ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

              Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya
Sai dai wani abu da yafi daga mana hankali yadda Hameed ko da yaushe sai ya zo gidanmu yana roKon son ganin Aziza don ta yafe masa, amma ba ma barin ya ganta, domin itama ta Ki bari su hadu.
Tsananin ramar da yayi da nacin da yake nunawa hakan yasa tausayin sa ya fara shigar mu ni da Ammi ku, domin kallo daya zaka yi masa ka gano ba ya cikin kwanciyar hankali. Duk ya rame ya yi baKi, ya zamo baya iya komai, bashi

da wani buri da ya wuce ganin Aziza, amma ina! Baya samu, komai na rayuwar sa ya tsaya cak, ya daina yin komai, haka ya zamo abin tausayi tsabar tsananin damuwar da yake ciki. Ba don dokar da Mustapha ya samana ba da tuni mun bar Hameed sun hadu da Aziza, to . amma ya Zamu yi? Dole haka zai zo ya Karaci surutansa ‘da sambatunsa ya hakura ya tashigudun kada Abban ki ya dawo ya same shi. . Tun yana jin

tsoron dawowar sa ya same _ shi ya zamana sai ya dawo ya same shi anan, ~ amma. ba zai kula shi ba zai wucewar sa ya barshi, domin shima ya gaji da yi masa fadan ~ tsabar nacinsa.  Kusan kowacce. rana haka muke – kasancewa da shi don haka kullum cikin tausayin sa muke har ma muke kamar zamu manta da tabon da ya yi mana. Yau kwana biyu bamu ji duriyar sa ba, “haka muka fara tunanin cewa ko ya gaji ya hakura ne. ‘ ” Ranar wata Lahadi ne zaune muke a falo muna hira dukkanin mu mun sa Aziza a gaba muna ta yi mata hira da bata labarin tarihi da duk Www.bankinhausanovels.com.ng
don mu kawo farin ciki cikin rayuwarta, domin har yanzu bata gano cewa ba ita kadai bace, mun kuma kasa fada.mata abin da take tare da shi, domin gudun abin da zai iya ta da mata da hankali, domin zuciyarta ta dan tabu saboda damuwar abin da ya faru da ita a baya. –
Sallamar Haj. Asiya muka ji, cikin mamaki muka amsa mata sallamar, domin tun ranar da ta bar asibiti bamu Kara ganinta ba sai _yau, domin mun doshi wata biyu da dawowa amma bata taba zuwa ba sai yau. Cikin wani irin yanayi ta shigo mana, ni ta fara gaidawa sannan su. Guri na nuna mata ta zauna, haka ta zauna jiki ba Kwari.
Cikin sanyin jiki ta ce, “Umma da ke da su Abban Aziza ina neman alfarmar ku da ku saurare ni ku ji abin da zan ce da ku, tabbas nasan mun yi muku laifi, ko me kuka yi mana dai-dai ne, kuma ina jin haushin janye dangantakar da take tsakanin mu, amma da farko Abban yara ga wannan takardar ka fara dubawa don ka fuskanci wani abu”, Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan take ya karba ya duba, yarjejeniyr da Alh. Jafar da Alh. Aminu suka yi ne a rubuce na
cewa kada ya kuskura ya bari abin da Hameed ya fada masa na game da fyaden da ya yi, sun yi alKkawarin ba zai fada ba, nan take ya yi masa kyauta tare da sa hannun ya yarda ba zai bari . duniya taji ba. Sai ta biyu kuma Alh. aminu ya yi_ ‘ alKawarin raba dukkan wani dangantaka da zumunci da ke tsakenin su, nan ma sun yi a rabuce idan anyi nasara ga abinda za a bashi da kuma sa hannun sauran ‘yan uwa, duk wanda ya * janye alaKa da shi ga irin tagomashin da zai’ samu. Nan yaga sunan kowa; Alh. Habibu ne – kadai bai ga nasa ba. Yana gama dubawa ya yi murmushi ya yi mana bayanin komai, ya ce. “Haj. Asiya babu komai, yanayin rayuwa ne, kowa yaje ya yi abin da zai iya yi, lokaci ne, . don haka wannan ba wani sabon al’amari ne _ game da dan Adam. da yake rayuwa cikin – wannan Karnin”. – – _ Cikin kuka ta ce, “Abban yara don Allah . kayi haKuri ku yafewa Hameed laifin da ya yi muku, domin hakkin ku shi ne yake aiki akansa, domin har yanzu baya cikin nutsuwa, yau —
kwanansa uku gadon asibiti an rasa gano kansa,_. domin a yanzu haka ance mana ya gamu da hawan jini. Don Allah da Manzon Sa ina nema masa afuwar abin da ya yi muku ko zai samu sassauci cikin rayuwar sa”.
Cikin kakkausar murya muka ji ance, “Asiya! Da izinin wa kika shigo gidan nan? MatuKar na sake ganin Kafar ki a nan gidan to ranar aure na da ke ya Kare, zo ki fice ki koma gida”. Cewar Alh. Jafar. ,
Kai kuma na dawo gareka, ka sani matukar na rasa rayuwar dana akan ‘yarka to wallahi ka sani sai kotu ta shiga tsakanina da kai idan ma wani Kulumboto ku ka je ku ka yiwa yarona ku ka zautar min da shi a kan diyar ku to ko zan rasa Naira data to duk sai naga bayan ku, ku Kara sanin cewa idan na rasa rayuwar dana sai iya inda Karfina ya Kare akan ku”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mukhtar ne ya shigo a fusace domin ya ~ tsaya ya gama jin abin da yake fadi, cikin zafi ya,
“Kai Jafar me ka dauki kanka ne? Kuma da me kake taKama ne da zaka na yin abu son ranka ana Kyale ka? Ba fa tsoron ka ake ji ba ake
yin shiru! Zo ka fice ‘mana daga cikin gida domin nan ba ikon ka bane, idan kuma ka Ki yanzu nima na gwada maka rashin mutunci domin ba fa tsoron ka ake ji ba”. ‘ Cikin mamaki ya dubi Mukhtar yace, ‘ “Mukhtar ni ka ke fadawa haka?” so
“An fada maka din, ka dauki matakin da zaka dauka, bana shakkar hakan”.
Cikin tsawa na ce, “Mukhtar zaka ja bakin – ka kayi shiru ko sai na zo na saba. maka a gurin nan?”
“Umma to haka za mu tsaya yana ci mana – mutunci ana barinsa?”Ka rufe min baki na ce ko?”
Nan take ya yi shiru bai sake cewa dani _ komai ba, ya samu guri ya zauna.
Cikin fushi Alh. Jafar ya ce da Haj. Asiya. “Ke! Shige mu wuce”.
– °Sannan. ya juyo ya sake cewa, “Samun sauKin Hameed shi ne farin cikin ku a cikin estate din nan, matuKar ya rasa rayuwar sa za ku rasa farin ciki kuma”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana gama fadin haka ya juya ya tafi, Asiya ta bishi a baya. . Kwanan Hameed goma sha biyu a asibiti aka sallamo shi, a ranar da ya dawo a ranar ya sato jiki ya shigo gidanmu, duk wanda ya ga Hameed a lokacin sai ya tausaya masa, idan akwai mai saurin kuka to a take zai yi. masa kuka don tausaya masa. –
Ni ya fara gani a falo, da sauri na tashi na ce masa ya zO ya zauna ga guri, sannan na ce masa ya jiki? –
Nan take naga fara’ar sa, ya ce, “Jiki da sauki Granny, don Allah Granny wai me yasa kema ba kya tausayina ne? Ace har yanzu ba za ku yafe min ba? Kuma har na gama kwanaki na  a asibiti ba kuje duboya na ba. Granny ki tausaya min don Adlah, wallahi ni nasan irin abin da nake ji a raina na game da abinda na yiwa Aziza, wallahi na tuba kuma Sharrin zuciya ne ya kai ni aikata haka, amma yanzu nayi nadama na tuba, so nake ku yafe min ku da ita. A yanzu yadda nake ji bana jin zan iya dogon rayuwa idan bana tare da Aziza, tun da abin nan ya faru nake jin tsananin so da Kaunar ta suna shiga ta har nake jin idan na rasa ta gaba
’ daya na rasa rayuwata, domin a yanzu bani da wani buri da ya wuce ku yafe min, sannen kuma a zo a Shirya rabuwar da ZURI’A tayi gida biyu, wanda duk ni ne na janyo faruwar hakan, shi ne yasa har yanzu na kasa samun kwanciyar rai da hankali.
Granny nayi miki alKawari idan har kun yafe min to ni kuma zan bi hanyar da za a shirya a daina wannan zaman gabar”. Tausayi ya kama ni, ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, nayi sauri na tare, na ce. “
“Hameed ba mune muke zaman gaba da su ba, sune suke zaman gaba damu, don haka ni dai daga yau na yafe maka, na yarda Kaddara ce ta gifta, babu kuma wani Mumini da zai ce bai san Kaddara ba”.
Da sauri ya zo ya rungume ni yana kuka yana yi min godiya, sannan ya ce.
“Granny na.gode sosai, yau kin kawo farin ciki cikin rayuwata wanda tuni na manta da shi tun fatuwar al’amarin nan, don haka ki daure ki roKa min yafiya gurin Abba da Ammi da ita kanta Aziza, idan kika yi min haka kin gama yi
min komai a rayuwata tunda bani da wata (power) a gurin kowa da zai saurare ni sai ke, kuma sai gashi tunani na ya zama gaske”.Hameed nima na yafe maka a matsayina na mahaifiyar ku kai da Ammi”.
Daga ni har shi farin ciki ne ya kama mu jin muryar ammin ku, tare muka juyo muka ganta tsaye bayanmu tana share hawaye itama.__. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri yaje ya rike Kafarta yana kuka, ta shiga goge masa hawaye tana cewa.  “Babu komai, komai ya wuce, na yafe maka ne ba don komai ba sai don babu yadda za muyi da Kaddara, nasan cewa haka Allah Ya rubuto, tun ran gini tun ran zane, kuma Allah Yana tare da mai haKuri da yafiya, domin kuma a ceto ZURI’A DAYA daga rabuwar da tayi. Kaje na yafe maka duniya da lahira, sai dai ni a yanzu bani da damar da zan saka Aziza ta yafe maka sai abin da mahaifinta ya ce”. Cikin muryar kuka ya ce, “Ammi alamun nasara ne ya zo gare ni, tun da kun yafe min jikina ya bani Aziza da Abba suma za su yafe min”,
“Karya kake ni ba zan taba yafe maka ba Ya Hameed, domin ka cuci rayuwata, ka hana ni yin komai na rayuwata, ka hana ni hulda da ‘yan uwana da abokai na da karatuna, haka mutunci na, don haka banga abin da zaka yi min ba naga farin ka cikin rayuwata. Don haka ka zo ka fice ka bar mana gidanmu, domin na tsani ganin – fuskar ka anan wajen, kaje can ku Karata da iyayen ka marasa tausayi da rashin tsoron Allah. . Naji duk abinda suka yiwa Abba na, kuma insha Allah haka rayuwar ku zata Kare cikin rashin farin ciki da kuma nadama. Ka fice mana daga cikin gida, (please) bana son ganin fuskar ka, macuci, azzalumi”. Ta fada cikin daga ,murya, nan take ta fashe da kuka. Dai-dai lokacin da Abban ku ya shigo gidan ya jiyo tashin kukan Aziza, da sauri ya Karaso gurin, yana ganin mu tsaye sannan ya hango Hameed, nan take ya yi turus, ya ce.
“Kai, ya akai ka shigo min gida ba tare da .izini na ba? Maza zo ka fitar min daga cikin gida -tun kafin nayi Kasa-Kasa da kai”.
“Kana taba min dana kotu na raba ni da kai, daga fitowar sa? To kayi kadan”. .
‘Gaba dayan mu. muka juya bakin Kofar ‘falon, nan muka ga Alh. Jafar tsaye yana magana cikin Bacin rai. Nan ya Karaso ya riKe hannun Hameed ba tare da ya sake cewa komai ba! Cikin sauri Hameed ya fisge hannunsa ya ce, “Daddy ka barni, idan zan shekara anan gidan ba zan fita ba, gwara ka juya ka tafi, Duk. wannan bala’i da nake ciki kai ne ka jawo min, da ka barni da tun. farko da hakan bai faru da ni ba, amma ka Ki yarda na zamo mai laifi tunda kana ganin kudi ne-za su iya siyo min farinciki, (Please) ka tafi ka barni donna nemi yafiyar su, ba ruwanka da maganar da muke yi Hameed! Ni kake. fadawa haka? Kanaida hankali kuwa? Za ka wuce muje ko kana.son na bata, maka rai ne -yanzun nan?! Shiru ya yi baice-da shi komai ba sai ma ‘guri: daya samu ya zauna, nan fa ya rufe ido ya shiga yi masa masifa, mu kuwa gaba dayanma sama) muka-hau muka barsu gurin. Mun. dauki fiye da awa sannani muka sakko Kasan nan muka iske Hameed zaune gurin da muka barshi. Ke na taKaita miki haka muka Www.bankinhausanovels.com.ng
sha fama da Hameed ya fitar mana daga gida, a ranar har kakarsa sai da ta shigo don ta fita da shi amma yaki, duk surutun da tayi bai ce da ita komai ba, bai motsa ba. Sai da Haj. Asiya ta shigo, ita ce kawai tayi nasarar tafiya da shi.
Kai haka dai kullum Hameed yake mana, tum abin na batawa Abban ku rai har ya zo ya fara tausayin sa, ya fara sawa ransa cewa yaron nan da gaske yake yayi nadamar abin da yayi a — baya, domin kullum cikin kuka zai tare shi yana roKon sa ya yafe masa, Ranar dai ya bude baki da kansa ya ce ya yafe masa.”
Ranar da murna ya bar gidan domin ya sa ma ransa sai ya yi (free) da kowa sannan zai zo ya dai daita ZURI’A dinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba komai yasa Abban ku ya yafewa Hameed ba sai tsananin kaunar da yake masa a baya, ya ga kuma a gurinsa ya taso, ya girma, . don haka ya duba zumuncin baya da kuma . daukan Kaddara.
Tun lokacin da ya yi (free) da kowa a gidan illa dai Aziza, ba sa takun saKa domin idan ya shigo gidan zata haye sama ba zata sakko baya tafiya sai yaji ‘dawowar Abban ku sannan zai tafi gida. ‘ A hankali dai ya shiga KoKarin da zai sa . ya ga sun fara magana, har ya samu bakin da zai . iya neman afuwar ta, amma ina! kullum haka. Wata rana Aziza ta zo ta same ni ina kwance a daki na, ta ce.  “Granny ni fa wani motsine yake yawan . damuna a ciki na, wallahi wata rana idan naji motsin har.tsorata nake yi, sai naji kamar kayan _ cikina ne suke son za fu fito. Kai ni na kasa ma _gane yadda zan yi miki bayani”. “Nan take gabana ya fadi domin na san ba – _. motsin komai take ji ba sai na dan da yake – ~ cikinta, domin yau cikinta ya kai wata biyar ko shida.  ‘Hankalina ya yi mugun tashi, nan take na ce.“To ki bari Abban ki ya dawo saiki fada — masa, sai asan me za ayi miki”Ta yi-murmushi ta ce, “To Granny, Ammi _ -da na fada mata itama haka ta ce. Granny kuma _ba kya ganin yadda na koma, duk nayi fari na

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *