ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
ta dauke ni mai son kansa da kuma rashin tausaya
mata kan halin da ta ke ciki. Nasan ba za ta ki abin
da ku ka sanyata ba, sai dai za’a tauye mata
hakkinta na aura mata wanda bashi ta ke soba. Ni kuma Www.bankinhausanovels.com.ng
burina naga ta samu farin ciki dauwamamme a
cikin rayuwarta, don Allah Abba ku fahimci
manufata, ba wai kawai son raina ne na ki
amincewa da abin da ku ke so ba sai dai don ni din
ni kadai ne abokin shawarar Amminka, ba don
sanin abin da ta ke so ba da tuni na amince kun
yanke hukuncin komai. Don haka Abba ina
rokonka da ka bar Amminka ta auri wanda ta ke sO,
ni kuma ka nemo min duk wacce ka ga ta dace da
ni don kasan cewar ba ni da wani zabi da ya wuce
naku, kuma wallahi zan riketa tsakani da Allah. ba
za ka sameni da saba muku ba, fatana dai na ga
Haana ta na cikin farin ciki.
Jikin Abba ya yi sanyi, nan take ya ji ya sauke
duk makamansa da duk wani fishi da ya ke dauke
da shi na Abban, ya kuma yaba masa Cikin ransa,
ya tabbatar da gaske ya ke ya na kaunar farin cikin
yar uwar tasa, ko kadan ransa ba zai so ace ba shi
ne mijinta ba, to amma ya zai yi idan haka Allah ya
tsara dole ba yadda zai yi tunda ma su magana sunce “Matar mutum kabarinsa
Nan Abba ya ce.Shikenan Mustapha na
fahimceka na kuma hangi abin da ka ke dubawa,
duk yadda muka so hada aurenku idan Allah bai
yarda ba babu yadda za mu yi. Allah ya yi maka
albarka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Naso na takuraka ka yi min abin da nake so, to
amma ka haska min abubuwa da dama wanda sai
yanzu na sake tunani akan su, na ji zan nema maka
aure da hannuna tunda ka rasa ‘yar uwarka yar
uwarka za ka aura yar wajen Yaya Ja afar, yau zan
kira shi a waya na ji ko ya yi mata miji duk da dai
bai san wannan kudirin namu ba.
Kanwarka ce, sunan Haj Babba ta ci, nasan ka
Santa tun tana yarinya zuwan da na yi kwanaki na
ganta, kasan lokacin da suka zo Nijeriya bai zo da
manyan ya’ yansa ba, shi yasa ba ka ganta ba, to
amma insha Allah babu abin da zai gagara, ka bani
lokaci zan ne me ka kan wannan maganar
Sai yanzu Granny ta samu abin cewa. “Gaskiya
idan ku ka yi hakan ya yi kyau, dole ne ku dawo da
auren zumunci a Zuri’ar nan ta mu, ta haka ne
zuciyoyinmu za su manta da abin da ya faru a
shekarun baya.
Kai kuma Mustapha karami Allah ya yi maka
albarka ya kuma faranta maka duniya da lahira
tunda har ka sadaukar da farin cikin ka ga yar
uwarka, lallai wannan shi ne zumunci na gaskiya,
kai ma Allah ya baka yaran da za su yi maka
biyayya sama da wacce ka yi
Abba ne ya amsa da Ameen Umma, insha
Allah cikin Zuri’ar mu ba tababbe albarkar
sayyaduna rasulillahi (s.a.w
Granny da Ya Abba suka amsa suma da
da Ameen ya Allah
Sannan Abba ya ce zan je na samu su Hamza
da wannan bayanin yadda muka tattauna da su sai
mu nemi Haj Bara mu fada mata, ko kuma mu jira
zuwa gobe ta zo tunda dama goben ne zuwan nasu
Granny ce ta ce. “Babu laifi, Allah ya baku Www.bankinhausanovels.com.ng
ladan kokarin daidaita wannan zumunci da ku ka
yi, Allah kuma ya albarkaci gabanku da bayanku.
Washe gari karfe sha daya motar su Mama
Bara ta karaso cikin Dan fillo Estate, yau ma da
Fadilah aka zo da kuma kaninta Muftahu su ne
yan rakiyar tata. Fadilah ta fi kowa dokin wannan
tafiyar zuwa Kano saboda burinta ya kusa cika don
a nan ne za ta samu tabbacin za ta samu Ya
Muhammad dinta ko kuma a’a.
Amma irin maganganun da Mamanta ta yi mata
na kwantar da rai tare da sanya rai, sai ta fara
hangen irin zaman farin cikin da za ta yi a gidansa,
tasan dai ba ta da wata matsala idan ta samu Ya
Muhammad dinta a matsayin mijinta don tana
ganin matan duniya ma kamar rakota suka yi don a
wajenta ba karamin dace bane da rabo samun mijin
aure irin Yaya Muhammad dinta.
Tun daga zuwansu yan mata da samarin
Zuri’ arsu suka dinga fitowa daga gidajensu don
zuwa su gaida Mama Bara duk da fadan da take da
shi kuwa, don akwai ta da son jama a kowa natane
a cikin family din, sai dai haka Allah ya yi ta da
zafi, idan ma ta ji ance ka zo kuma ba ka gaida ta
ba da kanta za ta zo gidanku ta yi maka fada,
domin ba wanda ba ta rike sunan sa a cikn
Zuri’arsu ba, babba da karami.
Duk kuma wanda ba ta gani ba sai ta tambaya.
Mama Bara kenan, akwai kokarin wannan wajen
Son yan uwanta da yaransu, shi yasa duk cikinsu
babu mai tsallake maganarta idan ka cire Alh
Ja’afar, da shi kawai suke musayar yawu.
Haana tare da Rauda tare suka shigo gidan
kakannin na su, Fadilah na ganin su ta zo ta yi
saurin rungume su, tunda suka saba ta daina yi
musu wulakancinta kamar dama can sun saba tun
Suna yara tare suka taso.
Fadilah tana matukar Son Haana saboda
kawancensu ma ya fi karfi da ita, sai dai duk da
hakan ma ba laifi suna yi da Rauda, don duk
lokacin da suka zo Kano suna tare da juna da ya ke
sa anni ne, sai dai Fadilah ta dan fisu da kadan.
Suna gaisawa da Mama Bara suka mike suka
nuti bangarensu inda Mama Bara ta ke sauka 1dan
ta zo. cikin murna da doki suke zaune Fadliah ce ta
fara magana ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana da Rauda ku tayani farin ciki zan samu
abin da nake so daga yau zuwa gobeYaya
Muhammad zai zamo nawa, burina da farin Cikina
sun kusa samuwa, don Mama ta gama tabbatar
min da cewa an ma gama hada auren mu kawai,
kuma daga kan mu auren zumunci zai dawo. Na fi
kowa farin ciki a wannan rana.
Haana ce ta fara magana da cewa. “Na tayaki
farin ciki ‘yar uwa da samun abin da ki ke so, sai
dai ni ko kadan ban san akwai wata doka da ta
hana auren zumunci ba, na jima da son wani cikin
Zuri’ata ban kuma same shi ba har na hakura, sai
kuma ga shi wani daga cikin Zuri a din tawa dai
ina so Zan aura. To amma yanzu idan sauran 1yayen
mu suka hana fa?
Haana ba za su hana ba, saboda Mama ta
karfafa min abin haka Abbanku da kawu Hamza
sun kyamaci abin. Wannan taron da za’ a yii za’a
tattauna maganar soke dokar auren zumuncin ne,
kuma dole za Su yi nasara
To Allah ya sanya a yi din, idan an yi ba mu
da matsala, idan ma kuma ba’a yi ba, muna dai
cikin Zuri’ar”.
Haana za mu yi nasara, saboda jikina yana
bani hakan, kuma Mama ta dada karfafa min guiwa
zan samu abin da nake so ko da Ya Muhammad bai
sani ba. Idan har ya areni zan fi kowa farin ciki
saboda irin son da nake masa
Sai yanzu Rauda sanu damar cewa wani
abu. Fadilah kina son ce min Ya Muhammad ba
son ki ya ke ba, kece ke son shi kawai?.
Kwarai kuwa ada, kusan hakan ne, saboda
Son da nake ma Ya Muhammad ko rabinsa ba ya
min, anmma ni ban damu ba. idan har zai aureni zan
jure duk abin da zai min
Rauda ba za ki gane irin son da nake masa ba,
Ya Muhammad daban ya ke cikin maza, mutum ne
mai tsada, life style dinsa da kuma Atitude dinsa
abin so ne ga kOwace mace, tabbas duk mace za ta
So ta samu irinsa. Da shi na girma, ban kuma san so
ba sai a kanshi, ban taba duban wani da namiji ba
sai shi.
Ba na iya boye masa son da nake masa a gaban
kowa ma nuna shi nake kaf family dinmu ba wanda
bai san ina son shi ba, amma shi ko a jikinsa, 1dan
Tada masa ya maganar aurenmu sai ya ce min
shi ba wannan batun bai son abin da zai janyo
matsala cikin Zuri’armu, idan har dangi sun yarda
da aurenmu to shi ba shi da matsala. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abin da na fuskanta da shi, ya fadi hakan ne
don yasan ba za’a bari ba, babu irin yadda banyi da
shi ba kan ya fadawa Daddy (Alh Ja’afar) cewa ni
yake so saboda shi ne matsalar. Daga karshe ne da
na gama karatuna ya ce tun da ba mu yi nasara ba
mu hakura kawai, shi ya ma samo wacce yake so
kuma ‘yar Nijeriya ce.
Kar ku so kuga yadda hankalina ya tashi, na yi
kuka na yi magiyar duk amma a banza. Dole na
hakura na baro gidansu na dawo gida, a kullum
burina mu yi nasara ammma ban samu ba sai yanzu.
Sunanku iri daya da yarinyar Raihanatu, na tsani
mai sunan ma, da na ganki ne na fara jin ina son
sunan dole na daina kyamatar sunan saboda ke. ta
karasa maganar ta na dariya.
Haana tace Lallai Fadilah kina da kishi na
tsiya, wato da har kin daina son mai sunana, ai
kuwa yanzu dole ki so tunda gani. Itama ta karasa
fada tana dariya.
Yar uwa ban san wane irin masifaffen kishi
ne da ni ba akan Ya Muhammad, zan iya batawa da
kowa shi yasa kOwa yake baya da shi don ba zan
iya barwa ko ma wace ba”.
Rauda ce ta dora da “Fadilah na tausaya miki,
saboda irin wannan son da ki ke akwai matsala, ni
kaina na fada cikinsa dakyar na samu na fito. Zan
tayaki da addu’a Allah ya baki Ya Muhammad.
Amma akwai shawara, ki dinga addu’a sannan
ki dinga halartowa kanki za ki iya samunsa kuma
Za ki Iya rasa shi, Wannan tunanin shi zai kawo
miki sauki idan har an samu wata matsala nan gaba
Rauda na gode, ki sanya ni a addu’a insha
Allah Ya Muhammad mijina ne, na ji hakan a
jikina
Haana ce taa kalli Rauda ta ce. “Sister wa ki ke
so amma ba ki taba fada min ba?. Rauda ta mayar
mata da AI ya wuce tuni har ya samu wata nima
na samu wani
Nan ta yi dariya ta ce Abduljalal kenan,
wallahi ina sonki da guy dinnan saboda ya yi.
Allah ya rabaki da tention din family, ni fa idan
ban samu M.r. Sameer ba ba wani tashin hankali
saboda kafin shi mutum biyu na rasa masu
muhimmanci a rayuwata, 1dan da sabo na saba, na
So kuma na rasa.
Fadeelah ta ce, Haana za ki sanmu ya Sameer,
shi ma ya na da kirki zai so ki ya baki farin ciki
Yau alhamis ita ce ranar da zuri’ar Nasir Dan
fillo ta tashi cikin farin ciki, don yau ne Babban
uba a Zuri’arsu ya dira a Najeriya tare da zuri arsa
sai yara biyu da ya bari a can, manyan Www.bankinhausanovels.com.ng
yaransa Muhammad da Abdulrahim wanda su daga
baya za su taho. Wannan zuwan da ya yi zal yi
matukar dadewa kafin ya koma, saboda zai aurar
da yaransa kamar yadda ya kudurta a ransa.
Haka Zuri’ar su ka cika da murna, iyaye na yi
yara ma na yi, ko wane gida ka shiga akwai inrin
tanadin da su ka yiwa bakin. hakan ya nuna Zuri ar
Su na matukar kaunar junansu. Duk cikinsu babu
Wanda ya ke cikin damuwa sai Fadilalh da ta samu
labarin rashin zuwan gwarzOnta Mulhammad a
wajen’yar uwarsa Haaya, duk sai ta JI dokn
Zuwansu bai wani burgcta ba.
Rauda da Haana su ne masu tausarta a kan
damuwar da ta shiga tun da an Ce zai z0 daga baya.
da kyar suka samu su ka shawo kanta ta daina
fushin, daga cikin daki su ka jiyo sowar yara na
murnar zuwansu, da sauri Fadilah ta mike ta ce
Haana da Rauda ku mu je ga ‘yar uwarmu Haaya
nan ta zo.
Cikin murna su ka rufa mata baya, su na fitowa
ba su tsaya ba sai waje, jerin motoci ne da aka je
tararsu, murna da doki suka cika zuciyar Haana,
yadda duk zuri ar su ka fito kowa fuskarsa dauke
da annurin ganin ZUwansu. Cikin zuciyarta ta ce,
Allah na gode maka da wannan tarin farin cikin da
ban taba tunaninsa a rayuwata ba, wai yau
ZURI’A DAYA ta hadu guri guda, kowa na farin
ciki da juna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tayi aune ba taji tunanin Malam M.J ya zo
mata na sakon da ya tura mata.
Ina mai i maki fatan alheri a dukkan
al’amuran rayuwarki, sai dai na ji haushi da na tafi
ba tare da na hadaki da zuri arku da ku da kika rasa ba,
amma insha Ailahu Allah zai kawo maki wani
cikin rayuwarki wanda zai taimaka miki don
Cikar burinki.
Mun hadu a littafi na hudu,
Taku har kullum
Sa ‘adatu Waziri Gombe.