ZUCIYA CHAPTER 4
Little ce rike da hannunta kawai tana tafiya amma idanunta nakan Ashraf dake tafiya, Aneesa kam har wuya tazo ganin yanda Ashraf ya hauta da fada akan wata banza kucaka, da saninta ta taho ta mangaje Nafi wanda har sai da ta kusa kai kasa, Little ta kalleta tace “Haba Yaya Neesa? “+ Aneesa ta kalli Nafi tace “Sorry ban kula ba.”tai gaba. Little ta kalli Nafi wanda ta kakaro murmushi tace “Maryam karki damu ai bata kula bane, kuma taban hakuri. ” Little tai karamin hucci tace” Nafi kiyi hakuri. ” D’aki suka shiga, Nafi ta zauna a kasa, little na shirin mata magana wayarta tai kara, da sauri ta d’aga tace “Naam Yaya. ” Daga can bangaren Ashraf yace ” Little ki samarmata abinci dan banaji taci wani abinci. ” To, little ta fad’a tana kallan Nafi wacce itama hankalin ta ke kan Little tunda taji ance Yaya. Little ta kashe wayar sannan ta kalli Nafi tace “kinga Yaya ma ya kula bakici abinci ba.” Nafi tad’anyi murmushi, hakab yasa Little tai waje. Ashraf kam yana shiga bangarensa ya kwanta a kan kujera doguwa dake falo, hannu yasa akan goshinsa, meyasa duk sanda akace za’ai meeting indai har saboda shine sai an b’ata masa rai? Yai dan karamin tsaki zai juya yaji sallama, muryar Mumy ce hakan yasa ya amsa sama sama. Mumy ta shigo ciki, shi kuma ya mike daga kwanciyar da yai ya sauka kasa, mumy ta karaso ta zauna akan kujera, kansa na kasa bai ce komai ba. Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace “Ashraf kayi hakuri. ” Batare da ya d’ago ba yace ” Ya wuce ai tunda dai ba wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan. ” Mumy ta jinjina kai sannan tace” Ashraf a gaskiya nima hukuncinka bai min ba, bana ganin dan ta taimakeka ya kamata ka taho da ita, sai dai in akwai wani dalili bayan wannan. ” Bai kalleta ba haka kuma baice komai ba, Mumy ta cigaba ” ba komai nasan tausayinta ne yasa ka taho da ita insha Allah nikuma zan kula da ita. ” Yanzu kam ya d’ago ya kalli Mumyn sai dai baice komai ba, tai murmushi dan ta gane yaji dadin maganar ne tace “Ashraf zuwa nai muyi wata magana. ” Inaji kawai yace. Tace ” Baka ganin lokaci yayi da zaka fara aiki a company d’in mahaifinka?? ” Kallanta yai cikin mamaki yace ” Ba Kawu da Asim suna kula da company d’in ba? Meye kuma nawa na fara aiki acan?? ” Mumy cikin damuwa tace ” Ash raf mai yasa kake abu kamar bakasan komai ba? Companin nan na mahaifinka ne fa? Kai kad’ai ne d’ansa sannan ya bar maka share d’in sa gaba d’aya kanada 50% na share d’in company d’in kafi kowa, akan me zakayi ta zama a gida bayan ka gama karatu? ” Ashraf ya mike tsaye yace ” Mumy banasan wannan maganar dan Allah. ” Jikinta a sanyaye tace ” Ashraf? ” Ya d’an kalleta sai dai bai ce komai ba, mikewa tai a hankali tai waje, yabi bayanta da kallo tare da dafa kansa, meyasa kowa ba ya hango abinda shi yake hangowa? Idanu ya runtse yana tuno sanda akace fatiha an d’aura auren Nafi da Ashraf, yai wani hucci sannan ya mike kawai ya zari makulli yai waje. ************ Sosai Nafi ta ci abinci, ji take wani dad’i na ziyartarta, tanaji tunda take bata tab’acin abinci mai dadi irin wannan ba, tas ta cinye wanda little ta zubo mata, ta kwankwad’i lemon kankana mai sanyi da ke cikin jug, wata gyatsa tai sannan tasa dariya ita ka dai. STORY CONTINUES BELOW Ita kad’aice a d’akin dan little ta fita, tace ” oh yau banyi gyatsar nono ko madara ba.” Ta sake yin dariya tace ” Kai abincin nan yayi dad’i, wannan kuma ko menene?” ta fada tana d’aga ragowar juice d’in kankanar data sha, tace ” Tabdi lalai akwai abin dad’i a birni.” Sai dataji abincin ya tsirga mata saboda cin datai dayawa, tad’au tiren kamar yanda Little tace mata ta maida kitchen. Ta fito ta kalli gabas inda little