ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 



ya fito da tarin wani (files) ya zo ya ajje su gaban Sa, yaCe. . Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aminu ka zauna ka duba (company) na ne da tarin manya-manyan filaye na ka zabi duk abin da kake so na baka shi duniya da lahira matukar zaka bar wannan sirrin tsakanin ni da kai, hatta shi Hameed din ba zan so ya san wannan sirrin ba, kai ko babban (company) na kake so mutuKar zaka rufa min asiri to a shirye nake na baka shi yanzun nan zan saka hannu na mallaka maka shi duk domin kada ka tozarta min Hameed a idanun duniya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaro idanu ya yi yana kallon sa cikin mamaki, ya jinjina kalaman da yake masa magana. Tabbas yasan girman wannan Company din da suna da daukaka da ya yi a Kasar nan, domin da wannan komfanin Zuri‘ar nan take ji da shi, kuma nashi ne halak malak, babu kudin~ kowa, amma haka yake KoKarin ganin ya sama kuwa nasa Investment a ciki shi ne yake masa maganar zai mallaka masa a matsayin toshiyar baki. Nan take yaji yana son gasgata kunnen sa, anya kuwa yaji abin da ya fada masa? “Aminu ko baka ji abin da na fada maka bane?” Cikin sauri ya ce, ” Company?”

Eh shi nake fada maka matukar ka amince zaka rufamin asiri to wallahi a shirye nake na mallaka maka shi yanzu cikin shiri
Komawa yayu ya zauna yana ajje numfashi ganin yanayinsa a haka sai yaji ya fara samun natsuwa don haka shima saiya zauna
Bazan iya karbar wannan Company din ba domin ni kaina idan nayi haka na shiga cikin tuhuma
Na yarda zan rufa maka asiri don haka saidai ka bani dukkan gaba daya kananun Company dinka biyu dake lagas dana kaduna idan kayi min haka nima zan fi samun nutsuwa domin babu wanda zai lura da hakan idan har ka amince to nima na amince ka douko muyi yarjejeniya a yanzu Www.bankinhausanovels.com.ng
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar jafar cikin hanzari yace wannan ba wani abun damuwa bane na amince matukar maganar bata fito ba shikenan
Amman idan idan har maganar ta fito to dole ne ka kawo min abuna


Hankalinsa a tashe yake kallon hameed dake kwance a kan gadon asibiti tsananin tausayin yaron nasa da kaunar sa sune suka rufe masa idanu lokaci guda hameed yana kallon mahaifinsa ya kauda kai don baya son ganinsa domin ya dauki laifin hanashi sukuni da kwanciyar hankali duk ya dora masa domin daya barshi ya alfadi abinda ya aikata da duk hakan bata taso ba
Hameed ka cika kafiya da taurin kai ka kuwa san irin tashin hankalin dana shiga da ban ganka ba, ashe kana cikin garin ka gama rudar damu to shikenan yanzu aika huve tunda kaje anyi maka bulalar ko ya karasa fada cikin kasa da muryarsa
Runtse idanu yayi don baison ganinsa haka ya karaci bayaninsa baice dashi komai ba
Hameed ba daddy dinka ne yake maka magana ba ka rabu dashi
Kawu mai zance dashi bayan baya son na samu nutsuwa cikin zuciyata
Alh. Aminu ya daka masa tsawa, ya Ce, “Hameed kana da hankali kuwa? Kasan me kake fada kuwa? Mahaifinka ne fa?” .
Cikin zubar hawaye yace, “Kawu to me zan fada ban da haka? MatuKar Daddy yana so na ci gaba da rayuwa cikin walwala da farin ciki to ya barni na je na wanke kaina gurin su Abba, na fada musu cewa ni ne na cuci Aziza, idan sun ji su yi min dukkan abin da idan suka “yi min zai zamo sun dauki fansar abin da nayi musu. . .Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko kuma shi da kansa yaje ya fada musu cewa ni ne na aikata mata haka, tunda yanzu na dan fara samun nutsuwa cikin raina a gurin Allah na tsarkaka da laifin da nayi masa, don haka ya zamar min dole suma na samu abin da Zai janyo nayi (free) a gurin su”.
“Hameed baka da hankali, kana tunanin akwai wani uba ko uwa da za su iya yafe maka wannan laifin da tashin hankalin da ka saka su? Idan kana tunanin za su yafe maka to kayi Karya, gwara ka ja bakinka ka yi shiru tunda Allah Shi Ya yafe maka”. Cewar Alh. Jafar. Runtscme ido yayi yana KoKarin gyara kwanciyar sa hade da datse baki don zafin da yakce ji a jikin sa. .Da sauri Alh. Jafar ya zo zai riKe shi, ya yi sauri ya daga hannu alamar kada ya taba shi.
Saroro suka yi suna kallon sa don abin ya yi matuKar bashi mamaki.
Hameed ya ce, “Daddy duk abin da kake magana akai da gangan kake yin sa, ka sani Allah Bai yafe hakkin wanda aka zalunta, kawai son zuciya da son da kake min duk su ne suka rufe maka ido, kana kallon gaskiya kake kaucewa. –
Dadddy, idan ba ka taimaka min gurin Allah na tsira ba to me zaka yi min a duniyar nan?” Ya fada yana mai kafe idanunsa akan shi. Jikin su ya yi sanyi, aka rasa mai iya cewa komai cikin su.
“Kawu kai idan kana son na samu farin ciki tun dazu na fada maka komai kaje ka sanar da su Abba su sani tun da shi Daddy ba zai iya ba”.
“Hameed naji, ka kwantar da hakalin ka insha Allahu komai zai zo cikin sauki, muna son abi komai a hankali don mu_ samu zumuncin mu kada yaz0 ya samu tangarda, abin cikin kwanciyar rai da yardar Allah za mu dai-dai ta yadda za’a fahimci juna”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi kenan Kawu, ina jiran lokacin, amma fa bada dadewa ba. Ina son kafin a , sallame ni ku sanar da su don matuKar baku yi min haka ba to ni da kaina zan je na fada musu kamar yadda na kawo kaina kotun Musulunci — babu wanda ya sani to haka can ma zani ba tare da kun sani ba”.
Daga hannu ya yi ya dauke Hameed da mari cikin Kunar rai, sam ya manta a cikin jinya yake. Cikin kaushin murya ya ce. Ranar kuwa da na tsine maka, na fitar da kai daga jerin ahalina na har abada tun da baka son rufin asirinmu, bayan wannan abin duk dan kada ka tozarta nake yinsa”. ‘ “Haba Yaya, me ya yi zafi haka? Ko ka manta a kwance yake bashi da lafiya ne?” Huci yake yi kamar damisa, ya ce.
“Aminu ni yaron nan zai kawo wa Sakarcin banza don yana yin abu ina bin bayan sa? Zo mu tafi, Allah Ya bashi sa‘’a yaje ya yi duk abin da zai yi, ni Kuma zai ga wane mataki zan dauka akan sa”,
Yana gama fadin haka ya sa kai ya fice zuciyar sa na yi masa zafi, yana mamakin wai Hameed dinsa ne ya zama huka.
Alh. Aminu tsaye gurin sa yana bashi baki akan ya daina yi ma mahaifin sa taurin kai, ya bi abin a hankali shi da kansa zai san abin da zai yi.
Kuka Hameed ya fara yi, yace”Kawu ni kaina ba a son raina na fadawa Daddy haka ba, nayi masa hakan ‘ne don ya tsane ni ya barni nayi abin da ya dace. Hakika nasan saboda son da yake.min yake hana ni na je na fada, to amma ya za ayi na ci gaba da rayuwa da Kunci a rayuwata da hakkin da ba a yafe min ba? Don haka Kawu dole ne na fada musu idan ku ba za ku iya ba”. .
“Hameed ka bar maganar nan tun da mahaifin ka baya so, ka bari cikin ruwan sanyi zan yi masa dole da kansa zamu je gurin su mu fada musu”.
Farin ciki ya kama shi, ya ce, “Kawu na gode sosai, kuma don Allah ka bawa Daddy hakuri, na san ya yi fishi da abin da na fada masa”,
“Kada ka damu, zan ganar da shi kuma insha Allah komai zai zo cikin sauki”.
A ‘yan kwanakin nan kullum cikin tashin hankali muke a cikin asibiti, domin Aziza kullum cikin firgita take da yawan yin Kara sai
dai kuma yanzu sam bata son ganin namiji a gabanta ko ma wane, domin ta dinga shiga razana dole ya zamo mu mata da likitoci mata su ne muke kula da ita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka abin ya ci gaba da tsorata mu har muke tunanin cewa ko ta samu tabin hankali ne, bayanan likitocin suka yi mana shi ne ya soma kwantar mana da hankali na cewa yin hakan na nuni da cewa tunanin ta ne yake Kokarin dawowa, kuma cikin yardar Allah za ayi nasara. . Ban da addu’a babu abin da muke yi  kullum, sannan haka muke haduwa akan Allah Ya bayyana Hameed da batan da yayi.
Zaune muke muna hira domin samun labari’ mai dadi da muke yi gurin likitoci na cewa kada mu daga hankalin mu na rashin — tashin Aziza daga bacci na tsawon kwana uku, tabbas suna tunanin nasara ce domin hakan yana nuna cewa kwanyarta na diban hutu ne, kuma da alamu idan Allah Ya farkar da ita ta dawo cikin hankalin.ta domin sun taba samun hakan ya faru a cikin wannan asibitin.
Murna muka shiga yi don sai muke ji a ranmu kamar ma taji sauki. Kwanan Hameed goma sha uku da bata har yanzu bamu samu labarin komai game da — batansa ba, haka dai muka ci gaba da addu’a. Kwance nake kan katifar dake kusa da gadon da Aziza take kwance, lokacin ni kadai ce a gurinta nima na dan kishingida bacci ya kwashe ni.
Ji nayi ana kiran sunana hade da bubbuga ni, sai nake jin kamar a cikin mafarki. Ina bude idanuna kawai sai naga Aziza zaune , kusa dani, da sauri na murtsike idanuna ina kallon ta cikin kaduwa domin ban san dame ta ; tashi ba, ta dawo cikin hayyacin ta ko har ~ yanzu tana nan yadda take?
Rike hannuna tayi ta ce, “Granny ni ce kuwa? Shin mafarki nake yi ko gaske ne abin da ya faru dani? Shin me ya faru dani na ganni a asibiti?” _ Rudewa nayi, murnamurna kuka-kuka, na rike hannunta na ce. Aziza kin gane ni, ni ce ko?”
Hawaye ne ya ciko idanunta, ta ce, “Granny abin da ya faru dani ba mafarki nayi ba gaske ne ko? (Pleasc) Granny ki fada min don na gasgata abin da nake ji a raina”. “Shin Granny da gaske Yaya Hameed shi ne ya yi sanadiyyar zuwa na asibitin nan ko dai mafarkin nake yi?” Ji nayi gabana ya yi matuKar faduwa, hankali na ya tashi, na ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aziza me kike cewa dani ne? Fada min me kike son fada ko me kika gani_ cikin mafarkin ki?”
Hawaye ne suka shiga zubowa a idanunta, ta Ce.
“(Please) Granny na roke ki da ki fara fada min me ya faru dani don Allah, domin na – fara gasgata wani abu cikin raina. (Please) da gaske ba mafarki nake yi ba yaya Hameed shi ~ ne ya cuce ni ya bata min rayuwata har na zo nan ko kuma mafarki nayi?”
Dafe Kirji nayi na shiga salati, hawaye na zubowa cikin idanuna na ce.
“Hakika wani abu ya faru da ke Aziza, sai dai cikin mu babu wanda yasan wane ya yi miki wani abu”.
Kuka ta saka mai tsuma rai, nan da nan tayi sauri ta rungume ni ta shiga kuka tana cewa. Granny na shiga uku na lalace, yaya
-Hameed ya cuce ni, shi ne ya hakke min. Wayyo Allah Granny, ya cuce ni”.
Kara rudewa nayi na Kara kanKame ta nima ina kuka ina sakin salati, haka ta shiga kuka tana bani labarin duk abin da ya faru da ita.
Tun da ta fara dani labari nake zubar da hawaye domin tsabar kaduwa da tausayin abin da ya faru da ita, daga ni har ita kuka muke tayi, domin na rasa abin da zan iya cewa da ita. Haka Abban ku da Ammin ku suka shigo suka iske mu a cikin wannan halin.
Gaban su ne ya fadi da suka hangi Aziza kwance kan gwiwata, da sauri suka Karaso gurin, ya ce.
“Umma me ya faru da Ammi na?” :
Jin muryar mahaifin ta tayi sauri ta mike tana ganinsa da sauri ta zo ta rungume shi tana kuka tana cewa.
“Abba Ya Hamecd ya cuce ni ya Bata min rayuwata”.
Bambarekwai yaji kalaman nata, domin sam bai fahimci abin da yake faruwa da ita ba. Nan da nan ya ji shi wani iri tare da jin wani faduwar gaba ya zo masa. Sauri ya yi ya rike hannayen ta ya raba ta da jikinsa, ya dube ta sosai ya ce. Ammi na me kike cewa dani ne?” Kuka ta Kara sawa ta sake rungume shi, kallon sa ya mayor gare ni cikin rudani nima kukan ya gani wa yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
A rude ya ce, “Umma wai me ke faruwa ne? Shin Ammi na ta warke ne? Wai me yake faruwa ne? Ni fa na rude naji tana kiran Hameed, me Hameed din ya zo ya yi? Ko an ganshi ne?” Abba gani, dama ba bata nayi ba”Gaba dayan su suka juyo suka kalli bakin Kofar shigowa inda suka jiyo muryar sa.
Hameed ne tsaye bakin Kofar yana mai Kokarin shigowa. “Kada ka sake ka Karaso nan gurin Ya Hameed, na tsane ka, ba zan taba yafe maka

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *