ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duk jikin mu ya yi sanyi ni da Maryam, take naji hawaye sun zomin, na ce.
“Abdulhameed kai yaro ne, a matsayin shekarun ka da karatun ka ai ya yi wuri ace kana da aure, kuma ga ta da lalura, shin ya zaka yi da karatun ka?”
“Granny idan za a yarda na auri Aziza a yanzu a cikin wannan halin zan iya hakura da komai har karatun na tsaya na lura da rayuwar ta saboda nasan na girma zan kuma iya kula da ita don haka yanzu na fadawa Daddy haka ne shi yasa muka zo nan tare domin ke kadai ce za ki yarda da haka auraminita”, Umma wannan haka yake, gaskiya ya fada, ki daure ki yarda da hakan”.
“Jafar babu damuwa tun da ZURI’A DAYA muke, babu wani abu da zai gagara a ciki, amma ku dan yi haKuri ka ci gaba da fahimtar Abdulhameed, insha Allahu shi ne zai

auri Aziza bayan ta ji sauKi, amma dai mu jira mu ga yadda hukuncin da Ubangiji zai zartar”.
“Shi kenan, Allah Ya bata lafiya, bari mu Karasa gurin Mustapha din”.
Haka suka mike suka shiga cikin gurin da aka kwantar da Aziza, nan suka hangeta kwance liyayenta sun zagaye ta sai kuka suke yi, gata nan gaban su kwance babu awani alamun tana motsi a tare da ita.
Suka yi sallama suka shiga, da yake lokacin ana barin na jiki su shiga don haka suka shiga tare gaba dayan su. Tsananin tausayi da dana sani su ne bayyane a fuskar Hameed, .bayan sun gaisa ne iyaye duk suka fita suka bar Hameed a gurin, dukKawa ya yi ya riko

hanunta, nan take hawaye suka wanke masa idanu, cikin kuka ya fara cewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aziza na ki yafe min abin da nayi miki, ban san ni azzalumi neba sai bayan na hakke miki, Aziza na ban taba tunanin zan jefa rayuwar ki cikin wannan halin ba sharrin zuciya da shaidan su ne suka kai ni ga haka. Aziza mai yasa na kasa tausaya miki ban cutar da ke ba bayan irin roKo da haKurin da ki
ka ba ni, amma tsabar rashin tausayina na manta da cewa ke Aziza na ce?
Hakika na san ba zaki taba yafemin ba har tsawon karshen rayuwar mu, na tsani kaina, na tsani rayuwata gaba daya tun bayan faruwar al’amarin nan, Aziza ina tsoro kada ace ni ne da hannuna Zan yi sanadin mutuwar ki. Wayyo Allah! Ya Allah Ka yafe min, Ka bawa Aziza na lafiya ta warke, ta yanke min duk hukuncin da take so, domin na zama azzalumi akan ta.
(Why) Daddy? Me yasa baka hukunta ni ba da ku ka gane kai da Mom abin da na aikatawa ‘yar uwata, Kanwata? Me yasa ba kwa so duniya ta gane cewa ni ne na cutar da Aziza na? Daddy me yasa ka nuna son kai bayan kasan ban Boye maka cewa ni ne na cutar da Aziza ba? Ya Allah Ka kawo hanyar da asirina zai tonu a gane ni ne, domin naji a yanzu gaba daya na tsani rayuwata gaba daya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ya shiga sharbar hawayen sa, ya Kara __ damKe hannun Aziza ya ce. “Aziza na ina so Allah Ya baki lafiya ki tona min asiri, kuma ba zan Karyata ki ba, ba zan  musa miki ba, domin nasan na cuceki, na cuci kaina, na kuma cuci ZURI’Ar mu. Na zamo mugu, mara imani. Aziza bana so ki yafe min har sai an hukunta ni dai dai da abin da na aikata miki, ko, da kuwa kashe ni shi ne mafita gare ni, idan haka ya faru to sai ki yafe min. Yau na zo gare kidon ki yafe min, ba zan taba barin asibitin nan ba har sai Allah Ya baki lafiya kin sa an hukunta ni da hannun ki sannan zan samu nutsuwa a cikin rai na, amma nasan ni da farin ciki har Karshen rayuwata, domin tun ranar da abin nan ya faru na rasa farin ciki na har abada.
Ya AllahY Ya Allah!! Ya Allah Ka bawa Aziza na laifya, ta dawo kamar yadda take rayuwa’.
“Ameen Abdul, bar kukan haka kayi_ , hakuri da sanin Allah, zata samu sauki”.
Zumbur ya yi ya yi sauri ya dago kansa da _ ya kifa a jikin gadon yana kuka, ni ya gani da sauri yaCe,
“Granny yaushe ki ka shigo ban ji zuwan ki ba?”
Na ce, “Shigowa ta kenan naji kana addu’ar Allah Ya bawa Azizan ka lafiya”.
Da sauri ya zo ya riKe Kafafuna yana kuka yana cewa.
“Granny ya zan yi da rayuwata? Ya zan yi da raina? Granny ba zan iya jure ganin Aziza na cikin wannan halin bane yasa haka ya faru da rayuwar Aziza? Me yasa na…
“Kai Hameed haukan me kake yi haka zaka tsaya kana kuka? Maimakon kayi mata addu‘a shi ne zaka sa ta gaba kana kuka kamar kukan ka ne Zai bata lafiya?” Shiru ya yi bai dago kansa ba domin ya gano muryar mahaifinsa ne ta katse shi da shirin tonawa kansa asiri da yayi niyya. Nan ya Karaso gurinsa ya kama shi ya dago shi, ya ce.
“Haba Hameed, ka daina irin wannan surutan kamar Karamin yaro, ka ci gaba da yi mata addu’a, hakan yasa bana son barin ka zuwa nan gurin domin idan ka ganta Kara ta da hankalin ka kake yi, don haka ka zo mu koma gida kai ma ka huta, kada ciwon kai ya kama ka”, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Daddy babu inda zan iya komawa tunda Allah Yasa ka bari yau na zo to na zo kenan har -sai Aziza na taji sauki ta yanke min hukunci da hannunta kan abin da nayi mata”. Gaba daya hankalin mu ya tashi jin irin furucin da Hameed yayi, da sauri muka hada baki da Mustapha muka ce. Hameed, me ka yiwa Azizan?”
Juyowa ya yi gare ni ya fara kuka, ya ce.
“Granny na yiwa Aziza laifin da ba zata yafe min ba, domin.na bari wani ya zo ya cutar da ita banzo na taimake ta ba, don haka nasan ba zata taba yafe min ba. Nasan a lokacin da abin zai faru ta kira suna na don na cece ta amma ban zo ba, hakan yasa na ce nayi mata laifin da ba zata taba yafe min ba”. .
Gaba dayan mu sai a lokacin ne muka yi ajiyar zuciya, domin mun gano nufin sa.
Mustapha ya Karaso gurin sa ya riko hannayen sa biyu idanunsa sun ciko da hawaye, ya ce.
“Hameed ba kai kadai ne Ammi na ba zata yafewa ba har dani, tunda ban zo nima na cece ta ba.
Hamecd ka saki ranka ka daina kuka, kaje kana addu‘’a akan Allah Ya bawa Azizan ka sauki, Ya kuma tona asirin wanda suka yi mata haka. Ka wuce ku je gida Daddyn ka ya yi min Www.bankinhausanovels.com.ng
bayanin komai game da burin ka don haka ban yi
“maka alkawari ba, mu jira har sai ta ji sauki na bata dukkan farin ciki a rayuwarta, na kawar mata da dukkan wani Kunci da damuwar da ta shiga.
Sai naga farin ciki a fuskar ta sannan zan yarda nayi mata maganar auren ka, amma ban da yanzu. Hameed na yarda da kai, na yarda da Kaunar da kake yiwa ‘yar uwarka, kuma ina da yakinin zaka iya bata dukkan farin cikin da nake hangowa zata samu a rayuwar ta, domin ba ka gujeta ba bayan wannan iftila’in da ya faru gare ta. Don haka na gode, na gode, ka wuce kuje gida domin ni kaina ba zan jure ganinka cikin tashin hankali ba”
“Abba kayi hakur, nasan ban kyautawa Aziza na ba da na bari haka ya faru da ita
“Nace Hameed kada ka karya mana_ zuciya, ka wuce ka tafi abin ka, inshaa Allah zata ji sauki”.
Daga nan bai sake cewa komai ba ya sa kai ya fice yana share hawayen da suke zubo masa, jikin Alh. Jafar a sanyaye ya biyo bayan_, sa shima suka fice.
Yadda al’amarin ya faru tun baya, a lokacin da Hameed ya gama biyan buKatar sa da Aziza bayan irin rashin tausayin da ya nuna mata, da rashin imani, tun tana neman dauki har ta yi shiru domin Karfinta da kuzarin ta duk sun Kare, tuni ta suma ta fita cikin hayyacin ta, amma duk da haka bai sa ya kai ga tausaya mata ba.
Bayan ya dawo cikin hayyacin sa ne ya shiga rudani da fargaba domin ganin irin jini da yake fita a jikin ta, nan ya rude ya shiga jijjiga ta amma ina! Babu wani sauran numfashi a jikinta, nan ya dimauce ya ci gaba da jijjigata tare da kiran sunanta, amma ina! babu wani motsi, hakan ya saka ma ransa cewa ta mutu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da gudu ya mike ya zo ya fita daga gidan cikin rudani, amma sai da ya yi taka tsantsan don
bai bari wani ya ganshi ba gudun tonuwatr asirin sa, haka ya shiga cikin gida cikin rudani da dimuwa, ya rasa inda zai sa kansa, sumbatu da surutai shi ne abin da yake ta yi.
Lokacin da ya shigo gidan bai iske kowa ba duk suna can gidan rasuwar da aka yi, safa da marwa ya shiga yi cikin dakinsa da ya shiga ya rufo abinsa yadda babu wanda zai iya cewa da wani a ciki. .
Ko kadan ya kasa samun nutsuwa, kuka yake so ya yi amma ya kasa yinsa. Tsananin Kunci da rudani da rashin samun nutsuwa duk sune suka gama zame masa abokai a wannan lokacin.
Duk yadda ya yi yaga ya samu nutsuwa Sai ya rasa, haka ya shiga zamar da kansa (busy) don ko zai samu ya yaji dadi da nutsuwa cikin ransa, amma ina! sai yawaitar damuwa da rashin nutsuwar ne suke ta daduwa cikin zuciyar sa, sai yake jin tamkar bashi da komai da kowa cikin duniyar baki daya.
Zulumin sa daya da fargabar sa, kada ace Aziza ta mutu, idan ta mutu ya zai yi da hakkin ta da rayuwar sa gaba daya? Tabbas da yasan
“ haka zai jefa kansa cikin wannan tashin hankalin da bai yarda zuciyar sa ta ingiza shi ya gwada mata wannan rashin imanin ba. Hannu yasa akan Sa yana cewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wayyo Allah na! Wayyo Aziza na, me ° yasa na yardar ma zuciya ta na cuce ki, na manta da ke da kuma kukan da naga kina yi kina . roKona? Idan kika mutu ban san ya zan yi da rayuwa na ba, wallahi nayi nadama, naji na tsani kaina, na tsani rayuwar gaba daya. Da na sani shi ne abinda nayi a yanzu”.
Tabbas hawaye rahama ne, sai yanzu ne Hameed yaji dan wani sanyi cikin ransa dalilin zubar hawayen nasa, haka ya zauna yana ta yin . kukan sa tare da aikin da na sami da ya zamo Keya. Haka ya wanzu cikin wannan ranar ya kasa assasa komai, don yana zaune cikin dakin yana ta aikin zubar da hawaye.
Yana jin lokacin da iyayen sa suka dawo cikin tashin hankali suna tattauna wulaKanci da keta haddin da aka yi ma Aziza, ga rashin tausayin da aka nuna mata. Hankalin sa ya Kara tashi, domin bai ji sunce tana raye ko a mace ba. Haka suka zo suna
buga dakinsa, tunanin su ko yana ciki yana barci, domin sun san halinsa, haka suka shiga bugawa amma shiru babu shi babu alamarsa. Har cikin dare.suka zo suna buga dakin yana jinsu amma ya Ki motsawa ko nan da can, yana guri guda ya takure da an buga sai ya takure ya rungumce jiknsa, ban da aikin zubar hawaye babu abin da yake yi na tarin nadamar . abin da ya aikata.
Su kuma henkalin su ya tashi, suka shiga tunanin ina ya nufa a wannan rana? Domin bai taba yin haka ba a rayuwar sa, haka suka hana kansu barci suka zo bakin dakinsa suka tsaya suna jiran ganin ta yadda zai bullo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna cikin haka sai suka ga an kashe wutar dakin, da sauri suka zo suka shiga kiransa da bubbuga Kofar akan ya zo ya bude, amma ina! Ya yi shiru ya Ki motsawa daga inda yake,
– nan mahaifinsa yaje ya zaga ta (window) ya hango shi. can matsin gadon sa ya takure yanakuka kamar mai jin sanyi. Nan ya shiga kiransa amma tamkar ba da shi yake ba, haka ya hakura ya dawo bakin Kofar ya shiga bugamasa Kofar, amma yayi fumfurus da shi.
Ransa ya yi matuKar baci, ya shiga yi masa fada tare da zaginsa amma ina! Haka nan ya haKura mahaifiyar sa itama. ta soma. nata – amma babu yadda suka iyi, dole suka rabu-da shi… Sun yi-sun yi akan ya fada musu me ya faru da shi yasa ya kulle dakinsa? Amma ya Ki, can da yaji sun daina motsi a gurin sai yaje ya bude Kofar ya nufo falo, nan ya iske su suna zaune sun yi jigum. Sun ganshi amma ko mikewa ba suyi ba, suka zuba masa ido, haka ya Karaso falon suka ga goshinsa da jini jaga-jaga, da sauri Alh. Jafar ya mike zai nufe shi cikin tashin hankali. “Hameed me ya faru da kai haka?” Ya fada cikin rudewa. Cikin Kunar rai Haj. Asiya ta ce, “Daddy – kada ka kuskura ka Karasa gurin yaron nan, domin gashi a bayyane zarginmu ya zama gaske”Cikin tsawa da bacin rai ya juyo ya kalleta, ya ce. “Asiya kin san irin mugun furucin da kike yiwa dan da kika haifa a cikinki kuwa? Don kawai — Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuciyar ki tana zargin wani abu sai kawai ki zartar da hukunci kai tsaye?” Daddy idan har kuna zargina da wani abu to haka ne nine na aikata, ni ne na jefa Aziza cikin halin da take ciki yanzu”.
Tasss! Ya dauke shi da wani wawan mari, sai da ya ga (stars) suna masa yawo a cikin idanunsa, ya yi sauri ya dafe kuncin sa, ya yi taga-taga zai fadi.
“Kana da hankali kuwa? Kasan abin da kake fada min da bakin ka? Yaushe ka fara hauka ne?” . ;
“Daddy wallahi sharrin zuciya da shaidan su ne suka debe ni na aikatawa Aziza haka, Daddy ku yafe min, wallahi nayi nadama fiye da tunanin ku”
– “Inna lilahi wa inna ilaihi raji’un! Hameed zargina ya zama dai-dai kenan? Ya Allah Ka dauki raina da ganin wannan rana mai tarin takaici, yanzu dama kaine ka aikata mata haka? Amma dai ka cuce mu, ka janyo mana gori da Surutu. cikin zuri’a, ka wulaKanta mu, ka wulakanta kanka. Ni Asiya yau naga ta kaina”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *