ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU
Kamar yadda Daddy yayiwa Hibba alkawari personally akan ranar monday zai barni na tafi bikin, hakan ya kasance. Wajen karfe daya muka dauki hanyar kano ni da driver dake kaimu unguwau, tunda na shiga motar nake bacci saboda kwana biyu bana samun isasshen bacci inayi, gaba daya na rame na lalace, idan ka kalleni ko baka tambaya ba zakaga yadda damuwa take kwance saman fuskata, it’s boldly written all over. Seda muka shigo kano sannan na farka sabida hold up da akeyi tun daga round about na mega station, kallon ko ina nake ina tuna dukkan memories din garin baki daya, gashi dai ko wata banyi da barin garin ba, amma abubuwan da suka faru a wannan kwanakin bana tunanin akwai abinda zai goge su daga cikin zuciyata, fact that Sahibi ko kuma Aliyu tunda bai cancanci na kira shi da wani sunan soyayya ba yace na yaudare shi, bayan sacrifices din da nayi making da kuma compromising abubuwa da dama da nayi kawai dan naga relationship din mu ya tafi babu matsala, na sha zan tafi weekends yace min nayi zamana Haka zan hakura saboda zai zo, duk fada irin nawa saboda son da nake masa na kasa biyewa Fatima na mayar mata da martani. Ashe abinda zai faru karshe kenan? Duk lokacin dana tuna se naji kamar zuciyata zata fito, had I known da ban bata lokaci na ba.+
A dakin Hibba na sauka, kasancewar ta yarinyar karshe a gidan, dukka sauran sunyi aure yasa take da daki daban, seda na gaida Mamaa tana ta korafin na tafi ban zo ba sannan Hibba ta jani muka wuce dakin ta. Seda na kira su Daddy sannan nayi wanka na canja kaya naci abinci na zauna ina sorting invitations din da aka kawo, Tunda muka kebe Hibba ke kallona, nasan bakinta is full of words amma bana son bata fuska balle tayi magana, da dai ace ba biki nazo ba da tuni na fada mata amma ba zan iya burdening dinta da matsaloli na ba. Kamar tasan abinda nake tunani se ta kyaleni, cigaba da kallon IVs din nayi,nayi snapping wanda zan posting a handles dina na social media, sannan muka cigaba da hira. Tuesday mukaje salon muka wanke kanmu aka kara gyara mata jiki nima na shiga umbrella dinta aka shafa min. Munyi kyau sannan washegari mukaje lallai wata uwa duniya. Lallen yayi kyau sosae, bayan mun gama tace mu jira zaa zo daukar mu da farko nace
” Ni dai mu tafi kawai “
Ta kalleni tace
” Kin gaji ko?”
Dan tsaki nayi dan wata irin yunwa nake ji, tun safe muke gidan kunshin ko breakfast bamuyi ba, da time din abinci yayi se ta tsallake taje ta cika cikin ta, rashin karar yayi yawa, na kuma ji haushi . Bamu kara thirty minutes ba Hibba ta dauki waya ta danyi magana sannan tace min
“Bae muje”
Mikewa nayi mukai mata sallama tana mana fatan alkhairi, Hibba ce a gaba ina biye da ita, jikin wata dalleliyar bakar corolla toyota wani gaye yana tsaye yayi pocketing hannunsa cikin aljihun wandon shi, yana sanye da kananan kaya wanda suka amshe shi . Kaina na dan dauke daga kallon kurillar da nake mishi saboda naga alamar gaze dina ya fara tasiri kan shi dan ya fara kokarin dagowa daga kan screen din wayar shi, dagowa yayi yana kallon mu a nutse, karasawa mukai, fuskar shi a sake ya fara zolayar Hibba, ni ya kamata ace na shigar mata amma saboda bamu saba dashi ba yasa ko uhmmm bance ba, itama gwanar magana ta biye shi sukai tayi bacin rai yasa nace
“Kukam dan Allah mu tafi mana”
Kallona yayi briefly sannan ya maida hankalin shi kan Hibba da take ce masa
“Dr Ayoub ga Nanah my best friend and my best sister, Nanata ga Dr Ayoub friend din Doctor ne”
Murmushi nayi nace
“Barka da yamma, it’s my pleasure meeting you”
Shima murmushi yayi min yace
“Nagode ya hidima”
Na amsa da Alhamdulillah sannan muka shiga ina front seat muna dan taba hira kadan kadan har na dan ware. Duk inda zamuje shi ke kaimu se ya zamana mun saba har muka karba contact din juna saboda Hibba batada lokacin zama su communicating dole dai ni zan dinga playing wannan role din. Anyi biki sosae seda mukai kwana uku muna event, na gaji nayi tikis saboda duk hayaniya ta ni ba fan din biki bace ga nasu Aminatu two weeks after. Ranar asabar aka daura aure, na kalleta nace
“Hibba ki zauna a karasa daurin mana angwayen will soon come”
Zama tayi tana wani murmushi da zan rantse ban taba ganin tayi irin shi ba tace
“Wai Hibba! Ai yanzun ni Matar aure ce sede Anty Hibba”
Friends din mu dake zaune suka dinga dariya ni kuma nace
“Aa uwar Anty!”
A ranar akai yini da yamma aka kaita gidan miji, seda muka jira aka dan baje sannan muka gyara abinda ya kamata mu gyara, tana bedroom a zaune, zama nayi nace
“Se yaushe zamu tafi?”
A birkice ta bude veil dinta tace
“Kai Nanah ku jira yazo mana”
“Tohm Anty Hibba, wa ba zaki cire kayan ba”
Hararata tayi na mike na bude wardrobe dinta na nemo wata sexy nighty na warware nace
“Hibba anjima kisa wannan kinji?”
Wani mugun kallo tayi min tace
“Ki barni naji da tunanin gado daya da zan kwana da wani mana ba se kin kara sa min wata fargabar ba”
Baki na rike nace
“Kiji dirty mind a gurin ki, idan kuma daki daban zai kwana fa?”
Dariya nayi sosae ganin yadda ta kwalalo ido sanann tace
“Ya isa ma, I’m someone he can’t resist!”
Bance komai ba na mike da niyyar na fita,
Se tace
“Nanah Thank you! Allah ya bar zumunci yasa miki murmushi akan fuskarki kamar yadda kika saka min, ya haskaka rayuwar ki kamar yadda kika haskaka tawa. Allah ya baki miji me kaunar ki”
A hankali na taka na rungume ta se naji gaba daya zuciyata is clouded with emotions, naji dadi sosae. ko mintina biyar baayi ba sega kiran Ayoub akan suna kofar gida, cikin sauri nace zan zo na bude musu gidan yanzun, gaban Hibba naje na kara rufe kanta na fito da ita parlon dake wani kamshi saboda incense din da muka banka masa, kallon sauran nayi nace
“Ladies ku shirya angwaye sunzo”
Daga haka nayi waje dan bude musu gidan, yana tsakiyar su yayi kyau cikin fararren kaya manya, murmushi ko digo yaki sauka kan fuskar shi, se na tuna Aliyu da tuni muna shirin namu bikin, amma rayuwa tayi sauri da yawa ta datse komai, lumshe idanuna nayi ina murmuring addua a kasan bakina. Muna shiga parlon friends dinsa suka fara fadin
“Kai dan iska ne Noafal, ba zaka je ka rungume ta ba, ai ba haka mukai da kai ba”
Shidai baice komai ba se zama da Yayi gefenta yana murmushi bai tanka ma duk tsokanar da suke masa ba, can akai addua aka musu nasiha sannan muka mike zamu tafi, nazo na rada mata abu a kunne ina dariya na tafi, kamar wanda muke gida daya se naji kewarta ta mamaye ni na kuma ji tausayin ta ya kamani dan nasan a big of responsibility lies on her shoulders!
Washegari da roko da komai na koma gidan Hibba na sameta ta can
canda kwalliyya yan uwan shi duk sunzo, yawanci yan nesa, kuma abinci tun daga safe har lunch din daga gidan su noafal aka kawo, so seda bakin suka tafi ni da wata sister din shi mukai wanke wanke na gyara gidan sannan muka dan taba hira na tafi. Kwana biyu na gyagije gajiyar bikin na fada tasu Aminatu, komai mun gama tsarawa yadda zai kasance kawai ranar muke jira ta karaso.
A bangarena ina iyakar bakin kokarin ganin na danne abubuwan dake taso min game da Aliyu, zuciyata na kaunar shi bayan duk abinda yayi min, ina jin haushin shi amma deep down in me ina ganin akwai abinda yasa yayi hakan, wani lokacin se na dakko na rubuta number shi da na riga na rike a kaina se na goge nayi tsaki, na kanji am so lonely kamar ni kadai ce duniya ta tsana, gashi so badly nake son tafiya gurin mamana dan Maman Hibba seda ta kara nanata min tace lallae lallai na cewa Daddy ya fada min inda take naje. So a wannan kwanakin se abibuwa suka kara min yawa, na kara ramewa se dan haske da nayi kadan, da dare na raba Ina tunanin rayuwata idan rana tayi jigilar gida da shirin biki.Dukka gidan ya cika babu wani space da yayi saura, dukkan mu daki daya muka hade kayan da muke so muka bar mawa baki sauran, kowa yan uwan shi sun zu daga bangaren Maman shi, ni daya ce kawai babu wanda yazo, to ina ma nasan dangin maman tawa balle na gayyace su. Ranar Wednesday sukai annoying bridal shower da ko attending banyi ba saboda i was totally against it, amma suma suka nace dole na hakura, da suka tafi se na zauna a daki ni daya ina kara tattara mana kaya, na kammalla ina waya da Hibba naji sallamar mama Asabe a kofar dakin, sallama nayi ma Hibba na tafi gurin mama Asabe nace+
“Mama ki shigo mana”
Shigowa ciki tayi ta zauna tace
“Me yasa ba kije gurin bikin ba?”
Dan murmushi nayi ina jera ma Amal bras din ta cikin wardrobe,
“Se mutane suga kamar wani abin ne”
Kaina na girgiza nace
“Ko daya wallahi, kawai inada abin yi ne a gidan shiyasa”
Kanta ta gyada tace
“To Allah ya sanya alkhairi ya kawo naku”
Nace Amin, se tayi shiru tana ta kallona kafin tace
“Nanah zan koma hadejia”
Da sauri na kalleta cike da mamaki nace
“Saboda anyi mene? Kin gaji damu ne? An miki wani abun ne? Haba Mama”
Dan murmushi tayi tace tana girgiza kai
“Babu ko daya, kawai naga duk kun girma, babu wanda yake bukatar kulawata, balle ma gaki a gidan”
Cikin rashin jin dadi nace
“Mama ki bar maganar kawai zamuyi daga baya idan bikin ya nutsa, amma dan Allah kafin lokacin ki canja shawara saboda mu muna bukatar ki cikin gidannan”
Daga haka na cigaba da abinda nake ita kuma ta fita, wajen maghrib nayi waya da wanda muka basu aikin abinci na basu menu na kullum da quantity sannan nayi sallah. Washegari gida ya gama hada mutane, a ranar zaayi kamu so tun safe muke shiri har yamma lokacin da zaa tafi wajen kamun a Hanan hangout dake cikin dutse. Amaren sunyi kyau cikin zani da veil da head na wani silver Ashoke like, rigar jikin su se muka samu gold holland da take silver sukai, sunyi kyau na gaske. Mu kuma muka cakare cikin atamfa golden dinkin mu dukka iri daya. Anyi taro an watse lafiya, anyi pictures kamar me. Washegari Friday akai daurin aure da yamma muka je dinner, washegari akai yini sannan aka fara shirin kai amare. Nasan ko ban fada ba kunsan munyi kuka, dukkan mu kasa raka su mukai se su Anty Sumayya ne suka kaisu. Washegari kuma amare sun tashi kowa ya tattara nashi ya nashi ya tafi amma Maman Aminatu seda ta tsaya ta gyara mana gidan ita da yan uwan maman su yaya Mariya so shi yasa bamu je gidan amaren ba.
Bayan sati daya babu inda muka je banda huce gajiyar biki da muke, Aminatu ta gaji da kiran mu da tambayar yaushe zamu zo, ita kuwa yaya Mariya tunda tayi sau daya tayi na biyu ta share mu. Da yamma ina zaune na gama abinci Daddy ya shigo muna zaune a tsakar gida, A’isha ta karbo kayan hannun shi, mu kuma muka masa sannu da zuwa ya shige ciki. Can ya fito da shirin masaallaci yace
“Gobe ku shirya zaku je gidan Amina, jibi se kuje gidan Mariya”
Nace
“To Allah ya kaimu Daddy!”
Se ya fita, ummu ta mike tana fadin
“Gobe bansan wanne kayan zan saka bama, wayyo Allah yaya Amina”
Lubna ta mike se kitchen wai zata hada mata cookies, ni dai kallon su nake kawai ina ayyana nima da tuni ina kano suna daukin zuwa gurina, se na samu kaina da fara tunanin kowa Zan aura? Ko ya yake ko a ina zan zauna, haka nayi ta tunani har seda Nawwara ta taba ni sannan nayi snapping out daga tunanin da nake. Wayar ta ta mika min nace
STORY CONTINUES BELOW
“Meye?”
Alama tayimin akan na kara a kunne na, da hannuna na mata alamar waye, kanta ta girgiza ta bar gurin se kawai na amsa sallamar da akai min,
“Yaya Nanah ko pharm Nanah zan ce”
Se nayi murmushi nace
“Nanan ma is ok”
“A’a zaifi dadi idan da title, anyways ya gida ya yara? An gama taro lafiya?”
Nace
“Alhamdulillah!”
Ina ayyana koma waye shi tabbas yana da surutu
“Naji dadin maganar da mukai dake, it worth it. Se anjima!”
Daga haka ya kashe wayar tun kafin ma na tambaye shi ko shi waye din, mikewa nayi da wayar hannuna na nufi Nawwara dake kitchen tare da yar uwarta Lubna sun kule se kuskus suke har basu ji sallamar da nayi ba, seda na karasa nace
“Nawwara waye kika hada ni dashi”
Murmushi tayi tace
“Shi ne wanda ya dakko mu daga gurin dinner kin manta shi?”
Kaina na gyada bance komai ba na fice, har na kwanta se ga Lubna ta zo tace
“Yaya Nanah har kin kwanta?”
Kaina na girgiza nace
“I just need a rest, ba bacci zanyi ba”
Se ta zauna tace
“Yaya Nanah ko dai akwai abin dake damunki ne? Naga duk kin zama shiru shiru”
Kaina na girgiza dan yanzun damuwar tawa kadan ce bamai yawa sosae ba, zuciyata ta fara hakurin rashin Aliyu, se nafi awanni ban tuna dashi ba kuma shima nasan he’s already over me, amma se naji anya da gasken we’re over each other, se kawai na girgiza kai nace
“Babu komai Lubna yau da gobe ce”
Se ta guada kanta tace
“Allah yasa! Dama na bada number ki?”
Bata rai nayi nace
“Zan ci uban ku keda Nawwara wallahi”
Hannunta ta daga in surrender tace
“Ni fa ba ruwana”
“To tashi ki barmin dakina ko na zazzage ki!”
Ta zumbura baki ta fita ni kuma na bita da dogon tsaki, inaga yarannan da karfi da yaji zasu min aure, I remembered bayan mun dawo daga dinner su yaya Mariya Amina tazo ta sameni wai uncle dinta ya ganni kuma yace yana sona, ita kuma tace mishi wai dama banida kowa, seda na bata rai sannan ta rabu da zancen.
Washegari very early muka gama ayyukan da zamuyi wajen karfe sha daya muka shiga motar Daddy yana zaune a gefena ya bani steeree yace na tuka shi, gabana nata faduwa na karba dukda na dan samu coaching daga sunusi driver plus babu nisa daga gida zuwa G9 inda Aminatu take aure, ride din was silent se gyarraraki da Daddy ke min, a haka muka iso gidan, ina parking suka fita Daddy yace nace yana jiran su a waje.
Kafin na shiga sega Salem din ya fito Amina na biye dashi, Daddy ya fito yana kallon yar shi, sena tsaya nima ina kallon rama da bakin da Amina tayi, nan da nan se naji gabana ya fadi, worse scenario na hassasso kodai She’s not happy, amma ai salem na sonta na ayyana.
Suka tsugunna suna a tare kowa na gaida Daddy, amma bai amsa ba se ya cire glasses din idanunsa yace
“Salim me yake damun Amina a haka na a
ura maka ita?”
Ni kaina seda naji kunya balle salem daya rikice baki daya yana fadin
“Daddy wallahi babu komai I’m really trying “
“A hakan? Kasan baka shirya aure ba ka aureta”
“Daddy ita ce bata cin abinci…”
“Kai meye aikin ka da ba zaka sakata taci abinci ba, kaga zan dawo wani satin kada na dawo na ganta a haka?”
Ya gyada kai da sauri yana mikewa, duk se Naji babu dadi cikin rai na, muka shiga ciki da Salem muka bar Amina da babanta, yace
“Yaya Nanah kina kallon abinda kanwar ki tayi ko? Babu yadda banyi da ita amma se taki cin abinci shi yasa na dinga addua kada kuzo”
Murmushi nayi nace
“Kayi hakuri haka Daddy yake kan yayan shi nasan kuma Amina haka take ko a gida, i hope baka ji komai ba”
Se yaji dadi yace
“I’m relieved!”
Yan gidana sun baje se kallo suke muka shigo sannan ta shigo muka daura sabuwar hira gwanin shaawa!Ni da Amina muka kule cikin daki bayan munyi lunch, ta dubeni tace
“Ya Nanah kin rame da yawa fa, kuma tun a biki na lura kamar kina cikin damuwa, kinsan dai I’m a good adviser ko?”
Dan murmushi nayi nace
“Babu komai, yanzun ke me ya hana ki cin abinci kika sa Daddy ya tsuye bawan Allah!”
Dariya tayi tace
“Nima naji tausayin shi fa, Daddy babu wasa kin tuna yadda yayiwa mijin yaya nasiba”
Muka kwashe da dariya muna tuna wannan dramar, gyara zaman ta tayi tace
“Yaya Nanah ya maganar uncle Nasir din ne?”
Kaina na girgiza nace
“Amina dole se munyi maganar nan ne? Dan Allah ku kyaleni haka!”
Ta marairaice tace
“Kinga yana son ki wallahi, kanin Umma ne matar shi daya da yara u…”
Cikin sauri na katse ta nace
“No! Wannan yasa bazan ma yadda ba Amina, ni na gama dating masu mata ai”
“Yaya Nanah daya fa kikai! Kinsan nawa nayi? I dated five guys kuma kowanne seda muka rabu wasu fault dina wasu nasu. Soyayya abu ne da ba zaka ce saboda past experience dinka baka bukatar shi ba, duk yadda ZUMA ya dalleki dukda haka kina bukatar ZUMA ta kara ma rayuwar ki dandano. You can’t just give up”
“Na yadda da kika ce daya nayi amma dayan da nayi seda nayi committing dukka rayuwa ta sannan akai stabbing dina ta baya”
“Yaya Nanah karki manta kaddara ce fa, Aliyu bashi da laifi kuma nasan kema kinsan hakan”
Se na tuna ni daya nasan message din Aliyu yayi min babu wanda yake da wannan labarin, a karo na farko nace bari na fada mata, seda ta gyara zama bayan jin abinda na gama fada mata
“Amma yaya Nanah something seems not right, anya Aliyu yayi miki text din?”
“To waye idan bashi ba? Ke seda ya kara maimaita wa ma da bakin shi, yana ganin son da nake masa zan dauki wannan iskancin ne? Nasan na so shi amma a yanzun na hakura Amina shiyasa soyayyar duka nake son na huta baki daya!”
Duk yadda nayi seda Amina tayi convincing dina nayi magana da uncle Nasir dinta, he was very calm ko a muryar shi hakan yasa na danji ko dai na gwada. Da yamma muka koma gida muka tarar mama Asabe ta tafi, nan muka dinga ma Daddy complaint akan hakan yace muyi hakuri, ni kam hadda kukana nida Ummu da Amal. Washegari muka tafi gidan Mariya dake ringim, tayi kiba tayi kyau muka dinga zolayar ta gidan miji yafi gida dadi, itama haka muka yini sannan muka dawo.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi da akasin haka, inata kokarin ganin ban sake jikina da Nasir ba amma abin ya faskara saboda kamar me using charm, ni a kasan zuciyata nasan ba son shi nake ba amma ina masa kara saboda halayen shi gaba daya nagartattu ne plus ina kunyar Amina da umman ta. Tafiya ta tafi aka sake result din mu and Allah’s mercy ni da Hibba mun gama tas, papers dinmu a cleared dama tuntuni munyi exams na shiga Pharmaceuticals society of Nigeria an bamu license din mu to practice. Abu na farko da mukai bayan anyi convocation an gama na dawo mukai fara processing nysc dinmu, ana posting aka kaini niger state anan zanyi camping dina. Da farko Daddy yace sede na hakura a wani badge din na kara applying amma bazan je niger ba, na same shi a daki na zauna nace
“Daddy baka so na hadu da mummy shi yasa baka son naje niger ko?”
Se ya kura min idanu yana kallona, hannun shi na rike nace
“Daddy ka barni naje, na maka alkawarin bazan nema kowa ba, zan jira har lokacin da kanka zakace naje niger gurin ta, I promised you!”
Wannan maganar tawa tasa ya barni na tafi, inata shirin tafiya ranar Sunday na gama yin su snacks da komai sega kiran Nasir kamar bazan dauka ba se kuma na dauka muka gaisa yace
“Yaushe zaki tafi?”
Nace
“Gobe inshaaa Allah!”
Se yace
“Allah ya kaimu, na kawo maman Amra gidan Amina I’m I free nazo na ganki”
Nayi shiru nayi jim ina tunani se can nace
“Ok!”
Tunda muke waya bamu taba haduwa ba duk yadda yake so se nayi ta dodging saboda bana son hakan, sede shi me kokarin turo min pictures din shi ne a whatsapp, inda ace ina son shi da tabbas nayi saa. Wanka nayi na shirya cikin abaya blue da balck sequence, na dan shafa powder ina ayyana first appearance matters alot, se na tuna zuwan Aliyu na farko irin hidimar da akai, gashi dai mun rabu kusan watanni uku bamu tare amma still lokaci zuwa lokaci nakan tuna shi and i felt how much I missed him, bansan se yaushe zan daina jin hakan ba amma yaya nasiba tace min daga lokacin dana hadu da wanda nake so zan manta da shi da wata soyayyar shi zanji kamar ma bata lokaci nayi then, nidai har yanzun ina tantamar hakan a raina ina ganin anya akwai wasu lokuta da zasui wiping memories din Sahibi daga zuciyata ina ganin hakan da wuya!
Bayan laasar Amal ta kai masa kujera a parking space din gidan, tareda tray wanda muka jera masa juice da snacks, Nawwara da Lubna suka hade min kai wai naki yadda da cousin din su amma na yarda da uncle din Amina, se nayi murmushi kawai nace suyi hakuri. Takalmina baki half cover flat na saka na dan kara kallan kaina a mirror sannan na fita nida Ummu, yana zaune Amal da A’isha na masa hira na karaso, zama nayi ina gaishe shi gaba daya ya tattara dukka hankalin shi akaina, kyakyawa ne kana kallon shi kasan sunada hadi da Amina dan duk gidan mu tafi kowa kyau saboda haka mamanta take, kai ni banga marar kyau a family din su ba kowa nada kyau, to shima haka yake kyakyawa kamar mace ko kuma astagfirullah kamar shi yayi kan shi.
“Finally yau naga yaya Nanah!”
Ya fada bayan su Amal sun tafi, nayi murmushi bance komai ba ya dinga min hira a hankali har nima na saki jikina muna hira,
“Nazo gobe na kaiki niger din?”
Kaina na girgiza nace
“No Daddy zai kaini”
“Kuna ji da Daddy dinnan naku sosae naga alama! Ya zanyi nima yara na su so ni har haka?”
Dariya nayi nace
“Daddy is my world, he’s my everything banida wani valuable abu kamar shi”
Kai ya gyada yace
“Haka Amina take magana daya biyu ta saka sunan Daddy a ciki”
Hirar Daddy tasa hirar tamu tayi tsawo sosae saboda indai kana son hirar mu tayi dadi to ka sako wannan bawan Allah, wajen biyar da mintina ya yi min sallama ya tafi bayan ya bar min envelope tare da min adduar Allah ya kiyaye hanya akan zamuyi waya. Kayan na kwashe na shiga ciki na tarar suna zaune suna kallon wapi korean movie 3days, zama nayi dan a episode 2 suke, Nawwara tace ita ta yi downloading mana, Lubna ta yaga envelope din taga mint note ne na 100 naira na 20k ajewa tayi tace
“Allah ya saka da alkhairi!”
Washegari dukka muka tafi niger state, a babban camp din s
u muka sauka aka gama screening da komai da komai sannan su Daddy suka juya, ba wanda na sani haka na dinga zama har nayi kawa da wata christian ce yar oyo state ce, mukan dan fita zuwa field tare, kullum muna waya dasu Daddy haka Nasir has always been there amma sede nace i like him amma zuciyata ta dan yi tsauri da yawa!