ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

               Www.bankinhausanovels.com.ng 



ZURI’A DAYA CHAPTER

Cikin wani irin yanayi yake mata magana, ya ce. Matar daga ina haka? Kamar kuwa kin san ke na fito ko zan hango ki sai gashi kuma na ganki”. Tayi murmushi ta ce, “Ba wani nan, don ka ganni ne yasa ka ce haka. To daga gidan rasuwar nan nake Haana ta hana mu sakat shi ne Ammi ta ce na zo gida da ita mu zauna ko tayi barci, don taga alamun fita kawai zata yi a gurin, gashi ta ishe mu da surutunta da baya Karewa, don ita ba zata gane wane hali ake ciki ba. Kuma nima dama na gaji, ji nayi kai na ya fara ciwo shi ne nake son mu koma gida mu dan runtsa kafin su dawo, gashi kuma rana ta soma takewa”.
““(Okay) nima ban jima da dawowa daga gidan ba, don bana son hayaniya. Oya to muje na raka ku gidan mana”, A’ah, da ka ma barshi mun Karasa, kaima kaje ka huta”.


Bai bata amsa ba ya sa hannu ya dauke ki ya saka ki a kafada suka jero suna hira, ke kuwa kin fara surutunki kafin ku Karasa har bacci ya dauke ki. A haka ya kai ku har Kofar gida, nan ya tsaya yana janta da hira har ta soma gajiya, nan ta ce masa ya miko ki taje ta kwnatar dake Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sauri ya mika mata ke, sai da yayi wayon da ya hada hannunsa da Kirjinta, sai tayi kamar bata san yayi ba, don ko kallon sa bata yi ba. A tunaninta cikin rashin sani ne, amma tana ‘daga ido suna hadawa sai ya sakar mata ~ murmushi, nan take taji wata kunya ta kama ta, ta dai dake ta ce. .
“Na gode, kaje abinka zamu shiga don na fara jin kaina na sara min”.

Ya yi murmushi ya. ce, “Shi kenan ku shiga, sai anjima din, idan kin gashi na shigo muyi hira”.
“(Okay) babu laifi, amma kai ma da ka koma gurin makokin don kowa yana can kar ace  baa ganka ba”.
“Kai share kawai, nima baccin nake ji, . idan na tashi na je”.
“Shi kenan sai anjima, bari mu shiga naji hannuna ya fara sagewa, kasan Haana da nauyin tsiya”. Ta fada tana murmushi.
Shima murmushin yayi ta juya ta shiga, ya bita da kallo har sai da ta shige ciki, nan da nan ya Kara dimaucewa da Kuanarta da sha’awarta, domin kasa iya daga Kafarsa yayi, haka ya tsaya
a gurin yana ta sake-saKe cikin zuciyar sa. A kalla ya kai fiye da minti ashirin a gurin yana ta sake-sake cikin ransa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ya yanke shawara ya shiga gurinta kawai domin a yadda yake jin sa idan har bai hada jikinsa da nata ba bazai taba samun nutsuwa ba, domin yau wata irin sha’awace ta addabe shi wadda bai taba jin irinta ba tunda yake jinta akan Aziza, don yana jin idan bai je gareta ba kamar zai iya mutuwa ko ya iya rasa hankalin sa. Nan ya Kara jin ya birkice da ya tuna surarta’a danzun da suka hadu. Kai tsaye ua yanke ma kansa _ tunanin kawai ya koma ciki ya Kara ganinta, don yana  tunanin yin hakan zai zama ya samu nutsuwar halin da yake ciki. Kai tsaye gidan ya shige, nan ya iske ta kwance kan gado ta (window) din. dakinta. Baccinta take sosai. cikin kwanciyar — hankali, daga ita sai ‘yar shimi mara hannu, gefenta ke kwance kina barcin ki.
Ya jima tsaye yana kallon ta daga nan shaidan ya shiga Kawata masa ita cikin ransa, haka ya shiga mugayen tunani daga Karshe ya samu ya shigo dakin. Ya jima akanta yana kallon kyawun surarta. :
. Maganar gaskiya kyawun da Aziza take da shi na jiki da na fuska domin Alah Ya yi ta mai kyau, gashi kuma wani girma da tayi wanda bai kai shekarunta ba, tsabar jin dadi da kwanciyar hankali duk sune suka kawo haka, saboda idan aka fada maka shekarunta za ka sha matuKar mamaki, domin haka allah Ya yi ta da karsashi Www.bankinhausanovels.com.ng
da kuzari. Don haka nan da nan ta zamo cikakkiyar budurwa, sai dai idan ka dubi fuskarta ko ka santa idan an fada maka shekarunta sai ka jima kana mamakin hakan.
Cikin sanda ya dauke ki daga kan gado ya dawo dake dakin Ammi kina ta barcin ki, haka * ya dawo cikin sanda duk tana barci bata sani ba, ya jima yana tsaye zuciyarsa ta kasu biyu, yana – tunanin kamar ya afka mata amma yana tunanin me zai je ya dawo? Tunanin da yayi matuKar bai yi abin da ya kawo shi ya tafi ba, to kuwa yasan mutan gidan za su iya zuwa su tarar da shi a haka.
. Kai tsaye ya je ya rufo Kofar, ya dawo cikin sanda ya hau kan gadon da take ta bayanta ya shiga shafa ta, haka ta dinga ji kamar a cikin mafarkinta, nan tayi juyi. Ya dan tsaya da taba mata jiki, ganin ta ci gaba da yin baccinta ya Kara ci gaba da shafa mata jikin, nan ta dora hannunta a inda taji ana taba ta.
Tsaraf taji ta riKe hannun mutum, a razane — ta bude idanunta zumbur tayi ta tashi zaune ta ce.
“Subhanallahi! Ya Hameed meye haka kuma me ya dawo da kai bayan mun rabu da kai?”
“(Pleasc) Aziza na ni da ke ne, kawai ki saya ki saurare ni kiji me ya kawo ni”.
Cikin tsawa tace “Ya Hameed ka fita ka barni, kana hauka ne? Kasan abin da kake fada min kuwa? Wallahi idan baka fita ba zan je na fadawa su Abba, ko ka fara shaye-shaye ne?”
Cikin irin wani yanayi na kamar ‘yan maye yace
“Aziza na (plcase) ki tsaya ki fahimce ni, ki gane cewa ina cikin rudani na sha’awar sonki, _ wallahi yadda nake ji na kamar zan iya rasa raina idan ban hada jikina da naki ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Allah Ya tsare ni Ya Hameed da aikata haka, ashe dama kai fasiki ne? Wallahi idan baka
. fitar min daga daki ba zan kurma maka ihu kowa yaji abin da ka zo yi, ai wannan keta haddi ne”.
, “Aziza ko me za kiyi sai dai kiyi, domin ba zan iya jure irin halin da nake ciki ba na tsawon shekarun da na shafe akan ki, ki kwantar da hankalin ki ba cutar da ke zan yi ba, ki tuna. cewa baki da wani miji sai ni”.Allah Ya kiyaye min na aure ka Ya hameed, wallahi na tsane ka har Karshen rayuwata, kuma na rantse sai na fadawa kowa abin da kake nufi akai na, banza mugu”. Nan ya fara matsowa kusa da ita, ta shiga ja da baya. Sam ta manta bata nemi wani abu ta ° rufe jikin ba, sai kawai hannu da ta sa ta KanKamce jikintata taho da gudu zata bude Kofa – ta gudu, nan taji Kofa a rufe babu kuma (key) a jiki. Nan ta Kara rudewa, ta juyo ta ga ya nufota, nan take ta shiga kuka cikin Karfinta. Ciro (key) din yayi ya nuna mata, ya ce. Zan barki ki fita, amma sai kin yi min abinda nake so”. Nan ta soma kurma ihu, ya yi sauri ya zo ya toshe mata baki ya hade ta da jikinsa, sannan ya ce.
“Duk ihun ki babu mai ji domin duk na – kulle gidan, sannan kuma ga sanin yadda gidan nan yake, duk ihunka a ko ina yake da wuya kaji – don haka sai ki yi ta ihun ki babu mai hana ni burina”™.
Cikin kuka tace, “Ya Hameed kasan me kake fada min kuwa? Azizan ka ce fa, na roKe ka
idan baka cikin hayyacin ka kayi sauri ka dawo ka gane wa kake tare da ita. Ka daure kada kayi abin da zai cutar dani, kayi haKuri ka bude min na fita daga dakin nan”. Murmushyi yayi, ya ce, “Kalau nake,
_ kuma nasan Azizan nawa ne da ba ita ba babu wanda zan yiwa haka, ki daure ki bani hadin kai kawai Aziza, ba zan iya jure halin da nake ciki ba a yanzu. Ki tuna fa ni ne zan aure ki, me kike jin tsoro?”
Ganin ya yo kanta gadan-gadan yasa ta soma ja da baya tare da hango abin da zata iya tsare kanta, nan idanunta suka hangi wani kwalba na lemo, da sauri taje ta dauka ta shiga nuna masa cewa.
“Wallahi idan ka matso ni sai na fasa maka kai, idan kuma kana jin wasa nake ka matso ka gani”.
“Bana jin akwai wani wargi da zaki yi min na fasa abinda zanyi tunda kin Ki bina ta lallami, don haka dole na aikata abin da nayi niyya tunda daga Karshe dai hannuna za ki dawo, ni kuma ba zan iya jira har sai wannan lokacin ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana gama fadin haka yayo kanta gaba daya. Ai kuwa bata yi wata-wata ba ta daga kwalbar nan sai ta sakar masa a goshi, nan da nan sai ga jini, haka nan ya cakumo ta tana thu  ya tikar da ita kasa yana cewa. “Ai tunda ta kaimu ga haka dole nayi abinda na ga dama, idan yaso kome zai faru sai dai ya faru”. :
Kuka take kamar ranta zai fita tana bashi hakuri, amma sam yaki saurara mata, haka ya shiga cire mata riga.

*******

Zaune muke gurin makoki duk muna cikin jimamin mutuwar, haka kawai sai naji gabana yana ta faduwa, naji zaman gidan duk ya gundire ni, sai dai babu yadda za ai na ce zan tafi tunda mu ne manya a gurin dole na hakura. Sai dai
haka na dinga jin zuciyata babu nutsuwa, duk sai na dinga danganta rashin jin dadin zuciyar tawa da mutuwar da aka yi ne.
An yi sallar la’asar kenan Aisha ta matso guri na ta ce. “Ummah, ni fa zan koma gida don tun dazu ina nan sai yawan jin faduwar dgaba nake tayi, na kuma rasa gane dalili. Kuma ni sam bana jin haka sai yau, tunda garin Allah Ya waye nake ta jina cikin damuwa amma da ina ta yawaita azkar. Na ce, “To Allah Ya rufa asiri, ina ganin ki tashi ki taf gida”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina sane na ce mata haka don kada na fada mata cewa nima ciki wannan halin nake ciki na. daga mata hankali, domin tunani zata yi wani abu ne zai same mu. Na ci gaba da bata Kwarin gwiwa akan ta dinga yin addu’a, nan take. hankalina ya tashi na dinga tunanin kowane abu ne zai faru da Mukhtar akan hanyar sa ta dawowa daga tafiyar da yayi, haka nima cikin raina na ci gaba da yin addu’’ar, amma ban nuna mata cewa nima ina da tawa damuwar ba.
Tana shirin tafiya ne Habibu ya shigo ‘cikin gidan yana salati hade da hawaye a fuskar shi yana fadin.
“Yau mun shiga tashin hankali a gidan Ya Mustapha, bara yi suka shiga gidan”.
Gabaki dayan mu muka mike cikin tashin hankali da rudu domin bamu san me suka yi ba, da sauri naje na riko hannunsa na ce. Habibu iya satar dai suka yi basu cutar da kowa ba?” Cikin kuka ya ce, “Umma ban sani ba dai, yanzu muna gama sallah aka zo mana da labarin”. Yana fada yana kuka.
Hankalin mu ya gama tashi gaba daya ganin yana kuka, na ce.
“Habibu ban yarda da maganar ka ba, meye ya sa ka kuka game da batun shigar Bbarayin? Ko dai wani abu ya faru ne?” Aisha hankalinta ya yi mugun dugunzuma, ta ce. Umma su Haana da Ammi na! Na shiga uku, Allah Yasa ba wani abu ne ya faru da su ba”. ‘ .Nan take hawaye suka soma. fita daga
_ idanuna, kafin na ce da ita wani abu har tayi waje da gudu, haka nima na biyo bayanta da Sauran Jama’‘ar da muke gurin.Tashin hankali mara misaltuwa muka je muka tarar wanda ya dugunzuma dukkan *hankalin ZURI’A. Aziza muka gani kwance cikin jini a hannun mahaifinta ya rungumeta yana ta sharbar kuka, ya hana kowa ya taba ta, duk ya susuce kamar wani Karamin yaro dan goye.
Da sauri Aisha tayi kansa ta karbeta a hannunsa ta shiga kuka, cikin tashin hankali ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Abba Haana! Me ya samu Ammi na? Ba dai kashe min ita suka yi ba?” Cikin kuka kamar yaro ya ce, “Aisha an kashe mana rayuwa, an kashe darajar Aziza da mu kanmu, domin wasu mara imanin sun zo har gida sun hakke mata, ma’ana sun yi mata fyade”Kurma ihu tayi ta saki Azizan ta riko masa_. kwala, cikn kuka ta ce.
“Me kake son fada min ne Mustapha? Me naji tace? Wayyo Allah na na shiga uku ni Aisha”.
Nan ta juyo ta kalli Aziza tayi saurin rungumeta a cikin wannan hali sai gani muka yi ta suma a gurin, ni kuma ina tsaye tsabar rudani
da na shiga sai ji nayi nima idanuna yana son rufewa, nan take naji jiri na dibana, a take nima na fadi sumammiya.
Salati suka shiga yi, dolc aka yiwa Mustapha aka debe mu gaba daya don zuwa asibiti, kusan babu wani namiji da yayi saura bai bimu asibiti ba in dai dan Zun’ar mu ne, haka muka fice cikin tashin hankalli.
Asibitin Malam Aminu Kano aka kaimu, ni ce na fara dawowa cikin hayyaci na sai Aisha, yawan kukan da take yi shi ne yafi dagawa kowa hankali, kowa yana bata haKuri amma ina sai kuka take. Nan take cewa Allah Ya dauki ranta ta huta da wannan bakin ranar da ya same ta. Haka muka hadu muna bata baki akan tayi haKuruta rungumi Kaddara babu wani bawa da zai iya tsallake Kaddarar sa. Tayi ta dai addu’a akan Allah Ya tashi kafadar ta. . WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Tun sanda muka zo asibitin ake ta KoKarin ceto ran Aziza amma ina! Har yanzu bata iya motsi, ga dai alamu tana da rai ba mutuwa tayi ba, amma idan ka ganta ka zata ta mutu. Alh. Jafar, Alh. Aminu da Mustapha suna zaune a (officc) din manyan likitoci guda biyu suna yi musu tambaya.
Dr. Sha’aibu yace, “Kamar yadda muka tambayeku cewa tsawon awanni nawa aka yi da faruwar wannan al’amari ku kace baku sani ba
Yadda binciken mu ya nuna ta shafe awanni uku cikin wannan yanayi wanda jinkin da rashin samun taimako a lokacin da abin ya faru ya janyo mata illoli da dama, na farko dai a yanzu tana cikin koma zata jima a haka, idan Allah Ya kawo cikin sauki zata iya farkawa ta dawo cikn tunaninta, idan kuma aka samu rashin sa’a zata iya zautuwa gaba daya ko kuma tayi mantuwar abinda ya gabata a baya (losing memory). Illa kuwa ta mutuncinta anyi mata sosai, amma zamu yi iya yinmu don ganin munyi nasara akan aikinmu”
“Lahaula wala Kuwwata illa billah! Ya Allah Ka fitar da yarinyar nan daga cikin wannan masifa da ta same mu”. Ya Karasa fada yana kuka.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *