ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

             Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ganin yadda ZURI’A ta soma yawa farin ciki yana ta samuwa a cikinta yasa Alh. Nasir yin tunanin yiwa yaransa gini yadda za su hadu guri daya har Karshen rayuwar sa, don baya son ya ga abin da zai raba kansu. Don haka ya samu Katon fegi (wato fili) iya ganinka ya ce anan yake son ya gina ma zuni’ar sa gidaje inda za su dunKule guri guda har zuwa lokarin da kowa zai yi nasa iyalin suma su zauna ciki. Lokacin duniya na kwance, ga filaye nan ko ta ina, kuma gashi babban mutum da suke da alfarma a wannan gwamnatin, don haka ya zuba kudinsa sosai ya samu abin da yake so don har matansa mun fara yi masa surutu ya ce mu dai
mu barshi, yasan abinda yake, kowa ya zo ya ga filin sai ya girgiza kai.Haka aka fara gini iri daya har gidaje  sama da sha biyu, kuma duk tsarinsu iri daya, sai dai guda daya da ya bambanta da sauran wurin girma. Nan ya fara gaya mana cewa gida ne zai . gina tunda yara maza har mata kowa ya dawo gurin da mazajen su, wanda kuma ba su yi aure ba gashi nan guri yana jiransu. Kowa ya shiga nuna murnar sa yiwa Allah godiya ganin inda aka tanadar musu don rayuwa guri guda. Tunda aka yi KoKarin daina nuna wariyar daki da daki sai rayuwar tayi dadi, kowa ka gani yana farin ciki da abin da dan uwansa zai samu. Soyayya da Kaunar juna ya gama kewaye zuri’ar, babu wani mai kuka da dan uwansa.

Nan-ma ya je Kaduna ya kara gina wasu gidajen masu tarin yawa, duk don yaransa da ‘yan uwansa. Tarin ariziki dai na ko maye Allah Ya bawa Alh. Nasir, sai dai fatan samun na labira shi din ma a zahiri kowa yana hango masa  Shekaru biyu da gama ginin ya tattara kan_ZURI’Ar sa guri ‘guda, shima yana cikin su, _ kowa da gidansa a ciki mata da maza., Burin sa  ganin zuri’ar sa guri guda ya cika; don haka ko. da ‘yaushe: yana tare.da su : idan ‘ya.fito daga.gidansa ya :ga-farin ‘

gidajen . ‘ya’yansa sai ya shiga farin ciki da yiwa Allah godiya da yayi masa arzikin yara da na dukiya, yana fatan Allah Ya hada kansu Gidaje ne ‘a jere wasu na‘kallon wasu, ko ’ da yaushe Alh. Nasir -yana tare. da jikokin sa a falon sa suna ta Www.bankinhausanovels.com.ng zuba hira, don a-lokacin yana da ~ tarin jikoki sun kai kusan goma. Babban..wanda ya yi fada da farin jini shi ne Hameed… – -. +Kullum burin Hameed Allah. Ya bashiKanwa mace, amma har yanzu shiru domin Kannen sa duk maza ne a cikin-family din, duk lokacin da ya tambayi kakansa cewa shi fa yana
-son a haifo masa Kanwa mace sai ya ce. ya kwantar da hankalin sa gashi nan iyayen sa – * kwanan‘nan za su haifa masa duk Kanne mata Lokaci guda aka yi haihuwa hudu duk – ” maza ne, nan fa Hameed ya yi ta rigima wai shi‘bai ga mace ba a ciki, duk Kanne maza aka yi. : Masa.Hatta’ mahaifiyar. sa haj. Asiya itama — namiji. ta haifa, sai Haj. -Aisha .ce.-matar:. . Mastapha ita ce kadai a cikin su bata haihu’ba.a tsokane ‘Asiya. tace, Abdulhameed ka: kwantar da hankalin. ka, kajegidan Ammin ka. Aisha ita ce zata haihu, sai ka  mata ta haifo maka kanwa mace” Www.bankinhausanovels.com.ng _Abinka da yaro da kuma abin da yake so, :nan kuwa tayi ‘masa hakan ne don–ya yi mata ‘ shira daga rigimar da yake damunta da shi. Yana fita daga gidan kuwa bai zame Ko’ * . ina ba sai gidan Ammin sa, nan ne ya iske mu ni da Aisha da Mustapha muna zaune a a falo muna ‘. hira, sai gashi nan ya shigo.  Cikin harshen’ Fulatanci. nayi. masa’ ‘ Magana, na’ce ya zo gurina, Da. yake lokacin. -munayi musu duk sun iya sosai, sai ya make kafada ya ce shi ba gurina ya zo ba, gurin Amminsa ya zo, duk sai muka sa dariya.
Sai ta kira shi, ya zo jikinta ya kwanta yana taba tudun cikinta. Ta ce, “Hameed me kake so na baka ne? Oya fada min”. “Ammi baby girl nake so ki haifo min na samu Kanwa, Mama ce ta ce na zo gurinki na fada miki ki haifo min baby girl tunda su basu_ -haifo ba Dariya muka yi gaba dayanmu, domin abin nashi gwanin dariya, nan ta ce. To Hameed, kai tayi min addu’a idan kayi sallah, Allah Ya sauke ni lafiya na haifo maka baby girl din da kake so”. :
Haba! Nan da jin ta fadi haka ya shiga murna yana tsalle wai za a haifa masa baby girl, bai jira kowa ba ya juya ya koma gida a guje ya – fadawa Maman sa. .
Tun daga ranar kullum Hamecd sai ya zo gidan wai ya duba ko an haifa masa baby girl dinsa, lokacin yana da shekara shida a duniya. Jin shiru baby bata zo ba ya fara nuna damuwar sa, lokaci guda ya dauke Kafa ya daina zuwa, a cewar sa ya yi fushi tunda Ammi ta Ki haihuwa. Nan ta shiga nuna masa lokaci ne bai yi ba, ya Kara haKuri. Ya ce, “To tunda haka ne zan dawo gidan na jira har sai kin kawo min babyn”Gudun fitinar sa yasa ta ce masa to, nan ya juya ya koma gida ba jimawa sai gashi da kayansa tili a hannu wai ya dawo gidan gaba daya sai lokacin da babyn ta dawo zai koma .gidansu. Duk wanda yaji labarin sai yayi dariya ya jinjina rigimar Hamecd.
Ganin da gaske yake nan Aisha ta shiga addu’a Allah Ya bata diya mace don ta cika ma Hameed burinsa, duk da kuwa itama burinta kenan haihuwar diya mace. Kullum idan ya tashi babu abin da zai tambaya sai cewa, “Kin haifi babyn nawa?” Sai ta ce a’a,Www.bankinhausanovels.com.ng addu’a ce baya yi sosai idan yayi sallah. Sai ya ce, “Eh haka ne, jiya sau haka nayi addu’ar”. (Ya nuna yatsun sa guda biyu) Tayi murmushi ta ce, “To dinga yi sau da yawa zaka ga na haihu lafiya, na kawo maka baby girl din taka”.Nan zai shiga murna, yace “Tam”.
Cikin yardar Allah wata Alhamis da daddare Allah Ya sauki Aisha lafiya, ta haifi Katuwar ‘yarta mace jajir da ita, lokacin Hameed yana bacci bai tashi ba. Cikin KanKanin lokaci labari ya iske ko ina cikin Zuri’a; tun daren aka cika gidan da mura.
Aisha ta yiwa Allah godiya da Ya cika mata burinta Ya bata abin da take son samu.
Bayan an dan nitsa ne nan aka shiga taya Hamecd murna ya samu abinda yake so, ba a — tashe shi ba sai da garin Allah Ya waye tangaran, lokacin ne ya farka. Kukan baby din neya tashe shi, zumbur ya mike ya ce.Lah! Ammi kin haifi baby girl din ne? Don jiya na yi miki addu’a da yawa sosai”.
Murmushi tayi ta ce, “eh mana, ai tun jiya kana barci Kanwar taka take ta neman ka baka tashi ba, shi ne yanzu ma take kuka da bata ganka ba”.
Dariyah ya saka yana kallonta, ya ce, * “Lah! Ammi dama ta sanni ne?” .
Gaba daya dariya gurin aka saka, nan ya shiga murna da rawar Kafa wai shi a bashi ita ya dauke ta, nan dai aka taimaka masa ya dauke ta
ya shiga murna hade da yin shirmen sa na yara.
– Haba! Abin nema ya samu gurin Hameed, sam bai son abin da zai raba shi da ‘yar Kanwar sa, ko da yaushe yana like da Ammin sa, da ta fara kuka zai tambayi me aka yi mata take kuka? Haka zai ce a bashi ita ya rarrashhe ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka dai ya zamana shi ma ya zama dan raino, don haka zai zauna ya tanKwashe Kafaa’ dora masa ita ya riKe, da ta soma kuka zaice karbe ta..
Ranar da Alh. Jafar-ya zo ganin yarinyar lokacin ba ya gari akai haihuwa, da ya ganta zai tafi saiyace. — Hameed, ai sai ka shirya mu koma. gida ~ tunda anyi maka abinda kake so”Ya tubure ya ce ai shi babu inda zai tafi, ya dawo gidan Ammi tunda ita ce ta haifa masa baby girl, ba zai koma gidan Mama ba tunda ya_~ ce ta haifo masa baby girl ta Ki. –
Dariya aka yi gaba daya domin shirmen Hameed din ko yaushe gaba yake yi, hakan yasa kowa yake son zaman sa a gidan domin yana nishadantar da mutane.
To idan na kenan na fadawa maman taka haka?” Ya gyada kai alamar, “Eh”’ Haka nan kuwa akai fafur ya ki komawa don haka dole aka barshi zuwa kwana biyu, ana tunanin da kansa zai nemi gida.
Ranar suna jaririya ta ci sunan margayya ‘yar uwata Aziza, mahaifiyar sa. Ni ce na ce a saka, da shi sunana yace na ce masa a’ah gaba a saka ni.
Ni da kaina na ce kada wanda ya boye mata sunanta, kowa yana kiranta da haka domin zan dinga jin dadi ina yawan tuna ‘yar uwata.
Haka kuwa aka yi, Aisha ce kadai ke kiranta da Ammi na don alkunya, haka sauran surukan amma cikin yara kowa da sunanta yake kiranta, ni kuma nafi son haka, dole sauran iyayen ma maza suke kiranta da haka. Abin kamar wasa Hameed Kememe ya Ki gidan su, dole haka aka haKura ya dawo gidan
gaba daya. Tun daga nan ya zamo dan gidan, har a zuwa girman sa, Amma kafin nan kusan kullum da shi ake rainon Aziza, idan Aisha tana aiki shi ne yake – zaune yana kula da ita. Wani ikon Allah ‘ya tana girma kamanninta yana fitowa sak da na mai sunanta, tamkar ita ce ta haife ta. Iko ne na Allah, babu abinda ba ya iyawa tabbacin Shi ne Yake da komai a hannun sa. Tsananin shakuwa da Kauna gami da sabo . shi ne ya Kullu tsakanin Ammi da Hameed da Kanwar sa Aziza, don yadda suke a yanzu ko Www.bankinhausanovels.com.ng mahaifiyar sa basu shaku da ita ba kamar suka shaku da Aisha. – Kowa ya yi farin ciki da hakan domin shi _ wata rana ma mantawa yake da zmaman sa, haka yake jinsa cikin wani sabon duniyar. . Azizas haka ta soma wayo, babu wanda ta fi sani a rayuwar ta daga Ammuinta sai Hamecd dinta. Haka yarinya ta taso da karsashinta da komai, kowa yana son ta domin kaf cikin su ita kadai ce ;ya mace karama. Haka kowa ya dauki son duniya ya dora shi akan Aziza. .
Kullum gidan cike yake da yara, cikin su babu wanda ya isa ya taba ta sai hameed ya bashi dama. Idan kuwa aka samu wani abu na sabani ya shiga tsakanin su, to ranar baka isa ka ga Azizan sa ba, don ko Kofar gidan ba zaka zo ba bare ka shiga gidan nasu.
Haka yaran za su ta kawo masa (sweet) daya nashi daya na Aziza, duk wanda bai kawo na Aziza ba to ranar ba za ayi wasa da shi ba.
Lokacin da Aziza ta cika shekara uku haka tayi wayo da surutu cakwai kamar kanari, gata ‘yar dabas a Kasa, sai dan banzan wayo da surutu. °
Tun tana Karama Allah Ya dasa mata kyau, wayon ta da surutun ta shi ne ya Kara mata farin jini har sai da ta zo ta zarce farin jinin Hameed. Ita kuma tunda Allah Yasa tayi Kafa ta –
, zamo bata son zama, kullum ta shiga wannan gidan ta fito wannan, haka ZURI’A gaba daya ta
_ dauki son duniya ta dora shi akan ta. Kowa so yake ta zo gurinsa, kuma duk wata fita da iyayenta maza za suyi sai an kawo mata tsarabarta daban. Duk ranar da Hameed ya dawo daga  makaranta bai ganta ba haka zai ta da hankalin sa ya fita neman ta gida-gida har sai ya nemota sannan ne hankalin sa zai kwanta. Nan zai ta yi mata fada yana cewa ta daina fita yawo, idan ba haka ba zai daina kawo mata (sweet) daga makaranta. Haka zata ce masa ta daina, gobe kuma sai ta sake. ° Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka wata rana ta faru lokacin Mukhtar ya — zo ya fita da Aziza suka tafi yawo har lokacin dawowa daga makarantar Hameed yayi ya dawo – gida bai ganta ba, ya shiga duk inda yake tunanin zai ganta bai ganta ba. Bayan an fada masa ga inda suka je haka ya je ya tsaya da (uniform) bai cire ba ya tsaya bakin get yana jiran dawowar su yaji shiru, da yake dama shi din dan shagwaba ne nan ya samu guri yana kuka wai Azizan sa.
Haka ya zauna yana kuka, nan ya hangi motarsu ta dawo, nan ya hangi Aziza ta fito da — gudu daga motar ta zo ta rungume shi tana tambayar cewa. — “Yaya Hameed me aka yi maka kake kuka? Ko Ammi ce ta dake ka?” Ture ta yayi ya ce, “Ba ke’ce na ce ki daina fita yawo ba sai ina nan mu fita tare, kin ce kin daina sai kuma gashi kina tayi”. Mukhtar ya ce, “(Sorry) Hameed, laifin (Uncle) ne ba na Ammi na bane, shiru ka daina. _ kuka tunda mun dawo”.
Nan ya share hawayen sa yace”To (Uncle) nayi shiru”.Ya sa hannu ya goge hawayemn sa, sannan ya mika hannu zai riko Aziza, ta ture masa hannu wai ita tayi fushi, ta wani make kafada.
Mukhtar ya nike haba, ya ce, “Ammi na ya haka? Kin manta da Yaya Hameed dinki ne? Baki ga akan ki yake kuka ba da bai ganki ba? Oya maza bashi hakuri”.
Turo baki tayi gaba, bata ce komai ba sai ta miKa masa hannu wai ya riKe ta su tafi. Dariya da mamaki ne suka kama Mukhtar, ya jinjina irin tarin Karancin shekarunta sai wayon tsiya da yin abu kamar ‘yar shekara goma. Anan dai suka shirya ta dalilin sa.
Tsananin shagwaba da rashin kwaba da Sangarci gurin Hameed ba a magana, domin baya
yin komai sai abinda ransa yake so, don haka baci yake yi son ransa ana biye masa, domin abin da yake na shagwaba Aziza ma bata yi tsabar gata da yake samu ta kowane bangare na iyayen sa.
Alh. Nasir yana matuKar farin cikin ganin yadda ‘ya’yansa suka hada kai guri guda suna zumuncin su yadda yake so, hakan yasa ya Kara gina musu wasu gidajen a can Kaduna, ganin
_ wasu suke ne da manyan kamfaninsa a can, don haka yadda ya gina na Kano haka ya gina tsantsarin su daya komai da komai, don haka ya ce, ko da wasu za su koma can ya kasance kowa yana da nashi a can, don bai son ya ga ya raba kan yaransa ta kowane fuska. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kullum burinsa akan yaransa shi ne su — hada kansu guri guda su yi zumunci kada su bari wani ya zo ya shiga tsakanin su har a zo a raba musu zumuncin su. Sau da yawa haka zai hada su yara da mu iyayen su yana ta yi mana nasiha akan zumuncin Allah.
Aziza na da shekara biyar aka yi mata Kani mai suna Nasir, a lokacin ne ma aka haifi Muhammad Kani na biyu ga Hameed. Sannan sai
a shekarar Allah Ya bama Maryam haihuwa, ya bata da namiji, ta yiwa Mustapha takwara, wato Ya Abban ki. Sannan kuma a wannan dai shekarar Murja matar Alh. Aminu dan wajen ‘Haj. Saude itama ta haifi da namiji mai suna Sameer. : – In taKaita miki a shekarar nan dai sai da – kusan duk yaran. mu suka haihu, a Kalla cikin shekaru biyu sai da muka yi jikoki sun kai bakwai, kuma duk maza, mata biyu.
Amma bayan shekara daya sai da muka rasa mutum uku, cikin su na farko Kabir wanda yake bin Hameed, sai Nasir Kanin Aziza, sai kuma Fiddausi ‘yar wajen Hajara. Shekarun Aziza goma a duniya lokacin Allah Ya dauki ran Alh. Nasir, rasuwar da har yanzu bamu mayar da gurbinta ba, tsayawa baki labarin irin tashin hankalin da muka shiga ba zai yiwu ba, domin kowa yasan mun yi rashin babban bango.
Ya je wata Umra ne cikin Azumi yana dawowa da sati biyu Allah Ya aiko masa da ciwon ajali, wani zazzafan ciwon ciki ne ya

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *