ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

tafiya da wata motar Mal. M.J ya kawo mata waccan. Yana ajje ta ya juya ya koma gida abinsa. Kai tsaye (class) ta nufa, nan ta tarar da su Zahra suma sun zo, tana shiga‘sai ga (lecturer) – dinsu ya zo Dr. David, nan suka shiga (lecture) ’ dinsu. _ Sai bayan da suka gama ne ta samu damar ” sanar da su yadda komai ya faru da ita, dama ta fara gaya ma Zahra zata bata mata rai ta kashe wayar abinta.  Su Salma dariya suka yi sosai domin sun san abin da yayi mata ya yi ne don ya Kona mata rai, yadda suka nuna abin bai dame su ba sai suka bata haushi. ku abin ma baku dairya ya yi, cikin ku babu wanda zai taya ni jin haushi ko?” Salma tayi dariya ta ce, “Haba Barrister, ai duk ku biyun mukewa dariya. Shi Malam M.J a

Ta ce, “Shi kenan Salma naji kuma na dauka, domin haka ma Granny ta ce min kafin na fito”
Zahra ta ce, “A to, ai.ita gaskiya daya ce Haana, kowa yasan ba halin ki bane rashin kyautatawa don haka akasi aka samu, sai ki sauri ki canza, ya gani kuma idan tafiya tayi gaba shima da kansa zai gane Barrister dinmu ba haka take ba” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Murmusiin ta sake yi ta ce, “Shi kenan naji kuma na dauka, insha Allah zan yi duk abin da ku ka ce min. Anjima sai ku raka ni naje har (office) na bashi haquri, zan kuma nuna masa
abin da ya yi min jiya ko kadan ban damu ba”. Duk sunji dadin furucinta. .
A ranar sau biyu suna zuwa ana ce musu yau bai zo ba, Haana har ta dau zafi sune suka shiga kwantar mata da hankali suna nuna mata cewa bata san abin da ya hana shi zuwa ba, dole da dalili. Babu yadda ta iya, dole haka ta sakko ta Kakura.
Wasa gaske yau gashi har kwana hudu da faruwar, al’amarin, yau Juma’a Karfe goma sha biyu suka gama duk (lectures) dinsu na ranar,
tun daga ranar da al’amarin ya faru. har kawo yau Haana bata kuma sa Malam M.J a idanunta ba, . don sau biyu suna zuwa ana ce msuu ya shigo ya
fita. Tun daga ranar ta cire tunanin sake ganinsa, duk da kuwa abin ya yi matuKar baKanta mata rai, gashi kuma Allah Ya taimake ta babu wanda ya yi meta maganer motar, saboda yawan da motocin suke da shi a cikin gidan a (park space), don duk a rufe suke, don haka ban da ita da — Granny sai Mal. Hamza babu wanda yasan ta fita da motar.
Kullum cikin ranta tana tunanin wane irin rashin mutunci zata yi masa duk ranar da suka hadu? Don haka ta ajje komai cikin ranta, don ta san matukar ta bayyanawa su Zahra ga abin da zata yi masa za su hana ta, ita kuwa yadda take ji a ranta ko da zata bar makarantar nan to sai ta  yiwa Malam M.J rashin mutunci. Ita kadai ta fito don zuwa_ tayi (submitting) (Assignmnet) da ta makara bata kai ba, don haka tayi gaba ta bar su Zahra don sun tsaya yin wani uzurin. Kai tsaye ta nufi (office) din Malamin don sauri take kada ya fita, kamar ance da ita daga kanki? Tana daga kanta ta duba (office) din ko yana ciki? Sai kawai ta hangi Mal. M.J da wani (lecturer) dinsu, nan take kawai taji gabanta ya fadi, kamar ta koma da baya amma ina! ya riga da ya ganta. Itam kuma tunaninta kada ya yi zaton ganinsa.ta zo, nan take zuciyarta ta bata kawai ta dake ta wuce abinta, don kada ta koma tayi asarar Www.bankinhausanovels.com.ng (Assignment) dinta. Sum-sum ta zo ta wuce kanta a Kasa tayi kamar bata ganshi ba, shima ganin yadda tayi sai ya dauke kansa yadda zata ji dadin wucewa tunda hakan take so. Sallama tayi ta shiga ta iske Mal. Suraj yana aikace-aikacen sa, nan ta gaida shi ta ce. ‘ “Dama (Assignment) dina na kawo”Ya dago kai ya dube taya ce, “(Okay) ke sai yanzu ki ka kawo? Garin yaya hakan ya faru?” “§ir na zo da shi na manta a motar data kawo nine sai da na kira aka dawo min da shi”(Okay) sai ki tsaya Mal. M.J ya shigo ki bashi, domin shi ne zai yi (marking) dinsu, don na hada masa sauran na bashi”.
Ya tsine fuska tayi ta ce, “Sir don Allah ko zan iya bari na wuce don anzo dauka ta kuma su Maman mu ne”.Zai bata amsa kenan sai suka ji sallamar sa ya shigo, a Kasa ta amsa.sallamar sai dai bata daga kai ta dube shi ba bare har tayi KoKarin gaida shi.
“Ai kuwa kin ci sa’a gashi nan ma ya shigo, kinga to sauri ya Kare”.
Burus yayi don sai yayi kamar ma bai ji abin da yake cewa ba, nan da nan ya shiga soma shan Kamshi da wani jin kansa don tana satan kallon yadda yake yi.
Guri ya samu ya zauna yana zama kuwa wayarta na soma (ringing). Gurin ( Mal. Suraj yake nan ta kalla, tace.”Sir (excuse)”.Ta saci kallon sa tayi sauri ta ajje Assignment din, tayi kamar ta daga wayar ta yi sauri ta fice. Sunan Zahra ne radau kan (screen) din, ta yiwa Allah godiya. Ta daga ta ce.
“Kai Kawata kin matufar taimako na da shigowar wayar ki, Allah Ya saka miki”. “Me ya faru kuma?” “Ke dai bari na Karaso kuna dai-dai ina?”. “(Okay) to gani nan zuwa”. . Da sauri ta Karaso ta same su, nan ta gaya musu duk abinda ya faru da kuma da tayi Zahra ta ce, “Haba Haana, me yasa kika yi haka? Ashe baki ji abin da muka fada miki ba?” “Naji mama
a wancan lokacin nayi muku alKawarin yin abin da kuka ce, to amma da hakan bai faru ba dole ne na canza kuma bayan  haka ku ga irin wulaKancin da yayi min, nasan tabbas an fada masa na zo neman sa ai kamata – ya yi yace wani abu, amma banza damu Mutumin nan me ya dauki kansa? To wallahi ko dame yake ji bai isa ya wulakanta niba, kuma mota yaje ya rike shi ne Www.bankinhausanovels.com.ng matsiyaci,  indai don sai naje zai bani to ya riKe ya Kara da waccan na bar masa”. Tana gama fadin haka ta wani hada rai. Salma ta ce, “Haana na ga alama kwanan nan so kike ki dauki wani hali da ba naki ba, ni, kuma na rasa gane dalilin ki na yin hakan”.Hmm! Salma ba zaki gane ba, mutumin nan dan rainin hankali ne, sai dai ya rainawa_wasu amma ba ni ba”.Zahra ta ce, “Ke din ma dole ya raina miki tunda Kasanshi ki ke, kuma kema kin san babu wani dalibi da ya isa ya ja da malamin sa a duk inda yake ko shi wane, na tabbata wannan zafin naki babu inda za shi dole ma ki dawo kina neman kamun Kafa a gurinsa”.Wa Ta zaro idanunta waje, ta ce.
“Allah Ya kiyaye, sai dai ke amma ba ni ba, don ni bana Kaunar wata magana ta shiga tsakanin mu da shi, don ya gama kai ni bango”.
Rufe bakinta kenan aka yi musu sallama, duk suka amsa. Wani matashin saurayi ne, ya ce. “Rainana wani yana son ganinki”Da sauri ta ce, “Wanene yake son gani na?” “Malam Suraj ne ya ce na fada miki ke Mal. M.J yake jira wai zai tafi””Je ka ce masa wai ta tafi gida”Murmushi yayi, ya ce, “Au bake bace Raihanatun? Ko sai na ce Haana?”Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Malam na ce ba zan zo ba, kaje ka ce na wuce gida a’ah, ko ana dole ne?” .
Kawai Sai jin murya tayi ta ce, “A’a ba a dole, amma wannan karon zan gwada yi miki dolen don son gane cewa ke din mai tarbiyya ce, a gidanku an baki tarbiyyar amsa kiran na gaba da ke”
Ranta bace ta juyo ta ga mai maganar, Mal. M.J ne tsaye yana dubenta. Ranta ya baci don jin kalaman sa, domin sai ta ji kamar cusa
. mata ashar yayi “Ina son ganinki a (office) dina idan kinga . za ki iya, idan kuma ba zaki iya ba zabi na gare ki, duk yadda kika yi hakan ne zan gane wane tarbiyya ki ka samu a gida”Bai tsaya ya ji me zata ce ba ya juya yayi tafiyar sa.
“Umbmm! Kin dai ji da kunnen ki abin da muke fada miki kina ganin kamar Karya muke fada miki, yanzu sai ki yanke shawarar abin da zai fisshe ki”. Zahra ta fada. Jikinta ya yi sanyi, ta ce, ““Mutuncin gidanmu zan kare, amma wallahi ba don haka ba bai isa na je kiransa ba”
Salma ta ce, “Haana ya kamata ki duba ki gani, mutumin nan da kansa ya taso ya zo har nan don neman ki, bayan kuma ya turo dan aiken ko barin gurin bai yi ba shima ya biyo bayn sa, kin san kuwa mutumin nan ya girmama ki.
Ni dai shawara ta daya da zan baki, ko me zai fada miki ki daure ki ji shi kawai, amma maganar furta masa kakkausan kalamai duk ba naki bane. Idan kuma maganar aji ne ke ce ke da aji, domin shi ne da kansa ya neme ki ba ke bace, nasan dai wannan shi ne Karyar taki”. . “Shi kenan naji ku zo muje”.
Cikin sauri Zahra ta ce, “Su wa? Wallahi _ babu mai binki don yanzu kin fara ban tsoro, ba zamu je ba ki bamu kunya a gabansa, don bamu san abin da yake ranki badon kin sauya cikin “ kwana kadan, kin zama wata HAMSHAKIYA dake”
Dariya Salma tayi, nan ta saki tsaki tayi gaba, ta ce.
“Idan kunga dama ku jira ni na fito, idan kuma ba za ku jira ba ko waccen ku ta yi gaba abinta”,
Zahra ta ce, “Mu mun isa?’ Kiije ki dawo muna nan muna jiranki ko awa nawa Za kiyi”.Www.bankinhausanovels.com.ng 
Bata tsaya ta saurari Zahra ba tasan tana yi mata haka ne don tasa taji haushi kawai tayi gaba abinta batas tsaya ba ta tafi tana saKe-sake cikin ranta don bata san ya za su Kare ba.
Zaune ta same shi shi kadai, da dukkan alamu shima shirin tashi yake don zuwa masallaci.
Sallama tayi masa, daga idanunsa yayi suka kalli juna, tayi saurin kawar da idanunta don kada su sake hada idanun, domin haka kawai taji bata shakkar shi kuma zata gaya masa  duk abin da ya zo bakinta, domin ya gama Kure ta.
“Da kin samu guri kin zauna, don ban fiye son naga mutum ya tsaya min a kai ba don sai ina jin jiri yana dauka ta”Ina ganin idan har so kake na zauna sai ka jira zuwa wani lokaci, don ni yanzu bani da lokacin zama”. Cikin tsawa ya ce, “Ke! Ba rashin kunya na kirawo ki kiyi min ba, da alama dai tarbiyyar nan baki sameta ba”. Dauko (key) din motar ta yayi ya cillo mata, ya ce. Ga tsiyarki nan ki je ki dauki motar ki a gurin da kika ajje”. DuKawa tayi ta dauki (key) din, ta ce. Mal. M.J am sorry da nake fada maka magana kai tsaye wanda ba kowa ne ya janyo ba sai kai, don haka ga (key) din nan kaje ka riKe don naga da alama ka nuna soyayyar ka akan ta ka hada da taka ka riKe, na bar maka”Tsawa ya sake daka mata, abin mamaki duk -yadda take da jin tsoron tsawa amma sai gashi ta dake. Ya-‘ce, “Ke mara kunya! Ban kirawo ki. nan don ki raina min hankali ba, na kira ki ne don kawai na baki (key) din motar ki, na kuma ja miki kunne”. To naji Malam, amma na riga da na furta maganar mota na bar maka, babu ita, don haka idan a kanta ka kira ni to mu gama maganarta”.Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Zo ki fitar min daga (office) mara mutunci, kije ki Karata da Karyar banzar ki, da kanki za ki gane kuskuren ki. Maza fice min daga nan”. “Yanzu kuwa zan fitar maka, don dama ba ni na kawo kaina ba, kai ka kira ni”, Tana gama fadin haka sai ta sa kai ta fice. Tana fita maimakon ya nuna fushin sa na abin da tayi sai ya yi wani irin murmushi yace. “Haana, (smart girl, I like this Attitude)”. Da murnarta ta Karaso gurinsu yadda suka ganta cikin fara’a suma sai suka fara yin tasu fara’ar, tunanin su komai ya dai daita tsakanin su. Zahra ce ta fara tararta da cewa, “Hajiya ta ya kuka yi ne? Da alama dai komai ya saitu? Don naga alamar farin ciki a tare dake”. Murmushi ta yi ta ce, “Yes Zahra na, komai ya dai-dai ta domin yau na amayar masa da dukkan abin da yake raina. Nan ta kwashe duk yadda sukai ta fada musu. . Mamaki ne Karara ya bayyana a fuskar su, nan suka hauta da fada kowa da abinda ya zo bakin su.
Murmushi tayi, ta ce, “Kan ku ake ji, idan za ku zo mu tafi tam, idan ba za ku tafi ba ni kunga tafiya ta, tunda naga alama ranku ya Baci tunda na taba gwaninku”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *