ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 



Lokacin babu wanda bai zubar miki da hawaye ba don tausayin ki, haka dai muka ci gaba da rayuwa cikin jiran tsammani.
Da yake Allah maji roKon bawansa ne, Gagara misali, wata rana na shiga bandaki Ammin ku ta fita waje don yin rakiyar ‘yan dubiya da suka zo, Abban ku yana can masallaci _ kamar yadda ya saba yana karatun AlKur’ani. : Ina fitowa sai kawai na iske Aziza zaune kan gadon gsibiti ita kadai garau da ita sai dube_ dube take, cikin murna da doki na ce. – “Aziza na.Na fada cikin Karaji da doki, sannan na daga hannu sama na fara yiwa Allah godiya. Abin mamaki Aziza bata juyo ba bare ta . Lura da abinda nake yi, ita dai hankalin ta gaba daya yana kan Www.bankinhausanovels.com.ng robar igiyoyin da suke. jone jikinta su tabi da kallo tana mamakin yadda aka maKala matasu. Da sauri na zo gabanta na riKe hannayen ta, hawaye na zubo min na ce. “Aziza ba ki ganni-bane? Granny dinki ce – fa?” ~ Wani irin kallo na rashin’ fahimta ta bini da shi kamar tana so ta yi tunani, sai ta kasa, nan dai Allah Yataimaka tace. “Wace ke?” ‘ Murmushi nayi mai hade da kuka, na sake damKe hannuwan ta nace.

“Aziza Granny ce fa? Ko baki gane ni bane?” .
Dai-dai lokacin Aisha ta shigo dakin tana hango Aziza zaune da sauri ta Karaso gurin cikin murna, ta Ce.
“Umma ba dai Ammi na ta farfado ba?” _ Ta fada cikin Karaji. –
Itama binta tayi da kallo irin na rashin fahimta, bata ce da ita komai ba, haka ta Kura
‘mata ido ta kasa cewa da ita komai. Ta rike hannunta tana murna, ta ce.Ammi na baki gane ni bane? Ni ce fa”.


Shiru tayi har yanzu ta tsaya tana kallon mu daya bayan daya kamar tana so ta tuno wani _ abu, sai ta kasa.Aisha ta soma rudewa da ta shiga tambayata cikin kuka. “Umma, ko dai Ammi na ta dawo kurma ne?” Girgiza kai nayi, na ce, “A’ah,; tana _ magana don tayi min magana kenan sai kika shigo”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ta dubi Aisha ta ce, “Kema wace?”Ta nuna ni, ta “Ke kince min Granny,  Aziza, ita kuma ta ce miki Umma, ni kuma Ammi, to ita kuma wace? Ni kuma wanne ne suna na, Aziza ko Ammi? Ni fa ban san wace ni ba, ku kuma su wane?” Nan da nan tashin hankali mara misaltuwa ya bayyana a tare damu, muka shiga cikin rudani da fargaba, kan kace komai Aisha ta juya ta fice da gudu cikin kuka. Nima hawaye ne ya shiga zubo min, nan take naji tausayin Aziza ya kama ni domin tunaninta na baya ya gushe kamar yadda likita ya fada a baya cewa idan ba. a yi. nasara ba tunaninta zai iya gushewa na wasu lokaci,.idan kuma Allah Ya nufa zata iya dawowa cikin hankalin ta ba tare da gushewar tunanin ta ba. Kalaman likitan ne suka dawo min cikin kwanya ta, nan take hawaye suka shiga zubo min  fuska ta, sai kawai na ga Aziza ta sa hannu tana goge min hawayen, tace, Mene ya sa ki kuka? Wai ku din su wane * ne? Na tambaye ku ba ku bani amsa ba”. – Na bude baki da niyyar bata amsa kenan saiga Abban ku nan ‘da gudu tare da wasu Www.bankinhausanovels.com.ng
likitoci guda uku sun shigo dakin, yana zuwa ya yi sauri ya rike Aziza ya rungume ta yana kuka yana yiwa Allah godiya da Yasa ta farfado. Nan ya shiga cewa. Ammi na Allah na gode da Ya baki lafiya”.
Yana rungume da ita bayan ya gama murna ya sake ta ya raba ta da jikin sa ya shiga dubanta yana cewa. .Ammi na kin yi shiru baki ce dani komai ba, ko nima ba ki gane ni ba?” Binsa tayi da kallo, ta ce, “A ina kake kai kuma? Meye sunan.ka? Na ji ka ce min Ammi_ na, suna ne haka?” Murmushi yayi mai hade da kuka, ya shiga girgiza kai yana cewa. . “Ni ne Abban ki”. : “Abba”. Nan take murna ta kama shi da yaji ta ambaci sunan sa, cikin doki ya ce. so “Kin gane ni ko?” . Girgiza masa kai tayi, sannan ta ce, “A’ah, ni ban sanka ba”.
Tashin hankali ne ya sake bayyana a tare da shi ganin yadda ya gigice yasa likitocin suka ce damu muyi hakuri mu basu guri za su yi aikin su. Dole bamu musa musu ba haka muka ‘fito jikinmu babu Kwari, muka tsaya jiran ikon Allah, domin duk mun shiga cikin rudani.Sun dauki tsawon lokaci kafin su fito daga baya, can sai gasu nan sun fito. Muna ganinsu muka yi saurin miKewa daga inda muke zaune, muka yo gurin su a sukwane.
Abban ku ne ya ce, “Doctor lafiya dai? Ya ake ciki ne?” Ku kwantar da hankalin ku, babu damuwa, mun yi mata allura ta koma barci. Su za su iya shiga kai kuma muje zuwa (office) za muyi maka Karin bayani”.
Suka tafi mu kuma muka shiga ciki, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. Mun dan jima kadan muna jiran dawowar sa muji ya ake ciki? Sai gashi nan ya shigo cikin sanyin jiki, muna ganin shi sai muma muka Kara shiga cikin damuwa, domin bamu san da me ya ZO mana ba. Guri ya zo ya samu ya zauna hawaye cike. a idanun sa, kowannen mu ya shiga jero masa tambayoyi.
Cikin Karfin hali ya ce, “Aziza tana cikin tashin hankali domin likitoci sun ce ta manta dukkan tunanin ta na baya, ba zata taba iya tuno abin da ya faru da ita a baya ba, komai na cikin Kwakwalwar ta ya shude, ba zai dawo ba sai lokacin da Allah Ya tsara hakan, don su kansu sun ce basu da tabbacin tunaninta zai dawo ko ba zai dawo ba, saboda muguwar firgitar da tayi a lokacin da abin yake faruwa, hakan yasa abin ya taba wurin ajiyar tunanin ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don haka sai dai mu ci gaba da addu’a da zubawa Sarautar Allah ido, sun ce abin da muka koyar da ita ko muka ganar da ita shi yanzu da shi zata dauka”.
Gaba dayan mu sai muka sa kuka da yin Salati, muka bi Aziza da kallo akan gadon da ° take kwance tsabar tausayin ta da muke ji, yarinya Karama ta gamu da babbar Kaddara a rayuwar ta.
Zuba mana idanu ya yi muna ta kuka domin kasa cewa damu komai yayi, domin shima ya yi nasa kukan har ya gaji. Muna cikin haka sai ga Mukhtar nan ya zo shi da Mama, shi ne ya samu ya hakurtar damu ya nuna mana babu yadda za muyi sai dai mu rungumi Kaddara, haka Allah Ya_ shiryawa  rayuwarta da mu kanmu baki daya.°
Sai yammaci sosai sannan ta farka, tana bude ido babu wanda ta kira sai Abban ku.Abba!”.
Abin da ta fada kenan duk muka juya da muka ji muryarta, domin a tunanin mu ta gane mu, ta dawo cikin tunaninta. Haka kowa ya fara
– murna, lokaci daya muka hada baki muka ce. ““Ammi kin tashi ne?” a Har da Mukhtar, domin yana nan bai tafi ba.
Sai hankalin ta ya yi kansa, domin kafin ta kwanta dazu bata ganshi ba, kallon sa ta shiga yi sannan ta ce. “Kaima din Abba na ne?”
Gaba daya sai suka yi saroro suna kallon “ta, haka itama ta Kura masa ido tana son jin Karin bayani daga gare shi.
Ganin yadda take mana kallon tuhuma sai Mukhtar ya yi sauri ya ce.
, ammi ni (Uncle) ne, Uncle Mukhtar suna na, wannan Abba, ga Ammin ki sannan kuma ga Granny dinki”
Murmushi tayi ta ce, “Uncle din ku nawa ne?”
“Eh mana”. Ya fada yana murmushi”.
“To na gode. Ta fada ba tare da tayi masa murmushi ba. Hannu ya‘miKa mata kamar yadda suka saba a da can idan ya yi mata abu tayi masa godiya sai ya miKo mata hannu su tafa, shiru ya gani bata miko masa ba, sai jikinsa ya yi sanyi, tausayin ta ya kama shi, nan ya Kara tabbatarwa cewa bata iya tuna komai.
Haka ya mayar da hannunsa domin ya lura ba zata iya gane me yake nufi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan da nan labari ya bazu cikin ZURI’A cewa Aziza taji sauki, duk wanda yaji sai ka ganshi ya zo amma idan ya zo ya ga bata gane shi ba sai ‘su ji ba dadi, haka za su koma tausaya
mata, wasu kuwa sai dai su yi ta kuka. . Haka ta tsaya tana ganin kowa sabo domin duk ba wandata gane, dole tayi haKuri ta daina tambayar su wane su domin ance mata duk ‘yan
uwanta ne. .Alh. Jafar tunda ya ji ance Aziza ta _ farfado hanalin sa da na Hameed ya yi mugun tashi, domin jira suke su ji anyi sallama ance su fito ana tuhumar Hameed abinda ya aikata, don haka bai samu ya je asibitin ba domin yana cikin . Amma kuwa Haj. Asiya cikin tawaga ta bi ‘yan uwanta suka je dubiya, ta sani sarai bata ‘ gane kowa amma ta Ki gaya musu domin bata son ganin kwanciyar hankalin su, ba don komai ba sai don yadda ya mantar da Hameed da .Kudurin sa tun yana nacin har ya daina domin kullum sai yana bashi UZURIn Karya dole ya barshi bai je anyi masa bulalar bayau tsawon . wata uku kenan cif.
Bayan kwana uku da faruwar haka Alh, Jafar ya shigo gida da murna ya kira Haj. Asiya da Hameed yake fada musu ya samu labarin cewa Aziza bata iya tuna abin da ya faru da ita a baya, haka ya daga hannu ya yiwa Allah godiya a gabansu.
Suka bishi da kallo kamar tababbe, ganin irin kallon da suke masa ‘sai yaji wani. iri, kai — tsaye yace.
“Ba za ku hana ni murna ba domin addu’a nayi akan rufuwar asirin mu kuma allah Ya
_ karba don haka dole ne nayi murna, don haka ku shiga ku shirya muje mu duba jikin nata yanzu”.
Babu wanda ya yi masa musu, haka suka bar yaran a gida suka taho abin su. Www.bankinhausanovels.com.ng
A can asibiti tunda Aziza ta ci abinci a ranar ya shiga tayar mata da zuciya, amai take babu misaltuwa. Hankalin su ya tashi, suna tunanin ko wani abu ta ci ya tayar mata da zuciya.Ni kuwa tuni na rude hade da fargaba Allah Yasa ba abinda nake zato bane, haka nayi daki na nayi shiru.
Zaune muke muna jiran dawowar Abban ku likita ya kira shi, hira muke tayi ita kuma . Aziza ta sha magani bacci ya dauke ta. Bamu yi aune ba sai muka ga Mustapha ya shigo a. rude yana kuka, gaba daya miKewa muka yi muna jiran me zai ce damu?
Mukhtar ne ya fara tambayar sa da cewa, “Yaya me kuma ya faru naga kana kuka?”
Cikin uka ya mika masa ‘yar takardar da take hannun sa, ya ce. .
“Mukhtar wata masifar ce ta Kara samun mu gaba daya, duba takardar nan ka gani, likita ne ya ce min Ammi na dauke da ciki wata uku cif”.Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”.
Abin da gaba dayan mu yake fitowa daga cikin bakunan mu, miKewa nayi amma ban san lokacin da na koma na zauna ba. Gaba dayan mu babu wanda yaKara cewa komai, ‘sai tausayin kanmu da na Aziza da ya kama mu. Haka na mayar da kallo na gareta tana ta baccin ta cikin kwanciyar hankali, hawaye suka zubo daga idanu na.
Mustapha ya soma kuka kamar Karamin yaro yana cewa. “Ya Allah Ka tona asirin wanda ya janyo mana wannan tashin hakalin, Allah kada Ka barshi cikin nutsuwa da farin ciki”. “Amecn Ya Allah, Allah Ka saka mana”, Www.bankinhausanovels.com.ng
Cewar Mukhtar, haka duk muka yi jigum _ , babu wani mai iya cewa komai tsabar jin radadin abin da kunnuwan mu suka jiyar mana.
Sallamar Alh. Jafar da iyalansa ita ce ta janyo hankalin mu zuwa gare su, ganin mu duk a tsaye cikin yanayin tashin hankali su ma sai suka razana, da sauri ya Karaso cikin gurin ya yi saurin riKe hannun Mustapha ya ce. “Mustapha, me ya faru? Ba dai rasuwa Azizan tayi ba?” Cikin kuka ya rungume dan uwansa ya ce. “Yaya Jafar ba mutuwa tayi ba, amma a yanzu zan so ace: Aziza ta rasu domin ta samu nutsuwa akan wadannan masifu da suke ta_ faruwa da ita, daga wannan sai wannan. Wai_ likita ne yanzu yake fada min wai tana dauke da juna biyu na tsawon wata uku”,. Mutuwar tsaye Alh. Jafar ya yi, nan da nan ya shiga cewa.”Ya Hayyu ya Kayyumu!”. _
Abinda ya yi ta maimaitawa kenan a bakin sa.
Haamwed da yake gefe dora hannu biyu yayi akai yana salati hade da kuka, haka itama Haj. Asiya. – .
Ya koma gefe yana ta buga hannunsa a jikin garu, Mukhtar ya yi sauri ya riKe shi ya ce. .
“Hameed baka da hankali? So kake ka ji: ma kanka rauni ne?”
“Uncle.ka barni, bani da wani amfani a rayuwata tunda har…”. . Hameed ba zaka yi shiru da bakinka ba sai kana mana surutan banza!”
Alh. Jafar ya katse shi cikin hanzari, da sauri ya zo ya riKe masa hannu ya ce.
“Hameed, idan ba zaka tsaya ka kwnatar da hankalin ka ba zan hana ka zuwa nan gurin, baka ganin mu ma kullum hakuri muke yi? Yadda kake jin abin nan mu ma haka muke ji”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *