ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

murmushi ta ce,Ya Sameer ya gida?
Bai amsa mata ba ya shiga kura mata idanu
ganin irin kallon da yake mata yasa ta yi kasa da
idanunta don ba za ta iya jurewa ba.
Rauda me yasa ki kuka?
Ni ba kuka na yi ba.
To me nake gani a idanun ki?
Idona ke min ciwo.
“Ban yarda ba.”
Me yasa ba za ka yarda ba?
Saboda ba gaskiya ki ka fada min ba.'”
Ya a kai ka san ba gaskiya na fada maka ba
tare ka ke da ni ko yaya?
Rauda nine na saki kuka a kaina ki ka yi
kuka,
Dam! Ta ji gaban ta ya fadi ta yis saurin cire
kanta ta dube shi ta y1 ta kasa cewa komai zuwa
can ta ce, “A kan me zan yi kuka domin ka?”
Kwarai kuwa domn n1 wannan hawayen ke
fita saboda ki na sona.
Kallonsa ta yi Cikin jajayen idanunta da suka
rune da hawaye ta ce,Son ka fa ka ce waya fada
maka haka? Eh to ina Son ka a matsayin ka dan
uwana na jini mana.
Ba gaskiya ba ne bayan wannan son akwai
wani a Cikin zuCiyarki,.
“Please Ya Sameer ka bar ni na tafi abu na
bana son jin wadannan furucin na fitowa a bakin ka please na roke ka.
Dole ki ji, idan ba kya sona to ki kalli kwayar
idanuna ki ce min Sameer bana son ka hakan ne
kawai zai sa na yarda. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Sameer a 1na kaji wannan maganar da ka
ke tuhumata da ita, ban taba son ka da wata siga ba
sai ta dangantaka, idan kana wannan tunanin ma ka
bari Look! Rauda kada ki boye min komai na san
halin da ki ke ciki kuma insha Allah zan nemo
mafita.

Ya Sameer babu wata mafita da ta wuce ka
cire wannan tunanin a ranka na cewa ina sonka.
babu wannan tunanin a raina ko daya,
Rauda ki gama duk zagaye-zagayen ki da boye-
Boven ki ni dai na ce miki kina sona, tun lokacin da
na sani na dinga ganin alamun hakan a tare da ke
Yau da na ga irin rudanin da tashin hankalin da kike ciki yasa na fito na fada miki, ko za ki kara
samun nutsuwa tunda na sani.
Is over Ya Sameer sanin ka da rashin sanin ka
babu abin da za su magance min in ban da kara jefa
ni cikin matsala, don gwara kawai mu bar maganar
nan ka kuma yarda da abin da na fada maka.
Don ina son Haana ba shi ne zai hana ni na So
ki ba, tunda ba ciki daya ku ka fito ba, ‘yan uwa ne
masu son junansu, idan har son da ku ke yi wa juna Www.bankinhausanovels.com.ng
na gaskiya ne to me zai hana ku iya hada miji daya
ni dan uwanku ne dukkan mu ZURI’ A DAYA ne
Idan mun auri juna abin zai bada sha’awa da
burgewa
Ya Sameer tunda har mun kai ga haka bari na
fada maka gaskiya, kwarai da gaske da na so ka s0
mai tsanani amma a yau na nemi son ka a zuciyata
na rasa tun jin furucin ‘yar uwata a kanka.
Idan har ba ka son raba mana dangantaka da
KAUNARMU to don Allah mu ajiye wannan


maganar daga ní sai kai ni ce ma sO, kuma na
janye lokacin da nake cikin ciwon sonka har na
Jure ba ka sani ba, yanzu Allah ya kawo na ji na
janye to ina son mu bar maganar a nan cikin sirri
ka je ku ci gaba da soyayyarku kai da ita.
“Ba zan bari ba Rauda idan ke ba kya sona ni
kuma yanzu na fara nuna miki nawa son ku biyu
nake so kuma ku biyu zan aura babu wanda zai hana ni wannan burin nawa.Akwia shi kuwa Ya Sameer?
To waye ne?Ni ce.”Ke kuma?”
Eh.”Kan wane dalili bayan na san kuma kuna sona
za kuma ki yi farin ciki na kasance mijinki kamar
yadda ki ka dade cikin wannan mafarki.
Ya Sameer ai mafarki ba gaske ba ne duk
lokacin da ka ke yinsa a wannan lokacin yake zama
gaske da zarar ka farka ka ganka ido bude to ka san ba zai taba zama gaske ba, tunda da me din ba
gaske ba ne. To yanzu kasa a ranka na farko na
kuma manta tuni cewa na yi wannan mafarkın a
Cikin rayuwata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ya yi ya ce, Nice dialogue Rauda,
ashe kina dabaki haka ban sani ba,   mu
je zuwa da ke, kin gane ki je abin ki ki bar komai a
guri na kamar yadda ki ka ce take care of ur selt.
Yana gama fadin haka ya juya abinsa.
Kuka ne ya so cin karfinta ta yi kokarin
dannewa saboda kada ta shiga gida a gane wane
irin hali take ciki, shin wai me ke shirin faruwa da
ita ne? A ina Ya Sameer ya gane tana dauke da son
shi, bayan ta aJiye abin a zuciyarta babu wanda ta
fito ta fadawa, lallai dole ta san ta ya kai ya san
halin da take ciki har ya zo mata da wannan
maganar, kuma me yasa tuntuni da ya sani bai fada
mata ba sai yanzu da ya bari Haana ta furta cewa
tana son shi, shi ne zai ce haka, ko dai so yake ya
kulla gaba a tsakaninmu? To ba zai yiwu ba babu
yadda za ta bari haka ya taba faruwa da ita da ‘yar
uwarta. Da wannan zancen zucin ta ta samu ta shige
cikin gida tana ta tufka da warwarewa.
Haana zaune a dakinta ita kadai tana mamakin
yadda take jin son Mr. Sameer yana shigarta a
hankali wai ita yau ta ji zuciyarta tana son wani da namiji ba Malam M.J dinta ba ashe wannan rana kake so a rayuwarka ka ke samu ba.
Malam M.J me yasa ka yi min haka ka bari ka
ki dawowa cikin rayuwata har zuciyata ta samu
damar da za ta so wani ba kai ba, ba ka yi min
adalci ba. Da ka san ba za ka so ni ba da ba haka zo
cikin duniyata har na saba da kai ba, da ban bari ka
shigo rayuwa ta ba har na ji zuciyata ta shaku da
kai haka.
Malam M.J har yanzu ina jin ka cikin ZUCIYA
DA RUHI na har yanzu ka kasa fita sai dai zan yi
duk yadda zan yi na ga na cire ka a cikin tunanina
tunda na fara son wani wanda ban so haka ta
kasance da ni ba
Nan wasu hawaye masu dumi suka wanke mata
fuska ba ta sa hannu ta goge su ba ta bar su suna ta
Zuba kO ta samu ta ji saukin radadi da KUNAR
ZUCIN da take ji
A can bangare daya kuwa Mama Bara’atu ce ta
zo Kano daga Abuja, don amsa kiran da kannenta
sukayi mata wato Abba da Alhaji Hamza kuma da
tata danmuwar da take da ita tafiyayya, domin
kullum cikin damuwa take na autarta Nabeela na
dage mata da take ita idan ba ta auri Ya
Muhammad ba za ta taba auran wani ba ko za,A
kashe ta ba za ta yi aure ba idan ba shi ba.
Suna cikin wannan rikicin nata ne ta samu
kiran da kannenta suka yi mata Mustapha da
Hamza wanda ya yi da1dai da irin matsalar wanda
dama tuni take da burin fitowa da batun a dawo da
auren dangi don kawai ta ga diyarta ta samu abin
da take so. Www.bankinhausanovels.com.ng
To fa anya kuwa ba wata matsala ce za ta kara
faruwa cikin ZURI’ A DAYA din nan ba? Ina
dokokin cikin ta na hana yara soyayya da junansu,
1na sharadi na nuna son kat ga dan cikin mutum?
Dama dai wasu dalilai da aka gindaya cikinsu to
dai ga wasu iyaye nan suna son bin son ran yaransu
bayan haka yana cikin doka ta ZURI’
A din. To mu
je zuwa kuna dai tare da gwanar taku SA ADATU
WAZIRI GOMBE a sannu za ta warware komai
Tare da Fadila suka zo da direbansu da alama
zaman za su yi shi ne cikin sirri ta karkashin kasa,
domin a gidansu Haana suka shirya yin taron ba
tare da kowa ya sani ba.
Zaune suke a falon da ya kasance don irin
wannan zama na sirri, Mama Bara (Kamar yadda
duk Zuir’a din kowa ke kiranta yara da manya da
Yake ita ce babba kaf cikin zurT a din) ne zaune
Gefenta ga Alh. Hamza sai Abba a daya bangaren
duk sun sa ta a tsakiya.
Bayan sun gaisa sun dan yi raha ta ‘yan uwan
juna Alh. Hamza ya ce, *Mama Bara kamar yadda
ki ka ji bayanin da na fara yi miki a waya yasa na
ce mu ne za mu zo ko ke ce za ki zo to ga shi kuma
Allah ya kawo ki don haka ga Yaya Mustapha nan
zai miki bayanin komai.
Murmushi ta yi ta ce, “Masha Allah babu damuwa sai mu bude taro da addu a don Allah ya
albarkaci zaman da za mu yi.
Bayan sun bude taro da addu’a Abba ya fara da
cewa. Na ji dadi zuwan wannan rana da ta jima
tana damuna tun bayan daidaituwar wannan
al amarin a baya. Bayan wasu sharadi da dokoki da
aka kafa a cikin zuri’a din nan na hana auren
DANGIN JUNA a wancan lokacin ni kaina na so
na nuna rashin amincewar, to amma jin dadi da
manta abin da ya faru ganin mun dawo mun hade
guri daya yasa na manta da wani alkawari da
kuduri da yake a zuciyata da muka gama ajiyewa
ni da Umma. Ganin a wancen lokacin da akayi
wancen zaman ku biyu ne kawai ku ka ki goyon
baya, da abindaya faru shi yasa nima ban goyi bayan Www.bankinhausanovels.com.ng
ku ba: Hakan ya sa na fara yanke shawarar na fara
tunkarar ku da wannan zancen don ku bani
Shawarar yadda zan yi, saboda kar a sake samun
wata matsalar ace kuma nine sila, shi yasa na fara
Zuwar muku da ita don a san yadda za’a duba
maganar.
Maganar kuma ba wata ba ce illa tun bayan
lokacin da muka rabu da ku ni da Umma muka
dauki aniyar hada auren Mustaplha karami da
kanwarsa Ammina. Da na so tun a ranar na fito da
maganar, to amma ganin yadda gida ya rabu biyu
ya sa na barta zuwa wani lokacin. To kuma yanzu
ne naga lokaci ya yi, amma fa shawarar ku nake so
ta tsakani da Allah matukar ba zan zamo mai laifi
ba ace na shigo da wata matsala cikin Zuri’a ba. To
1dan har ana ganin akwai wata matsala tun kafin
maganar ta fito fili ina so ku bani shawara sai mu
maganceta a nan, tunda duk cikinsu babu wanda ya
sani, burin mu ne da tunanin mu wanda idan muka
yi hakan za mu tsinci farin ciki a nan gaba.
Don haka ina son shwarar ku, ya ku ke gani?,
saboda ba na son ko da nan gaba wani abu ya faru
ace ni ne silar sa cikin Zuri ata. Yanzu ku fada min
abin da ku ke ganin ya dace, duk tsaurina ku fada
min don ba na son yin abu kai tsaye aje kuma nan
gaba ace ban kyauta ba .
Gaba dayansu sun yi shiru. Bayan sun gama
sauraren abin da ya ke fada musu, Mama Bara ta
muskuta ta ce.
Gaskiya ne Mustapha ka yi kyan kai da kuma hangen nesa
Wannan haka ya ke Mama Bara. Cewar Alh
Hamza, sannan ya cigaba da cewa.”Har ku’llum
dan Adam kamata ya yi duk abin da zai yi tunini to
yayi tunanin positive (kyau) ba wai ka dinga
Zartarwa kan ka da sabanin hakan ba. Dukkan mu
musulmai ne kuma ZURI’A DAYA, babu wanda
bai rayu cikin bakin ciki ba da faruwar wancen
al’amarin da suka wuce a wadancan shekarun na
baya.
Idan har abin da ya faru a baya za mu kira shi
da sakaci. to yanzu kuma sai mu dauki aya kowa ya
dinga dora idanu akan ‘ya’yansa, amma wai mu
dauki abin da ba Allah ne ya hana ba mu daukarwa
kan mu. Abin da ya faru a baya dama can kaddarar
hakan za ta faru a cikin littafin mu an rubuta shi.
Ni dai har yanzu ina goyon baya da a baiwa
yaro ko yarinyar da duk suke cikin Zuri’a dinnan
damar duk wanda suke son juna, koma dai ya ya ne
mu duba mu gani matukar bai sabawa Allah (s.w.a)
ba, to banga wani abu na aibu ba. Ku ma ni dai na
goyi bayan wannan maganar . sai dai kuma
ban san abin da Mama Bara za ta ce ba
Gyara zama ta yi sannan ta ce. “Ni ce: kuwa na
ke da abin cewa, har gobe nima ina kan nawa
batun, kuma ni da Alh Ja afar mun jima da wannan
maganar tun Fadilah na wajensa na ce masa mu
hada aurenta da Muhammad tunda waje daya suka
taso. ga kuma shakuwa da suka yi da jlina, na ce
masa idan muka yi hakan za mu haskawa sauran
yan uwa da su hada auren suma da sauran ya’ yan
su kamar yadda mu ma muka taso aka yi mana
Taurin kan da ya nuna min a kin amincewa Www.bankinhausanovels.com.ng
shi ya sa na barshi, sai kuma ga sh1 yanzu yara
suna sOn junan su, tunda duk tunaninSu ai ZURI’A DAYA suke komai zal warware, sai kuma ga shi an zo an kara sa doka a kai, wanda hakan bai yi musu dadi ba.
Har yanzu Fadilah cikin damuwa ta ke da kuka.
ta ma ki tsayawa ta kula kowa balle ma har ta basu dama su turo da magabatansu, wai ita ba za ta auri
kowa ba idan ba Yayanta Muhammad ba. Wannan
tashin hankalin da muke ciki ya fi komai daga min
hankali fiye da koma1, hakan ta sa tun farkon
zaman na ki na amince da auren zumuncin, saboda
ba kowa za mu jefa cikin damuwa ba sai
ya yanmu, nasan kuma 1dan yaranmu suna cikin
damuwa to kuwa mu ma namu hankalın ba zai
taba kwanciya ba
Alh Hamza ne ya karba da cewa. “Duk na ji
bayanin kowa, kuma na gamsu, mafita dai yanzu a
garemu 1ta ce. Dole ne mu tara kowa cikin Zuri’a
dinmu mu kuma sanar da su cewa
mun janye
ra ayinmu na hana auren zumunci domin nemawa
kan mu mafita. Saboda muna da yara maza da mata
wanda idan har muka bar su a hakan za mu jefa kan
mu Cikin matsala, saboda za su fara zuwa kuma
Suna sOyayya a boye ba tare da mun sani ba, daga
Daya kUma mu gane wanda kuma idan za mu raba
Su sai kOwa ya shiga damuwa.
Mama ke da Yaya Ja afar ku ne manyan mu, ba
mu isa mu hana ku abin da ku ka so yi ba, tunda
bai sabawa addinin mu ba, don haka ku ne ku ke da
dama da za ku fito ku yaki wannan kirkirarriyar
al’adar da aka gadar wa wannan Zuri’a ta karfi da
yaji dole ne kowa kuma ya bi.
Idan kun yi haka to shi ma Yaya Mustapha sai
ya fito da nasa kudirin. Ina ganin wannan ita ce
mafitar da za mu warware wannan kullin babu
tsoro kuma babu son rai. Idan har muka bayyana
musu wannan nasan kowa zai gamsu
Nan Abba ya ce. Wannan maganar taka ta
karbu, tunda dama ga shi wannan satin ma muke sa
ran dawowar shi Yaya Ja’afar din da ta shi Zuri’ ar
nan Nijeriya. Duk da dai ya ce ba wai zai dawo
gaba daya ba ne, amma za su yi matukar dadewa
kafin su koma, ka ga kenan idan sun zo sai a yi
zaman baki daya
Sun karasa tattaunawar su tare da tsayar da
matsaya kan abin da za su gudanar. Zuciyar Mama
Bara fari tas don diyarta za ta samu nasarar samun
abin da ta ke so, sai dai nmatsalarta Yaya Ja afar, to Www.bankinhausanovels.com.ng
amma dole ya yi mata abin da take so tunda ita ce
gaba da shi. Idan har da ta yi masa abin da ya ke
so, to wannan lokacin shi ma dole ya yi mata abin
da take so.
Fadilah ce ta fado jikin Mamanta tana murnar
Jin abin da ta fada mata, nan ta ji zuciyarta ta yi
sanyi saboda za ta samu abin da ta ke so. Ta sani
sarai ba wai karbuwa ta wani samu a wajensa ba,
amma dai matukar Mama ta yi magana dole ne a
yarda a aura mata sh1
Mama na gode, Allah ya baki abin da ki ke so
duniya da lahira na j1 dadi sOsai, su ma su kawu
Hamza da Kawu Abba Allah ya saka mu su
Murmushi Mama Bara ta yi tace “Fadilah idan
ban yi miki abin da ki ke so ba Wa zan yiwa?, sanin
kanki ne ina son na ganki cikin farin ciki, don haka
aurenki da Muham
mad kamar anyi an gama.
Wannan karon ba zan bar ubansa ya juyani ba,
babu mai hana auren nan matukar ina raye
To Mama idan kuma Ya Muhammad din ya
ce ba zai aureni ba fa?.
Fadilalh ki kwantar da hankalin ki, Muhammad
ba shi ne matsalar mu ba, ubansa shi ne matsala.
Kaf cikin Zuri’armu ba mu da kamarsa wajen
taurin kai, amma yanzu tunda ina da mataimaka
insha Allah za mu yi nasara a kansa
Cikin murna ta sake Tungume mahaifiyar ta ta.
Na gode Mama da son sani farin ciki
Suna cikin haka sai ga Haj Babba ta shigo
dakin, ta samu waje ta zauna. Nan Mama Bara ta
fada mata yadda suka yi, itama ta yi murna sOsai,
saboda ta fi kowa son ganin an hada auren don
wannan shi ne tsohon burinta. Nan suka shiga
shirya yadda za su bullowa da al’amarin idan sun
dawo.
Mama Bara’atu macece mai zafi da kuma
takama da kuma rashin son daukar raini. Kaf a
Cikinsu ita ce Babba babu wanda ya ke tsallake duk
abin da ta gindaya sai kaninta wanda ya ke binta
wato Alh Ja’afar. Gogaggiyar mace ce kuma
ma’ aikaciya ce babba a CBN na cikin garin Abuja,
ita da mijinta da kuma yaranta duk a can suke.
Fadilah ce auta cikin yaranta mata, Www.bankinhausanovels.com.ng
kannenta maza guda uku, ta na da yayye biyar,
maza biyu mata uku, duk kuma sun yi aure a can
Abuja din. Ta na da matukar burin ganin cikin
ya yanta an samu wanda ya auri wani daga cikin
ya yan dan uwanta, wannan ne ma ya sa ta tura
Fadilah karatu can gidansa da ya ke London tun
bayan hada karatun ta na Secondry.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *