ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
***
Washegari haka na tashi sukukui! Babu kuzari ko yaya a cikin jikina. A wannan lokacin, babu abinda nake tunani illa hanyar da zan bi na gyara girgidadden aurena tun lokaci bai kure min ba.
Kaunar Fa’iz da soyayyar sa ke lallasa ni ta duk hanyar da suka ga dama. A duk lokacin da na daga ido na dubi tangamemen hotonmu (window size) da aka manna a (main-palour) kamar za muyi magana, sannan tsananin kamar mu da juna ta fito sosai a hotunan. Kyau ne ke bugun kyau na mallawan usili, sai kwarjini da ya dara mini da wasu ilhamomi na daban da aka halicci Fa’izun dasu da ban taba ganinsu a tare da wani da namiji ba.
Nakan tuno abubuwa da dama na irin cin kashi da rashin arzikin da na shekara yiwa iyayena da ‘yan uwana akan auren mutumin da na tabbatar ban dace da kowa ba cikin duniyar nan face shi, sai inji na tsani kaina da mata masu irin halina na kafiya da taurin zuciya, riko da zuciyar rashin afuwa da yafiya, bayan dukkaninmu da Allah ba Ya hakuri damu, Yana afuwa a garemu albarkacin mai albarka, da bamu kawo yanzu ba.
Hakika da Allah Baya afuwa ga al’ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) da tuni an shafemu a doron kasa kamar yadda aka shafe al’ummar sauran Annabawa da suka gabacemu saboda kura-kuran da muke tafkawa Ubangijinmu da tsakanin mu kanmu ‘yan Adam.
Misalin karfe uku na yamma na dauki waya na bugawa Momi, jikina a matukar sanyaye, kamar yadda zuciyata ta mace, babu karsashi ko kankani a tare dani.
Jin muryar Momi tana yi min sallama wani matsanancin tausayinta yazo ya lullubeni. Kenan ita bata da kowa a duniya da zata kalla ta ce nata ne, bayan mijinta. Baiwar Allah koda wasa bata taba gaya min ba don kar hankalina ya tashi.
Ni Allah Ya bani dangin kamar ruwa masu kaunata da son yiwa rayuwata gata amma nake wulakanta su ina bata musu rai akan abinda sunyi ne amma sai nafi kowa cin ribar sa. Wato zaba min miji daya da daya a cikin ‘ya’yansu wanda sun tabbata ko bayan ransu zai rikeni amana kamar rikon da uwa da ubana za suyi min.
Momi taji nayi shiru, bayan ta jima da amsa wayar, ta ce.
“Lafiya?”
Na ce, “Lafiya”.
“Kin kirani kuma kinyi min shiru”.
Na sharce hawaye da suka yo wani irin ambaliya akan kuncina, sai naji ba zan iya tambayarta komi akan rayuwarta ba, kada in tado mata abinda ta riga ta manta dashi, tana cikin rayuwarta mai tsafta. ‘And a total submission to ALLAH’ da yadda Ya kaddara mata rayuwar. Na kasa ‘controlling’ kaina da tausayin Momi, kawai sai na fashe da kuka gaba daya.
Kuka kawai nake ta rusa mata a wayar har na gaji don kaina bata katse ba, kamar yadda bata nemi taji dalilinsa ba, balle ta lallashe ni akansa. Sai da nayi mai isata sannan naji muryarta cikin sanyi tana magana.
“Na rasa ke wace irin yarinya ce, na rasa a cikin mutane ke wacce iri ce, na rasa abinda yake damunki, ba mamaki gata ne yayi miki yawa.
Menene aibun Fa’izu? Me kika fishi? Dame kike takama nayin butulci da irin wannan miji da Allah Ya baki? Har sai yaushe zaki shiga hankalin ki kisanAnnabi Ya faku? Duk sa’o’inki da tsararrakin ki kowanne na dakinshi cikin kwanciyar hankali, ga albarkar aure, sai ke don dai ki tabbatarwa da danginku da cewa uwarki bare ce abinda suke gudu a bare dai-dai ne.
To ni dai wannan hali naki ba a wurina kika gado ba (kafiya da taurin kai na rashin tunani) ke kadai kika san inda kika kwaso abinki. Yanzu da kika ki kwantar da kai kibi Fa’izu ribar me kika ci? Meye ribar zaman da kike yi? Ke ba ga ladar aure ba, ke ba kwanciyar hankali ba, ke ba ga komawa karatun ba, ba wan ba kanin wai karatun dan kama… Saboda ke shashasha ce kuma dabba, wadda bata san ciwon kanta ba ko?”
Hawaye ya ci gaba da wanke min fuska, ita bata san cewa tausayinta da nake ji ya rinjayi tasirin fadan da take yi min.
Muryata cikin sanyi da shasshekar kuka mai yawa, na ce.
“Don Allah Momi kiyi hakuri, ni yanzu babu abinda yake damuna. Hakuri zan baiwa Fa’iz din ma in ya dawo. Insha Allahu nayi alkawarin daga yau ba zaku sake jin wani abin assha daga gareni ba. Shima Baba zanzo in bashi hakuri.
Walida nake so ki taimaka min tunda sauran sati biyu su koma wannan hutu, ba wanda ke zuwa min daga Giwa har Jabi Road, ni kadai cikin wannan katon gidan… Don Allah Momi…”.
Na rushe da kuka sosai wanda ya tayar da hankalin Momi, maimakon kalamaina su sanyaya mata domin kukan nawa mai zafi ne irin na kauna da tausayin DA ga MAHAIFIYARSA, yafi karfin ace akan fadan da tayi min nake yinsa.
Wani irin kuka ne mai fitowa tun daga karkashin zuciya na wani abu mai nauyi da ya taba rayuwar mahaifanka.
“Don Allah don Annabi Momi kiyi hakuri, ba zan kara ba… ba zan sake ba… Na tuba na bi Allah na bi ku… Zan bi Fa’iz sau da kafa kamar yadda kike bin Baba, ba zan sake tada muku hankali ba… Ni kaina na gaji, na gaji da wahalar da kaina, ina son mijina yanzu. INA SON SHI Momi…”.
Banga Momi ba, amma nasan murmushi tayi, (a very deep smile) kasancewarta mai yin murmushi mai fidda sauti. Ta jima bata yi magana ba, daga baya kuma ta yin.
“Ki yiwa Abubakar waya, ki nuna nadamarki gareshi. Wannan zai sa shi watakila dawowa nan kurkusa. Amma in ba haka ba, mawuyaci ne yasan hakan, har ya yi marmarin dawowa gareki. Babu kunya tsakanin mace da mijinta, akwai inda ya dace aji kunyar, amma ba a irin nan ba, musamman idan baya ganin ki”.
Na ce, “Ba zan iya ba Momi, wallahi bazan iya ba, ina jin kunya, ina jin nauyinshi sosai domin sai a yanzu na fahimci abubuwa da yawa wadanda ada ban fahimta ba. Tsiyar dana tsula tana da yawa, tijarata gareshi mai yawa ce, da kyar in zai yarda ya kara hada rayuwa dani…”.
Na ci gaba da kuka mai tada tsigar jikin mai kaunar ka, musamman UWA!
A sanyaye Momi ta ce, “Ai sai kiyi tayi, tunda kinga shi zai fisshe ki. Ki tsaya jin kunya ya dawo da matar dake son shi, ina ce shi kenan ko? ‘It’s not too late for you to correct your misdeed’ ba’a tsufa da tuba muddin ana raye. Mutuwa ce kadai shinge ga tuba da nadamar bawa. ‘Atleast ya san kinyi, koda ba zai karba ba… Walida da Kausar duka na nan zuwa”.
Jikina duka ya saki a yayin da Momi ta kashe wayar. Na kifa kaina cikin kujera na rasa me yake min dadi. A yinin ranar baki daya, na kare shi ne cikin tunanin ceto kima ta a idon Fa’iz da sauran son, in akwai.
Yamma lis misalin karfe shidda na yamma, direban Bababn ABU ya sauke Walida da Kausar a harabar gidan. Walida tayi sallama ta aje (trolly) dinsu, ta dube ni duk nayi firgai-firgai dani, tun safe banyi wanka ba ga yunwa, tun kofin ruwan lipton dana zuba ma cikina da safe. Da yake yarinya ce mai hankali bata yi magana ba, gaisheni kawai tayi ta aje mayafinta ta shige (kitchen) ita kuwa Kausar wai wanka zata yi.
Uffan na kasa ce masu, ashe Walida girki take yi, sai bala’i kamshi mai tada tsohuwar yunwa naji yana bugun hanci na kafin ince wannan ta aje min (tray) a gabana, (fried-rice) da taji kayan lambu tayi sharr da farfesun koda na tiriri da tashin kamshi.
Nayi ajiyar zuciya na dubeta cike da kauna a raina, na ce.
“Dan uwa rabin jiki”.
Na sa cokali na soma ci hannu baka hannu kwarya. Rabona da su tun ranar da Fa’iz ya kore su.
Kausar ta fito ta dau wanka ta dau gayu da tirare dai-dai sanda na kammala cin abincin. Ta samu kujera ta hakimce ta kunna t.v tashar ‘Bollywood’ na galla mata harara na ce.
“Inda Walida ta fiki kenan, hankali da sanin ya kamata. Wawuya kawai, kashe talbijin din nan bana son hayaniya”.
Kausar ta zumburo baki, “Ni fa hutawa nazo yi ba aikatau ba. Tun ranar da maigidan ya koremu ban kara marmarin zuwa gidanku ba. Yanzun ma ba don Momi ce ta takura min ba da banzo ba”.
Na kama baki na ce, “To yi mana rashin kunya ke da aka turo ki taimakeni mu sada zumunci. Tashi maza-maza ki wanke (plates) din da aka yi amfani dasu da tukwanen, kiyi ‘mopping’ (kitchen) din ko mu raba gari yanzu-yanzun nan har bakin ‘gate’ a jiyo mu”.
Ta mike tana kumburi kamar zata fashe tayi (kitchen) din Walida na yi mata dariya.
Na ce, “Lallai Momi tana fama da wannan yarinyar, Allah Yan shiryeta”.
Walida ta ce, “Ai in tana yi Momi cewa take gadon Fa’izah”.
Nayi murmushi sosai cikin raina na ce, “Fa’izar da”.
Da daddare muna kwance a gado daya, Walida Kausar nata barci abinsu cikin kwanciyar hankali amma ni sai juye-juye nake daga wannan gefen zuwa wancan. Na kasa barcin magan-ganun da muka yi da Momi ke cina ta ko’ina, suna babbaka ni.
A karo na farko nayi tunanin jarraba shawarar Momi na. To amma in kira Fa’iz ince masa me? Ince Fa’izu Abubakar, yanzu ina son ka? Da wane baki? Da wane harshe? Da wacce siga? Na ciza na hura na kasa samo sigar. Ina cikin rukunin mutanen da basa iya fadin abinda ke zuciyarsu a fatar baki, sannan ni mutum ce mai tsananin kunya da kama kaina.
Wata zuciyar ta ce, “Fa’izu ba matsayin miji kadai yake takawa a gareki ba. Dan uwa ne na jini. Ba lallai sai kince sonshi kike ba, ‘actions show feelings atimes…”.
Da wannan shawarar da wannan tunanin na kira Ummi, cikin barci mai nauyi ta daga bayan wayar ta sha (ringing) ta gode Allah. Har bana jin abinda take fadi sosai sai da na harhada na gane cewa take.
“Waye?”
Ajiyar zuciya na saki mai nauyi, tattare da jin nauyi, na ce.
“Ni ce, kiyi hakuri ‘for’ damun barcinki. Lambarshi nake so ki bani”.
“Shi wa?”
Ta katseni cikin kaguwa.
Sai na kasa bata amsa, don naga alamun rainin hankali cikin tambayartata. To lambar wa zance ta bani ba ta mijina ba? Ko zance ta bani lambar wani kato ne bayan mijin da Allah Ya halatta mini? Sai na kasa ce mata komai.
A fusace ta ce, “Wai lambar wa zan baki? Yaya Bashir yana kirana”.
Na tattara sauran karfin halina da guntun kashi na a katara na ce.
“Yaya Fa’iz”.
Sai cewa tayi, “Wanne?” Cikin iya shege.
Kamar na fashe da kuka na dai daure na ce.
“Na Hajjah”.
Dariya Ummi ta saki mai ban haushi da bakanta zuciyar wanda aka mawa. Sai da tayi ta harda hawaye duk da bana ganinta ina jinta tana share shi, sai da ta mula cikin ginshira irin ta su ta ‘ya’yan A.B sannan ta ce.
“Gashi kuma ya gargademu baki dayanmu kada mu sake mu baki lambarshi don gudun kada kisa mai (bomb) a kunnen wayar ya tashi da shi, kin san makiyinka har kullum nesa-nesa kake yi da shi musamman wanda ka sanshi farin sani cewa makiyinka ne dole ka sha masa lahaula”.
Cikin tsananin takaici na ce, “Umm!”.
Ta ce, “Na’am Fa’izatu!”
“Bana cikin kayan ‘yan wulakancin ki. In banda dole banga me zai sa in neme ki ba balle har ki wulakanta ni…”.
“To ni na ce ki neme ni?” Ta katse ni.
“Sanda ki ke shuka rashin mutuncin ki wa kike nema? Wane irin zagi da wulakanci ne baki yi min ba a lokacin da kike tsula tsiyarki? Sai yanzu da taki ta kawo ki ne kika san ina da amfani?”
Na ce, “Shi kenan Ummi, zan nemi Zaneerah, nasan ba zata yi min abinda kika yi min din nan ba. Na dauka abokin kuka shi ake gayawa mutuwa, dalilin da yasa na neme ki kenan”.
Ta ce, “A’ah ba shi ake gayawa ba, abin dariya ake gaya masa kuma ni abokiyar dariya ce ba ta kuka ba, Allah Ya raba mu da duk abinda zai sa mu kuka…”.
Ban tsaya jin karshen iskancin nata ba na kashe wayata. Na kudure a raina ba zan sake neman Ummi a duniya ba. Don haushi sai da hawaye suka zubo min.
Ban yi kasa a gwiwa ba na kira Zaneerah dake Lagos, (with full confidence on her) don kowa yasan Zaneerah ‘is nice’ kuma yarinya ce mai sanyi da sanyin hali fiye da kowa cikin A.B baki daya.
Bugun farko layin ya shiga, amma har ya katse bata daga ba. Ban hakura ba na sake kira a karo na biyu, ya jima yana ringing shima kafin naji sassanyar muryar Zaneerah ta ce.
“Hello!”.
Da sauri na ce, “Kinyi barci ne Zaneerah?”
Ta ce, “Ko nayi barci ko banyi ba ina ruwanki Fa’izah? Kiyayyar Yayana da ta shafe ni… Ba kya nemana balle YAYA ALIYU! In maye na cin kowa baya cin kansa, Yaya Aliyu bai cancanci burus din da kika yi dashi ba in ni na cancanta saboda Yayana Abubakar. Diyata mai sunanki wadda aka sawa sunan domin KAUNAR ki balle wadda na sake haifewa ita ko darajar Allah Ya raya ko da ‘text message’ ne bata samu ba. A lahira da kallo akan ZUMUNCI da kuke yin wasarere dashi a yanzu akan wasu hujjoji marasa madafa. Yanzu ma zancenki da irin butulcin ki muka gama ni da Yaya Aliyu. Umh! Ina sauraron ki yanzun da wacce kika zo?”
Sai kalamai suka kare a yawun bakina domin na yarda na amince nayi amanna da gaske ni din mai laifi kan laifi ce ga Zaneerah wadanda bazance ban san nayi ba, sai dai a wancan lokacin basu dameni bane domin ina da damuwata ta kashin kaina da ta dame ta kowa, ta mantar dani kowa da komai har da YAYA ALIYUN.
Gaskiyar Zaneerah a LAHIRA da kallo akan zumunci, zamani ya canza al’umma da dama muna wasa da zumunci da hakkokinsa ta yin amfani da uzrorin kanmu da suka sha gabanmu, wadanda in ka bibiya duk na neman duniya ne wadanda ba zasu karemu gaban mahalicinmu ba ranar da yake binciken wannan amana da hakki mai girma mai suna ZUMUNCI da Ya bamu a hannayenmu cikin Alqur’ani da Hadisi.
Zumunci abu ne mai girma. Allah Ya kawo mu wani zamani da baka neman dan uwanka na jini don jin lafiyarsa ko ta iyalinsa da halin dayake ciki, sai kana bukatar amfanuwa dashi ‘in any way or the other’. Ina rokon Allah Yasa al’umma MU GYARA mu dawo da zumunci a muhallinsa irin na iyaye da kakanninmu a inda baka bambance dan wa da dan kani ko da shi ne beran masallaci saboda talauci, ko da shi ne karuna saboda arziki ba zaka bambance dan wa da dan kani ba koda da fatar baki ne ba za’a bambance maka ba sai dai ace “DUKA DAYA!”
Na nisa cikin mutuwar jiki da ta zuciya da tunanina yazo nan. Na rantse na manta waya muke ni da Zanira kuma kudin wayata na tafiya.
Zanira bata aje ba haka nima sai dai kawai taji shasshekar kukana.
Allah Sarki Zaneerah, Zanin Hajjah, Zanin Mama, Zanin Yaya Aliyu… Sai ta kama dariya, dariya sosai mai nuna maida komai wasa, kuma ta fada ne don ta huce fushinta ba don ta kullace ni ba ‘And she’s relieved by expressing it’.
“Ni fa komai ya wuce kuma har ga Allah nayi miki UZRI dai-dai har saba’in Fa’izah Fa’iz Abubakar…”.
Murmushi nayi, wani irin dadi ya ratsani da wannan suna mai sanyi data kirayeni da shi.
“Bani da bakin da zan wanke kaina, sai dai ince KIYI HAKURI, KIYI HAKURI, KIYIHAKURI ZANEERAH…!”
“Kema kiyi hakuri ‘for hurting your feeling with my words’. Na fada ne don in huce bacin raina kuma na huce”.
“Nayi miki alkawarin zuwa har Lagos in Yaya Fa’iz ya dawo inga ‘yata da takwarata, in baiwa Yaya ALiyu hakuri. Yanzu ma ina bashi wani na bin wani, kamar yadda na baki.
Bayan nan ki bani lambar Yaya Fa’iz ko ki tambayo min Yaya Aliyu in baki da”.
Sai bayan da na fada ne wata kunya ta rufeni, wai macece take neman lambar mijinta a wurin ‘yan uwa da dangi wannan abin kunya har ina! Ai kiyayyah ba hauka bace, sai ko in ta hadu da tabin hankali. Abin kunyar ma kuma ga kanwar mijin uwa daya uba daya. Allah ka agajeni.
Wata irin guda Zaneerah ta sakar min a kunne wadda har saida ta dode min dodon kunne, nayi saurin kauda wayar daga kunena. Sannan na jiyota tana cewa.
“Mafarki nake ko ido na biyu?”
Na amsa da karsashi, “Idonki biyu Zaneerah, don Allah ki bani. Kada kiyi min abinda Ummi tayi min, kada ki hukuntani da laifina bayan na riga na amshe shi, na kuma aikata shi ne bisa kuskure. Don Allah Zaneerah…”. Na karasa cikin karkarwar murya da rishin kuka.
“Saurare ni Fa’izah”.
Ta fada cikin jin kai da kauna irin ta dan uwa shakiki.
Na rage sautin kukan ina sauraronta.
“Wallahi kinji nayi rantsuwa ta ‘yan Musulmi kenan Yaya Fa’iz ya hana kowa ya baki lambarsa. Ya hana ni, ya hana Yaya Aliyu, ya kuma yi rantsuwa duk wanda ya baki ya yanke zumunci dashi har abada! Ki karbi uzurina domin ina daga cikin mutanen da yake mutuntawa, ya kuma yarda da amanarsu”.
Sai na zamo ‘standstill, wordless, speachless, motionless! Me Fa’iz yake nufi da hakan? Kuma me yake nufi da katse duk wata hanyar sadar dashi gareni? Bani da sani akan hakan, haka itama Zanirar. Don haka tambayar ta ma baya da amfani.
Hawaye ya sake ciko idona. Muka yi sallama kowanne jiki ba kwari. Tana fadin sai sunzo ganin gidan Malali, ko da yake ta gani a hoto wai Mama ta tura mata ta watsapp.
A wannan daren, mai cike da sauyin sabbin al’amura masu dama a gareni, dai-dai da minti daya ban runtsa ba. Kuka nake yi wanda ni kaina ban san dalilin sa ba. Nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. Idanuna suka shiga radadi, da zugi dole na sassauta musu.
Anya ba asiri Fa’iz yayi min ba? Domin ko ga marigayi Nazir S. da Yaya Aliyu dana so a baya, so mai azalzalar zuciya ta, yake azabtar da ruhina bai kama kafar na yanzun akan Fa’iz Bamalli ba.
To ko Mama ce tayi min asirin? Nayi saurin kawo A’uziyyah da Istigfari a bisa wannan mummunan zato da yake darsuwa a zuciyata. Na tabbata Mama, ko wani cikin zuri’armu ta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ba zai taba yi min asiri wai don in so Fa’iz ba. Domin bamu san shi ba, bamu san hanyar nemoshi ba, bamu san inda ake yinsa ba haka bamu san yadda ake yinsa ba.
Abinda muka sani shi ne idan muna da bukata, mu tashi cikin dare mu tsarkake kanmu da tufafinmu mu daura alwala, mu fuskanci alkibla muyi sujjadah ga Ubangiji mu fada mishi bukatar mu. Wannan ce tarbiyyar da aka rainemu da ita yaranmu da manyanmu. Ko da zata yi yunkuri akan inso Fa’iz sai dai tayi addu’a na Allah Ya daidaita tsakaninmu in da ALHERI (sunan wani littafin Takori).
Idan kuwa har ta yin to ta tabbata an amsa addu’arta, ina sozn Fa’iz a yau, wani irin so da bazan iya fassarawa ba!!!
Abinda na yarda da shi a tsayin daren baki dayansa shi ne. NA SOMA SON FA’IZ A DAN ZAMAN DA MUKA YI TARE na gajeren lokaci wanda yayi tsayin dare dubu da goma sha hudu a idanu da zuciyata. Dabi’unsa, saukin kansa, barkwancinsa, rayuwarshi gaba daya, addininsa, nutsuwarsa, ‘his unique personal attributes’ da tsananin KISHINSA akaina a fili da boye su suka ja ni ga kaunarsa.