ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya

Dariya Rauda tayi ta ce, “A’ah Malam M.J ba haka bane, ai tuni tayi laushi ta kuma bi, babu yadda za ayi dalibi ya ja da malamin sa”.
: Yadda ta ga ya sake yana magana da Rauda sai taji dadi kamar sun taba ganin juna ko don ba _ dalibarsa bace yasa ya sakar mata fuska? .
“Raihanatu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko na kashe miki bakine”.
Murmushi tayi ta ce, “A’ah ba haka bane  Sir, . “To meye?” Ya fada yana mai kallon ta cikin murmushi. _
Mamaki ne ya Kara kama ta, wai shi wannan mutumin wane iri ne shi? Har yanzu ta kasa gane halinsa. . Babu komai”. Ta fada tana mai tsare shi da  ido.
.

“Shi kenan na yarda, Rauda ne sunanki, dan haka naji ta fada ba” Ya fada yana mai duban ta. °
Cikin murmushi ta ce, “Haka sunan yake Malam MJ”
To ku barni na zaba ma saurayin nata turare mai Kamshi yadda idan ya gani zai yi murna ace budurwar sa ta siya masa turare”.
* Zaro idanu Haana tayi, ta ce, “Sir Brother dina ne Imran fa ya bani sallahu na siyo masa”. _ Dariya Rauda ta shiga yi ganin yadda-Haana ta rude jin ance saurayin ta.
, “Rauda wai haka ne? Don ban yarda ba, don ku ‘yan matan yanzu haka ku ke da son shagwaba saurayi, da zarar an samu abu sai ance nashi ne”.


Murmushi Rauda tayi, ta ce, “Gaskiya ta fada, (Brother) dinmu ne”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“(Okay) ke nafi yarda dake duk da haka bari na zaba masa da kaina don kada ku dauko masa mara dadi
Hada ido suka yi ita da Rauda suna dariya, tayi saurin rufe bakinta don kada dariyar ta fito.
Kusan kala uku ya dauka sannan ya ce su ma kowacce ta dauki wanda take so, wannan na Imran ne. .
Tirjiya suka tsaya yi, nan da nan ya tsare gida, ba shiri Haana taje ta dauki nata, Rauda ma haka.
Saka hannu ya yi ya karbi na hannunsu, sai ya yi dariya ya ce.
Wannan din ya muku? Haana ban da gulma fa?”
Sakin baki tayi tana mamakin wai da gaske Malam M.J. ne ko. kuwa gizo yake mata? Shi ne yaje da kansa ya sake daukar kala biyu, daga ganinsu masu tsada ne, ya ce. Gashi na Kara muku”. — Godiya za su yi ya dauki hannunsa, ya dora kan bakinsa alamar su yi shiru.
Dole suka yi shiru suna kallon sa, ya ciro (master card) dinsa ya miKa suka ciri kudin da ya yi musu ciniki, sannan ya miKawa Rauda ta karba tana godiya. . Sai me kuma ku ke so?” _.
. “Sir mun gode, don wallahi mun gama siyan komai, ka gansu nan Www.bankinhausanovels.com.ng
“”Rauda ki fadi da bakin ki ka da ta hana ki naki ra’’ayin, don naga tana kallon idanunki”.
Murmushi tayi ta ce, “Sir gaskiya ta fada maka mun sai komai da ya kawo mu, (thank you so much)”.
“(You are welcome) sai na ce ku gai da gida Rauda, sai gani na biyu”.
Yana gama fadin haka yasa kai ya yi ciki abinsa ba tare da ya tsaya jin wani furuci a gare su ba.
Mamaki ne da al’ajabi suka gama kashe Haana hade da dumbin abin da yake faruwa, wai shin da gaske Malam M.J din ne kuwa?
Bugar hannunta ta yi, ta ce, “Hello, Hajiya ina ki ka nufa ne ki ka saki baki da hanci kina kallon sa?.
“Rauda mamakin abin da ya faru nake yi kamar a (film) ko mafarki, dole na bude baki, duk ya canja min tunani”. Binsa suka yi da kallo har sai da ya shige wani (shopping) din sannan suka daina kallon
“Haana, dama haka Malam M.J din naki yake dan gayu ga wnai mugun (class) da yake da
shi? A lallai kam dole ya ja muku.aji, domin ganinsa yafi jinsa, wannan (handsome guy) da shi haka. ,
Kuma ni yadda ki ka fadi halinsa duk ashe. ba haka yake ba, (I like his attitude) kuma wallahi sai nake ganin yana diban kama da Ya Abba, ko ke baki gani ba? Maganar gaskiya ni dai Malam M.J din nan naki ya yi min sosai da sosai ina son alaKa da shi”.
-“Rauda gaksiyar ki, wallahi na jima ina tunanin da wa yake min yanayi ina mantawa bana tsayawa ina tunanin da wa yake min kama? Haka bayan nan ma akwai wanda yake min kama da shi duk naki yarda naga hakan da zuciyata take nuna Www.bankinhausanovels.com.ng
Rauda ba ke kadai ba, yau Malam M.J ni kaina ya burge ni, naji kuma ina son nayi (personal) mu’amala da shi, don (guy) din yau ya zuKe min ruwan kai. Shigar sa tayi mugun tafiya dani, don dan gayu ne, ga tsafta, kuma ina matuKar son duk mai wannan (personality) din.
Indai Malam M.J zai sauya yana yi min haka zamu yi shiri da shi sosai, domin na tsani jin kan da yake nuna min”.
“Haana (guy) din nan ba Karami bane fa, ni – banga laifin duk me zai muku ba, domin duk abin da zai yi ni dai-dai ne guri na, saboda haduwar sa da ajinsa ya ci ace dama hakan yake”.
“To muguwa, sai ki zuga shi ya ci gaba da dagawar da yake mana”.
Dariya tayi tace “Gaskiya na fada ke ce ba ki fahimce shi bane bugu da Kari ga ta inda ku ka fara gina alaKar ku shi yasa, ba don haka ba bana jin za ku samu matsala”.
Har suka bar cikin (Country Mall) suna hirar sa, haka kawai sai Haana take jin abin daya yi mata har cikin ranta. A‘yan kwanakin nan Zahra da Salma sun  sa mata idanu akan al’amuranta da Malam M.J,
; domin duk sun canza ‘yar tsamar da suke yi*babu ita, sannan duk zaman da za suyi sai Haana ta sako hirar Malam M.J haka take ta so suna yin hirar sa.
‘ Zahra ce ta ce, “haana wai me ke faruwa  ne ke da Malam M.J, ko har Hajiyar tamu tayi
‘ kamu ne? Ni naga duk kun sauya, ga wani sabon  shiri da naga kuna yi, ko dai sai tayi tsami zamu ji?” Ta Karasa fadi cikin dariya.
Salma dariyar tayi, ta ce, “Gaskiya ne, nima naga alama” Nan da nan ta daure fuska, tace, “To iyayen sa ido, abin da ku ke tunani ba shi bane, – ban da alaKar malami da dalibar sa bani da wata alaKa da shi. Don haka zan yi KoKarin dakatar da shi tun da kuma ku ka fara surutu ina ga sauran jama’a?”
Zahra murmushi tayi, tace “Ki gama noKe-noken ki idan tayi tsami maji, mu dai muna nan gafe”.
“Zahra ke da kada ki yi tunanin komai, ni da Mal. M.J sau da yawa nima ina mamakin yadda akai muke haduwa gurare da dama ba tare da na sani ba, a hankali ya dinga shiga cikin rayuwata ban sani ba, kuma bana boye muku Www.bankinhausanovels.com.ng
– duk inda naje sai na ganshi, kuma ba shi ne yake gani na ba ni ce nake ganin sa, tun ina mamaki har na zo na daina. Don abin ya fara daina bani mamaki, hakan da yake faruwa ya janyo sam ya daina nuna min zafin da yake yi, nima ganin haka yasa tsanar da nake masa na zo na neme shi na rasa, ban da wannan abin babu wanda ya . sani”.
Zahra tace “Dama haka rayuwa take, ai tun farko ke ce kika fara nuna daukan zafi akan
sa yaui maganin ki, don dama ance idan zaka qi to kayi kadan, haka shima so, saboda komai na iya canzawa lokaci guda.
Sai dai ni abin da na dade ina hasashe shi ne, akwai wata alaKa da ku ka gina ma junanku, amma kun Ki ku yarda da cewa haka ne, kowa na jin kansa.
Maganar gaskiya Haana naga kamar zuciyar ki ta kamu da son Malam M.J, amma. kina KoKarin Karyata kanki, don wani hange naki, ko ya kika ce Salma?”
“Zahra muyi dai shiru mu Kara bata lokaci da kanta zata bayyana mana, don na fuskanta bata so mu sani ne yanzu”
Ire-iren hirarrakin da suke yi akan dangantakar ta da Malam M.J wanda hakan yake yawan jefata tunanin don son gano gaskiyar abin da take son boyewa zuciyar. Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali ta soma ganewa cewa sabon da tayi da Malam M.J yana son rikicewa zuwa soyayya, don ta rasa yadda aka yi Malam M.J ya .Shigo rayuwarta haka sosai.
Tsananin shaquwar su a yanzu ba sai a makaranta suke haduwa ba, haka ya shirya musu
suke yawan haduwa a (cour?) don ganin yadda (cases) ke gudana idan sun fito, nan za su zauna suyi hirarsu su rabu, idan an hadu makaranta a nuna kamar ba a tare da juna.
Sarai su Zahra sun gama gane duk abin da yake faruwa, sun ji dadi domin ganin hadin ya yi
Cikin hikima Malam M.J ya fara son jin tarihin rayuwar su Haana, domin yasan ya zai yi ya bayyana mata shi wane a gurinta? Domin ya san cewa yanzu Haana ta gama sakin jiki da yarda da shi, don haka yanzu ne zai tabbatar da cewa zai bayyana mata ko shi wane.
Tun da (exams) ta fara Karatowa Malam M.J ya shiga bawa Haana lokaci har su Zahra lokaci akan su yi karatu don son ganin sun samu sakamako mai kyau.
Wata rana suna zaune lokacin su Zahra basu Karaso ba, hira suke yi da shi yake cewa.
“Reeha”. Kamar yadda yake kiranta lokutan da yaso nishadi.
Ta dago idanunta ta kalle shi don jin yadda ya kira sunanta kamar ba malaminta ba, to amma da ta tuna ba a cikin makaranta suke ba
(state librarv) suka zo nan suka ware don suna dan taba karatun su.
“Wane irin gudunmawa ki ke shirya ma Zuri’ar ku da suka tarwatse ko kina da burin ganin sun dawo guriguda? Jin maganar tayi sama ta ka, kanne idanunta tayi, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Me kace?” Ta ci gaba da duban sa cikin mamaki. “Abin da kunnen ki ya jiyar miki shi na fada,’ wanne shiri ku ke gudunmawa ki ke da shi? Amsar tambayar nake son ji gare ki”. Cikin mamaki ta ce, “Sir, ya akai kasan
wani labari na tattare da Zuri’a ta da ka ke min
magana akai? Sir nayi mamaki fa”Murmushi ya yi, ya ce, “Raihanatu a shirye nake na baki gudunmawata ta duk inda kike so, amma ina son jin shin ki na da buri ne akan dawowar sauran dangin ki da suka rabe?”
Ba don Malam M.J dinta bane da ta fada masa wata magana mai zafi, don mene ne zai yi  mata wannan tambayar bayan ba shi da wani hurumi ga Zuri’a dinsu? Shin ko kuma a tsananin
sabon su da shaKuwar su ne ya kai har yana
Shiga cikin zuciyarta ya gano abin da yake cikinta a Boye. Sauri tayi ta kawar da wannan tunanin, sai tace, “Sir a ina ka samu labarin abin da. yake faruwa cikin Zuri’a dinmu? Wanene ya fada maka cewa mun rasa wasu cikin Zuri‘a dinmu? (Please) Sir mu bar wannan maganar, karatu ya kamata muyi”.Murmushi ya yi ya ce, “Raihanatu ni din nan da kika gani babu abin da ban sani ba na game ‘da abin da ya faru cikin ZURI’A dinku, shekaru ashirin da suka wuce ba ina kaji? Wa ya fada maka? Sannan kuma kai wane?” * Wayar ta ce ta shiga Kara, tana dubawa ta ga sunan Ya Abba, murmushi tayi ta ce. “Excuse Sir””Ya Abba kai ne? Kasan nayi fishi tun yaushe nake neman layin ka sam ban.‘same kaba Daga can ya amsa ya ce,,”Sister ina (busy) yaSa na kashe wayar gaba daya. Ya shiryeyen (exams)? Ana nan ana ta yi ko?” a “Eh”Ya yi kyau, don haka zan fasa dawowa wannan watan har sai kin gama dukkan (exams) dinki don kada na dawo na hana ki karatu”. Bata san lokacin da tayi wani ihu ba, ta ce. “Ya Abba da gaske zaka dawo a wannan watan?”Eh, da ba, amma tunda (exams) za ki fara zan daga, ba zan bar London ba har sai ranar da ki ka gama, to ranar za ki ganni, Don haka ki fada min yaushe ne za ki yi (final exams) dinki sai_na saita na dawo ranar”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin murna da zumudi ta ce,”(Please) Ya abba ka daure ka dawo a wannan watan, zan yi farin ciki sosai, don kasan mun yi matuKar _ (missing) dinka kowa da kowa”.
“A’ah Sister, ki dai barni nayi hakan, don zai sa ki yi karatu a nutse, idan na dawo zan hana __ ki karatu, kuma gashi (first semister) dinki na (level three) don haka kamata ya yi ki fito da . sakamako mai kyau”.
“Shi kenan Ya Abba, ka bari idan na dawo gida zamu yi waya, gamu nan za muyi karatu”.
“(Okay) ya yi kyau, mu yi wayar anjima”.
. Nan suka yi sallama ta juyo cikin farin _ ciki ta dubi Malam MJ, ta ce. “Ka yi haKuri Yayana ne ya kirani” Kafin ya bata amsa sai ga su Salma sun Www.bankinhausanovels.com.ng Karaso gurin, nan suka ganta tare da shi. Murmushi suka yi suka kalli junansu suna son yin gulma amma ganin yadda ya tsare su da idanu sai suka fasa, nan dai suka samu suka yi karatun su suka tashi.

BIRNIN LONDON

Zaune yake cikin (garden) na (Hilton ; Whatford Hotel) dake birnin London, yana — kallon (Rushing waterfall) din da aka yi (designing) cikin hotel din.
Ya harde Kafa daya kan daya, duk wanda ya hango shi-a lokacin zai dauka yana kallon kyan (waterfall) din ne yana yabawa, sai dai abin ba haka yake ba, asali ma idanunsa da tunanin sa sun tafi ga rikicin da Haaya take.son jefe shi da wannan jarrababben son da take masa wanda ya

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *