki.” Ashraf ya kalleshi cikin zakuwa da sanjin menene. Malam yace ” mu shiga ciki.” Nan suka nufi makarantar. ********** Yau Datti yana tsakiyar bacci ya tashi cikin firgice tare da kwallama Nafi kira, sai kuma ya saki wani irin kuka mai ban tausayi. Yayansa ya shigo d’akin a tsorace ganin tsakar dare ne gashi ya tashi mutane da dama. Datti yana kuka yana cewa ” a kiramin Nafi dan Allah ku taimaken ku kiramin Nafi.” Yayansa ya shiga lalabashi yana cewa kai shiru Datti da alama ka samu lafiya tunda ka fara magana. Sai dai ina Datti kam abin ya canza salo daga kuka sai a kira masa Nafi kawai yake cewa. Nan suka shiga tambayarsa a wani gari Nafin take a kirata?” Kai kawai ya girgixawa alamar bai sani ba. Mamaki da tsoro ya kamasu. Mahaifiyarsa dake kwance ba lafiya tace “kila saidata yai saboda tsabar san kudinsa nikam na shiga uku na.” Datti kam cewa yake a kira masa Nafi…… Nace ta yaya kenan?🤔