ta mata kwatance, ta fara tafiya, tafiya kawai take, gani tai ta b’ata nan ta shiga waige waige, jitai ance ” Ke.” Juyowa tai cikin mamaki, Ganin umma uwar Aneesa yasa tai saurin yin kasa dakanta, Umma tace ” Dan gidan ku uban me kike anan? ” Nafi cikin tsoro ta fara magana cikin in in na tace ” Um kitchen nake nema. ” Umma ta kalli kwanon sannan tad’an tabe baki tace ” Kwarai dole ai, a can kauye ba’a sami damar zakewa aci abinci ba shiyasa ake neman bud’e mana ciki? ” Nafi wanda jikinta duk ya gama mutuwa ta kasa magana sai motsa baki kawai take. Umma ta kalleta kallan banza tace ” wuce muje kitchen d’in. ” Nafi ta kalleta da mamaki, Umma tace ” To munafuka bakijini bane kike kif kif da ido? ” Nafi tai saurin yin kasa dakai, nan tai gaba Nafi ta bita. Sun isa katon kitchen d’in inda masu aiki keta hidima Umma ta tafa hannun ta hakan yasa duk suka taho, Umma ta kallesu tace ” Yauwa dama so nake in sanar daku kun samu kari. ” Kallan juna sukai na mamaki, tasa hannu ta finciko Nafi tace ” gatannan da safe zatazo ta tayaku aiki sannan da rana ma haka.” Nafi ta kara kasa da kanta, Umma tace “na umarceku ku sata aiki sosai, saboda ita ta fiku cin riba dan inda zata kwanta yafi naku haka abincinta da suturarta tafi taku. ” Suka amsa da to, ta kalli Nafi tace.” Ke kuma dan gidanku kullum da sasaafe in ganki anan hakama da rana, bazaki dinga cin abinci a banza ba. ” Nafi ta d’aga kai, Umma taja kunenta tace ” kuma wlh inji maganarnan abakin wani ko da Little ce bare Ashraf Allah sai kin gane kuranki. ” Tana kai nan tai gaba. Nafi tai shiru, jitai ance ajiye kwanukan ki tafi gobe kya fara zuwa, Nafi ta kalli mai maganar wata babba ce a kalla zatai sa’ar Innarta, ta ajiye tiren sannan ta gaidasu tare da musu sallama. ********** D’aki ta koma ta zauna a kasa tai shiru, bacci ne yai gaba da ita. Ashraf kam bayan ya fito daga d’aki Aneesa yama waya yace ta fito ta rakashi an guwa. Jifatu ya wuce da ita, tanata murna ganin yau gata ga masoyinta, suna tafiya ne ta kalleshi tace ” Yaya ya maganar sa ranar da akai ai tana nan ko? ” Ya kalleta tare da murmushi yace ” eh mana ko musa a kara matsowa da shi? ” Idanu ta rufe tace ” Kai yaya wata biyu ai kamar yau ne. ” Aneesa ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace ” Yaya wlh ni kad’ai nasan missing dinka danai jiya. ” Titi kawai ya kalla baice komai ba sai murmushi da yai. A bakin jifatu yai parking, nan ta fito shims ya fito suka shiga ciki, bangaren kaya na atamfofi lace da mayafai sukai, ce mata yai kawai ta zab’a, hakan yasa tai tunanin nata ne, sosai ta jidi kaya shima yana tayata, suks wuce gun takalmi, nan ne dai yace banda takalmi sai dai jaka, saboda shikam yasan baisan size dinta ba. STORY CONTINUES BELOW Itakam Aneesa sai farin ciki take har suka gama zaben suka fito, sun shiga mota ta kalleshi cikin kauna tace ” Yaya na gode sosai. ” Ya kalleta cikin mamaki yace ” name fa? ” Tace “na kaya mana. ” Murmushi yai yace “Aneesa ke kuma mai zakiyi da kaya? Duk yawan kayanki? ” Fuska ta had’e tace ” na waye to? ” Ya kalli titi yace ” Nafeesa. ” Gabanta ne ya fad’i cikin tsoro ta kalleshi sai dai gani tai shi ko a jikin sa, ranta yai mugun b’aci…….. Ashraf ne ya kalleta kadan yace “Aneesah tailorn ki kuwa yana nan? ” Fuska ta kara daurewa tamau tace ” menene? “+ “kayan Nafisa nake tunanin muje akai mai can naga ba laifi ya iya d’inki sosai. ” Jitai zuciyarta na neman tsagewa saboda takaici, rasa ma mai zata cemai tai, kawai sai ido ta bishi dashi, ganin kamar bai ma fahimci ranta a b’ace yake ba yasa tace ” Yaya d’anyi parking.” Cikin mamaki ya kalleta yace ” parking kuma? ” Kai ta d’aga hakan yasa ya gangara gefen titi, ta bud’e kofar ta sannan ta kalleshi tace ” randa zaka fita domin ni ka d’aukoni amma bazan zauna kusa da kai domin wata ba. ” tana kai nan tai waje, ya bita da kallo cikin mamaki, me take nufi domin wata? Yana kallanta ta tari adaidaita, ga magrib ta kawo kai,shima ya ja mota yai gaba. Aneesa na shiga mota ta fara matsar kwalla dan tsabar takaici ita zai d’auka su zaboma wannan kucakar kaya? Tana isa gida ta wuce gun ummanta da gudu nan ta sanar da Ummanta duk abinda ya faru sannan ta d’ora da cewa ” Umma kinga lesukan dana zab’a kuwa? Na d’auka nawa ne? Ina wannan kucakar ina sa kayan dubu talatin? ” Umma ma da ranta yakai kololuwar tashi tace ” kwantar da hankalinki ita d’in banza? Har ta isa tasaki kuka? Bare har ta had’aku fad’a da Ashraf?” Aneesa ta goge kwallarta tace ” Umma me Ashraf yake cemin? ” “Neesah mana, tun kina karama yake fad’a miki haka shi yasa wasu ma haka suke ce miki.” Aneesa tai kwafa tace ” to Umma tunda na cemai wannan yarinyar ta d’auka ita ya kira d’azu bai sake cemin Neesah ba har yanzu. ” Umma ta kanne ido cikin b’acin rai tace ” Aneesa kada ki kuskura ki kara yadda Ashraf yasan bakyasan yarinyar nan, sannan karki kara yimai musu akanta.” Aneesa ta mata kallan mamaki, Umma tace ” tabayan gida zamu b’ulo mata, ni na fad’a miki bazata cika sati a gidan nan ba zata d’auki tsuman kafafuwanta tayi gaba. ” Aneesa ta jinjina kai alamar gasuwa tace ” Umma ni ko ganinta ma bana sanyi wlh. ” Umma tai murmushi tace ” d’aure kinji ‘yata, sati d’aya yayi yawa. ” Nan sukai murmushin mugunta su dukansu. Nafi kam tana zaune a d’aki ita kad’ai mahaifinta ne ya fad’o mata a ranta tace ” ko baffa yana me? ” Jitai an kwankwasa kofa hakan yasa ta mike tare da yafa d’an kwalinta ta bud’e kofar, Matar data gani d’azu itace ta gani yanzu, ko ba’a fad’a ba tasan Mahaifiyar Ashraf ce, murmushi ta mata sannan tace “fito falo muyi magana.” Tai gaba Nafi ta bita a baya, akan kujera ta zauna hakan yasa Nafi ta zauna daga nesa kadan a kasa, Mumy ta kalleta tace ” ya sunan? ” “Nafi. ” ta fad’a kanta a kasa. Mumy tace ” Nafisa kenan ai.” Nafi tace ” Eh.” tai maganar cikin sanyin murya. Mumy ta kalleta da gani batafi sa’ar Little ba tace ” kinsan ko ni wacce? ” Nafi tad’an kalleta kad’an sannan tace ” Mamar Dan Binni ko? ” Mumy tai dariya tace ” Ashraf kenan? ” Kai ta d’aga itama tana murmushi, Mumy tace ” Nafi iyayenki fa? ” Kallan Mumy tai jiki a sanyaye batace komai ba, Mumy tace ” Nafi karkiji komai ki sanar dani duk abinda ya faru babu wani abu, ni mahaifiyar Ashraf ce.” STORY CONTINUES BELOW Nafi tai shiru me zatace? Me zatace? Jitai Mumy tace ” Nafi!! ” A hankali Nafi tace ” Mahaifiyata ta koma saudiyya da zama, mahaifina shine yake kokarin aurar dani ga babban mutum shine Dan binni ya taho dani. ” Mumy tai shiru ba shakka yarinyar abin tausayi ce amma ita tasan Ashraf sarai shi ba mai shiga abinda bai shafeshi bane bare har ya d’auko yarinya daga gaban mahaifinta. Ta kalli Nafi tace ” Kidinga kirana Mumy kamar yanda kowa yake cemin, sannan ki saki jikinki kamar nan ma gidanku ne. ” Nafi ta d’ago ta kalli Mumy idanunta suka ciciko, Mumy tai murmushi tace ” Karki damu kinji? Sannan karki kara cema Ashraf dan binni kidinga cemai Yaya kamar yanda kowa ke cemai. ” Ta d’aga kai, ba shakka yanda taga yanayin ‘yan gidan lalai in tsautsayi ya sa akasan an d’aura musu aure da Ashraf to fa lalai tanaji ko Mumy bazata sakar mata fuska ba. Nan Mumy ta mike tace ” Little ba ta dawo ba? ” Nafi tace ” eh. ” Mumy ta jinjina kai sannan tai waje. Nafi tabi bayanta da kallo sannan tai murmushi. Mumy na fitowa daidai nan Ashraf ya dawo daga masallaci yana shirin yima little magana, ganin Mumy ta fito yasa gabansa ya fad’i, yasan mumy da fasaha da iya bugar ciki da alama taje ta bigi cikin Nafi ta fada mata komai, Mumy na wucewa yai wuf ya shiga bangaren. Nafi lokacin ta mike kenan zata shiga d’aki, jin sallamar Ashraf yasa ta tsaya cak ta kasa juyowa sai dai ta amsa, Ashraf ya shigo da hanzari yazo daf da ita yanda har numfashinsa take jiyowa hakan yasa gabanta ya shiga bugawa, juyowa tai cikin tsoro hakan yasa suka fuskanci juna daf da daf, gabanta ne ya cigaba da fad’uwa har tanaji kamar shima yanajin bugun da zuciyarta yake. Shikam cikin rashin damuwa yace ” Nafi me kika cema Mumy?” Kasa magana tai sai bakinta dake motsi shi kadai, Ashraf cikin takaici yace ” kin fada ko? ” Kai ta girgiza alamar a’a, yace ” ke nake jira me kika ce mata? ” Gaba d’aya jitai ta kasa magana, da sauri ta murda kofar d’aki ta shige tabarshi a nan, tana shiga ta sulale ta zauna a kasa, ya za’ai ya matso mata haka daf yace wai tai magana? Ashraf yabi dakin da kallo cikin takaici ya juya yai waje, yana zuwa kofa Aneesa na shigowa, tana ganinshi tai murmushi tace ” Yaya sry ina gun Umma ne. ” Fuskar nan a had’e dama ransa ya gama b’aci yace “Ni har zaki rainawa hankali muna tafiya dake ki fita ki hau adaidaita? ” Kallansa tai cikin mamaki ta d’auka hakuri yazo bata, ta daure tace ” Yahkuri Yaya dazun ne raina a b’ace yake. ” “Na gane” kawai yace ya wuceta yai gaba. Kallansa tai cikin mamaki. Ashraf yai waje a zuciye, d’akinsa ya wuce. Itakam Nafi anan take a zaune har Little ta dawo wajen Isha’i, ta kalleta tace ” Nafi me kike a nan? ” Nafi ta mike ba tare datace komai ba ta nufi ban d’aki, sai kuma ta dawo tace ” Maryam taramin ruwa inyi alwala dan Allah. ” Little tai murmushi sannan ta ajiye takardun data amso ta tara mata. Little ta kula da yanda Nafi take sallah tasan kuma da alama batamasan me ake cewa ba, sunci abinci wanda Little ta d’auko musu sannan suka zauna hira, Little tace Nafi ta bata labarin rayuwar kauye. Nan Nafi ta fara bata labaruruka tace ” ni ba shiga mutane nake ba amma fulanuwa masu tsayawa a rafi gunsu nake zama. Little tayi dariya sosai in taji wani labarin cikin labarin ta bige cikinta akan sallah. Nafi tace ” Ni kawai yi nake yanda naga Innata tanayi. ” Little tace “Zan koya miki yanda akeyi. ” Nafi cikin farin ciki ta amsa da to. Sun dade suna hira sosai kafin su kwanta. *********** A bangaren Mumy kuwa ta sanar da mijinta abinda ya faru acan sannan ta karasa maganar da cewa ” Alhaji kasan halin Ashraf tunda kaga ya d’auko yarinyar nan to tabbas tausayinta ne yamai yawa gashi ta taimakeshi. ” Kawu yai shiru can yace ” shikenan Hajiya dama ni ban ce komai ba mamaki nake yanda akai Ashraf har ya shiga abinda ba nashi ba. ” Mumy ta ce” nima wannan abun ya ban mamaki sai dai inaji a jikina akwai dalilinsa nayin haka. ” Kawu yai murmushi yace ” ai dama Ashraf baya laifi. ” Ta kalleshi kawai tai murmushi batace komai ba. Ashraf kam ya kasa zama,yanzu in akaji ya auri wannan kucakar ai an gama zubar mai mutunci, hakan yasa ya kira wayar Mumy. Da mamaki Mumy ta kalli mijinta sannan ta kalli wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace “Ashraf? ” Gyaran murya yai sannan yace ” Mumy dazu me Nafi ta ce miki? ” Mumy da mamaki tace ” me ya faru? ” Yace ” ba komai, sai da safe. ” Da sauri ganin zai kashe wayar tace ” Ashraf!” Naam kawai yace. Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu. Ashraf yabi wayar da kallo tare da furzar da wata iska yace ” Da alama tanada wayau.” Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa. Karfe hud’u Nafi ta bud’e idanunta kamar yanda ta saba, shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci.+ Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab’a Nafi, da karfi Nafi tace ” Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. ” Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad’anyi dariya tace ” Nafi nice! Da alama Baffan nan bulala yake miki. ” Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace komai ba. Little tace ” Tashi kiyi sallah. ” Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace “kin tarar mi….. ” Katseta Little tai tace “Na tarar miki ke da bakya mantawa. ” Nafi tai toilet tana murmushi. Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace ” Maryam naga kin kwanta?” “Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d’aya zan fita?” Nafi tace” nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. ” Little ta zauna tare da kallan Nafi tace ” Bacci mana. ” Idanu Nafi ta zaro tace” Bacci kuma? Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta? Tab di. ” Little tai dariya tace ” Uhm hm i kam dai bacci zanyi. “tai maganar tare da kwanciya. Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al’amari, mutum ya kwana yana bacci sannan ya kara kwanciya da safe? Shi ba ciwo yake ba? Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike sanye da hijabin datai Sallah tai waje. Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace” Masu gini sun sha aiki. ” Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha’awa, sukam ‘yan kitchen sunata hada hadar aiki, ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska, Matar jiyar nan ta kalleta tace ” yanaga kinzo da wuri? ” Nafi ta dan murmusa tace ” in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. ” Kai ta jinjina, Nafi ta kallesu tace ” me zan fara? ” Wata daga ciki ta kalli matar tace ” Goggo me zatayi? ” Goggo tai shiru can tace ” ke wani bangare kika fiso? Akwai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. ” Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace “Nafisan b’angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. ” Dariya suka sa mata, Goggo tace ” Bangaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai, wani sa’in da rana ko dare ma haka.” Nafi tace ” Bakomai.” Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za’ama kowa yau, sunyi sa’a wasu suna zuwa iri d’aya, nan suka shiga aiki. Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa. An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma ‘yan gida su kuma nasu aka fita dashi. Nafi kam abin sai birgeta yake, sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi. Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci, Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud’e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa. Bacci ne yai gaba da ita, wajen 9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa, da sauri Nafi ta mike tare da bud’ewa, Wasu yarane su biyu d’auke da ledoji suka kalli Nafi sukace ” Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. ” STORY CONTINUES BELOW Little dake zaune akan gado tace “Amra ku shigo mana. ” Nan suka fara kokarin jan ledar, Nafi ta amsa ta shiga dashi, little ta kalli kayan tace ” me yace?” Wacce ta kira da Amra tace ” cewa yai mukawo miki zai kiraki. ” Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf, da sauri tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin, tace “Yaya ina kwana? ” Yace ” kinga dama kin tashi? ” Kallan Nafi tai sannan tace ” Yaya ba bacci nai ba. ” “Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki.” Little ta d’an turo baki sannan tace ” Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji.” Yace ” Yanzu za’a kawo manyan, naga su bazasu iya d’auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. ” Little tace ” to kana ina? ” Ina gun motor park, Sai Amra ta rakota. ” Little tace ” to amma yaya kayan meye? ” Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d’au driver ya rakaki gun mai d’inkinki sai a gwadata a mata. ” Baki little ta bud’e to kawai tace tanaji ya kashe wayar. Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiya daga nan duk ke ya siyowa kayan. ” Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace ” eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d’an miki yawa. ” Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata. Little ta katseta “ki tashi dan Yaya baisan jira. ” Nan suka mike itada Amra. Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa. Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi, kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace ” kema daga baccin kike? ” Kai ta girgiza alamar a’a, yace ” ki d’au kayan suna bayan mota.” Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d’auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da ‘yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace ” Nafeesa da wani abun ne? ” Yawo ta had’iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima. Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana, Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace ” Yaya. ” Dasauri ya d’ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan. Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya. Ta kara daurewa tace ” Yaya Na gode. ” Tana fada ta juya zata d’au kaya, jitai yace ” Nafisa!! ” Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro, ya kalleta kad’an sannan yace ” Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?” Kanta na kasa sai gabanta dayake fad’uwa, Ashraf yace ” meye dalili? Ko raini ya fara shiga tsa…… ” Katseshi tai da sauri da cewa ” Wlh ba haka bane, matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad’uwa shiyasa na rufe. ” Da mamaki yake kallanta yace ” Nafisa yaushe kika koyi karya? ” Idanu ta zaro cikin mamaki tace “Wlh ba karya nakeba Yaya. ” Ya d’an kura mata ido hakan yasa tai kasa da kanta, a ransa yace ” dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. ” Wani abu ya tuno ya d’auke kansa daga kanta a hankali yace ” da alama sanda kika ciren riga gaban naki bai fad’i ba ” Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya, ya kalli yanda take sauri yace ” kayan fa? ” Idanu ta rufe, cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe, batasan har tazo inda yake ba, jin tayi dan tun tube da kafa yasa ta bud’e ido da sauri, Ashraf ya kalleta yace ” Toh da alama gaban naki baya fad’uwa ko? ” Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta, idanunta suka ciciko, Ashraf ya mike tare da d’anyin murmushi, ya matso saitin kunnenta yace ” in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. ” Tanaji ya tafi, ta dade kafin ta mik’e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar, jin goshinta ya fara zafi yasa ta d’au kayan tare da rufemai mota tai gaba. Tana isa d’aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune, gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai. A hankali cikin tsoro ta shiga d’akin, tare da ajiye kayan, Umma tace ” Yauwa Ke muga ledar nan. ” Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya, Umma ta kalli Aneesa tace ” wanene lace d’in? ” Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske. Little ta kalli Umma tace ” Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?” Umma tai murmushi tace ” Little kenan bakiji me nace ba? Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. “ta fada tana nuna Nafi. D’aukan lace din sukai suka tafi, little ta shiga toilet ranta duk a b’ace. Nafi kam ko ajikinta dan batasan darajarsu ba, itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi?