ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 17 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Haaya ba, hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata jan ido don tayi fishi ta haKura da shi. Sam ba wai baya son Haaya bane, tana da kirki da nutsuwa ya yaba da tarbiyyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai kash! Babu wanda zai samu wani matsayi a cikin zuciyar sa idan ba Haana ba, don ko kadan babu wata mace da zuciyar sa take so da gani idan ba Haana dinsa ba, don haka ya yanke shawarar sulalewa ya bar Kasar ba tare da _~ Haaya ta san shirin sa ba, domin idan ya tsaya tausaya mata haka zai yi ta zama ba tare da ya duba abin da ya dace da rayuwar sa ba.
Ya Abba fari ne shi sosai kamar ka taba hannunsa jini ya fito, kana ganinsa ka ga Bafulatanin asali. Suna matuKar diban kama da haana sosai da sosai, domin duk kamar mahaifin Haana suka debo, domin tun yana jariri yake kama da Alh. Mustapha, wannan yasa Kanwarsa Maryam ta yiwa yayanta takwara. .
Dogo ne shi sosai amma mai dan jiki, gashi baki ne ke da shi, a fuskar sa bashi da wani tarin Kasumba, dan kimanin shekaru talatin ba daya. . Tsananin haduwar sa yasa mata da dama da Turawa da baKaKen mu na nan suke mugun kai kansu don ya nuna yana son su, amma ina! babu wadda take ganin fuskar sa bare tayi ‘Duk cikin su Haaya ce kadai tayi nasarar samu yana kulata, domin shima haka kawai yake jinta har cikin ransa, don a lokacin da take cewa yana kama da yayanta sai shima yake ganin kamar tana yi masa kama da
wani nasa, don haka yasa har dangantakar su tayi nisa, amma ba don wannan ba ya sama zuciyar sa babu wata da zai duba da kalon su yi soyayya idan ba Haana ba. Wannan kenan.
******
Cikin damuwa ta baro makaranta ta Karaso gida, ba komai bane ya sata damuwa illa rashin Malam M.J da tayi sama ko Kasa, babu inda ta samu labarin sa tun sanda suka fara jarrabawa har gashi a yau saura kadan su gama amma bata sake hada ido da shi ba..
_ Babban abin da yafi damunta da bai bari ‘ sun yi maganar da ya fara yi mata rannan nan game da Zuri’a dinta ba, ta so Kwarai ya barta suyi maganar, amma ya hana ta, ya ce ta bari su gama (exams) sai suyimaganar. Wannan ma ya Kara jefata cikin damuwa, sai kuma na gaba yadda ta ke kasa samun duk wani sukuni na rashin ganinsa. Bata Kara tabbatarwa ta shaKu da shi ba sai yanzu da ta daina ganin gilmawar sa, tayi KoKarin Boye damuwarta ga Kawayenta, amma sai da suka gano ta. Haka gida ma Ammi da Granny sun gano tana cikin damuwa da sun tambaye ta sai ta ce musu jarrabawa ce take hana tasukuni.
Su Zahra kuwa tsiya suke mata domin sun gama harbo jirginta, ta KarKkashin Kasa ta shiga nemo labarinsa.
A yau ne ake fada mata cowa Malam M.J ya koma can gida London, domin yadda suka ji ance mahaifiyar sa ce ciwon ta ya tashi. Ya dai tabbatar ba zai dawo ba har sai ya ga yadda jikin nata ya yi idan kuma ba haka ba bashi da wani lokaci da zai ce ga ranar dawowar sa, domin ya ce abin da ya kawo shi ma bai yi ba.
Jin wannan sharhin shi ne ya baro da ita daga makarantar cikin yanayin damuwa, domin a nata ganin Malam M.J bai kyauta mata ba,. domin ya zai yi taifiya basu yi sallama da shi ba, , kamar suna zaman gaba?
Daf da zata shiga cikin Danfillo estate daidai lokacin motarta ta mutu, tayi-tayi da ita ta tashi amma ta Ki, tayi tsaki ta godewa Allah da
Yasa sai da ta zo gida ma sannan ta bata matsalar.
Fitowa tayi ta rufe ta taho ta fadawa direban gidansu wani ya zo ya shigo da ita.
Tafiya take cikin estate din a Kafa tana ta
– duba jerin rukunan gidajen nasu da a yanzu zai fi
kyau ka kira su a kango ba wai don” sun lalace ba, a’ah don kawai babu wanda suke rayuwa a cikin su. Tun tashinta har yanzu babu wani mahaluki da ta ga yana rayuwa a ciki.
Cikin alhini ta dinga kallon gidan, nan take furucin Malam M.J ya dawo kunnuwanta, inda ya Ce.
“Wane irin gudunmawa kika shirya bama Zuriar ku da suka tarwatse? Ko kina da burin ganin sun dawo guri guda?” “Eh”. Ita ce amsar da zata iya bashi da ace
yanzu yana gurin. .
A cikin zuciyarta ta ce, “Malam M.J bani da wani buri a yanzu da ya wuce na ga Zuri‘ata sun hadu guri guda, sai dai ban san ta ina zan fara ba, amma ina jiran Ya Abba ya dawo, domin zan zauna da shi na gaya masa buKata ta da buri na, domin Ya Abba komai na fada masa zai yi min saboda son farin ciki na da yake yi. .
Sannan ban yi mamaki ba da har kasan ba ma tare da wasu daga cikin Zur’a dinmu, domin ance zancen duniya ba ya buya, amma na san buri na akan Zuri’ata insha Allahu ya zo Karshe tunda Ya Abba na zai dawo, shi ne zai bani
dukkan wani ,,,,,, da zai kaini ga cika burina akansu”.
. Da wannan tunanin da take yi tana tafiya, can zata wuce ta wani daga cikin jerin gidan nan ta hangi (gate) din gidan a bude cike da mamaki, ta tsaya cak ta sake duba gidan. Da har tayi kamar taje ta shiga sai ta fasa, haka ta taho tana waige ko zata ga wani ya fito daga ciki.
Har ta kai zuwa nasu (gate) din tana juyowa babu wani da ta ga ya fito daga ciki, – haka ta haKura ta shige zuciyarta cike da tunanin yadda akai aka bude gidan nan.
Yau kusan kwanaki uku kenan idan ta wuce makaranta ta dawo sai ta ga gidan a bude, haka kawai ta dinga jin hankalinta yana fusga akan anya kuwa ba zata leKa ta ga ko wasu ne ciki don ta yiwa Granny tambayar tana ganin . (gate) -din gidan a bude ko ta samu wani labani ne.
Sai ta dauki maganar tata sama-sama, ta ce babu mamaki ko mahaifin ku ne yasa ayi wani gyara a ciki. Don baka yau ta yanke ma zuciyarta cewa ko ma me ke faruwa sai ta shiga ciki ta gano su wane a ciki?
Gefe guda ta yi (parking) din motarta ta rufe ta fito don shiga ta ga da mutane a ciki? Don ta tabbatar da me ke faruwa?
Cikin sanda ta tura bakin (gate) din ya Karasa budewa sosai don ganin abin da ke ciki.
Katuwar mota ta gani gefe guda an wnake ta sai sheKi take Kirar Muran motar da take matuKar so, mamaki ne Karara ya kama ta. Can cikin falo ta dinga jin sautinkida, nan kanta ya Kara daurewa, ta Kara cikewa da
mamaki ta kuma tabbatar da cewa akwai wadanda suke rayuwa cikin gidan nan. To su wanene? Yaushe kuma suka dawo? Dole tana son wadannan amsoshin, don haka nan take ta juya da sauri ta koma gida don ta fada ma (Granny), hasali ma daukota zata yi ta gani da idanunta don ta gasgata bayanin ta.
Da sauri taje ta shiga motarta ta fada gida, tana zuwa donta sanar ma Granny ta tarar sun je unguwa, haushi ya kama ta.
Dole ta haKura ta fito waje ta tsaya ko zata ga fitowar wasu daga cikin gidan, ilai kuwa tana tsaye gurin sai ga motar nan Murano baka wulik ta fito daga ciki, sai sheKi take.
Nan da nan ta fice daga cikin estate din ta sha tint, hakan yasa bata iya gano su wanene a ciki ba. Nan ta yanke ma zuciyarta bari taje gidan ta duba ko zata ga wasu. Tana zuwa ta ga gidan a rufe ruf, jinjina kai tayi ta ce bari su Granny su dawo dole yau ta gasgata ta.
Ko da suka dawo ta gaya musu – har da Ammi suma mamaki suka yi, domin basu da labarin komai na jin wasu na rayuwa cikin gidan.
Haana ta ce, “To a tambayi Abba mana, wata Kila zai san wani abu akai”.
Ammi ta ce, “Ke ban son shirmen banza, yana can China din zan buga masa waya na ce kince kinga wasu cikin gida suna rayuwa, idan bai sani ba na sa shi cikin damuwa? To ko ke ban baki damar yi masa wannan tambayar ba, a’ bari idan ya dawo ma fada masa, sai mu ji me zai ce mana?”
Sam bata so jin haka ba daga gurin Amminta, ta so yadda ta fada musu cikin zafi su kira shi su fada masa, to amma jin yadda ta yi mata bayani sai ta gamsu, don itama ba zata so ace an sa shi cikin damuwa ba, tunda bai fada musu ba to shima kenan bai sani ba, to su wane wadannan?”
Kadan ta dan taba karatun ta cikin dare ta. kwanta barci, ta jima baccin bai dauke ta ba don banda tunanin Malam M.J babu abinda yake aranta
Jifa-jifa kuma tana son tantance yadda za ‘ayi ta shiga wancan gidan da yake. bude, domin tasa a ranta ba zata iya hakuri ba har sai Abbu ya dawo taji wani abu a tare da shi ba. Da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba da ita.
Yau yanayin garin ya yi dadi sosai, duk garin ya yi luf-luf sosai (weather) din garin tayi wa al’umma dadi, sam babu hasken rana tamkar dai haduwar hadari, amma ba hadarin bane, sauyin gari ne kawai daga Allah. Karfe uku ta gama jarrabawarta don haka ta shiga motarta ta nufo gida, Allah-Allah take yau idan ta zo ta ga gidan nan a bude, don kwana
Biyu a rufe take ganinsa idan ta tafi, haka ma idan ta dawo.
Mutum ta hanga a Kofar gidan zaune kan wasu jerin: fararen kujeru irin na Turawa guda uku, yana zaune kan daya tsakiyar kuma dan wani (center table) ne irin kujerar ya dora Kafarsa akai yana karatun (news paper) gefensa kan teburin C’est Bon ne da kofi da kuma lemo (five alive), -Sanye yake cikin wata jar riga mai yankakken, hannu (amless) da wandon. safari _(three quater), karatun (magazine) dinsa yake sosai cikin nutsuwa, babu wani damuwa a tattare da shi, fari ne shima sosai
A hankali tayi (slow) tana kallonsa ko zata gane wane ne? Amma ina! iya (side view) dinsa take iya gani. Nan ta cika da mamakita ce, “To wannan kuma wanene?” Daga nesa take hangowa, amma ba nesa sosai ba.Nan ta yanke shawarar bari kawai ta fito taje ta ganshi, take taji zuciyarta ta gargade ta kan cewa,
“A wane dalili zaki yi haka?”
Sai ta canza shawara ta taka kawai ta wuce gaba don ta je ta janyo Granny ta zo ta gani ko yau zata gasgata abin da take fada mata. “Granny! Granny!! Granny!!!”. Haka ta shiga Kwala mata kira.
“Ina kike? Ki zo muje yau ki ga abin da nake fada miki ko za ki yarda dani”.
Toshe kunenta tayi don haka ta shiga tana ta faman Kwal!a mota kira.
Cikin gajiyawa tace, .”Kai Raihanatu wanne irin kira ne haka? Ai sai ki toshe min dodon kunnena na daina ji, sai kace Karamar yarinya?”
Murmushi tayi a gaggauce ta ce, “Yi hakuri Granny; zo muje ki gani, gidan nan da nake fada miki ina ganinsa a bude, to yau na iske wani matashi zaune a waje yana hutawa, har karatun (newspaper) yake yi”
Bata bari ta bata amsaba ta ce, “(Please) Granny tashi muje ki gani kada ki ce ba zaki ba’Haka ta kamo hannunta suka fito falon suka iske babu kowa, Haana taji dadi don bata son wasu su gansu suce me yake faruwa.
Suna fitowa suka hango shi, Haana ta yiwa Allah godiya don haka tayi saurin nunawa Granny shi. Ita din ma ta cika da mamaki. Granny ba tsaywa zamu yi ba, muje gurinsa muga ko wane”.
Tafiya suke Haana ce kadai ke magane amma ita Granny bata ce komai ba, Allah-Allah take ta je ta ga ko waye? Kuma ya akai har ya samu damar reyuwa cikin gidan ba tare da sun san wanene ba?
Suna zuwa gurin Granny ce ta fara yi masa sallama, juyowa yayi don amsa sallamar. Kash! Sai, ku daka ce ni a nan zan dakata sai mun hadu.a kashi na uku don jin yadda zata kasance,
daga taku:
SA’ADATU WAZIRI GOMBE
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG