ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya

Jin furucinsa sai abin ya bashi mamaki, domin bai tambayi halin da diyarsa take ciki ba sai wannan maganar ya jefe shi da ita. Nan take yaji ransa ya baci, amma sai ya tuna shi din gaba yake da shi, dole yana girmama shi tun da sun taso da wannan tarbiyyar a gidan su.
“Yaya banyi tunanin cewa da wannan maganar zaka fara yi min ba, tun dazu muka dawo babu wanda ya zo ya duba jikin Aziza

amma sai gashi ka aika an kirawo ni saboda wani dalili”Daga masa hannu yayi, ya ce, “Dakata Mustapha, dole dama zan yi maka wannan maganar, amma tunda wannan ita ce a gabanmu ai dole na fara yi maka ita ‘saboda ita na kira ka. Shin ka janye ko baka janye ba?”
Ransa ya baci, yace, “Yaya dole zaka yi . min ko UMARNI kake bani akan dole nayi abin da kake so?”
Girgiza kai yayi, ya ce, “Ko kusa ko alama, idan ban tilasta ka ba to kai ka tilasta kanka ka janye ko kuma kai a kai ka Kara saboda wasu dalilai da kai ka sani a

tsakanin ku wanda mu bamu sani ba cikin sirri ku kayi shi”. Gaban Mustapha ya fadi jin furucin da dan uwansa yake masa, yace. Yaya Aminu me kake nufi? Shin kana goyon bayan zalunci ne?” Girgiza kai yayi, ya ce, “Ko alama bana goyon bayan zalunci, saKo aka bani na baka don haka baka da wani hujja da zaka kira ni-da mai goyon baya bayan zalunci,
Ga wannan takardun ka duba ka gani, nasan zaka gane na meye. Takardu ne na sirrin ku da irin Www.bankinhausanovels.com.ng yarjejeniya da alKawari da ku ka yiwa juna kai da shi babu wanda ya sani sai da lokacin da kowa ya kamata ya sani din yanzu. Mustapha ashe duk wani abu da kake takama da shi ba naka bane kai kadai, yawanci duk na dan uwnaka ne? Hatta Company da kake ji da shi ba naka bane kason ka kadan ne a ciki? To gashi ka duba ka bani amsar da zan fada — masa, idan ka shirya bashi komai nasa a cikin satin nan to ya yarda kaje ka kai shi duk inda kake son kai shi Kara. Ya ce bai so ka janye ~ tunda ka furta hakan, idan kuma ka Ki to shi a cikin satin nan zai kai ka Karar akan ka dawo masa da dukkan abinsa da yake gurin ka”Murmushi yayi ya ce, “Yaya Aminu kenan, duk abin da ka fada babu Karya a ciki, wannan haka yake, naji  kuma na amince zan dawo masa da komai nashi.
Sannan maganar kaishi kotu tun jiya mahaifiyata ta,sa na janycme, kuma bana jin zan yi fishi da shi tunda mun barwa Allah komai.
Ka mayar masa da takardunsa ba sai na duba ba tunda nasan da maganar, cikin. sirri muka yi kuma tunda ya buKaci komai a yanzu zan bashi duk abinsa da yake guri na. Nayi maka alwashi ko zan yi yawo tsirara zan danKawa Yaya Jafar dukkan abin da nasan nashi ne a hannu na”.
Murmushi yayi ya ce, “Kayi Kokari sosai domin ka nuna jarumtaKa ta neman rufin asirinka, don haka tun da ka yanke shawarar dawo masa da dukiyar sa ina ganin kamar yadda na fada maka ina so ka dawo dasu ta hannuna Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza kai yayi, yace, “Ba da kai muka yi maganar ba, domin lokacin da hakan ya faru baka sani ba. Don haka a matsayin ka na dan . sako to dole ne ka tsaya a matsayin da kake, don haka ka huta lafiya, ka kuma fada masa ya saurare ni cikin satin na zan dawo masa da komai”. Yana gama fadin haka ya juya ya yi ficewar sa. Fitar sa kenan Alh. Aminu_ yace, “Mustapha ka burge ni, kayi min komai cikin – sauki, domin ban zaci sauKin naka haka zai zama
ba. Zan maye gurbinka a gurin Jafar, domin na sha matuKar mamakin tarin kudin da kadarorin _ da ya tara maka”. Kwanaki uku da faruwar haka abu ya fara tsamari cikin Dan Fillo Estate, yadda Zuri’a suka – juya mana baya, babu wani wanda yake shiga ~ hurumin mu, don ko da na koma gida haka kishiyoyi na suka dauke min wuta, babu wanda maganar arziki take hada nidashi:’Abin ya ci gaba da daure min kai ganin ~ _mun dawo da mara lafiya amma babu wanda yace.dani ya mai jiki? Sannan babu wani gida daya leKa mana. Kowa na yiwa magana.cikin gidan’ ~ babu wanda yake kulani. Nan. take abin ya daina bani mamaki’. _ domin tuna yadda muka yi rayuwar baya can, nan take na gane hade mana kai aka yi. Mu aka cuta kuma mu ne za a dinga ganin laifinmu. — _ Nan take na cire dukkan wani shakku da mamaki, saboda rashin tsoron Allah ga ‘yan ‘ ’ Kwana hudu da dawowar mu Mustapha ya tara mu ni da Mukhtar da Maryam da kuma Ammin ku, duk mun hallara muna sauraron abin ‘da zaice damu.” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya fara’ da ‘cewa, “Dukkan ku ina so ku zama shaida akan zan mayarwa da Ya Jafar _dukkan dukiyar sa da kuma dukkan abin da-ya malaka min da hannunsa
kyauta wanda kuka sani “da wanda baku sani ba, tsabar shaKuwar mu da’ KAUNARMU yasa muka boyewa kowa abin da muke gudanarwa a tsakanin mu cikin sirri…”. Nan ya, gaya mana duk yadda suka yi da _ Aminu,yafara dacewa. . “A cikin kaso. goma na dukiyata da . _kadarorina kaso uku da rabi shi ne nawa, sauran .- duk nashi ne, Wannan Company na ‘auduga’ da nake riKe da shi ba-nawa bane nashi na, munyi – wata yarjejeniya ni da shi akan idan ya bude – wani zan bashi wasu kudi daga gare ni ya mallaka min shi. Tun tsawon shekaru muka yi – wannan sirrin tun mahaifin mu na raye, ya roke _ ni akan kada na bari kowa. ya san wannan – ‘ maganar har Karshen rayuwar mu. Duk abinda muke yi a rubuce muke yinsa. To a yanzu ya buKaci na dawo masa da_ komai nashi, shi ne yasa nake bayyana muku .
komai,.amma ba-don haka ba babu wanda zai sani tunda alKawari muka yi a sirrance babu wanda ya sani.
Saboda haka ku zama shaida, daga yau na tattara komai nashi zan mayar masa, ko zan rasa abinda zan ci zan mayar mai da komai nashi, tunda Allah Ne Yake bayarwa. Ya yi hakan ne don ya tozarta ni kuma insha Allah babu abin da zai faru dani tunda da Allah muka dogara”. “Yaya Mustapha kada kaji tsoron komai, ka tattara komai nashi ka_mayar masa, kuma_ – _ insha’ Allah dukkan’su za su sha mamaki, ba dai sun ware mu ba? Baba dayansu babu mai son . zumunci da mu don kawai sun ga shi ne mai tarin dukiya zai iya magance musu matsalar su, ga kuma tarin ‘yan ubanci da suka dawo mana da shi, to za su sha mamaki, kada Allah Yasa su yi _ zumuncin ya su ne suka jiyo”.  ta ce, “Yaya mun goyi bayan ka,’ mayar masa da komai nasa, ni da mun yi maka alKawarin baka dukkan kadarorin mu a daga a siyar ka hada da naka kayi (investing) duk wani abu da kake muradin yi”.Murmushi ya yi ya ce, “Maryam, Mukhtar, duk na gode muku. Sai dai abin da baku sani ba a yanzu yadda nake bana jin zan girgiza sosai don na mallakawa Ya Jafar dukiyar sa, ina da abin da .zan juya ya kawo mana kudi”,
“A’a Ya Mustapha, idan baka goyi bayan abin da Ya Maryam ta fada ba to kana mana nuni da cewa zaka ki karba ne don gudun kada wata rana muma muyi maka abin da ya faru yanzu. Tunda har ka karbi abinsa a baya mu ma a yanzu dole ne ka karbi namu tunda anyi hakan ne akan a tozarta ka”.
“Wannan gaskiya ne abin da Mukhtar ya fada, idan ka ki zamu yi tunanin hakan kake gudu”. Cewar Maryam.
“Shi kenan, na gode Allah Ya_ bar zumunci, Ya kuma hada kanmu. Umma banji kince komai ba?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin kuka na ce, “Me zan ce ban da godiyar Allah da Ya bani ku? Don Allah ku hada kanku da na yaran ku tunda ku an ware ku cikin ZURI’A, insha Allah sai kun zama abin kwatance a cikin su. Kuma naji dadin hadin kankun nan, Allah Ya tsare muku Zukuncin ku, don haka maza ku tashi kuje ku kai masa kayan sa”.
Alh. Jafar ya yi matuKar mamakin yadda ya ga Mustapha ya dawo masa da komai nashi cikin KanKanin lokaci, domin a tunaninsa zai razana ya zo ya bashi haKuri yadda zai ci gaba da yi masa dukkan abinda yake so a matsayin sa na mai kudin cikin ZUBI’A. Lokacin da yake a gaban jama’a ya bashi irin su Alh. Aminu da ‘yan uwansa, a take ya ce.
“Aminu gashi nan ku karba kuje duk ku raba kai da Kannen ka, me zanyi da su?”
Nan take ya shiga murna suna yi masa godiya, minti biyar basu Kara ba shi da Mukhtar domin tare suka je. Akan hanya ne Mukhtar ya shiga mamakin yadda akai ‘yan uwansu suka . juya musu baya lokaci guda don kawai rashin_ – son gaskiya.
Mustapha ya ce, “Kada kayi mamaki, . tsabar son kudi ne yasa suke goyon bayan su,maganar gaskiya Ya Jafar yana da tarin dukiya
musamman wanda ba kowa bane zai sani sai ya jaka ya fada maka, don haka ya siye su da kudi dole ne su yi mana haka, musamman ma Ya Aminu da yake son ya kashe zuciyar sa da son abin hannunsa bayan wanda Allah Ya bashi. Don – kada kayi mamaki, a wannan rayuwar idan ‘ kana da arziki duk rashin gaskiyar ka kaine mai gaskiya, ka dai duba lokaci guda yadda ZURI’A DAYA ta koma kashi biyu tsabar rashin gaskiya da son abin duniya sun ware mu sun fitar damu — daga cikin ZURI’A bayan mu aka yiwa laifi, amma tunda yana da kudi sai aka goya masa baya”. . – “Ya Mustapha kadaka damu, iya mu kadai din nan za mu iya hada Karfi da Karfe mu ’ tashi tamu ZURI’A din tunda dama mu din — ZURI’A DAYA ne, musa a Www.bankinhausanovels.com.ng ranmu cewa wani abu kadan muka rasa cikin ZURI’A dinmu, insha Allah sai anyi Alfahari da tamu ZIRI’Ar da aka, ware, Allah dai Ya ja kwananmu a gani”. . Murmiushi yayi ya ce, “Ameen Ya Allah, . Mukhtar mu barsu mu zuba musu idobabu wanda muka Ki a cikin su wanda ya shigo cikinmu muyi da shi. wanda ya Kimu babu ruwanmu da shi, mu dai zamu dinge sauke abinda Allah Ya ce damu”.
Hameed . ya tashi hankalinsa da na iyayensa akan dole shi a san yadda za ayi a daidaita dangantakar sa da Aziza ya samu ta yafe masa, amma mahaifinsa ya hana shi fita nan da can, ba ma shi kadai ba gaba daya ZURI’A  ya siye iyayenen da matansu da kudi akan baya sO ya ga wani gida ya yi mu’amala da gidan su Mustapha da ‘yan uwansa, don kawai ya jefa su cikin Kuncin rayuwa. Hakan kuwa aka yi, duk aka ja da baya da su, babu mai mu’amala da su tsabar son abin duniya da rashin jin tsoron Allah.
Tsananin naci da son zuwa wurin Aziza — ranar nan haka Hameed ya zo ya nace -sai an barshi ya shiga ya ga Aziza, ranar ya.saka wani mugun naci akan sai ya shiga gidan. Allah Ya sa Mustapha yana gidan, haka ya zo ya dauke shi da mari, dai-dai lokacin da Alh. Jafar ya zo Kofar gidan don tsawatarwa da Hameed akan kada ya Kara ganibnsa a Kofar gidan.
Ai kuwa nan ya zo yana ta masifa akan ba zai yarda ba tunda ya dokar masa da, a take ya kira (police) suka zo wai su tafi da shi a ramawa dansa marin da aka yi masa, nan da nan sai gasu
nan mota guda a cikin estate din. Mustapha bai yi mamaki ba domin yasan ‘duk borin kunya ne, domin Hausawa sun ce tabarmar kunya da hauka ake nade ta . Police suka je suka shiga KoKarin _ tafiya da Mustapha, sai ga Habibu nan ya zo, nan _ aka tasa masa abinda ya faru nan take ya kori jami’an tsaron tare da zazzagin su domin shi _ babban police ne, nan take suka bar gurin-a‘” sukwane. Bai ce da su komai ba ya barsu a gurin yai wucewar sa, nan fa Alh. Jafar ya shiga yi masa masifa ta Kin Karawa. Ni ce na zo naja Mustapha ya shiga cikin gida da shi, nan Alh. Jafar ya shiga fadansa na borin kunya wanda yanayin haka ne don kawai ya Kona mana rai mu zama_.” abin tausayi, to kuma Allah Ya fishi. _
‘ Tsananin tsana da Kiyayya ‘su ne suka yi — mana yawa cikin ZURI’A dinmu, kowa ya yi baya damu, -baya son wata harka ta shiga
Tsakaninmu tsahar rashin son gaskiya da gudun kada Alh. Jafar ya juya musu baya. Don maganar gaskiya Alh. Jafar yana da tsananin tarin dukiya wanda Allah ne kawai Ya sani, domin cikin ganKanin lokaci Allah Ya wadata shi, don haka duk wani dan uwansa a jikinsa yake samu, . domin shi ne da kansa ya shiga nunawa cewa – yana son taimakawa kowa, don haka kowa sai ya raja’a da shi, domin yadda ya ajje kyashi yana taimakawa Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ya zamanto gaba daya zama na ya dawo wurin Mustapha, jifa-jifa nakan je can gidan amma ba wai don zuwan dadi ba sai don na kawar da gaba da aka dauka damu.
Sai dai wani abu da yafi daga mana hankali yadda Hameed ko da yaushe sai ya zo gidanmu yana roKon son ganin Aziza don ta yafe masa, amma ba ma barin ya ganta, domin itama ta Ki bari su hadu.
Tsananin ramar da yayi da nacin da yake nunawa hakan yasa tausayin sa ya fara shigar mu ni da Ammi ku, domin kallo daya zaka yi masa ka gano ba ya cikin kwanciyar hankali. Duk ya rame ya yi baKi, ya zamo baya iya komai, bashi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *