ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Raihanatu ki nutsu ki bani hankalin ki, yanzu zan baki_ cikakken tarnhin = ryauwar ZURI’Ar ki da taki rayuwar gaba daya”Ji tayi dadi ya kama ta, ta ce.
“Yauwa Granny, shi yasa nake son ki, idan na gama ji ni kuma sannanzan fada miki burina da mafarki na akan ZURI’A ta”.
“Babu laifi, Allah Ya cika mana burinmu da mafarkinmu, yanzu za ki ji komai domin kema hakan ya zama izna gareki da mutanen duniya gaba daya, domin darasin dake cikin labarin”.
********
“Zuri’ar Alhaji Nasir Dan fillo Zuri’a ce da tayi fice da suna daga cikin tsatson su, asalin su mutanen Rano L.G.A ne, sannan Fulani ne na asali gabansu da bayan su, sun fito. cikin yankin fulanin garin ‘yan asali.
. Tun duniya na kwance Allah Ya yi masa tarin dukiya mai dumbin yawa tare da wayewa ta
duniya, wasu Turawa da aiki ya hada su tare har . aminci da sabo ya shiga tsakanin su ta harkar sana’ar auduga. Da girman sa sosai suka sa ya shiga makaranta wanda hakan yasa ya goge sosai ta yadda za su cigaba da gudanar da sana’ar su cikin kwanciyar hankali ba tare da wasu sun tsaya suna yi musu tafinta ba.
Basirar sa da Kwazo da amana da yake nunawa a tsakanin su, hakan ya Kara daukaka darajarsa gare su. Ana cikin hakan ne suka dauke shi zuwa Kasar su can Burtaniya, da da farko
_ anki yarda a gurin iyayensa domin surutu ne ya _ yi yawa cikin rigarsu wanda har ya kusa yin tasiri, amma kasancewar dagacin garin yasa baki dole iyayensa suka haKura suka saki lamarin tare
, da sharadin duk abinda ya faru ga dansu da shi za suyi kuka, haka ya amsa da eh ya yarda.
Sai da ya shafe shakara uku bai zo gida ba,
babu irin masifa da surutu da ba a yiwa dagaci
ba, daga baya ya ja.bakinsa ya yi shiru domin yasan babu abada zai faru da shi domin ba wannan ne farau ba don haka bai wani saurari Www.bankinhausanovels.com.ng
. hayaniyar su ba. Rana daya sai gashi ya dawo gida tare da tarin alherin da ya bawa kowa mamaki, da da farko kamar basu gane shi ba tsabar kyau da fari da yayi hade da gogewa irin na ‘yan boko, hakan ba Karamin dadi ya yiwa iyayensa ba ya zamo shima tamkar Bature ba dan Kauye ba.
Haka iyaycnsa suka rufe ido da kunyar su suka je suka ba ma dagaci haKurin irin abinda ya faru a baya can. Murmushi ya yi ya nuna musu babu damuwa komai ya wuce.
Bayan komai ya nitsa ne suka yanke : shawara da dansu akan’ da kansu za su je gidan * dagaci su nema masa auren diyarsa, bai yi musu musu ba sai dai ya nuna musu yana son komawa idan ya dawo sai ayi auren da duk wacce suka zaba masa.
Fau-fau suka Ki yarda, suka ce ba zai bar Kasar nan ba sai tare da aurensa, sai dai idan anyi ya barta ya tafi. Bai yi musu ba ya ce to, su dan bashi lokaci kadan zai yi magana da iyayen gidansa.
Lokacin da suka je gurin dagaci kan batun auren diyarsa da suke nema yaji dadi sosai,
lokaci guda ya amince, da yake dama yana da yara mata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dukkanin su Fulanince, dama basu fiye bawa junan su auren wasu ba idan ba Fulani ‘yan uwansu. ba, dama tun can da_akwai DANGANTAKAR AURE a tsakanin lardinsu. Lokacin da Alhaji Nasir yaji wadda aka zabar masa zai aura yayi mura sosai domin dama tunda yaji an ambaci auren yaran gidan dagaci ita ya kawo a ransa, domin ya santa tuntuni har ya taba kawo ta cikin ransa ga wadda yake son aura, amma sanin -wannan zamanin duniya tana kwance kai da baka da wani a aurenka na fari sai abin da iyayenka suka zaba maka yasa tuni ya yi watsi da hakan.
Lokacin da ya diba don komawa Burtaniya a lokacin ne iyayen gidansa suka dira a Rano suka ce sun bashi goyon baya yayi aurensa ya tafi da matarsa can su zauna, ai kuwa ba Karamin farin ciki ya dadu a zuciyarsa ba, cikin KanKanin lokaci aka daura auren Alhaji Nasir da Haj. Kubra. Bayan bikin su irin na Fulani da akai mai farin al’adu wanda hakan ya Kara burge iyayen
gidansa Turawa, domin dama haka suke da son al’adun gargajiya (culture). Bayan biki da sati daya suka dage Burtaniya abinsu.
A Kalla sai da suka yi shekara biyar cikin shekarun.nan sau uku suka zo ganin gida, lokacin da suka dawo Nigeria har sun samu Karuwa na yara biyu, Bara‘atu da Ja’afar, sannan ne suka dawo Rano da zama. Nan fa arziki ya ci uban na da, domin a cikin birnin Kano suka bude wani katafaren (Company) a cikin Kwaryar Kano na audiga, kuma shi ne yake kula da komai, sai dai tura musu da komai can suka daina zuwa shi ne yake musu komai.
A cikin ZURI’Ar mahaifinsa aka Kara aura masa wata mai suna Safiyya, suka zauna lafiya ita da Haj. Kubra lafiya lau, suka hade kansu zaman lafiya, babu wanda yake jin kansu. Sai da suka shekara hudu kowacce na haihuwa, nan fa
_ ya fara tara ZURI’A, a wannan lokacin ne mahaifiyar sa ta nuna tana sha’awar ya auri ‘yar Kanwarta da suke ciki daya. Nan fa Haj. Kubra da Safiya suka ta da hankalin sa akan su sam basu yarda ba, tashin hankali babu irin wanda ba su yi masa, shi kuwa ya dage akan cewa babu wanda ya isa ya hana shi bin UMARNI da mahaifiyar sa ta ba shi.
Wannan kurarin da ya yi bao sa sun saduda ba, nan ya ga abin nasu sai dada yawa yake yi, . haka ya sa su gaba ya ce suk wacce zata iya zama da shi to ta shirya don babu abin da zai faru a gurinsa. Nan suka hada baki suka ce masa bai isa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsawa yayi musu, ya ce wacce ba zata iya zama ba to ta tattara ta bar masa gidansa, suka ka da baki suka ce babu inda za suje su da shi mutu ka raba.
Haka ya koma Rano can wata riga ta asalin Fulani inda nan dangin mahaifiyar sa suke, nan suka gaisa da Gwaggonsa mahaifiyar Aziza da ake kira da Azi, wadda ita ake son hada su da ita. Da Kyar ta yarda suka gaisa saboda kunyar da take ji tashi, nan yayi KoKarin su hadu da Azi amma fau-fau taki zuwa don kunyar sa da take ji, sai ‘yar uwarta Kanwa gareta wadda suka zamo tamkar Hassana da _ Usaina, wato Raihanatu, ni kenan”,Sai a lokacin ta saki murmushi, ta kalli haana, tace Kina biye dani ko?”
Haana ta gyara zama, tace
‘ “Granny har da ke cikin labarin kenan? Gaskiya ina jin dadin labarin, to ya aka yi? Anyi auren kuwa sun zauna lafiya a gidansu? Gaskiya labarin yana min dadi”. Murmushi tayi ta ce, “Bini a hankali za ki ji komai, saurin me kike yi? A sannu za ki ji komai, ina yi miki baya ni ne dalla-dalla don ki fahimci komai yadda za ki gane kowa cikin Zuri’ar ki, ba kiji komai ba ke dai ki bani nutsuwar ki kawai”.
Ta cigaba, “Ba irin KoKarin da ban yi da Azi Innawuro ba taki yarda su hadu da Alh. Nasir amma taki, domin mace ce miskila da kunyar tsiya, ba wai son shi ne bata yi ba, tsabar kunya ne irin nata. Haka ya hakura ba don ya so ba, sai dai dani ya yi hira a ranar. Sai washegari da ya dawo aka tursasa dole suka hadu.
Cikin dan KanKanin lokaci magana tayi Karfi, magana ta yadu kowa yana sawa al’amarin albarka. Amma a bangaren iyalinsa kuwa haj. Kubra da haj. Safiya sun hade kansu sai rashin kyautatawa suke masa babu sassauci, haka suka hade kansu ya kasa sarrafa su, dole ya tattara su ya barsu don basu isa su hana shi abinda ya yi ra’ayi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka har Allah Ya yi aure tsakanin Alh. Nasir da Innawuro, aka dauko ta daga niga zuwa Kwaryar cikin birnin Kano, wanda tunda take .zuwanta garin Kano sau daya, sai gashi zama na dindindin ya kawota. Gata a lokacin ita ce Karama cikin su, duk sun girme mata, haka aka kawo ta cikinsu. – Tsananin kewar da muka yiwa junanmu shi ne ya hana ta sakewa a gidan, ga uwa uba wata tsangwama da take fuskanta gurin abokan zamanta, domin sun hade mata kai ta kasa sakin ranta, kullum cikin kuka take akan wai ita a mayar da ita gida, ba zata iya zama ba. Nan ya yi ta tausarta ta Ki, dole sai da ya zo ya sanar da mahaifiyar sa halin da suke ciki, da Kyar ta ce to idan dai ana son zamanta sai sai a kawo mata ni mu Zauna tare. .
Abin sai ya bata dariya, ta ce idan haka ne (a kwantar da hankalinta a yau zata sa a kawo ni matuKar zata saki ranta.
A. ranar kuwa nazo gidan, gani na tare da ita yasa ta saki ranta. Sai dai a lokacin zamana a gidan na fuskanci irin zaman takurar da take a ciki, amma tsabar haKuni irin nata da zurfin ciki bata taba fadawa kowa ba.
Haka suka hadu suna dada nuna mana Kiyayya da wariyar launin fata, gaba daya sai suka dauki tsanar suka mayar da ita kaina don sun ga ni ce nake tanka musu, sai dai ma tana bani haKauri. Dole tayi mini na daina kula su don bana son ganin bacin ranta, domin ita dama haka take da haKuri da rashin son tashin hankali. Ana cikin wannan irin zaman Allah Ya
bawa Innawuro ciki mai tsananin wahala, domin ta sha baKar wahala kamar ba zata dore ba. Nima na rasa nawa kwanciyar hankalin ganin ‘yar uwata tana cikin damuwa da wahala, a wannan lokacin har gida sai da aka mayar da ita da ciwon ya yi tsanani.
Cikin ikon Allah da cikin ya yi Kwari sai gashi ta ware, sannan aka fara Kokarn Www.bankinhausanovels.com.ng
komawarta gidanta. A wannan lokacin Baffanmu ya ce babu inda zan koma, nayi zamana saboda manema na suna ta damuwa akan yaushe zan dawo? Kuma girma na ya yi yawa. A dole na hakura na dawo na tsayar da wanda nake so a aurar dani.
Babu yadda na iya dole ina kallo ta dawo ita kadai, satin ta daya saiga Goggo Hanne (wato mahaifiyar Alh. Nasir) ta zo gidanmu, ta ce na hada kayana na koma Kano gurin ‘yar uwata.
Murna gurina kamar na zuba ruwa a Kasa na sha, babu yadda Baffa ya iya dole ya hakKura na dawo gurinta. Nan na Kara samun labarin wani sabon takura da kishiyoyinta suke mata.
A ranar sai da muka rabota da su domin babu wacce na ragawa a cikin su, dama kuma suna jin shakkata domin tun da na dawo gidan kishin ya koma kaina har Allah Ya kawo lokacin haihuwar ta, ta haifi da namiji mai kama da ubansa fitik, don duk cikin ‘ya’yan sa babu wanda yake da (sananin kama da shi irinsa.
– Murna a ranar: tamkar akansa ya fara samun haihuwa, wanda hakan ya dasa tsana da Kiyayya akan wannan haihuwar.
Ko kadan Alh. Nasir baya iya boye murnar sa ta haihuwar yaron, ranar suna aka saka masa suna Mustapha.
Shekarar Mustapha biyu a duniya a lokacin ne Baffan mu ya matsa min akan dole sai na baro nan na dawo gida, ya gaji da masu yi masa maganar aure na. Wannan karon haka muka hakura na dawo gida cike da kewar ‘yar uwata da dana Mustapha.
Maganar bikina ta kankama, har an fara shirin biki wanda zan aura ya ce ya fasa, ni dai nasan ba laifi nayi masa ba dole aka nemi sanin dalili aka rasa, haka aka hakura dole. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da Baffana ya zaci ni ne na Ki shi, wasa gaske har mutum uku suna sake fitowa rimi-rimi sai magana ta rushe. Baffa ya shiga damuwa, Alh. Nasir da kansa ya zo ya roki Baffa ya barni
– na koma can ko mijina a can yake da Kyar ya yarda don dai babu yadda zai yi ne.
Lokacin da na dawo nan na iske ‘yar uwata Innawuro na dauke da ciki na biyu wanda sam
bata wahala kamar wancan ba, haka murna ta kama ni domin dama ni da za a barni tare da ‘yar uwata mu rayu guri guda da haka ya fi min dadi.
Wannan haka yake itama a gurinta, domin idan ina tare da ita ta fi jin dadin gidan da kuma samun sukunin tsangwamar da take samu gurin abokan zamanta, domin har yanzu sun ki su barta ta sake a cikin gidan su, kuma suna bakin cikin zamana a gidan, domin babu abin da nake ban Innawuro tayi da kanta, komai ni ce nake mata na hidimar gida da na yaro wanda ya danganci na mijinta ita ke yi da kanta, su kuma hakan na Kona musu rai. Daf da cikinta ya kusa isa haihuwa lokacin
abokin Alh. Nasir ya fito za’a yi mana aure, an
gama shirin komai za ai biki ranar da Innawuro
ta haihu ta haifi diya mace, a ranar muka samu
labarin Allah Ya yiwa Alh. Kabir rasuwa,
hankali na ya tashi har na fara tunanin ko ba zan – taba yin aure ba daga wannan sai wannan.
Ranar suna aka sanyawa jaririya suna Maryam, lokacin ‘ya mai kama da uwarta fitik kamar an tsaga kara, haka muka wanzu cikin murma da kuma jimamin rashin da muka yi na Www.bankinhausanovels.com.ng
Alh. Kabiru, babu wanda bai tausaya min ba, amma ni samun Maryam shi ne ya Kara dauke min damuwar, tun daga lokacin na fara fitar da rai na akan aure. Mustapha na da shekara hudu Maryam na – da shekara daya a duniya Innawuro ta samu ciki wanda tun daga samun sa take cikin matsala, ga kuma laulayi na Kin Karawa, domin kullum tana cikin larura, dole yasa aka cire Maryam daga shan Mama ganin itama ta fara yin rashin lafiya. ‘Kullum muka zauna ni da ita ta dinga yi min magana akan cikin nan, da kuma cewa. “Rehana anya kuwa wannan cikin zai barni na rayu da ku? Domin tunda nake ban taba daukar ciki mai wuya haka ba. Idan har na mutu ki daure ki kular min da Maryam da Mustapha, ki riKe su tamkar yadda za ki riKe yaran da kika haifa a cikin ki, bana so ki bar su hannun su Saude, domin ba za su riKe su tsakani da Allah ba. Domin na fuskanci tsanar da suke min ita ce ta koma kansu idan har na haifi wannan cikin shima ki hada ki riKe, domin ji na nake kamar rayuwata ta zo Karshe.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG