ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wankan da nake ninkaya ina yi cikin kwami yau (unexpressable) ne. Wani irin wanka (slow-slow) da ban taba yin irinsa a rayuwata ba. Fatar jikina ta wanku har santsi take da silki tamkar mai canza launin fata…
“Kazo ga jikin nan FA’EEZ, zan baka abinka, ba na yawon dandi bane naka ne, mallakinka ne, a yau sai yadda kayi dashi… Nayi kuskure Yaya Fa’iz, kuskuren da nayi farin cikin amsar shi tun a duniya na kuma yi dammarar gyara shi tun a duniya kafin Mahalicci ya tambaye ni shi”.
Karar wayata ne ya katse min sambatun da nake yi, na mika hannu na daga. Mama ce.
“Yaya magungunan da na aiko miki dasu dazun Fa’izah? Kin shanye ko?” Cikin jin kunya irin wanda bai taba faruwa tsakaninmu ba, na ce.
“A’ah!”.
“Dalili?” Ta tambaya.
“Aiki nake tun safe Mama, su Walida sunce yau Yaya zai dawo”.
Wata matsananciyar kunya tazo ta lullube ni, na kuma kasa fadin wane yayan? Tunda yayun namu yawa gare su.
Tayi murmushi na manyance, “Shi bai gaya miki da kansa ba sai su Walida?”
Nasa hannu na kautar da zirin gashina dake disar da ruwa a jikina, na ce a hankali.
“Ya yo waya ina bacci, ya sake yowa ina cin abinci, daga nan bai sake yowa ba. Kuma laifin Walida ne da bata bani wayar ba, sai ta ce wai ina bacci, ko ta ce abinci nake ci don shirme irin nata”.
Mama ta ce, “Ai shi kenan. DOn Allah kiyi amfani da kayan lefenki kinji Fa’izah! Ya gaya min baki taba amfani da duk abinda ya dauka ya baki ba. Sakon da Shu’aib ya kawo kuwa kada kiyi wasa da yadda na ce a cikin takarda kinji Fa’izah na?”
Tausayin Mama da wani bala’in son danta ya kara kamani, na kara kwantar da kai a cinyoyina na kasa magana. SHin ita din wacce irin UWA ce mai maida nata ba nata bane?
Ta ce, “Ba abinda kike bukata ta fannin kayan girki?”
Na ce, “Ba abinda Shu’aib bai kawo min ba Mama, har da wanda bana bukata duka ya kawo”.
“Yayi kyau”. Inji Mama.
Muka yi sallama cikin girmama juna. Ni na fara aiwatar da umarninta.
Wata irin kwalliya na soma da Voyal din Hilton pitch and maroun, kasancewata wankan tarwada sai kalar ta wani irin kwanta ta bi fatar jikina. Na dauki voyel din ne cikin kayan da Mama ta kira da lefe na a dinkensa na ganshi, dinki mai kayatarwa da daukar ido na doguwar riga budaddiya, sai dai daga sama ta kama jikin tsam. Na nada dankwalin a kaina ya kwanta lambam.
(Make up) dina bai yi yawa ba, (very cool and sexy). Don karawa aya zaki na dauko takalmi cikin kayan, (flat) ne pitch dan Italy na zura siraran kafafuna. Turaruka kala-kala nayi amfani da su, duk dakin ya dumame da kanshi mai sanyi da sanyaya zuciya.
Na karashe shanye romon kazar Mama, na shiga (toilet) nayi (brush) na fito na dawo falo na kishingide cikin (three seater) ina kallon tashar ALJEZEERAH. Dai dai lokacin da agogon bangon dake ‘main palour’ yua buga karfe hudu da minti talatin. A lokaci daya na murdo radio daga I-pad dina ina sauraron sashen Hausa na BBC, ni kaina ban san wanne nake sauraro ba tsakanin Radio da talbijin.
Sai dai babu wanda hankalina ke kansa cikinsu, hankalina ya karkasu ne. Wani ya tafi ga tunanin wace irin tarba zan yiwa Fa’izun in ya shigo? Sannu da zuwa ko sannu da hanya? Sannu da hanya ko ina wuni? Ni kaina ban sani ba.
Wata mutum ce ni din a yau dake ninkaya cikin maliyar SO, take neman a karbeta ko yaya ne a zuciyar da bata da tabbaci a kanta.
Daya kashin kuma ya lula ne cikin tunanin tarbar da shi zai yi min. ‘Will I be accepted? Appreciated? Trusted? Believed? Ignored or abandoned???
Karfe biyar ta buga na soma waiwaye ina duban kofa, haka duk motsin da masu karanta labaran Aljezeera da na BBC suka yi tsammani nake shigowar mota ne, ko kararrawar shigowa falo.
Biyar da rabi… shida na yamma babu Fa’eez babu mai kama da shi. Bakwai na dare ta shude babu labarin Fa’eez Bamalli balle sallamarsa.
Na soma karaya, kwalliyar ta soma gushewa da kanta, Gwiwata ta soma sagewa da kagara da zakuwa. Mutumin da akace zai zo biyar na yamma, shi ne har karfe takwas na dare, babu shi babu alamarsa.
Da kyar na iya mikewa na bada faralin magariba da isha. Takwas da rabi na samu wayar Mama, ina dagawa ta dora da tamabayar da ta girgiza ni ko ince ta firgita ni.
“Fa’eez Malali ya soma isowa kenan? Ni ina nan ina ta zuba ido shiru, to kice da shi in ya huta Babanku na son ganinsa da safe kafin yaje ko’ina…”.
Ban san sanda hawaye ya barke min ba, na soma shasshekkar kuka da ma kiris nake jira. Hankalin Mama ya tashi.
“Ke lafiya? Babu lafiya yazo ko kuwa?”
Cikin kuka na ce, “Bai fa dawo ba kwata-kwata, kuma babu wayarshi babu ta Yaya Bashir. Nayi (trying) ta Yaya Bashir din a rufe take. Shi kuma wadda ya kira da ita dazu da na duba sai naga ashe anyi (hidden No.) din”.
Mama tayi dan jim! Kafin ta ce, “Ya isa! Nan da karfe tara in bai iso ba zan turo Malam Isa ya dauke ki, Babanku sai ya bi sawun su Kanon shi da Shu’aib, idan yayi tafiya irin wannan ba inda yake fara sauka sai nan Jabi Road, daina kukan hakanan, watakila suna Kanon”.
Nayi shiru ina goge hawayena tana bani hakuri, da cewa kukana yana tayar mata da hankali.
Jikina a matukar sanyaye na aje wayar gefe, lokaci guda hankalina ya kai ga abinda ake fade a tashar ALJEZEERAH, tare da wanda BBC ke fadi duk a lokaci daya, wato;
“JIRGIN BRITISH DA YA TASO DAGA HAVERFORDWEST AIRPORT DA KARFE GOMA NA SAFE, YA FADI A SYCHELLS ISLAND TSAUNIN DAKE HADAKAR KASAR SINGAPORE DA……
Ihu da kururuwa na saka, wanda ya tafi tare da yin fatali da I-pad din da kafata ta kwankwatse a kasa, na mike tsaye ina ta kururuwa hade da INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’OUN. Na dora hannuna duka biyar a kaina, wani irin azababben kuka na saka dake ketowa tun daga cikin hanji da koda ta, cewa nake.
“Noooooo!”.
Na yunkura na doshi kofa hannuwana aka, juwa ta kwasheni ta kayar. Ban daddara ba na sake yunkurawa, burina in bar gidan zuwa inda za’a ce min ba dai dai naji ba, ko kuskuren hanyoyin sadarwa ne. Juwar ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen sake kayar dani. Sai na soma rarrafe akan gwiwoyina dai-dai lokacin da wayar da ta fashe a kasa ke nata kuwwar duk da tsagewarta.
Da rarrafen na isa gareta na sata a ‘handsfree’ dukkan hannuwana da jikina baki daya rawa suke da karkarwa. Tun kamin inyi magana naji muryar Surajo cikin karaji da kuwwa yana tambayata.
“Fa’izahhh! Fa’eez ya sauka karfe hudu na yamma?”
Na kara rikicewa da kuka, cikin in’in’ina…, “Naji…naji…nima…nima Suraj…jir…jirginsu ya fadi ko?” Surajo ya ce, “Hasbunallahu wani’imal wakeel! Ni’imal maula wa ni’imal naseer!!! Gani nan zuwa yanzun, nima bisa hanya nake”.
Na durkushe anan na cigaba da kuka ba kakkautawa, hawaye na hade da majina. Dai dai lokacin da ALJAZEERAH suka shiga hasko jirgin a tsaunin daya fadi, ban san sanda na kwarara ihu da dukkan muryata ba. Abinki da unguwa irin GRA Malali, ba ruwan kowa da kowa balle wani yasan halin da nake ciki ya kawo min dauki, buzu yayi nisa domin na tabbata akwai tazara tsakanin bakin gate da cikin gidan wadda mota ma sai tayi tafiya zata iso. Ya’u kuwa tin dazun yayi min sallama da cewa ya tafi gida. Haka nan yanayin gininmu mawuyaci ne ko zubar ruwan sama aji balle a jiyoni, daga ni sai Ubangiji na muka san halin da nake ciki.
A wannan halin Isa direba ya cimmani har cikin falon, ko yayi sallama ko bai yi ba ni ban sani ba, na dai ganshi tsaye a kaina, shi kanshi yayi wujiga-wujiga, idanunshi sun firfito sunyi jawur.
“Mama ta ce inzo in tafi dake…”.
Ko tunanin rufe gidan banyi ba balle yafa mayafi na bi bayan Isa, sai shi ne ya dawo ya rufe kofofin.
Tunda muka hau titi nake rasgar kuka, babu abinda nake tunawa illa musgunawa da kaskanci gami da rashin albarka, dana shekara yiwa mijina Abubakar Fa’iz tun ranar da aka daura mana aure. Muka kuma rabu, ba tare da na nemi cikakkiyar gafararsa ba, ashe Allah Ya rubuta iya tafiyar kenan, iyakacin sallamar kenan, iyakacin zaman kenan SAI A DARUS-SALAAM….!
Na tuna yadda naci burin sauya akalar rayuwarmu, (from negative to positive). (So, kauna da mutunta juna. Ashe Allah Ya riga ya kaddara cikin kundin rayuwata BAZAN TABA CIN WANI BURI A RAYUWATA IN SAMU BA… BA ZAN TABA SON WANI ABU KO WANI MUTUM A DUNIYA IN SAMESHI BA!!!
Inama ban zo duniya ba… YA LAITANI KUNTU TURABA…!!! Idan kuma zuwan duniyar kaddarata ce, inama ban kawo wannan lokacin ba, ina ma ban kawo wannan ranar ba, inama na rungumi KADDARA TA ta auren Abubakar ZABIN IYAYENA kowanne irin hali gareshi na yiwa iyayena biyayya kamar yadda Ummi ta ce! Kamar yadda Ummi tayi, kamar yadda Zaneerah tayi… gasu nan da manyan rabo tun a duniya kafin aje Lahira, da tabbataccen farin ciki da kwanciyar hankali wanda na tabbata ni har tawa mutuwar ta riskeni ba zan same su ba…!!!
Inama mun rabu ne bayan na bashi jikin da yake rokon na bashi ya dauki budurcina da nake tattalawa shekaru ishirin da uku yana mai sa min ALBARKA??? Inama ban taba yin ramuwar gayya a rayuwata ba? Inama ban taba nunawa Fa’iz kiyayya ba… Inama mun rabu lafiya… da ko ba komai na tsira da wannan koda ban haifi kyakkyawan Da irin Fa’iz ba… inama…inama…inama… Inaman tana da yawa!!!
A halin yanzu bani da abinda zan fuskanci Ubangijina dashi, ranar da tawa mutuwar ta riskeni. Banyi biyayya ga mahaifina da iyayensa ba tun farko, na sanya shi cikin bakin ciki da bacin rai maras misali. Na bashi kunya… na ba mahaifiyar shi da ‘yan uwanshi… wadda ta sadaukar da kacokan rayuwarta da inganta rayuwarmu kuma komi tayi tayi ne ‘for our own betterment’ bata da ribar da zata tsinta a ciki, ta riga ta gama rayuwarta, ta gama cin ribarta ta Allah kawai take jira Hajjaty… bata cancanci abinda nayi mata ba ko sakayyar dana yi mata. Har kaurace mata nayi, don ta bani abinda tafi so a rayuwarta. Babu wanda ta yiwa zabi irin wanda tayi min, tabbacin ni din ma tana so na! Shin ni FA’IZAH cikin butulallun ‘yan Adam wace iri ce??? Anya ba ni ce SHUGABAR su ba???
A yau FA’EEZ din ya bar min duniyar baki daya, in ci ta yadda nake sonta, da tsinke koda cokali, koma da cokalin kaya (fork). Banga amfanin sauran rayuwata ba, rayuwar da babu FA’EEZ a cikinta. Wanda suna ma daya aka sa mana, kamar yadda kamanninmu suke daya, duk da zuciyoyinmu basu samu daidaito ba tun muna kanana.
Na tabbata na kuma yi amanna da cewa baki daya zuri’ar A.B ni zasu zarga da gushewar Fa’eez a doron kasa, tunda na sha faden ina addu’ar ALLAH YA KASHE FA’EEZ BAMALLI IN HUTA.
Duk da cewa tsakanina da Ubangijinnawa ban taba yi ba sam. Kuma ban taba fadin hakan daga karkashin zuciyata ba, sai, dai a fatar baki.
Banga amfanin sauran rayuwata ba! Idan nayi la’akari da manya-manyan kura-kuran da na tafka ban yi ‘repenting’ dinsu ba. Wadanda nake ikirarin LOKACI zai bani damar goge su, gaskiya ne babu wanda yake sama da KUSKURE sai dai lokacin da nake ikirarin zai canza komai… bai bani wannan damar ba…!!!
Kuka da gunjin da nake gunzawa da shekawa a fili da zuci, yasa ban san tuni munzo gidan Baban Kaduna ba sai da naji Isa na kira.
“Munzo fa Hajiya…”.
Na sunce kullin kaina na zagayo dashi wuyana don sai a lokacin na lura ko mayafi ban dauko ba. Na rarrafa na fito daga motar. Bana ko ganin abinda yake gabana.
Banyi mamakin rashin haduwa da kowa a harabar gidan zuwa ciki ba, bana ganin hanya, illa kafata da tuni ta riga ta gane kowanne sako da kowanne lungu na gidan Baba Mukhtar A.B Giwa.
Gaba dayansu suna tattare a babban falon gidan inda na sanya kafata, manyan gidan da yaransu, babu wanda baya kuka na fitar rai a falon cikin matukar kidima na doshi Mama Asma’u, wadda idanunta suka yi luhu-luhu don kukan da harshe ba zai iya bayyanawa ba… Nayi zaton ma zan tadda FA’EEZ a falon. In hadiye bakin cikina. Amma yanzu na tabbata FA’EEZ YA RASU A HADARIN JIRGIN SAMA!!!
Na kama Mama cikin gigicewa ina wani irin kuka hawaye na min lugulgude da ambaliya a fuska…
“Mama da gaske Fa’eez ya mutu??? Da gaske bazan ci ribar wannan SON ba ma a wannan karon???”
Mama kuka kawai take, ko amsa daya cikin tarin tambayoyina ta kasa bani, Ta kankameni a kirjinta kawai amma ta kasa magana.
Baban Kaduna ne ya shigo yana dafe fa kansa, yana fadin.
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN… da gaske jirgin ya fadi, daga Kanon muke, Bashir din ma ya kamo hanya ne don ya gaya mana yayi (accident) yana asibitin koyarwa na Zaria babu yadda yake… Bamu san wa yaje ya gayawa Hajjah ba ta fadi! Barin jikinta ya jikkata.
Allah daga gareka muke kuma gareka zamu koma… Ba Ka daurawa rai abinda ba zata iya ba, amma wannan jarrabawoyi da kayi a garemu masu tsauri ne… muna rokon sassaucinka da afuwarka idan mun kasance ne masu saba maka a kan sani ko bisa rashin sani. Hakika Kai Kaine Sarkin da bashi da mahadi, muna rokonka kudurah da iradarka akan wadannan jarrabawoyi namu zuciyoyinmu sun gaza dauka, kwakwalen mu sunyi rauni ga rungumarsu… Yaa ASSAMADU, KADIRAN ALAA MAN YA SHAA’U muna rokon sassaucin ka….!!!”
Wani rugugi da hargagi naji a cikin kaina. Na tabbatar dai yanzu FA’EEZ YA RASU!!! Bayan wannan ban sake sanin me ke faruwa a duniyar ba… Ban sake sanin inda kaina yake ba…!
***
Sanyin ruwan da ya ratsa kwanyar kaina, ya dangana da hakarkarina, ya zagayo zuwa wuyana da kirjina, shi ne ya maido ni hayyacina. A hankali nake bude idanuna ina lumshe su da son tantance halin da nake ciki? A ina nake? Me ya same ni? Cikin mafarki nake, ko kuwa idona biyu?
Cikin ‘yan sakanni na fahimci a gadon asibiti nake, akan cinyar mutum mai taushi, fanka na wulwulawa, A.C na burari. A hankali kwakwalwata ta soma tariyo abinda ya faru, da kuma musabbabin abinda ya kawoni gadon asibiti, wanda ba zan gushe cikin addu’a da fatan Allah Yasa mafarki nake ba!
Nayi salati cikin wara idanuna sosai da jin muryoyi mabambanta na tashi cikin kunnuwana, daga mutanen dake zagaye dani. A lokacin memory dina (is back on network) duk abinda ya faru, ya kuma yi musabbabin zuwan nawa gadon asibitin ya dawo ‘fresh’ a kwakwalwata.
Na yunkura zan mike zaune cikin fashewa da sabon kuka, sai naji an kamani an maidani kwancen.
“Koma ki kwanta, ‘relax Fa’iza, relax… ‘Main Hoon Naa… (I’m here now)! And I will be here for ever, I’ll not die and leave you… We are meant for each other!!!”
Wata tattausar murya ke fadi, cikin turanci mai gardi da taushin amo. Sai kuma dariyar Mama akunnena da muryar Momina na fadin.
“Ta gama suman, ta koma iya shegenta. Da dai ba ita din ce ba…”.
Muryar Walida, “Kai Momi! ‘She’s no longer the FA’EEZAH YOU KNOW… Na rantse tana son mijinta”.
Muryar Shu’aib, “Kaji Momi da wani zance mara dadi, ai mijinka-mijinka ne, kana son shi ko baka sonshi”.
Na daga kai a sukwane, na dubi wanda ke rike dani, kuma wanda nake kwance akan cinyoyinsa, wanda ke shafa min ruwan a fuska, wuya zuwa kirjina… FA’IZ (ABUBAKAR), FA’IZ BAMALLI NE, FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA…!
Mijina abin sona, sanyin idaniyata, cikon farin cikina… ‘The one that is always hunting my dream!!!
Makiyina, abokin fadana ada can, masoyin da babu kamarsa a yanzu…Wanda zaton guhewar sa a doron kasa kadai ke neman aikawa dani nima.
Mikewa tsaye nayi cikin wani irin zafin nama na rungume shi. Wata irin runguma kakkarfa, mai tafiya bisa umarnin zuciya da jagorancin gangar jiki, cikin kuka mai yawa wanda ya kasa tsayuwa daga idanu da zuciyata, amma wannan karon NA GODIYA GA UBANGIJI NE da ya kaddara zan sake ganin Fa’iz kafin Allah Ya dau raina. Zan rungume shi cikin jiki na kafin saduwata da Ubangiji na!
Sosai yayi min masauki a katafaren kirjinsa, ya rufe ni ruf da gaba dayan gangar jikinsa ya zagayeni da hannayensa, ba tare da la’akari da iyayenmu da kannemu dake zagaye damu ba, su din dariya suke suna karawa, har da masu yin tafi, cikin nasu farin cikin, da godiyar Ubangiji.
Na dago kaina na dube shi ina kuka, na shiga bugun kirjinsa da hannayena biyu.
“Don me kayi mana haka yaya Fa’iz? Don me? Me yasa ka tsoratani ka tayar min da hankali irin wanda zai iya sawa zuciya ta buga! Kasan baka cikin jirgin kace kana ciki kawai don ka tayar da hankalinmu? Eye Yaya Fa’iz me yasa? Me yasa?? Me yasa???”
Na koma na rukunkume shi da karfin gaske na cigaba da kuka kamar mai tsoron kada ya sake tafiya ya barni, ko wani al’amari makamancin wannan ya sake rabamu.
Baice komai ba, idanunshi ya rufe bai bude ba, ina iya jiyo bugun zuciyarsa mai bugawa da sauri-da-sauri. Wannan wata rana ce mafi soyuwa cikin ranakun rayuwarsa da ba zai iya fassarata ba, ranar da yake tsammanin har ya koma ga mahaliccinsa ba zata taba zuwa ba!
Ya rasa abinda zai yi ko zai ce da zai nuna dumbin farin cikin da yake ciki. Yau Fa’izah ce rungume da shi gaban BABA da MAMA, BABAN A.B.U da MOMIN A.B.U… Wata rana cikin ranakun rayuwarsa mai dumbin tarihi in ka cire ranar da ya karbi aninin zama cikakken matukin jirgin sama, da ranar daurin aurenshi da FA’IZAH A.A GIWA.
Duk dakin asibitin ya dauki tsit, bayan shasshekar kukana dake tashi a hankali a dakin da bugun zuciyar Fa’iz Abubakar. Abinda ya iya cewa a wannan lokacin cikin sassaucin murya, inka cire ni Fa’izar dake rungume dashi, babu wanda ya iya yaji a dakin, ni din ma don na kasance cikin masu karfin ji ne.
“FA’IZAH, ashe kina sona kike wahalar dani?”
Ya fadi tare da kai hannu ya dago habata, ya dubeni cikin ido. A hankali Baba Muntari ya zame ya fice daga dakin, Baban A.B.U yabi bayansa, Momi da Mama suma ficewar suka yi, Shu’aib da Yahya suma suka fice. Amma Walida da su Junior suna tsaye kyarr idanunsu na kallon soyayya mai dumbin tarihi cikin zuri’arsu. Kallo daya Yayan yayi musu, suka fice cikin murmushi da susar keya (It’s a show that they don’t want to miss). TAKORI.
Muka yiwa juna kirr da ido, kamar kowanne so yake ya karanto adadin kaunarsa cikin idanun dan uwansa. Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwarmu wadanda duka marasa dadi ne, kowanne kuma yana ‘blaming’ dan uwansa da shi ne SANADI. Amma a yau mun yarda mun amince haka rayuwarmu ta zo a rubuce babu wanda shi ne SANADI. Mu din da rayuwarmu gaba daya kamar wani rubutaccen KUNDI ne wato LITTAFI mai dadin karantawa da koyarda darussa da dama. MUhimmi shi ne na ‘YAN ADAM MU DAUKI RAYUWA DA SAUKI BAMU SAN INDA KADDARA ZATA KAIMU BA. ZA KA KI ABU, BAYAN WATA KILA ABIN NAN ALKHAIRI NE A GAREKA, ZAKA JARABTU DA SON ABU, ALHALIN SHARRI NE A GAREKA. DON HAKA NE IN ZAMU YI SO KO KI MU YI SU SAISA-SAISA. MAFI A’ALA SHI NE MU BAIWA UBANGIJINMU ZHABI A DUKKAN AL’AMURANMU NA DUNIYA BA WANDA MUKE SO KO MUKA JARABTU DA KIN SA BA!!!
Ubangijin da ya halicce mu shi ya halicci SO ya kuma halicci ki ya sanya su a zukatan bayinsa. Kamar yadda ya halicci komai mace da namiji (feminine and masculine) ya kuma ya halicci komai da kishiyarsa (opposite) dukkansu kuma halittar Allah ne da babu dan Adam da ya isa yayi yadda yaga dama dasu face UBANGIJIN da ya halicce su.
Mu karbi rayuwa a duk yadda ta zo, mu kasance cikin GODIYAR UBANGIJI.
***
Mintuna masu dama suka shude kafin Fa’iz, yayi magana. ‘It’s not my fault’ (Ba laifina bane). Akan me zanyi irin wannan mummunan ‘joking’ gareki har ma da IYAYENMU? ‘I missed my flight’, karfe goma na safe zan tashi nayi zaton na safe ne shi yasa na gayawa Walida da yaya Bashir zan taso goma na safe. A daren ranar kuma na kwana akan ‘internet’ ina gudanar da wasu muhimman ayyukana. Koko ince rai bata tafiya a lokacin da Ubangijinta bai kirata ba. Abu in aka ce miki da karar kwana to babu dabara. Idan kuwa rai bai zo wa’adinsa ba, ruwa da iska, mutum da aljan basu isa suyi ajalinsa ba balle abin hawa.
Wani irin bacci ne mai tsananin nauyi ya kwasheni bayan nayi sallar Asuba da yake ma banyi bacci ba sai da na bada faralin Asubahi gudun kada in kwanta ya wuce ni, dana idar na ce bari in dan kishingida zuwa takwas na safe in shiga wanka in wuce Airport. Wallahi shi kenan, nayi ta baccin da ban tashi farkawa ba sai karfe goma sha daya na rana.
Don haka da na tashi banji dadi ba, don na riga na fadawa Walida da Yaya Bashir na sake yin ‘booking’ na samu na goma na dare. Ina zuci-zucin in kira Shu’aib in gaya masa canjin da aka samu abokina Jeved yayi min waya matarshi Barya na labour in taimaka mishi inje in tsaya dasu a asibiti shi yana bisa aiki a Lusaka. Sai hakan ya janye min hankali na tafi garesu aka ce sai dai ayi mata ‘CS’ ba zata iya haihuwa da kanta ba. Don haka ina wajensu har karfe takwas na dare.
So ina komawa gida bayan an ciro mata yaron shi kuma Javed ya dawo, wanka kawai nayi na wuce ‘Airport’ karfe goma na dare muka taso zuwa Asuba muna Abuja, ban samu jirgi ba aka ce sai sha biyun rana kuma ban tsaya kiran Yaya Bashir ba kawai na biyo wani wanda muka sauka tare wanda shima Kaduna zai zo akazo daukarshi filin jirgin saman Abuja.
Lokacin da na iso Maigadi ya ce duk gidan suna asibiti, lokacin ne na kira Shu’aib yazo ya sameni. Da ya ganni sai ya rungume ya fashe da kukan da ban san dalilinsa ba. Shima Malam Amadu (maigadi) kuka ya saka yana fadin.
“Alhamdulillahi”.
A lokacin ne suke gaya min sunyi zaton ina cikin jirgin da ya fadi wanda dalilin hakan Yaya Bashir yayi hatsari, Hajjah ta samu paralysed, ke kuma kinyi dogon suma tun daren jiya har zuwa lokacin baki farfado ba, kina gadon asibiti.
Muka garzayo muka taho. Na ganki cikin wani hali daya bani mamaki wai a dalilina kika shige shi. Ina tantama har yanzu… Ina shakkah… I still doubt! Fa’izah tabbatar mini, kin fadi ne don baki so na mutu……kin fadi ne don kina son mu rayu tare ko akasin haka? Am I not dreaming..?.”.
Hannu na kai na rufe mishi baki, ‘before I start kissing him passionately’. Fatana ya yarda ni ce… ya yarda nayi nadama… Nadama irin wadda Ubangiji Yayi alkawarin karbarta. Na tuba nabi Allah na bishi… Na tuba na bi umarnin Allah! ‘He is the one I love today and always…
Burina Allah Ya barmu tare har zuwa karshen rayuwar mu. Mu rayu tare idan wa’adi yazo mu cika tare. Ina rokon Allah Ya cika min wannan buri… Yasa na rayu tare da FA’IZ rayuwa mai tsaho da nagarta…
Sauran al’amuran da suka biyo baya (unexpressable) ne. Wata sabuwar duniya ce kuma wata rayuwa ta daban da biro ba zai iya bayyanawa ba. Wadda daga ni har shi bamu taba tsintar kanmu a ciki ba sai ‘kintace’ wato (Imaginations) tun lokacin da muka fara kamuwa da son junanmu. Muke kissimata cikin mafarki da ido biyu, muke kintacen ta da ‘how deep it will be, how passionate, and how romantic! It’s indeed the pleasurable one, EVER!
Cikin wannan duniyar ne wadda bata kintatuwa ‘no matter how efficient the description of a WRITER’ wato duk kwarewar mai rubutu baki iya rubuta ta ba, muka kwashe awanni biyu, ban gaji ba, bai gaji ba, ZUCIYA da GANGAR JIKI kadai ke aiki a tare. Har sai da suka samu ‘healing’ na ciwon da ya kassara su, yayi ‘overwhelming’ Abubakar shekara da shekaru, ya kayar da Fa’izatu watanni uku. Ubangiji da Ya halicce mu, Shi kadai Yasan adadinsa a zuciyoyinmu.
Dr. Alkasim Bello, kwararren likita a A&E na asibitin da muke, ya kwankwasa kofar Nurse na biye dashi. Bai shigo ba sai da Fa’iz ya yi mishi izinin shigowa. Amma hakan bai sa ya rabani da barin jikinsa ba.
Murmushi Dr. Alkasim ya yi, “Darling didn’t die, Fa’izah will not die…”.
Maganarshi ta bamu dariya dukkanmu. Yayi rubutu a (file) dina ya rufe ya dubi Fa’iz fuska fal fara’a.
“Kana iya daukar amarya ku tafi Mr. Fa’iz, She’s o.k, is a normal shock. Allah Ya kara dankon kauna”.
Babu kowa a (reception) din cikin ‘yan gidanmu tabbacin duk sun tafi gida. Mukullin motar Baba yana hannunsa, don haka shi ke janmu zuwa Malali.
Tafiya sosai mikakkiya, don asibitin yana unguwar Rimi ne. Ina gefensa yana tukin cikin sukuni da kwarewa. Na lalace a kallonsa tamkar wani furen fulawa don kyau. Ubangijin da ya halicce shi ya suranta shi, ya kyautata halittarsa da haiba da kamala. Idan na dube shi kallo daya kaga nitsatstsen mumini mai kiyaye iyakokin Ubangijinsa. Wanda kuma ya dama, ya kutsa cikin ilmin zamani mai tsada da daraja. A goshinsa tabon Sujjadah ne, ya taru yayi baki sidik cikin nuna babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai russuna ga Ubangijinsa ba, Ma’abocin wata iri tsafta bayyananniya da ko cikin faratansa ya nuna. Komai nashi garai-garai kuma tsaf-tsaf kamar a lashe.
Babu abinda nake yi cikin zuciyata sai tasbihi ga Ubangiji na da Ya mallaka min wannan ‘giant-handsome’ a matsayin miji a gareni mai so na da kaunata ba. Idan bance nafi sauran mata sa’a ba to hakika ina cikin sahun masu sa’ar ta kowanne bangare a rayuwa.
Sautin Sheikh Mahmoud Khaleel Al-khusairi ke tashi a rediyon motar cikin Suratul-Ankabut.
Watakila jikinsa ne ya bashi kallonsa nake yi kamar zan cinyeshi, ya juyo a gicciye ya saci kallona. Murmushi yayi, wanda ya fadada shi har fararen hakoransa suka fito.
“Da yanzu wata na nan da lullubi aka, ta fara takaba”.
Na galla masa harara wadda ta fito ne hakikatan daga zuciyata, na dauke kai na mayar gefen titi.
“Na matsu mu isa gida, (am running at a speedly level) amma motar bata sauri. Na matsu inji dalilin da yasa makiyinka yake kokomawa mutuwarka, har ya sume dominta”.
Juyowa nayi na kalleshi na ‘yan sakanni, na sake maida kaina a titi cikin jin zafin maganganunsa. Na sadda kaina kasa, sai hawaye suka fito, suna diga akan tafukana.
Sanyin na’urar motar yayi min yawa domin har raba ke naso daga kofofin A.Cn. Ga sanyin da jikina yayi da kalamansa, suka hadu suka haifar min da zazzabi-zazzabi, na soma jin kaina a sama, ban bari mun hada ido ba, don bana so yaga hawayena.
Ya karya kan motar ya shiga layinmu, wannan karon yana tafiya ne cikin (slow-motion). Tamkar baya so mu karasa gidan.
“I’m hungry, yaya za’ayi kenan? Gashi nayi alkawarin bazan sake cewa ki dafe min wani abu ba, ‘above all’ kema din baki da cikakkiyar lafiya, kin jigata kin wujijjiga da mutuwar maigida ba zaki iya girkin ba ko na janye alkawarin nawa. ‘I still wonder’ dalilinki na damuwa da mutuwata maimakon kiyi farin ciki na baki duniyar ki sha sharafinki…”.
Wannan karon ma shiru nayi, banyi magana ba, hawayen ne dai suka ninka na baya.
“Insha sharafina, ko in shiga uku na?” Zancen zuci nake, ban san cewa ya subuto fili ya shiga kunnensa ba.
Yi yayi kamar bai ji ni ba, ko da gasken ne bai ji ni ba bazan iya sani ba. Domin cewa yayi.
“Kina jina? Na ce don mene kika damu da mutuwa ta?”
Har tsakar kaina naji shock, cikin kwanyar kaina naji kunya, wata irin kunya da ban taba jin irinta a rayuwata ba. Wadda ta haifar min da dabarbarcewa.
Ya sake maimaita tambayarsa. Wannan karon, tambayar tasa tana dauke da ‘intonation’ na ba da umarni kuma da gaske amsata yake bida, ko rai ya baci.
CIkin karkarwar murya da in-ina na ce.
“Uhm… uhm abincin yana… yana gida, na riga na dafa… ba sai ka sayo ba!”.
Dariya yayi mai hade da kallo daga can kasan ido.
“Shi kluma cefanen fa?”
Nima sai abin ya bani dariya, ganin ya saki daga daure fuskar da yayi.
“Tambayar da nayi miki daban take da amsar da kika bani Fa’eezah!. ‘Anyway’ jikina ya bani kinyi kewana, idanuwanki sun nuna, kwayar idonki ta fada, kazalika kasusuwan da suka yiwa cikakken wuyanki ado, suka kuma maida dara-daran idanunki lungu. Don haka ne na zamo ‘curious’ wajen son jin dalili? Dalilin da ya sumar dake don NA MUTU! Alhalin sanin kowa ne mutum yana murna ne da mutuwar makiyinshi…”.
Na katse shi cikin kosawa, “Indai cefane ne ai Shu’aib ya kawo, Ya’u ya sanya su a (kitchen) da (store) da firinji, don Allah ka rabu dani haka!”. Sai hawaye.
Dai-dai sanda ya sanya hancin motar cikin gate din gidanmu. Buzu ya bude bakin shi yaki rufuwa don murnar isowar Ubangidan shi lafiya. Ya sanya motar a ma’adanarta, ya kashe fitilunta amma ita motar bai kasheta ba.
Na murda mabudin motar don in fita, ko motsi ya ki yi. Na juyo a hankali na dube shi, da idanun bidar dalili. Har yanzun murmushi yake, ya ce.
“Cefanen? Guda nawa ne?”
Na ce cikin kauda kai, “To bude min kofar mana tukunna muje ciki kaga yawan cefanen da idanunka?”